rashin mutuncin kai ma?"
Cikin sanyi hali irin UMMIE tace " haba Mama kiyi haƙuri ki daina biyewa MODDIBO haka Nan don Allah, kai kuma tashi kayi sama ka ba mutane wuri Anan"
"Dole yamin rashin mutunci nasan da ubansa na raye ai sai inda qarfinsa ya qare wajen ganin, shima yaci mutuncin wanda ya taɓa mahaifiyarsa, amma ba komi duk nasan maganin ku daga kai har futulan taka, na rantse cikin danginmu na ƙyauye zan bada tallarka, har Allah yasa a dace na samo maka mata"
A fusace ya jiwo yana zabga mata harara haɗi da fadin. "ba sai kisamo ɗinba tunda kece uwata! Kuma bance miki idan bazaki ce wa matata FADEELAH ba kiyi shiruuu, idan na kuma jin kince mata futulan wallahi sai kin"
"Sai uwarka nace sai uwarka MODDIBO, Hajiya Maman kake faɗawa maganar daka ga dama? Ashe dama baka da mutunci MODDIBO, ka wuce kabe muta ne wuri ko saina ɓara ranka!"
UMMIE ta faɗi maganar cikin fushi dajin kamar ta janyo JALAAL ɗin tayi ta mari.
"To bakiji mai tace mini ba? Cewa fa tayi zata je ƙyauye ta zaɓomin mata! Ko an faɗa mata niɗin bani da zaɓin rainane?"
"Oyoo ashe ban isa dakai ba kenan MODDIBO, shi yasa nake faɗa kake faɗ"
Ai kuwa UMMIEN bata kai ga dire qarshen zancen nata ba sukaji Hajiya Mama ta fashe da kuka haɗi da fatar fajina fafatt, "Ehhhhhhhhh lallai Annabi yayi gaskiya lallai qarshen duniya yazo, tunda kake dubar tsabar idanuna ina matsayin uwar UBAN ka kake faɗamin baƙaƙen maganganun na gode sosai JALALU, to bari kaji ma yanda naci wuyar ka ko ita uwar taka gata Nan atsaye bata ciba"
Takai qarshen zancen nata tare da nuna UMMIEN dake tsaye da bakinta.
INAAAAAA shi kuwa ma jalaal tuni yabar wurin.
Zama UMMIEN tayi kusa da Hajiya Maman tana faɗa mata maganganu masu sanyaya zuciya, dan danan mutuniyarku ta saƙƙo, sai gata an baje ana shan fira da ummie wacce duk yawanci kuma akan jalaal ɗinne.
**********
JALAAL
*********
Hankali kwance cikin nutsuwarsa na mutumin daya gama sanin kansa, yake tunkarar ƙaton ploorn nashi.
"ya rabbi" na faɗa loqacin da hancina ya gama shaqo mini dauwamammen qamshim sa wanda ya riga da ya gama kama ɗakin, parlour ne haɗaɗɗe domin iya haɗuwa kam ya haɗu don alqalamina bazai taɓa iya rubuta muku tsaruwar ploorn ba, idan kuma nace zan tsaya rubuta muku ya tsaruwar ploorn yake, to ashe kammm zamuy kwanan zaune ne kawai abinda nasani, kowannen ku yayi Emeg acikin RAI da kuma RUHINSA.
Paulour mae girman gaske wanda yake
ɗauke da sassa guda uku, wanda ko wanne ɓangaren da irin qawatuwar da yake da kana idan mutum yana tafiya, yana kallon kansa da kansa ne ta cikin glass mirror ɗin ɗakin, wanda shi kuma na ciki kai tsaye yake sanin wanda yake tafen, shi kuma mai tunkarar ɗakin iya kansa da kansa kawai yake kallo.
Directly qofar tsakiyar parlournan uku ya nufa bi ma'ana qofar tsakiya kenan, ta yadda sauran sassan suka sanyashi tsaƙiyarsu kenan.
***Tunda yake tunkarar qofar nake iya qare mashi kallo, ya shimfiɗa wani irin ni'imantaccen murmushi saman kyakkyawar fuskarshi, idanunsa tsaye akan qofar bangaren hannun damansa, wanda akawa qofar wani irin decoration na musamman.
Tun kamin yakai ga qofar shiga ploorn qofar glasses mirrorn ta fara wani irin rubuta da red and blue colors, inda take rubuta ~welcome to JALAAL AREEF place~ da wani irin style gwanin burgewa ga ba'acin kallon wurin.
Saita ƙwayar Idanunsa yayi da ta wani ɗan sisirin abu inda aka zagaye abin in a style akayi abun, kana cikin sillent voice nashi yace.
"you on accepted back JALAAL AREEF"
Zuuuuu qofar tayi sama baki ɗayanta, subhanallah shine kawai abinda baƙina ya iya furta wa, domin wani irin mahaukacin ploor ne wanda yaci uwar ma farkon komi da komai, gaba ɗaya ploorn an ƙawatashi da wasu Italian fashion rug masu masifar haɗuwa da burgewa, ɓangare gudan bangon ɗakin gaba ɗaya anshafe da plasma wanda idan har ba sani mutum yayi ba, bazai taɓa cewa plasma bace loqaci guda.
Daga ɗayan gefen kuma wani irin haɗaɗɗan dining area ne inda aka masa adon ƙoyaye masu ɗan girma suka sakko qasa kaɗan da dining ɗin, ɗaya ɓangaren kuwa wani irin azababben beni ne wanda yayi wani irin lankwasa, wanda kai tsaye zai sada mutum da bedroom ɗin hasalin ploorn kenan, gefe kaɗan da wurin kuma an ajje wani ƙaton dum lightning ne shima domin bada haske kaɗan, wanda idan ma'abocin wurin baison haske yakan sanja hasken ya zuwa dum light ɗin kamar dai da night kenan.
wanda mutun A kallon farko yakan iya bama wannan ploorn aljannar duniya, domin iya tsaruwa ploorn ya tsaru kuwa.
Kai tsaye JALAAL yake taka mata kalar benen cikin sassarfa, don ya gama ƙosawa ya ganshi cikin bedroom nashi, babban burin sa a yanxun bai fice ace yaji shi cikin ruwa mai ɗumi ba kana ya ganshi yana barci domin hutawa ba.
Ya ilahi kai wannan gida gaba ɗayansa da azabar ƙyau yake baki ɗayansa, yana sanya kansa cikin hasalin bedroom nashi kuwa da wani haɗɗaɗɗe lafiyayyan gado naci qaro, gadone iyaka gado amma irin ɗan dadai misalin nan, ba irin wargajejen Nan na six by six bane daga saman gadon kuwa wata haɗaɗɗiyar benc Centre ce mai lokoki wanda samanta akayi wasu qananun sink guda biyu a wurin, sai kuma tsakiyarsu akayi adon wata madaidaiciyar fulawa, ɗaya gefen bedside drawer ɗin kuma wani ƙaton Electric kindle ne, mai bama ɗakin ɗan qaramin haske da night shima irin wanda yake sassanja colors Innan.
Cikin muryarsa wacce ta zama slocoly loqaci guda ya furta "ALHAMDULILLAH" yana jin wata iriyar nutsuwa na sauƙar masa ta Musamman, tare da sanya hannunsa yana shafa lallausan sajen dake kwance akan kyakkyawar fuskarshi.
Sau cikin qafarsa ya shiga zarewa tare da fara ɓalle aninayen maɓallan gaban rigarsa, tare da zare dogon wandon getner ɗin shima ya rage daga shi sai boxes da farar best ɗinsa, direct toilet yace ruwa masu ɗumin gaske ya haɗama kansa tare da zuba tularen wanka acikin. Iumsassun idanunsa da akoda yaushe suke a lumshe ya kuma lumshe wa, jinsa cikin ruwan ɗumin gaba ɗaya ɗumi da kuma ƙamshim tularen, suka taru suka kuma sanya mashi wata iriyar nutsuwa, Ahankali ya buɗe idanun nashi kuma jin wani babban al'amari na shirin sanyo masa kai.
"Ya Allah" ya faɗi hakan yana wani irin lumshe idanun tare da buɗesu ahankali, Ahankali abinda yake taso masan ya fara qoqarin cin galabarsa hakan yasa shi fara furta wasu adda'oi daga cenn qasar zuciyarsa, "Ya ilahi" ya kuma furta wa karo na ba adadi jin wani irin azababben ciwon mara, da sauri ya dafe saitin marar nashi tare da datse lips ɗinsa da qarfin masifa, innalillahi ya shiga furta wa cikin muryar galabaituwa da azabtuwa.
Cikin ƙanqanin loqaci gumi ya gama rufe shi shirgat, a daddafe ya qarisa yin Wonkan nashi tare da zarar towel ruwan madara yana ɗaura shi saman waist nashi, ahankali ya mirza handle ɗin toilet ɗin tare da ficewa daga cikin toilet ɗin baki ɗaya, kwantaccen gashin kansa sai ɗigar ruwa yake ko zaman tsane shi bai tsaya Yiba, gaban wani wuri ya wanda da dukkan halamu ya gama bayyana cewar wannan wurin wurine na musamman, ahankali ya shiga dandana wasu mabuɗan sirri danda nan abun ya buɗe nima kaina bansan abinda yayi, kawai dai naga ya zira wani abune mai kamar littafi.
Da sauri ya tashi a wurin yana faɗawa saman haɗaɗɗen austra bed nashi, juyi kawai yake faman yi haka har barcin wahala yazo yayi awon gaba dashi.
**************
FADEELAH
*************
A guje take jan motorn tamkar zata tashi sama saboda azabar fushin da take a ciki, gudu take bana hankaliba ikon Allah ne kaɗai ya kawota gida lafiya, mahaifiyarta suna Zazzau ne tare da yaranta biyu sai mai gidan Alhaji JABBER SHETTIMA mahaifi ga fadeelah kenan, kawai sai ganinta sukayi ta shigo a guje tare da zubewa jikin mahaifiyarta.
Gaba ɗaya hankulan su idan yayi dubu toya gama tashi, hakan yasa cikin kiɗima suka shiga tambayarka lafiya, cikin son qara ingiza mahaifiyarta ga tsanar UMMIE ta fashe da kuka tare da cewa.
"Mum wallahi matar Nan bazata taɓa ganin daidai ba a rayuwarta! bata sona ta tsaneni! Bansan mina mata ba gaba ɗaya ta shiga tsakanin mutane, ta rabaki da mahaifiyarmu!¡! Sannan ta haɗa kowa da Hajj Mama.
Daga zuwanmu ta koroni wai wai wai na bar mata ɗanta ya huta haka nan nima naje wajen tawa UWAR tunda ina da ita nima! Sannan inajin wannan makirar tsohuwar tana ta zaginmu nidake wai fa har cewa tayi Allah saiya saka mata haihuwarki da tayi, ita kum"
Tsittt tayi sakamakon jin an kai ma bakinta wani irin shegen bugu, A fusace mahaifinta Alhaji JABBER SHETTIMA yace , "Fadeelah FADEELAH Fadeelah wai samm mai yasa ahar kullum kike son kawoma mahaifiyar ki qarar surukuwarki!,, bayan na tabbata darajarta da kika cine harya sanya ABDUL-JALAAL Yarda da AURENki, amma ke burinki bai wuce ace kin kawo saɓañ"
"Dakata Alhaji JABBERU kafa daɗe kana shiga cikin hurumin daba baka ba! I na ruwan ka da family na ina Ruwan ka da rayuwar cikin gidanmu Meye naka Acikin?"
Mum ce ta katse shi ta hanyar dakatar dashi daga maganar tashi, wanda bata barima ya qarasa zancen nashi ba
Cikin ɓacin rai ya miƙe tsaye tare da faɗin "kin kyautata ma kanki kenan yanxun yaranki ace sune masu son haɗaki da mahaifiyarki da matar babban yayanki, wanda yanxun take matsayin surukuwarki, kin haɗa da wasu shashashun Banza wanda suke shirin ganin sun tarwatsa miki rayuwarki, kota halin yayane! Amma dake ke banza ce baki ganewa, kodan irinku dama Allah baya taɓa baku rabon shiriya!, saidai ya nuna muku ishirarsa da kuma ikonsa akanku, Anan ne zaku gane cewar Allah ɗaya yake , aloƙacin da baku da damar tube masa saidai kuji kunyar duniya, cen kuma kuje ku tarar da hisabinsa mafi tsanani!"
Allah ya shirye duk wani mutum ɓata gari maison ganin, shi saiya ga bayan waninsa ameern ya rabbil alamin.
***********
JALAAL
**************
Ƙarar wayar sane ya tashe shi daga nannauyan barcin daya yi gaba dashi
Kuyi haƙuri da wannan sakamakon rashin da aka mana,
Kana nima bana da Lafiya ku sanyani acikin adda'oinku pls don Allah 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Sannan pls kuyi shering kana naga ruwan comments naku.
Ta yadda zanji qwarin muku wani typing ɗin cikin sauri da yaƙinin tabbas, littafin yana qarɓuwa a wurin ku.
Ngd
Comments
Comments
Comments
Naku pls 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
**By AMMEY LAYLERH*
https://chat.whatsapp.com/FZOG6TDjDid2W63LyRn3XP
________________
*💐🌼 JALAAL AREEF 🌼💐*
~💸THE BILLIONAIRE💸~
A story of pure love that touches the ♥️
NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
Page 11&12
*STORY*
*PLANNING*
*AND WRITING*
*Ammey laylerh ✍️*
~HAPPY NEW YEAR ALL FRIEND 01/01/2024🫂🫂~
*Happy New year {2024} may Almighty Alla's barakat Rahman, for giveness be with us forever wishing u joyous 2024💃🎆🗽🚼*
Alhamdulillah ala kulli halin, ahar kullum ina qara miƙa godiyaa na ga Ubangijiin Al'arshi, wanda ya bani Aron Rai da kuma lafiya, kana ya wadatani da tarin Ni'imominsa ta kowacce siga.
Shine ya nufeni da sake dawo muku a karo na biyu, kana inason inyi amfani da wannan dama ta hanyar miƙa dubun gidiyana ga MASOYA na AMANA🤙🏻, masu qirana da masu tura min messages ganin bana online🫠, ina godiya ga tarin qaunar ku gareni🙏🏻 kana ina roƙon Allah subhanahu wata'ala da yaci gaba da zame mana gata🤲🏻.
__________________________________
★★★★★★★★
Ahankali yaɗan ware lumsassun Idanunsa kaɗan tare da laluben wayar nashi, cikin barcin da bai gama sakin saba cenñnn qarshen gado ya jiyota, hakan yasa ya janyo ya anutse yana amsa qiran kai tsaye ba tare da yasan waye mai qiran ba.
A ƙalla yakusa ɗaukan 20 minute da wayar a kunnensa, sai kuma kawai ya rumtse idanunsa da qarfin masifa, kafin jikinsa ya ɗauki wani irin karkarwa tamkar mai rawar ɗari, tuni idanunsa ya sanja launi daga farare xuwa jawur, gaba ɗaya jijiyoyin kansa kuwa sun tashi sunyi raɗa².
Ba tare danaji mene aka faɗamar daga cikin wayar ba, amma dai da alamun koma mene aka gaya masa mai girma ne.
Wani irin zazzafan numfashi ya fesar sabo da jin kalaman na barƙa dukkan wata lakar dake jikinsa, nan yaji wani irin abu na sauƙa tun daga ƙwaƙwalwarsa har xuwa tafin qafafunsa, inda gaba ɗaya yaji jikin sa yayi wani irin sanyin da tunda yake bai taɓa jin koda kwatankwacin hakan ba. Fesar da numfashi yayi mai zafi tare da zare wayar a kunnensa yana jifa da ita baki ɗayan, kansa ya tallafo ta hanyar dafesu da dukka hannuwansa biyun wani irin ja idanunsa sukayi ga kuma wani ruwa ruwa da suka tara suna ƙallin wahayen da suka taran masa. Shi kansa bazaice ga yadda yake ji acikin RAI da kuma RUHINSA saba, kawai abinda ya sani zuciyarsa tayi masa wani irin nauyin da yake tunanin ko haɗiyar yawu bazai taɓa haɗiyewa ba, cike da matsanancin tashin hankali marar misaltawa kana cikin galabaituwa ya fara jero dukkan adda'oin da suka mashi.
"Ya ilahi ya mujibud da'awati, ya hayyu ya qayyum bi rahma tika astaghisu, la haula wala quwwata illa billah!"
Haka yayi ta duk wata Adda'ar ta tazo bakinsa, faɗar irin tashin hankalin da yake ciki ma faɗa loƙacine, amma kai tsaye bazaka taɓa fuskantar halin da yake aciki ba, kasancewarsa mutum mai taurin zuciya yasa sammm farat ɗaya ba zaka taɓa fuskantar yanayin da yake aciki ba.
Sai kuma ya shiga sakin ajiyar zuciya akai akai alamun zuciyarsa ta saussauta daga irin zafin da take yimar, ahankali ya shafa sajen dake kwance a kuncinsa, wanda yake fidda wani irin shining ɗin kyau da iyakar gyaran da yake sha.
←←←→→→
Cikin matsanancin kuka take faɗin.
"Don Allah! don darajar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama baffa kayi haƙuri kada ka auramin Iliya!.
Na yarda ka auramin koma waye amma banda Iliya, baffa Iliya ɗan shaye shaye ne manemin mata ne nasan kasan hakan, baffa koda makaho ko kuturu ka auramin Wallahi na yarda zan rayu dashi amma don darajar fiyayyen halitta banda Iliya!, baffa kasan waye Iliya kuwa? mutumin daya kasance, You are a drunkard, you are looking for women and an infidel who does not pray, na haɗaka da GIRMAN UBANGIJIIN sammai bakwai kayi haƙuri baffa!
Ta karashe maganar
Cikin matsanancin kuka, laylerh take roƙôn mahaifin nata, shi kuwa cikin ainihin gaskiyarsa yace mata.
"Saidai kiyi haƙuri MARYAMU aure nekam babu fashi insha Allah, domin na gaji da ganin ki haka Nan na gaji idan na barkin waye zaki aura? Yaushe kuma zakiyi AUREN? To Ni gaskiya na gaji da ciyar da balagaggiya kamarki ke wai ko haushin kanki baki jine kammmm!, ki duba fa ki gani gaba ɗaya ƙannenki duk sunyi aure daga masu ƴaƴa biyu sai masu ƴaƴa uku don haka kuwa dole ne na aura miki Iliya!'
Ya qare maganar yana shigewa cikin ɗakinsa .
Inna ladiyo da hajja kuwa farin cikin duniya ya gaba isarsu, tabbas boka yayi gaskiya domin dama yace musu zasuga irin MIJIN da MARYAM ɗin zata aura, kana yace musu koda wasa babu wani mahalukin daya isa yazo wurinta da sunan zance.
{Kunji shegu sun manta cewar Allah shine mai kowa mai komai}
A tare suka tafa tare da sakin shewa, sai kuma suka ɗauki guda irin ta ƴan duniyar nan tare da fara yada wasu baƙaƙen maganganu marasa daɗinji.
Umma kuwa dake zaune a cikin ɗakinta murmushi mai ciwo ta saki, tare da ci gaba da karatun Alqur'ani mai girma da take karantawa. Kamar kazar da kwai ya fashewa haka laylerh ta shigo ɗakin tare da zama kusa da umman, tana zamewa ta ɗora kanta bisa qafafun umman nata, cikin son ta kwantarma da yarinyarta hankali ta shiga lallashinta, tare da ce mata taci gaba da adda'a insha Allah tanaji acikin jikinta Allah zai musanya mata da mafi Alkhairinsa, haka dai tayi ta mata nasihohi masu ratsa zuciya a qarshene kuma ta ɗago idanun laylan tace mata.
*"Kiyi haƙuri Maryam! ƙarshen haƙuri nasarace, ƙarshen tsanani darajace, ƙarshen wahala ɗaukakace, ƙarshen jarabawa kuma Alkhairi ne, don haka ki kasance cikin yaƙini da kuma godiya ga Allah"*
"Baffa! baffalo!! Baffalota!!!"
Lawandine ya shiga rarakawa mahaifin nashi qira tamkar maqogwaran sa zai fito, cikin buɗaɗɗiyar muryarsa irin ta mashaya yaci gaba da faɗin.
"Wai kana ina neeeeee nasan kana jina, idan an isa ayi wannan auren shege nake laylan za'a aurawa Iliya!, Iliyan da kowa ya sani mugun ɓarawone! Ɗan daba!! Wanda kabbb garin nan babu wanda baisan shiba, yaron da kusan kullum yana hanyar birsin, ƴan daba fa yake ma aiki to wallahi yau dai nima sainawa Maryam ɗin da mahaifiyarta Rana "
Sai kuma ya shiga kwalama mahaifiyarsa qira cikin gabjejiyar muryarsa data gama buɗewa.
"Inna! Inna!! LADIYOOO! Danma kin samu ana ce miki Innan to ladiyo fita kina INAAAAAA, nasan wannan ba aikin kowa bane daya wuce ke da wannan shegiyar hajjar"
Inna ladiyo kuwa da tunda taji shigowar ɗan nata ta shige qarqashinsu gadon ko ƙwaƙƙwaran motsi bata kuma yiba, saida taji yana zabba mata wannan uban qiran ne kuma bata san sanda ta saki fitsarin azabar tsora ba.
Hajja kuwa da tayi wani irin tambulan ta shige cikin macaccen sif ɗinta, ɗaya riga ya gama macewa, cikin tsananin tsoro ta shiga zazzara ido tamkar wacce tayi ma sarki sata.
Shi kuwa lauwali yaci gaba da faɗin.
"YARINYAR da kakaf gidan daga ita sai mahaifiyarta ne kaɗai ke qaunata, amma ina raye ace za'a aura mata Iliya ɗan shola shili kafuri kuma !"
Cikin mazarin jiki da matsananci tsoron ɗan nashi baffa dake ɓoye a bayan ƙyauren ɗakin sane yasa shi fara magana cikin tsoran ɗan nashi.
"Wannan anyi ɗan shegiyar yaro, samm ganinka babu alkhairi acikin sa"
shifa har mantawa yake da yana da wani ɗa lauwali.
Umma dake zaune har yanzu ce ta miƙe tana fita a ɗakin don xuwa wurin lauwalin da kafa gidan maganar tane kaɗai yake ji, acikin sassanyar muryanta wanda ya qara sanyi fiye da da ta nufo shi tare da faɗin.
"Haba lawan ayi haquri haka nan mana kowanne bawa yana da nashi irin kaɗɗarar, ita kuma nata a haka yazo mata, idan har wannan aure shine mafi Alkhairinta to Ubangijii ya tabbatar mana shi da Alkhairi!"
Ganin ita ma umman yau tanason ta ɓata masa raine yasa yace mata.
"Taya auren Iliya zai zama Alkhairi umma?, bayan kinsan irin abubuwan da yake aikatawa na rantse idan da wanda ya isa ya ɗaura auren Nan shege nake, idan kuwa anyi to na rantse niba ƊAN HALAK bane SHEGE ne"
Fuuuuuuuuuuuu ya fice a gidan yana fita kuwa yaransa suka rufa mishi baya.
************
Zaune yake gaban ummiensa cikin tattara dukkan nutsuwarsa zuwa ga mahaifiyar nashi yace.
"Ummie wannan shine kaɗai alfarmar da zakimin!, kana kamar yadda na faɗa miki haka nakeson abun ya kasance, kuma Ni da kaina zance wurin baba hashimun na sanar dashi!"
Cikin wani irin yanayi ummien ta kalla tilon yaron nata, kana tace.
"ABDULJALAAL kana ganin babu wata matsala kuwa, idan har muka ɓullo ta wannan al'amarin!?"
Ta qare zancen tana jin tamkar hakan baiyi mata ba, cikin tabbatar wa yace mata.
"Idan harba ta wannan hanyar ba to kuwa bazan taɓa samun cikin muradina ummienaaaa"
Yaja sunan nata, cikin yarda tace na amince maka ABDULJALAAL"
Cike da tsananin farin ciki marar misaltawa ya rubgume mahaifiyar nashi tare da cewa.
"Na gode ummiena Ubangijii ya biya ki da gidan aljannatul Firdausi!"
***********
BAUCHI
************
Wasu dattijai ne tsaye cikin wasu irin koɗadɗun kaya, wanda kallo ɗaya zaka musu kasan cewa talauci ya samu wurin zama a jikinsu, amma ga mai cikakken hankali kuma kallo ɗaya zaiyi musu yasan cewa dattijaine masu daraja, dattako, nagarta.
A guje yaron da suka aika dan yimusu iso da alh ya zuro tare dace musu.
"Wai yace yana zuwa"
Sallamar yaron sunkayi da wata koɗaɗɗiyar Murtala data gama koɗewa matuƙa.
Babu jimawa kuwa Alh Yusuf mai kaba ya iso yana wani ɗage kai sama , shiga tunda wannan ɗan kut bazan dai qarisa ba dai🙀😍 ya faɗa masa zancen auren Nan yakejin bala'i dama kowa ye, kuma yariga yayi alqawarin cewa wannan karon kammm ko waye yazo da buqatar, naiman auren MARYAMU to tabbas kuwa zai bada.
(Tofa wannan shine ana wata ga wata🙀🙀 kome ke shirin faruwa haka ohooo)
Cikin daraja shi suka shiga gaidashi tare da faɗa masa akan maganar data kawo su, na naimawa ɗansu alfarmarta naiman auren ƴarsa LAYLAH.
Aikuwa babu binciken komi yace ya basu a turo, cike da mamakin wasu iyayen masu hali irin na Alh Yusuf suke kallon sa.
Cike da matsanancin tsoro Iliya shola Ameobi ke kallon su lauwali, domin yasan karon ba daɗi.
Wani irin shegen kallo da lauwali ya wurga masa ne yasa shi qara mannewa guri ɗaya, shi kuwa yaya lauwali cike da tacewa a rashin mutunci, ya sake dubun iliya shola Ameobi yace.
"Mene nace maka wato duk abinda na maka a banza kenan baka janye batun auren ƙanwas ba ko?"
Cikin tuno irin baƙar izayar da yasha a wancen loqacin ne yasa Iliyan wani irin zazzaro idanunsa waje, tare da fara magana cikin kiɗima haɗi da tsoro yace.
"Na ranshe da Allah na janye, daba ai na faɗa maka ita ladiyon ai itace ta bani kuɗi tace in aureta, kuma tun ranar da da kabani kashedin nan nace wa babanku na fasa auren ƴarsan!"
Ya faɗi maganar yana sauƙe ajiyar zuciya don ganin kamar ya tsira.
Shi kuwa lauwali wani irin murmushin mugunta ya jefa ilya dashi tare da faɗin.
"Duk da haka sai an ɗan baka sadaka"
Gaf ya buga kan iliya da jikin bishiyar da suke tsaye, yaja tawagarsa suka qara gaba.
*JALAAL*
Zaune yake akan ɗaya daga cikin lumtsuna lumtsuman kujerun office ɗin sa, cike da zallar farin ciki yake gudanar da ayyukansa cikin nishaɗi, domin tunda baffanninsa suka shaida mashi cewar lallei mahaifin yarinyar ya amince da batun auren su, da gaba ɗaya RAYUWAR yakejin kansa cikin wani irin matsanancin farin ciki, haɗi da jin wata irin nutsuwar da hakima baiji irin taba.
Yana
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 22