Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJuEWNnTjRk6AmcQ9FKtLk *~IDAN HAR KINSAN BA KARATUNE YA KAWO KIBA pls kada ki shiga. Kana idan har kinsan ba zaki comments ba kada ki shiga ko kin shiga zanyi waje dake🫰🏻~* *💐🌼 JALAAL AREEF 🌼 💐* ~💸THE BILLIONAIRE💸~ A story of pure love that touches the ❤️ NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨ Page 1&2 *STORY* *PLANNING* *AND WRITING* *Ammey laylerh ✍🏻♥️* Marubuciyar 👇🏻👇👇👇 *~KAREN BANA~* ✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟ ********* Alhamdulillah, Alhamdulillah, indeed, God is always grateful , is the one who gave me the opportunity to come back to you In this book of mine called JALAAL AREEF. Alhamdulillah masoya na Asali am back na dawo muku da labarin dazai qayatar daku💃, Bazan iya misalta muku meya qunsa ba sai inhar kun biyoni zakuji da kanku. 😌 Masoyana qauna ta har abada naga ƙauna, A last littafina, naga masoya masu qaunar ci gabana, Allah ya qara buɗi da ƙauna, inji ta sambaɗo muku littattafai masu ɗan karen daɗi🤏🏻. ______________________________ Ahankali ta tsallako kai tsaye kuma ta shige dogon layin dake gabanta, ta dubi uban tsayin dogon layin duk da yawan al'ummar da yake da, amma gaba ɗaya anguwar shiru kakeji tamkar ba'a taɓa rayuwa acikin ta,haka take shiru duk da kuwa cewa anguwar marasa qarfi ce sosai. Sannu Ahankali take ci gaba da taka qafafunta tamkar mai tausayin qasa,wanda Azahirance idan kaga yadda take takun nata zakayi tsammanin da gayya take takun. Saidai sammm abun ba haka yake ba, haka halittar ta take idan tana tafiya kowa yana ganin tamkar tsabar kwaunane ce, Allah Allah take taga ta Isah gidansu, dan tasan yanxun duk inda hankalin ummanta yake to yana a kanta ne. duba da cewa yauɗin ta tashi a makare ne daga wurin aikin nata by 6.am aka magana da woni abu. Babu wata doguwar tafiya ta Iso qafar gidan nasu,wanda ke rukunin gidajen marasa qarfi sosae acikin anguwar ƘOFAR DUMI dake cikin garin Bauchi. Kanta tsaye ta nausa kanta cikin zauren gidan nasu, tana gyara ratayar jakarta dake maƙale a kafaɗarta, turus taja da tsaya sakamakon ganin ƙanwarta dije da tayi tsaye da wani matashin saurayin,,dake fuskantar ta wanda yanayin tsaiwarsu kaɗai ya isa ya shaida maka cewar fira suke yi, ɗauke kanta tayi tamkar bata gansuba, don wannan dabi'a ta dije kai bama itaba duk yaran gidan na bata haushi matuƙa. Ta tsakiyar su ta raɓa ta huce, don dole sai tabi tsakiyar nasun kana ta wuce cikin gidan nasu. Sauƙar muryar qanwar nata tayi tana faɗin "Haka dai aka iya kullum azira zumbulelen hijjabi, ace an tafi wata uwa aiki! Alhalin da inda ake zuwa ake fakewa da wani gurin aiki". Wani irin tsalle taji zuciyarta yayi tare da wani irin bugu, hakan yasa ta ɗago kanta ahankali tana sauqe idanunta, Akan dije babu yabo babu fallasa. shigewa cikin gidan tayi ba tare data iya ɓunta mata koda Aa bane. Sallama tayi cikin gidan kamar yadda ta saba duk da tasan babu mai amsa mata, inhar ba ummanta bane a tsaƙar gidan ko Khadijah qanwarta wacce suke uwa ɗaya uba ɗaya. In banda su babu mai amsa mata sallama, koda kuwa zata shekara dubu arba'in tana yi ɗin kuwa, aikuwa tamkar yadda ta tsammata ɗin, haka abin ya faru, don kuwa ko kallon arziƙi bata samu daga wurin matan BABAN NATA BA. Bata fasa musu sannu da gida ba tamkar dai kullum ɗin, tsaki ladiyo da hajja suka ja atare, kanta kawai ta ɗan girgiza loqacin data tsinkayo muryoyinsu, suna sana'ar tasu wato munafincinta. "Lallai idan da ranka kasha kallo yo wama ya sani ko an gama gantalewa a saman kwalta, sannan adawo gida simi simi cikin kwaton hujja i tamkar wata ta gari ana fakewa da wani uwa, wai shi aiki" Gatsinewa hajja tayi loqacin data gama jin maganganun ladiyon. "Hmmmm ladiyo kenan nikam kaina mamaki kike bani wani bin, in banda abinki kina tunanin yarin ya mai jini ajika, maiji da tashen ƴan matanci kamar LAYLERH. Harma kice yo ai babu tamtama tagama sanin takan harkar bariki." Wata uwar shewa ladiyo tayi tare da faɗin "shi yasa yinki hajja domin akwai fashimta" { Kunji fa Itan kenan bata da fashimtar.} Tafawa sukayi tare da qara ɓarkewa da wata uwar shewar a tare. Da sallama bakinta ta shiga cikin ɗakin mahaifiyar nata, jin ba'a amsa ta bane yasa ta shiga cikin ɗakin kai tsaye. Zaune ta tarar da ita bisa darduma tana da Alqur'ani ahannunta tana karanta wa. Zama tayi gefen mahaifiyar nata tare da cire toms ɗin ƙafarta. Daga ɗakin nasu suke jin irin wulaƙancin da sukaci gaba dayi, akan laylerh. Daga har mahaifiyar ta babu wanda ya tankasu, daga laylerh har ummanta, domin inda sabo yaci ace sun saba da irin wannan maganganun daga abokan zaman nata. Fitowa tayi ta ɗauka buta ta ɗebo ruwan alwula tazo zata gitta su Hajja, ladiyo tace "Hmmmmm Allah wadaran naka ya lallace kuwa, dan wataran tabbas za'a tabka abin kunya a wurin nan". Bata saurari zantukan da suke ta faɗi akan nata ba, duk da kuwa cewar Acen cikin ƙasan ranta maganganun da suke faɗi ɗin, akanta suya suke mata acikin zuciyarta. Amma haka ta share su tayi shigewarta ɗaki bayan ta gama alwular tan, darduma ta shimfiɗe tana tada sallah. Bayan idar da sallan nata hannuwanta ta cira sama tana roqon Allah, ya kawo mata ɗauki cikin dukkan al'amurranta, tare da sauqaqa mata. Ta daɗe tana kaima Allah kukanta kafin ta sallame. Jin sauƙar muryar mahaifiyartane kuma ya dawo da ita Cikin nutsuwarta, "Kiyi haƙuri MARYAMA! insha Allahu wata rana sai labari, kici gaba dayin haƙuri insha Allahu, Allah zai miki zaɓi na gari! Kullum cikin Adda'ar zaɓin MIJI na gari nake miki." Cikin tausaya wa da ƙaryewar zuciya ummanta tayi maganar, don tana tsananin tausayin ƴar Tata sosai. Cikin zallar hikima da tarin nutsuwarta tace, "Na gode da adda'oinki gareni ummana, na komai kada ki damu Allah yana sane da dukkan al'amuran. Kuma insha Allah shine zai kawo min mafita cikin halin tsananin da nake ciki". MARYAM YUSIF shine cikakken sunana na yanka, wanda ummana tamin laƙabi da LAYLERH. Kasan cewar ashirin da biyar ga watan azumi ta haifeni, wanda Atsakankanin waɗannan kwana ake saka ran ganin, DAREN LAYLERTUL ƘADDR. Wato daren Ashirin da biyar da kuma daren Ashirin da bakwai da daren Ashirin da tara! Inda Ni kuma mahaifiyata ta haifeni a daren Ashirin da biyar. Hakan ne yasa ta sanya min suna LAYLERH. Mahaifina yana da mata uku Hajja itace matarsa ta farko, kana sai mahaifiyata {Ummata} sai kuma ladiyo wacce yaran gidan suke ƙiranta da Inna ladiyo. Mahaifiyata tasha wuya matuƙa awurin Hajja, dan babu irin izayar da bata gana mata ba. Haihuwar ta ɗaya Babana ya qaro wani auren, inda ya auro Inna ladiyo nan kuwa sabuwar duniya ta buɗe musu. Don sun ware mahaifiyata sunce ita JININ BAƘIN JINI ce. Tunda ƴaƴa mata take haifa, yayin da su suka kasance ko waccensu tana da ƴaƴa maza. Hajja haihuwar ta ta farko Namiji ne wato yaya jamilu sai INDO sai kuma Habibu sai Isah sai AUTAR Dije. Yayinda Inna ladiyo take da yara huɗu ɗanta na fari itama Namiji ne lawal sai kuma sani sai Kabiru sai kuma fatsima. Inda mahaifiyata taka sance haihuwarta ta farko ta haifi mace wato Ni MARYAM sai kuma Khadijah AUTARMU, don ita haihuwarta biyu ne sai haihuwar ta tsaya mata cakk. Inda gaba ɗaya wannan gida namu yake cike da tarin ƙalubale acikin sa. Dan kuwa gida ne na rashin tarbiya qarara inda ya kasance gidan iya ba gwaba baba ba tausa, wato dai irin gidan nanne da na zaman kai da kai. Mahaifinmu alhaji yusif {amma fa tun irin alhazan nan masu zuwa maka a JAKI babanmu yake}. Ba irin alhazan yanxun masu zuwa a jirgi ba, yana da wani irin hali wanda ya kasance babu ruwan shi da haƙƙin matansa damu ƴaƴan shi. Wanda ko ƴar makarantar Arabi baya da ƴaƴan sa bare kuma boko, amma yace bai hana ba duk wacce take da kuɗinta, To kuwa bai hanata ba tasa ƴaƴan ta. Wannan dalili yasa mahaifiyarmu cin akwatin ganin ci gabanmu, tun ina ƴar shekara biyar ta sanyani makarantar allon anguwarmu, Da kuma boko. Sam bai damu da woni fidda haƙƙi ba, amma idan har yana dashi yakan kawo ko ba yawa a girka, inda sau da dama saidai muji qamshi daga nesa dan ba rabonmu ciki. Wanda hakan yake matuƙar ƙona raina fiye da tunanin mai karatu!. Zafin abinda ake ma mahaifiyata da kuma mu biyun data haifa, yasa naci alwashi akan zan tsaya tsayin daka wajen nema mana ƴancin Rayuwa da kuma gata. Wanda yanxun haka ina aikin cike takardu a woni campany na J M Company. Wannan kenan. ******* *🏞️EGYPT🪐🏞️* ~L... IN MY LIFE BEACH RESORT - EGYPT🎢🏙️~ ←←←→→→ ******** Babban Beach ne mai girman gaske daya amsa sunan shi, BEACH ne babba daya samu world recognition wanda kabbbbbbb duniyar ta bashi World Best Beach A shakarar 2019. Duk da kasan cewar na ɗaya daga cikin ƴan africa ne African ma 9j {Nigeria}. Gaba ɗaya wurin wani irin blue ɗin haske ne ke ta faman kaida komo a wurin, gefe guda kuma wani irin haɗaɗɗan Swimming pool ne, wanda gaba ɗaya ruwan cikinsa ya kasance blue sosai. Wata irin sanyin qamshine keta faman tashi, irin mai ratsa jikin nan tare da sanya nutsuwa a tattare da ma,abocin wurin. Wani kyakkyawan matashin saurayine! zaune daga bakin ƙaton Swimming pool ɗin, sanye yake dawani Brown shirt da farin dogon wando na Jessy. Ya zira ƙafafuwanshi cikin ruwan, Ahankali yake karkaɗa qafafunsa cikin ruwan. A duk loqacin da yake cikin ɓacin rai ko kuma bege da kuma kewar abu mafi soyuwa acikin Rayuwarsa, yakan zo wurin ne don yakan ɗebe mashi kaso mafi rinjaye, na daga cikin abinda ke damunsa. Aƙalla yafi ƙarfin sama da 40 mints awurin yana jin sassaucin abinda ke son taso mashi, duk da yana qoqarin dannewa tsayin shekaru masu ɗan dama. Jin barci nason fin qarfin sane yasa shi tashi yana layi, irin na masu barcin nan hannuwansa riƙe da wani haɗaɗɗen diary, gaba ɗaya hankalin mafi rinjaye daga wurin ne ya dawo kansa, cikin sauri bodyguards nashi suka mimmiƙe tsaye, tare da saurin nufar parking space na cikin Beach ɗin,, wata farar haɗaɗɗiyar Bugatti ɗaya daga cikin yaran nashi ya buɗe mashi, cikin tafiyar sassarfa ya kutsa kansa cikin lafiyayyar motar. Babu ɓata loqaci suka ja motocin aguje, ajere a kuma tsare suke tafiya suuuuuu cikin tsakiyar titin na qasar EGYPT 🪐. Basu yi wota tafiya mai zurfi ba suka isa wata qayatacciyar anguwa, anguwace guda ta musamman inda a bakin ƙaton Get na anguwar yake ɗauke da harrufan, L.... IN MY LIFE MENTIONED 9j. Horn suka buga get man yayi saurin buɗe musu get ɗin, tare da solid na motorn, ko gama daidaita parking basuy ba. Cikin sauri ɗaya daga cikin guards nashi ya fito ya buɗe mashi murfin motorn. Qafafuwanshi ya fara zirowa kafin ya fito baki ɗayansa. Eyephone nashi kawai ya iya ɗauka tare da yin gaba abunshi. Babban parlourn su ya nufa cikin sauri² gudu² yake tunkarar parlourn gidan, saidai me yana sanyo kansa yaja yayi turus, ganin gaba ɗaya ploorn ahar mutse tamkar kullum, da kwalayen picanto, dominos pizza for lunch ya fara cin karo. Hakan ya bashi tabbacin tun lunch na rana ɗaya fita ya barine bata gyara ba. Ɗan ƙaramin tsoki yaja ganin gaba ɗaya komi da komi na parlourn babu abinda yake a kimtse, Numfasawa yayi kaɗan, aransa yana faɗin shikam, ya rasa wacce iriyar MATA ce FADEELAH! Gaba ɗaya rayuwanta bata san daidai d rashin daidai ba. Deda trow pillows idan ya faɗo daga saman sopa bata iya ɗaukewa, every where is unkept and scatterd ko kaɗan babu kimtsi acikin rayuwarta. Hakan yasa cikin wani irin zafin zuciyar daya daɗe, yana dannewa ya nufi cikin bedroom nata, wanda tsabar azabar zafin rai yasa har step bibbiyu yake takawa, afusace ya turo ƙofar ɗakin tare da ware idanunsa. Wanda sukafi kama dana masu jin barci, dan koda yaushe every time suna alumshe ne. Ja yayi ya tsaya ganin ya kwance cikin wasu matsiyatan kayan barci, wanda dasu kara babu kuma yana da tabbacin haka tayi ta yawonta dasu a cikin gidan, Sam-sam fadeelah batasan rayuwa ba shikam dade da rana ɗaya bata taɓa fito ta faɗi batare da sunyi rikici ba. "FADEELAH! FADEELAH!! FADEELAH!!!" Ya shiga ƙiran sunanta tare da jijjaga ta, cikin tsabar rashin tarbiya ta shiga faɗin. "JALAAL AREEF what happened? Meye damuwarka dani ne kammm! Kake min wannan uban qiran, yau kuma dame kazo? Dan nasan akullum Ni bana rasa laifi awurin ka! Duk kuwa da cewa ina iyaka bakin qoqarina, wajen ganin na faranta maka". Kasa cewa uffan yayi saima zuba mata lumsassun idanunsa da yayi, tare da sarƙe hannuwansa cikin ƙirjinsa, yama rasa bakin magana. Ɗan numfasawa yayi tare da tattara dukkan kalmomin da yakeson amfani dasu, wajen ganin ya fashimtar da fadeelah irin girman laifukanta gare shi. Hakan yasa shi fara magana cikin hosky voice nashi yace. " Mene kika ɗauki aure ne kammm? Dasam bakisan kima da kuma darajar shiba, kullum ke burin ki kiyi ta chart da ƙawaye, amma Sam sam bakisan yadda ake kula da miji ba, but kawai abinda kika sani shine kiyi sleeping kiyi chatting!, bana ce tunda aka auroki kin taɓa koda kwatankwacin shiga kitchen ne, da sunan girki dade pant and Bra naki masu aiki ke wanke miki. Waikam ke ko kunya ma baki jine don Allah?. Na gaji da dukka halayenki marasa ƙyau FADEELAH, dan haka ya zamar miki dole ki tsaya ki fuskanci rayuwa yadda ya kamata, idan har kinason cigaba da zaman aure dani!". Cikin zallar iya tsageranci da sakalci ta mashi, kallon sama da qasa tare da faɗin. "Ka gama?" Ko ikon magana bata samu ya mata ba hakan yasa ta qara fusata. Zaune ta miƙe tana tattaro uban gashin dokin dake kitse akan, ta fara magana cikin rashin tarbiya da rashin girmama na gaba dakai. "Kai ko kunya bakaji ba don Allah da kace na shiga kitchen?. Kana a matsayin THE BILLIONAIRE of African kai harda ma sauran qasashen waje, amma kake maganar only you ni MATARKA FADEELAH JABBER SHETTIMA na shiga kitchen?, Sannan nayi worshing, nayi Garbage, washed and washed?. Dama baiwa aka kawo maka kenan, to me amfanin DUKIYAR da ALLAH ya baka Keenan? Idan har zan shiga kitchen kana nayi duk sauran aikin gidanka. Kaga Keenan babu amfanin DUKIYAR da muke da, idan har nice ƴar aikinka JALAAL AREEF THE BILLIONAIRE!" Numfashi yake sauƙewa domin ganin abubuwa da yawo na neman suyi, crosing mind nashi marasa daɗi. Musamman abubuwan dake faruwa a zaman auren shi shida FADEELAH , yasan dole ne yayi zaman aure da fadeelah tunda zaɓin mahaifiyar sace. Ƴar ƙanwar tace Hajiya Rabi'atou Aliyu. Idanunsa ya lumshe tare da buɗesu akanta, yarrr tsikar jikinta suka zuba ganin irin kallon da yake binta dashi, baiyi aune ba yaji shi jikinta ta janyo shi saman gadon tare da haɗe shi da jikinta. Kunnensa ta kama ta shiga raɗa mishi "haba my only you, ka tsaya kayi tunani da ƙyau muyi rayuwarmu cikin hutu dajin daɗi! Allah ne ya hutar damu dan haka kaga dole ne mu huta" Hugging nashi tayi tare da faɗin "good night baby dreams, kayi barci mai daɗi kaga Ni ka tadani da hayaniyar kan, gashi kaga ina off bare ka rage Zafi" Ta faɗi hakan tana juya mashi baya. {Niko AMMEY LAYLERH nace mene rage Zafi kuma fan's🥰} Haushi baƙin ciki takaici sune suka taru suka tokare maƙoshin JALAAL , wato ma mayen mata ta ɗauke shi kenan ko me, dan kawai tana matar shi shine take da zarrar faɗa masa duk kalaman da suka zo cikin bakinta. Shikenan zaiyi maganin ta. Nan ya tashi tare da zare tshrt ɗin jikinsa tare da dogon wandon, comfy white towel ya ɗaura tare da shigewa cikin bathroom... Shower kawai ya sakar ma kansa, kafin daga bisani ya tara ruwa masu ɗumin gaske acikin jacuzzyn, duba da yanayin garin wanka yayo mai rai da lafiya tare da shafe jikinsa da tularenv dolcy & gabbana kayan barci mai santsi ya zura, tare da ficewa a ɗakin nata baki ɗaya, ɗakinsa ya nufa yayi kwanciyar shi hankali kwance, ya daɗe yana tunanin rayuwar aurensu da fadeelah for the past 3 years, amma ace samm mutum bai fuskanci gobensa ba bai kuma san miye rayuwa ba. Ita dai kawai taci mai ƙyau tasha mai ƙyau ta tonƙoshe ƙafafu tayi chatting ta sani, in banda hakan babu abinda ta sani, dade da school nata ta bari, tace dama sabo da kuɗi ake karatu gashi ita kuma tana auren THE BILLIONAIRE of African. To karatun mene zatayi kuma turanci dai ta iya kana babu abinda mai master's zasu gaya mata. Wannan halayya nata suna maƙurar kaishi bango, ahaka da wannan tunane tunane har barci ɓarawo yazo yayi awon gaba dashi, ba tare daya ankare ba. Zan dakata anan sai mun haɗu xuwa safe. Insha Allah 👏🏻👏🏻👏🏻 https://chat.whatsapp.com/EJuEWNnTjRk6AmcQ9FKtLk *💐🌼 JALAAL AREEF 🌼💐* ~💸 THE BILLIONAIRE 💸~ A story of pure love that touches the ♥️ *NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨* Page 3&4 *STORY* *PLANNING* *AND WRITING* *Ammey laylerh✍️* ★DAZZLING S★T★R'★WRITERS =========================== ________________ A haka da wannan tunane tunanen har barci ɓarawo yazo yayi awon gaba dashi, ba tare daya ankare ba.....cen ɓangaren oga fadeelah kuwa tana jin fitar shi ta tashi zaune daram tana jan tsuka, wayanta ta ɗauko daga qarqashin fillow, Deta nata ta kunna tana faɗin. "Shi mutum tamkar woni doki samm ace baya gajiya da abu ɗaya" WhatsApp nata ta shiga taci gaba da chatting ɗinta da ƙawayenta ƴan duniya, sai wajajen ɗaya da rabi na dare tayi barci hakan ma ba dan taso ba. ******** Cikin tafiyarsan na sauri²gudu² yake taka mata kalan benen babban parlourn nashi wanda ya gaji da haɗuwa, gaba ɗaya malale yake da wani irin ƙayataccen grass carpet mai tsananin azabar ƙyau da ƙayatuwa. Cikin zallar nutsuwar da Allah (S .W. T) yamar yaci gaba da saƙƙowa yana kuma tunkaro ƙayataccen parlourn gidan baki ɗaya. Kai tsaye bayan gama sauƙowarsa palon, ƙofar ɗakin ta ya kalla, har yayi kamar ya fice sai kuma wani tunani ya faɗo masa, hakan yasa shi nufar ƙofar ɗakin nata tare dayin Knoking, jin shiru ba'azo anbude mishi bane yasa shi tura ƙofar, dan yasan idan zai shekara yana Knoking ba zata taɓa buɗe mashi ba. Ƙafafuwan sa ya sanya cikin parlourn nata, turus yaja ya tsaya ganin tun kayan ƙazantar ta na jiya na Nan a parlourn, babu abinda aka gyara hakan yashi ajje ƙaramar jikar dake riƙe a hannunsa tare da zare farar rigarsa, gaba ɗaya saida ya tabbatar ya gama gyara parlourn tass, babu inda ya saura kana ya nufi bedroom nata. Tana kwance tayi balance akan makeken gadonta, wanda gaba ki ɗaya ya gama harmutsewa yabi duk ya cukuwkuye, sai sharar barcinta take kai tsaye babu abinda ya dameta, cikin zallar takaicin ta ya shiga ɗan bubbuga gefen fillown da take a kai. Wata miƙa tayi tare da fara sambatun daya riga ya zame mata jiki. "JALAAL kayi tafiyarka, nace ma zanyi sallar nan idan na tashi! Pls kaje I promise nayi alqawari dana farka zanyi sallar nan!" Wata uwar tsawa ya buga mata tare da cakumo tulin gashin dokin dake kanta, tsaye ya miƙar da ita tare da ɗauke ta da wani irin gigitaccen mari, cikin fusata ya shiga nunata da yatsar shi tare da faɗin. "Zaki iya min duk rashin mutunci da rashin tarbiyyar da kika ga dama, amma Sam sam bazan juri wasa da Sallah ba! Ki duba time ki gani by 10.AM amma ace kina ƴar musulmi baki yi sallar suba shi ba?" Cilli yayi da ita kanta ya bugu da jikin gado, hakan yasa fadeelah fasa wata uwar ƙarar azaba, ko takanta baibi ba ya raɓe gefen ta ya fice a fusace, bayan ya gama buga mata worning akan lallai kafin ya dawo, ta tabbatar tayi Sallar nan. Saida tayi kuka mai isarta kana ta miƙe ta shige toilet wankan ta, ta tsalo ta shirya kanta cikin wasu azababbun riga da wando pallazo, pink color da farar riga mai adon duwatsu wacce a gaban rigar aka mata rubutu da manyan baƙaƙe, D

Chapter 1 of 22