idanuwan tare da buɗe su Ahankali, a take komae daya faru da ita ya dawo kanda da wani irin sauri ta rumtse idanunta tare da buɗesu tana ambaton sunayen Allah a qasan ranta, hasken data gani ne ya bata tabbacin cewa lallea safiya tayi keñan.
Qaton mutumin dake tsaye kanta ne ya buga mata tsawa ganin kamar bata san da wanzuwar sa a wurin ba, da sauri ta dafe saman mararnta da taji ya harba mata, sai kuma ta dube shi a jigace tare da cewa. "INASON zanyi sallah". Shine kaɗai abinda tace dashi domin shine kaɗai abinda take son yi, a tsawace yace mata, "ubanwa kika fi sanin Allah kuma" kanta ta kawar gefe domin tana jin ne tamkar ta kikkifa masa mari.
"Don Allah"
Shine kaɗai abinda ta kuma ce masa, da hannu ya mata nuni da wani ɗan corridor, daƙyar ta mike domin qafafunta sunyi mata mugun tsami. Bayan da idar da sallah ta fara azkar nata kamar dai yadda ta saba, wajajen 10:30am tana zaune a idda take wasu samudawan mutane suka danno kansu cikin ɗakin, ko wannensu yana riqe da manyan gunsa a hannunsa.
Gaba ɗaya zagaye taga sunyi bi ma'ana sunyi mata ƙawanya keñan, kanta dake duƙe ta ɗago tana qare musu kallo cikin dakewar zuciya da taurin rai irin nata ta dubi waɗannan manyan samudawan, tace musu
"Su wa ye ku? Me kuke nema a wurina? Sannan mene haɗin ku dani??"
"Basu ke da haɗi dake ba, Ni! Ce Nan wadda ya kamata kima wannan tambayar tsohuwar karuwa, tunda har kika san yadda kikayi kika rabani da MIJINA Abin sona!"
Wani irin murmushi mai sauti tayi domin ta fuskanci ko waye, tare da juyowa xuwa gare ta tana kanta idanunta suka faɗa cikin na fahad da tunda suka shigo ɗakin ya qureta da wasu matsiyatan idanunsa.
Kafin Ahankali idanunta suci gaba da sauqa akan duk mutanen dake jere daga tsakiyar ɗakin. Momin Fadeelah, Maman Nafisa, fareeda, fahad, Messi, susu biyar ne cifff, inda matan suke cikin shiga ta alfarma amma banda fadeelah wacce ta tsuke cikin wasu ɗamammun riga da wando baƙaƙe, sai fahad dake sanye da gajeren wando da wata riga irin maras hannun Nan sai Messi dake cikin wasu haɗaɗɗaun suit baqaqe inda ya tsuke a cikin su.
Ahankali suka shiga takowa har xuwa inda take zaune akan kujera, irin na zaman meeting ɗin nan, messi ne ya fara zama kujerar dake facing da ita kafin fahad ya zauna kujerar dake dab da ita, suma sauran duk suka Zazzau na a saman kujerun. Wani irin cool smile ta saki acikin zuciyarta tana saqa wasu abubuwa masu girman gaske.
{To fa Hajiya LAYLERH. Ko mene kike saqawa acikin zuciyarkin? Kuma ohooo 🤷}
Tuni wurin ya ɗauqi wani irin shiru bayan kowa ya gama zama inda ya dace suma ƴan dabar Nan duk kowannensu ya qame daga inda yake sun sanya su a tsakiyar taron nasu, wani makeken mutum ne tsaya dab da Messi hannunsa riqe da babbar bindiga A/k 7, da sauri Messi ya ɗago kansa tare da cewa "gaskiya ka ɗan yi baya kaɗan Malam da wannan bindigar naka daka seta Ni da ita!" (Kada ku manta fa Messi akwai shi da shegen tsoro dama)
Cikin rashin walwala mutumin yaja baya, shi kuma Messi ya juyo gareta yana matse fuskarsa da take ɗan dibar yanayi data JALAAL kaɗan🤏, sai kuma ya fara magana cikin dakewa dason aro jarumta ya ɗorama kansa yace.
"Ni! Ne komae nashi haka za nine akan komea nashi duk wani abu daya mallaka a duniyar nan nasan da zaman sa wanda nake da yaqinin ko uwarsa bata san da zaman wasu abubuwan nashi ba!, amma Ni nasan komae nasa, sabo da nine babban yaronsa wanda ya ɗau amanar duniya da yardar duniya ya ɗora min!, sai dai kashhh.
Nine nan wanda ya dace da Wannan matsayi da kuma uban dukiyar daya tara, wanda shi kansa bai san wasu abubuwan nashi ba 🤗 kinga keñan nine wanda zanfi iya dacewa da matsayin da JALAAL AREEF yake akai A yanxu!, Ni HUSSEIN AREEFULLAHI MUHD MAI NASARA Ni Ne Nine Nine nafi dacewa da wannan matsayin"
Ya faɗi maganar yana miƙewa tsaye tare da fuskantar laylerh wanda zuwa yanzu da ɗaura qafar ɗaya kan ɗaya ta hakimce dake inda take zaune, samm babu alamun damuwa a tattare da fuskarta, kafin ku ma cikin izzar data samu kanta a cikinta ta dube shi tace "tabbas na jinjina maka kaida jatimanka, domin kunyi qoqari kwarai dahar kuka iya shirya satoni" kamar Maman Nafisa zatayi magana sai kuma ta dakata a dalilin alamar da momin Fadeelah ta mata .
Cike da nuna cewar shi jarumine yace
"Da kyau MASOYIYAR JALAAL AREEF"
Ya faɗi hakanne yana tafa hannuwansa sai kuma ya juyo a fusace yace.
"Ina da tambaya gare ki, Nida JALAAL AREEF waye yafi dacewa da wannan matsayin da yake kai a yanxun?"
Wani irin murmushi ta saki tare da qara harɗe qafafunta tace.
*"JALAAL AREEF!"*
"Uyummmmmmmm" ya fadi hakan yana yana tafe center table ɗin dake kewaye da wurin.
"Wa ye A sama?"
*"JALAAL AREEF"*
Ta faɗi hakan irin ko a jikin nan nata.
Amma duk da haka bai haƙura ba ya ce mata.
"WAYE waye yafi ƙwaƙwalwa a cikin mu?"
*"JALAAL AREEF"*
"Hhhhhhhhhh Gaskiyane! soyayya makauniyace tambaya ta qarshe idan har kikace Nine Nine baxan sa a sheqeqibaaaa, amma idan kikace shine hummmm". Ya faɗi maganar yana wani irin mutsurtsuke hannuwansa na irin yadda zai sa ayi kutsi kutsi da itan nan.
"Wa ye Chanchantar mallakar wannan matsayin?"
Sammmm babu alamun tsoro tattare da ita tace.
*"JALAAL AREEF "*
Gaba ɗayansu a firgice suka miqe suna Binta da wani irin matsiyacin kallo mai cike da tsananin mamakinta.
Sai ita kuma ta saki murmushi tace "kuna mamaki na kooo?, kasancewata mutum mai ilimin nazartar halayyar ɗan Adam nakan nazarci mutum cikin sauqi. Ku abinda kuka sani cuta da kuma zalumci haɗi dacin amana, gaba ɗayanku kuɗin bara gurbine acikin mutane, ke matar mahaifinsa ne! Ke kuma qanwa kike ga mahaifinsa sannan MIJIN ƴarki kinga keñan kin taka muqami biyu"
Ta faɗi maganar tana kallon cikin tsakiyar idanun momin Fadeelah wacce sai itace tayi qasa da kanta sabo da tsananin kwarjinin data mata, kafin taci gaba da faɗin, "kai kuma qani kake a gare shi wanda ya ɗau yardar duniya ya damqa maka amma kuma daga qarshe ka shirya cin amanar sa, ke kuma mata kike a gare shi hmmmmmmm"
Taja numfashi alamar akwai maganganun da yawa a bakinta keñan.
Sai kuma ta kalli Fahad wanda ta lura da irin mayataccen kallon da yake jifarta dashi, "kai kuma qani kake a gare sa kenan tunda ɗan yayar mahaifiyarkane, amma duk MA YE HAKANnnnnn?, me kuke shirin aikata masa"?
Ta yi maganar wani irin azababben hawaye mai zafin masifa yana ziratowa daga cikin ƙwayar idanun ta.
Gaba ɗayansu dariya suke mata suna nuna taaa da Hannuwansa, kafin su tsagaita da dariyar da suke momin fadeela tayi wata iriyar haɗaɗɗaiyar dariya tare da cewa, "yaro yarone kuma Yaro bai san wuta ba saiya taka, mu dukka Nan maqiyan wannan matsiyacin yaron ne, kuma mun shirya tsabbbb don ganin mun kawar da duk wani abu nasa daga cikin duniyar baki ɗaya!, ta hanyar raba shi da RAYUWARSA baki ɗaya, sai kuma akayi katari muna tsaka da shirye-shiryen yadda zamu dagar gaza RAYUWAR nasa ya bayyanawa Duniya cewar KECE RAYUWAR NASA.
Wannan dalili yasa muka dakata dason cika burikanmu muna son idan gawarki a matsayin rayuwarsa shin wanne irin tashin hankali ne zai shiga, sai gashi kuma abin ya qara armashi harda qarin ON BORN IN daya BAKI!, wanda Ni ya hana ƴata kamar yasan quɗirinmu gare shi shegen yaro!, kinga kenan zamu jefi tsuntsu ɗaya da DUTSI BIYU"
Hhhhhhhhhh hhhhhhhh hhhhhhhh hhhhhhhh hhhhhhhh haka suka shiga ƙyaƙyata dariyar da tafi kama data mahaukata,kafin Fahad ya tako xuwa gabanta sai kuma ya dubi mahaifiyarsa yace.
"Amma kafin Nan Mum za'a ɗan Aron ta domin tun Ranar dana fara ɗaura idanuna akanta naci alwashin saina ɗan ɗani zumarta domin da ganin wannan kaya kasan zai nada ruwa yadda ya kamata".
Da wani irin sauri JALAAL ya rumtse idanunsa jin kalmar da fahad ya ce da dukkan alamu zata bada Ruwa yadda ya kamata, haka maganar ta ringa masa amsa kuwwa a tsakar kansa, tunda suka fara banzayen maganganun su babu wacce ta Soke shi kamar wannan kalma ta zata bada ruwa yadda ya kamata. Ji yake tamkar ransa ake gasa masa acikin tsakiyar garwashin wuta, jin kalmar yake tamkar zata tashi rayuwarsa, a take jikinsa ya shiga wani irin mazari, lura da yadda jikin ogansu ke rawa ne ya sanya ɗaya daga cikin mutanen saurin dafe saman
Shoulder na JALAAL ɗin tare da faɗin "B A MAN man mana saura qiris fa"
{Tofa mene ake shirya mana jama'a da dukkan alamu kammmm hmmmm amma dai bara nayi gummmm da bakina🤐🫣}
Daga cenñnn ɓangaren su Layla kuwa itama dariyar ta saki ganin tana dariyarne itama ya sanya su datse tasu dariyar suna zuba mata na mujiya, ita kuwa saida tayi mai isarta kana ta kallesu baki ɗaya tare de cewa.
"Dukanku macu tane maha'inta Don haka babu abinda zaku iya min sabo da ku tamkar kankare ce,
Shi kuma na musamman. A zahiri idan ƙanƙara ta faɗa wuta NARKEWA take. Haka idan wuta tana kusa da ƙanƙara MUTUWA take yi.
Idan wuta da ƙanƙara suka haɗu wannan *JALAAL AREEF keñan* LAYLERH ta kasance tamkar *RAYUWAR JALAAL AREEF CE* idan har LAYLERH tana cikin Matsala taya kuke tsammanin cewa *JALAAL AREEF ZAIYI SHIRU MAMA?"
Ta faɗi maganar cike da wani kafurin murmushi kwance a saman fuskarta ɗan rankwafowa tayi kan momin fadeela tare da faɗin.
*"I DON'T CARE! MAMA"*
Tayi Maganar tana nuna musu ɗan yatsarta manuniya alamar akwai Qura keñan.
{Ho ho ho wai kammm meke shirin faruwa ne mene?🤩🥰}
Gaba ɗaya wurin babu wanda maganganun Layla bata girgiza duniyar saba, hakan ya sanya a fusace fadeelah tayi kan laylan tana faɗin.
"Kinyi qarya kinyi qarya kinyi qaryaaaaa, wllh babu idda zaki ɗara daga Nan WURIN UBAN WAYE YA BAKI WANNAN KWARIN GWIWAR HAR HAKA?"
*"NINE!"*
Suka jiwo murya da ko acikin barcinsu ba zasu gaza gane taba.
Hakan ya sanya gaba ɗaya Mutanen ɗakin juyowa suna kallon bakin qofar, da wani irin tsoro ruɗu kiɗima tashin hankali suke kallon bakin qofar ganin JALAAL AREEF ke waye daaaaaaaa......🫣
Shin su WAYE suka gani tare da JALAAL AREEF?
Ya akayi reshe ke neman juyewa da mujiya?
WAYE JALAAL AREEF? Me yake shirin aikata ma su M?
Tofa duk amsar tana cikin littafin *JALAAL AREEF* ɗin dai
Ku biyo AMMEY LAYLERH donjin yadda zata kaya tsakanin su momin Fadeelah da *JALAAL AREEF* wanda yake matsayin surukinta ɗan gidan yayan mahaifiyar MATARSA FADEELAH JABBER SHETTIMA.
*AMMEY LAYLERH ce AMMEY LAYLERH ce AMMEY LAYLERH ✍️*
https://chat.whatsapp.com/Ljz11YuLEQYDc7N90XW21i
_____________________________________
*💐🌼 JALAAL AREEF 🌼💐*
~💸 THE BILLIONAIRE 💸~
A story of pure love that touches the ♥️
Page 41&42
*BY AMMEY LAYLERH*
~I wish all Muslims around the world a blessed Friday~
_______________________________________
♥️🤍♥️
★★★
Ganin JALAAL AREEF ke waye da National and national security officials ba qaramin girgiza duniyar su yayi ba, hakan ne ya hana kowanne daga cikin su koda ƙwaƙƙwaran motsi ne kuwa, domin sun tabbata qaryansu kammm yasha qarya.
Ja yayi ya tsaya yana lumshe firgitattun idanunsa wanda suka gama bayyana tsananin ɓacin ran da yake a ciki, da wani irin saurin bala'i Messi ya hantsilo bayan mamanshi yana afkawa jikinta, ganin yadda waɗannan manyan qartan sojojin ke kewaye da JALAAL, sun sanya shi tsakiyarsu ko wannensu kansa yana a qasa ne umarni kawai suke jira daga ogansu jalaal wanda ya kasance babban sojan da qungiyar sojoji suke ji dashi, na kasancewarsa shugaban sojojin 9j amma na qarqashin qasa domin ya qiya ya musu aikin bayyane, da farko yana matukar qaunar son ya zam soldier hakan ne ma yasa ya harya fara aiki tare da su ba tare da kowa nasa ya sani ba tun mahaifinsa na darai.
Amma bisa wasu dalilai nasa ya sanya shi ajje aikin nashi a gefe, yaci Gaba da business nashi kawai. Su kuma hukumar sojoji kodan ganin irin baiwa da kuma fikrar da yake da ne ya sanya su, suka yi qoqarin ganin ya dawo aiki dasu amma sammm ya qiya, hakan ne yasa suka duk wani fafatuka ganin da gaske idan suka yi saken daya sa suka rasa JALAAL AREEF a matsayin sojan qasar su, wasu qasashen ka iya janye ra'ayin sa, akan qasar nashi. Da qyar ya yarda ya dawo aikin bawai aiki bane kamar yadda kuke tsammata irin na sauran sojoji ba, a ahhhh shi aikinsa na daban ne domin aikin sirri ne wanda duk wani alfahari nasu yana akan jalaal Areef ne, yana hakimce yana a zaune a gida yake aiki da hukumar sojojin Nigeria harda ma sauran qasashe, saidai yaƙi bari sunansa ya fita da kuma pisc nashi inda yake amfani da AA ataƙaice dai *JALAAL AREEF He is a great soldier but I am hidden* wanda yake da babban matsayi. Wanda shine ginshikin su kuma bayya Nannun, da wata iriyar muryarn da tunda suke dashi a duniya basu taɓa jin yayi ba yace musu.
"What are you waiting for? You wouldn't have cut their meat in front of me"
Ya faɗi hakan ne yana sauqe rikiɗaɗɗun idanunsa akan FAHAD.
"A matsayin ka na wa? da kake bada umurni akanmu, So you can bring it to us yourself."
Cikin dakewa Mum fadeelah tayi maganar domin tabbas tasan tana da qwarin gwiwar hakan, kasancewar mijinta Alh JABBER SHETTIMA babban soja ne kuma sananne a qasar 9j , shi yasa take da qwarin gwiwar yin magana har haka. Kasancewar shi shugaba a gare su ne ya suka ja da baya a yunkurin su na dagargaza namomin su momin, da ido kawai ya musu wata ƴar alama hakanne yayi sanadiyyar daka dakatawarsu.
Shi kuwa boss ln har yanxu idanunsa yana akan fahad ne wanda yake tunanin irin azabar da zai bana fahad ln yake.
wanda a take yasha jinin jikinsa. A take kalmomin daya furta akan rayuwarsa suka shiga dawo masa tsakar kansa, babu wanda ya anqara sai jin harbin bindiga su kayi, atare Mum da Momi suka rumtse idanunsu domin kowa ɗansa ne ya fara xuwa ransa, wanda qarar harbin ne ya firgita Messi wanda ya zunduma uban ihun da ya sanya kowa yayi tunanin shine aka harba, shi kansa JALAAL AREEF ɗin neman inda harbin ta fito yake, kamar ance waiwaya yaga general MALEEK TOUFIQ ɗin JADDERH *{NA CIKIN LITTAFIN KAREN BANA}* na AMMEY LAYLERH ne tsaye hannunsa zube jikin aljihun kakin dake jikinsa, wanda suka masa wani irin fitinannen ƙyau.
Da wani irin kallon mamaki jalaal Areef ya shiga bin MALEEK TOUFIQ dashi, "Is that what she did?" Va tare daya san a fili ya furta hakan ba.
"Don't worry, it was my job that brought me here."
Cikin ƙasaitacciyar muryansa ya faɗi maganar.
tuni jikin sa ya jiki da gumi domin badai shegen tsoro ba, da wani irin tashin hankali suka shiga buɗe idanunsu, a razane Mum fadeelah ta zunduma uban ihun daya cika ɗakin ganin fahad ne aka harba.
"Alhamdulillah" momin Messi ta furta a cenñnn qasar zuciyarta ganin ba yaronta aka harba ba.
Da wani irin mugun kallon tsana fadeelah ta shiga bin LAYLERH dashi wanda har yanxun take hakimce a inda take zaune qafar ɗaya na kan ɗaya har zuwa wannan loqacin kuwa, babu tsoron komai domin ta ma rigada ta mance cewar Jalaal tare yake da manyan jami'an tsaro, hakan ne ya sanya tayi kan laylerhn wuqa riqe a hannun ta domin kamar yadda tayi alqawarin feɗe cikin laylerhn to kuwa tabbas saita cika alqawarinta ta cira kakkaifar wuqar dake a hannun ta da niyar daɓa ma Layla aciki, taji an riqe tsinin wuqar, ɗago kanta tayi a razane ta saki wuqar ganin jalaal ne tsaye hannunsa riqe da wuqar da tayi niyar sokata a cikin Layla, ba tayi wani aune ba taji an buga kanta da jikin ginin ɗakin, inda ta faɗa saman fahad dake riqe da gefin cikin sa inda general MALEEK TOUFIQ ln ya harbe shi,
★★★
A hankali ya saki wuqar tare da lumshe lumsassun idanunsa yana ware mata hannuwansa, alamun ta taho xuwa gare sa. Duk yadda ta kai dason ta tashi ɗin hakan ya gagara sakamakon qafafunta sunyi tsami sunyi taruwan jini. Da ido ta masa alamun bata iya tashi, cikin natsuwa ya durƙushe a gabanta tare da miqar da qafafunta ya shiga matsa mata, "aucccch, da zafi fa my mine"
Cike da tsananin zallar soyayyar da yake mata ya ɗago kansa tare da ɗaura hannunsa saman laɓɓansa yana cewa "shiiiiiiiiiiiiiii" gum kuwa ta rufe bakin nata tana lumshe idanun ta jin wani irin daɗin tausar da take ji. Tuni SOLDIER'S ɗin dake tare su Jalal da kuma general MALEEK TOUFIQ sunyi gaba da ƴan dabar Nan gudun kada matar oga ta shiga wani tashin hankalin ne, ya sanya su fita dasu wojen wurin Saida suka ci uban daya haifi uwar su ma kafin ayi gaba dasu.
Momin Nafisa ce ta dubi jalaal cikin bariki domin sammmm batayi tsammanin yaji duk maganganun da suka yi bane, ya sanya ta qara sowa gaban sa tare da sakin murmushin makirci tace "ɗauko ta mu tafi gida kada loqaci ya qure mana" wani matsiyacin kallon da jalaal ɗin ya wulga mata ne ya sanya ta ja baya babu shiri.
"Wanne loqacin ke gare ki Hajiya Hafsa ai kin bar loqacin ya qure miki tun tuni".
Tsananin tsoron dake cikin ranta bai hana ta kuma dubar shima tace "Abduljalaal"
" Ma'am hafsa haka kike son ji koooooo"
Kamar da gama sama suka jiwo maganganun Mum fadeelah tana cewa.
"Me kake taqa ma dashi? Kuɗi don kawai kana taqama da kuɗi shine zaka nemi kashe min ya'ya Waye kai?}
"Shine shugaban duk wani sojan dake cikin Nigeria! Shine katan marar gata, shine gamji sha sassaqa shine
uban marayu ɗan yayanki, wanda na jima ina faɗa miki ki guji zuwan wannan ranar, shine Qarsheeeeee qarshen qarshe na jami'an mu saidai shi jami'an ɓoye ne mai cike da tarin nasarorin rayuwa, shine shugabana jenarally AA keñan"
Gaba ɗaya har fadeela take kwance warwas Saida ta juyo jin abinda mahaifin nata ya faɗa.
Ta yunqura da niyar tashi daga jikinsa wani irin jiri ya ɗebata, lu'ulu'u tayi baaaaaaa.
Bana da charging pls manege kawai.
Bisa sanin muhimmanci alqawari
BY AMMEY LAYLERH
https://chat.whatsapp.com/Ljz11YuLEQYDc7N90XW21i
_____________________________________
*💐🌼 JALAAL AREEF 🌼💐*
~💸 THE BILLIONAIRE 💸~
A story of pure love that touches the ♥️
✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟
Page 43&44
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
*I really have no words to thank you for You are my world, my parents, my pride May God bless my father and may he rest in paradise*
*But I say that God will reward you with the house of Jannatul Firdausi🤲🤲* i miss You mahaifin da bana da kamarka, Ubangijii yakai haske cikin qabarinka Abba Naaaaaa, Ubangiji yasa kana gidan aljannatul Firdausi 🤲🤲 ameern ya rabb.
🗣️🗣️🗣️🗣️MY TALIYAR ZUCIYAR JALAAL AREEF kina INAAAAAA waikammmm?
___________________________________
♥️🤍♥️
Da wani irin mugun sauri jalaal ya tallafo ta xuwa jikinsa da idanunsa ya bita wanda suka sanja launi xuwa jajaye, saurin rungumota yayi yana manneta cikin jikinsa yana jin bugun k'irjin ta a hankali yake furta "Ki daina kuka wifey Crying is more important than my heart and soul because of the situation I am in!."
Ya ƙarashe maganar yana mai ƙurama waje guda firgitattun idanunsa, shi kaɗai yake imagining kalan azaban da zai baiwa su Fahad da kuma messi musamman ma dai Messi da second by second kalaman da ya faɗ akan laylerhn sa ke dawo masa, sosae maganar tayi hurting ɗinsa, yama rasa wanne kalan azabar zai bama fahad ɗin.
Ita kuwa Layla ganin yadda hannunsa ke zubar da jini ne ya sanyata qoqarin tashi, sai kuma jiri ya ɗebeta,ba kaɗan ba hankalin ta ya tashi shine dalilin daya sanyata fashewa da kuka kawai, kwantar da kanta yayi saman jikinsa,
A zahiri idonsa a lumshe suke, amma kuma abaɗini yana kallon Messi ne daya naɗe jikin mahaifiyarsa, shi kansa shaida ne Messi yana da tsananin uban tsoro kamar farar kura.
***
Fadeelah kuwa daƙyar ta yunqura ta tashi zaune idanunta akan jalal yanda yake rungume da laylan ba qaramin soya mata zuciya yayi ba, shin wannan wane irin musiba ce? Lokaci guda tasa hannu ta goge hawayen da ya gangaro mata, haka zuciyarta taci gaba da raya mata har abada bazata taɓa barin wata mace ta raɓi Jalal.
(Hhhhhhhhhh Hajiya Fadeelah saidai kamar kinyi wasa da damar ki loqacin kamm ya riga da ya wuce ki en mata🫣🕺).
Tamkar wata mahaukaciyar zararriya haka Mum fadeelah shiga binsa da ido, daidai loqacin ne kuma wayarsa ya ɗauka ruri zaro wayar yayi cikin hamzari yana amsa qiran kai tsaye.
"Ummie is fine, nothing happened to her ki kwantar da hankalinki pls keda Hajj Mama"
Shine kawai abinda yace yana datse qiran, umarni ya bada da suma suma su Mom ɗin a tafi dasu kafin ya zo. Sai yanxu fadeelah ta samu bakin magana cikin rashin mutunci ta dubi jalaal dake riqe da layla tace, "wllh duk daran daɗewa saina datse munafukar wannan qaunar naku",sai kuma ta dubi Layla tare da cewa "ke kuma tsohuwar munaka ki jiriya dawowana saina rabaki da Numfashnki, sai kin barmin gidana, domin ba zaki taɓa rusamin famar kina na zama mallakin jalal Areef Ni ƙ@ɗai ba"
Cikin tsananin wayo da kuma hikimar da Ubangijii ya mata ta saki wani irin ɗan banxan murmushi, tana kuma mannuwa da jikin jalaal in kafin ta dube ta tace.
"Haba aunty fadeelah follow everything with chameleon's style, with change and being steady, optimally utilise what's in your possension with care, cease from doing what you hate to others, you'll be just.
Get a grip of your tongue, close your ears, shine your eyes to be. Opened to see the truth , and to stay away from obvious or obscure lies, kiyi haƙuri aunty fadeelah ki sanja pls ko ba dan kowa ba kodan mahaliccin mu"
Da wani irin kallo jalal ya shiga bin Layla dashi, ita kuwa fadeelah sumar tsaye tayi cike da mugun jin haushin ta ta tsinkayi muryansa mai ɗauke da amo da amsa kuwwa yace.
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 22