Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ganin juna ba tare da mun cika burinmu ba". Sa'adda sarkin Farisa ya zo nan a zancensa sai Zarina ta kamu da tsananin tausayinsa har hawaye ya zubo ma ta. Nan take ta rungume shi tana mai cewa, "Ya kai dan uwana ka kwantar da hankalinka ka sani cewa babu abin da zai same ka muddin ina tare da kai, duk tsautsayin da zai taɓa ka sai dai bayan ya taba ni. Ka tuna cewa yanzu fa saura daji daya jal a gabanmu mu isa kogon Darul Iksina bayan mun gama da wannan wanda ke gabanmu. Bai kamata a ce wannan wahala da muka sha ba a baya ta zama ta banza ba dama masu magana sun ce 'Idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi' Amma kuma ai bayan wuya sai dadi." 132 TASKARNOVELS.COM.NG Ya yin da Zarina ta zo nan a zancenta sai jikin sarkin Farisa ya yi sanyi. Haka dai ya sauko daga kan aljani Marhabul Zaurus ba a son ransa ba. Yana sauka sai Zarina ta goya shi a bayanta ta ɗaure shi tamau sannan ta matsa gaba tayi taku bakwai sai ta waigo ta dubi su Imran ta ce, "A nan za ku tsaya ne ko kuwa za ku biyo ni?" Da jin haka sai gaba dayansu suka sauko da sauri daga kan aljani Marhabul Zaurus sannan gimbiya Lahira, boka Muzaffar da sarki Laffaru suka bi su a baya aka nausa cikin wannan daji na biyar. Zarina na kan gaba tana dube-dube da waige-waige har suka shafe dan dogon lokaci ba su gamu da komai ba, kuma ba su ji sautin komai ba a cikin dajian tamkar babu wani abu mai rai a cikinsa. Kwatsam! Sai suka iso wata mararraba wacce ke dauke da alamar hanyoyi guda bakwai. Da zuwansu wannan wuri sai Zarina ta tsaya cak ta zaro takobinta. 133 TASKARNOVELS.COM.NG Koda ganin haka sai kowa ma ya gyara makaminsa. Zarina ta dubi kowacce hanya daga cikin guda bakwan ta yi nazarinsu sosai amma ba ta ga sawun wata dabba ba a cikinsu. Ta tsugunna ta dora kunnenta a kan kasa, nan ma sai ta ji shiru. Kawai sai ta mike tsaye ta dubi abokan tafiya cikin alamun karayar zuciya ta ce, "Ya ku abokan tafiya ku yi sani cewa na kasa gano ainihin halin da wannan daji ke ciki a yanzu domin babu wata alama ta wata dabba a cikinsa. Tabbas idan ma akwai dabbobi a cikin wannan daji sun kasance masu wayon gaske, kuma ba mamaki sun kasance masu yawo a sama, wato fuka-fukai ne da su domin babu alamar sawun kafafunsu akan kasa. Saboda haka yanzu ba mu da wani zabi wanda yafi mu yi kundunbala mu afka cikin dajin ta cikin daya daga cikin wadannan hanyoyi bakwai, in yaso idan ma mun haɗu da wata dabbar a gaba sai mu yake ta". Koda gama fadin haka sai Zarina ta kunna kai izuwa cikin dajin ta bi hanyar farko daga cikin bakwan, suma suka rufa ma ta baya. 134 TASKARNOVELS.COM.NG Nan fa suka yi ta tafiya Zarina ta raba hankalinta biyu ya zamana cewa tana kallon kasa ko za ta ga sawun wata dabba, kuma tana kallon saman bishiyoyi ko za ta ji wani motsi, amma shiru kamar an aiki bawa garinsu. Wani babban abin tashin hankali shi ne, suna fara nisa a cikin dajin suka tsinci kansu a cikin wadansu irin dogayen bishiyoyi masu yawa har gaba daya dajin ya yi dan duhu. Tabbas wata muguwar dabbar za ta iya ɓuya a cikin wadannan duhuwoyi na saman bishiyoyin. Haka dai suka ci gaba da tafiya har tsawon rabin sa'a amma ba su hadu da komai ba. Kwatsam Sai Zarina ta ga wani katon sawu na Gwaggon Biri. Saboda girman sawun har wajen rami ya yi wanda su duka suka shige cikin ramin suka tsaitsaya. Kowa ya rika kallon sawun cikin tsananin mamaki. Cikin firgici boka Muzaffar ya dubi Zarina ya ce, "Ya ke masaniyar daji, wannan sawun wacce irin dabba ce haka?". 135 TASKARNOVELS.COM.NG Zarina ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ba sawun komai ba ne face na gwaggon biri". Koda jin haka sai kowa ya firgita aka zazzaro idanu ana mamaki. Muzaffar ya ce, "Yanzu dama akwai biri mai tsananin girma kamar haka?" Zarina ta ce, "Ai a duniya gaba daya kaf irin wadannan birirrika guda uku ne kacal. Daya yana wannan nahiya. Na biyun yana can nahiyar Bimin Sin. Shi kuma na ukun yana can nahiyar Birnin Hindu. Su ne birirrika guda uku wadanda babu kamarsu a duniya. tabbas idan muka yi gaba da gaba da wannan biri dayanmu ba zai tsira da rayuwarsa ba kuma daga yanzu zuwa koda yaushe za mu iya yin arba da shi. Ni dai a tawa shawarar zai fi kyau mu koma da baya mu sauya wata hanyar". 136 TASKARNOVELS.COM.NG Sa'adda sauran abokan tafiya suka ji wannan batu sai hankalin kowa ya dugunzuma aka yi shiru ana tunani. Daga can sai boka Muzaffar ya ce, "Ya ku abokan tafiya kun sani cewa a cikinmu nan gaba daya babu wanda ya san sirrin daji da sirrin mugayen dabbobin dake cikinsa sama da jaruma Zarina, saboda haka dole ne mu yi amfani da dukkan shawarar da ta ba mu. Ina ganin cewa zai fi kyau mu koma da baya mu sauya hanya kamar yadda ta shawarce mu". Da jin haka sai kowa ya aminta, ba a sami wanda ya yi gardama ba. Nan take suka dunguma suka juya da baya suka koma izuwa farkon hanyar inda ta rarraba izuwa kaso bakwai. Da zuwa sai suka tsaya suna shawarar hanyar da ya kamata su bi daga cikin bakwan, aka rasa wanda zai zaɓi hanyar. Kawai sai boka Muzaffar ya dubi Zarina ya ce, "Ya ke wannan jaruma ki yi sani ccwa ke ce shugabarmu a cikin wannan tafiya don haka ke ce za ki zaɓar mana hanyar da ya kamata mu bi". Sa'adda Zarina ta ji haka sai ta yi ajiyar zuciya sannan ta cc, "Zan zaɓi hanya daya daga cikin ragowar guda shidan da 137 TASKARNOVELS.COM.NG suka rage mana. Amma fa ku sani cewa duk hanyar da muka bi babu komawa da baya komai bala'in da muka gani a cikinta". Koda jin wannan batu sai kowa yai shiru aka rasa wanda zai zo da jayayya. Kawai sai sadauki Haiman ya ce, Mun yarda da wannan sharadi naki. Koda jin haka sai gimbiya Zarina ta nufi wata hanya da ke tsakiyar hanyoyi shidan da suka rage ta durfafi cikinta kai tsaye ko waige ba ta yi. Sadauki Haiman wanda ke goye da matarsa Lumaira shi ne ya fara bin bayanta sannan Imran goye da mahaifiyarsa, sai Shaharan sannan gimbiya Rahila, boka Muzaffar, sarki Laffaru. Aljani Marhabul Zaurus ne a karshe dauke da dokin Shabaran wanda ko yaushe a durkushe yake bisa kafafunsa ko mikewa baya iya yi sakamakon rashin lafiyarsa. 138 TASKARNOVELS.COM.NG Haka dai waɗannan jarumai suka wanzu suna tafiya a cikin wannan daji har tsawon sa'a guda ba su ga koami ba kuma ba su ji motsin komai ba. Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai suka ji wani irin gagarumin gurnani wanda ba su taɓa jin irinsa ba a rayuwarsu. Gurnanin ya cika dajin gaba daya kuma suka rasa ta inda gurnanin ya fito. Lokaci guda su duka suka dimauce babu wanda jikinsa bai kama kyarma ba, hatta Zarina kuwa wacce ke kan gaba tana yi musu jagora. Nan fa suka ji kamar su juya da baya su ranta ana kare. Har sarki Laffaru da boka Muzaffar sun yunkura za su juya da baya sai Zarina ta daka masu tsawa ta ce, "Duk wanda yake son ya juya da baya sai ya yake ni ya kawar da ni tukunna. Ai mun yi sharadi da ku kafin mu shigo wannan dajin, saboda haka babu gudu kuma babu ja da baya, ko mutuwa ce sai dai mu tunkare ta". 139 TASKARNOVELS.COM.NG Gama fadin hakan ke da wuya sai Zarina ta daga takobinta sama ta ci gaba da tafiya izuwa gaba. Babu shiri kowa ya bi bayanta cikin alamun tsananin tsoro. Lokacin da Zarina tayi taku bakwai kacal sai tsulum! Suka ga wani murjejen Zaki ya dako tsalle daga can nesa bisa wani tsauni ya duro kasa daf da su. Saboda nauyin Zakin yana dira sai kasa ta yi girgiza, gaba daya dajin ya yi tambal-tambal kamar zai rufta kasa. Ko a tarihi ko a labarai su boka Muzaffar ba su taɓa jin zaki mai girma ba kamar wannan, domin sai an cure manyan giwaye guda uku a waje guda sannan za su kai girman wannan Zaki. Da ni Maiboko da ku makaranta, bari mu jira zuwa gobe domin mu ga wane ne zai rasa rayuwarsa a cikin wannan dajin domin kuwa 140 TASKARNOVELS.COM.NG tabbas! Kwarjinin wannan dajin ya ci a ce an rasa rayuka a cikinsa. Zakin ya wangame bakinsa mai kama da bakin rijiya ya yi wani sabon gurnani Karfin gurnanin ya sa bishiyoyi suka dinga kakkaryewa suna zubewa kasa. Duwatsu suka kama mirginowa suna karo da junansu suna farfashewa. Ba shiri kowa ya tsugunna ya toshe kunnuwansa biyu don gudun kada su kurmance. Sai da gurnanin ya lafa sannan su Zarina suka ďago da kawunansu. Bisa mamaki, sai suka nemi wannan Zaki sama ko kasa suka rasa kamar an yi ruwan sama an dauke dif. Al'amarin da ya matukar dugunzuma hankalinsu kenan, suka rasa abin da ke musu dadi duniya, don sun tabbatar da cewa Zakin buya ya yi domin ya kawo musu MAMAYAR BAZATO. Cikin hanzari gabadayansu suka taru a waje daya kowannensu ya daga makaminsa sama yana kalle-kalle da waige-waige kawai jira suke yi su ga ta inda Zakin zai 6ullo musu. 141 TASKARNOVELS.COM.NG A wannan lokaci ne Zarina ta ga cewa ashe Lumaira mahaifiyar Imran da sarkin Farisa wanda ke goye a bayanta tuni sun suma saboda tsananin firgitar da suka yi bisa ganin wannan katon Zaki. Suna cikin wannan hali ne Zakin ya yi fitar burgu daga cikin karkashin kasa ya dako tsalle a sama izuwa kansu kai ka ce cillo shi aka yi daga cikin baka. Cikin bakin zafin nama gabadaya jaruman suka daka tsalle sama domin su tare shi da nufin su sassara shi. Kash! Rashin sani ya fi dare duhu. Inda wadannan jaurmai sun san abin da zai biyo baya da ba su yi wannan ganganci ba. Koda Zakin ya hadu da su a sama sai ya kai wa dukkaninsu hari da kafafunsa na gaba da na baya, da kuma bakinsa a wangame. Cikin sa'a kauwa ya cisge hannun Haiman na dama da hannun Shaharan na Thagu. Jarumi Imran kuwa akan cinyarsa ya lafta masa wawan sara sai ga 142 TASKARNOVELS.COM.NG naman cinyar ya bude yana lage- lage kamar an farke cikin dabba. Sarki Laffaru kuwa a gadon bayansa ya tsira masa farcen, wajen ya yi rami. Boka Muzaffar kuwa a gefen cikinsa ya soke shi, jini yai tsartuwa. Shadira kuwa kanta ne yai karo da kan Zakin jini yai tsartuwa daga cikin hancinta da bakinta, tun a saman ta suma. Zarina ce kadai Zakin bai yiwa rauni ba amma takobinta ta rabe gida buyu sa'adda ta dankarawa Zakin sara a kuiɓin cikinsa. Lokaci guda jaruman duka suka rikito kasa suka baje a kas sumammu. Zarina ce kadai a tsaye bisa kafafunta jikinta na kyarma saboda tsananin razana bisa ganin abin da ya faru ga sauran abokan tafiyarta. Ita kuwa gimbiya Rahila Zakin ya mangare ta ta je ta buga kanta akan wani dutse, kan nata ya dare jini na kwarara ko motsi ba ta yi ba babu alamar akwai rai a jikinta. 143 TASKARNOVELS.COM.NG Nan fa Zarina da ke goye da dan uwanta Sarkin Farisa ta fara ja da baya-baya a lokacin da Zakin ya tsaya a gabanta suna kallon-kallo. Shi dai Zakin tsananin mamaki ne ya sa shi ya kasa afka mata, domin a iya tsawon wanzuwarsa a cikin wannan daji komai yawan rudnunar mayaka in dai ya dako wannan tsalle ya dira akansu to fa babu wanda zai tsira da rayuwarsa. Amma yau ga shi wata hatsabibiyar bil'adama guda daya ta tsallake wannan mugun hari nasa. Zarinata ci gaba da ja da baya yana tunanin dabarar da za ta yi ta tsira daga sharri wannan Zaki don tabbas kwaf daya zai yi mata ta mutu. Abu na biyu kuma da ya kara dugunzuma hankalinta shi no, ta san ba za ta taɓa iya tsere masa ba da karfin gudu sai dai ta yi ta 'yan zillezille da guje-guje. Kuma a hakan da zarar ta gaji zai banke ta kuma kasancewar tana dauke da 144 TASKARNOVELS.COM.NG goyon dan uwanta ta san cewa da wuri za ta gaji kuma ba za ta iya yin gudu mai yawa ba. Kawai sai ta yanke shawarra ta fara guje-gujen. ta cikin bishiyoyi tana zulle-zulle wata kila ta shiga wani sakon inda Zakin ba zai iya shiga ba. Gama aiyana hakan ke da wuya sai ta juya da sauri cikin zafin nama ta falfala da azababben gudun tsiya. Ai kuwa sai suka kasa tsere ita da Zakin. Kafin ta yi taku uku sai ta ga Zakin ya daka tsalle ya dira a gabanta, amma kafin shi ma ya juyo ya fuskance ta tuni ta juya ta sauya hanya tana mai ratsawa ta cikin bishiyoyi, shi ma ya tuso ta a baya. Sai dai ka ga Zakin yana banke bishiyoyin suna ratattakewa tamkar daka su aka yi a cikin Turmi. Kai ba ma bishiyoyi kadai ba, duk dutsen da Zakin ya bangaza da kirjinsa take yake tarwatsewa. Nan fa aka ci gaba da tsere tsakanin Zakin da Zarina ta dage iya karfinta tana gudun ceton 145 TASKARNOVELS.COM.NG ranta dana dan uwanta wanda ke goye a bayanta. In ba don Zarina ta kasance tana da zafin nama ba gami da juriya da kuma sanin daji ba da tuni Zakin ya gama da ita. Wani lokacin idan ta hango kwazazzaɓo sai ka ga ta bi ta cikinsu da gaiya saboda shi ma Zakin yana shiga cikinsu sai ka ga karfin gudunsa na raguwa. Babu abin da ke daga mata hankali face ganin duk sa'adda ta waiga bayanta sai ta ga ashe Zakin yana daf da ita kamar ma a ko yaushe zai iya wangame bakinsa ya hadiye ta. Haka dai Zarina ta ci gaba da masifaffen gudu irin wanda ba ta taɓa yi ba a rayuwarta. Shi kuwa Zakin ya a ci gaba da binta babu alamar zai gaji. Sakamakon shiga ko ina da take yi ne jikinta ya rinka buguwa da duwatsu da bishiyoyi ta rinka samun raunika a jikinta wani lokacin ma sai dai ta ji ice ya soke ta ta kwala uban ihu. Wani icen 146 TASKARNOVELS.COM.NG ma idan ya soke ta karyewa yake yi a jikinta sai dai tana cikin gudun ta zare shi, kana ganin jini na fita a jikinta amma ba ta fasa gudun ba. Sai da aka shafe sa'a daya da rabi ana wannan yseren gudu tsakanin Zakin da gimbiya Zarina, shi bai cim mata ba ita kuma ba ta tsere masa ba. A sannan ne jiri ya fara dibarta ta kama tangadi, amma saboda naci da tsaurin rai ba ta daina gudun ba. Tana cikin wannan hali ta je ta gwaru da wata bishiya ta fadi kasa ta dinga mirginawa a kasa. Ai kuwa sai Zakin ya dako wawan tsalle da nufin ya diura akanta. Abin da zakin bai sani ba shi ne, ashe sun iso daf da wani katon rami mai tsananin fadi da zurfin tsiya. Zakin na dira akan Zarina sai santsi ya kwashesu duk su biyun suka gangara cikin wannan rami. Zarina ta kurma uban ihu a 147 TASKARNOVELS.COM.NG lokacin da ta ga ta fada cikin wannan rami. Shi ma Zakin sai ya wangame bakinsa ya kwarara uban gurnani domin ya tabbatar da cewa shi ma halakarsa ce ta zo, domin komai zai iya faruwa idan suka isa karshen wannan rami da nisan kasansa ya wuce a misalta shi. Sai da suka shafe. lokaci mai dan tsawo suna fadawa can kasan ramin. Tun kafin su isa iskar da ke kadawa mai karfi ta sa duk suka sume ita da Zakin. Bisa rashin sa'a sai Zakin ya fado akan wani dogon kahon dabba wacce ta dade da mutuwa a cikin ramin. Take kahon ya fasa gadon bayan Zakin ya bullutso ta cikinsa. Zakin ya kwarara uban ihu na karshe a rayuwarsa sannan ya ama gawa. Ita kuwa Zarina akan wata ruɓaɓɓiyar gawar dabbar daji ta fado da rub da ciki. 148 TASKARNOVELS.COM.NG Sai bayan sama da sa'a biyu sannan Zarina ta farfado daga dogon suman da ta yi tun sa'adda take fadawa kasan ramin. Idanunta ne suka fara budewa a hankali, ta yi arba da gawar wannan Zaki a gabanta. Nan take farin ciki ya lullube ta. Jin nauyi a bayanta ne ya sa ta tuna cewa duk wannan gumurzu fa da tayi tana dauke da dan uwanta sarkin Farisa ne a bayanta. Cikin hanzari ta kwanto sarkin Farisa daga bayan nata, ta shimfideshi a kas a lokacin da kansa ya langabe idanunsa suka kafe kuma gaba daya jikinsa ya sandare. A zaton Zarina dogon suma ya yi, don haka sai ta mike zumbur ta rufa izuwa cikin wani kwazazzaɓo dake cikin ramin inda ruwan sama ya dan taru. Zarina ta kwarfo ruwa a cikin tafin hannunta ta zo ta watsa ruwan a fuskar sarkin Farisa amma sai ta ga ko motsi bai yi ba. Al'amarin da ya firgita ta kenan. Ta shiga girgiza 149 TASKARNOVELS.COM.NG shi tana yi masa fifita har izuwa tsawon lokaci amma shiru babu labari. Cikin dimaucewa ta sa bakinta cikin nasa ta hura masa iska, duk dai a banza. A wannan lokaci ne ta tabbatar da cewa rai ya yi halinsa. Kawai sai Zarina ta takarkare ta kwarara uban ihu wanda ya cika dajin gaba daya da amsa kuwa sannan ta kama gawar ta rungume a kirjinta ta sake fashewa da matsanaicin kuka. Allah Sarki, rayuwa ba ta da tabbas! Duk wanda ya ga Zarina a wannan hali da ta shiga dole ne ya tausaya mata matuka musamman idan ya yi la'akari da tsananin wuyar da ta sha ta tserar da rayuwar abokan tafitarta daga sharrin wannan Zaki, amma sai duk abin ya zamo ma ta a banza tun da ga shi ita ta rasa dan uwanuta wanda a dalilinsa ne kadai take son ta je kogon Darul Iksina. Wannan shi ne abin da ya faru ga gimbiya Zarina bayan Zakin da ya far musu ya hallaka 150 TASKARNOVELS.COM.NG tare dan uwanta Sarkin Farisa a cikin wannan rami ma matukar zurfi. ********************* A can inda Zarina ta baro sauran abokan tafiya kuwa, al'amarin ba kyan gani, domin su duka sun yi fata-fata a cikin jini, kuma dayansu bai farfado ba sai bayan shudewar sa'a daya da rabi. Jarumi Imran ne ya fara farfadowa. Koda ya ga naman ciyarsa ya fafe yana lage-lage sai yai sauri ya kamoshi ya hade sannan ya dauko jakar guzurinsa da ke zagaye a kugunsa ya fiddo zare da allura ya shiga dinke raunin. Yana dinkin yana ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da yake ji. Ko kadan hankalinsa bai kai kan sauran abokan tafiya ba saboda ta kansa yake. Sai da ya gama 151 TASKARNOVELS.COM.NG dinke raunin tsaf ya shafa magani akai sannan jini ya daina zuba. A wannan lokaci ne ya dawo cikin haiyacinsa. Koda ya dago da kansa ya dubi sauran abokan tafiya ya ga halin da suka shiga sai ya kamu da tsananin bakin ciki kuma ya fashe da matsanaicin kuka. Babu abin da ya fi dugunzuma hankalinsa face ganin yadda Haiman da Shaharan suka rasa hannayensu daidai. Har izuwa wannan lokaci babu wanda ya sake farfadowa daga dogon suman da suka yi. Imran ya sake daga kansa ya dubi can inda Shadira take ya hango ta baje a kas jini a hancinta da bakinta ko motsi ba ta yi, sai ya zata ta mutu. Cikin firgici ya yunkura don ya mike tsaye yaje wajenta amma sai ya kasa domin cinyarsa tai masa nauyi ko motsa ta bai son yi. Kawai sai ya kama jan jikinsa a kas, a haka ya je har inda Shadira ke kwance ya dago ta ya rungume ta a kirjinsa ya sake fashewa da matsanaicin kuka. 152 TASKARNOVELS.COM.NG Yana cikin wannan hali ne ya ji Shadira ta numfasa. Cikin tsananin farin ciki ya janye ta daga cikin kirjinsa ya dubi fuskarta sai ya ga ta bude idanunta har tana yi masa murmushi. Imran ya sake rungume ta, duk su biyun suka fashe da kukan farin ciki. A dai-dai wannan lokacin ne mahaifiyar Imran da Lumaira matar Sarki Haiman suka farfado. Koda mahaifiyar Imran ta ga danta a raye kuma rungume da masoyiyarsa Shadira, sai ta cika da dumbin farin ciki ta kama kyalkyala dariya. Ita kuwa Lumaira matar Haiman ya yin da ta ga mijinta da dungulmin hannu kwance a cikin jini face-face sai ta dafe kai ta runtuma uban ihu sannan ta cicciɓe shi ta rungume tana mai tsala kuka domin zatonta ya dade da mutuwa. Ba zato ba tsammani sai ta ji ya kawo numfashi. Cikin murna ta kwantar da shi a kas tayi sauri ta cire mayafin jikinta ta naɗe dungulmin hannun nasa domin har a sannan bai daina zubar da jini ba. 153 TASKARNOVELS.COM.NG Sai duk suka kurawa junansu idanu suna masu zubar da hawaye. Duk da yake ba ganinsa take ba. Daga can sai ta dube shi ta ce, "Ya kai mijina hakika in da na san za ka rasa hannunka a wannan tafarki da na kashe kaina domin kada ma ka yi wannan tafiya domin lafiyarka ta fiye mini rayuwata." Koda jin wannan batu sai Haiman ya sake fashewa da kuka kamar ba zai daina ba, daga bisani ya dube ta ya ce, "Ya ke masoyiyata ki tuna cewa kin yi mini komai a rayuwa kuma ba dan ke ba, da ban rayu ba na kawo i yanzu. Sai da muka shafe shekara da shekaru muna jinya sakamakon kaunarki da kulawar da kike ba ni. Ashe kuwa raina da lafiyata ba su da wani amfani muddin ban faranta miki rai ba. Na rantse da darajar kaunar da ke tsakanina da ke, lafiyarki tafi rayuwar dukkanin mutanen 154 TASKARNOVELS.COM.NG duniya a wajena kuma ina tabbatar miki da cewa, koda zan rasa daya hannun nawa sannan na rasa duka kafafuna biyu muddin ina numfashi a doron kasa zan iya tafiya da jan ciki, to fa ba zan janye ba bisa wannan tafarki na nema miki lafiya har sai idan babu ruhi a jikina. Koda jin wannan batu sai Lumaira ta sake rungume shi suka kankame juna suna masu ci gaba da kuka. A dai-dai wannan lokaci ne Shaharan da abokan tafiya kowa ya farfado. Koda Shaharan ya ga ya rasa hannunsa guda kuma ya ga bai ga Zarina da dan uwanta Sarkin Farisa ba sai ya kamu da tsananin bakin ciki ya rushe da kuka. Cikin hanzari ya yage rigar jikinsa ya nannade dungulmin hannunsa don tsaida jini sannan ya ruga izuwa cikin dajin yana kwallawa Zarina kira. 155 TASKARNOVELS.COM.NG Da kyar da siɗin goshi sauran abokan tafiya suka mimmike zaune sannan masu kwarin cikinsu suka shiga yiwa sauran magani. Shi kansa Boka Muzaffar sai da aka yi masa dinki a cikinsa. Shi kuwa Sarki Laffaru a gadon bayansa aka yi masa dinki. Gaba dayansu dai ba su dawo cikin hayyacinsu ba sai bayan shudewar sa'a uku. A wannan lokaci ne kowa ya ji nadama bisa baro kasarsa don zuwa kogon Darul Iksina domin zukatansu duk sun karaya sun san cewa abu ne mawuyaci dayansu ya isa kogon Darul Iksina a raye duk da cewa saura daji daya kacal a gabansu. Al'amarin jarumi Shaharan kuwa, lokacin da ya nausa cikin daji yana kwala wa Zarina kira, sai ya ji shiru kamar maye ya ci shirwa. Bisa sa'a kuwa sai ya bi wannan hanya wacce Zarina da wannan Zaki suka bi suna masu kasa tsere kuma sai ya yi ta bin sawunsu. 156 TASKARNOVELS.COM.NG Duk da haka sai da ya shafe sa'a biyu da rabi yana ta bilinbituwa a cikin daji yana dada ci gaba da kwala wa Zarina kira amma bai ganta ba kuma bai ji ta amsa kiran ba. Kwatsam! Sai ya iso gaban wannan raini mai zurfi wanda Zarina ta fada. Yana lekawa cikin ramin kuwa ya hango ta zaune dirshan rungume da gawar dan uwanta Sarkin Farisa tana kuka. Shaharan ya sake kwala ma ta kira har sau uku amma ko dago kai ba ta yi ba bare ta kalle shi. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa ke nan ya rasa abin da zai yi. Bayan Zarina ta sha kuka ta gaji har hawayenta ya kafe sai ta dago kai ta dubi Shaharan wanda ke can saman ramin ta yi masa wani irin kallo mai nuna alamun bankwana har tana daga masa hannu. Kawai sai ta zare wata zabgegiyar wuka a kugunta ta daga sama za ta cakawa kanta a 157 TASKARNOVELS.COM.NG ciki. Tsawar da Shaharan ya daka mata ne ya sa ta kasa lumawa kanta wukar ta dago kai ta dube shi a lokacin da hawaye ya zubo ya masa. Shaharan ya bude muryarsa da karfi ya ce, "Ya ke masoyiyata kiyi sani cewa, kina kashe kanki nima zan fado cikin wannan ramin na kashe kaina, domin ban ga amfanin rayuwata ba muddin babu ke. Haka dai Shaharan ya ci gaba da gayawa Zarina kalmomi masu taushi irin wadanda ke kwantar da zuciya amma da kyar da sidin goshi ya shawo kanta ta fasa kashe kanta. A sannan ne fa ya fara tunanin hanyar da zai bi ya iya fito da ita daga cikin wannan mugun rami mai zurfi, amma sai dabara ta kwace masa. Koda ya ga ya rasa yadda zai yi sai ya ce da ita ta zauna ta jira zai koma inda ya baro sauran abokan tafiya domi su taru su hada tunani da 158 TASKARNOVELS.COM.NG basirarsu waje daya a sami yadda za a iya fito da ita a cikin ramin". Zarina ta ce, "Shi ke nan za ta jira ya je ya dawo". Shaharan ya ce shi ba zai tafi ba har sai ta yi masa alkawarin cewar ba za ta kashe kanta ba bayan tafiyarsa ba. Nan take Zarina ta yi rantsuwa da darajar kaunar da take yiwa dan uwanta marigayi cewar ba za ta kashe kanta ba. Sannan Shaharan ya juya ya falfala da gudu izuwa inda ya baro su Muzaffar. Da isarsa gare su kuwa ya tarar kowa ya dawo cikin baiyacinsa amma duk sun yi zugum-zugun kamar suna zaman makoki. Nan take ya shaida musu duk abin da ya faru ga jaruma Zarina cewar ita ce sanadin mutuwar wannan katon Zaki wanda yai musu wannan mugun lahani kuma dan uwanta Sarkin Farisa ya mutu. Da jin haka sai dukkaninsu suka kamu da tsananin tausayin Zarina, wasu kuma suka kama 159 TASKARNOVELS.COM.NG kuka, wasu kuma suka kama zubar da kwalla. Jim kadan sai Boka Muzaffar ya dubi can gefe daya inda Aljani Marhabul Zaurus ke kwance dauke da dokin Shaharan kawai sai ya ga ashe shima ya rasa rabin fuka-fukinsa guda, shi kuma dayan fuka-fukin ya tsage a tsakiyarsa tamkar an sa Zabira an yanka tsakiyar takarda. Koda ganin wannan al'amari sai Boka Muzaffar ya yi ajiyar zuciya sannan ya dubi Shaharan ya ce, "Babu wanda zai iya fito da Zarina daga wannan rami face Aljani Marhabul Zaurus kuma ga shi shi ma yana da nakasa amma ban sani ba ko zai iya a hakan ba, mu je gare shi mu ji". Nan take Boka Muzaffar ya yunkura ya mike tsaye da kyar, shi ma Shaharan ya kama kugunsa da hannun nasa daya jal da ya rage suka durfafi inda Aljani Marhabul Zaurus ke kwance. Da isarsu garshi sai Boka Muzaffar ya dube shi ya daka masa tsawa ya

Chapter 6 of 18