ya san cewa yana sa ran
cewa ba tafiyar bazan yake ba yana kan tafarkin
cika burinsa na duniya, wato zai ci gasar tseren
doki ta duniya, zai mallaki dukiya irin wacce bai
taɓa mallaka ba, kuma zai mallaki gimbiya
Shalirat 'yar Sarkin birnin Hairil Salas. Koda ya
zo nan a tunaninsa sai zuciyarsa ta ce da shi, "To
wai shin me yasa yanzu kake son Zarina wacce a
wannan tafiya ka hadu da ita, alhalin ga Shalirat
can wacce ka shafe shekara da shekaru kana
begenta da burin son aurenta?"
Koda Shaharan ya zo nan a zancen zucinsa sai
ya kasa bai wa kansa amsa, kuma hankalinsa ya
kara dugunzuma.
Sai da aka yi kwana hudu a bakin wannan
korama ana jinya sannan kowa ya ji kwarin
jikinsa aka yi shiri domin a shiga wannan daji na
biyu.
A wannan lokaci ne jikin boka Muzaffar ya yi
sanyi ainun ya kasa cewa a tashi da sauri a tafi.
Shi da ya kasance jagoran tafiya sai ga shi ya
kasa mikewa tsaye ma bare ya wuce kan gaba a
ci gaba da tafiyar.
49
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda ganin haka sai Sarki Laffaru ya je gaban
boka Muzaffar ya tsugunna suka fuskanci juna
ya ce, "Ya kai wannan boka, ka yi sani cewa
gabadayanmu nan jikinmu ya yi sanyi bisa ganin
yadda kai ma jikinka ya yi sanyi a cikin wannan
tafiya. Shin ka fitar da tsammani ne bisa samun
nasararmu?"
Sa'adda boka Muzaffar ya ji wannan tambaya sai
ya sunkui da kansa kas yai ajiyar zuciya, kuma
yai shiru kamar ba zai ce komai ba.
Daga can kuma sai ya dago kai ya dubi Sarki
Laffaru cikin alamun tausayawa, kuma cikin
sauke murya yadda babu wanda zai ji abin da
yake fadi face Laffarun, ya ce, "Ya kai abokina ka
yi sani cewa tun a baya sa'adda muka keta ta
cikin wannan daji mai mugayen aljanu rukuni
na uku zuciyata ta karaya ga samun nasararmu.
Ka tuna da irin tsananin wahalar da muka sha
sa'adda muka riski rukuni na biyu da na ukun
50
TASKARNOVELS.COM.NG
wanda in ba don jaruma Rahila ba da tuni gaba
dayanmu mun hallaka. Yanzu kuma da muka
shigo cikin daji na farko daga cikin guda biyar
waɗanda daga su sai kogon Darul Iksina, na ga
wannan masifa da muka shiga sai na tabbatar
da cewa babu mai isa kogon Darul Iksina face
mai tsananin NISAN KWANA.
Ka sani cewa bala'in da ke cikin ragowar
dazuzzukan hudu yafi na wannan daji na farko.
Ni kam na yi matukar nadama bisa yi muku
jagora a cikin wannan tafiya, domin a yanzu na
tabbatar da cewa kunya zan ji domin na dora ku
akan hanyar da ba za ta bulle ba. Koda boka
Muzaffar ya zo nan zancensa sai Sarki Laffaru ya
bushe da dariya. Al'amarin da ya matukar bai
wa boka Muzaffar mamaki ke nan.
Lokaci daya sai Sarki Laffaru ya murtuke fuska
ya ce, "Ya kai wannan boka, ka yi sani cewa shi
bala'i kafin ya zo ne ake tsoronsa ko kuma ake
nadamar tunkararsa, amma idan ka riga ka
shige shi sai a rungumi duk abin da ya zo da shi.
Ina tabbatar maka da cewa har a yanzu ba na jin
51
TASKARNOVELS.COM.NG
tsoro ko fargabar komai, duk da cewa ban yi
kokarin komai ba a cikin wannan tafiya. In da
ace karfin damtsena zai dawo jikina a yanzu ina
tabbatar maka da cewa jarumtakar da zan yi ko
jaruma Rahila ba za ta lya irinta ba. Ina mai
shawartarka da ka daina nuna karayar
zuciyarka ga abokan tafiya, domin kada suma su
karaya su janye ci gaba da wannan tafiya. Ni
kam gwara na rasa rayuwata da dai na koma
gida babu biyan wannan bukata, tunda dai ni da
gawar babu bambanci tunda zan rasa komai
nawa, kuma dan cikina yavzo ya zama ajalina.
Kai ma idan ka yi tunani rayuwarka a cikin
mugun hadari take, idan har ba mu sami nasara
ba bisa wannan bukata da ke gabanmu, domin
ka kulla gaba da matata Sharlis, tunda kai ne ka
kubutar da ni daga sharrinta. Ka fi ni sanin
iyakar karfin Sharlis, don haka kai ne ka san
abin da zai biyo baya fiye da ni".
Sa'adda Sarki Laffaru ya zo nan a zancensa sai
kwalla ta cika idanun boka Muzaffar ya ce, "Ya
kai abókina hakika duk abin da ka fadi gaskiya
ne, kuma a yanzu ma inda ka san irin
mummunar 6arnar da Sharlis ta yi mana ni da
52
TASKARNOVELS.COM.NG
kai da ka dada tabbatar da cewa ba mu da wani
kwanciyar hankali wanda ya fi mu sami nasarar
abin da muka fito nema. Cikin firgici Sarki
Laffaru ya dubi boka Muzaffar ya ce "Wane irin
mugun abu Sharlis ta yi mini a yanzu bayan na
baro kasata?".
Muzaffar ya girgiza kai sannan ya ce, A halin
yanzu Sharlis ta yi yaki da mayakan Sarki
Nurbas ita kadai ta tarwatsa su, kuma ta kashe
Sarki Nurbas. Aljani Shalbasha ibini Rauhuba
kuwa, wanda muka baro a matsayin halifanka ta
gano ko wane ne shi, har ta tura shi izuwa
birnin Zaruf yana wakilcin Shugabancin birnin.
Akan karagarka kuwa ta mulki, ta dora danta
Shaddad yana mulkin jama'arka cikin adalci da
kyautatawa talakawa, saɓanin na ka mulkin. Ina
tabbatar maka da cewa danka Shaddad ya sami
farin jini ainun a wajen jama'ar Kasarka, basa
fatan ka komo gare su. Dubi tafin hannuna
domin ka ga zahiri".
Koda gama fadin haka sai boka Muzaffar ya
bude tafin hannunsa. Nan take hoton fadar Sarki
53
TASKARNOVELS.COM.NG
Laffaru ya baiyana, sai ga Shaddad yaro dan
shekara uku akan karagar mulki, mahaifiyarsa
Sharlis na zaune a gefensa, kuma ga fadawa sun
kewaye Shaddad ana tafiyar da harkokin mulki,
talakawa sai shigowa suke cikin fadar suna
zubewa kasa suna kwasar gaisuwa, yaro
Shaddad na sawa ana basu kyautar suturu,
dukiya da kayayyakin abinci.
Koda ganin wannan al'amari sai bakin ciki ya
sake turnuke Sarki Laffaru fiye da ko yaushe,
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar za ta kone,
bai sansa'adda idanunsa suka ciko da kwallah
ba suka fara zubar da hawaye.
Lokacin da boka Muzaffar ya ga halin da Sarki
Laffaru ya shiga sai ya yi sauri ya shafi tafin
hannunsa, hoton komai ya ɓace, sannan ya dafa
kafadar Sarki Laffaru ya ce "Kada ka damu ya
kai abokina, ita rayuwa dama haka take, wata
rana kai ne a sama, wata ran kuma ka zamo a
kasa. Shin ka manta sa'adda kake kan
sharafinka ne lokacin da ka buwayi gaba dayan
kasashen da ke nahiyarka gaba daya?
54
TASKARNOVELS.COM.NG
Ina mai kara maka karfin guiwa akan wannan
gagarumin aiki da ke gabanmu domin ba mu da
wani zaɓi wanda ya fi mu tabbatar da cewa mun
sami nasarar abin da muka fito nema. Koda
gama faɗin haka sai boka Muzaffar ya yi shiru
yana mai sunkui da kansa kas cikin halin
tsananin damuwa. Sarki Laffaru ya dube shi ya
ce, "Ya kai wannan jarumin boka, dazu ka gaya
mini cewa kai ma Sharlis ta yi maka mummunar
barna amma ba ka gaya mini irin ɓarnar da ta yi
maka ba".
Boka Muzaffar ya dago kai ya dubi Sarki Laffaru
ya ce, "A halin yanzu Sharlis ta kama matata da
dana guda daya jal ta kai shi can wani gidanta
da ke can dajin Bairul Aswan da ke karshen
birnin Kisra, ta kulle su a cikin kurkuku, kuma ta
yi alkawarin cewa ba za ta sake su ba face ta
kama ni ta yi mini azaba mai radadi, sannan ta
yi mini kisan gilla bisa taimakon da na yi maka.
Ka sani cewa a duniya babu abinda nake so
sama da matata da dana, a dalilinsu ne ma nake
son na mallaki rabin mulkin kasarka da rabin
55
TASKARNOVELS.COM.NG
dukiyarka domin na cika musu babban burinsu
a rayuwa. A takaice dai burin da nake son ya
cika ba nawa ba ne na iyalina ne. Yanzu ga shi su
kansu iyalan nawa suna cikin mugun hali kuma
ba zan iya ceton rayuwarsu ba face da taimakon
aljani Maruful Dauwaz, domin shi kadai ne zai
iya zuwa wancan gida na Sharlis ya dauko mini
iyalina saboda tsananin tsaro da karfin sihirin
da ke gidan.
Duk duniya gidan Sarki Nashmir ne kadai ya fi
gidan Sharlis tsaro" Da jin wannan batu sai
Sarki Laffaru ya dubi Muzaffar cikin tsananin
damuwa ya ce, "Amma hakika Sharlis ba
karamar hatsabibiya ba ce. Ni kaina na yi
mamakin yadda aka yi ta sami nasara a kaina
har tsafinta ya ci ni ta raba ni da jarumtakata."
Koda jin wannan batu sai boka Muzaffar ya
bushe da dariya, al'amarin da ya bai wa gaba
dayan abokan tafiya mamaki ke nan, duk da
cewa basu san dalilin yin dariyar tasa ba, tunda
basa jin abin da suke tattaunawa, saboda a can
gefe daya suke zaune.
Bayan boka Muzaffar ya yi dariyar har ta ishe
shi sai ya dubi Laffaru ya ce, "Ya kai abokina ai
dole ne ka yi mamaki. Amma abinda nake so ka
56
TASKARNOVELS.COM.NG
fahimta shi ne, ka kiyayi ramuwar mutumin da
ka zalunta bisa ka fi karfinsa, babu yarda zai yi,
domin zai iya shafe shekara dari yana yi maka
TANADIN FANSA.
Ka yi sani cewa tun daga ranar da ka yi wa
iyayen mahaifin Sharlis da sauran iyalansa kisan
gilla, ka yi babban kuskure da ba ka kashe boka
Narwas ba, domin sai da ya shekara bakwai
yana neman karfin ilimin tsafi har ya gawurta
ainun, amma duk sirrikan da ya samo sai ya
dinga zuba su a jikin 'yarsa Sharlis, bayan ya
samo ta a wajen wani masunci da ya tsince ta,
ya dinga horar da ita akan yadda za ta dauki
fansa a kanka har ta girma, kuma ya hane ta da
kada ta kuskura ta ce za ta je ta tare ka har sai a
ranar da aka zo har gida aka kama ta aka kai ta
gabanka ka tara da ita, a sannan ne za ka rasa
gaba dayan kuzarin jikinka ta sami damar yin
ramuwar gayya akanka sannu a hankali har
izuwa lokacin da danta zai girma ya yi maka
kisan gilla". Sa'adda boka Muzaffar ya zo nan a
jawabinsa sai jikin Sarki Laffaru ya yi sanyi,
kuma yai shiru ya kasa cewa komai, Jim kadan
sai Sarki Laffaru ya mike tsaye zumbur! Kamar
57
TASKARNOVELS.COM.NG
an soke shi da takobi, kawai sa ya dubi abokan
tafiyar ya ce, "Ku zo mu ci gàba da tafiya..
Ba tare da jiran komai ba Saki Lafaru ya zare
takobinsa ya nausa cikin dajin kamar zai iya
tsinana wani abu. Da ganin haka sai shi ma boka
Muzaffar ya mike tsaye ya yafito aljani
Marhabul Zaurus da hannu ya take masa baya
suka bi bayan Laffaru.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba sauran
gabadayan jaruman suka goya masoyansu a
bayansu suka bi bayan su Muzaffar aka ci gaba
da tafiya. Lokacin da boka Muzaffar ya fahimci
cewar an iso farkon wannan daji na biyu sai ya
ďaga hannu sama yana mai nuni da a dakata.
Nan take kuwa kowa ya tsaya cak. Boka
Muzaffar ya dubi jaruma Shadira ya ce, Ya ke
wannan jaruma mai jarumtakar ban al'ajabi, ki
yi sani cewa yanzu ne za mu shiga dajin da ke
kadai ce za ki iya yi mana jagora har mu sami
damar fita lafiya, sai ki zo ki wuce kan gaba
domin bai fi taku goma ba ya rage mana mu
shiga wannan daji.
58
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin haka sai Shadira ta ciro Bakanta daga
bayanuta. Wohoho! Ita dai wannan baka ta isa
abin kallo, domin Baka ce ta musamman wacce
mutum bai taɓa ganin irinta ba. Bakar, ta
kasance katuwa ga tsawo ga nauyi, idan mutum
bai cika sadauki ba ko daukarta ma ba zai iya yi
ba, taɓe bakar kuwa sai karti biyar sun hada
karfi suke iyawa. Amma wani abin mamaki da
hannu daya jaruma Shadira ta rike wannan
Baka, da hannu ďaya kuma sai ta zaro kibiyoyi
ashirin daga cikin kwanson kibiyoyin da ke
daure a bayanta ta ďana su akan Bakan sannan
ta wuce kan gaba ta nufi cikin dajin cikin sanda
da kalle-kalle tana duban kowacce kusurwa.
A wannan lokaci ko kibiya ce ta zo gilmawa sai
Shadira ta ɓaro ta kasa saboda zafin namanta da
iya saitinta. Sa'adda boka Muzaffar ya ga
Shadira ta wuce kan gaba sai ya dubi sauran
abokan tafiya ya ce "Kowa ya zauna cikin shiri.
Ku sani cewa kokarin Shadira kadai ba zai
kwace mu ba sai mun haɗa da namu kokarin.
Gama fadin hakan ke da wuya sai shi ma boka
59
TASKARNOVELS.COM.NG
Muzaffar ya zare tasa takobin ya bi bayan
Shadira. Lafaru ne ke biye da shi rike da
takobinsa, kai kace shi ma zai taka wata
muhimmiyar rawar gani a gumurzun da za a yi,
musamman idan mutum ya yi la'akari da
kwarjininsa da kuma kirar jikinsa irin ta
manyan sadaukai.
Nan dai sauran jaruman suka bi bayan Sarki
Laffaru gabadaya aka nausa cikin dajin.
Sai da aka yi tafiyar rabin sa'a a cikin dari-dari
da tsoro-tsoro, amma ba su ga wadannan
mugayen Birirrika ba.
Kwatsam! Sai suka fara jin sautin giftawar
Biririkan a sama kan bishiyoyi. Yif! Shif!! Shif!!!
Da kuma dirarsu, jif! Jif!! Jif!!! Amma ko daya
daga cikinsu basu gani ba. Al'amarin da ya
dugunzuma hankalin jaruman ke nan, domin
sun fahinici cewa a ko yaushe Birirrikan za su
iya saukar mikiya a kansu.
60
TASKARNOVELS.COM.NG
A wannan lokaci ne jaruma Shadira ta fusata
ainun bisa rashin ganin Birirrikan, sai jin sautin
giftawar tasu da dirarsu kawai. Nan ake Shadira
ta yi amfani da basirarta da lissafin
kwakwalwarta kawai sai ta harba kibiyoyinta
izuwa saman wadansu bishiyoyi masu duhuwar
ganyaye da ke gabas da yamma, kudu da arewa.
Wato a cikin dakika goma sha shida ta harba
kibiyoyi tamanin.
Ba zato ba tsammani sai suka ga Birirrika
tamanin sun fado kasa matattu, wadannan
kibiyoyi sun cake a cikin kirajensu.
Kaico! Rashin sani yafi dare duhu. Inda Shadira
ta san bala'in da zai biyo baya sakamakon
wannan ɓarna da ta yi wa Birirrika da ba ta yi
ba. Fadowar wadannan Birirrika guda tamanin
kasa ke da wuya sai kawai sauran Birirrika
kimanin su dubu dari uku da doriya suka taho a
sama gabadayansu suka yi yo kan su Shadira.
Nan fa aka kasa mugun tsere. Duk da tsananin
gudu irin na sadauki Shaharan sai da ya raina
61
TASKARNOVELS.COM.NG
kansa a wannan rana, domin ya kasa tserewa
Birirrikan, har shan gaban gabansa suke in ba
don ma Shadira na kado su ba da kibiyoyi da
tuni sun yagalgala shi.
Lokacin da jaruman suka fahimci gudu ba zai
tserar da su ba sai su ma suka fara amfani da
makamansu suna yakar Birirrikan, amma sai
abin ya wuce saninsu, domin ko biri daya sun
kasa kashewa, kuma Birirrikan suna kawo musu
sara da suka cikin tsananin karfi da tsafin nama.
Yawan Birirrikan ne ya fara rikita su, tun suna
iya kai martani har suka kasa, sai dai kokarin
kare kai. Gashi ana cikin gudu ne. Har sai da ya
zamana cewa jaruman sun kasa ma kare
martanin sun fara faduwa kasa, amma sai suka
rinka mikewa zumbur suna daďa ci gaba da
gudu suna kare harin saboda juriyarsu da
nacinsu. In ba don jaruman sun kasance masu
matukar juriya ba da tuni an gama hallaka su.
Shi kuwa Sarki Laffaru, boka Muzaffar ne ya
rinka kare shi. Lokacin da masifa ta kai masifa
sai boka Muzaffar ya goya Sarki Laffaru a
bayansa domin idan ya bar shi yana gudu da
62
TASKARNOVELS.COM.NG
kansa wadannan Birirrikan za su iya hallaka shi
a ko yaushe. Haka boka Muzaffar ya ci gaba da
yaki yana goye da Sarki Laffaru. Ga nauyin sarki
Laffaru a bayansa, kuma ga shi yana gudu yana
kare mugayen hare-hare na Birirrikan. Hakika
shi bala'i ba shi da dadi komai kankantarsa.
Tunda wadannan jarumai suke gumurzu a
yakuna da dama da suka halarta a rayuwarsu
basu taɓa tsintar kansu a cikin yaki mai tsanani
ba irin wannan, domin ga shi dai suna iya
kokarinsu amma sun kasa kashe koda biri daya
daga cikin Birirrikan. Ita kanta jaruma Shadira
da ta fara samun nasarar kashe su da farko,
yanzu kuma al'amura sun sauya, domin koda ta
same su da kibiyoyin sai ka ga sun ki fadowa
kasa daga saman, sai dai kawai su sa
hannayensu su zare kibiyoyin su ci gaba da kai
mata mugun hari, duk da cewa jini na бulɓula a
jikinsu.
Al'amarin da ya matukar girgiza hankalinta
kenan ta gane cewa lallai shayi ba ruwa ba ne.
Ana cikin haka ne Biririkan suka fusata ainun da
63
TASKARNOVELS.COM.NG
irin ɓarnar da Shadira ke yi musu, don haka sai
suka afka mata su da yawa kimanin su dubu
saba'in a lokaci guda da nufin su yagalgala ta su
yi filla-filla da sassan jikinta yadda wani ma
daga cikinsu ba zai sami koda tsoka daya ba
daga jikinta.
Koda Imran ya hango abin da ke shirin afkuwa
sai ya kwarara uban ihu ya daka wawan tsalle
sama, bisa sa'a sai ya dira akan wuyan daya
daga cikin Birirrikan da suka lulluɓe ta, ya
dankara masa duka da sanda aka. Take kwanyar
kan birnin ta tarwatse ya sulale kasa matacce.
Cikin zafin nama Imran ya bar kansa ya dira
akan wani ya ci gaba da yi musu rotse a ka. Nan
da nan ya tarwatsa gaba dayan wadannan
Birirrikan da suka yanyame Shadira, a lokaci
guda wanda tuni sun kai Shadira kas har sun yi
mata rauni biyar a jikinta da kaifin faratansu
tamkar da kaifin takobi aka yanke ta, har jiri ya
fara dibarta.
64
TASKARNOVELS.COM.NG
Yaro Masnur da ke goye a bayanta yaji ciwo a
kansa jini na zuba har ma ya suma. Koda ganin
wannan hali da Shadira ke ciki kuma ga shi yana
goye da mahaifiyarsa a bayansa wacce ita ma ta
ji raunika a jikinta sakamakon yawan faduwa
kasa da suke yi ta fita daga haiyacinta sai
hankalinsa ya dugunzuma ainun, zuciyarsa ta
fusata, kawai sai ya sungumi Shadira ya goyata a
kirjinsa ya daure ta tamau da wani rawani nasa
sannan ya ci gaba da yakin a haka ya zamana
cewa rai uku yake dauke da su shi kadai.
( WATO SADAUKI IMRAN YA CIKA GWARZON
NAMIJI)
A haka yake yakin kuma yana gudu bai fasa ba
yana ragargazar birirrikan ta sama da kasa.
Wohoho! Idan maza sun kai maza dole ne ka ga
suna jarumtaka ta ban mamaki. Shi kansa
sadauki Imran ya yi mamakin ganin yadda ya
iya yin wannan jarumtaka, domin bai taɓa yin
kamarta ba a rayuwarsa. Sai ga shi yana
samarwa da abokan tafiya hanya da karfin tsiya
fiye da kokarin da Shadira ta yi da farko. A
65
TASKARNOVELS.COM.NG
wannan lokaci Shadira ta fita daga haiyacinta
matuka, amma tana iya ganin fuskar Imran
dishi- dishi a gabanta kuma tana jin nauyin dan
uwanta Masnur a gadon bayanta.
Haiman, Rahila, Zarina, Shaharan da boka
Muzaffar kuwa, a wannan lokaci duk sun shiga
cikin wani irin mugun hali domin ta kai cewa an
birirrikan sun fara samun nasarar yi musu
rauni. Boka Muzaffar an soke shi da tsinin farce
a gefen cikinsa, wajen ya bule jini na zuba,
amma sai yai sauri ya sa tsumma ya toshe бular
kuma ya daure wajen tamau ya ci gaba da gudu
a haka yana kare harurruka duk da cewar jini
bai fasa digaba daga cikin 6ular ba.
In ba don tsananin juriya da jarumtakarsa ba da
tuni ya fadi kasa domin shi ma jiri ya fara
dibarsa. Su kuwa su Haiman babu wanda
Birirrikan ba su sare shi ba a kafa, hannu da
kafada, har jan kafafunsu suke suna kasa gudu
sosai, amma saboda naci sun ki yarda su fadi
66
TASKARNOVELS.COM.NG
kasa domin sun san cewa suna faduwa za su
zama gawa abincin Birirrikan.
Babu abinda zai baibwa mutum tausayi face
ganin yadda gaba dayan jaruman suka jigata
ainun ya zamana cewa babu sauran wani gwani
a cikinsu, kuma babu wanda ke da tabbacin zai
tsira da rayuwarsa. Lumaira da ke goye a bayan
mijinta tana jin yadda yake ihu idan an sare shi
ko an soke shi har jini na fantsamuwa a
fuskarta, sai ta fashe da kuka, ta yi nadamar
baro gida bisa cikar wannan buri da ke gabansu.
Duk da cewa ba ta iya ganin zahirin abin da ke
faruwa.
Shi kuwa Sarkin Farisa da ke goye a bayan 'yar
uwarsa Zarina, lokacin da ya ga jikin 'yar
uwarsa ya yi fata-fata da jini da raunika, sai shi
ma ya kama kuka saboda tsananin tausayinta.
Hakika dan uwa rabin jiki ne. A duk sa'adda
wadannan Birirrikan suka kawo sara ko suka za
su sami Sarkin Farisa da zarar Zarina ta ankara
kuma ta ga ba za ta iya kare hare da makaminta
ba sai ta juya baya a sami jikinta. Sai dai ka ji ta
67
TASKARNOVELS.COM.NG
kwalla ihu ta durkushe kasa, amma kafin
Birirrikan su sake lulluɓe ta sai ka ga ta sake
mikewa ta ci gaba da gudu da artabu
Lokacin da aka kara shafe wani lokaci ya
zamana cewa Zarina ba ta iya ci gaba da gudu
sai tafiya tana tangadi kamar wacce ta sha giya
ta bugu sakamakon yawan jinin da ke zuba a
jikinta, jiri na dibarta. Ana cikin haka ne wani
Biri ya make ta da tafin hannunsa a fuska.
Saboda karfin dukan da ya yi ma ta sai da tayi
katantanwa sau uku sannan ta kife kasa da rub
da ciki a cikin mugun yanayi, tana gani dishidishi.
Wannan Biri sai ya dira a gabanta da nufin ya
cisge wuyanta da wuyan dan uwanta Sarkin
Farisa da ke goye a bayanta.
Ba zato ba tsammani sai wannan Biri ya ji an
dankara masa naushi a tsakiyar kansa. Take
kwanyarsa ta ɓare, sai ga kwakwalwa ta yi
68
TASKARNOVELS.COM.NG
ɓullutso ta tarwatse a sama, ya baje a kasa
matacce.
Cikin matukar zafin nama Shaharan ya suri
Zarina da dan uwanta ya goya su a bayansa ya
manta da batun dokinsa, wanda ke goye a bayan
aljani Marhabul Zaurus ya falfala da azababben
gudu irin wanda bai taɓa yi ba a rayuwarsa. Sai
ga shi wannan karon ya tserewa Birirrikan duk
da cewa a sama suke binsa, amma ya ba su
muguwar rata.
Al'amarin aljani Marhabul Zaurus kuwa, shi ma
a wannan lokaci ya sami raunika sama da guda
arba'in a jikinsa, da kyar yake iya gudu goye da
dokin Shaharan, har ma yana faduwa yana tashi
saboda juriya da na ci.
Shi kansa dokin na Shaharan an sassare shi ya
pmfi sau goma, kamar ma ba zai rayu ba, domin
ko motsin kirki ba ya iya yi akan aljani
Marhabul Zaurus, sai numfashi sama-sama.
69
TASKARNOVELS.COM.NG
Hakika wannan rana dai babu wanda bai ga
mutuwa ba muraran a cikin wannan abokan
tafiya. Kuma babu wanda bai sami raunika sama
da guda goma ba a jikinsa ba. Har 'yan uwan
jaruman wadanda bavsu iya kare kansu bare su
kare wani.
Sarki Laffaru kuwa, rauni tara ne a gadon
bayansa, kuma ya daɗe da suma a bayan boka
Muzaffar, amma saboda bala'i ya kai bala'i, shi
kansa boka Muzaffar din yana cikin mugun hali
bai san abinda ya faru ga Sarki Laffaru ba.
Ita ma gimbiya Rahila wacce ake ganin cewa tafi
kowa jarumtaka, juriya da na ci, sai da ta sami
manyan raunika guda uku a jikinta, ya zamana
cewa da kyar take iya gumurzu kuma tuni ta
karaya, ta san cewa dayansu ba zai tsira ba daga
sharrin wadannan Birirrika.
70
TASKARNOVELS.COM.NG
Sai da aka shafe sa'a hudu cur! Ana wannan
bakin gumurzu tsakanin wadannan Birirrika da
su sadauki Shaharan, amma ba a sake kashe
wani biri koda guda daya ba.
Lokacin da jaruma Shadira ta dawo cikin
haiyacinta sa'adda ta baje a kasa da rub da ciki,
tana bude idanunta ta ga jini na malala akan
fuskarta, kuma ta taɓa dan uwanta Masnur
wanda ke goye a bayanta ta ji ya langwaɓe
kamar ba shi da rai, sai ta takarkare ta kwarara
uban ihu cikin tsananin fusata.
Kamar sifirin haka ta do ki kasa da hannayenta
biyu, sai gani aka yi ta yi sama kamar an janye ta
da majajjawa. Tana saman ta janyo kibiyoyi a
kuttun bakanta ta dana akan bakanta ta taɓe ta
sakarwa Birirrikan harbi. Nan fa kibiyoyin guda
ashirin suka cake a cikin idanun Birirrika guda
ashirin. Take suka zube kasa matattu.
71
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda ta ga ta sami wannan nasara sai ta ki
yarda ta duro kasa kawai sai ta rinka dira akan
bishiyoyi tana dada yin tsalle sama kamar
tsuntsuwa mai fuka-fuki. A saman ta ci gaba da
zaro kibiyoyi tana dada ďanawa akan kwarin ta
yi ta harbin Birirrikan cikin bakin zafin nama
wanda ita kanta tavyi mamakin yadda aka yi ta
iya wannan jarumtaka.
A wannan lokaci tuni sauran abokan tafiyarta
duk sun sare suna zubewa kasa cikin tsananin
galabaita, wasu ma a sume suke, Shadira ce
kadai take gumurzu da Birirrikan.
Ganin irin muguwar ɓarnar da Shadira ke yiwa
Birirrikan ne yasa Birirrikan suka rabu da
sauran abokan tafiyar suka mai da hankalinsu
akanta suna daka tsalle sama domin su cafke ta
amma sai ta zame musu alakakai ta rinka zulle
musu ta zama kamar shaidaniya a tsakiyarsu,
tana dada ci gaba da ragargazar su.
72
TASKARNOVELS.COM.NG
Haka dai aka ci gaba da wannan azababben yaki
tsakanin jaruma Shadira ita kaɗai da waɗannan
mugayen Birirrikan ba ji ba gani, kuma ba
sassauci domin tana yin yaki ne da dukkan
karfinta cikin kunar rai da dakewar zuciya ko ita
ko su. Su ma Birirrikan sai suka haukace suna ta
yin wannan ruri mai dimauta bil'Adama suna ta
kai wa Shadira mugayen hare-hare. Duk sa'adda
ta ga za a kaiwa Masnur hari sai ta wurkila
bayanta ta goce, ta gwammate a sami jikinta. Da
zarar an sari jikinta ko an soketa sai ta kurma
uban ihu ta yi kamar za ta rikito kasa, amma
saboda na ci sai ka ga ta daure ta ci gaba da
gumurzu. Sai da aka shafe sa'a biyu da rabi ana
wannan masifaffen artabu sannan Shadira ta
sami nasarar kashe gabadayan Birirrikan, itama
ta rikito kasa, ji kake bam! fuskarta ta gwaru da
kasa ta baje a kasa sumammiya.
A wannan lokaci sadauki Haiman ne kadai a
zaune cikin haiyacinsa, amma kowa ya suma.
Sadauki Haiman yai sauri ya kwance matarsa
Lumaira daga bayansa ya kwantar da ita a kasa.
Koda ya ga bata wani motsi kuma ga raunika
har guda uku a jikinta sai ya rude ya kidime yai
73
TASKARNOVELS.COM.NG
zumbur ya samo ruwa ya yayyafa ma ta a
fuskarta. Faruwar hakan ke da wuya sai ta
farfado tana mai jan dogon numfashi. Koda ta
bude idanunta ta ga mijinta zaune a gabanta a
raye sai ta rungume shi, duk su biyun suka
kamu da tsananin farin ciki. Jim kadan kuma sai
sauran abokan tafiya suka fara farfadowa suna
dawowa cikin haiyacinsu, duk wanda ya bude
idonsa ya ga masoyinsa a raye sai ya rungume
shi yana murna.
Sai da kowa ya nutsu sannan aka ga cewa har
yanzu jaruma Shadira bata farfado ba, shi ma
dan uwanta yaro Masnur wanda ke goye a
bayanta bai farfadoba kamar maya zama gawa,
domin babu ko alamar numfashi a jikinsa.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin kowa ke
nan. Cikin hanzari aka kwance Masnur daga
bayan Shadira aka shiga yi musu magani ana ta
yayyafa musu ruwa domin su farfado. Da kyar
da sidin goshi aka sami nasara Shadira ta fara
numfashi sama-sama, shi kuwa yaro Masnur
babu labari. Nan take hankalin kowa ya kara
dugunzuma aka shiga shawarar abin da ya
kamata a yi. Boka Muzaffar ya mike
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 18