Layla kai tsaye.
Tana cikin toilet kuka kawai take yi domin a duniya ta tsani taji anciwa iyayenta mutunci, a sanyaye ya shigo cikin bedroom nata, ganin bata nan ne ya sanya shi nufar toilet ɗin ɗakin sheshsheƙar kukanta ya jiyo hakan ya sanya hankalin sa idan yayi dubu toya tashi, bubbuga qofar toilet ɗin ya shiga yi amma sammm taƙi buɗe masa safaya key nashi ya ɗauko tare da buɗe toilet ɗin tana zaune dirsham a tsakar ban ɗakin tana rusar kukan. Cilak jalaal yayi sama da ita tare da mannata da jikinsa yana sakin wata iriyar ajiyar zuciya.
Ruwan Shower mai sanyi ya sakar musu hakan ya sanya layla shigewa cikin jikinsa, tare da sakin wani wahalallen kuka wanda kawai ji tayi yazo mata, bawai wanda take yi ɗin bane itafa Idan ma har hancin ta ba qarya yake mata ji tayi kamar yana qamshin tularen mata.
{Wooo laylerh kishi lol🤓😱 A ina kika jiwo qamshin tularen matan ajikinsa?"}
Lallausan sajen dake kwance fuskarsa ya shiga goga mata akan gefen fuskarta cikin wata kasalliyar murya yace.
"Pls kiyi shiru kinsan kuwa yadda nakejin zafin kukan nan naki acikin qirjina?, Who knows what kind of pain I feel in my heart ? "
Sai kuma kawai ya ya haɗe bakinsu wuri guda yana bata wani irin birkitaccen kiss, wanda ya sanya layla shigewa cikin jikinsa babu shiri, don ji tayi tamkar tare da ranta yake shirin tafiya.
Haka dai ya mantar da ita damuwar data ke ciki cikin wata narkyakkiyar muryar da yayi amfani da ita yace mata.
"Pls get ready tomorrow, God willing, around six o'clock we have a flight to Egypt"
A makan kance maganar tazo mata domin ko akanta bata taɓa kawoma kanta hakan ba, hakan yasan ya ta faɗin.
"And I, even if you forget who you are with?"
Qara shigar da ita cikin jikinsa yayi loqacin da yake tafiya da ita akan qafafunsa, xuwa cikin clothers nata wata duguwar riga mai ɗan kauri ya ɗaukko mata tare da cewa.
I want to know who I am with, because she is the link of my life."
"Hmmmmmmm"
Kawai ta iya faɗi loqacin da ya rabata da rigar jikinta, saurin faɗawa jikinsa tayi ganin hatta bra nata bai bari na ya zare mata, shi kuwa ko a jikinsa haka ya cire mata komai tare da sanya mata wanda ya ɗebo mata.
Kwantar da ita yayi shima ya koma cikin clothers ɗin yana ɗebe wasu riga da wando na barci tare da sanya wa ajikinsa, kai tsaye gadon ya haye tare da janwota jikinsa yana ja musu duvet ya rufe su.
******
Washe gari shine ya ɗan dibar mata abinda yasan tana da buqata kawai amma bai ɗauka kaya ko kala ɗaya ba, domin baya da buqatar hakan shi da kansa zai sai mata idan sun je cenñnn ɗin.
Cikin sauri sauri gudu gudu ya nufi bangaren mahaifiyarsa tare da qara mata sallama duk da cewar sun riga da sunyi sallamar jiya.
Yana qoqarin tashi tashi ya tsinkayi muryan ummien tana cewa
"Ina yarinyar nawa kuma?"
Gashin kansa yaɗan shafa tare da faɗin.
"Saida nace tazo kuyi sallama tace wai ita kunya take ji"
"Ƴar mutunci kenan ai dole taji kunya tunda kai baka data IDO, har ka dubi tsabar idonuna kace min yawon cin amarci zaka tafi"
Suka tsinkayi Muryar Hajj Mama.
Shi kuwa jalaal cike da rashin son hayani yau ɗin ya dube ta yana cewa "kawai kimin fatan Alkhairi "
"Ɗan nema ungo wannan ka bata domin zaiyi muku amfani, ko daga baya na qiraku na faɗa muku yadda za kuyi dashi"
Cikin sauri ya amsa yana shirin fita da sauri ummie ta miƙe tana nufi jalaal tare damka mishi wata leda madaidaiciya a hannunsa "ka bama LAYLAH" dake sauri yake shine abinda ya yana shi maganar da yake son yi kawai ya wuce da cikin sassarfa a inda ya barda tsaye yaa kuma samunta hannunta ya kama kawai suna barin wurin.
Cikin private jet nashi jirgin su ya lula xuwar qasar masu jajayen kunnuwa,ance hajja mama Nina na ɗan ɗana.
✈️🛫🛬✈️🏞️🌌 Haka inaji ina jirgin su ya ɗaga xuwa qasar EGYPT.
Saidai mu musu fatan sauqa lafiya.
Na ke ce wa mu haɗe a page na gaba
*By AMMEY LAYLERH 💫✨*
https://chat.whatsapp.com/FZOG6TDjDid2W63LyRn3XP
___________________________________
*💐🌼 JALAAL AREEF 🌼💐*
~💸 THE BILLIONAIRE 💸~
A story of pure love that touches the ♥️
NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
Page 31&32
*~Story planning and writing ammey laylerh ✍️~*
_______________________________
♥️🤍♥️
Tafiyar Awa huɗu ce ta kaisu qasar EGYPT. Loqacin da jirgin su ya fara landing na sauqa da wani irin sauri Layla ta damki damtsen hannunsa, tana qanqame shi gamm acikin qirjin ta gaba ɗaya ya shigar da ita cikin jikinsa, ganin kamar a tsorace take yana sakin Ajiyar zuciya da haka har jirgin su ya kammala sauqa.
A hankali ya fesar da sassanyan numfashi loqacin da jirgin su ya daidaita tsayuwar sa a qasar Egypt ɗin, hannuwansa cikin nata ya fara taka step na farko wanda ya fito da kansa sararin garin Egypt ɗin, cikin nutsuwa da kwanciyar hankali Layla ta shiga qarema garin Egypt ɗin kallo.
"Ya ilahi"
Layla ta faɗa jin wata iriyar ni'imantacciyar iska na ratsa dukka sassan jikin ta, wani irin amintaccen numfashi mai cike da yanayin sauqe ajiyar zuciya ta shiga sauqewa, wani irin rumtse idanunta tayi jin wani irin sanyin daya fara ratsa ilahirin jikinta, matsa jikin nata tayi wuri guda, tana kuma shigewa cikin jikin jalaal. Cikin sanyin daya fara ratsa jikinsa shima ya shiga ɓalle aninayen gaban jacket ɗinsa gaba ɗaya ya qarasa rungumo mota jikinsa yana maida gaban rigar nasa ya rufe ta rubb acikin rigar sanyin dake jikinsa, kasancewar dama tun daga cenñnn gida ya ziro abarsa, dake ita ba ma'abociyar sanya rigar sanyi bane loqacin dayace ta sanya rigar qiya tayi tace bata so, domin batayi zaton irin sanyin da zata zo ta taras ba keñan.
Wasu haɗaɗɗun motocine suka Parker a gabansu, wanda ke ɗauke da harufan L & J ɗoɗar ajikin dukka motocin, inda suke ɗauke da welcome mr & Mrs JALAAL AREEF Cikin wani irin salon qawatuwa. Kai tsaye motar da aka buɗe musu ya shiga har loqacin kuwa Layla na manne da jikinsa, cikin qanqanin loƙaci suka isa qayatacciyar anguwar da jalaal yake da zama. L....IN MY LIFE mentioned 9j, haka ta gani rubuce a bakin qaton get na gidan, hong suka shiga dannawa tuni get man ya buɗe musu get ɗin gidan.
Inda su kuma suka cilla hancin motocin su cikin tsararren gidan, Saida ya tabbatar sun daidai ta parking na cars nasu kana ya ziro qafafunsa zuwa wajen gidan, ni'imantaccen ƙamshin furanni daya shaqa ne ya sanya shi ware birkitattun idanunsa ba shiri, "Ya rabb" ya furta Ahankali jin wani irin baqon yanayin daya tsinci kansa aciki sanadiyyar qamshin furannin daya shaqa.
Cikin kamewa da son kawar da abinda yake ji yayi qoqarin ganin ya danne hakan, hannunsa ya sanya cikin nata tare da miqar da tsaya ta hanyar qara fitowa da ita daga cikin motar, da kasancewar taɗan jigatune acikin jirgin duba da wannan shine hawanta na farko, kai doguwar tafiya ba zata iya rantse bata taɓa yinta ba, hakan yasa a galabaice take tana ida fito tayi tangal tangal tana qoqarin zubewa a wurin, da sauri babban yaronsa yohan yayi qoqarin taro ta kasancewar shine a bayanta.
Wani irin mugun kallo ya wurgama yohan ɗin tare da ɗaukar matarsa cilak yana yin cikin gidan da ita kai tsaye, saida ya tsaya ya sanya security na mashigar kana qofar ta buɗe. Ya sanya kansa cikin ainihin parlourn gidan, cikin tafiyarsan nan na ƙasaita yaci gaba da tafiya da ita tamkar wata jaririya ajikinsa directly bedroom nashi ya nufa da ita.
Akan qayataccen gadon sa wanda ya gaji da haɗuwa ya shimfiɗe ta, toilet ya wuce kai tsaye ruwan wanka ya haɗa musu masu ɗumi da qamshi, Ahankali ya shiga ɗan shafa saman kuncinta ware lumsassun idanunta tayi tare da sauqe ganinta akan jalaal dake ɗan rankwafe daga saman kanta, wanda har yanzu yake qoqarin ganin ya danne tsananin peelings ɗinta dake taso mishi.
Kayan jikinta ya shiga zame mata yana ɗauke kansa daga gare ta ganin saura daga ita sai fant da iyaka bra suka rage a jikin tane, ta sanyata saurin cukuwkuye jikinta da zanin dake shimfiɗe saman gadon.
Wani irin murmushi ya saki mai cike da ma'anoni daban wanda shi kaɗai yasan ma'anar kayansa, babu zata kawai taji anyi sama da ita bai zarce ko ina ba sai cikin toilet , cikin bathtube ɗin dake cike taff da ruwa ya sanya ta yana barin cikin toilet ɗin.
Wankanta tayi cikin kwanciyar hankali domin sosea ruwan ya mata daɗi, saida ta gama wankan kana ta rasa abinda zata dau ra ajikinta , sai iyaka wasu guntayen towel dake rataye jikin hanger. Jalal dake tsaye dab da jikin qofar ne yaji shirun yayi yawa ne ya sanya shi yin Knoking, a kiɗime tace "pls taima kamin da rigan dana cire zan fito"
"Akwai towels ki duba"
Shine kaɗai abinda yace mata bakinta ta ɗan turo gaba tare da cewa.
"Duk sunyi qanqantane ai"
Wani kafurin murmushi ya saki yana cize saman laɓɓansa tare da danna kansa kawai cikin bayin. A razane tayi baya tana wawurar towel ɗin tana kare saman qirjinta, ganin wani wurin daban yake kalla ba qirjin nata bane ya sanyata bin inda ya zubawa idon.
Wani razanannen ihu ta buga tare da daka uban wani tsalle tamkar biranya tana barin toilet a guje, kai tsaye wajen kayansu tayi amma duban duniya ta rasa kayan ta, gaba ɗaya ta zazzage jakar amma babu kayanta sai wasu guntayen kayan barci kawai a aciki, tana Nan zaune harya fito ɗaure da towel ɗan madaidaici daure a qugunsa.
Ganinta zaune ya bashi mamaki jin alamun motsin sane ya sanya Laylan juyowa ta dube shi, da sauri ta ɗauke kanta daga gareshi ganin ba kaya ajikinsa, shi kuwa ko a jikin sa saima tambayar ta da yayi.
"What are you doing until you're ready?"
Cike dajin haushin abinda ya mata tace.
"Since you brought me the clothes to prepare this"
Shifa sai yanxun ya tuna da bai taho mata da kaya ko kala ɗaya ba, gaban wadrop nashi yaje ya tsaya yana qarema kayan kallo, da wata coffee colour jallabiya yaci karo wacce ya siyo ta tamai kaɗan janyo ta yayi yana nufo wurinta da ita tsaye ya miqar da ita tare da zira mata jallabiyar wanda da kaɗan ta mata yawa kasancewar dama sabuwa ce ya saya, bai kuma taɓa amfani da ita ba.
Ita dai har yanzun taƙi tayi magana cikin sauri sauri gudu gudu ya shirya cikin wasu riga da wando masu azabar ƙyau, landline ɗin ɗakin ya ɗauka tare da yin magana ataƙaice ya musu order na abinci , komawa yayi saman sopa yana kwantawa babu daɗewa aka danna karaurawar neman izni, a kasalance ya miqe ya amso musu abincin yana dawo wa ciki ajje musu yayi ya samo musu plate ya zuba musu sukaci abincin a tare, qiran sallar da akayi ne ya sanya shi fita ita kuma ta shiga bayi ta ɗaure alwula.
Sai bayan sallar isha'i ya shigo gidan hannuwansa dauke da manyan ledoji, da sallama ya shigo ɗakin acennn ƙarshen Carido na ɗakin ya hangeta tana saman darduma, Alqur'ani ɗauke a hannun ta tana bitar karatun Alkur'ani mai girma.
Ledojin ya zube akan canis carpet ɗin dake malale da wurin, tanajin wani irin daɗi marar misaltawa acikin ransa wai yau shine ake karanta Alqur'ani mai girma acikin gidan sa, lallei Allah shine abin godiya daya azirtashi da samun mace kamar layla a matsayin matar sa ta sunna.
Zama yayi yana ciro wani kwalin waya ya ilahi wata damfareriyar waya ya ciro qirar Samsung Galaxy S24 , in banda dauqar idanu babu abinda take yi sai faman walqiya kawai take.
Ayar qarshe ta dire acikin suratul Ahqaf.
Rufe Qur'anin tayi tana linke dardumar tare da nufo wurin da yake zaune, zama tayi ɗan nesa dashi kaɗan tare da cewa "Barka da dare"
Bai ɗago daga abinda yake ba yace mata.
"How are you doing tonight?"
"Lafiya alhamdulillah"
Ta amsa tana tonƙoshe ƙafafunta ɗan dubanta yayi tare da ce mata .
"Help us with the dishes in the kitchen"
Tsammm kuwa ta miqe tana nufar kitchen ɗin tare da ɗauko plate ɗin kamar dai yadda ya buqata, tana kuma zama .
Plate ɗin yaja gabansa yana juye Hot chicken ɗin, sai kuma ɗayar ledar dake ɗauke dasu picanto, pizza, dominos, don yasan iyaka su ne kaɗai abubuwan da zata iya ci, sai dafin kayan ciki mai ɗan ruwa ruwa.
"Bismillah ready eat"
Ya faɗa yana tonƙoshe ƙafafunsa shima tamkar yadda tayi ɗin, Bismillah tayi suka fara cin abincin cikin nutsuwa. Bayan sun kammala cin abincin ya janyo musu gorar madaran shanu mai ɗumi suka kora da ita, brush suka yo tare da da komowa cikin ɗakin kwanciyar ta tayi shi kuma saida ya tsaya yayi wasu ƴan ayyukansa don gobe ne suke da muhimmin meeting ɗin da suke dashi, sai wajajen sha biyu da wani abu kana yayi switch na laptop nashi, tare da haurawa saman gadon yana kwanciya bayan ya tofesu da adda'oi.
Jikinsa ya janyo ta yana rungume abarsa a take shima barcin yayi awon gaba dashi.
♥️🤍♥️
Eleven o'clock in the morning
Mr colonel abied, Mr ajied titian, VP president, S akeel, Mr Rogers, Mr cillians. Su wajejen Ashirin da biyar ne acikin qayataccen ɗakin taron wanda suka tara dukkan wasu manyan tycoon na qasashen waje duk son su da birinsu nason suga sun haɗa hannu da JALAAL AREEF ɗan ƙasar 9j.
Cikin irin zallar kwarjinin da Ubangijii (S. W. T) yama sa ya ke ratso tsakiyar taron TUNI kowa ya shiga cikin nutsen sa tare da kamewa, domin JALAAL yana da wani irin baiwa da kuma kwarjinin da yasa sammm abokan kasuwancinsa basa iya fuskantarsa su kawo masa wargi cikin al'amurransa, cikin nutsuwa ya bi ɗan wani Carido take ya bayyana cikin wani zagayayyen glasses irin mai narai narai ɗin nan yana zaune ya hakimce cikin wasu rantsantstsun Suit coffee colour ya ɗaura qafa ɗaya kan ɗaya fesar da iska yayi mai ɗan zafi, yana jin kansa tamkar ba daidai yake ba.
Microphone ɗin dake saqale a ajikin maɓallan gabar rigansa ya yadan hura tare da furta.
"Peace b upon you"
A take manyan ƴan jaridu suka tattaro duka attention nasu zuwa gare su domin tattauna wace mai zafin gaske za'a gudanar, hakan yasan ya wasu daga cikin producer's ɗin suka ɗakko ƴan jaridu domin haskaka musu irin babbar nasarar da suka yi na zama da suka samu da JALAAL AREEF MAI NASARA. Shi kansa baima san da wannan shirin nasu ba.
Gaba ɗaya amsa shi sukayi cikin amintaccen harshen English suna rusuna kawunansu qasa halamar bada girma, domin qasashen waje badai sanin daraja ɗan Adam ba, za kaga duk tsufan mutum idan har yana qasa dakai a wurin aiki duk qanqantarka zakaga ya rusuna maka.
Gaba ɗaya wurin ya ɗauki wani irin shiru, wanda kuma already ƴan jaridun har sun fara record na abinda zaman nasu zai wakanar
Tamkar daga sama tamkar sauqar rugugin aradu haka suka ji kalaman daya furta.
"*Sunanta LAYLERH! Laylerh!! SHE IS THE ONE I LOVE I WANT THE WHOLE WORLD TO KNOW!, Yeah's Inason gaba ɗaya duniya tasan cewa. LAYLERH ce LAYLERH CE LAYLERH CE in my heart ♥️. Shi is the best no! The bestest*"
wanda hakan yasa suka qara daidai ta natsuwansu wuri guda tare da qara seta cemara recordings nasu, domin sun tabbatar wannan abu ba qaramin nasarori zai janyo musu ba. An zauna da JALAAL AREEF THE BILLIONAIRE domin tattauna babban kasuwanci tare da manyan tycoon na sauran qasashen waje.
Saitin zuciyarsa ya dafe tare da lumshe firgitattun idanunsa da suka sirka alamun ja acikin su, ga wani ruwa ruwa da ƙwayar idaniyarsa ta tara.
Ayanxun kammm ya gasgata tabbas ɗaukarsa ake amma kuma bai wani damu da hakan burinsa kawai ya bayyana ma duniya iriyar tsananin ƙaunar sa gare tare da amintacciyar soyayyarta gare shi, aqalla saida yaja wasu mintoci kafin yaci gaba da faɗin.
*"I myself do not know her love for me! I just know that I love her so much since I didn't know who she is! I also love her very much. Gaba ɗaya rayuwana na tashi ne da tsananin qaunar LAYLERH yarinyar da kullum itane mafarkina burina muradinah!"*
Sai kuma ya ya shiga wani irin mutsurtsuke hannuwansa tare da dunkule su wuri guda sai kuma ya ware gaba ɗaya GIRMAN IDANUNSA baki daya, wanda suka yi wani irin rinewa duk juriyarsa da taurin zuciyar sa yaukam ya gaza iya control na kanshi.
Gaba ɗaya tamkar wasu jakuna ko mace wani statu ko photo haka suke bin jalaal da wani irin kallo, inda suke cike da tsananin mamakin dama wai a NIJERIYA ana samun irin waɗan nan mutanen waɗanda suka san darajar soyayya har haka?.
Tambayar da sukewa kansu kenan cikin abinda bai wuce 3 minutes ba wani tunani yazo kan Mr. Roger's tamkar wanda aka bama umarni haka ya tsinci kansa da furta.
"L.....IN MY LIFE, That's if I understand correctly L.....IN MY LIFE "
Kansa yayi saurin ɗagowa tare da zubawa mr. Roger's jajayen idanunsa hakan da yayi shine dalilin daya hana Mr Rogers qarasa zancen nashi, domin ba qaramin kwarjini da tsoro kallon da JALAAL AREEF ya bashi ba. Kansa ya shiga jujjuyawa tare da tallafe kansa yanajin wani irin ciwo daga cenñnn qasar zuciyarsa.
*"L, LAYLERH, IN MY LIFE, ITANE RAYUWA NA, komi da komae nawa L... IN MY LIFE! Sabo da ITANE RAYUWA NA MARYAM YUSIF MAI KABA soyayyarta itane sanadiyyar bugun numfashi na, amma hammmmmm "* sai kawai ya kife kansa akan ɗan lig ɗin dake gabansa wanda sauqar ajiyar zuciyar sa kawai suke ji, cikin son fusgo maganar dake ɗanqare a cikin qirjinsa ya ɗan jijjaga kansa.
*"UMMIE Naaaaaa! Ita kaɗai ne tasan iriyar baqar azabar dana sha sai kuma mahaifina kafin rasuwarsa, I cried, I nursed, I did things I don't know how many times I have done it because of my love for her."*
Sharrrrrr haka yana ji yana gani hawaye suke zirato daga cikin idanunsa, bayan hannunsa ya sanya yana sharce hawayen, cikin sauri mr Rogers ya miqe yabi ɗan dogon caridon da Jalal yabi hanka ya bashi yana komawa wurin zamansa shi kuma, bayan ya amshi hanka ɗin ya tsane hawayen dake sauqo masa ya kuma fuskantar su sosae tare daci gaba da faɗin.
*"I CAN'T LIVE WITHOUT YOU LAYLERH!, I am myself I don't know what kind of S0 do I do LAYLERH!!, I just know that I love you with all my heart ♥️ and soul LAYLERH INA INAAAAA IN"*
Sarqewar da yayi ne ya sanya shi tsagaita wa da maganar da bai gama qarasa ta ba.
Tuni turawan dake Zazzau ne suka fara tafa masa tare da jinjina masa suna wani irin Yaren su da ko za'a karni bansan mene suke faɗi baaaaa.
Gaba ɗaya dai wurin ya kaure da gwala-gwalantasu nacen haka.
Su kuwa ƴan jaridu harsun fara baza duk wani abu daya faru, ta hanyar haskawa a gidajen television, kan kace mene gana ɗaya ko ina ka gimla a yankin qasar EGYPT wannan video ake kalla na JALAAL kasan cewar shi sananne, duba da yanke yake da rassa da dama acikin qasashen wajen, qaton BEACH RESORT nashi kuwa ya zam shine lamba ɗaya a qasar ta Egypt
∞∞∞Ω←↑→↓
Cike da matsanancin gudu motocin nasu suke shigewa ganin yadda mutane suke son haɗa musu traffic a hanya. Kuma suma sun tabba wannan videon shine abinda ya sanya mutane suke son haɗa musu traffic ɗin, don kawai suna son ganin jalaal ɗin.
Shi kuwa jalaal tun lokacin da Rogers yazo ya ciro shi daga kifa kan da yayi akan leg chain ɗin bai kuma koda gigin buɗe idanunsa bane, har xuwa lokacin da aka sanya shi cikin car nashi bai yarda ya buɗe idanunsa ba har zuwa yanzun kuwa da suke sharara uban wannan gudu.
Hong ɗin dayaji suna dannawa ne ya bashi damar fuskantar sun iso gida keñan, bayan an buɗe musu get suka danna hancin motocin su cikin gidan, saida suka kammala parking da ƴan wasu mintinan ya samu zarrar iya ziro qafafunsa waje, sai yanxune yaa sami kwarin gwiwar buɗe idanunsa, wanda suke nan har yanzun.
Cikin tafiyar sassarfa ya nufi ainihin cikin gidan kai tsaye, handle ɗin qofar ya tura tare da sanya kansa cikin wargajejen parlourn nasu, da wani irin masifar qarfi laylerh ta faɗa Jalaal tana shigewa cikin jikinsa baki ɗayanta, kafin ta saki wani irin wahalallen kuka mai tsayawa aran nan, tana faɗin.
*"Me ya sa I'm the only one who did this ko ance maka niɗin bana sonka ne? Or is it said that I have a need for the world? Me ya sa kayi hakan me ya sa? Me ya sa!?"*
Sai kuma ta shiga dukan qirjinsa tana faɗin.
*"Kayi duk yacce kake son yi dani! Niɗin mallakin kace halaliyar kace wanda dubban jama'a suka shaida auren mu,Since the day I put my eyes on your body, I know that it is you, saidai bana da tabbacin cewa kaidin dana sani a da ko a yanxun da banbanci ashe ba haka bane ba haka baneeeeee "*
Sai kuma ta shiga qoqarin zare jikinta a nasa, ɗumin abinda taji yana sauqa saman wuyan tane ya sanyata ɗago kanta,
"HAWAYE KUMA, again bayan wanda kayi acennn uyummmmmmmm mene dalilin zubarsu a yanxun kuma?"
Shi kammm baya da bakin magana domin shi kaɗai yasan iriyar baqar azabar daya sha na danne tsananin azabar sonta acikin RAI da kuma RUHINSA, kawai qare matseta yayi cikin jikinsa tare da ɓalle aninayen dake jere a gaban rigarsa, rub ya shigar da ita cikin ainihin jikinsa, inda fatar jikinsa da nata fatar suka mannu wuri guda, sai kawai ya kife kansa akan wuyanta ya shiga takawa da ita, xuwa cikin bedroom nashi.
*FADEELAH*
Cike da wani irin tashin hankali tayi sama da wayar dake riqe a hannun ta tana sakin ta qasa, cike da wani
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 22