Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tana fita a ɗakin don xuwa wurin lauwalin da kafa gidan maganar tane kaɗai yake ji, acikin sassanyar muryanta wanda ya qara sanyi fiye da da ta nufo shi tare da faɗin. "Haba lawan ayi haquri haka nan mana kowanne bawa yana da nashi irin kaɗɗarar, ita kuma nata a haka yazo mata, idan har wannan aure shine mafi Alkhairinta to Ubangijii ya tabbatar mana shi da Alkhairi!" Ganin ita ma umman yau tanason ta ɓata masa raine yasa yace mata. "Taya auren Iliya zai zama Alkhairi umma?, bayan kinsan irin abubuwan da yake aikatawa na rantse idan da wanda ya isa ya ɗaura auren Nan shege nake, idan kuwa anyi to na rantse niba ƊAN HALAK bane SHEGE ne" Fuuuuuuuuuuuu ya fice a gidan yana fita kuwa yaransa suka rufa mishi baya. ************ Zaune yake gaban ummiensa cikin tattara dukkan nutsuwarsa zuwa ga mahaifiyar nashi yace. "Ummie wannan shine kaɗai alfarmar da zakimin!, kana kamar yadda na faɗa miki haka nakeson abun ya kasance, kuma Ni da kaina zance wurin baba hashimun na sanar dashi!" Cikin wani irin yanayi ummien ta kalla tilon yaron nata, kana tace. "ABDULJALAAL kana ganin babu wata matsala kuwa, idan har muka ɓullo ta wannan al'amarin!?" Ta qare zancen tana jin tamkar hakan baiyi mata ba, cikin tabbatar wa yace mata. "Idan harba ta wannan hanyar ba to kuwa bazan taɓa samun cikin muradina ummienaaaa" Yaja sunan nata, cikin yarda tace na amince maka ABDULJALAAL" Cike da tsananin farin ciki marar misaltawa ya rubgume mahaifiyar nashi tare da cewa. "Na gode ummiena Ubangijii ya biya ki da gidan aljannatul Firdausi!" *********** BAUCHI ************ Wasu dattijai ne tsaye cikin wasu irin koɗadɗun kaya, wanda kallo ɗaya zaka musu kasan cewa talauci ya samu wurin zama a jikinsu, amma ga mai cikakken hankali kuma kallo ɗaya zaiyi musu yasan cewa dattijaine masu daraja, dattako, nagarta. A guje yaron da suka aika dan yimusu iso da alh ya zuro tare dace musu. "Wai yace yana zuwa" Sallamar yaron sunkayi da wata koɗaɗɗiyar Murtala data gama koɗewa matuƙa. Babu jimawa kuwa Alh Yusuf mai kaba ya iso yana wani ɗage kai sama , shiga tunda wannan ɗan kut bazan dai qarisa ba dai🙀😍 ya faɗa masa zancen auren Nan yakejin bala'i dama kowa ye, kuma yariga yayi alqawarin cewa wannan karon kammm ko waye yazo da buqatar, naiman auren MARYAMU to tabbas kuwa zai bada. (Tofa wannan shine ana wata ga wata🙀🙀 kome ke shirin faruwa haka ohooo) Cikin daraja shi suka shiga gaidashi tare da faɗa masa akan maganar data kawo su, na naimawa ɗansu alfarmarta naiman auren ƴarsa LAYLAH. Aikuwa babu binciken komi yace ya basu a turo, cike da mamakin wasu iyayen masu hali irin na Alh Yusuf suke kallon sa. Cike da matsanancin tsoro Iliya shola Ameobi ke kallon su lauwali, domin yasan karon ba daɗi. Wani irin shegen kallo da lauwali ya wurga masa ne yasa shi qara mannewa guri ɗaya, shi kuwa yaya lauwali cike da tacewa a rashin mutunci, ya sake dubun iliya shola Ameobi yace. "Mene nace maka wato duk abinda na maka a banza kenan baka janye batun auren ƙanwas ba ko?" Cikin tuno irin baƙar izayar da yasha a wancen loqacin ne yasa Iliyan wani irin zazzaro idanunsa waje, tare da fara magana cikin kiɗima haɗi da tsoro yace. "Na ranshe da Allah na janye, daba ai na faɗa maka ita ladiyon ai itace ta bani kuɗi tace in aureta, kuma tun ranar da da kabani kashedin nan nace wa babanku na fasa auren ƴarsan!" Ya faɗi maganar yana sauƙe ajiyar zuciya don ganin kamar ya tsira. Shi kuwa lauwali wani irin murmushin mugunta ya jefa ilya dashi tare da faɗin. "Duk da haka sai an ɗan baka sadaka" Gaf ya buga kan iliya da jikin bishiyar da suke tsaye, yaja tawagarsa suka qara gaba. *JALAAL* Zaune yake akan ɗaya daga cikin lumtsuna lumtsuman kujerun office ɗin sa, cike da zallar farin ciki yake gudanar da ayyukansa cikin nishaɗi, domin tunda baffanninsa suka shaida mashi cewar lallei mahaifin yarinyar ya amince da batun auren su, da gaba ɗaya RAYUWAR yakejin kansa cikin wani irin matsanancin farin ciki, haɗi da jin wata irin nutsuwar da hakima baiji irin taba. Yana a wannan yanayin ne kuma ya jiyo qarar wayarsa, cike da shauƙi ya janyo wayar nashi, yana mannata da kunnensa ba tare da ya duba mai qiran ba. Kasan cewar yana a yanayin shauqine. Jin Muryar Fadeelah ne cike da kausasa kalamanta ta shiga faɗin. "Yanxu ka kyauta min kenàn, zakayi wannan uwar tafiyar ba tare da ko ka faɗamin ba?, bani da wani matsayi ko martaba kenan a wurin ka JALAAL!" Jalaal kuwa zamansa ya gyara tare da ce mata. "Duk yadda kika ɗaukana duk ɗaya ne Fadeelah, ina Nima bana da wannan matsayin awurin ki, aduk sanda kika so ko miye aikata kayanki kike, sannan duk inda zakije bani da kima ko kuma matsayin da zaki tambayi sahalewana,kawai abinda kika dama kike!" Ya qarishe maganar cikin suyar zuciya domin ta taso mishi mikin dake ɗankare a cen qasan rushinsa. "Ohhhh oh naji malam masifatu Sarkin ƴan qorafi na dukka DUNIYAR, yanxun dai tambayarka nake da gaske kana BAUCHIN!?" Ta datse maganar ta hanyar qara tambayar shi, jalaal kuwa ganin tana son ɓata masa farin ciki ne yasa shi datse qiran nata baki ɗaya. Yaci gaba da abinda yake. ★★★★★★★★★★★ Tsaye take daga bakin zauren gidan nasu tare da wani matashin saurayi, wanda kai tsaye bazaka taɓa gane ainihin fuskar saba. Cikin qasa da murya sosae ya kalleta yana sakin murmushin da yayi masifar tafiya da imaninta, ya furta. "Alhamdulillah yau Allah Ubangijii ya cika mini fata da kuma burin dana daɗe, ina fatan samunsa, acikin tsayon rayuwana!" Sai kuma yaja numfashi, Alamar dai maganar irin mai girman nan ce. Ita kuwa qasa tayi da kanta sosae jin zuciyarta na wani irin beating ahankali ta soma murza hannunwanta, sai kuma ta sake ɗago kanta a karo na ba adadi da qara dubansa, idanunsa idanuwansa tabbas idanunsa suna mata kama da wasu idanuwan data kasa mance su tsayin rayuwarta, ta manta jikinsa fuskarsa amma ta kasa mance idanuwansa tsayon rayuwarta, ahankali ta sake ɗago kanta zuwa gare shi. A take gabanta ya sake yankewa ya faɗi tare da wani irin bugu da zuciyarta yake mata, bakinta ne ya shiga mamul mamul da alama tana son furta wata maganar ne, amma bakin nata yaƙi bata haɗin kai ta hanyar yi mata nauyi. A daidai wannan loƙacin kuma Inna ladiyo ta fito daga cikin gidansu tare da qarewa mutumin dake tsaye kallo,sai kuma ta kwashe da wata uwar dariya, ganin wani irin kayan dake jikinsa wani koɗaɗɗan yadine irin ishurunka marayan Nan da yaga ji da koɗewa matuƙa, ga wani shafta shaftan takalman da suka wa qafarsa yawa inda qafar take sanye cikin wata yagwalalliyar Safa, sai kuma ta sake ɗago kanta ganin fuskarsa duk irin tamburan tabo ne, ga kuma wata uwar yaƙunanniyar farar rigar daya sanya irin wannan mai kwalar mai dogon hannu gaba ɗaya ya gama fita a hayyacinsa, hakanne yasa ta kuma kwashewa da wata uwar dariyar tare da soma kwala qiran sunan Hajja. "Hajja! hajja!! hajjaaa!!!" Hakka kuwa data ke tsaya daga bakin zauren ce ta fito wajen, ganin Inna ladiyon nata ƙaƙata dariya ne yasa ta duban abinda take ma dariyar, ai kuwa itama atake ta kwashe da uwar dariyar datafi na Inna ladiyon, tare da nuna wanda yake tsayen da hannunta. Sai kuma ta shiga faɗin. "Na shiga uku Ni hajja mezan gani haka, Gashi dai anqi cin BIRI ana NAIMAN aci DILA" sai kuma ta qara duban wanda yake tsayen ata taa kuma kwashewa da uwar dariyar datafi ta farko tace . "Ikon Allah ladiyo wannan kuma fa daga ina?" Inna ladiyo datake dariyar muguntane ta dakata tare da faɗin. "Daga duniya mana duniyar wahalallu kice qara da aka farke auren Nan da iliya, ashe ga wanda yafi Iliyan talauci, tabbas boka yayi gaskiya dama yace mudai idone namu, domin zamuga irin mijin da shegiyar nan zata aura!, sai gashi kuwa mun gani ɗin domin wannan daga ninsa ai kaga ɗan wahala" Hajja ce tayi caraf ta hanyar cafe zancen tare da soma faɗin. "Ohhhhhhh ashe haka zamu sha biki kuma, naji malam na cewa bikin bazai wuce nan da sati mai zuwa" Sai kuma ta ɗago kanta ta kalli mutumin dake tsaye tace "To bawan Allah Ubangijii ya baka ikon zama da GUZUMAR KARFA kana UWAR MATA wacce ta gama gantalewa a saman kwalta guntun wasu ƙattin" Ta faɗi maganar da gayya. Shi kuwa wannan bawan Allahn tuni jikin sa ya shiga wani irin tsuma haɗi da mazari tamkar wanda kejin ɗari, cikin wani mugun yanayi ya ɗago kansa zuwa garesu. A zabure suka ja baya tare da wani irin ihu da kurwa ganin yadda idonsa, ya wani sanja launi atakeeeeeeeee.. Hhhhhhhh tofa qaqa qara qayi, shin waimeke shirin faruwa ne? Wane wannan mutumin daya zo zance wurin LAYLERH baiwar Allah😌? Shin ina kuka baro mana labarin JALAAL ɗin mune? Don ganin yadda abin zai kaya kuci gaba dabin AMMEYN ku domin walwale muku 🤣🤣🤣🤣😂😂😂😂😍 wannan biyayya lamarin Asha karatu lafiya 👐🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻👐🏻😽 *💐🌼 JALAAL AREEF 🌼💐* ~💸THE BILLIONAIRE💸~ A story of pure love that touches the ♥️ NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨ Page 11&12 *STORY* *PLANNING* *AND WRITING* *Ammey laylerh ✍️* ~HAPPY NEW YEAR ALL FRIEND 01/01/2024🫂🫂~ *Happy New year {2024} may Almighty Alla's barakat Rahman, for giveness be with us forever wishing u joyous 2024💃🎆🗽🚼* Alhamdulillah ala kulli halin, ahar kullum ina qara miƙa godiyaa na ga Ubangijiin Al'arshi, wanda ya bani Aron Rai da kuma lafiya, kana ya wadatani da tarin Ni'imominsa ta kowacce siga. Shine ya nufeni da sake dawo muku a karo na biyu, kana inason inyi amfani da wannan dama ta hanyar miƙa dubun gidiyana ga MASOYA na AMANA🤙🏻, masu qirana da masu tura min messages ganin bana online🫠, ina godiya ga tarin qaunar ku gareni🙏🏻 kana ina roƙon Allah subhanahu wata'ala da yaci gaba da zame mana gata🤲🏻. __________________________________ ★★★★★★★★ Ahankali yaɗan ware lumsassun Idanunsa kaɗan tare da laluben wayar nashi, cikin barcin da bai gama sakin saba cenñnn qarshen gado ya jiyota, hakan yasa ya janyo ya anutse yana amsa qiran kai tsaye ba tare da yasan waye mai qiran ba. A ƙalla yakusa ɗaukan 20 minute da wayar a kunnensa, sai kuma kawai ya rumtse idanunsa da qarfin masifa, kafin jikinsa ya ɗauki wani irin karkarwa tamkar mai rawar ɗari, tuni idanunsa ya sanja launi daga farare xuwa jawur, gaba ɗaya jijiyoyin kansa kuwa sun tashi sunyi raɗa². Ba tare danaji mene aka faɗamar daga cikin wayar ba, amma dai da alamun koma mene aka gaya masa mai girma ne. Wani irin zazzafan numfashi ya fesar sabo da jin kalaman na barƙa dukkan wata lakar dake jikinsa, nan yaji wani irin abu na sauƙa tun daga ƙwaƙwalwarsa har xuwa tafin qafafunsa, inda gaba ɗaya yaji jikin sa yayi wani irin sanyin da tunda yake bai taɓa jin koda kwatankwacin hakan ba. Fesar da numfashi yayi mai zafi tare da zare wayar a kunnensa yana jifa da ita baki ɗayan, kansa ya tallafo ta hanyar dafesu da dukka hannuwansa biyun wani irin ja idanunsa sukayi ga kuma wani ruwa ruwa da suka tara suna ƙallin wahayen da suka taran masa. Shi kansa bazaice ga yadda yake ji acikin RAI da kuma RUHINSA saba, kawai abinda ya sani zuciyarsa tayi masa wani irin nauyin da yake tunanin ko haɗiyar yawu bazai taɓa haɗiyewa ba, cike da matsanancin tashin hankali marar misaltawa kana cikin galabaituwa ya fara jero dukkan adda'oin da suka mashi. "Ya ilahi ya mujibud da'awati, ya hayyu ya qayyum bi rahma tika astaghisu, la haula wala quwwata illa billah!" Haka yayi ta duk wata Adda'ar ta tazo bakinsa, faɗar irin tashin hankalin da yake ciki ma faɗa loƙacine, amma kai tsaye bazaka taɓa fuskantar halin da yake aciki ba, kasancewarsa mutum mai taurin zuciya yasa sammm farat ɗaya ba zaka taɓa fuskantar yanayin da yake aciki ba. Sai kuma ya shiga sakin ajiyar zuciya akai akai alamun zuciyarsa ta saussauta daga irin zafin da take yimar, ahankali ya shafa sajen dake kwance a kuncinsa, wanda yake fidda wani irin shining ɗin kyau da iyakar gyaran da yake sha. ←←←→→→ Cikin matsanancin kuka take faɗin. "Don Allah! don darajar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama baffa kayi haƙuri kada ka auramin Iliya!. Na yarda ka auramin koma waye amma banda Iliya, baffa Iliya ɗan shaye shaye ne manemin mata ne nasan kasan hakan, baffa koda makaho ko kuturu ka auramin Wallahi na yarda zan rayu dashi amma don darajar fiyayyen halitta banda Iliya!, baffa kasan waye Iliya kuwa? mutumin daya kasance, You are a drunkard, you are looking for women and an infidel who does not pray, na haɗaka da GIRMAN UBANGIJIIN sammai bakwai kayi haƙuri baffa! Ta karashe maganar Cikin matsanancin kuka, laylerh take roƙôn mahaifin nata, shi kuwa cikin ainihin gaskiyarsa yace mata. "Saidai kiyi haƙuri MARYAMU aure nekam babu fashi insha Allah, domin na gaji da ganin ki haka Nan na gaji idan na barkin waye zaki aura? Yaushe kuma zakiyi AUREN? To Ni gaskiya na gaji da ciyar da balagaggiya kamarki ke wai ko haushin kanki baki jine kammmm!, ki duba fa ki gani gaba ɗaya ƙannenki duk sunyi aure daga masu ƴaƴa biyu sai masu ƴaƴa uku don haka kuwa dole ne na aura miki Iliya!' Ya qare maganar yana shigewa cikin ɗakinsa . Inna ladiyo da hajja kuwa farin cikin duniya ya gaba isarsu, tabbas boka yayi gaskiya domin dama yace musu zasuga irin MIJIN da MARYAM ɗin zata aura, kana yace musu koda wasa babu wani mahalukin daya isa yazo wurinta da sunan zance. {Kunji shegu sun manta cewar Allah shine mai kowa mai komai} A tare suka tafa tare da sakin shewa, sai kuma suka ɗauki guda irin ta ƴan duniyar nan tare da fara yada wasu baƙaƙen maganganu marasa daɗinji. Umma kuwa dake zaune a cikin ɗakinta murmushi mai ciwo ta saki, tare da ci gaba da karatun Alqur'ani mai girma da take karantawa. Kamar kazar da kwai ya fashewa haka laylerh ta shigo ɗakin tare da zama kusa da umman, tana zamewa ta ɗora kanta bisa qafafun umman nata, cikin son ta kwantarma da yarinyarta hankali ta shiga lallashinta, tare da ce mata taci gaba da adda'a insha Allah tanaji acikin jikinta Allah zai musanya mata da mafi Alkhairinsa, haka dai tayi ta mata nasihohi masu ratsa zuciya a qarshene kuma ta ɗago idanun laylan tace mata. *"Kiyi haƙuri Maryam! ƙarshen haƙuri nasarace, ƙarshen tsanani darajace, ƙarshen wahala ɗaukakace, ƙarshen jarabawa kuma Alkhairi ne, don haka ki kasance cikin yaƙini da kuma godiya ga Allah"* "Baffa! baffalo!! Baffalota!!!" Lawandine ya shiga rarakawa mahaifin nashi qira tamkar maqogwaran sa zai fito, cikin buɗaɗɗiyar muryarsa irin ta mashaya yaci gaba da faɗin. "Wai kana ina neeeeee nasan kana jina, idan an isa ayi wannan auren shege nake laylan za'a aurawa Iliya!, Iliyan da kowa ya sani mugun ɓarawone! Ɗan daba!! Wanda kabbb garin nan babu wanda baisan shiba, yaron da kusan kullum yana hanyar birsin, ƴan daba fa yake ma aiki to wallahi yau dai nima sainawa Maryam ɗin da mahaifiyarta Rana " Sai kuma ya shiga kwalama mahaifiyarsa qira cikin gabjejiyar muryarsa data gama buɗewa. "Inna! Inna!! LADIYOOO! Danma kin samu ana ce miki Innan to ladiyo fita kina INAAAAAA, nasan wannan ba aikin kowa bane daya wuce ke da wannan shegiyar hajjar" Inna ladiyo kuwa da tunda taji shigowar ɗan nata ta shige qarqashinsu gadon ko ƙwaƙƙwaran motsi bata kuma yiba, saida taji yana zabba mata wannan uban qiran ne kuma bata san sanda ta saki fitsarin azabar tsora ba. Hajja kuwa da tayi wani irin tambulan ta shige cikin macaccen sif ɗinta, ɗaya riga ya gama macewa, cikin tsananin tsoro ta shiga zazzara ido tamkar wacce tayi ma sarki sata. Shi kuwa lauwali yaci gaba da faɗin. "YARINYAR da kakaf gidan daga ita sai mahaifiyarta ne kaɗai ke qaunata, amma ina raye ace za'a aura mata Iliya ɗan shola shili kafuri kuma !" Cikin mazarin jiki da matsananci tsoron ɗan nashi baffa dake ɓoye a bayan ƙyauren ɗakin sane yasa shi fara magana cikin tsoran ɗan nashi. "Wannan anyi ɗan shegiyar yaro, samm ganinka babu alkhairi acikin sa" shifa har mantawa yake da yana da wani ɗa lauwali. Umma dake zaune har yanzu ce ta miƙe tana fita a ɗakin don xuwa wurin lauwalin da kafa gidan maganar tane kaɗai yake ji, acikin sassanyar muryanta wanda ya qara sanyi fiye da da ta nufo shi tare da faɗin. "Haba lawan ayi haquri haka nan mana kowanne bawa yana da nashi irin kaɗɗarar, ita kuma nata a haka yazo mata, idan har wannan aure shine mafi Alkhairinta to Ubangijii ya tabbatar mana shi da Alkhairi!" Ganin ita ma umman yau tanason ta ɓata masa raine yasa yace mata. "Taya auren Iliya zai zama Alkhairi umma?, bayan kinsan irin abubuwan da yake aikatawa na rantse idan da wanda ya isa ya ɗaura auren Nan shege nake, idan kuwa anyi to na rantse niba ƊAN HALAK bane SHEGE ne" Fuuuuuuuuuuuu ya fice a gidan yana fita kuwa yaransa suka rufa mishi baya. ************ Zaune yake gaban ummiensa cikin tattara dukkan nutsuwarsa zuwa ga mahaifiyar nashi yace. "Ummie wannan shine kaɗai alfarmar da zakimin!, kana kamar yadda na faɗa miki haka nakeson abun ya kasance, kuma Ni da kaina zance wurin baba hashimun na sanar dashi!" Cikin wani irin yanayi ummien ta kalla tilon yaron nata, kana tace. "ABDULJALAAL kana ganin babu wata matsala kuwa, idan har muka ɓullo ta wannan al'amarin!?" Ta qare zancen tana jin tamkar hakan baiyi mata ba, cikin tabbatar wa yace mata. "Idan harba ta wannan hanyar ba to kuwa bazan taɓa samun cikin muradina ummienaaaa" Yaja sunan nata, cikin yarda tace na amince maka ABDULJALAAL" Cike da tsananin farin ciki marar misaltawa ya rubgume mahaifiyar nashi tare da cewa. "Na gode ummiena Ubangijii ya biya ki da gidan aljannatul Firdausi!" *********** BAUCHI ************ Wasu dattijai ne tsaye cikin wasu irin koɗadɗun kaya, wanda kallo ɗaya zaka musu kasan cewa talauci ya samu wurin zama a jikinsu, amma ga mai cikakken hankali kuma kallo ɗaya zaiyi musu yasan cewa dattijaine masu daraja, dattako, nagarta. A guje yaron da suka aika dan yimusu iso da alh ya zuro tare dace musu. "Wai yace yana zuwa" Sallamar yaron sunkayi da wata koɗaɗɗiyar Murtala data gama koɗewa matuƙa. Babu jimawa kuwa Alh Yusuf mai kaba ya iso yana wani ɗage kai sama , shiga tunda wannan ɗan kut bazan dai qarisa ba dai🙀😍 ya faɗa masa zancen auren Nan yakejin bala'i dama kowa ye, kuma yariga yayi alqawarin cewa wannan karon kammm ko waye yazo da buqatar, naiman auren MARYAMU to tabbas kuwa zai bada. (Tofa wannan shine ana wata ga wata🙀🙀 kome ke shirin faruwa haka ohooo) Cikin daraja shi suka shiga gaidashi tare da faɗa masa akan maganar data kawo su, na naimawa ɗansu alfarmarta naiman auren ƴarsa LAYLAH. Aikuwa babu binciken komi yace ya basu a turo, cike da mamakin wasu iyayen masu hali irin na Alh Yusuf suke kallon sa. Cike da matsanancin tsoro Iliya shola Ameobi ke kallon su lauwali, domin yasan karon ba daɗi. Wani irin shegen kallo da lauwali ya wurga masa ne yasa shi qara mannewa guri ɗaya, shi kuwa yaya lauwali cike da tacewa a rashin mutunci, ya sake dubun iliya shola Ameobi yace. "Mene nace maka wato duk abinda na maka a banza kenan baka janye batun auren ƙanwas ba ko?" Cikin tuno irin baƙar izayar da yasha a wancen loqacin ne yasa Iliyan wani irin zazzaro idanunsa waje, tare da fara magana cikin kiɗima haɗi da tsoro yace. "Na ranshe da Allah na janye, daba ai na faɗa maka ita ladiyon ai itace ta bani kuɗi tace in aureta, kuma tun ranar da da kabani kashedin nan nace wa babanku na fasa auren ƴarsan!" Ya faɗi maganar yana sauƙe ajiyar zuciya don ganin kamar ya tsira. Shi kuwa lauwali wani irin murmushin mugunta ya jefa ilya dashi tare da faɗin. "Duk da haka sai an ɗan baka sadaka" Gaf ya buga kan iliya da jikin bishiyar da suke tsaye, yaja tawagarsa suka qara gaba. *JALAAL* Zaune yake akan ɗaya daga cikin lumtsuna lumtsuman kujerun office ɗin sa, cike da zallar farin ciki yake gudanar da ayyukansa cikin nishaɗi, domin tunda baffanninsa suka shaida mashi cewar lallei mahaifin yarinyar ya amince da batun auren su, da gaba ɗaya RAYUWAR yakejin kansa cikin wani irin matsanancin farin ciki, haɗi da jin wata irin nutsuwar da hakima baiji irin taba. Yana a wannan yanayin ne kuma ya jiyo qarar wayarsa, cike da shauƙi ya janyo wayar nashi, yana mannata da kunnensa ba tare da ya duba mai qiran ba. Kasan cewar yana a yanayin shauqine. Jin Muryar Fadeelah ne cike da kausasa kalamanta ta shiga faɗin. "Yanxu ka kyauta min kenàn, zakayi wannan uwar tafiyar ba tare da ko ka faɗamin ba?, bani da wani matsayi ko martaba kenan a wurin ka JALAAL!" Jalaal kuwa zamansa ya gyara tare da ce mata. "Duk yadda kika ɗaukana duk ɗaya ne Fadeelah, ina Nima bana da wannan matsayin awurin ki, aduk sanda kika so ko miye aikata kayanki kike, sannan duk inda zakije bani da kima ko kuma matsayin da zaki tambayi sahalewana,kawai abinda kika dama kike!" Ya qarishe maganar cikin suyar zuciya domin ta taso mishi mikin dake ɗankare a cen qasan rushinsa. "Ohhhh oh naji malam masifatu Sarkin ƴan qorafi na dukka DUNIYAR, yanxun dai tambayarka nake da gaske kana BAUCHIN!?" Ta datse maganar ta hanyar qara tambayar shi, jalaal kuwa ganin tana son ɓata masa farin ciki ne yasa shi datse qiran nata baki ɗaya. Yaci gaba da abinda yake. ★★★★★★★★★★★ Tsaye take daga bakin zauren gidan nasu tare da wani matashin saurayi, wanda kai tsaye bazaka taɓa gane ainihin fuskar saba. Cikin qasa da murya sosae ya kalleta yana sakin murmushin da yayi masifar tafiya da imaninta, ya furta. "Alhamdulillah yau Allah Ubangijii ya cika mini fata da kuma burin dana daɗe, ina fatan samunsa, acikin tsayon rayuwana!" Sai kuma yaja numfashi, Alamar dai maganar irin mai girman nan ce. Ita kuwa qasa tayi da kanta sosae jin zuciyarta na wani irin beating ahankali ta

Chapter 6 of 22