Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya bude fuka-fukansa ya tashi da su sama ya keta ta cikin rufin saman kogon kamar yadda danshi ke tsattsafowa daga cikin kasa. Nan da nan ya luluka a cikin gajimare ya fara tsala azababben gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya. 245 TASKARNOVELS.COM.NG A daidai wannan lokci ne Rahila ta tuno da sauran abokan tafiyarsu wadanda suka baro a cikin kogon Darul Iksina. Nan take hankalinta ya dugunzuma ta dubi Aljani Maruful Dauwaz ta ce, "Kash! Na manta ban nemi alfarma a wajenka ka ceto rayuwar sauran abokan tafiyarmu da muka baro a cikin kogon Darul Iksina". Koda jin haka sai Aljani Maruful Dauwaz ya gyada kai cikin alamun takaici da tausayi ya ce, "Ai kuwa kin yi babban kuskure domin yanzu bakin Alkalami ya bushe. Babu wani mahaluki da ya isa ya shiga cikin daya daga cikin gidajen da ke kogon Darul Iksina face ya zama gawa. Ni kaina na manta da batun abokan tatiyar taku kuma ya kamata ki yi mini uzuri saboda mu aljanu babu halittar da ta fi mu yawan mantuwa". Koda jin haka sai hankalin Rahila ya sake dugunzuma ainun ta ce, "Yanzu kana ganin kuwa su Imran za su iya fitowa daga cikin kogon Darul Iksina?" 246 TASKARNOVELS.COM.NG Koda jin wannan tambaya sai Aljani Maruful Dauwaz yai ajiyar zuciya sannan ya ce, "Tun kimanin shekaru dubu uku baya da wanzuwar kogon Darul Iksina babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da ya taɓa shiga cikinsa ya fito a raye sai ni din nan yanzu sai kuma ku biyun nan. Saboda haka ba ni da wata amsa da zan iya ba ki akan wannan tambaya. Amma dai na san cewa in ba wanda ya san dalasiman tsafin da ake karantawa ba kofar kogon ta bude babu wanda zai iya shiga cikinsa ko kuma ya fito daga cikinsa. Ina tabbatar miki da cewa duk duniya babu wanda ya san wadannan dalasiman tsafi face mutum daya da Aljani daya. ba wasu ba ne face ni kaina da kuma wannan hatsabibin Boka naku, wato Boka Muzaffar wanda a halin yanzu na san tuni ya ďauki mashi galilul Haras ya tafi da shi izuwa can dakin halwar tsafinsa. 247 TASKARNOVELS.COM.NG Ba zai fito ba daga cikin dakin tsafin nasa sai bayan cikar kwana arba'in. A ranar da ya fito ne zai mallaki kowa da ke cikin wannan duniya, kun ga ke nan, gagarumin aikin da ke gabanmu ba kadan ba ne. Ya zama dole mu yi iya kokarinmu mu tabbatar da cewa mun sami nasarar sato Gimbiya Ramlatul Siyam gami da yawun barcin mahaifinta kafin cikar kwana arba'in din har mu je mu binne yawun a can gidan tarihi na Birnin Kisra. Ku sani cewa samun nasarar wadannan abubuwa biyu dai-dai yake da tafiya neman Jaki mai kaho! Lokacin da Aljani Maruful Dauwaz ya zo nan a jawabinsa sai jikin Rahila da na Sarki Laffaru ya yi sanyi matuka kuma hankalinsu ya dugunzuma ainun suka sami karayar zuciya bisa samun nasara akan wannan gagarumar bukata tasu don haka duk su biyun sai suka yi shiru suna tunani. Sa'adda Aljani Maruful Dauwaz ya ji su Rahila sun yi shiru sai ya bushe da dariya sannan ya ce, "Ya ku abokan alkawarina, kada ku dakushe 248 TASKARNOVELS.COM.NG zuciyoyinku da tunanin rashin samun nasara. Ku sani cewa tsakanin RASHI DA SAMU taki ne dan mitsitsi. Tabbas matsoraci ba zai taba zama gwani ba, kuma sai an gwada akan san na Kwarai. Lallai za mu siyar da rayuwarmu ko don mu ceto mutanen duniya daga sharrin Boka Muzaffar domin idan ya fito daga wannan halwar tsafi ta kwana arba'in sai ya buwayi mutane da aljanu. Kai hatta dabbobi ma da ke cikin daji sai sun shiga uku. Yanzu sai ku fada mini inda za mu je mu keɓe kanmu domin ina son ni ma na shiga halwar tsafi ta kwana uku rak saboda na gano matsalolin da za mu fuskanta ya yin da muka tafi izuwa Birnin Hindu don sato Ramlatul Siyam da samo yawun barcin mahaifinta, na san yadda zan tare su kuma na gano yiwuwar samun nasararmu da rashinta". Koda jin haka sai Rahila ta dubi Sarki Laffaru ta ce, "Ko Birninka za mu je ne? Laffaru ya zazzaro idanu ya ce, "Shin kin mantane da bala'in da nake ciki? Yanzu haka Sharlis tana nan a masarautata ta dora danta Shadaddu akan karagar mulkina. 249 TASKARNOVELS.COM.NG Burinta shi ne yanzu ta kama ni ta tsare har sai danta ya girma sannan ya yi mini KISAN GILLA bayan ya yi mini mugun wulakanci ya tozarta ni a kasata gaban talakawana. Ni a yanzu ma in ban da muna tare da Maruful Dauwaz da ba zan taba samun kwanciyar hankali ba. Abin da nake bukata yanzu shi ne, idan Maruful Dauwaz ya shiga halwar tsafinsa ya yi mini bincike shin gaskiya ne idan na auri Gimbiya Ramlatul Siyam zan haifi 'yar da za ta kare ni daga sharrin dana Shaddadu? Hakika na tsorata da maganganun Boka Muzaffar babu mamaki karya ya shirya mini". Koda jin haka sai Aljani Maruful Dauwaz ya bushe da dariya sannan ya ce, "Ya kai wannan Sarki, ka kwantar da hankalinka ka sani cewa na yi maka alkawari muddin muna tare babu abin da zai same ka, amma fa sai idan ka tabbatar da cewa a zamanin da kana kan sarautarka ba ka yi mulkin Zalinci ba domin ni a rayuwata babu 250 TASKARNOVELS.COM.NG abin da na tsana sama da zalunci, cin amana da rashin gaskiya." Koda Sarki Laffaru ya ji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma kuma cikinsa ya duri ruwa domin ya san cewa a lokacin mulkinsa ne ya zalunci Sharlis da zuri'arta kuma a dalilin haka ne mahaifinta ya yi gagarumin tanadi na daukar fansa akansa. Nan take Laffaru ya aiyana a zuciyarsa cewar ba zai taɓa gaya wa Aljani Maruful Dauwaz gaskiyar labarinsa ba bisa irin mulkin zaluncin da ya yi a kasarsa da yadda ya cutar da Sharlis dadanginta. Haka dai Aljani Maruful Dauwaz ya ci gaba da tsala gudu a sararin samaniya har izuwa tsawon sa'a biyar ya zamana cewa Rahila da Laffaru ba su kara cewa uffan ba har ma suka fara gyangyadi. 251 TASKARNOVELS.COM.NG Koda Aljani Maruful Dauwaz ya fahimci halin da suke ciki sai ya dan kada jikinsa suka farka a firgice. Aljani Maruful Dauwaz ya ce da su, "Ku yi hakuri na tashe ku daga barci, hakan ta faru ne saboda har yanzu ba ku zaɓi inda ya kamata mu je ba. Muna bukatar inda za a karɓe mu hannu biyu kuma mu sami damar gudanar da harkokinmu cikin sirri". Caraf! Sai Lahir ta ce, "Mu je kasarmu dornin a can ne nake da yakinin ba za mu fuskanci wata matsala ba, kuma ina son na sake saduwa da mahaifinatun gabannin burina ya gama cika saboda na san cewa na bar mahaifina a cikin kewata". Koda jin wannan batu sai Aljani Maruful Dauwaz ya bushe da dariya ya ce, "Tabbas kin yi mana zaɓin wuri mafi dacewa kuma ina mai yi miki albishir da cewa kafin cikar rabin sa'a za mu isa Birninku na Shauful". 252 TASKARNOVELS.COM.NG Kamar yadda Aljani Maruful Dauwaz ya fadi haka al'amura suka kasance, wato a cikin rabin sa'a cif suka iso kofar Birnin Shaufi.Nan take Aljani Maruful Dauwaz ya sauko kasa ya dira daf da Birnin ya zamana tazararsa da bakin kofar garin bai wuce taku ashirin ba. Koda masu gadin kofar Birnin suka yi arba da Aljani Maruful Dauwaz sai suka firgice suka ruga izuwa cikin gari suna ihu, dayansu bai yi jarumtakar tsayawa ba duk da cewa yawansu ya kai dari uku. Saboda tsananin razanar da suka yi basu ma lura da cewa Aljani Maruful Dauwaz na dauke da 'yar Sarkinsu ba, wato GIMBIYA RAHILA. Nan da nan labari ya riski Sarki cewar ga wani bakon Aljani wanda babu mai girmansa daga cikin aljanun duniya ya sauka a kofar gari. Koda jin wannan batu sai Sarki ya mike tsaye zumbur ya sa aka busa kahon fita yaki. Nan da nan Dakaru suka shiga shiri ka rifa debo makaman yaki. Shi ma Sarkin ya ruga izuwa cikin turakarsa ya yi damarar yaki ya debo dukkan 253 TASKARNOVELS.COM.NG gurayensa da layunsa na tsafi ya sanyasu a jikinsa sannan ya jagoranci Dakarun yakin nasa kimanin su dubu dari uku suka yi hawa bisa dawakai rike da muggan makamai suka sukwane su i zuwa can kofar gari. Da isar wannan runduna bakin kofar gari sai gaba dayan dawakan nasu suka firgice suka kama tirjiya da haniniya, suna daga kafafunsu sama suna zubar da mahayansu, kuma suna komawa da baya a guje izuwa cikin gari. Ba komai ne ya haddasa hakan ba face tsorata da dawakan suka yi sakamakon yin arba da Aljani Maruful Dauwaz saboda kwarininsa da cikar surarsa ta sadaukantaka da girman halittarsa. Dokin Sarkin kadai ne bai juya da baya ba amma shi ma ya tsorata ainun da ganin Aljani Maruful Dauwaz. Shi kansa Sarkin taurin zuciya da 254 TASKARNOVELS.COM.NG kishin mulkinsa ne da jama'arsa ya sa ya dake ya ki ya gudu. Koda ya dubi mutane biyu da ke kan Aljanin da kyau sai ya shaida 'yarsa Gimbiya Rahila. Cikin tsananin farin ciki ya duro daga kan dokin nasa ya ruga izuwa inda Aljani Maruful Dauwaz yake. Itama Rahila sai ta duro kasa daga kan Maruful Dauwaz ta ruga izuwa wajen Sarki. Suna haduwa suka rungume junansu cikin farin cikin sake saduwa. Sarki ya yi ta sumbatar fuskarta da gashinta kamar ba zai daina ba. Bayan sun nutsu sai ya dube ta ya ce, "Ya ke 'yata ki gayawa abokin tafiyarki Sarki Laffaru cewa shin ya taba cika alkawari a rayuwarsa kuwa?" Koda jin haka sai Laffaru ya bushe da dariya sannan ya sauko da sauri daga kan Aljani Maruful Dauwaz ya ruga izuwa wajen mahaifin Rahila ya mika masa hannu suka gaisa sannan 255 TASKARNOVELS.COM.NG ya ce, yau ne ranar farko a rayuwata da na taba cika alkawari dawo maka da 'yarka cikin koshin lafiya". Sarki ya yi murmushi ya ce, "Ai dama ba kai ba ne ka dauki wannan alkawari ba, Boka Muzaffar ne, ina kuka baro shi? Koda jin wannan tambaya sai Rahila da Laffaru suka yi sunkui da kansu kas sukai shiru ba su ce komai ba. Rahila ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Labari ne mai tsawo sai mun zauna. Yanzu dai mu shiga cikin gari domin jama'a su ganmu tare hankalinsu ya kwanta." Sarki ya yi murmushi ya ce, "Kin yi gaskiya yake 'yata, amma ku gayawa wancan abokin tafiya taku ya tsaya anan kadanya biyo mu domin koda an ganshi tare da mu sai jama'a sun firgice. Wai shin ma wane ne shi?" 256 TASKARNOVELS.COM.NG Rahila ta yi murmushi ta ce, "Wannan shi ne Sadaukin Sadaukan aljanun duniya, jarumi uban jarumai dodon maza kuma gwarzon mayaki ma'abocin gaskiya da amana, Aljani Maruful Dauwaz." Koda jin wannan batu sai Sarki ya cika da tsananin farin ciki ya ruga izuwa wajen Aljan Maruful Dauwaz ya rungurne shi yana mai cewa "Lale marhaban da babban bako aminin Talmara ibni Saumur. Koda jin wannan batu sai jikin Aljani Maruful Dauwaz ya kara yin sanyi, kuma ya ji ya kara aminta da Gimbiya Rahila dari bisa dari. Nan dai Sarki, Rahila da Sarki Laffaru suka dunguma suka tafi izuwa cikin gari suka bar Aljani Maruful Dauwaz anan bayan gari yana mai warwasa kafarsa yana rangadi domin rabonsa ma da ya wasa kafafunsa bisa turba shekaru dubu biyu da dari biyu ke nan. 257 TASKARNOVELS.COM.NG Da shigarsu cikin gari jama'a suka ga Sarki tare da 'yarsa Rahila sai suka cika da tsananin murna. Nan fa aka shiga taya shi murna. Nan da nan gari ya gauraye da kade-kade da raye-raye. Sarki, Laffaru da Rahila suka shige izuwa cikin gidan sarauta suka zauna a cikin dakin cin abinci aka kawo musu nau'in abinci iri-iri sama da kala dari. Nan fa Sarki Laffaru ya bude cikinsa ya yi ta zuri domin rabonsa da cin lafiyayyen abinci haka tun kafin ya baro Birninsa. Tuni Sarki yasa aka gyara manyan raguna guda arba'in gami da ruwa cikin duro arba'in ya ce a kaiwa Aljani Maruful Dauwaz ya fara taɓawa kafin a kawo masa nau'in abinci. 258 TASKARNOVELS.COM.NG Da kyar aka sami wadansu dakakkun Dakaru masu taurin zuciya suka daure suka mika wannan sako. Koda Maruful Dauwaz ya ga an kawo masa wannan abinci sai shi ma ya cika da tsananin farin ciki domin ya shafe dubunnan shekaru bai ci irinsa ba, sai ma wanda ya fishi dadi da ni'ima a cikin kogon Darul Iksina. A wannan rana dai sai da Rahila da Sarki suka raba dare suna hira inda ta kwashe labarin duk abin da ya faru a cikin wannan tafiya tasu ta zaiyane masa tun daga lokacin da su Boka Muzaffar suka zo suka dauke ta a gida kawo izuwa sa'adda suka sami nasarar keta wadannan dazuzzukan guda biyar har suka isa kogon Darul Iksina da yadda suka hadu da Aljani Maruful Dauwaz suka baro su jarumi Imran a can. Koda mahaifin Rahila ya ji wannan labari sai ya kamu da tsananin tausayi, bai san sa'adda ya kama zubar da hawaye ba kuma ya cika da tsananin mamaki bisa yadda Boka Muzaffar ya yaudari sauran abokan tafiyarsa ya jefa su cikin masifa haka. 259 TASKARNOVELS.COM.NG Bugu da kari, sai hankalinsa ya dugunzuma ainun da ya ji cewar Boka Muzaffar ya mallaki Mashin Galilul Haras domin yana da cikakken tarihin mashin, ya san cewa duk wanda ya mallake shi zai iya mallakar duniya gaba dayanta. Sai da mahaifin Rahila ya shafe lokaci mai tsawo yana juya al'amarin a cikin zuciyarsa sannan ya yi ajiyar zuciya ya dubi Rahila ya ce, "Ya ke 'yata, ki yi sani cewa aikin da ke gabanku ba karami ba ne domain yaki da Sarki Nashmir na Birnin Hindu daidai yake da ninkin wahalar da kuka, sha a dazuzzuka biyar din da kuka ratsa kuka je kogon Darul Iksina. Kuma tabbas babu wani Aljani da zai iya kai ku fadar Sarki Nashmir har ku iya dauko 'yarsa kuma ku samo yawun barcin bakinsa face Maruful Dauwaz. Ni babban abin da nake ganin cewa ma ba za ku iya samowa ba shi ne, yawun barcin Sarki Nashmir, domin ga yadda na sami labari a wajen masana, Sarki Nashmir bai taɓa yin barcin dare ba kuma a duk tsawon mako guda sau daya yake barcin sa'a shida da rana. Babu 260 TASKARNOVELS.COM.NG takamaiman ranar da ya ware domin yin barcin nasa. Ma'ana ranakun Litinin zuwa lahadi bai ware ranar yin barcin ba a kowacce rana zai iya yin barcin kuma a kowanne lokaci kin ga ke nan, ba karamin dace za ku yi ba ku riski lokacin barcin nasa. To wai shin ma ta yaya za ku iya shiga Birnin nasa ma bare har ku shiga gidan sarautarsa alhalin duk duniya babu wani wuri da ya kai masarautarsa tsaro? In ba don ba a raba rai da buri ba, da sai na ce ku hakura da wannan bukata domin ban ga yiwuwar hakan ba." Lokacin da mahaifin Rahila yazo nan a zancensa sai Rahila ta ji zuciyarta ta karaya kuma nan take hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abin da ke mata dadi a duniya, amma da ta tuna irin bakar wahalar da suka sha a cikin tafiyarsu ta zuwa kogon Darul Iksina da yadda suka tsira da rayuwarsu a lokacin da basu taɓa zaton samun kuɓuta ba sai ta sake samun kwarin guiwa ta dubi mahaifin na ta ta ce, "Ya kai Abbana kayi sani cewa babu wani abu da zai 261 TASKARNOVELS.COM.NG gagara a wannan duniya, don haka ba na fid da rai ga samun nasara bisa wannan gagarumin aiki da ke gabanmu face ba ma numfashi a doron kasa. Lallai za mu ba iwa Aljani Maruful Dauwaz dama ya shiga halwar tsafinsa ta kwana uku domin ya binciko mana ta yadda za mu fuskanci wannan gagarumar tafiya ta neman ceto rayuwar dukkan mutanen duniya da aljanun duniya daga sharrin azzalumi bakin mugu Boka Muzaffar. In da sauran Sarakunan duniya sun san halin da ake ciki da tabbas sun ba mu hadin kai an hada KARFI DA KARFE an tafi wannan gagarumin aiki". Sa'adda Rahila ta zo nan a jawabinta sai mahaifinta ya kawo gwauron numfashi da ajiye sannan ya dube ta ya ce, "Ya ke 'yata ina tabbatar miki da cewa da yawan manyan Bokayen duniya sun san halin da ake ciki, kuma sun sanar da Sarakunansu tsananin tsoron Sarki Nashmir ne ya sa kowa ba zai iya hada kai da ku ba. 262 TASKARNOVELS.COM.NG Duk fadin wannan duniya mutum daya ne wanda inda zai hada kai da ku da sai kun sami nasara farat daya akan Sarki Nashmir. Ba wani bane wannan mutum face Sharlisa mahaifiyar yaro Shadadd, wanda a nan gaba zai yi shuhura ya zamo gagarumin jarumin da ba shi da sa'a. Ko hauka ne ya sami Sharlisa ba za ta taбa hada kai da ku ba saboda idan ta yi hakan ba za ta taɓa cika burinta na son daukar fansa akan Sarki Laffaru ba. A yanzu haka Sharlisa tana nan tana shiri da bincike akan yadda za ta tarwatsa dukkan shirinku, don haka, ku yanzu bala'i biyu ne a gabanku, akwai na Sarki Nashmir kuma akwai na Sharlisa. Shi kansa Sarki Nashmir a halin yanzu yana kan shirye-shiryen yadda zai kwace mashin Galilul Haras daga hannun Boka Muzaffar domin ya san cewa ya dauko mashin 263 TASKARNOVELS.COM.NG daga kogon Darul Iksina kuma in dai ya kammala aikin da yake yi a yanzu acikin dakin halwar tsafinsa na tsawon kwanaki arba'in tabbas sai burinsa ya cika. Ita ma Sharlisa yanzu hankalinta ya rabu gida biyu, domin tana son ta tarwatsa shirinku kuma tana son ta mallaki wannan sihirtaccen mashi na Galilul Haras. Saboda haka, BAKIN ARTABUN da za a yi akan wannan mashi yafi karfin masifar YAKIN DUNIYA gaba daya. Ya ke 'yata, ki yi sani cewa tun kafin ku iso nan na yi bincike a cikin tawa halwar tsafin na ga dukkan wannan al'amari." Yayin da mahaifin Rahila ya zo nan a jawabinsa sai hankalin Rahila ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe, ta ji kamar ta tashi a sannan ta tafi izuwa masaukin Sarki Laffaru domin ta sanar da shi halin da ake ciki su dunguma su je bayan gari wajen Aljani Maruful dauwaz shi ma su sanar da shi don su san irin sabon shirin da ya kamata su yi bisa wannan al'amari. 264 TASKARNOVELS.COM.NG Daga can kuna sai ta taushi zuciyarta ta ce a cikin ranta, "Tunda dai Maruful Dauwaz ya ce zai shiga halwar tsafi ta kwana uku domin ya yi nasa binciken ya kamata na saurara na ji abin da binciken nasa zai samo". Kamar yadda aka tsara haka al'amuran suka gudana; wato sai da Aljani Maruful Dauwaz ya kwana uku a cikin halwar tsafi bai sake ganawa da su Gimbiya Rahila ba. A ranar kwana na uku da yammaci ya kammala bincikensa. Koda ya ga sakamakon binciken sai ya dimauce ya firgita ainun, bai san s'adda ya kwarara uban ihu ba ya kama gwara kansa da kasa. Al'amarin da ya janyo karamar girgizar kasa ke nan a gaba daya Birnin na Shaufil. Gidaje suka rinka rugujewa suna danne mutanen da ke cikinsu, garin ya yamutse aka yi ta guje-guje da 265 TASKARNOVELS.COM.NG iface-iface kai ka ce duniyar ce za ta tashi. Har sai da Aljani Maruful Dauwaz ya daina ihu sannan komai ya lafa. A wannan lokaci Maruful Dauwaz ya daddauje fuskarsa bai sani ba, har ta yi kaca-kaca da jini. Kawai sai ya fashe da kukan bakin ciki. Yana cikin wannan hali ne Rahila, Sarki Laffaru da mahaifin Rahila suka zo gare shi a sukwane bisa dawakai cikin halin firgici domin a zatonsu yakin bazata ne ya ɓarke tsakaninsa da wakilan Sarki Nashmir ko wakilan Sharlisa. Koda isowar su Rahila sai suka iske Maruful Dauwaz shi kadai a zaune babu alamar ya yi yaki da wata runduna, amma ga fuskarsa a daddauje, jini yai masa kaca-kaca, kuma yana ta rusa kuka. Cikin dimauta duk su ukun suka yi sauri suka sauko daga kan dawakansu suka zube kasa gabansa. Rahila ta dube shi cikin tsananin damuwa ta ce, "Ya kai Sarkin Sadaukan 266 TASKARNOVELS.COM.NG duniya, mene ne ya faru gare ka muka riske ka a cikin wannan hali?" Koda jin wannan tambaya sai Aljani Maruful Dauwaz ya fusata ya daka musu tsawa. Nan take suka dimauce, Sarki Laffaru da mahaifin Rahila basu san sa'adda suka saki fitsari ba a wando. Ita kanta Rahila gaba daya jikinta ne ya kama karkarwa tamkar an tsoma ta a cikin ruwan kankara. Aljani Maruful Dauwaz ya dube ta a fusace ya ce, "Ya ke wannan 'yar Sarki, ki yi sani cewa kun cuce ni da kuka je kuka fito da ni daga cikin kogon Darul Iksina. Inda na san abin da zai faru ke nan da na kashe kaina tun a can kogon na Darul Iksina sa'adda kuka zo mini da bukatarku. Hakika a cikin bincikena na gano masifu da tashin hankali iri-iri. Tarzoma za ta yawaita a doron kasa, kuma za a yi asarar miliyoyin rayuka da dukiya. Kun riske ni a cikin bakin ciki 267 TASKARNOVELS.COM.NG kuma gashi kun sake jefa ni a cikin wani sabon baki cikin wanda ban san ranar karewarsa ba." Koda Aljani Maruful Dauwaz yazo nanjawabinsa sai ya sake fashewa da matsanaicin kaka, Al'amarin da ya kara dugunzuma hankalin su Rahila ke nan suka rasa abin da ke musu dadi a duniya. Tsawon dakiku masu yawa dayansu bai ce affan ba. Daga can sai Rahila ta dago kai ta dubi Aljani Maruful Dauwaz ta ce, "Haba ya koai GWARZON MAYAKI mai DAKAKKIYAR ZUCIYA! Shin ka manta ne cewa in dai akwai rai, akwai buri, kuma akwai nasara da sa'a? Karfin dantse da karfin sihiri ba su ne kadai suke tabbatar da nasara ba, akwai tsananin rabo da tsananin sa'a. Ina son ka tattaro hankalinka a waje daya, ka sani cewa idan bala'i ya kunno kai babu wata hanya da za a iya kawar da shi face a rungume shi.' 268 TASKARNOVELS.COM.NG Ka tuna cewa idan ma ba ka fito ba daga cikin kogon Darul Iksina sai wannan masifa ta faru, gwara ma da ka fito din wata kila ka iya taбlbuka wani abu wajen kokarin kawar da ita. Ka tuna da alkawarin soyayyar da ke tsakaninka da masoyiyarka marigayiya Rashmin. Shin idan ka ki karanta wasiyyar da ta bar maka ka yi ma ta adalci ke nan? Ta mutu da bakin cikin rashin mallakarka kuma ta mutu da bakin cikin rashin cika burinta guda daya jal a duniya. Me zai sa ba za ka sallama rayuwarka ba wajen ganin ka cika wannan buri nata bayan ranta, domin ka bar abin tarihi wanda babu wani masoyi da ya taba yiwa masoyiyarsa a doron kasa". Lokacin da Rahila ta zo nan a dogon jawabinta sai jikin Aljani Maruful Dauwaz ya yi sanyi gabadaya, yai shiru ga barin kuka kuma ya sake shiga sabon kogin tunani. Daga can sai ya dago kai ya dubi Rahila ya yi murmushi mai taushi a gare ta ya ce, "Madallah da jaruma mai dumbin hikima da hangen nesa. 269 TASKARNOVELS.COM.NG Ki yi sani cewa wannan jawabi da kika yi mini na karshe ya zare mini dukkan tsoro daga cikin zuciyata domin kin tuno mini da wata kalma wacce mahaifina ya taɓa gaya mini tun ina yaro karami ban fi shekara bakwai ba. Kalmar ita ce; "Ya kai dana, duk wuya, duk rintsi kada ka goyi bayan rashin gaskiya. Ka rike amana, ka zamo mai cika alkawari. Idan ka yi haka za ka yi tsawon rai a duniya, kuma makiyanka ba za su sami nasara akanka ba." Har yau, har gobe ina amfani da wadannan kalmomi ba zan taɓa watsi da su ba. Tabbas yanzu na sami kwarin guiwa kuma ina ji a jikina kamar ni kadai zan iya tunkarar duk mayakan duniya muddin ban saɓawa wannan nasiha ta mahaifina ba Abinda nake so da ku shi ne, daga yanzu ku je ku fara shiri, ni kam na gama nawa. Lallai gobe da 270 TASKARNOVELS.COM.NG sassafe za mu tashi mu durfafi Birnin Hindu domin aikata wannan gagarumin aiki da ke gabanmu!!" Sa'adda Aljani Maruful Dauwaz ya zo nan a zancensa sai Rahila, Sarki Laffaru da mahaifin Rahila suka sake cika da tsananin farin ciki. Nan take suka yi wa Maruful Dauwaz godiya sannan suka yi masa sallama akan cewa za su koma cikin gari domin su fara shirye-shiryen wannan gagarumar tafiya. Maruful Dauwaz ya yi murmushi ya ce,. "Ma za ku aikata hakan lallai zaku dawo da safe ku riske ni cikin jiranku kawai". Nan take suka mike tsaye suka kama Dawakansu suka hau suka zabure su da gudu izuwa cikin gari. 271 TASKARNOVELS.COM.NG A wannan rana sai da Rahila da Sarki Laffaru suka kwana suna tanadin kayan yaki iri-iri, kai ka ce miliyoyin Dakarun yaki za su diba su tafi da su. Har sai da gari ya fara wayewa ba su rintsa ba Bayan sun gama tara kayan yakin a waje guda, sai Sarki Laffaru ya kurawa kayan yakin idanu. Nan take idanunsa suka ciko da kwalla. Kafin ya ankara tuni hawaye ya fara sartu akan kumatunsa. Yayin da Rahila ta gan shi a cikin wannan hali sai ta cika da tsananin mamaki kuma hankalinta ya tashi don haka sai ta mike tsaye ta zo gabansa ta tsugunna tana mai rike hannunsa ta ce "Ya kai mijina na gobe, ina dalilin zubar wannan hawaye naka?" Koda jin wannan tambaya sai Sarki Laffaru ya yi ajiyar zuciya gami da share hawayensa sannan ya ce, "Ya ke matata ta gobe, ki yi sani cewa yau ne ranar farko a rayuwata da na ji na yi nadama bisa abubuwan da na aikata a baya. Ki sani cewa da can ni gawurtaccen jarumi ne kuma SADAUKI, sannan GWARZON MAYAKI wanda gabadayan Sarakunan da ke nahiyata 272 TASKARNOVELS.COM.NG suke tsorona kuma suke yi min biyayyar dole, amma yau ga shi an wayi gari ko Kura ba zan iya kashewa ba a daji da hannuna. Ba ni da sauran karfin dantse a jikina kuma ba ni da sauran karfin sihiri, Sharlis ta raba ni da duk wadannan abubuwa kuma mugun halina ne ya jefa ni a cikin wannan yanayi. Lokacin neman gafara a wajen Sharlis ya wuce a gare ni, ba ni da sukuni ko sauran kwanciyar hankali face na auri Gimbiya Ramlatul Siyam 'yar Sarki Nashmir na Birnin Hindu. A sannan ne karfin damtsena da na sihirina zai dawo amma duk da haka ba zan iya kare kaina ba daga sharrin dana SHADDADU face na haifi 'yar da za ta zamo mashahuriyar BASADAUKIYA. Yaushe ne wannan rana za ta zo? Yanzu fa shekaruna sun haura arba'in. Yaushe ne zan sami kwanciyar hankali da nutsuwa a rayuwata? Tabbas yanzu ne na gane cewa 273 TASKARNOVELS.COM.NG zalunci da son zuciya ba sa haifar da komai a rayuwa face asara da nadama. Yau ga shi na rasa mulkina, dukiyata da kimata a duniya, kuma na yi hijirar dole na bar mahaifata ina garari a cikin duniya ba tare da na san makomata ba." Koda Sarki Laffaru yazo nan a zancensa sai ya fashe da matsanaicin kuka. Nan take Rahila ta kamu da tsananin tausayinsa har itama hawaye ya zubo ma ta, kawai sai ta rungume shi a karon farko tun haduwarsu tana mai shafar gashin kansa kuma tana rarrashinsa. Al'amarin da yasa Sarki Laffaru jin wani gagarumin farin ciki ya baibaye shi domin bai taɓa zaton zai sake samun wani mutum da zai tausaya masa ba a rayuwarsa. Bayan gari ya waye sosai sai Rahila da Sarki Laffaru suka yi gagarumar shigar yaki. Idan mutum ya dubi Sarki Laffaru a wannan lokaci ya ga irin shigar da ya yi da kuma irin kirar da Allah Ya yi masa ta sadaukantaka sai ya dauka cewa shi kadai zai iya yakar kasa guda. Amma ga wanda ya san sirrin al'amarin sai

Chapter 10 of 18