yi shiru ta shiga tunani mai zurfi.
Babban tashin hankalinat shi ne, ba za ta iya
tafiya ta bar danta Shaddad shi kadai akan
mulki ba, domin ta bi bayan su Sarki Laffaru ta
wargatsa duk shirinsu. Nan fa ta fara tunanin
wata dabarar da za ta yi ta wargatsa shirin nasu
ba tare da ta bi bayansu ba.
Sharlis ta ce a ranta, "Yanzu dai kokarinsu shi ne
su sami damar da za su isa kogon Darul Iksina
su dauko aljani Maruful Dauwaz domin ya je ya
24
TASKARNOVELS.COM.NG
sato musu gimbiya Ramlatul Siyam 'yar Sarki
Nashmir na birnin Hindu. To ai kuwa abu ne
mawuyaci su iya tsallake wadannan masifu da
ke cikin dazuzzukan nan biyar har su isa kogon
Darul Iksina domin fiye da shekaru dubu biyu
baya ba a sami wanda ya keta ta cikin su ba face
shi kansa aljani Maruful Dauwaz aljanin da aka
tabbatar da cewa babu kamarsa a zafin nama,
karfin gudu a sama da kuma tsananin juriyar
wuya kowacce iri ce.
Abu na biyu kuma shi ne, ai koda ma sun ami
nasarar dauko aljani Maruful Dauwaz shiga
fadar Sarki Nashmir har a dauko gimbiya
Ramlatul Siyam daidai yake da tafiya neman jaki
mai kaho. Domin hatta Sarki Bokayen aljanu na
duniya almajirin Sarki Nashmir ne, a wajensa ya
yi karatun tsafi. Tsaron da ke cikin gidan
sarautar Sarki Nashmir da irin abubuwan
masifun da ke cikinsa sun ninka wanda ke cikin
wadannan mugayen dazuzzuka biyar na hanyar
kogon Darul Iksina sau arba'in. Koda Sharlis ta
zo nan a zancen zucinta sai ta bushe da dariyar
murna, ta ce, "Ai babu wata hanya da burin su
Sarki Laffaru zai cika, to amma duk da haka ba
25
TASKARNOVELS.COM.NG
zan saki jiki ba na zuba ido kawai, dole ne na yi
tunanin matakin da ya kamata na dauko, koda
tsautsayi zai sa su sami nasarar daga yanzu
zuwa lokacin da za su sami nasarar dauko aljani
Daruful Dauwaz."
Wannan shi ne abin da ya faru a birnin Kufa
bayan ɓacewar Sarki Laffaru.
*****
AL'AMARIN su boka Muzaffar kuwa, kamar
yadda boka Muzaffar ya bayar da shawara haka
aka yi, wato sai da aka kwana biyu suna jinyar
jikinsu ya zamana cewa dukkanninsu sun ji
kwarin jikinsu sannan suka yi shiri domin su
shiga daji na farko.
Bayan kowa ya gama kintsawa sai sukai cirkocirko gaba dayansu aka rasa wanda zai fara
wucewa kan gaba, har ita kanta kuwa gimbiya
Rahila saboda tsananin fargaba da tunanin
abinda ke cikin dajin.
26
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda ganin haka sai boka Muzaffar ya dubi
sadauki Haiman ya ce, Ya kai wannan jarumi
mai jarumtakar ban al'ajabi ka yi sani cewa
yanzu ne zamu shiga dajin Maridai, kai kadai ne
za ka iya tarwatsa wadannan Maridai mu kutsa
ta cikinsu mu wuce. Saboda haka kai ne za ka
wuce gaba sanann gaba dayanmu mu bi ka a
baya. Koda jin wannan batu sai sadauki Haiman
ya zare takobinsa ya wuce gaba. Da ganin haka
sai jaruma Shadira ma ta goya yaro Masnur a
baya, jarumi Imran ya goya mahaifiyarsa,
gimbiya Zarina ta goya dan uwanta sarkin
Farisa.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin sadauki
Shaharan ke nan, domin shi ba zai iya daukar
dokinsa ba.
Koda boka Muzaffar ya ga hankalin Shaharan ya
tashi ainun, sai ya yi dariya, sannan ya dubi
aljani Marhabul Zaurus ya ce, "Dauki dokin
Shaharan ka taho da shi. Cikin matukar firgici
27
TASKARNOVELS.COM.NG
aljani Marhabul Zaurus ya dubi boka Muzaffar
ya ce, haba ya shugabana ya za ka ce na karawa
kaina nauyi alhalin ka san irin bala'in da za mu
shiga a cikin wannan daji.
Cikin fishi boka Muzaffar ya dakawa Marhabul
Zaurus tsawa ya ce, "Ba wai rokonka nake ba
umarni nake ba ka. Bisa dole Marhabul Zaurus
ya dauki dokin sadauki Shaharan ya dora shi a
gadon bayansa,sannan aka ci gaba da tafiya.
Sadauki Haiman na kan gaba, jaruma Shadira na
biye da shi, sai Zarina, Imran da Shaharan. Boka
Muzaffar, Sarki Laffaru, gimbiya da Rahila ne a
karshe sai kuma aljani Marhasul Zaurus wanda
ke goye da dokin Shaharan.
Hakan dai suka ci gaba da tafiya har suka wuce
iyakar dajin da suka baro suka shiga cikin
farkon dajin gaba daya, wato dajin mugayen
Maridai. Da shigarsu cikin wannan daji sai suka
kamu da matukar fargaba. In ka dauke jaruman
guda hudu da gimbiya Rahila da boka Muzaffar
gaba daya sauran abokan tafiyar jikinsu
karkarwa yake kamar wadanda aka tsoma a
28
TASKARNOVELS.COM.NG
cikin ruwan kankara. Ba komai ne ya haddasa
hakan ba face ganin yanayin wannan daji.
Wadansu irin gabza-gabzan bishiyoyi ne a dajin
dogaye masu siffofin mutane kirar mutanen
farko. Babu abinda zai bai wa mutum mamaki
face yadda siffofin bishiyoyin suka zama haka
tunda ba sassakasu aka yi ba, a haka suka tsiro
suka girma. Da zarar mutum ya kalli bishiyoyin
sai ya ji zuciyarsa na dukan uku-uku saboda
munin siffofinsu kuma sai ya ga kamar za su
kawo masa hari a ko yaushe. Dajin ya yi tsit
tamkar wani abu mai rai bai taɓa wanzuwa ba a
cikinsa, amma da zarar su sadauki Haiman sun
taka busassun ganyayyakin wadannan bishiyoyi
sai ka ji karar ruburбushewar ganyayen ta cika
dodon kunne, kuma ta cika dajin gaba daya
harda amsa kuwwa. Ga shi babu inda mutum zai
taka inda babu ganyayen.
Abin da su Haiman basu sani ba shi ne, wannan
kara ta ganyaye ita ce alamar da mugayen
maridan suke ganewa cewa an shigo cikin
mahallinsu.
29
TASKARNOVELS.COM.NG
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai ga
wadannan zabga-zabgan Maridai suna fitowa
daga cikin wadansu ɓoyayyun ramuka a
karkashin kasa tamkar an tashi matattu a
makabartar da ta kunshi gawar da ba ta da dadi.
Koda su Haiman suka yi arba da wadannan
Maridai sai suka firgice ainun, nan take
dukkaninsu suka ji sun yi nadamar baro
kasashensu don cika burin kansu.
Shi kansa sadauki Haiman da aka ce shi ne zai
iya tarwatsa maridan sai da ya tsorata ainun ya
raina kansa, domin ya tabbatarwa kansa cewa
boka Muzaffar karya ya yi da ya ce da shi shi ne
zai iya tarwatsa su, domin ido ba mudu ba ne
amma ya san kima, kuma ko ba a gwada ba
linzami ya fi karfin bakin kaza.
Sadauki Haiman yaji kamar ya yar da takobinsa
ya juya da baya a guje, amma da ya ga cewar
tuni maridan sun yi musu kawanya babu hanyar
gudu sai ya tsaya cak!
Hakika masu iya magana sun yi gaskiya da suka
ce, "Idan mutum ya ga mutuwa ta ritsa shi, to fa
a sannan ne yake zama jaurmin dole, domin ya
30
TASKARNOVELS.COM.NG
ceci rayuwarsa ta kowane hali." Lokacin da
sauran jaruman tafiya suka ga sadauki Haiman
ya tsaya cak bai yi yunkurin komai ba sai kallon
maridan yake kawai sai suma suka gyara
tsayuwa suna wasa da makamansu.
Su kuwa sauran abokan tafiyar tun sa'adda suka
yi arba da halittun suka sume duk da cewa ana
goye da su. Shaharan, Sarki Laffaru ne kawai ba
su suma ba saboda su ma zuciyoyinsu na
sadaukai ne
A iya tsawon rayuwar wadannan Maridai a dajin
shekaru dubu biyu baya ba su taɓa ganin
mutane ko aljanu masu dakakkiyar zuciya ba
kamar su sadauki Haiman, domin duk wanda ya
yi arba da su take yake sumewa ko ya haukace,
amma su ga su daram a gabansu.
Sannu a hankali maridan da ke gabansu suka
fara marmatsowa suna wangame manyan
bakunansú masu kama da bakin rijiya da nufin
su dasawa su Haiman wawaso su cinye su.
31
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda Haiman ya ga mutuwa na durfafo shi
gadan-gadan sai ya ďaga takobinsa sama ya
kwarara uban ihu sannan ya ruga da gudu ya
durfafi maridan. Cikin hanzari sauran abokan
tafiyar suka yi koyi da shi.
Koda Haiman ya riski maridan sai ya hau su da
sara da suka cikin tsananin zafin nama ya rinka
tarwatsa su da karfin tsiya a guje yana samar
musu. hanya suna wucewa, amma takobin tasa
ba ta iya datsa jikinsu, sai dai mammake su suna
zubewa kasa, amma da zarar sun fadi sai su
mike zumbur a ci gaba da kasa tsere da su.
Jaruma Shadira, sadauki Imran, gimbiya Zarina,
gimbiya Rahila da boka Muzaffar ne suka rinka
taimakawa Haiman suna sara da dukan maridan
ta gefe da gefe, da kuma bayansu. Babban
abinda ya fi dugunzuma hankalin su Shadira shi
ne, a duk sa'adda maridan suka kawo musu
wafta ko sara da kaifafan faratan hannayensu
idan suka goce suka sami kasa sai ka ga sun
haifar da katon rami, idan kuwa bishiya suka
samu sai ka ga sun datsata gida biyu, in kuwa
dutse ne tarwatsewa yake ya farfashe. Haka
kuma zafin naman maridan ya wuce misali,
32
TASKARNOVELS.COM.NG
domin a cikin dakika biyu suna iya kawo hari
goma.
Nan fa maridan suka ruda su suka rikirkita su.
Idan ba don gimbiya Rahila na da matukar zafin
nama ba da karfin dantse da tuni maridan sun
gama hallaka dukkan abokan tafiyar da ke
bayan sadauki Haiman, domin ita ce take wata
irin gagarumar bajinta tana kare hare-harensu
ta hanyar shawagi a sama, tayi gabas, tayi
yamma, kudu da arewa tana saran maridan da
takobinta tana karkadar da su.Duk wannan
kokarin da Rahila ke yi sai ya
zamo a banza, domin ta kai cewa maridan sun
far make jaruman suna faduwa kasa suna dada
kai wawan taku da nufin mutsittsike su amma
sai ka ga Rahila na janye su daga kasan cikin
zafin nama tana kubutar da rayuwarsu. A haka
aka ci gaba da gudu ana daďa ratsawa ta cikin
maridan. Tunda sadauki Haiman yake gumura a
yaki bai taɓa tsintar kansa a cikin bala'i irin
wannan ba. Hatta bala'in da suka fuskanta a
wadanna dazuzzukan da suka wuce bai kai na
wannan ba. Lokacin da maridan suka ga an
dauki dogon lokaci suna artabu da wadannan
shu'uman mutane sai suka fara wani irin ihu
33
TASKARNOVELS.COM.NG
mai tsananin karfi wanda ka iya sa mutum ya
kurmance. Lokaci guda su Haiman suka kasa ci
gaba da gudu suka toshe kunnuwan da
hannayensu, damar da maridan suka samu ke
nan suka ritsa su a waje daya suka ci gaba da kai
musu sara da suka da faratansu.
Saboda karfin harin maridan da zafin namansu
ya zamana cewa tun jaruman na iya kare kansu
da makamansu har sun fara gajiya. Boka
Muzaffar aka fara cakawa tsinin farce a saman
kafadarsa. Farcen maridin ya faso ta bayansa,
Muzaffar ya kwarara uban ihu sakamakon
mugun zafin da yaji. Maridan na zare farcen
nasa daga cikin kafadar Muzaffar sai jini yai
tsartuwa, Muzaffar ya fadi kasa sumamme. A
sannan ne hankalin sauran jaruman ya
dugunzuma ainun domin sun zata ma boka
Muzaffar ya mutu. Shi kuwa Sarki Laffaru da ya
ga abin da ya faru ga boka Muzaffar abin
dogaronsa sai yai sauri ya kwanta a kasa ya yi
kamar ya mutu saboda sanin cewa ba zai iya
tsinana komai ba a wannan gumurzu.
34
TASKARNOVELS.COM.NG
A dai-dai wannan lokaci sadauki Imran ba
karamin kokari ya yi ba yana ta bubbuge
kawunan maridan da sandarsa kuma yana
samin damar tarwatsa su amma jaruma
Shardira ta fi shi kokari domin a duk sa'adda ta
dana kibiyoyinta ta harba sai dai ka ga kibiyoyin
na cakewa akan maridan suna faduwa kasa
amma saboda taurin ransu da nacinsu sai dai ka
ga sun sa hannu sun zare kibiyar sun mike tsaye
sun ci gaba da kai mugun hari duk da cewa jini
na zuba a jikinsu.
Ita kuwa jaruma Zarina abin da ya taimake ta
kawai shi ne, ta iya zulliya matuka. Duk ta inda
maridan suka kawo ma ta farmaki sai ka ga ta
goce ba sa samunta, amma tashin hankalinta shi
ne ta fara gajiya, don haka a ko yaushe komai
zai iya faruwa. Sadauki Shaharan ma karfin
gudunsa ne ya cece shi domin a tsakiyar
dodannin yake ta tsala gudu yana shiga
karkashinsu, wani lokacin har jikinsu yake hawa
yana gudu suna kawo masa mangari yana
gocewa. Inda matsalar take shi ne, shi ma ya
fara gajiya su kuwa maridan ko alamar gajiya ba
sa yi, kamar ma kara kuzari suke. Ana cikin haka
35
TASKARNOVELS.COM.NG
ne wani maridi mai shegen naci ya shammaci
Imran ya yi masa dundu a take Imran ya baje a
kasa da ruf da ciki a lokacin da ya ji kamar
kasusuwan bayansa sun kakkarye, don haka sai
ya kasa mikewa.
Maridin ya daga hannu zai caka faratansa a
gadon bayan Imran. Koda Shadira ta hango
abinda ke shirin faruwa sai ta daka wawan
tsalle daga inda take ta dira a inda Imran ke
kwance da nufin ta dauke shi, da yake zafin
naman Maridin ya fi nata, sai ya sami nasarar
kartar hannunta a lokacin da ta sami nasarar
janye Imran har ya juyo da fuskarsa ya ga irin
ceton da ta yi masa. Nan take hannun Shadira ya
dare jini ya yi feshi, itama ta kwala ihu kuma ta
fadi kasa a galabaice. Koda Imran ya ga yadda
Shadira ta ceci rayuwarsa kuma ya ga abinda ya
faru gare ta, sai ya fusata ainun ya daka tsalle
sama tamkar an cilla shi daga cikin baka ya
narkawa wannan maridi sanda aka. Take kan
maridin ya tarwatse ya kife a kasa matacce.
36
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda ganin haka sai Imran ya buďu baki ya
buɗe muryarsa gaba daya ya yiwa sauran
abokan tafiya bushara da su yi kokarin dukan
kan maridan domin anan lagonsu yake. Kamar
maridan sun fahimci abinda Imran ya fadawa
'yan uwansa sai suka daina sunkuyo da
kawunansu. Nan fa bala'i ya kai bala'i, masifa ta
yi masifa, turnuku ya kara tsanani. Zarina na
cikin yin zilliya a karkashin maridan sai wani
maridi ya tarfa ta ya naushe ta a kirji ta baje a
kasa tana numfashi sama- sama, kuma tana gani
dishi-dishi. Kawai sai maridin ya daga kafarsa
zai tatsileta. Cikin bakin zafin nama Shaharan ya
janyeta daga kasan amma kafin ya bar wajen
kafar maridin ta take tasa kafar, fit sai babban
dan yatsansa ya fice ya tsandara ihu, amma
saboda juriya bai yarda ya fadi ba sai ya
sungumi Zarina ya goya ta a bayansa ya ci gaba
da gudu a tsakankanin maridan. Sai da aka shafe
sa'a guda cur ana wannan bakin gumurzu ya
zamana cewa babu wanda maridin ba su yi wa
rauni biyu zuwa uku ba face Sarki Laffaru da
kuma 'yan uwan jaruman wadanda dama
tuntuni su tsoro ya sumar da su. Shi kuwa
Laffaru don ya бuya ne a kasan boka Muzaffar
wanda shi ma tunda ya suma bai farfado ba. A
37
TASKARNOVELS.COM.NG
wannan lokaci ita kanta Rahila ta gaji ainun har
ta fara sarewa ta sallama cewa lallai duk hallaka
za su yi.
Sadauki Haiman ma ya karaya, domin ta kai
cewa da kyar yake iya ci gaba da tarwatsa
maridan kuma ga shi tunda maridan suka
kewaye su a waje daya ake ta gumurzun
sakamakon ihu da maridan suke ta yi ba su fasa
ba. A wannan lokaci aljani Marhabul Zaurus ne
kadai bai gaji ba, amma shi ma ya san cewa in
dai aka kara 'yan dakiku a haka shi ma ba zai kai
labari ba Lokacin da aljani Marhabul Zaurus ya
ga mutuwa muraran na shirin afko masa sai ya
tuna cewa shi aljani ne yana da fuka-fukai da zai
iya tashi sama ya dunga dukan kan maridan,
kawai sai yai kundunbala yai sama yana mai
surar sadauki Haiman da gimbiya Rahila suka
kama shawagi akan maridan suna saran
kawunansu.
Ai kuwa sai ga shi maridan na zubewa kasa
matattu kamar ana sassabe a gona. Damar da
suka samu ke nan suka sauko kasa cikin zafin
38
TASKARNOVELS.COM.NG
nama suka kwashe, dukkan abokan tafiyar tasu
sannan suka ci gaba da ragargazar maridan.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin maridan
kenan domin su kansu ba su taɓa shiga bala'i ba
irin na wannan rana domin ba su taɓa haduwa
da shaidanun da har suka sami damar iya
hallaka koda daya daga cikinsu ba. Ya yin da
maridan suka ga mummunar 6arnar da aka yi
musu kuma ana daďa ci gaba da yi musu sai
suka fara guduwa suna shigewa cikin ramukan
da suka firfito. Kafin a jima wajen ya zama babu
irinsu face matattunsu. Koda ganin hanya ta
samu sai farin ciki ya kama su Rahila, nan take
Rahila ta umarci aljani Marhabul Zauwas da ya
yi sauri ya kai su karshen iyakar wannan daji
inda za su iya tsayawa su yi jinyar raunikansu
ba tare da fargabar kada maridan su sake kawo
musu farmakin sumame ba.
Nan take kuwa aljani Marhabul Zauwas ya cika
wannan umarni bai sauka a ko ina ba sai a
gaban wata korama da ke karshen dajin
Maridai!
39
TASKARNOVELS.COM.NG
A wannan lokaci ne Sarki Lafaru ya tsugunna a
gaban boka Muzaffar ya kara kunnensa a dai-dai
hancinsa sai ya ji yana numfashi, cikin tsananin
farin ciki Sarki Laffaru ya ruga cikin wannan
korama ya debo ruwa ya watsa wa Muzaffar nan
take Muzaffar ya farfado daga dogon suman da
ya yi yana mai ajiyar numfashi. Nan dai aka
watsawa duk wadanda suka suma ruwa suka
farfado.
Koda Zarina ta dawo haiyacinta sai ta je gun
Shaharan ta durkusa a gabansa ta dube shi cikin
tsananin mamaki ta ce, "Me ya sa ka sallama
rayuwarka domin ceton tawa?". Da jin wannan
tambaya sai Shaharan ya yi murmushi ya ce,
"Zuciyar da ta kamu da soyayyar gaskiya ba ta
shakkar mika rai da jikinta ga abin kaunarta?".
Koda jin wannan batu sai Zarina ta turbune
fuska ta ce, "Kaiconka ya kai wannan
jarumi...Ina mai shawartarka da ka yi kokari ka
goge wannan kauna daga cikin zuciyarka har sai
izuwa lokacin da bukatarmu ta biya muka sami
abin da muka je nema akogon Darul Iksina,
amma daga yanzu har izuwa wannan lokaci ba
40
TASKARNOVELS.COM.NG
za ka sami amincewar abin da kake so ba. Na yi
matukar bakin ciki da ka rasa babban dan
yatsanka na kafa guda daya, amma idan har ba
ka sami muradin zuciyarka ba ina yi maka fatan
samun madadinta. Koda gama fadin haka sai
Zarina ta mike tsaye ta koma inda take.
Shi kuwa sadauki Imran lokacin da ya dawo
cikin haiyacinsa sai suka kama kallon-kallo
tsakaninsa da Shadira. Ga shi dai ya san cewa ta
ceci rayuwarsa kuma yana son ya yi ma ta
godiya, amma sai ya kasa.
Ba tare da ɓata lokaci ba aka shiga yi wa masu
rauni magani. Mahaifiyar Imran da kanta ta
sawa Imran magani. Koda ta ga yadda ya samu
manyan raunika sai ta fashe da kuka. Al'amarin
da ya matukar dungunzuma hankalin Imran ke
nan ya rike kafadunta suka fuskanci juna
sannan ya ce, "Ya ke Ummina ina dalilin wannan
kuka naki?"
Koda jin wannan tambaya sai mahaifiyar tasa ta
yi ajiyar zuciya gami da goge hawayenta sannan
ta ce, "Ya kai ďana, ka yi sani cewa ba wani abu
ba ne ya sa ni wnanan kuka ba face ganin yadda
41
TASKARNOVELS.COM.NG
ka sami wadannan raunika saboda kawai ka
cika mini burina. Hakika wannan tsautsayi da ya
same ka ya sa na yi nadama bisa neman
maganin nan. In da na san cewa wannan
tsautsayi zai same ka da na hakura da wannan
bukata tunda dai ni na tsufa, ba lallai ba ne na
kara shekaru masu yawa a duniya".
Koda jin wannan batu sai kwalla ta ciko a
idanunsa ya rungume mahaifiyar tasa yana mai
cewa, "Ya ke Ummina ki yi sani cewa raina da
lafiyata ba a bakin komai suke ba muddin zan
sami damar faranta miki rai. A duk sa'adda na
tuno irin tsananin wahalar da kika sha a kokarin
ganin na rayu sai na ga cewa har abada babu
abin da zan yi miki na saka miki da shi. Ya za a
yi na kasa yin wannan tafiya alhalin na san cewa
ba ki da burin da ya fi ki ga kin mike da kanki
kin taka kafafunki? Sa'adda Imran ya zo nan a
zancensa sai mahaifiyarsa ta sake kankame shi a
jikinta, a lokaci guda duk su biyun suka fashe da
kuka.
42
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda ganin wannan al'amari sai gaba dayan
abokan tafiya suka kamu da tsananin
tausayinsu. Wasu suka yi kwallah, wasu kuwa
sai da suka zubar da hawaye.
A wnanan loakci Sarkin Farisa na sa wa gimbiya
Zarina magani, lokacin da shi ma ya ga raunikan
da ke jikin 'yar uwar tasa sai ya kasa ci gaba da
sa ma ta maganin ya kama zubar da hawaye. Da
ganin haka sai Zarina ta yi murmushi ta ce
"Haba ya kai dan uwana akan wane dalili
zuciyarka za ta karaya bisa abinda ya samevni?
Ka sani cewa farin cikinka farin cikina ne, haka
ma bakin cikinka nawa ne. Har abada ba zan
taɓa samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba
face na ga ka yi aure har ka haihu, sannan ne ni
fa zan fara tunanin yin auren.
Ka tuna cewa tun muna yara da muka taso tare
komai a lokaci guda muke yi, wani ba ya riga
wani, don haka har abada ina kan wannan baka
ba zan sauya ba.
Lokacin da gimbiya Zarina ta zo nan a zancenta
sa sai Sarkin Farisa ya kara kamuwa da tsananin
tausayinta ya ce, "Ya ke 'yar uwata rabin jikina
43
TASKARNOVELS.COM.NG
ki ya sani cewa idan har kina son na yi aure to fa
sai dai mu yi a rana daya Ina nufin a ranar da na
sami lafiya. Idan kuwa ba ki amince da hakan ba
to har abada ba zan yi aure ba. Koda jin haka sai
hankalin Zarina ya dugunzuma ta yi shiru tana
tunani, daga can sai ta lok daga kai ta dubi
Sarkin Farisa ta ce, "Haba ya kai dan uwana
saboda me za ka fadi haka? Sarkin Farisa ya ce,
"Saboda na fuskanci cewa ko soyayyar ma ba
kya so ki yi. Idan har za mu yi aure a rana guda
dole ne ki nemi masoyi da wuri tun yanzu kafin
lokaci ya yi domin hankalinki da shi ki tabbatar
da soyayyarsa ta gaskiya yake yi miki ko saboda
matsayinki yake yi miki ita ba. Tun a yanzu na
fuskanci cewa kin sami wannan masoyi."
Cikin matukar mamaki Zarina ta dubi dan
uwanta Sarkin Farisa ta ce, "Wa kake nufi?"
Sarkin Farisa ya ce, "Wanda ya ceci rayuwarki
dazu a can inda muka fafata da maridai, wato
sadauki Shaharan. Tabbas sadauki Shaharan ya
kamu da matukar kaunarki, kuma ta kauna ta
gaskiya, domin inda da akwai algus a cikin son
da yake yi miki da ba zai iya sallama rayuwarsa
ba da ceton taki. Koda jin wannan batu sai jikin
gimbiya Zarina ya yi sanyi, ta sunkui da kanta
kas kuma ta yi shiru tana tunani. Daga can sai ta
44
TASKARNOVELS.COM.NG
dago kai ta dubi Sarkin Farisa ta ce, "Ya kai dan
uwana ka sani cewa na yi alkawari cewa ba zan
taɓa yin soyayya ba face na ga ka sami lafiya
Tabbas har yanzu ina nan akan wannan batu ba
zan sauya ba, saboda haka zai fi kyau ka daina yi
mini batun soyayya daga yanzu har izuwa
lokacin da bukatarmu za ta biya.'
Da jin haka sai Sarkin Farisa ya ci gaba da sawa
Zarina magani akan ciwonta, yai shiru bai kara
cewa uffan ba.
A ɓangaren Lumaira da mijinta sadauki Haiman
kuwa, lokacin da ta farfado daga dogon suman
da tayi sai ta ji ta a jikin mijinta. Cikin dimauta
ta rungume shi ta kama shafa jikinsa, ai kuwa
sai taji ta tabo jini a wuri biyu.
Nan take hankalinta ya dugunzuma ta rasa abin
da ke ma ta dadi. Kawai sai ta janye jikinta daga
cikin nasa ta fashe da kuka. Cikin matukar
tausayi Haiman ya ruko hannayenta ya danka
mata garin magani ya ce, "Ya ke matata kukan
me za ki yi kuma alhalin muna daf da samun
biyan bukata? Kawai ki shafa mini wannan
magani akan raunin da navji, domin ba komai
45
TASKARNOVELS.COM.NG
ba ne face alamun masu tabbatar da cewa zamu
sami nasarar samun abinda muka fito nema".
Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa
Lumaira ta ce, "Ya kai mijina ka yi sani cewa zan
iya zama da kai babu idanu har izuwa karshen
rayuwata muddin zan rinka jin numfashinka a
kusa da ni gami da koshin lafiyarka, duk da
cewa ina matsayin makauniya. Ka yi sani cewa
ba don komai na damu na warke daga cutar
makanta ba sai dan kawai na ga irin fuskarka
kafin ajálina ya riske ni, duk da cewa ina ayyana
fuskarka a zuciyata. Da jin haka sai Haiman ya ji
ya kara kamuwa da tsananin tausayinta. Kawai
sai ya rungume ta ya kama zubar da hawaye.
Duk wannan abu da ke faruwa Shadira da
Masnur sun nutsu suna kallon Lumaira da
Haiman. Koda yaro Musnur ya ga abin da ya faru
tsakanin Lumaira da mijinta sai shi ma ya dauki
garin magani ya kama sa wa 'yar uwarsa
Shadira a jikin raunikanta, yana yi yana zubar
da hawaye. Ga shi dai akwai alamun cewa akwai
maganganu a bakinsa amma saboda ba shi da
46
TASKARNOVELS.COM.NG
bakin maganar sai yai shiru kawai. Lokacin da
Shadira ta fuskanci halin da dan uwanta ke ciki
sai ta fashe da kuka kuma ta rungume shi a
kirjinta ta kamu da tsananin tausayinsa tana
mai cewa, "Ya kai dan uwana kada ka damu da
wannan matsayi da ka gan ni a ciki, domin ina ji
a jikina cewar bukatarmu na daf da biya. Tabbas
akwai alamun cewa zamu iya shan tsananin
wuya a cikin wannan tafiya, wata kila ma
wasunmu su rasa rayuwarsu, amma ni dai
fatana shi ne ka sami lafiya, koda zan rasa
rayuwa ta. Da jin haka sai yaro Masnur ya janye
jikinsa daga cikin na Shadira suka fuskanci juna
ya fara bayani a gare ta cikin yaren bebaye,
wato amfani da hannu ya ce, "Ya ke 'yar uwata
kin sani cewa tun da iyayenmu suka mutu kika
ci gaba da kula da rayuwa ta ya zamana cewa ke
ce uwata, kuma ke ce ubana. Babu wani mutum
wanda na shaku da shi a duniya sama da ke.
Yaya kike zaton zan kasance idan babu ke?
Lallai idan kika rasa rayuwarki a cikin wnanan
tafiya ni ma tawa ba ta da amfani, domin ba zan
taɓa samun sukuni da kwanciyar hankali ba.
Duk abincin da zan sa a bakina komai dadinsa
ďaci zai yi mini. Yadda na ga rana haka zan ga
dare, domin bazan iya rintsawa ba. A takaice dai
47
TASKARNOVELS.COM.NG
komai na duniya zai dagule mini har bakin ciki
ya haddasa mini cutar ajali. Da jin wannan
bayani na hannu da Masnur ya yi mata, sai
Shadira ta yi sauri ta janye jikinta daga cikin
nasa suka fuskanci juna. Bisa mamaki sai ya ga
ta yi masa murmushi sannan tasa hannu ta
share masa hawaye ta ce, "Kwantar da
hankalinka ya kai dan uwana, albarkacin kaunar
da ke tsakanina da kai ba zan mutu ba a cikin
wannan tafiya har bukatarmu ta biya mu koma
gida lafiya. Sa'adda Masnur ya ji haka sai ya cika
da farin ciki, fuskarsa ta cika da murmushi.
Ba shakka soyayya tana cikin litattafan yaki.
*********************
Al'amarin Shaharan kuwa, lokacin da ya ga
Zarina ta ki yarda ma su yi wata magana duk da
cewar ya ceci rayuwarta, sai hankalinsa
dugunzuma ya rasa abin da ke masa dadi, domin
shi hankalinsa dai ya san cewa ya kamu da
tsananin kaunarta kuma ba zai iya sarrafa
zuciyarsa ba ga barin abin da take so, amma da
ya dubi dokinsa ya gan shi a raye sai zuciyarsa
ta yi sanyi, ya ji, dadi a ransa, saboda ko ba
48
TASKARNOVELS.COM.NG
komai dai har yanzu
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 18