Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wani ba ne ke rike da wannan mashi ba face abokin tafiyarku wanda ya yaudare ku ya jefa rayuwarku a cikin TSAKA MAI WUYA, Kunci da bakin ciki mara tukewa, wato Boka Muzuffar. Ku yi duba izuwa jikin wancan bango yanzu zan nuna muku abin da ya wakana."Koda gama fadin haka sai Ramlatul Siyam ta yi nuni da hannunta izuwa ga jikin bangon Falon wanda ke Kudu. Nan take suka ga Boka Muzaffar a cikin dakin Halwar tsafinsa ya dukufa yana ta nazari. 428 TASKARNOVELS.COM.NG Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai suka ga Sarki Nashmir ya diro cikin dakin daga sama kamar haske. Kai tsaye Nashmir ya durfafi inda Boka Muzaffar ya jingine mashin GALILUL HARAS da nufin ya dauka. Har ya kai hannunsa i zuwa kan mashin zai dauka ke nan sai ya ji an doki fuskarsa. Yai tsalle sama ya gwaru da bangon dakin ya fado kasa. Cikin hanzari ya mike tsaye zumbur! Yana mai zare takobinsa sai yai arba da Boka Muzaffar tsaye a gabansa shi ma ya zare tasa takobin. Muzaffar ya dubi Nashmir a fusace sannan ya daka masa tsawa ya ce, Kai tsohon azzalumi ka yi sani cewa yau shekara talatin da biyar ke nan ina gwagwarmaya akan na mallaki wannan mashin ban same shi ba sai yanzu. Kai ma kuma ka dade kana nemansa kuma ka kasa zuwa kogon Darul Iksina ka dauko shi. Yanzu da na gama shan wahalata shi ne kai kuma kake son 429 TASKARNOVELS.COM.NG ka same shi a banza? To ka sani cewa Karyarka ta sha karya ya kai Nashmir. Ina tabbatar maka da cewa, ka kawo kanka GIDAN AJALI, sai dai gawarka ta fita daga nan". Sa'adda Muzaffar ya zo nan a zanensa sai Sarki Nashmir ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan ya murtuke fuskarsa kamar an aiko masa da sakon mutuwa ya ce, "Ai kuwa idan har ban sami nasarar raba ka da wannan mashi ba sai dai a dauki gawa guda biyu, ni da kai babu wanda zai fita daga cikin wannan daki a raye." Kafin Nashmir ya gama rufe bakinsa tuni Boka Muzaffar ya afka masa sun kacame da azababben yaki, suka wanzu suna masu kai wa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta. Sai da Muzaffar da Nashmir suka shafe kwana uku suna wannan masifaffen yaki, ya zamana 430 TASKARNOVELS.COM.NG cewa kowannensu ya yi amfani da dukkan karfin sihirinsa da karfin damtsensa amma aka rasa wanda zai samu nasarar kashe wani. A karshe suka yiwa juna fata-fata, har ya zamana cewa ko ina a jikinsu raunika n. Lokaci guda suka yanke jiki suka fadi kasa matattu, dayansu bai sake shurawa ba. Faruwar hakan ke dawuya sai ga wani haske ya baiyana a cikin dakin. Nan take hasken ya rikiďe ya zama Sharlis. Sharlis ta je inda aka jingine Mashin Galilul Haras ta dauki mashin ta daga shi sama sai ta kyalkyale da dariyar farin ciki ta ce, "Na tsinci dami akala! Tabbas yanzu na zama Sarauniyar sadaukai ta duniya. 431 TASKARNOVELS.COM.NG Da sannu zan dauki gagarumar fansa akan babban makiyina Sarki Laffaru sannan na mallaki wannan duniya gaba dayanta. Da wannan mashi a hannuna, babu wani sadauki ko matsafi da zai gagare ni. Babu wani wuri da zai yi mini wuyar zuwa. Komai yawan rundunar mayaka sai na tarwatsa su, komai nisan tafiya sai na ketata. Gama fadin hakan ke da wuya sai ta shafi wani ɓangare na jikin mashin na Galilul Haras. Nan take ita da mashin suka zama wani irin gagarumin haske suka cilla sama ta cikin rufin dakin. Kafin kiftawar ido sun kule a cikin gajimare sun ɓace ɓat. Koda gama ganin wannan al'amari sai Gimbiya Ramlatul Siyam ta fashe da matsanaicin kuka, tana mai duban su Aljani Maruful Dauwaz ta ce, "Kun ga yadda karshen mahaifina ya kasance, 432 TASKARNOVELS.COM.NG shi ya sa na gaya muku cewa ba zan sake saduwa da shi ba. Lokacin da Sarki Laffaru ya ga wannanal'amari sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya dubi Ramlatul Siyam cikin tsananin tsoro ya ce "Yanzu ta yaya zan tsira daga sharrin Sharlis tunda ga shi ta mallaki mashin Galilul Haras, wannan yana nufin ke nan za mu iya fadawa hannunta a ko yaushe ta ci gaba da tsarona har izuwa lokacin da za ta cika burinta a kaina, koda kuwa na aure ki mun haifi 'yar da za ta kare ni? Koda jin wannan batu sai Ramlatul Siyam ta yi murmushi ta ce, "Ba haka ba ne, akwai inda za mu je mu yi rayuwa babu abin da zai same mu daga yanzu har izuwa tsawon shekara goma sha takwas, a sannan ne Shaddadu dan Sharlis ya cika shekara ashirin da daya a duniya, kuma mahaifiyarsa ta mallaka masa mashin Galilul Haras a sannan ne zai bazama farautata cikin duniya. 433 TASKARNOVELS.COM.NG A sannan ne kuma 'yarmu za ta cika shekara goma sha takwas a duniya ta zama gagarumar BASADAUKIYA kuma MAYAKIYA, wacce za ta kare ka daga sharrin Shaddadu. Amma fa ka sani cewa duk ranar da Shaddadu ya yi arba da kai babu 'yarmu a kusa taka ta kare, don sai Shaddadu ya kama ka ya tafi da kai izuwa ga mahaifiyarsa. Ma'ana sai ya kai ka har can Birnin Kufa ya wulakanta ka sannan ya yi maka kisan gilla. Ya yin da Ramlatul Siyam ta zo nan a zancenta sai hankalin Sarki laffaru ya kara dugunzuma ainun fiye da ko yaushe, ya dubi Gimbiya cikin tsananin damuwa ya ce, "Ashe dai tashin hankali da rashin kwanciyar hankali bai kare mini ba? Yanzu ta yaya zan magance wannan fargaba?" Koda jin wannan tambaya sai Ramlatul Siyam ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Hanya daya ce 434 TASKARNOVELS.COM.NG maganin wannan fargaba, sai dai ita ma 'yar tamu ta fita farautar Shaddadu kamar yadda shi ma zai fito farautarka, ta raba shi da mashin Galilul Haras ta hanyar yaudara ba ta hanyar karfi ba. Da zarar ta raba shi da wannan mashi shi ke nan ta karya lagonsa ba zai taba samun damar kama ka ba bare ya iya hallaka ka." Lokacin da Ramlatul Siyam ta zo daidai nan a zancenta sai suka ji Rahila ta turnuke da tari har tana aman jini. Al'amarin da ya kara dugunzuma hankalin Aljani Maruful Dauwaz ke nan, ya zo kanta ya ciccibe ta ya tashe ta zaune yana mai zub da hawaye, bai san sa'adda ya kama sambatu ba yana cewa, "Ya ke Rahila shin kin manta da alkawarın da ke tsakaninmu ne?Ga shi na taimake ki na biya miki bukatarki, idan kika mutu yanzu ba ki yi mini adalci ba. Ki gaya mini 435 TASKARNOVELS.COM.NG inda kika boye wasiyyar masoyiyata kafin ki tafi!" Gama fadin hakan ke da wuya sai suka ga Rahila ta bude idanunta da kyar a hankali sannan ta bude bakinta yana karkarwa domin ta yi magana, amma sai ta kasa. Koda ganin haka sai Ramlatul Siyam ta kwalawa wani Likitanta kira ya rugo ya zo ya bai wa Rahila wani magani. Tana gama hadiye ruwan maganin sai barci ya dauke ta. A sannan ne Likitan yai ajiyar zuciya ya mikawa Ramlatul Siyam kwalbar maganin ya ce, "Dole ne a rinka bai wa Rahila wannan magani bayan kowacce sa'a uku idan ba haka ba kuwa za ta ci gaba da aman jini wanda zai iya zama sanadin ajalinta, kuma digo daya na maganin za a dinga disawa a cikin bakinta. Idan aka bata sama da digo daya shi ma zai iya yi mata illah." 436 TASKARNOVELS.COM.NG Nan take Ramlatul Siyam ta dubi Sarki Laffaru da Maruful Dauwaz ta ce, "Yanzu sai ku tashi mu yi shiri mu bar wannan Birni na Hindu domin idan muka ci gaba da zama a nan, nan da tsawon kwana daya rak Sharlis za ta gano inda muke ta zo a cikin dakiku kadan ta hallaka mu ta kama Laffaru ta tafi da shi. Koda gama fadin hakan sai Maruful Dauwaz ya ce, "To yanzu ina ne inda za mu je mu yi jinyar Rahila har ta warke ta cika mini alkawarina kuma ke da Laffaru ku yi aurenku". Ramlatul Siyam ta ce, "Babu inda za mu je mu tsira face wani daji da ake kira Rauful Mausur. Shi dai wannan daji na Rauful Mausur yana tsakanin Birnin Kisra da Birnin Istanbul. In dai akwai sihirin tsafi a jikin mutum bai isa ya shiga cikin dajin Rauful Masnur ba face ya zama 437 TASKARNOVELS.COM.NG gawa saboda haka a nan ne kadai za mu iya zama mu yi rayuwarmu a cikin kwanciyar hankali. Fatana shi ne Rahila ta sami lafiyar da za ta iya budar baki ta gaya mini inda wasiyyar masoyiyarka take kafin rai ya yi halinsa". Koda gama fadin hakan sai Ramlatul Siyam ta mike tsaye ta sa aka debo musu kayayyaki da guzuri ana dorawa akan Aljani Maruful Dauwaz. A wannan lokaci ne Maruful Dauwaz ya fada cikin kogon tunani yana mai cewa a ransa, "Inda ina da tabbacin cewa Rahila ba za ta sami lafiyar da za ta iya yi min magana ba da tabbas yanzu zan kashe kaina na huta da bakin cikin rayuwar duniya domin ban ga amfanin rayuwar tawa ba. Yana cikin wannan tunani ne aka gama shiryeshiryen tafiya. 438 TASKARNOVELS.COM.NG Koda Ramlatul Siyam ta zo yin bankwana da jama'arta sai ta fashe da kuka, suma suka fashe da kukan saboda shakuwa. A lokacin ne Ramlatul Siyam ta tuno da mahaifinta Sarki Nashmir kuma ta tuno da irin tsananin kaunar da ya nuna mata gami da gata, sai ta je gaban wani gunkinsa da aka sassaka mai matukar kama da shi wanda ke tsaye a tsakiyar falonta ta rungume gunkin ta sake fashewa da matsanaicin kuka. Da kyar da sidin goshi Sarki Laffaru ya ɓanɓare Ramlatul Siyam daga jikin gunkin sannan ya ja ta suka je suka hau kan Maruful Dauwaz suka zauna. Dama an shimfide Rahila a kan Maruful Dauwaz a gefe daya kuma an lulluɓe jikinta duka da mayafi fuskarta ce kadai a bude. Nan take Aljani Maruful Dauwaz ya bude fuka-fukansa ya tashi sama a hankali. Ramlatul Siyam tana dagawa 439 TASKARNOVELS.COM.NG jama'arta hannu, su ma suna daga mata kowa na zub da hawaye har Maruful Dauwaz ya kule a cikin sararin samaniya..... Aljani Maruful Dauwaz ya wanzu yana mai tsala gudu a cikin sararin samaniya babu sassauci har sai da ya shafe tafiyar sa'a biyu da rabi cif sannan ya iso dajin Rauful Masnur ya sauka a tsakiyar dajin. Daji ne mai dauke da ni'ima sosai akwai kyawawan bishiyoyi, duwatsu da dabbobin daji iri-iri, babu kalar da babu masu hadari da marasa hadari. Koda saukar Maruful Dauwaz a cikin wannan daji sai shi da Ramlatul Siyam suka kamu da tsananin sha'awar dajin shi kuwa Sarki Laffaru sai ya ji ya kamu da tsananin tsoro musamman da ya jiyo kukan manyan namun daji daga nesa suna gurnani. Koda Ramlatul Siyam ta fahimci 440 TASKARNOVELS.COM.NG halin da Sarki Laffaru ke ciki sai ta bushe da dariya, al'amarin da ya bai wa Maruful Dauwaz da Laffaru mamaki ke nan. Maruful Dauwaz ya dube ta ya ce, "Ya ke wannan Sarauniyar kyawawan matan duniya ina dalilin wannan dariya taki?". Ramlatul Siyam ta yi shiru ga barin dariya sannan ta ce, "Gani na yi mijin da zan aura rago ne kuma matsoraci ga shi ba zan taba yarda ya kusance ni ba face ya kawo mini kan rikakken Zaki a matsayin sadakina". Koda jin wannan batu sai hankalin Laffaru ya dugunzuma ainun ya ce, "Haba dai! yaya ni da na rasa dukkan karfin dantsena za ki ce sai na je na kashe zaki na yanko kansa?" Da jin haka sai Ramlatul Siyam ta murtuke fuska ta ce, "Ai kuwa ashe ba za ka taɓa zama mijina 441 TASKARNOVELS.COM.NG ba. Ai mu a kasarmu wannan ita ce al'adarmu ta aure. Kafin namiji ya kusanci matarsa sai ta zabi irin jarumtakar da take son ya yi, ya yi ta. Inda za mu tsufa a haka a matsayinka na mijina ba zan taɓa yarda da kai ba sai ka zo mini da kan zakin da ka kashe da hannunka saboda haka, ka shirya daga gobe da safe za ka fara shiga cikin wannan daji domin farautar rikakken Zaki. Ka sani cewa idan ka kawo mini kan yaron Zaki ka yi wahalar banza." Koda gama fadar hakan sai Ramlatul Siyam ta dauki tanti daga kan Aljani Maruful Dauwaz ta fara kokarin kafa shi. Shi kuwa Sarki Laffaru sai ya koma gefe daya ya yi tagumi yana tunanin wannan sabon al'amarin da Ramlatul Siyam ta zo masa da shi. 442 TASKARNOVELS.COM.NG Nan take ya ji ya tsani kansa kuma nadama ta zo masa ya ce a zuciyarsa, "In da ya san cewa zai shiga cikin wannan tsananin tashin hankali da tun farko bai yarda ya baro kasarsa ba ya sha wannan bakar wahala da fuskantar tashin hankali, da gwara ma ya kashe kansa ya huta da takaici da bakin ciki. Har Ramlatul Siyam ta gama kafa tantin ta dauko Rahila ta shigar da ita cikin tantin ta kwantar da ita, sannan ta debi kayayyakinta ta kai ciki ta zube, Laffaru bai daina tunani ba. Yana cikin tunanin ne Ramlatul Siyam ta fito daga cikin tantinta ta dube shi ta ce, "Ai sai ka tashi ka yi kokarin kafa naka tantin domin ba zai yiyu ba na kwanta a waje daya tare da kai ba face ka kawo mini sadakina". Tana gama fadin hake ta juya ta koma cikin tantinta. Shi kuwa Sarki Laffaru sai hankalinsa 443 TASKARNOVELS.COM.NG ya kara dugunzuma ainun ya rasa abin da ke masa dadi a duniya. Kawai sai ya ji Maruful Dauwaz ya bushe da dariya. Al'amarin da ya fusata shi ke nan ya dakawa Maruful Dauwaz harara ya ce, "Kai kuma mene ne ya ba ka dariya?" Maruful Dauwaz ya ce, "Gani na yi za ka ba mu kunya a matsayinka na ďa namiji. Ka tuna cewa Ramlatul Siyam yarinya ce kankanuwa a kanka, tunda shekarunka sun ninka nata. Ka tuna cewa manyan mazajen duniya sun mutu da bakin cikin rashin mallakar Gimbiya Ramlatul Siyam, amma kai ga shi yanzu za ka mallake ta a karon banza saboda kawai ta ce ka kawo kan rikakken Zaki a matsayin sadakinta shi ne za ka karaya? 444 TASKARNOVELS.COM.NG To ka sani cewa ba ka da wani zabi wanda ya fi ka kawo wannan sadakin in ba haka ba kuwa, har abada ka rasa ta, kuma sai makiyanka sun sami nasarar hallaka ka a cikin kankanin lokaci. Ina tabbatar maka da cewa ni ma ba zan taimaka maka da komai ba akan samo wannan sadakin domin idan har ka kasa samo sadakin da kanka 'yar da za ku haifa ba za ta zamo gagarumar jaruma ba saboda ba a samu sadauki sai daga tsatson sadaukai. Duk da cewar kai GWARZON SADAUKI ne ada, ai a yanzu ka zama rago, kuma sadaukantakarka ba za ta dawo ba sai bayan ka haifi wannan 'ya taka har ta girma". Koda gama fadin hakan sai Aljani Maruful dauwaz ya ɓace ɓat, ya sake baiyana a bakin tantin Gimbiya Ramlatul Siyam ya yi gyaran murya. Nan take Ramlatul Siyam ta fito daga 445 TASKARNOVELS.COM.NG cikin tantin ta dubi Maruful Dauwaz ta ce, "Me kake da bukata?" Maruful Dauwaz ya risina cikin biyayya ya ce, "Ina son na ji lafiyar Gimbiya Rahila ne domin na san matsayin da nake ciki". Koda jin wannan batu sai Ramlatul Siyam ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Rahila ta farka daga barci har ma na ba ta ruwa ta sha, amma fa har yanzu ba ta iya bude bakinta ba bare ma ta yi magana, kuma idanunta ma da kyar take iya bude su. Yanzu dai na sake ba ta wannan digon magani ta sha ta koma barci. Ka kara hakuri wata kila nan da kwana uku ta sami sauki sosai har ta iya magana". Koda Maruful Dauwaz ya ji haka sai hankalinsa ya dan kwanta ya yi godiya ga Ramlatul Siyam kuma ya roke ta akan ta ci gaba da kula da Rahila har izuwa sa'adda za ta sami lafiya. Gimbiya Ramlatul Siyam tayi masa alkawari 446 TASKARNOVELS.COM.NG cewar lallai za ta bata kyakkyawar kulawa iyakar yadda ya kamata. **** Ba tare da ɓata lokaci ba Sarki Laffaru ya mike tsaye ya fara kafa nasa tantin. Bisa mamaki sai ya ji ya sami dan kwarin jikinsa amma bai ji rabin karfin dantsensa ba irin na da ba.vNan take farin ciki ya lullube shi har ya fara tunanin cewa zai iya shiga dajin ya yi farautar rikakken Zaki. Haka dai ya ci gaba da aikin kafa tantin nasa cikin murna har ya kammala sannan ya shiga ciki ya yi kwanciyarsa ya ci gaba da tunanin zuci har barci ya sace shi bai sani ba. Ya yin da dare ya soma yi sosai sai mugayen dabbobin daji suka fara zarya a kusa da inda tantin su Ramlatul Siyam yake. 447 TASKARNOVELS.COM.NG Amma duk dabbar da ta yi arba da Aljani Maruful Dauwaz sai ka ga ta firgita ta koma da baya guje izuwa cikin daji tana koke-koke. Wato dai sai Aljani Maruful Dauwaz ya bayar da cikakken tsaro a a gare su. **** Kashe gari da safe Sarki Laffaru ya farka daga barci sai ya mike zumbur! Ya fito daga cikin tantinsa domin ya ga lafiyar abokan tafiyar tasa yana fitowa sai ya iske Ramlatul Siyam a zaune tana buda baki. Aljani Maruful Dauwaz na zaune a gefe daya kusa da ita cikin nishadi suna ta hira har da dariya. Nan take Laffaru ya gangara izuwa cikin wata korama da ke bayan inda suka kafa tantunansu ya tube kayansa ya fada cikin koramar domin ya yi wanka. Kash! Rashin sani yafi dare duhu. Ashe akwai wata katuwar Kada a cikin wannan korama bai sani ba. Ai kuwa yana cikin wanka sai ya ga 448 TASKARNOVELS.COM.NG wannan Kada ta taso masa. Ya yunkura domin ya ruga waje daga cikin koramar sai ya ga ai ba zai iya gujewa Kadar ba. Cikin tsananin tsoro Sarki Laffaru ya kurma uban ihu. Ai kuwa sai Ramlatul Siyam da Aljani Maruful Dauwaz suka rugo izuwa bakin koramar. Da isowarsu suka iske katuwar Kadar ta wangame bakinta za ta hadiye Sarki Laffaru. Cikin zafin nama Laffaru ya goce bai san sa'adda ya rungumi Kadar ba suka fara kokawa a cikin ruwan tana danna shi kasa, shi ma yana kokarin tasowa sama, kuma yana ci gaba da ihu gami da kiran taimako. Har Maruful Dauwaz ya yunkura zai kai masa dauki sai Ramlatul Siyam ta hana shi ta ce, "A haka ne zai iya samo sadakina? Wannan fa kada ce ba rikakken Zaki ba.Mu kyale shi kawai ya fara bai wa kansa horo tun kafin ya yi arba da rikakken Zaki. 449 TASKARNOVELS.COM.NG Nan fa aka ci gaba da gumurzu tsakanin wannan kada da Sarki Laffaru a cikin wannan ruwa. Sarki Laffaru ya ci gaba da rukunkume Kadar iya karfinsa ya ki yarda ya sake ta. Da yake Kadar ta ruku sosai sai kuwa ta kasa kwacewa amma sai ta yi amfani da jelarata ta rinka dukan jikin Laffaru. Duk sa'adda ta maka masa jelarta sai ka ga kamar da takobi aka yanke shi, take jikinsa ke darewa jini ya yi tsartuwa ko feshi yana mai fwalla ihu, amma duk da haka ya ki yarda ya saki Kadan duk da cewa wani lokaci tana danna shi izuwa karkashin ruwan numfashinsa na daukewa. Da zarar kadan ya taso sama sai ka ga sun ci gaba da gumurzu. 450 TASKARNOVELS.COM.NG Kafin a jima jikin Laffaru ya yi kaca-kaca da raunika. Ita kuwa Kadan sai ta ji ta fara gajiya don haka sai tayi nutso kasa taki dagowa sama. Koda Laffaru ya ga numfashinsa na neman daukewa gaba daya sai ya saki Kadan babu shiri ya fara iyo da sauri don ya kaj bakin gaɓar koramar. Ai kuwa sai kadan ya juyo da sauri suka kasa sabon tsere. Yayin da Sarki Laffaru ya auna ya ga cewa kafin ya isa bakin gabar koramar sai kadan ya cim masa sai kawai ya juya ya tare shi.Wannan karon sai Kadan ya kai wa kafarsa hari. Laffaru ya goce cikin zafin nama, amma duk da haka sai da Kadan ya wawuri tsokar nama mai kauri a cinyar Laffaru. 451 TASKARNOVELS.COM.NG Laffaru ya kurma uban ihu a lokacin da yai wuf ya sake rungumar Kadan suka ci gaba da kokawa a kan ruwan. Da kyar da sidin goshi Laffaru ya samu ya zare wata siririyar wuka a jikinsa ya daga sama ya kirɓawa Kadan. Bisa sa'a sai ya soke ido guda na Kadan. Take idon ya fashe, sai ga jini yana bulbula. Laffaru ya sake daga wukar ya luma ta a kan daya idon na Kadan. Ai kuwa sai Kadan ya yi wata irin gagarumar kara yai kasa ya lume izuwa karkashin koramar bai sake tasowa sama ba. Nan fa Laffaru ya fara iyo da kyar har ya samu ya fito bakin gaɓar koramar. Yana fitowa ya baje a kas sumamme. 452 TASKARNOVELS.COM.NG Koda Gimbiya Ramlatul Siyam da Maruful Dauwaz suka ga irin raunikan da wannan Kada ya yi wa Sarki Laffaru sai suka kamu da tsananin tausayinsa. Nan take Ramlatul Siyam ta ruga da gudu izuwa bakin koramar ta dauko Laffaru ta kai shi cikin tantinsa. Da kanta ta shiga yi masa magani ta dinke raunikan da suke bukatar dinki. Wannan rauni da ke kan cinyarsa kuwa sai magani ta zuba masa sannan ta nannade shi da kyalle mai kyau saboda wajen ba shi da kyan gani. A sannan ne Sarki Laffaru ya farfado daga dogon suman da ya yi. Yana bude idanunsa ya yi arba da Gimbiya Ramlatul Siyam tsugune a kansa tana yi murmushi kawai sai ta dube shi ta ce, "Tabbas ka yi Namijin kokari, Akwai alamun 453 TASKARNOVELS.COM.NG cewa za ka iya kawo sadakina amma fa sai ka yi matukar jajircewa." Koda gama fadin haka sai ta mike tsaye ta ce, "Ga abincin kalacinka nan na ajiye maka, lallai sai ka yi jinyar kwana bakwai sannan za ka sami kwarin jikinka har ka iya fita faratar sadakina. Nan take Ramlatul Siyam ta juya ta fice daga cikin tantin tana waigen Sarki Laffaru tana yi masa wani irin murmushi mai kama da na mugunta. Al'amarin da ya fusata shi ke nan ya ji kamar ma ya hakura da aurenta, amma da ya tuna cewa idan bai aure ta ba duk wahalar nan da ya sha a baya ta zamo ta banza sai ya ga batun hakura bai taso ba, koda zai rasa rayuwarsa, don haka sai ya ji ya karfafi zuciyarsa akan cewa lallai sai ya kawo sadakin auren Gimbiya Ramlatul Siyam ta kowane hali ko da kuwa shi ne sanadin ajalinsa. 454 TASKARNOVELS.COM.NG Lokacin da Ramlatul Siyam ta fito daga cikin tantin Laffaru sai ta hango Aljani Maruful Dauwaz zaune a can gefe daya ya yi tagumi, hawaye na zuba daga cikin idanunsa. Cikin tsananin mamaki Ramlatul Siyam ta karasa gare shi ta zauna daf da shi ta dube shi ta ce, "Ya kai Sarkin sadaukan aljanu me ya faru kake tunani mai zurfi haka har da zubar da hawaye?" Koda jin wannan tambaya sai Maruful Dauwaz ya yi ajiyar zuciya sannan ya share hawayensa ya ce, "Ya ke tauraruwar taurarin mata ta duniya, ki yi sani cewa, ba komai ne ya sa ni wannan zubar da hawaye ba face tsananin takaici bisa halin da muke ciki a rayuwarmu ni da ku. Zaman da na yi anan yanzu na tuno da irin labarin su Lafaru bisa tsananin wahalar da suka sha a cikin wadannan dazuzzuka guda biyar kafin su iso kogon Darul Iksina, da yadda wasunsu suka rasa masoyansu, ga shi kuma shi 455 TASKARNOVELS.COM.NG kansa wanda ya yaudare su ya jefa su a cikin wannan bala'i ya tashi a tutar babu, karshe ma ya rasa rayuwarsa a banza bai cika burinsa ba. Hakika abin da na fahimta a rayuwa shi ne, kowane mahaluki ya kan mutu da burinsa ne, domin buri ba ya yankewa face ajali ya riske shi. Babu mamaki mu ma nan da burinmu duk za mu mutu. Sa'adda Maruful Dauwa ya zo nan a zancensa sai Gimbiya Ramlatul Siyam ta yi ajiyar zuciya, a lokacin da idanunta suka ciko da kwallah sannan ta ce, "Ya kai sadaukin aljanu na duniya ka yi sani cewa, ita wannan rayuwar babu wani abu madawwame a cikinta, walau farin ciki ko bakin ciki. Yanzu dai ka dauki misali a kaina. Tun da na taso ina karama ban san wata wahalar duniya ba, kuma ban san kowa ba sai mahaifina tunda sa'adda uwata ta mutu ban fi shekara uku ba. 456 TASKARNOVELS.COM.NG Babu mahalukin da na shaku da shi sama da ubana amma yau ga shi mutuwa ta raba mu. Na rasa daular da nake ciki, yau ni ce a cikin daji ina rayuwa shigen irin ta dabbobi wacce ba ni da tabbacin tsaro na lafiyata kuma abin da zan ci ma sai na nema, Komai ni zan yi wa kaina. Koda jin haka sai Aljani Maruful dauwaz ya kamu da tsananin tausayin Gimbiya Ramlatul Siyam har hawaye ya sake zubo masa. Koda ganin haka sai ita ma Ramlatul Siyam ta fada kan kirjinsa ta rungume shi kuma ta fashe da matsanaicin kuka yana mai rarrashinta. Kamar yadda Ramlatul Siyam ta fadi haka al'amarin ya kasance, wato sai da Sarki Laffaru ya kwana bakwai yana jinyar jikinsa sannan ya samu lafiya gami da kwarin jikinsa. 457 TASKARNOVELS.COM.NG A ranar kwana na bakwai ne da hantsi Ramlatul Siyam ta kawo wa Sarki Laffaru takobinta gami da garkuwarta ta yaki ta mika masa ta ce, "Ga shi ya kai mijina na gobe, ka yi sani cewa lokaci ya yi da za ka tafi neman sadakina saboda haka, daga nan zuwa faduwar rana ina sauraron dawowarka tare da sadakin nawa sai ka kama hanya ka nausa cikin daji". Sa'adda Ramlatul Siyam ta zo nan a zancenta sai Sarki Laffaru ya ji tsoro ya baibaye shi kuma ya ji kamar ya ce ya fasa auren nata amma sai ya daure bai ce kala ba. Cikin sanyin jiki da alamun karayar zuciya ya karbi takobin da garkuwar sannan ya ce, "Shin za ki iya ba ni aron Maruful Dauwaz ya yi mini rakiya?". Ramlatul Siyam ta yi murmushi irin na mugunta ta ce, "Babu mai yi maka rakiya face takobinka da garkuwarka. Idan har rana ta fadi gari yai 458 TASKARNOVELS.COM.NG duhu muka ga ba ka dawo ba mun san ka mutu sai mu jira izuwa ranar da Rahila za ta gaya wa Maruful Dauwaz inda wasiyyar masoyiyarsa take sannan mu tashi mu bar wanan daji. Koda gama wannan jawabi sai Ramlatul Siyam ta juya ta tafi izuwa cikin tantinta. Cikin fushi da kunan rai Sarki Laffaru ya juya ya durfafi cikin daji yana tafe yana huci kai ka ce zai iya tarwatsa rundunar mayaka guda saboda kwarjininsa da kirarsa irin ta sadaukai amma ga wanda ya sani, banza ce ta kori wofi, domin ba zai iya tsinana komai ba, abu ne ma mawuyaci ya iya tsira da rayuwarsa. Sarki Laffaru ya ci gaba da tafiya har ya yi nisa a cikin daji, duk da cewa ya san cewa ba shi da wata jarumtaka a jikinsa wacce zai iya kashe rikakken Zaki har ya ciro kansa amma sai ya ji dukkan tsoro ya kau daga cikin zuciyarsa ko mutuwa ce ta tare shi ba zai gudu ba saboda ya fusata ainun kuma zuciyarsa ta kekashe. 459 TASKARNOVELS.COM.NG Sau tari a rayuwa dakewar zuciya shi ke haifar da samun nasara ba wai karfin jarumtaka ba. Sai da Sarki Laffaru ya yini a daji yana farautar rikakken Zaki amma bai gan shi ba. Wani abu da ya daure masa kai shi ne, ko daga nesa idan wadansu mugayen dabbobin suka hango Laffaru kamar su Damisa, Kura da sauransu sai ka ga suna komawa da baya ko su sauya hanya. Abin da bai sani ba shi ne, tsananin kwarjinin sa ne

Chapter 16 of 18