kafin ya kuma ware mata su akanta, sai kuma ya kama yatsar hannun ta ya zira mata a hannunta na kusa da yatsarta na qarshe yace.
"Zoben alqawari"
Sai kuma ya sauqe ajiyar zuciya haɗi da kuma ware mata lumsassun idanunsa baki ɗaya, kuma yin qasa da kansa tare da furta mata.
"Are you marry m"
Babu zato babu tsammani yaji ta faɗa saman jikinsa tare da cusa kanta cikin qirjinsa, tana kanainaye jikinsa da hannayenta. Ko kalmar bai qarasa faɗi ba yaji ta faɗo masa saman jikinsa.
shima hannuwansa yasan ya baki ɗaya yana zagaye kugunta. Yana sakin wata iriyar kyakkyawar ajiyar zuciya yana jin wani irin daɗin daya daɗe baiji koda kwatankwacin sa bane.
Me kenan hakan tana nufin ta gano shi keñan kome?
Kukan da yaji ta saki ne tare da fara kai masa bugu a qirjinsa sane ya sanya shi qara shigar da ita Cikin jikinsa, ita kuwa Layla cikin matsanancin kuka take faɗin.
"Me ya sa? Me yasa ka gudu ka barni a karo na biyu!? Mai yasa ka tafi kabar rayuwana cikin wani hali, halin dani kaina na gaza sani ko fashimtar me ne ne shi!, kayi min nisan daya sanya ni manta komi da komae naka, na mance kamanninka na mance muryarka! Na mance komai da komai naka, abu ɗaya ne na gaza mancewa sune ƙwayar idanun ka!. Sammm na gaza mance waɗan Nan idanuwan, kullum sune acikin mafarkina! Sune tunani sune suka sanja komi da komae nawa, sune sune sune suka sanya na gaza ganin ƙyau da girman idanun ko wanne Namiji acikin duniya, waɗannan ƙwayar idanun sune suka sanya na zama mai taurin kai da zafin zuciyar daya sanya ko wanne Namiji yake kasa tun karana da sunan SO! Waɗan nan tsadaddun idanuwan sune suka min shamaki ga duk wani mai son kawomin hari ta fannin soyayya, ba kamar yadda su Inna ladiyo suke zata bane tabbas ina da tarin masoya na ban mamaki wanda Ni kaina wani loqacin har mamakin irin tarin masoyan da suke amfani da kalmar kawai amma ba tare da sun tun kareni ba!"
Sai kuwa ta sauqe ajiyar zuciya mai tsananin zafi wanda hakan yasanya jalaal qara gyara mata kyakkyawar rungumar daya mata, sai kuma taci gaba da faɗin.
"Wasu zanci zancen ne daga bakin Rahama wasu kuwa acikin gari zanga ana nunani da sunan Masoyiyar wane da wane, amma na toshe kunnawana na rufe idanuwana bana ganin komi face ƙwayar idanun da suka min shamaki ga ko wanne irin idanun ne, sai dai! Sai dai! Abduljalaal wanda yaje naiman aure na na farko, a wurin sane kaɗai naga wannan irin ƙyawar idanun!, wanda sabo da hakan nema ya sanya kai tsaye na amince da aurensa!.
Sai dai ganinka da nayi a Companynmu ya tayar min da hankali fiye da zaton mai zato, na shiga shock sosae da ganinka a matsayin shugaban Companyn mu! Ban kuma tsorata da labarin kaba saidai nayi nayi nayi tamkar mai yin barci da farko amma daga qarshe sai barcin gasken yayi gaba dani, hakan yasa abubuwa kaɗan na fashimta, Why did you go to Kabar Ni?Why did you run away and leave me missing you so much?, why did you run away the second time?who why akan me akan mene!?"
Sai kuma ta shiga wani irin kuka irin mai qona zuciyar nan.
FADEELAH
"Haba momie nikam gaskiya ki bar Ni na koma gidan mijina ai kishi ba HAUKA bane! Toma wai ina ruwan ki da kishiyar da aka min? Ki barni da ita mana idan har baki ga abinda zai biyo baya ba, kawai zan koma gidan mijina da kaina kuma yau! Kai yau ɗin ma ba yanxu ba.
Ni kaɗai yasan irin abinda zan aikatawa duk wacce tayi kuskuren shiga hurumin daba nata ba, domin JALAAL na fadeelah ne ita kaɗai ba qari"
Cike da gatsen ganin ko zata iya tafiyar ne ya sanya momie faɗin.
"To maza tashi kar guɗa ya riga ki"
Ko gama rufe baki kuwa bata yiba taga ta tashi cikin sauri ta nufi upstairs nata, cikin ƙanƙanin loƙaci sai gata tana janye da qatuwar toroly ɗinta.
Directly kuma hanyar fita ta nufa hakan yasan ya momien tashi da sauri tana faɗin.
" Keeee fadeelah ki kiyasheni, banza Bara zuciya, ke yanzu idan akace ki ɗebi qafafunki, ki maida kanki da kanki gidan miji saiki yarda ki koma!"
Ita kuwa irin ko a jikin nan nata ta ɗaga qafarta tare da cewa.
"Whatever you think, that's it mommy"
Tare dajan qatuwar toroly nata tana shirin barin parlourn, Fahad dake tsaye tun farkon fara rigimar tasu ne yayi saurin tare hanyar tare da duban Fadeelahn yana binta da wani irin kallon, dana kasa gane meya ƙunsa ne yasan yata ɗan rusunar da kanta qasa, kome ta faɗa masa kuma ohooo kawai dai naga yana dariya, tare da cewa
"Momie kiyi haƙuri Ni da kaina zan maidata gidan mijin nata"
Sai kuma amshi akwatun hannunta yana ja ita kuma ta rufa masa baya.......
Tofa fan's muje zuwa
Kuyi haƙuri yau ban samu yadda nake soba, naso typing ɗin yafi haka tsawo amma ba komai zaku fanshe wata rana🤓😎
Sai mun haɗe a fage na gaba
Asha karatu lafiya daga taku AMMEY LAYLERH 🥰🫶🏻🫶🏻
Nake ce muku bye 👋🏻
https://chat.whatsapp.com/FZOG6TDjDid2W63LyRn3XP
_______________________________
*💐🌼 JALAAL AREEF 🌼💐*
~💸THE BILLIONAIRE 💸~
A story of pure love that touches the ♥️
*NA AMMEY LAYLERH*
Page 23&24
08104493215
________________________________
♥️🤍♥️
A tsakiyar coumpaund ɗin gidan ya faka motarsa bayan sun shigo get ɗin qarshe na gidan, fadeelah ce ta fara fitowa cikin jiki dakai da taqama haɗi da nuna Isa dajin taka ta taka ko wanne shege ko shegiya.
Directly nasu bangaren ta nufa haɗi da gasawa part ɗin ummie wata kafurar harara, ji take da za'a bata dama tsabbb saita ga bayan matar Nan, amma yanxun ma tana nan sai tayi maganin ta wllh.
Fahad dake jaye da uwar trolyn data sha uban kayane ya sanya shi ɗan cira murya yana faɗin.
"Syster kiyi jirana mana!"
Cakk kuwa ta tsaya ɗin yana isowa suka jera tare da nausawa cikin ainihin parlourn gidan, handle ɗin ta murɗa tare da tura qofar suka shige cikin parlourn, komea na parlourn ta shiga qarewa kallo ganin duk yawanci ba abubuwan data sani bane acikin parlourn bane, wata ƴar qaramar tsuka taja acen qasan ranta.
Tana faɗawa saman sopa tare da sakin ajiyar zuciya mai ɗan qarfi, shima zaman yayi ganin Fadeelahn ta zauna dab da ita ya zauna yana tamyarta, me yasa ta zauna a parlour kuma?, dake ba'a daidai take bane ya sanya ta ɗan juyowa ta kalle shi sai kuma ta ɗauke kanta daga kanshi.
Akayi kuma katari a daidai wannan loƙacin jalaal ya fito daga cikin part ɗin Layla, dummmm taji wata mummunar faɗuwar gaba ta ziyarceta, ganin jalaal D ONLY ɗin nata hannunsa sarqafe cikin na wata, Layla kuwa da jalaal ke riqe da hannuntane ta gama fitowa baki ɗayanta cikin cikin parlourn.
Wani irin tsalle zuciyar fadeelah tayi, ganin wata haɗaɗɗiyar beb tare da mijinta wacce tafi kama da ƴaƴan larabawa, kallon ta ta soma tun daga qasa har sama, wasu haɗaɗɗun riga da wando ne acikinta samfurin qirar pallazo pink color sai rigar ta kasance pitch color inda bajajjen hips ɗinta suka gaba baiyana kansu ta cikin wandon, kanta sanye da irin hular nan mai raga ragar Nan uban shimilin gashin kanta ta naɗe tayi gammo dashi ta cusa cikin hular.
Ko inda suka jalaal bai kalla ba sai ma dawo da laylan shi ɓangaren hannun damarsa da yayi, ganin da wannan bunsurun ɗan akuyar suke, domin tsabbb babu abinda jalaal ɗin bai sani ba na irin bin matan da yake.
Saidai sammm bashi da masaniyar irin alaqar dake tsakanin sa da ƙanwarsa Nafisa, fahad da tunda ya ɗaura idonsa akan Layla bai ɗauke ba har sanda jalaal ɗin ya janye ta ya maida ta ɓangaren damar sa, zai iya rantsewa tunda yake yawan bin matansa bai taɓa ganin koda kwatankwacin irin wannan halittar ba.
Fadeelahnku da tayi suman zaunane yasan ta ɗan jijjaga kanta haɗi da fesar da huci irin mai zafin nan, kardai ace wannan tsinanniyar yarinyar itace matar jalaal ɗin, tabbbb idan kuwa hakan ta tabbata lallei kashinta ya gama bushewa murus ma kuwa. Hakan ya sanyata lalubo wayarta dake jikin jaka, kai tsaye numbern da aka rubuta my blood ta dokawa qira, tanajin anyi picking na qiran ne yasan ya ta cewa.
"Bloody ki shigo shashina ina jiran ki" kit ta datse qiran a kiɗime kafin ta juyo ɓangaren da fahad yake wanda ya riga ya lula duniyar tunanin irin daɗin da zai sha a tare laylan.
{Tofa ikon Allah ikon gaske, wato har ma zai sha daɗi tabbas bubu laifi hakan🤓 idan rabon kaci uwarka ne ke janka a wurin jalaal kuma ai shikenan 🤕🤷🏻♀️}
Ganin idanunsa a rufe ne kuma sai sakin wani irin murmushi yake ne, yasan yata ɗan zungurinsa, cike da juyewar tunani wanda ya lula duniyar tunanin wani abinne daban ya sanya shi faɗin.
"D gaske ina matuqar buqatarta! Kallo ɗaya dana mata amma naji gaba ɗaya hankali na ya gushe,banjin zan iya dawowa cikin hayyacina har sai na samu buyan buqatana a tare da ita fadeelah!"
Cike da takaici take kallon sa Nafisa da soma maganarsa kenan ta shigo, amma bata sami zarrar qarasa shigowa ba ta hanyar jin zantukan da fahad yake ɓararwa, babu wanda yayi tunanin tana wurin.
Hakan yasan ya a gaɗace a zuciye fadeelahn dake duban yayan nata cike da wani irin takaicinsa ta soma cewa.
"To ɗan akuya kaida ako ina saika nuna cewar kai ɗan akuyane, to Bismillah wata kai tama yadda zaka kasance da ita kake ma keñan? Ba tani kake ba, nikam ga gurin nan ai"
A hankali ya buɗe idanunsa ta suka zama ja zawur loqaci ɗaya, ware idanun nasa kuwa tarrr ya sauqe ganinsa akan Nafisa babynsa, suna haɗe ido ta saki wani irin azababben kuka irin mai ciwon nan da tsayawa azuciya, kafin ta juya a guje tana barin bangaren baki ɗaya, hakan yasanya shi miqewa a kiɗime shima ya rufa mata baya shida Fadeelahn har qoqarin buje juna suke, domin ko wannensu akwai burinsa dan gane da nafisar
BAUCHI
Cike da rashin yadda hajja take duban Inna ladiyo.
"Naga akan idanuna kika fita da dijen dake sheqa uban amai, amma har wani ma kice min kema bakisan inda take ba!, kawai dai kice kin kaita azubar mata da ciki, dama ai nasha faɗa miki cewar dije ciki ne da ita amma kika ƙi yarda, yanxu wa gari ya waya?"
Ta faɗi maganar cikin ko in kula gami da ɗage kafaɗunta, irin baida meni ɗin Nan ba.
Cen kuwa bangaren Dr ema idan da abinda yafi kuka to kuwa dije tayi shi, domin Dr ema irin marasa tausayin nan ne kwana yayi abu ɗaya gashi ba sallah yake ba, ko Nan da cenñnn yaqi fita.
Domin dijan ba daga Nan ba ga yabinka da mai qaramin ciki, ni'ima kaɗai koda Inna ladiyo ta saci hanya ta tazo taga ko ina na gidan a garqame da qaton kwaɗo, dake ema irin ƴan duniyar Nan ne shi yasa daya fito saiya sama qofar gidan kwaɗo, ya koma ta cikin shagonsa shima dake me irin gurin rufewar nan ne ta ciki data waje, hakan yasa ya rufe ta cikin, Haka ta haqura ta koma gida jiki a saɓule.
Yau kimanin kwanaki uku kenàn kullum zata saci hanya ta fita zuwa shagon ema amma harwa yau shagon a qarqame, xuwa wannan loqacin idan hankalinta yayi dubu toya tashi, Dr ema kuwa bayan ya gama shagalinsa da dijen ne yayi qoqarin ɓarar da cikin amma ciki sammmm yace bazai fita ba.
Shima hankalinsa ya tashi sosae amma bai faɗa mata ba, saima ci gaba da shagalinsa da yayi cikin kwanciyar hankali.
♥️🤍♥️
Aknan ce zaune tana buga gema acikin wayarta, kamar kuma wacce aka tsikara ta miqe tsaya tare da qoqarin barin ɗakin, dan wllh ta manta shaff da matar yaya bata kuma naimanta ba, hakan yasa yanxu takeson xuwa wurinta dan ita kawai taci matar yayan nasu ta birgeta sosae tare da shiga ranta farat ɗaya,har taje bakin qofar barin parlourn taji maganar mahaifiyarta tana cewa mata.
"Aknan ina zakije kuma?"
"Zanje wurin matar yayana Mommah sammm wllh nama manta ban kuma naiman taba"
Kamar bazata yi magana ba dake Hajiya Turai irin matan nanne masu masifar qaunar ƴaƴansu, sammmm bata yarda da shiga hurumin kowa ba shi yasa ake mata kallon itace asalin muguwar, yayinda ake ma Hajiya Hafsat kallon mutum mace ta gari maison jama'a tare da hada hada da kowa lafiya, amma hakan baya taɓa damun Hajiya Turai tasan loqacine zai bayyana kansa.
Sai kawai ta ɗagama ƴar nata kai alamun taje, murmushin farin ciki ta sakarwa Momman nata tare da barin ɗakin baki ɗaya, tana nufar ɓangaren yayansu kai tsaye.
★★★★★
Hajiya Hafsat dake zaune tana kallo a qatuwar plasma ɗin ne tayi saurin juyowa jin an banko qofar parlourn nata da mugun qarfi, Nafisanta ta gani ta shigo aguje tana wani irin kuka, a kiɗime ta nufeta tana tambayar ta meya faru amma ba amsa saima kawai saman jikinta data faɗa, tana ci gaba da kukan.
Shigowar fahad a kiɗime shine ya kuma tayar ma da Hajiya Hafsat hankali, sai kuma ga fadeelah itama a guje ta faɗo cikin parlourn, hakan ya sanya Hajiya Hafsa a mugun tashin hankali cike da kiɗimewa ta shiga faɗin.
"Me ya faru? Ku faɗa min mene ya faru!?, me akawa Nafisan?"
Itama Fadeelahn jikin maman nafisan ta faɗa tana rungume nafisan, tana sakin nata kukan itama na baƙin cikin abinda idanuwan ta suka gane mata, tanaji idan batayi kukan nan ba hankalinta bazai taɓa kwanciya, ita ita ita FADEELAH JABBER SHETTIMA Jalal zaici amana, ehhhhhhhhh yaci amana mana ta hanyar yi mata kishiya, hakan tada kuma tunanowane yasata qara sakin wani azababben kukan mai ƙona zuciya,
shi kuwa fahad zama yayi akan ɗaya daga cikin sopar parlourn yana sauqe numfashi.
Cikin matsanancin kuka nafisan ta shiga faɗin,
"Mama na yarda dashi amma yana naiman cin amanana, idan na fashimci maganar fadeelah kenàn yayanta manaimin mata ne! Qarya yake min keñan bani ce kaɗai yake naima!, kuma wai kuma kuma"
Sai kawai kuka yaci qarfinta sosae, ita kuwa mama tama rasa yadda zatayi dasune ga fadeelah ga kuma ita nafisar kanta, jin abinda ƴar Tata ta faɗa kuma baisa ta shiga tashin hankali ba saima ɗan soma faɗa da tayi kafin cikin hargowa da hasalowa tace.
"To danya nemi mata sai meye kuma?, ai naga keɗin AURENki zeyi keman nafisa na rasa wacce iriyar yarinyarce ke, ayi mutum ba abinda ya iya sai ɗan banzan kishin tsiya da mugun hali, ayi zuciyarki kullum akan abu ɗaya!, toga guri nan zauna kiyi ta kuka, ku duka kunfi kowa sanin menene burinmu da kuma manufarmu, idan har kukace wannan haukar zaku tsaya saimu zare ku daga cikin tafiyarsu!.
Ai iya Nida Hajiya Asiyan ma zamu iya cika dukkan wani buri namu da qudiri basai daku ɗin nanba, ke kuma fadeelah ba kukane ya kamace kiba ki koma sashenki nasan kishiya da ciwo!, kuma kishiya abar ƙice domin anyi min ba ɗaya kuma kuna ganin abinda kishiyar ta jazamin, waima a hakan ina da ƴaƴan danma, bare ke daba ko ɗayane dake ba".
(Ya ilahi kunji fa wata magana, uwa uwarka mahaifiya wacce tafi kowa na duniyar nan sanin ciwonka, amma wai ai hakan ba komai bane tunda shine zai aureta!, Innalillahi wa'inna ilair raji'un Allah ka mana tsari da irin tarbiyyar irin wannan iyayen.)
Tana qarasa maganar ta janye su daga jikinta tana barin parlourn, domin abinda ya taso mata acen qasan ranta.
Fahad ne ya qaraso wurin su tare da rungumo Nafisan jikinsa, yana manna bayansa da jikinta, yana bata haquri tare da fashimtar da ita ainihin gaskiyarsa, akan qudirin yayar tashi.
Ɓangaren Alh Yusuf mai kaba kuwa, ɗaki na daban aka ware masa kullum yana cikin A/C da A/C, ga zabbi da kaji sune suka zama abincinsa, har zuwa wannan loqacin kuma laylan bata san mahaifin nata na gidan ba, kasancewar ba yawo take ba ga kuma gidan da shegen girman gaske, idan mutum yaga dama sai yayi shekara ma ba tare daya ga ɗan uwansa ba idan yaso, domin akwai tafiya mai ƴar tazara a tsakan kanin ɓangarorin.
Loqacin da akazowa da baffa batun komawa gida yace alan furrr babu inda zai koma cikin wahalar nan, shifa yace ko mai gidan gidan nema a bashi amma babu batun komawa BAUCHI, daƙyar da suɗin goshi JALAAL da UMMIE suka rarrashi baffan yace ya yarda zai koma amma da sharaɗin zai dawo kuma gidan gaba ɗaya da zama.
Jin ya yardan ne yasanyasu amincewa, domin kare mutuncin ƴarsa Layla tunda a babban gidane suke kana gata da kishiya,sun tabbata idan har maganar ta fita wajen gidan, to kuwa tabbas babu makawa da wannan abin ma kaɗai saiya gagareta zaman gidan baki ɗayansa, hakan ma shine yasa sammm suka san duk yadda sukayi suka tsare duk wani hanyar da suka san za'a gano da surukin nasu acikin gidan, kuma wai da sunan ZAMAN LAFIYAR zai yiwa ƴarsa.
Da ƙyar da wayo haɗi da lallami suka lallaɓa baffan zai koma gida.
Ai kuwa cikin SIRRI aka maida baffan BAUCHI bayan Jalaal ya bashi maqudan kuɗaɗen dashi kansa baima san iyakar saba, yace yaje da wannan kafin yazo daga baya.
Da haka aka shawo kan baffan laylan, har ya yarda ya koma BAUCHIN Yakubu.
Aknan
Cike da nutsuwar ta nufi part na laylan kai tsaye, ahankali ta murɗa handle na qofar tare da turawa ta shiga. Babu kowa a parlourn hakan yasan yata jan burki, ganin babu yadda zata yine yasan yata zama acikin parlourn kamar ta qira yaya jalaal kuma tana ɗan jin tsoro, domin ba kasafai suka fiye qiransa ba.
Dan suna masifar shakkar sa kammm babu laifi, tana zaune a inda take kusan mintuna goma sha biyarne taji kamar ana saƙƙowa ne, hakan yasan yata ɗago kanta Jalaal ta gani yana saƙƙowa daga upstairs nashi, saida ya gama saƙƙowar ta gaidashi tare da miqewa tsaye bayan ta gama gaidashi ɗin, duban ta yayi tare da cewa
"Why are you living here?"
Cike da nutsuwa tace
"Nazo na gaida Aunty bane"
Ɗan duban ta yayi sanin basa wani yi da fadeelahn amma saiya kawar da hakan tare da ce mata
"Look at her side, I see she's back"
Ita kuwa ganin kamar bai fashimci abinda take nufi bane yasan yata faɗin "Aunty Layla fa yaya"
Cakkkkk ya dakata da fitar da yayi niyar yi, saida yaja numfashi kafin ya mata nuni da ɓangaren da take, cike da zumuɗi kuwa tayi ɓangaren da ɗan saurinta.
Layla dake tsaye gaban wadrop nata tana son ta shirya, taje ta gaida ummiene taji an faɗo jikinta, tare da rungumesu cikin wani irin farin ciki aknan ta shiga faɗin
"I miss you Matar yaya"
Murmushi kawai Layla tayi domin ta riga ta gane ko wacece, amma dan ta kuma tabbatar wA sai tace "Aknan ko" kanta ta gaɗa mata tare da sakin ta tana faɗin, "wallahi shaff mantawa nayi da batun ki Aunty Layla" ita dai Layla murmushi kawai take saki domin yarinyar ta masifar kwanta mata arai, haka nan take jin qaunarta tamkar wacce suka fito ciki ɗaya.
Bayan ta kammala sanya doguwar rigar materials ɗin daya gama amsar jikintane,tace suje ta rakata ta gaida UMMIE, babu musu kuwa taja hannunta suka fita kai tsaye ɓangaren ummien suka nufa bayan sun gaisa ne ummein tace ma aknan ta raka ta duk sauran bangarorin gidan.
Haka kuwa akayi gaba ɗaya ta rakata duka sashinan gidan suka gaggaisa, kuma duk aqafa suka zaga saidai ummie tace ga mukullin motar ta su baya direba ya kaisu, amma Laylan ta ce a ahh ta barshi suke ta qafafunsu, a ganinta duk ana gida ɗaya harma ace sai anhau wata mota.
Babu laifi kuwa sun gaisa da kowa cikin mutumtaka, kuma kowa yayi qoqarin ganin ya bata Gift wanda aknan ke amshe mata, domin ita kammm taƙi amsa.
Suna fita daga ɓangaren Hajiya Hafsat taja wani uban tsoki, tare da cewa "shegiya mai kama da SADAKA YALLA, wo irin wannan kyau haka wama ya sani ko mayyace, rana a tsaka ta shigo cikin target nasu da yake gabb da kammaluwa amma ba komi ita ɗin ma ba gagara zatayi ba ai kammm"
Sai kuma ta lalubi wayarta tare da dokawa babbar aminiyar , aqalla sunyi maganar data kusan zanrce mintuna arba'in kafin suyi sallama da juna.
Inna ladiyo
"Innalillahi wa'inna ilair raji'un, likita kace mene ba zai meba!?, bazai fita bada kaceeeeee"
Kamar daga sama taji Muryar data kusan zauta tunaninta ana cewa.
"DAMAaaaaaaaa"
Tofa mene yake shirin faruwa Ni ƴar Nan?
Kaiiiiii gaba ɗaya kaina ya gama kullewa. Yachinnnnn.
Nayi cenñnn 🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🚶🏻♀️🚶🏻♀️🚶🏻♀️😅🚶🏻♀️
*By AMMEY LAYLERH*
https://chat.whatsapp.com/FZOG6TDjDid2W63LyRn3XP
____________________________
*💐🌼 JALAAL AREEF 🌼💐*
~💸 THE BILLIONAIRE 💸~
A story of pure love that touches the ♥️
*NA AMMEY LAYLERH*
Page 25&26
Wannan fejin nakune
Kyautarsa aka baku sukutummm👐🏻
*ASHANTY Love*
*Mom sani Mommah Naaaaaa*
*Sis REEMAH*
*Maman mubina Dashen Allah*
*GIMBIYAR JARUMAI FAWANA*
*Hauwa Musa Rijau*
~Kuyi yadda kuke so dashi~
_____________________________
♥️🤍♥️
"Dama duk wanda yake tukunyar wani bazai tafasa ba, to kuwa tabbas nashi ko ɗumi ba zai yiba, ita kuma dama wata SAKAYYAR tun Anan gidan duniya Allah yake bayyana maka iyaka matsayinka"
Tamkar saukar aradu
Haka Inna ladiyo ta ji yo wannan munanan kalaman daga gudan jininta lauwali, wanda yake tsaye daga bayanta cikin kamilalliyar shiga, domin tasha banban da irin wacce kuka saba ganinsa, yana tsaye daga bayanta cikin kamilalliyar shiga domin tasha banban da irin shigar da kuka saba ganinsa, yana cikin wata jallabiya ruwan sararin samaniya da carbi riƙe a hannunsa yana ja, wanda dukkan alamu suka bayyana cewar ya shiryu ne.
"Kin cucutawa rayuwar mutanen da basu ji ba basu gani ba, kin ƙuntatawa rayuwarsu! Kin jefi ƴarta da mugayen kalamanki Inna!, Inna miye duk meye wannan ɗin? Kince ƴarta ƴar kwaltace gashi Ubangijii ya nuna miki iyakar ki tun Anan gidan duniya ma kenàn, ki duba irin mijin da LAYLAH ta aura wanda kusan ko ina ansan shi ansan waye shi, ansan kuma waye ubansa acikin qasar nan, ke kuma ga naki sakamakon nan a gabanki.
Dubeni da ƙyau da yanxun ɗaya suke a wurina?, Na zama cikakken mutum sanadiyyar su waɗanda kika ɗauka tsanar duniyar kika ɗaura musu, A ranar ɗaurin Layla naje wurin a buge domin inason na halarci ɗaurin auren laylan, domin sune mutane na farko da suka taɓa nunamin nima cikakken mutum ne mai daraja, shi yasan ya duk wani abu nasu nake kaffa kaffa dashi nake kuma ankare da komi nasu, a ranar mijinta wanda son banzarku ya bashi, to dama ku sani a duniy@ ko wanne shege yana da wanda yafi shi iya shegan takar, yayi amfani da mugun kuɗiri da kuma nufinku akanta yazo muku naiman aurenta a matsayin TALAKA!, TALAKA ƘASƘANTACCEN da kuke ta aura!"
Sai kuma yaja numfashi tare da fesar da iska mai zafin gaske, zuwa wannan loqacin kuwa wata kafurar zufa ce ta shiga karya kowa Inna ladiyo, jin irin zazzantukan da suke naiman tasar kanta.
"Wannan dai TALAKAN FAƘIRIN ƘASƘANTACCEN da kuka tawa dariya, shine JALAAL AREEF THE BILLIONAIRE 💸 ɗaga tsohon shugaban kasar mu AREEFULLAHI MUHD MAI NASARA, wanda yanxu yake a matsayin miji ga ƙanwata MARYAM YUSIF
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 22