Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels TASKARNOVELS.COM.NG 1 TASKARNOVELS.COM.NG MAZAN JIYA 3 MAZAN JIYA Littafi na biyu 3 Part C Na Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey MAZAN JIYA! (3) Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai! **************************************** LOKACIN da Sharlis ta gama wannan zancen zuci sai kawai ta juya ta fice daga cikin turakar Sarki Laffaru ta nufi inda bargar dawakai take. 2 TASKARNOVELS.COM.NG Da zuwa sai ta shiga cikin bargar ta kamo wani farin ingarman doki ta fito da shi. Koda bawan da ke kula da dawakai ya hango Sharlis ta fito da doki sai ya rugo da gudu ya dauko mata siddi ya daura mata. Cikin hanzari Sharlis ta daka tsalle ta haye kan dokinta tana goye da danta Shaddad, sannan ta zaburi dokin da gudu ta fice daga cikin gidan sarautar gabadaya ta nufi kofar gari kai tsaye. A wannan lokaci ne Sarki Laffaru ya fito daga cikin turakarsa ya iso babbar harabar gidan sarautar inda ya iske Dakarun yakin kasar kimanin mutum dubu dari uku da hamsin suna ta shiryeshiryen fita wannan yaki, sai fito da makamai suke. Masu daurawa dawakai siddi na daurawa, masu tanadar guzuri na yi. Haka ma masu gyaran Baka da Kibiyoyi. Koda ganin haka sai Sarki Laffaru ya daka musu tsawa ya ce, A yi sauri a kammala shiri domin ga abokan gaba can har sun iso kusa da kofar gari. Koda jin wannan batu sai gabadayan Dakarun suka cika da mamakin yadda aka yi Sarki ya san 3 TASKARNOVELS.COM.NG cewa abokan gaba sun iso kusa da kofar gari alhalin yana can cikin gidan sarauta kuma daga can nesa ake jiyo tambarin yaki na abokan gabar. Ai kuwa nan take sai ga Sarkin kofa ya rugo da gudu a firgice! Da zuwansa sai ya zube kasa gaban Sarki Laffaru ya ce, "Ya shugabana, ga abokan gaba can sun iso kofar gari kunia baou Kowa a waje face matarka Sharlis ita kadai akan doki ta fuskancesu". Koda jin wannan batu sai Sarki Laffaru ya ce, a yi maza a kawo masa doki. Nan da nan kuwa aka kawo dokin ya hau ya zabure shi da gudu ya yi waje. Ai kuwa sai gabadayan dakarun suka bi bayansa duu!! kamar tururuwa da iyalanta sun fito daga rami. A can kofar gari kuwa, lokacin da Dakarun su Sarki Nurbas suka iso kusa da kofar birnin Kufa, Sarki Nurbas na kan gaba sai ya ja linzamin dokinsa ya tsaya. Lokaci guda gaba dayan miliyoyin Dakarun nasa waɗanda adadinsu ya kai miliyan uku da tsirari sai suka tsaitsaya. 4 TASKARNOVELS.COM.NG Sarki Nurbas ya waiga baya ya dubi wadannan dakaru nasa ya ga yawansu sai ya ji wani irin dadi a ransa domin ya san a yau dai ko sama da kasa za ta hade sai ya murkushe birnin Kufa ya kama Sarki Laffaru ya yi masa kisan gilla, sannan ya kwashe duk dukiyarsa ya dora wakilinsa akan karagar mulkin. Gama aiyana hakan ke da wuya a cikin zuciyarsa sai ya waigo ya dubi kofar birnin Kufa domin ya ba da umarnin a afkawa garin a fasa kofa da karfin tsiya a shiga. Yana waigowa haka sai ya ga wata jaruma guda daya jal bisa doki sanye da farin sulke ta rufe fuskarta da hular karfe kuma ta zare takobi tana kallonsu. Al'amarin da ya matukar bai wa Sarki Nurbas mamaki kenan, kawai sai ya bushe da mahaukaciyar dariya, ya juya ya dubi Dakarunsa ya ce, "Hakika Sarki Laffaru ya haukace. In ban da wanda ya sami tabin kwakwalwa waye zai turo jaruma guda daya jal ta zo ta yaki wannan runduna tamu?" Koda gama fadin hakan sai Sarki Nurbas ya sake bushewa da dariya sannan ya dubi waɗansu 5 TASKARNOVELS.COM.NG zakwakuran mayakansa guda uku wadanda ya yarda da jarumtarsu ya ce, "Maza ku je ku kama waccan jarumar ku yi mata tsirara sannan ku ja ta a kas bayan kun daure hannayenta da igiya ku kawo ta nan gabana tana mai wulakanta. Koda jin wannan batu sai wadannan Dakaru uku suka zaburi dawakansu suka nufi bakin kofar birnin Kufa in da Shalis ke tsaye. A daidai wannan lokaci ne Sarki Laffaru da Dakarunsa suka fito daga cikin birnin. Koda Sharis ta gan su sai ta daga musu hannu tana mai yi musu nuni da kada su karaso inda take. Nan take kuwe Sarki Laffaru ya ja tunga suma gabadayan Dakarunnasa sai suka yi koyi da shi. Ya yin da Sharlis ta ga wadannan Dakaru uku na Sarki Nurbas sun durfafo ta a sukwane bisa dawakai sai ta mayar da takobinta cikin kufe sannan ta zaburi dokinta a guje domin ta tare su tun kafin su zo su riske ta. Lokacin da ya rage sauira bai fi taku biyar ba su hadu ita da Dakarun uku sai ta daka tsalle daga kan dokinta ta yi sama kamar tsuntsuwa tasa kafarta ta gabza musu naushi a fuskokinsu duk su ukun suka tuntsuro daga kan dawakansu suka zube a kas. Ita kuwa akan dokinta ta duro ta zauna dirshsan. Koda ganin wannan bajinta da Sharlis ta yi sai 6 TASKARNOVELS.COM.NG gaba dayan Dakarun Sarki Laffaru suka hau rafka tafi. Cikin tsananin fishi Dakarun uku suka mike tsaye zumbur suka zare takubbansu suka ruga kanta cikin kunan rai da mugun nufi, domin su huce kunyar da ta ba su. Da isowarsu sai daya daga cikinsu ya sokawa dokinta takobi a ciki, take dokin ya durkushe kasa zai kayar da ita amma sai ta yi sama ta ci gaba da gabzar Dakarun da kafarta su kuwa suka yi ta kai mata sara tana gocewa suna samun iska. Nan fa duk jama'ar da ke filin yakin suka cika da matukar al'ajabin irin wannan jarumtaka ta Sharlis domin sai da ta shafe kusan dakika dari uku da sittin a sama kafarta ba ta taɓa kasa ba tana yi wa wadannan Dakaru uku luguden duka da kafafunta har katantanwa take yi a saman ta juya gabas da yamma, kudu da arewa cikin tsafin nama. Har tsawon wannan lokaci dayansu bai sami nasarar taɓa jikinta ba da takobinsa kuma duk ta farfasa musu baki da hanci jini na zuba. 7 TASKARNOVELS.COM.NG Ya yin da duka ya kai duka duk sai ta galabaitar da su suka zube kasa magashiyan. A sannan ne ta diro a gabansu ta yi nuni da hannunta na hagu a gare su sai ga rigunansu da wandunansu a hannunta ya zamana cewa kowannensu babu komai a jikinsa face dan kamfai. Nan fa Dakarun uku suka kamu da tsananin kunya suka manne da junansu suna бoye fuskokinsu. Al'amarin da ya sa Sarki Laffaru da Dakarunsa suka bushe da dariya ke nan. Nan take Sharlis ta jefa wata igiya izuwa kan Dakarun su ukun ta sarkalo wuyansu a tare sannan tayi tsalle ta sake hawa dokinta tana rike da wannan igiya ta ja Dakarun uku a kas ta durfafi inda abokan gaba suke. A wannan lokaci ne zuciyar Sarki Nurbas ta kama tafarfasa kamar za ta kone saboda fusata bisa ganin yadda Sharlis ta wulakanta Dakarunsa da yake ji da su. Lokacin da ya rage saura bai fi taku uku ba Sharlis ta hadu da su Sarki Nurbas sai ta ja linzamin dokinta ya yi turjiya, har kura ta tashi sannan ta dubi Sarki Nurbas a fusace ta ce, "Ya kai wannan Sarki ka yi kuskure har da ka ke tsamanin za ka iya wulakanta ni, domin ni murucin kan dutse ce 8 TASKARNOVELS.COM.NG ban fito ba sai da na shirya, kuma ni ce mace mai kamar maza, daya tamkar da dubu. Ni ce tarwatsa maza (Ni Maiboko har na tuna da littafinTARWATSA MAZA labarin DODO GURMAZU), kuma guguwar annoba. Ina mai ba ka shawara da ka janye Dakarunka ka hakura da wannan yaki domin babu nasara a gare ka. Idan kuwa ka ki, ina tabbatar maka da cewa ni kadai zan iya da ku domin duk yawan nan naku taron yayo ne baku isa ku yi mini komai ba. Wanne ka zaɓa?" Kafin Sharlis ta gama rufe bakinta sai Sarki Nurbas ya tofa mata yawu ya sami goshin hular karfenta ya ce, "Kaiconki ya ke wannan takadiriyar mace. Kina zaton ban san ko ke wace ce ba? Ke ce Sharlis 'yar boka Narwas wacce ke shirin daukar fansa akan Sarki Laffaru bayan yaron da ke bayanki ya girma ya zama gawurtaccen sadaukin da babu kamarsa. Ina tabbatar miki da cewa kin yi babban sakaki a yanzu domin abu ne mawuyaci ki cika burinka saboda tuni Sarki Laffaru ya bi tafarkin da zai iya tsira daga tarkonki. 9 TASKARNOVELS.COM.NG Ina mai sanar da ke cewa wancan Sarki Laffaru da ke tsaye a kofar birnin Kuffa ba Sarki Laffaru na gaskiya ba ne, wani takadarin aljani ne mai suna SHALBASHA BIN RAUHUB. A yanzu haka Laffaru na gaskiya ya tunkari kogon Darul Iksina tare da boka Muzaffar bokan da ya zo ya gaya masa hanyar da zai bi ya kuбutar da shi daga sharrinki. Ba don komai suke son zuwa kogon Darul Iksina ba sai domin su riski wani aljani wai shi Maruful Dauwaz wanda suke son ya amince yaje ya sato musu gimbiya Ramlatul Siyam 'yar Sarki Nashmir na birnin Hindu budurwar da babu mai kyanta a duk fadin duniya face gimbiya Rahila 'yar Sarki Huzaika na birnin Sabbar. Ki sani cewa idan har aljani Maruful Dauwaz ya sami nasarar sato gimbiya Ramlatul Siyam Sarki Laffaru ya aure ta za su haifi wata kyakkyawar 'ya wacce za ta zamo basadaukiya mai karfin dantse irin na Shaddad, kuma ita ce za ta kare Laffaru daga sharrin dan uwanta Shaddad. Shawara da zan baki ita ce, ki fita daga cikin 10 TASKARNOVELS.COM.NG wannan yaki ki ba ni dama na ragargaza Dakarun Sarki Laffaru sannan na kashe aljani SHALBASHA IBNI RAHUBA sannan na dora wakilina akan karagar Laffaru koda ya dawo daga kogin Darul Ikisina bai isa ya shiga birninsa ba in yaso a sannan sai mu hada karfi ni da ke mu hallaka shi. Idan kin amince da hakan zan bar miki duk dukiyar Sarki Laffaru bana bukatar koda tsinke daya daga cikinta! Sa'adda Sarki Nurbas ya zo nan a zancensa sai Sharlis ta yi shiru tana tunani tsawon dakiku sittin saboda maganganun nasa sun ratsa ta ainun kuma taji a jikinta cewa duk abinda ya fada gaskiya ne domin biri ya yi kama da mutum. Amma da ta yi wani tunanin daban sai ta ga cewa idan ta yi amfani da wannan shawara ta Sarki Nurbas ba za ta dauki fansa ba akan Laffaru kamar yadda take so. Koda gama wannan tunani sai Sharlis ta dubi Sarki Nurbas a fusace ta ce, "Na ji duk abinda ka faɗa kuma na gamsu gaskiya ne, amma ba zan iya amfani da shawararka ba. Da jin haka sai 11 TASKARNOVELS.COM.NG Sarki Nurbas ya zare takobinsa ya ce, Ai kuwa sai dai mu yi yaki domin ni duk abinda na sa a gabana sai na yi shi ba na ja da baya saboda haka ka'idar sihirin tsafina yake! Tun kafin na baro gida na yi bincike na tabbatar da cewa ni ne da nasara a wannan yaki, don haka ba gudu ba ja da baya!" Lokacin da Sharlis ta ji haka sai ta zaburi dokinta ta je can karshen kusurwar arewa ta sa tsinin takobinta ta karto layi tun daga farkon kusurwar har izuwa karshen kudu, sannan ta dawo tsakiyar fili ta dubi Sarki Nurbas ta ce, "Idan ka ga dayanku ya hauro layin nan da na karta sai idan ba na numfashi". Cikin tsananin fishi Sarki Nurbas ya ce, Ai kuwa yanzun nan za ki daina numfashin! Kawai sai ya zaburi dokinsa da nufin ya ketara wannan layi da Sharlis ta shata. Koda dokin yaje daf da layin sai ya yi tirjiya ya dinga daga kafafuwansa sama yana haniniya domin ji ya yi kamar ana tsikarinsa da karfen da aka gasa a 12 TASKARNOVELS.COM.NG cikin wuta" Sarki Nurbas ya yi ta kokarin tilasta dokin ya haure layin amma dokin sai ya ki ya juya da baya. Cikin fishi Sarki Nurbas ya sauka daga kan ya gabza wa dokin dokin naushi a wuya. Ta ke dokin ya fadi kasa. Sarki Nurbas ya dubi Dakarunsa gaba dayansu ya daka musu tsawa ya ce, Me kuke jira ne da ita ku afka mata mana! Gaba dayan miliyoyin Dakarun sai suka zaburi dawakansu da nufin su haura wannan layi. Ai kuwa sai dawakansu suka rinka turjiya kamar yadda dokin Sarki Nurbas ya yi. Saboda turmutsutsu sai dawakan suka rinka karo da junansu suna zubar da mahayansu kasa suna tattake su. Nan take wasu daga cikin Dakarun suka rinka mutuwa. Koda ganin wannan al'amari sai Sarki Nurbas ya sake fusata ainun kawai sai ya yi nuni da hannunsa na hagu ga Sharllis. Nan take wata iska mai karfin tsiya ta zuko Sharlis ta direta a gabansa suka kaure da azababben yaki shi da ita.Nan fa Dakarun nasa 13 TASKARNOVELS.COM.NG ma suka yi caa! a kanta suka yanyame ta suna masu kai ma ta sara da suka. Koda Sharlis ta yi wata irin katantanwa da takobinta sai ta tarwatsa su sai dai ka ga mutane a sama kamar janyesu ake da kugiya. Wohoho! Hakika gwani ya ji daɗinsa, domin idan ka iya ka huta da takaici. Inda Sharlis ba ta kasance jarumar kwarai ba da tuni wadannan Dakaru sun yagalgalacta sun yi filla-filla da sassan jikinta, amma sai ga shi ta zame musu alakakai, sannan kuma ta rinka girbar kawunansu. Nan fa sama ta cika da kasuwar kawuna, jini ya rinka tsartuwa da feshi yana tsiri izuwa sama yana zubowa kasa. Babu abinda zai bai wa mutum mamaki face yadda Sharlis ke yaki biyu a lokaci guda, wato tana fama da harin Sarki Nurbas wanda shi kadai ne ma yake iya kai mata munana harin kuma tana fama da harin Dakarunsa. Su Sarki Laffaru da ke tsaye a can baya suna kallon wannan bakin gurmurzun yaki da ake fafatawa sai suka cika da matukar al'ajabi suna mamakin yadda akayi Sharlis ta sami irin 14 TASKARNOVELS.COM.NG wannan gagarumar jarumtaka. Nan take aljani Sharbasha ibini Rauhuba ya ji zuciyarsa ta buga da karfi ya ce a ransa, Tabbas jaruma Sharlis ba karamar shaidaniya bace, lallai tana da karfin sihirin tsafi da kuma karfin dantse, idan na yi wasa ma za ta iya gano sirrina." Haka dai su aljani Shalbasha suka ci gaba dazuba ido suna kallon ikon Allah. Lokacin da Sarki Nurbas ya ga irin mummunar ɓarnar da Sharlis ke yi musu, sai zuciyarsa ta kara harzuka fiye da ko yaushe kawai sai ya dakawa Dakarunsa tsawa ya umarce su da su ja da baya gabadayansu, su bar shi da Sharlis shi kadai. Ba tare da ɓata lokaci ba kuwa Dakarun suka ja da baya, kuma suka yi wa Sharlis da Sarki Nurbas kawanya suka zuba ido su ga abinda zai faru. Sharlis da Nurbas suka fara zagaya juna kowannensu na tunanin hanyar da zai shigi kowa. Daga can sai suka kaure da sabon azababben yaki, suka rinka kai wa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta. Sai da 15 TASKARNOVELS.COM.NG suka shafe sa'a guda suna gumurzu amma dayansu bai sami nasarar koda taɓa jikin daya ba. Al'amarin da ya sa Sharlis ta cika da tsananin mamaki kenan domin tun daga lokacin da ta koyi yaki kawo i yanzu ba ta taɓa haduwa da jarumin da ta kasa kai shi kas ba a cikin dakiku dari da ashirin ba, amma yanzu ga shi Sarki Nurbas ya gagare ta a tsawon sa'a guda. Lokacin da suka gaji sai suka ja da baya suka yi cirkocirko suna haki. Nan fa suka kurawa juna idanu kawai suna nazarin irin salon fadan da ya kamata su sauya. Jim kadan suka sake kaurewa da sabon fada, amma wannan karon sai kowannensu ya sauya sabon salon fada, suka rinka tsalle-tsalle suna alkafira sama kuma suna katantanwa a kasa suna dada kai wa juna mugun hare-hare. A haka ne kowannensu ya sami nasarar yankar kowa. A kafada Sharlis ta yanki Nurbas, shi kuma a damtsen hannunta na dama amma nasa raunin yafi nata zurfi da tsawo, ita nata raunin ma dan karami ne. 16 TASKARNOVELS.COM.NG Koda Sharlis ta ji zogi a hannunta ta shafa hannun ta ga jini sai ranta ya ɓaci ta afkawa Sarki Nurbas da dukkan karfinta ya zamana cewa ta hada abu uku a lokaci guda, yana kai masa sara da takobi, tana kai masa naushi da bugu da hannu da kafa, kuma tana yin tsalletsalle a samansa. Nan da nan kuwa ta ruda shi don haka sai ya fara amfani da karfin sihirinsa, amma sai sihirin ya ki ya yi tasirin komai domin bai iya kare hare-hare na ta ba kuma bai iya cutar da ita ba. Ana cikin haka ne duk su biyun ska daka tsalle sama na ban al'ajabi domin gani aka yi sun luluka a can kololuwar sama kamar an zurou igiya an janye su. A can saman ne suka kai wa juna mugayen sara. Nurbas ya kai ma ta sara a ciki, sai ta goce ta mikar da jikinta baya, takobintasa ta sari iska. Kafin ya sake kawo ma ta wani saran ta dunkule ta zama 'yar mitsitsiya ta fice fit ta tsakankanin kafafunsa. Nurbas ya waiga da sauri domin ya kai ma ta wani mugun harin, amma sai ya ji kaifinu takobinta ya tsarge wuyansa gida biyu. Caraf sai Sharlis ta ruko gashin kansa, nan take kan ya rabu da wuyan sai ga jini na 6ul6ulowa 17 TASKARNOVELS.COM.NG daga gangar jikin nasa ta subuto kasa ta fado a tsakiyar Dakarunsa a lokacin da Sharlis ke saukowa kasa a hankali tamkar tsuntsuwa mai fuka-fuki. Koda Dakarun Sarki Nurbas suka ga gangar jikin Sharlis ta fado babu kai sai suka firgice suka kama guje-guje suna barin filin yakin. Sharlis ta dira bisa turba rike da kan Sarki Nurbas. Ko da su aljani Shalbasha ibini Rauhub suka ga abin da ya faru sai suka cika da tsananin mamaki. Aljani Shalbasha bai san sa'adda jikinsa ya kama kyarma ba musamman da ya ga jaruma Sharlis ta nufo kansa gadan-gadan. Abin da ya fado a ransa shi ne, shi ma kashe shi za ta yi, domin babu mamaki ta gano cewa, shi ba Lafarun gaskiya ba ne. Koda Sharlis ta iso gaban aljani Shalbasha ta ga jikinsa na kyarma sai ta yi murmushi sannan ta ce da shi, "Ka tafi da wannan kan izuwa birnin Zaruf ka shiga har cikin fadarsa ka hau kan karagar mulkinsa ka zauna. Ina son ka yi 18 TASKARNOVELS.COM.NG zamanka a cikin garin ka zamo halifana ka ci gaba da mulkin birnin Zaruf tunda na ci su da yaki. Koda jin wannan batu sai aljani Shalbasha ya zaro idanu cikin alamun tsananin damuwa ya ce, "Haba yake matata! Yaya ni da nake mulkin babbar birni kamar wannan na Kufa za ki ce na koma birmin Zaruf na mulke su, ai na ci baya". Sa'adda Sharlis ta ji haka sai ta sake yin murmushi a karo na biyu sannan ta matso daf da aljani Shalbasha ta yi masa rada a kunne ta ce, tunda ba ka son maigidanka Lafaru ya wulakanta, idan za ka shiga cikin birnin Zaruf dauke da kan Sarkinsu sai ka juye izuwa wani kamannin daban kamar yadda yanzu ka juye izuwa na mijina. Ya kai Shalbasha ka sani cewa umarni na ba ka a yanzu, idan kuma ka zo mini da tangarda yanzun nan takobina za ta sha jininka kamar yadda ta sha na Sarki Nurbas! Koda jin haka sai jikin aljani Shalbasha ya ci gaba da karkarwa fiye da farko, amma don kada jama'a su gane abinda ke faruwa sai shi ma ya yiwa Sharlis rada a kunne ya ce, "Tuba na ke ya shugabata na yarda zan bi umarninki, kuma ina rofonki da ki 19 TASKARNOVELS.COM.NG yi mini rai kada ki kashe ni. Ki sani cewa ni bawa ne kawai mai bin umarni, ba ni da laifin komai". Sharlis ta yi murmushi sannan ta ce, "Bana cutar da wanda bai cutar da ni ba, in da dai ban gano ko kai waye ba har aka cutar da ni da tabbas sai na cutar da kai. Yanzu ka debi Dakarun nan birnin guda dubu dari ka tafi da su izuwa can birnin Zaruf, amma kafin sannan ina son ka juye izuwa kamannin wazirin Sarki Laffaru domin a halin yanzu wazirin na kwance agidansa yana jinyar rashin lafiya. Lallai idan mutanen birnin Zaruf suka ganka a cikin siffar wazirin Laffan kuma rike da kan Sarkinsu tare da Dakarun Sarki Laffaru dubu dari babu wanda zai yi ma ka tawaye, dole ne su yi biyayya a gare ka ka mulke su. Duk ranar da Sarki Laffaru ya dawo gida zan sa ya aika maka ka dawo a tura wani ya karɓi matsayinka. Daga wannan lokaci sai ka san inda dare ya yı maka, idan kuwa na sake ganinka koda a kusa da birnin nan ne sai dai tsohuwarka ta haifi 20 TASKARNOVELS.COM.NG wani. Gama fadin hakan ke da wuya sai jaruma Sharlis ta tafi izuwa cikin birnin Kufa kai tsaye, ta bar Dakarun yaki a tsaitsaye suka bi ta da kallo kawai cikin tsananin mamakin yadda akavyi ita kadai ta tarwatsa dukkan abokan gaba har kuma ta sami nasarar kashe Sarki Nurbas Daga wannan rana Sharlis ta rinka dora ɗanta yarima Shaddad akan karagar mulkin ubansa tana koya masa yadda ake tafiyar da mulki yana wakiltar mahaifinsa. Al'amarin da ya jefa fadawan Sarki Laffaru cikin tsananin damuwa da bakin ciki ke nan, akan an bai wa kankanin yaro dan shekara uku shugabancinsu. Suna ji suna gani suka hakura dole da Shugabancin nasa, aka rasa wanda zai ce an yi ba dai-dai ba saboda tsananin tsoron kada fushin Sharlis ya tabbata a kansu. Su kuwa sauran mutanen gari na Kufa kuwa, sai wannan sabon mulki na ďan Sarki Laffaru ya zame musu abin alheri, domin gabadaya zaluncin da ake yi a kasar an daina. An daina kwacewa talakawa dukiya, yi wa mata fyade da zalunci na ba gaira 21 TASKARNOVELS.COM.NG ba dalili. Al'amarin da ya matukar kawo kwanciyar hankali da daukakar kasuwanci da arziki domin kowa ya saki jiki yana fito da hajarsa kasuwa ya kasa ta komai yawanta. Nan da nan fatake suka rinka yi wa birnin Kufa shigar burtu ya zamana cewa kasuwar garin na ci har sau uku a sati maimakon sau daya jal da take ciki. Nan fa birnin Kufa ya bunkasa ainun a karfin kasuwanci da arziki, mutane suka rinka yin hijira daga sauran kasashe makwabtaka suna dawowa birnin Kufa har garin ya cika ya batse, yawan al'umma ya wuce misali saboda haka sai Sarki Shaddad ya kafa doką aka hana baki shigowa su zauna sai dai su yi cinikinsu su fita. Babu abinda yake bai wa jama'ar birnin Kufa mamaki face yadda wannan sabon Sarki nasu dan shekara uku jal! a duniya ke da basira da hangen nesa. Idan kuwa yana yi wa mutane jawabi sai ka rantse dan shekara dari ne yake zance. Nan da nan labari ya cika duniya cewar Sarki Laffaru ya ɓata ba a san inda yake ba, amma dansa Shaddad yaro dan shekara uku ya gaje shi har ma ya bambanta da ubansa domin 22 TASKARNOVELS.COM.NG shi adali ne saɓanin mahaifinsa da ya kasance azzalumi. Bisa wannan dalili ne mutane suka rinka zuwa daga kasa-kasa, manyan Sarakai, attajirai da manyan bokaye domin kawai su ga Sarki Shaddad da idanunsu su tabbatar da abin al'ajabin da ake ta fada. Babu abinda zai burge mutum face yadda ko yaushe Sarki Shaddad yake zama a fada tare da mahaifiyarsa Sharlis a kodayaushe tana damansa. Ga ta kyakkyawar gaske, kuma ga dan nata shi ma kyakkyawan gaske, duk sun yi shiga iri daya abin gwanin ban sha'awa. Duk abinda Sarki Shaddad zai yi sai ya nemi shawarar mahaifiyarsa Sharlis, sai abinda ta ba shi umarni shi yake zartarwa, kawai dai sunan shi ne Sarki, amma Sharlis ce ke tafiyar da komai na mulki. Sai da Sarki Shaddad ya sami kwana goma sha hudu akan karagar mulki sannan Sharlis ta sami 23 TASKARNOVELS.COM.NG nutsuwa ta shiga halwar tsafi domin ta binciko halin da Sarki Laffaru ke ciki. Ai kuwa nan take ta ga duk abinda ya faru tun daga lokacin da boka Muzaffar ya zo ya dauke Sarki Laffaru kawo izuwa sa'adda suka je suka dauko gimbiya Rahila sannan suka je suka dauko sauran abokan tafiya har suka iso wannan mugun daji inda suka fafata kazamin yaki da wadannan mugayen aljanu. Koda gama ganin wannan al'amari sai Sharlis ta kurma ihu cikin tsananin bakin ciki, hankalinta ya dugunzuma fiye da ko yaushe a rayuwarta, ta tabbatar da cewa an shammace ta Sharlis ta

Chapter 1 of 18