dai ya yi
274
TASKARNOVELS.COM.NG
masa dariya, domin huhun-ma'ahun ne, da
wanzuwarsa a filin yaki gwara ma a ajiye dutse
wanda ba shi da rai, wata kila abokin gaba ya yi
tuntuɓe da shi.
Lokacin da su Rahila suka gama kintsawa sai
mahaifinta ya zo gare su domin su yi bankwana.
Tun kafin mahaifin nata ya karaso daf da ita, ita
da shi suka fara zubar da hawaye.
Rahila ta karasa gare shi a guje ta rungume shi
kuma ta fashe da kuka tana mai cewa, "Ya kai
Abbana an zo an raba ni da kai a karo na farko
bisa niyyar cewa zan tafi don cika burin
rayuwata amma ga shi har yanzu burin bai cika
ba. Yanzu ga shi zan sake rabuwa da kai a karo
na biyu. Tabbas wannan ita ce rabuwarmu ta
karshe domin idan na dawo na dwo ke nan ba
za mu sake rabuwa ba. Ka kasance mai yi min
fatan samun sa'a da nasara."
275
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan batu sai shi ma ya fashe da
kuka ya ce, "Ya ke 'yata, tabbas zan kasance a
cikin yi miki fatan samun nasara dare da rana
har ki dawo daga wannan gagarumar tafiya. Ki
tuna cewa ni ma dukkan burina ya dogara akan
samun nasararki saboda ke ce kadai 'yata a
duniya. Ba ni da burin da ya fi na ga aurenki
kafin cikar ajalina domin na sami jikoki
wadanda za su yada zuri'ata a doron kasa bayan
rayuwata. Yanzu ga shi ba za ki yi aure ba face
kun sami nasara a wannan gagarumin yaki da za
ku tafi. Babu wanda yake da tabbacin za ku sami
wannan nasara amma in dai da rai, akwai rabo."
Koda jin wannan batu sai Rahila ta sake
kankame mahaifinta a jikinta tana mai daďa
rushewa da kuka kuma ta ji kamar ta fasa
wannan tafiya.
Da kyar Sarki Laffaru ya janye Rahila daga jikin
mahaifinta ya dora ta a kan doki shi ma ya hau
wani dokin sannan wasu Dakaru suka kwashi
dukkan kayan yakinsu suka yi musu rakiya
izuwa bayan gari inda Aljani Maruful Dauwaz ke
276
TASKARNOVELS.COM.NG
jiransu. Da zuwansu kuwa suka iske Aljani
Maruful Dauwa a tsaye cikin wata irin
gagarumar shigar yaki irin wacce ba su taɓa
gani ba a rayuwarsu.
Maruful Dauwaz na sanye cikin waɗansu
bakaken kayan karfe na riga da wando. Hatta
fuka- fukansa ya lulluɓe su da bakin karfen,
sannan a kugunsa akwai wata zabgegiyar takobi
mai tsananin tsawo, fadi da tsinin tsiya, gami da
kaifin gayawa jini na wuce. Ita kadai takobin sai
sheki da walwali take yi tana dallare idanun
wanda duk yai arba da ita.
Sannan a wuyansa ya rataya wata garkuwa
wacce aka yi ta da zallar karfe Lu'u-lu'u fari tas,
ita ma sai sheki da walwali take yi.
Sa'adda Rahila da Sarki Laffaru suka ga Aljani
Maruful Dauwaz a cikin wannan gagarumar
shigar yaki sai suka cika da tsananin mamaki
domin a duk tsawon tafiyar da suka yi tun daga
277
TASKARNOVELS.COM.NG
kogon Darul Iksina ba su ganshi da wadannan
kaya ba.
Abin tambaya anan shi ne, a ina Maruful
Dauwaz ya samo wadannan kayan yaki? Amsar
da suka kasa bai wa kansu ke nan, amma sai
suka kudurce a ransu cewa lallai nan gaba idan
an sami sukuni sai sun yi masa wannan
tambaya.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba aka zuba gaba
dayan wadannan kayan yakin akan Aljani
Maruful Dauwaz, sannan Rahila da Sarki Laffaru
suka hau kan Maruful Dauwaz din suma suka
zauna.
Nan take Maruful Dauwaz ya bude fuka- fukansa
ya tashi sama. Kafin kiftawar ido ya luluka a
cikin iska ya fara tsala azababben gudu yana
mai tunkarar hanyar da za ta kai shi Birnin
Hindu.
278
TASKARNOVELS.COM.NG
Duk wannan abu da ya faru tsakanin su Rahila
da Aljani Maruful Dauwaz, Sarki Nashmir na
Birnin Hindu ya gani a cikin madubin TSAFINSA
a lokacin da yake zaune a kasaitacciyar fadarsa
tare da 'yarsa Gimbiya Ramlatul Siyam,
tauraruwar taurarin matan duniya na wannan
zamani.
Gimbiya Ramlatul Siyam ta kasance kyakkyawar
mace ta gaban misali, domin babu wani mutum
da zai iya fasalta ainihin kyawun fuskarta da
kyan dirin jikinta daidai da Yadda Allah Ya ba ta,
sai dai Ya kwatanta daidai iyawarsa. A takaice
dai akan batun kyau sai dai a kira Gimbiya
Ramlatul Siyam Kurun-kus!
Masu bincike da masana tarihi sun tabbatar da
cewa a wannan lokaci babu wata fada daga cikin
dukkan fadodin duniya wacce ta fi ta Sarki
Nashmir girma, ginuwa da katuwa. Domin
komai arzikin BASARAKE da bunkasarsa in dai
ya shiga cikin fadar sai ya zama cikakken dan
kauye wanda bai taɓa shiga Birni ba. Kai! irin
wannan daula da aka tanada a cikin gidan
279
TASKARNOVELS.COM.NG
sarautar kuwa, sai dai a kirashi da "ALJANNAR
DUNIYA.
Lokacin da Sarki Nashmir ya ga su Aljani
Maruful Dauwaz sun taho izuwa fadarsa domin
raba shi da 'yarsa Gimbiya Ramlatul Siyam
kuma su debi yawun barcinsa, sai ya bushe da
mahaukaciyar dariya,gabaďaya daya
Fadawansa ma da ke zaune a fadar sai suka taya
shi dariyar domin sun san cewa abu ne wanda
ba zai taɓa yiwuwa ba.
Ita kuwa Gimbiya Ramlatul Siyam sai hankalinta
ya dugunzuma har kwalla ta ciko a idanunta. Ba
komai ne ya jaza ma ta hakan ba face ta dade
tana yin wani mugun mafarki, kuma a cikin
mafarkin ana nuna ma ta cewar an raba ta da
mahaifinta
Ramlatul Siyam ba ta taɓa gayawa Sarki
Nashmir labarin wannan mafarki nata ba,
280
TASKARNOVELS.COM.NG
domin a rayuwarta idan akwai abin da ta tsana
bai wuce ta ga tashin hankalin mahaifinta ba.
Lokacin da Sarki Nashmir ya ga alamun
tsananin damuwa a fuskar Gimbiya Ramlatul
Siyam sai ya cika da tsananin mamaki ya dube
ta ya ce, "Ya ke 'yata, ina dalilin wannan
damuwa taki bisa wannan al'amari da muke
gani a madubin tsafina? Shin kin manta ne cewa
duk duniya babu wani matsafi kama ta, kuma
babu wani cikin gwarzon mayaki da ya fi ni
shuhura? Na rantse da darajar tsafina da kuma
kaunar da nake yi miki, inda duk mutanen
duniya da aljanun duniya za su yi shirin yaki su
zo nan fadata ba za su iya raba ni da ke ba!"
Ya yin da Gimbiya Ramlatul Siyam ta ji wannan
batu daga bakin mahaifinta sai ta yi ajiyar à
sannan ta ce, "Ya kai Abbana ka sani cewa ba ni
da shakkar komai bisa al'amuranka. Amma ka
sani cewa, masu iya magana sun ce, "Dan Hakin
da ka raina, shi ke tsone maka idanu". Ni dai
abin da nake so da kai shi ne ka dauki matakin
gaggawa akan wadannan makiya namu da suka
281
TASKARNOVELS.COM.NG
taho. Kada ka bari su iso nan. Lallai ka tura
Dakaru su tare su tun akan hanyarsu su
ragargaza su".
Koda jin wannan batu sai Sarki Nashmir ya sake
bushewa da dariya a karo na biyu sannan ya
murtuke fuska ya ce, "Ya ke 'yata ki yi sani cewa
yau shekarata hamsin da hudu ke nan akan
karagar mulki, kuma duk shekara sai na yi yaki
da babbar kasa wacce gagarumin matsafi ke
mulka, amma ba a taɓa ci na da yaki ba. Ban
taba zuwa filin yaki da kaina ba sai sau daya,
sa'adda gaba dayan Sarakaunan duniya suka
hada KARFI DA KARFE domin su kawar da ni.
Ina zuwa filin dagar na ci su da yaki a ciikin sa'a
uku kacal.
A wannan lokaci kina yarinya karama ba ki fi
shekara hudu ba a duniya. Ki yi duba izuwa ga
Madubin tsafina domin ki ga abin da ya faru a
filin yakin a wancan lokaci".
282
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda gama fadin hakan sai Sarki Nashmir ya yi
nuni da hannunsa izuwa ga wani katon farin
Allo na zinare da ke fadar.
Nan take filin yaki ya baiyana cike da abokan
gaba kimanin Dakaru miliyan dubu daya. A gefe
daya kuma Dakarun Sarki Nashmir ne basu fi su
miliyan goma ba.
Koda Dakarun Sarki Nashmir suka ga tsananin
yawan abokan gabarsu sai suka firgice suka juya
da baya suka zaburi dawakansu domin su gudu,
amma sai abokan gabar suka taso su a gaba a
kan dawakai suna kure musu gudu suna rafke
su.
Wohoho! Nan fa aka fara cinikin daukar rai,
ihun mazaje ya cika dodon kunne, sannan jikin
bil'adama ya rinka shawagi a sararin sama, jini
kuwa ya dinga feshi da fantsama yana malala a
kas kai ka ce kogin jini ne ya ɓalle.
283
TASKARNOVELS.COM.NG
Kafin cikar sa'a guda an kashe sama da kaso
biyu cikin kaso uku na Dakarun Sarki Nashmir.
Ana tsaka da wannan masifaffen yaki ne aka ga
wata dunkulalliyar guguwa ta fado daga can
kololuwar sama. Nan take ta tarwatsa dukkan
wadannan abokan gaba. Duk wanda yake bisa
kan doki sai da ya fado kasa, wanda ke kasa
kuwa sai da ya baje.Nan take wannan
dunkulalliyar guguwa ta rikide ta zama Sarki
Nashmir, sai ga shi ya baiyana a cikin
gagarumar shigar yaki ta farin sulke sama da
kasa yana rike da wadansu tagwayen takubba
sihirtattu masu matukar kwarjini da ban tsoro.
Sarki Nashmir ya kasance gabjejen katon
mutum, ga tsawo kuma ga kauri tamkar
Basamude. Gabadayan jikinsa a murde yake
kamar curin nakiya, kuma cike yake da jijiyoyi
da kwanji.
284
TASKARNOVELS.COM.NG
Kaico! Kallo daya mutum zai yi masa ya san
cewa yana da karfin Allah Ya isa!
Koda baiyanar Sarki Nashmir sai gabadayan
wadannan Dakarun abokan gaba kimanin su
miliyan dubu daya suka yi dauki kansa shi
kadai.
Kaico! Tsautsayi ba a sa masa rana. Ita kuwa
masifa idan ta taho babu hijabin da ya isa ya
tare ta. Koda Sarki Nashmir ya ga wadannan
miliyoyin Dakaru sun rugo izuwa kansa sai shi
ma ya falfala da azababben gudu na gaban
kwatance izuwa kansu ya ratsa ta cikinsu da
karfin tsiya ya hau saransu da sukarsu. Sai dai
ka ga yana tsarga gangar jikin bil'adama tamkar
takardu yake kekketawa. Duk inda ya sa
gabansa maza faduwa suke tamkar ana sassabe
a gona. Kafin cikar sa'a uku cif gabadayan filin
yakin ya cika da gawarwakin abokan gabar
babu dayansu a raye.Kai ba ma su ba hatta
dawakansu sun zama gawarwaki domin Sarki
Nashmir ya daddatsa su kai ka ce mahauta ce.
285
TASKARNOVELS.COM.NG
Filin yakin ya yi tsit! Tamkar wani mahaluki bai
taɓa wanzuwa ba a wajen, in ban da sautin iska
da ke kadawa babu abin da kunne ke iya ji.
A dai-dai wannan lokaci ne ragowar Dakarun
Sarki Nashmir da suka tsere suka fara dawowa
filin yakin. Koda suka ga gagarumin aikin da
Sarki Nashmir ya yi sai dukkaninsu suka zube
kasa a gabansa suna masu yi masa sujjada.
Nan take Sarki Nashmir ya rikide ya zama
wannan gagarumar guguwar, Guguwar ta yi
sama ta ɓace ɓat a cikin gajimare.
Lokacin da Gimbiya Ramlatul Siyam ta gama
ganin wannan al'amari a cikin madubin tsafin
mahaifinta sai ta ji hankalinta ya kwanta
matuka, ba ta san sa'adda murmushi ya kwace
ma ta ba.
286
TASKARNOVELS.COM.NG
Ta dubi Sarki Nashmir ta ce, "Tabbas yanzu na
gamsu cewa babu wani mahaluki da zai iya
cinka da yaki. Amma dai duk da haka ina son ka
tura Dakaru su tari wadannan abokan gaba
namu tun kafin su iso domin mu ga irin
jarumtakarsu da karfin sihirinsu".
Ya yin da Sarki Nashmir ya ji wannan batu sai ya
yi murmushi ya ce, "Ya ke 'yata ki yi sani cewa,
babu wata alfarma da za ki nema awajena na ki
yi miki ita. Saboda haka lallai zan yi yadda kika
bukata.
Nan take Sarki Nashmir ya kirawo waɗansu
zakwakuran mayakansa su uku wadanda ya
yarda da jarumtakarsu, kuma shi da kansa ya
tsuma su da tsumin tsafinsa ya umarce su da su
hau kan daya daga cikin manyan hadiman
aljanunsa su je su tari su Aljani Maruful Dauwaz
tun gabannin su iso Birnin Hindu. kuma su
tabbatar da cewa sun yanko kan Aljani Maruful
Dauwaz da na abokan tafiyarsa sun zo da su".
287
TASKARNOVELS.COM.NG
Nan take mayakan uku suka yi shiri suka hau
kan wani Aljani wai shi SHARKAMUZA ya tashi
da su sama ya luluka a cikin gajimare.
Aljani SHARKAMUZA ya kasance narkeken kato
wanda girmansa ya ninka na Aljani Maruful
Dauwaz sau uku.
A bangaren kwarjini da kira ta sadaukantaka
kuwa, Aljani Maruful Dauwaz jariri ne akansa.
Su kuwa wadannan zakwakuran mayaka guda
uku da aka tura su kashe su Aljani Maruful
Dauwaz sun kasance tagwayen sadaukai, domin
uwarsu daya ubansu daya, kuma rana daya aka
haife su.
Tsawonsu da kaurinsu yazo daidai da na Sarki
Nashmir, kawai abin da ya fi su shi ne
sadaukantaka da karfin sihiri. ,
288
TASKARNOVELS.COM.NG
Ana kiran wadannan tagwayen sadaukai da
suna, SHARMAL, ZARHUF da HAZWAN.
Shi kansa Sarki Nashmir akwai wata rana da ya
umarci su Sharmal da su hada karfi su ukun su
yake shi domin ya jarraba iyakar jarumtakarsu.
Ai kuwa da ya fafata da su sai da ya sha bakar
wuya, kuma sai da suka yi masa rauni sau biyu.
Da kyar ya sami nasarar bazar da su kas ya
sumar da su
Tun daga wannan ranar ya kara musu matsayi
babba a cikin Dakarunsa babu wanda ya fi su
face Sarkin yakinsa wanda ake kira RAJWAN
BIN SAMMAR.
Sarkin yaki Rajwan ya kasance barden jarumi,
FASA TARO mai TARWATSA MAZA.
289
TASKARNOVELS.COM.NG
Ya kasance gawurtaccen Sadauki wanda
jarumtakarsa kiris ya rage ta zo dai-dai da ta
Sarki Nashmir. Domin kuwa a ranar da suka
gwada 'yar kashi sai da suka kusan yin RAGAS.
Da kyar da sidin goshi Sarki Nashmir ya sami
rinjaye akan Rajwan. In ba don ma ya nuna
masa kwarewa da sanin makama ba da ba zai yi
nasara a kan shi ba.
Gabadaya mutane Birnin Hindu babu mutumin
da suke tsoro sama da Sarkin yaki
Rajwan domin ya fi Sarki Nashmir rashin imani
da zalunci, sannan kuma shi ne wazirin Sarki
Nashmir don haka ana tsoron kada Sarki
Nashmir ya riga Rajwan mutuwa, muddin hakan
ta faru sai Rajwan ya dora kansa akan karagar
mulki da karfin tsiya, ko ana so ko ba a so ba zai
bari Gimbiya Ramlatul Siyam ta hau ba.
A bangaren karfin sihirin tsafi kuwa, Rajwan da
Sarki Nashmir sun yi kunnen doki kuma kowa
na shakkar kowa.
290
TASKARNOVELS.COM.NG
Sarkin yaki Rajwan bai taɓa yin aure ba kuma a
duniya babu macen da yake mutuwar so sama
da Gimbiya Ramlatul Siyam, amma sai ya bar
abin a cikin zuciyarsa saboda ya san cewa
Wutsiyar Rakumi ta yi nesa da kasa.
A kullum Rajwan ba shi da wani buri a cikin
zuciyarsa wanda ya fi ya ga Sarki Nashmir ya
mutu domin ya sami damar haye karagarsa,
kuma ya aure 'yarsa Gimbiya Ramlatul Siyam.
Bisa wannan dalili ne Sarkin yaki Najwar ya
kasance mai tsananin biyayya ga Sarki Nashmir
don kada ya gane abin da ke zuciyarsa kuma bai
taɓa yarda ya nunawa Gimbiya Ramlatul Siyam
alamun soyayya ba.
Haka ya danne abin a zuciyarsa ya zamana cewa
yana fama da tsananin begenta dare da rana.
291
TASKARNOVELS.COM.NG
Saboda kwarjinin Gimbiya Ramlatul Siyam da
kuma tsoron mahaifinta ba a taba samun wani
dan Sarki ko dan Boka da ya taɓa fitowa ya nuna
yana sonta da aure ba saboda a dalilin hakan ma
an kashe sama da samari dubu wadanda suka yi
gangancin nuna soyayya a gare ta.
Dangane da ita kanta Gimbiya Ramlatul Siyam
kuwa, ba ta taɓa son wani da namiji ba, kuma
babu namijin da ya taɓa koda yin hira da ita
tsawon dakiku sittin face mahaifinta.
Tsakaninta da maza sai kallo da marmari daga
nesa, amma babu wanda ya isa ya kusance ta.
Hadimanta ma gabadaya mata ne. Kai idan ta
dauro Gimbiya Ramlatul Siyam tana shekara ba
ta ga da namiji ba face a cikin fadar mahaifinta.
Wannan al'amari yana matukar daurewa
mutanen Birnin Hindu kai domin suna wasiwasi
a cikin zuciyarsu bisa tunanin cewa Gimbiya
Ramlatul Siyam ba ta da cikakkiyar lafiya.
292
TASKARNOVELS.COM.NG
Domin a matsayinta na baligar mace ya kamata
a ce ta bukaci namiji.'
Abin da ba su sani ba shi ne; Mahaifinta ya yi
amfani da karfin sihirin tsafi wajen cire mata
sha'awa, kuma an rasa wanda zai iya karya
wannan sihiri
Lokacin da su Sharmal suka ci gaba da tafiya
bisa kan Aljani Sharkamuza a sararin samaniya
sai suka kagu ainun akan su riski su Aljani
Maruful Dauwaz domin sun dade basu yi kan
mai uwa da wabi ba. Bisa wannan dalili ne
Sharmal ya dakawa aljani ysawa Sharkamuza ya
ce, "Wai shin wacce irin tafiya ce wannan kake
yi ne har yanzu mun kasa cim ma abokan gabar
ta mu?"
Koda Aljani Sharkamuza ya ji wannan batu sai
numfasa ya ce, "Ka yi mini uzuri ya shugabana.
ya Shin kun manta ne cewa ku uku ne a zaune
bisa kaina. Nauyin kowanne daya daga cikinku
293
TASKARNOVELS.COM.NG
ya kai na giwa fa. Dole ne karfin guduna ya ragu
ainun, amma ina tabbatar muku da cewa nan da
sa'a biyu kacal lallai za mu riski su Aljani
Maruful Dauwaz a kusa da wani daji da ake kira
HIRZUL ASWAD."
Koda jin wannan batu sai Sharmal ya ce, "Ni
kuwa na taɓa ganin siffar wannan Aljani
Maruful Dauwaz a cikin madubin tsafina a wani
lokaci can baya da na yi nazari akan kogon
Darul Iksina. Wai shin ya ya karfin jarumtakarsa
da karfin sihirinsa yake ne?".
Sa'adda Aljani Sharkamuza ya ji wannan
tambaya sai ya bushe da dariya ya ce, Tabbas
Maruful Dauwaz ya cika gawurtaccen jarumi
kuma ya yi suna sosai a cikin jaruman aljanu na
duniya amma fa na fi shi komai, abin da ya ya fi
ni shi ne daukaka. A halin yanzu babu wani
Aljani mai tsananin karfin gudunsa a sararin
samaniya. Sannan yana da matukar juriya da
naci a filin yaki da shanye wuya komai
tsananinta.
294
TASKARNOVELS.COM.NG
Haka kuma yana da matukar sa'a bisa duk abin
da ya sa a gabansa. Saboda haka ina yin arba da
shi zan yi kokari na yi masa kwaf daya cikin
shammata yadda zan hallaka shi da wuri, in ba
haka ba kuwa zai iya wahalar da ni matuka ko
kuma idan na yi wasa mu yi RAGAS!"
Koda jin wannan batu sai Sharmal, Zarhuf da
Hazwan suka bushe da dariya. Hazwan ya ce,
"Yaya ma za a yi mu bari har Maruful Dauwaz ya
sami nasara akanka? Ai tuni za mu gama da shi.
Rahila da Sarki Laffaru kuwa ta farat daya za mu
gama da su, babu abin da Laffaru zai iya
tsinanawa".
Gabadayansu sai suka bushe da dariyar
mugunta, sautin dariyar tasu ya cika sararin
samaniya gaba ldaya har yana amsa kuwwa.
*
295
TASKARNOVELS.COM.NG
AL'AMARIN Aljani Maruful Dauwaz kuwa
lokacin da suka iso tsakiyar dajin Hirzul Aswad
za su gifta sai Rahila ta yi gyaran murya ta ce
"Bukata ta kama ta don haka tana son a sauka
kasa domin ta kawar da bukatar"
Koda Aljani Maruful Dauwaz yaji haka sai ransa
ya baci, ya yi tsaki ya ce, "Ai ka ji irinta! Shi ya sa
bana son tafiya ta hada ni da mace, saboda ku ba
kwa iya jure bukata. Inda za ki yi hakuri nan da
rabin sa'a za mu isa daf da Birnin Hindu, in yaso
sai nа sauka a bayan gari ki biya bukatar taki".
Rahila ta ce, "In ban da abinka ai cikin dakiku
kadan na hattama. Bawali kaɗai zan yi'.
Koda jin haka sai Aljani Maruful Dauwaz ya saki
fuka-fukansa ya yi kasa. Nan da nan ya dira akan
turba cikin dajin Hirzul Aswad.
Daji ne mai matukar kwarjini da ban tsoro,
domin yana dauke da manya-manyan bishiyoyi
296
TASKARNOVELS.COM.NG
masu yawan ganyaye a samansu, sannan akwai
makeken fili wanda sama da mutum miliyan
dubu za su iya yin yaki a cikinsa. Akwai manyamanyan duwatsu da tsaunika.
Da saukar Aljani Maruful Dauwaz sai Rahila a yi
wuf ta dirga kasa sannan ta ruga izuwa bayan
Wata bishiya. Sai da ta dubi gabas da yamma,
kudu da arewa ta yi nazarin wajen sosai sannan
ta sugunna domin tayi bawalin.
A daidai wannan lokaci ne wata irin gagarumar
iska ta taso daga sararin sama ta dugunzuma
hankalin su Aljani Maruful Dauwaz, domin ji
suka yi kamar iskar za ta sure su ta yi sama da
su, har ma sai da Sarki Laffaru ya fado kasa daga
kan Aljani Maruful Dauwaz.
Cikin firgici Maruful Dauwaz da Sarki Laffaru
suka daga kawunansu sama. Itama Rahila ba
shiri ta mike tsaye zumbur! tana mai daga kanta
sama.
297
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda duk su ukun suka yi arba da abin da ke
shirin faruwa sai suka firgice suka ji kamar su
ruga da gudu. Ba komai suka gani ba face
jaruman nan uku, wato su Sharmal bisa Aljani
Sharkamuza.
Aljani Sharkamuza na dira bisa turba sai dajin
gaba daya ya yi girgiza da tambal-tambal kamar
kasa za ta koma sama saboda tsananin
nauyinsa. Sharlisa ta ruga da gudu ta dane kan
Maruful Dauwaz shi ma Sarki Laffaru ya yi sauri
ya koma kan Maruful Dawaz, du su biyun suka
zare makamansu a lokacin da jikinsu ya kama
karkarwa kai ka ce daga cikin ruwan kankara
aka tsamo su. Tabbas su Rahila sun firgita ainun
bisa ganin
yanayin surar su Sharmal da kuma mugayen
kayan yakin da suke dauke da şu.
A bangaren Aljani Marufu! Dauwaz kuwa, shi
ma ya razana matuka da ganin Aljani
298
TASKARNOVELS.COM.NG
Sharkamuza, domin ko ba a gwada ba linzami ya
Karfin bakin kaza. Tabbas ya san cewa
Sharkamuza ya fi shi karfi, girma da duk abin da
yake takama da shi, amma saboda taurin rai irin
na Maruful Dauwaz firgitar da ya yi ba ta sa
jikinsa ya kama karkarwa ba.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su Aljani
Maruful dauwaz da su Aljani Sharkamuza. Ana
cikin haka ne Maruful Dauwaz ya ce da su
Rahila, "Duk irin bala'in da za a yi kada ku yarda
ku sauka daga kaina. Kai Laffaru ka maida
takobinka ka dauki kwari da baka domin babu
abind a za ka iya yi a wannan gumurzu face
harbi. Ni kam zan yi iya kokarina na ga cewa ba
su tarfa mu ba a waje daya domin idan har suka
tarfa mu kashinmu ya bushe sai sun hallaka mu.
Koda gama fadin hakan sai Aljani Maruful
Dauwaz ya bude fuka-fukansa ya tashi sama
kadan ya tsaya cak a cikin iska sannan ya dubi
Aljani Sharkamuza ya daka masa tsawa ya ce,
"Ya kai wannan ma'abocin karfi da kwarji mene
ne dalilinka na zuwa gare mu?"
299
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin aljani Sharkamuza ya ji wannan
tambaya sai ya bushe da dariya, lokaci guda
kuma ya murtuke fuska ya ce, "Sunana
Sharkamuza ibini Zarlala na kasance daya daga
cikin manyan hadiman Serki Nashmir na Birnin
Hindu. Waďannan jaruman da ke tare da ni
kuwa Sharmal, Zarhuf da Hazwan kenan,
manyan Dakarun yaki na Sarki Nashmir.
Sarkinmu ya aiko mu ne a gare ku domin mu
ragargaza ku mu yi filla-filla da sassan jikinku
domin kun kasance manyan abokan gabarsa
masu son raba shi da 'yarsa da kuma wani sirrin
tsafinsa. Idan kuna da wasiyya ta karshe ga
iyalanku sai ku furtata yanzu kafin mu zare
muku ruhin numfashi. Lallai za mu isar da
wasiyarku. Wannan shi ne iyakar alfarmar da za
mu iya yi muku."
Kafin Aljani Sharkamuza ya gama rufe bakinsa
sai Aljani Maruful Dauwaz ya tari numfashinsa
yana mai kara daka masa tsawa a karo na biyu
ya ce, "Ya kai tsohon azzalumi ka yi sani cewa
karyarku ta sha karya ba ku isa ku ida nufinku
300
TASKARNOVELS.COM.NG
ba akanmu. Ina tabbatar maka da cewa da cewa
sai mun yi fata-fata da ku mun maishe ku gawa
sannan mun dangana da fadar Sarkin naku mun
kawar da shi kuma mu dauke 'yar tasa gami da
sihirin tsafin nasa."
Koda jin wannan batu sai Aljani Sharkamuza da
su jarumi Sharmal suka fusata ainun jikinsu ya
kama tsuma. Cikin bakin zafin anma
Sharkamuza yai sama ya kawowa Maruful
Dauwaz wawan naushi da zabgegen hannunsa.
Maruful Dauwaz yai wuf ya sunkuya hannun
Sharkamuza ya naushi iska amma sai iskar
hannun nasa ta yi fatali da Maruful Dauwaz ta
dauke shi ta makashi a jikin wani tsauni ya
sulale kasa a matukar galabaice.
A zaton Sharkamuza kasusuwan bayan Maruful
Dauwaz sun kakkarye amma bisa mamaki sai ya
ga ya mike tsaye zumbur kamar babu abin da ya
same shi sannan ya zare takobinsa yana mai
gyara tsayuwa.
301
TASKARNOVELS.COM.NG
Duk wannan abu da ke faruwa Rahila da Sarki
Laffaru na rike da gashin wuyan aljanu Maruful
Dauwaz suna reto ba su yarda sun fado kasa ba.
Koda ganin abin da ya faru sai Aljani
Sharkamuza da su jarumi Sharmal su ma suka
zare takubbansu suka sake rugawa izuwa kansa
aka ruguntsume da sabon azababben yaki ya
zamana cewa suna kai wa junansu sara da suka
cikin zafin nama, juriya da bajinta.
Shi kuwa Sarki Laffaru wanda ya fara kokarin
kai harbi da kibiya sai Sharmal ya daka wawan
tsalle sama daga kan Sharkamuza ya doki
kirjinsa da kafa daya. Kamar ya daki tamaula
haka Laffaru ya lula can baya ya gwara kai a
jikin wani dutse. Nan take kan nasa ya dare jini
tsa jini yai tsartuwa ya fado kasa sumamme ko
motsin kirki bai yi ba. Nan fa gumurzu ya dawo
tsakanin rai biyu da rai hudu.
302
TASKARNOVELS.COM.NG
Wohoho! Hakika idan mutum ya ga mutuwa
muraran a sannan ne yake iya yin abin da shi
kansa bai taɓa tsammanin zai iya ba. Nan take
Rahila da Maruful Dauwaz suka fusata ainun
sakamakon ganin abin da ya faru ga Laffaru ya
zamana cewa sun kara ZAGE DANTSE iya
karfinsu aka cigaba da bakin artabu.
Duk sa'adda takubba suka haɗu sai dai ka ga
tartsatsin wuta da hayaki na tashi.
Da yake su Sharmal sun kasance sadaukai masu
karfin Allah Ya isa, nan da nan suka fara jigita
Rahila da Maruful Dauwaz har ta kai cewa ba sa
iya mai da martani sai dai kokarin kare kai.
Koda aka sake dan jimawa a haka sai su Sharmal
suka sami nasarar buge takobin Rahila ta fadi
can gefe daya kafin ta yi wani yunkuri tuni
Sharmal, Zarhuf da Hazwan sun kai ma ta hari a
lokaci guda.
303
TASKARNOVELS.COM.NG
Sharmal ya dankara ma ta sara a gadon bayanta,
Zarhuf ya sare ta a cinyarta, shi kuma Hazwan
ya soke ta a gefen kirjinta 6angaren hagu Take
Rahila ta kwarara uban ihu a lokacin da jini yai
feshi da tsartuwa daga jikinta sannan ta subuto
daga kan Maruful Dauwaz ta baje a kas wanwar
babu alamar rai a jikinta.
Koda Maruful Dauwaz ya ga abin da ya faru da
Rahila sai ya fusata ainun irin fusatar da bai
taɓa yi ba a rayuwarsa, kawai sai ya kurma
wawan ihu ya sake afkawa su Aljani
Sharkamuza su duka hudun ya hau su da SARA
DA SUKA ba ji ba gaji.
Duk da cewa su hudun suka tarar masa sai ga
shi ya zame musu alakakai domin sun kasa koda
kwarzanar jikinsa.
Abin da ya tayar wa da Mauruful Dauwaz
hankali shi ne shi ma ya kasa yivwa koda
304
TASKARNOVELS.COM.NG
dayansu rauni. In ba don ma yana da matukar
naci da juriya ba da tuni sun hallaka shi.
Ana cikin wannan gumurzu ne Aljani
Sharkamuza ya shammaci Maruful Dauwaz ya
durma masa wawan dundu a gadon baya.
Saboda tsananin zafi da zogin da Maruful
Dauwaz ya ji bai san sa'adda ya saki takobinsa
ba ta fadi kasa kuma ya durkushe bisa
guiwoyinsa ya kama amai da gudan jini.
Har Sharmal, Zarhu da Hazwan sun daga
takubbansu na sihiri sama za su gididdiba Aljani
Maruful Dauwaz sai Sharkamuza ya yi musu
nuni da su tsaya, sai suka saurara. Sharkamuza
ya dubi su Sharmal ya ce, "Haba! ai abin kunya
ne a ce mun kashe wannan Aljanin da makami,
da karfin dantsena zan kashe shi. Gama fadin
hakan ke da wuya sai aljani Sharkamuza ya cafi
makoshin Maruful Dauwaz da hannun hagu
sannan ya shiga gabza masa naushi da
hannunsa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 18