Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na dama a fuska. Karar naushin ta cika dajin gaba daya tamkar ana dukan dutse da katuwar guduma. Nan da nan cikin kankanin 305 TASKARNOVELS.COM.NG lokaci ya kumbura fuskara Maruful Dauwaz ko ina ya duri jini, tun Maruful Dauwaz na iya ihu har sai da muryarsa ta dashe, jikinsa gaba daya ya saki kamar an jika tsumma a ruwa ya zamana ccwa ko motsa dan yatsan hannunsa ba ya iya yi a lokacin da jini ke ta kwarara daga fuskar tasa. Sai da Aljani Sharkamuza ya ga ko kadan babu alamar numfashi a tare da Maruful Dauwaz sannan ya daina naushinsa, sannan ya bushe da mahaukaciyar dariyar mugunta, kuma ya shiga yi wa kansa kirari yana koda kansa. A daidai wannan lokaci ne Sarki Laffaru ya farfado daga dogon suman da ya yi, kawai sai ya ji kansa ya yi masa nauyi ainun har ma ya fi sauran gangan jikin nasa don haka sai ya kasa mikewa. Koda ya bude idanunsa a hankali sai ya hango Aljani Maruful Dauwaz a hannun Aljani Sharkamuza ya shake wuyansa, kafafun Mauful Dauwaz na reto babu alamar rai a tare da shi. Nan take hawaye ya zubowa Sarki Laffaru 306 TASKARNOVELS.COM.NG domin ya sa cewa yau dai karshen rayuwarsa ce ta zo. Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai Aljani Sharkamuza ya ji Maruful Dauwaz ya gabza masa wawan naushi a ido. Saboda karfin naushin sai da hannun Maruful Dauwaz ya shige cikin kwarmin idonsa ya fito ta keyarsa. Maruful Dauwaz na zare hannunsa daga cikin kokon kan sai Sharkamuza ya yanke jiki ya fadi kasa matacce. Koda Shamral, Zarhuf da Hazwan suka ga wannan gagarumar jarumtaka da Maruful Dauwaz ya yi alhalin a zaton su ma ya mutu ba shi da rai sai suka firgaita ainun, jikinsu ya kama karkarwa suka kasa sake afkawa Maruful Dauwaz. Maruful Dauwaz ya dube su a fusace sannan ya takarkare ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa. Ai kuwa sai su Shamral suka dada 307 TASKARNOVELS.COM.NG dimaucewa suka falfala da gudu izuwa cikin dajin Hizurul Aswad ba tare da sanin inda suka dosa ba. Maruful Dauwaz ya ruga inda Gimbiya Rahila ke kwance ya rungume ta a jikinsa ya fashe da kukan bakin ciki. Ba zato ba tsammani sai ya ji ta kawo gwauron numfashi. Nan take Maruful Dauwaz ya cika da tsananin farin ciki da ya ga ba ta mutu ba dama tuni ya ga Sarki Laffaru yana numfashi ya san cewa yana raye. Cikin gaggawa Maruful Dauwaz ya shiga dinke raunika ukun da ke jikin Rahila. Bayan ya gama dinke mata raunikan sai ya shafa mata magani jini ya daina zuba sannan ya sa mata battar ruwa a bakinta ta sha. Daga nan sai ya koma kan Sarki Laffaru shi ma ya dinke masa wannan rauni da ke kansa ya sa masa magani. Lokacin da Rahila ta farfaɗo sosai ta dawo cikin haiyacinta ta ga yadda fuskar Maruful Dauwaz 308 TASKARNOVELS.COM.NG ta kumbura kuma ta yi kaca-kaca da jini har ya zamana cewa ba a shaida kamanninsa sai ta fashe da kuka kuma ta dube shi cikin matukar alamun tausayawa ta ce, "Ya kai jarumin jarumai, ka gafarce ni, hakika ni ce na janyo maka wannan masifa kuma yanzu ne na gane irin wahalar da ka hango mana za mu shiga bayan ka yi halwar nan ta kwana uku". Koda jin wannan batu sai Aljani Maruful Dauwaz ya budi baki da kyar a lokacin da yake numfashi sama-sama kamar ba zai rayu ba ya ce, "Ya ke wannan 'yar Sarki ki yi sani cewa wannan wahalar da muka sha yanzu ba komai bace fac somin taɓi daga cikin irin wahalar da za mu sha nan gaba. Bai kamata ki ba ni hakuri ba ko ki nemi gafarata ba tunda ban fito wannan gwagwarmaya don ke ba sai domin na cika burin masoyiyata marigayiya Rashmin. Abin da nake so da ke kawai shi ne idan har mun sami nasara bisa abin da muka fito nema ki kasance mai cika alkawari a gare ni". Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa Gimbiya Rahila ta yi shiru ba ta ce komai ba. 309 TASKARNOVELS.COM.NG A wannan lokaci ne Sarki Laffaru ya mike da kyar daga inda yake kwance ya dawo wajen su Maruful Dauwaz ya zauna sannan ya dubi Maruful Dauwaz cikin alamun karayar zuciya ya ce, "Zai fi kyau mu hakura da wannan bukata da ke gabanmu domin babu yadda za a yi mu kai ga samun nasara. Ku duba fa ku gani, wadannan Dakarun Sarki Nashmir ne su hudu kacal suka jefa mu a cikin wannan hali, idan kuma muka isa fadarsa ya za mu yi da miliyoyin Dakarun nasa?" Kafin Sarki Laffaru ya gama rufe bakinsa tuni Maruful Dauwaz ya tari numfashinsa yana mai cewa, "A kul! Ka kara yi mana irin wannan furuci. A iya rayuwata duk abin da na sa a gabana sai na yi nasara. Duk wuya duk rintsi ba na gudu kuma ba na ja da baya. Babu abin da zai sa mu janye akan 310 TASKARNOVELS.COM.NG wannan al'amari face ba na numfashi a doron kasa. Lallai yanzu za mu zauna anan mu yi jinyar raunikan jikinmu har izuwa tswon kwana goma sha hudu sannan mu ci gaba da tafiya, saboda kasusuwan fuskata guda bakwai ne suka karye. Hakika a iya rayuwata ban taɓa yin karo da sadauki mai tsananin karfin naushi ba kamar Aljani Sharkamuza. Tabbas na jinjina masa domin ya cika gwarzo, ba zan taɓa mantawa da shi ba. Koda jin haka sai Rahila ta yi ajiyar numfashi ta çe, ai komai gwarzontakarsa da karfin naushinsa bai kai naka ba, tunda kai ka iya shanye naushinsa da yawa amma da ka yi masa naka guda daya sai ga shi ka burma masa kai ya zama gawa". 311 TASKARNOVELS.COM.NG Cikin mamaki Maruful Dauwz ya dubi Rahila ya ce, "Yaya aka yi kika san da faruwar hakan alhalin sa'adda abin ya faru kina kwance a sume?" Rahila ta yi murmushi cikin karfin hali ta ce, "ban gan sa'ad da abin ya faru ba amma lokacin da na farfado na ga gawar Sharkamuza kuma na ga kansa a 6ule alamar shatar hannu ce ta bula shi, shi ne na aiyana faruwar al'amarin a cikin zuciyata". Koda jin haka wannan batu sai Maruful Dauwaz ya kwanta a kas ya baje sosai don ya huta yana mai cewa, "tabbas kina da hikima da basira Idan kun huta ke da Laffaru za ku taru ku gyare karayar kasusuwan fuskata. Wannan shi ne abin da ya faru ga su Aljani Maruful Dauwaz bayan sun yi MUGUN GAMO da su Aljani Sharkamuza sun fafata kazamin yaki. 312 TASKARNOVELS.COM.NG ***** A can Birnin Hindu kuwa cikin fadar Sarki Nashmir, duk abin da ya faru tsakanin su jaruma Rahila da su Aljani Sharkamuza a dajin Hizurul Aswad Sarki Nashmir da dukkan fadawansa sun gani a cikin madubin tsafinsa. Koda gama ganin wannan al'amari sai Sarki Nashmir ya kamu da tsananin bakin ciki. Cikin tsananin fishi ya mike tsaye ya kwarara uban ihu wanda ya zamo sanadiyyar girgizar fadar gaba daya, duk mutanen da ke cikin fadar suka dimauce sannan kuma sai ya naushi katon madubin tsafin nasa wanda ke manne a jikin bango. Nan take mdubin ya rugurguje ya tarwatse yai gutsun-gutsun. Sarki Nashmir ya sake dakawa fadawansa tsawa ya ce, "Kowa ya bar su su biyu rak daga shi sai Sarkin yakinsa sadauki Najwar. 313 TASKARNOVELS.COM.NG Nan da nan kuwa kowa ya fice ya bar su fadar tayi tsit tamkar babu wani mahaluki mai numfashi a cikinta. Tsawon 'yan dakiku Sarki Nashmir da Najwar na kallon juna dayansu bai ce uffan ba. Daga can sai Sarki Nashmir ya kyalkyale da dariya, lokaci guda kuma ya murtuke fuska ya dubi Najwar ya ce. "Ya kai Sarkin yakina abin alfahari a gare ni, ina son ka yi shiri yanzu ka tafi izuwa dajin Hizurul Aswad ka hallaka Aljani Maruful Dauwaz da abokan tafiyarsa tunda su Aljani Sharkamuza sun kasa kawar da su." Sa'adda sadauki Najwar ya ji wannan umami sai ya dubi Sarki Nashmir cikin alamun tsoro da matukar damuwa ya ce, "Ya shugabana ka yi sani cewa Aljani Maruful Dauwaz ba karamin hatsabibi ba ne don haka ina matukar shakkar tararsa da yaki duk da cewa kuwa na san na fi karfinsa. Ina mai baka shawarar ka yi shiri da kanka ka je ka gama da shi tun gabannin ya iso nan ya yi maka muguwar ɓarna". 314 TASKARNOVELS.COM.NG Koda sadauki Najwar yazo nan a zancensa sai Sarki Nashmir ya sake bushewa da dariya a karo na biyu daga bisani kuma sai ya murtuke fuskarsa kamar an aiko masa da sakon mutuwa ya nuna Najwar da yatsa cikin fishi ya ce, "Ya kai Najwar ka yi sani cewa duk wani motsi da za ka yi akan tafin hannuna kake. Na san sirrin zuciyarka fiye da yadda kake tsammani. Karya kake yi ka ce da ni kana shakkar yin karo da Aljani Maruful Dauwaz domin ka fi karfinsa nesa ba kusa ba. Na sani cewa ka daɗe kana da burin ka ga na mutu ka haye kan karagata sannan ka auri 'yata Gimbiya Ramlatul Siyam da karfin tsiya, amma baka sami damar hakan ba. In da za ka iya hallaka ni da tuntuni ka kawar da ni. Bisa dole ne ka hakura ka ci gaba da jira. Yanzu zan ba ka zabi guda biyu. Ko dai mu yi yakı yanzu take anan cikin fadata idan ka kashe ni ka sami karagata da 'yata. Idan kuma ni ne na kashe ka shi ke nan sai na je na tari su Aljani Maruful Dauwaz. Idan. kuwa ba za ka iya yakata ba sai ka shirya ka tafi izuwa dajin Hizurul Aswad. Maza ka yankewa kanka shawara yanzuyanzu" 315 TASKARNOVELS.COM.NG Sa'adda Najwar ya ji wannan zaɓi da Sarki Nashmir ya ba shi sai hankalinsa ya dugunzuma ainun yai shiru yana tunanin abin da ya kamata ya yi. Kawai sai Sarki Nashmir ya mike tsaye ya zare takobinsa ya ce, "Tunda ka kasa bai wa kanka zabi sai mu yi yakin. Da jin haka sai sadauki Najwar ya yi murmushi sannan ya risina cikin biyayya ya ce, "Haba ya shugabana, wane ni na ce zan yi yaki da kai alhalin tuntuni na jarraba na gani cewa kana gaba da ni. Na amince zan tafi na tari su Aljani Maruful Dauwaz kuma na rantse da darajar karagarka ba zan dawo nan gare ka ba sai da kan Maruful Dauwaz da na abokan tafiyarsa". Koda gama fadin hakan sai sadauki Najwar ya juya ya fice daga cikin fadar da sauri. Cikin kankanin lokaci ya isa gidansa ya shiga kimtsawa. Cikin hanzari ya yi gagarumar shigar yaki, ya debo dukkan gurayensa da layunsa na tsafi ya daurasu a jikinsa sannan ya fito ya hau 316 TASKARNOVELS.COM.NG kan wani basamuden Aljani wai shi BARUKUL MASNUR wanda ya ninka Sharkamuza sau uku a girma da karfin dantse da na sihiri. Nan take Barukul Masnur ya bude fuka- fukansa ya tashi sama dauke da sadauki Najwar suka luluka a cikin gajimare. Lokacin da Sarki Nashmir ya fito daga cikin fadarsa bayan ya gama ganawa da sadauki Najwar sai ya wuce kai tsaye izuwa cikin gidan sarautar ya nufi bangaren da turakar Gimbiya Ramlatul Siyam. Duk inda Sarki Nashmir ya ratsa sai ka ga wadannan Dakaru na aljanu da na bil'adama suna sujjada a gare shi kuma suna buɗa masa hanya yana wucewa. Koda Sarki Nashmir ya dubi miliyoyin Dakarun aljanun da ke shawagi a kan saman rufin turakar Gimbiya don tabbatar da tsaro sannan ya dubi miliyoyin Dakarun bil'adama da suka kewaye harabar turakar gaba daya sai ya cika 317 TASKARNOVELS.COM.NG da farin ciki ya kama zancen zuci yana mai cewa a ransa, ya ma su Aljani Maruful Dauwaz za su iya shigowa har cikin wannan fada su kashe gabadayan wadannan Dakaru sannan su sace Gimbiya Ramlatul Siyam? To wai shin ma shi yana ina har hakan za ta faru? Abu na biyu kuma, ta yaya su Maruful Dauwaz za su sami yawun barcin bakinsa alhalin shi ba ya barci sai sau daya a cikin kwanakin mako?" Koda Sarki Nashmir ya zo nan a zancen zucinsa sai ya kyalkyale da dariya a fili bai sani ba har Dakaru, barori da kuyangin gida sarautar suka bi shi da kallo suna mamakin dalilin dariyar tasa. A daidai wannan lokaci ne ya iso daf da kofar turakar Gimbiya Ramlatul Siyam, Dakarun da ke tsaron kofar turakar suka bude masa ya kunna kai ciki. Sai da ya yi doguwar tafiya a cikin turakar sannan ya iso cikin dakin barcin 318 TASKARNOVELS.COM.NG Gimbiya Ramlatul Siyam, ko ina ya duba sai dai ya ga kuyangin na ta hidima iri-iri. Da shigar Sarki Nashmir cikin dakin barcin sai ya iske Gimbiya Ramlatul Siyam ita kadai kwacen akan gado ta yi rub da ciki tana ta faman rusa kuka. Cikin tsananin mamaki da tashin hankali Sarki Nashmir ya karasa gare ta ya zauna a gefen gadon ya tashe ta zaune a lokacin da idanunta suka cika sharkaf da hawaye ya dube ta a cikin matukar damuwa ya ce, "Ya ke 'yata, mene ne ya faru gare ki wanda har ya sa ki zubar da hawaye? Kin sani cewa ban taɓa ganinki ba a cikin wannan hali". Sa'adda Ramlatul Siyam ta ji wannan tambaya sai ta yi shiru tana mai sunkui da kanta kas ta ki cewa komai. Kawai sai Sarki Nashmir ya zare wata wuka a jikinsa ya yanki kansa a damtsen hannun hagu, jini yai tsartuwa akan fuskar 319 TASKARNOVELS.COM.NG Ramlatul Siyam ya sake daga wukar zai daďa yi wa kansa rauni sai Ramlatul Siyam ta yi wuf ta rike hannunsa kuma ta fashe da kuka tana mai cewa, "Saboda me za ka cutar da kanka? Nashmir ya dube ta a lokacin da idanunsa suka cika da kwallah ya ce, "Ina amafanin rayuwata idan har ba zan iya yi miki maganin matsalar da ta same ki ba? Lallai akwai wani babban al'amari wanda kika daɗe kina ɓoye min shi, lallai sai kin sanar da ni shi a yau kuma a yanzu. Idan kuwa kika ki sai dai a fitar da gawata daga cikin wannan ďaki naki. Koda jin wannan batu sai Gimbiya Ramlatul Siyam ta rungume Sarki Nashmir ta fashe da wani sabon kuka sannan ta ce, "Ya kai Abbana ka yi sani cewa na dade ina yin wani mugun mafarki amma ban taba sanar da kai ba. Wannan Aljani da ka nuna mini a madubin tsafinka shi nake gani a cikin mafarkina kuma 320 TASKARNOVELS.COM.NG ana nuna mini cewa ya zo har cikin gidan sarautarmu ya yaki Dakarunka an yi kazamin yaki wanda ya zamo sanadin asarar miliyoyin rayuka da dumbin dukiya har sai da dukkan ginin gidan nan ya fadi kasa kuma gagarumar gobara ta kama ko ina. Ina ji ina gani wannan Aljani ya shiga tsakanina da kai ya raba mu ya dauke ni yai sama da ni a lokacin da kai kuma kake cikin wani mugun hali ka kasa koda mikewa tsaye". Koda Gimbiya Ramlatul Siyam ta zo nan a zancenta sai Sarki Nashmir ya takarkare ya kwarara uban ihu. Al'amarin da ya firgita gabadayan jama'ar da ke cikin gidan sarautar ke nan. Dakaru suka rugo da gudu izuwa cikin turakar rike da makamai tsirara. Da shigowar Dakarun suka ga rauni a hannun Sarki amma kuma babu kowa a cikin turakar sai su biyu jal shi da 'yarsa sai suka cika da dumbin mamaki. 321 TASKARNOVELS.COM.NG Nan take Sarki Nashmir ya yi wa Dakarun inkiya suka juya da baya suka fice suka kullo kofar. Sarki Nashmir ya dubi Gimbiya Ramlatul Siyam cikin tsananin takaici ya ce, "Ya ke 'yata hakika kin yi babban kuskure da kika boye min wannan al'amari. Inda ace kin sanar da ni tun a ranar da kika fara yin mafarkin da tuni na dauki matakin gaggawa na kawar da waďannan abokan gaba nawa. Yanzu dole ne na zuba ido na ga abin da zai faru tsakaninsu da Sarkin yakina Najwar. Idan har bai sami nasarar hallaka su ba dole ne na zauna na jira karasowarsu sannan ayi ta ta kare amma kafin sannan yanzu zan shiga cikin dakin halwar tsafina domin na binciko mafita. Duk abin da ake ciki kada ki kuskura ki fito daga cikin wannan daki face ni da kaina na zo na ce ki fito. Ina tabbatar miki da cewa in dai kina cikin wannan daki babu wata masifa ko wani tsautsayi da ya isa ya same ki." Koda gama fadin haka sai Sarki Nashmir ya mike tsaye ya juya ya fice daga cikin dakin da 322 TASKARNOVELS.COM.NG sauri ya nufi inda dakin tsafinsa yake, ya bar Gimbiya Ramlatul Siyam a zaune cikin tsananin tashin hankali da rudewa. Wannan shi ne abinda ya faru a Birmin HINDU bayan Sarki Nashmir ya tura Dakarunsa na farko izuwa dajin Hiuzurl Aswad domin su kashe su Aljani Maruful Dauwaz. Al'amarin su Aljani Maruful Dauwaz kuwa, bayan sun shafe rabin sa'a a kwance suna hutawa sai Aljani Maruful Dauwaz ya karanta waďansu dalasiman tsafi. Nan take wata irin murtukekiyar sarkar tsafi ta fito daga cikin karkashin kasa ta nannaďe hannayensa, kafafunsa da fuka-fukansa sannan ta daure su tamau yadda ko motsa su ba zai iya ba. A sannan ne ya dubi Rahila da Sarki Laffaru ya ce, "Ku zo ku gyara mini karayar kasusuwan fuskata". Koda jin haka sai Rahila ta dubi Sarki Laffaru ta ce, "Je ka ka karyo mini dogayen itatuwa kamar guda bakwai masu dan kwari." 323 TASKARNOVELS.COM.NG Nan take Laffaru ya tafi domin cika umarnin. Koda ya hau kan wata bishiya ya fara karyo itatuwan sai takaici ya kama shi saboda ya tuna cewa shi fa Sarki ne mai cikakken iko wanda duniya take tsoro amma yau ga shi mace tana sa shi aiki, tana ba shi umarni yana bin umarnin cikin rawar jiki. Nan dai ya hanzarta ya je ya kai wa Rahila wadannan itatuwan. Tana karɓar itatuwan sai ta hau kan kirjin Aljani Maruful Dauwaz ta zauna kai ka ce akan wani katon tsauni take. Take ta umarci Maruful Dauwaz da ya bude bakinsa. Ba tare da gardamar komai ba kuwa yawangame bakin nasa mai fadi tamkar rijiyar mutanen da. Rahila ta zura hannayenuta a cikin bakin. 324 TASKARNOVELS.COM.NG Kodata kamo kasusuwan fuskar tasa wadanda suka kakkarye ta fara gyarawa tana daure su da itatuwa sai Maruful Dauwaz ya fara kwarara uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogi. Ihun nasa ya haddasa wanzuwar iska mai karfi a cikin dajin wacce ta rinka zubar da bishiyoyi kasa. Hakan bai sa ta tausayawa Maruful Dauwaz ba sai ta ci gaba da aikinta har ta kammala. Saboda tsananin azabar da Maruful Dauwaz yaji sai da hawayen wuya ya zubo masa. Bayan Rahila ta gana gyara wa Maruful Dauwaz karayar kasusuwan fuskarsa ne suka bude jakar guzurinsu ita da Sarki Laffaru suka fiddo da abinci suka ci. Shi kuwa Maruful Dauwaz sai ya gangara izuwa cikin wata katuwar korama ya kafa bakinsa ya kama shan ruwa, sai da ya sha ruwan mai yawan gaske wanda adadinsa ya kai duro 325 TASKARNOVELS.COM.NG ashirin da biyar sannan ya fito daga cikin koramar ya koma wajen su Rahila ya kishingida suka fara hira, inda Maruful Dauwaz ya dubi Rahila ya ce, "Ya ke wannan 'yar Sarki me ya sa na ga kamar kina cikin damuwa ne kin kasa sakin jikinki ki ci abinci sosai?" Koda jin zuciya wannan batu sai Rahila ta yi ajiyar sannan ta ce, "Ya kai jarumin jarumai, ka yi sani cewa ba komai ba ne ya sa ka ga ina cikin wannan hali ba face abubuwa biyu da suka dame ni. Abu na farko shi ne, hankalina a tashe yake bisa ganin irin mummunan yakin da muka yi da Dakarun Sarki Nashmir wanda da kyar muka tsira da rayuwarmu. Tabbas na san cewa har a yanzu fa ba tsira muka yi ba kuma a ko yaushe za mu iya ganin waɗansu mugayen Dakarun nasa. 326 TASKARNOVELS.COM.NG Saboda haka ni yanzu ina ganin cewa zamanmu ma a nan yana da hadarin gaske. Ko dai mu nemi wajen buya ko kuma mu tashi mu ci gaba da tafiyarmu in ya so mu yi jinyar jikin namu akan hanya. Abu na biyu da yake damuna shi ne, yawan tunowa da sauran abokan tafiyarmu waɗanda muka baro a can kogon Darul Iksina. Hakika ina matukar tausaya musu musamman idan na tuno da irin tsananin wuyar da muka sha tare da su da yadda wasunsu suka rasa masoyansu. Yanzu ga shi mun baro su a cikin kogon na Darul Iksina kuma babu yadda za su iya fitowa. Yanzu shi ke nan duk burinsu ya yanke ke nan, sun hallaka bisa wannan tafarki?".Koda Rahila ta zo nan a zancenta sai ta fashe da matsanaicin kuka. Al'amarin da ya karya zuciyar Aljani Maruful Dauwaz da Sarki Laffaru ke nan su ma 327 TASKARNOVELS.COM.NG suka kama zubar da hawaye saboda tausayi! Tsawon 'yan dakiku dayansu bai ce uffan ba. daga can sai Maruful Dauwaz ya dubi Rahila ya ce, 'Ya ke wannan 'yar Sarki, hakika kin zo da shawara mai kyau bai kamata mu ci gaba da zama anan ba domin masu iya magana sun ce, 'Zama waje daya tsautsayi ne in ji kifi'. Yana da kyau mu nemi maboya inda za mu yi jinyar jikinmu domin ina tabbatar muku da cewa ni kaina ba zan iya ci gaba da tafiya ba mai tsawon koda rabin sa'a a cikin wannan hali da nake. Batun abokan tafiyarku kuwa da muka baro su a can kogon Darul Iksina ni kaina na yi matukar bakin ciki bisa halin da suka kasance kuma zan so ace sun kubuta sun fito daga kogon a raye amma maganar gaskiya abu ne mai matukar wuya. Na yı muku alkawari idan har mun sami nasarar shiga fadar Sarki Nashmir mun dauko Gimbiya Ramlatul Siyam lallai sai mun biya ta tsibirin Darul Iksina mu gani ko abokan tafiyar taku sun fito." 328 TASKARNOVELS.COM.NG Koda Rahila da Laffaru suka ji wannan batu sai farin ciki ya lulluɓe su suka ji kaunar Aljani Maruful dauwaz ta karu ainun a cikin zuciyarsu. Duk su biyun sai suka fada kansa suka rungume shi suna masu yi masa godiya. Maruful Dauwaz ya ce, "Yanzu sai mu tashi mu tafi neman inda zamu buya a cikin dajin nan domin mu ya jinyar kanmu. Za mu yi wasu tambayoyi kafin mu sako kashi na Hamsin da uku. Zan yi farin ciki idan na samu gamsassun bayanai daga gare ku wanda shi ne zai kara mini kwarin guiwa har mu samu mu shiga littafi na Huďu. Na gode! Kafin daya daga cikin su Rahila ya ce wani abu sai Maruful Dauwaz ya sure su su biyun ya aza su a gadon bayansa sannan ya yunkura da kyar cikin matukar karfin hali ya tashi sama ya kama yawo a cikin dajin yana neman inda za su бuya. 329 TASKARNOVELS.COM.NG Bai daďe da fara shawagi a sama ba kuwa sai ya hango wani katon tsauni mai yawan kofofin kogo. Kai tsaye Maruful Dauwaz ya durfafi wannan tsauni ya dira a cikin kofar kogon. Dirarsa ke da wuya sai ya yi tsafi wutar ice ta baiyana a kan hannayensa. A sannan ne Rahila da Laffaru suka sauko daga kansa suka tsaitsaya suna kallonsa kawai. Maruful Dauwaz ya dube su ya ce, "Ku zo mu duba ko ina a cikin dukkan kogon da ke kan wanna tsauni domin mu tabbatar da lafiyar tsaunin. Ba tare da gardamar komai ba kuwa su Rahila suka amince da wannan shawara. Sai da ska shafe sa'a uku cur suna ta shige da fice a cikin ramukan da ke kan tsaunin amma ba su ga halitta guda daya ba a ciki, koda kuwa kwaro ko tsuntsu. Abin da ya fi daure musu kai shi nc, duk ramin da suka shiga sai su ga ya bulle zuwa cikin wani, sannan sun ga wadansu irin manya-manyan tukwane irin na mutanen farko a cikin kogon gami da gidajen itatuwa da shimfidu na fatun dabbobi iri-iri, wata fatar ma ba su taɓa ganin 330 TASKARNOVELS.COM.NG irin ta ba kuma dukkan wadannan abubuwa sun yi kura matuka kuma yana ta lullube su alamar cewa an shafe shekaru masu yawa ba a yi amfani da su ba. Koda ganin wannan al'amari sai Aljani Maruful Dauwaz yai ajiyar zuciya ya ce, "Tabbas akwai maridan da suka yi rayuwa a cikin wannan kogo shekaru aru-aru da suka shude". Koda jin wannan batu sai Sarki Laffaru yai sauri ya goge yanar da ke kan wani gadon ice sannan ya yaye shimfidar da ke kansa sai suka yi arba da wani katon kwarangwal na wani maridi. Hatta Aljani Maruful Dauwaz sai da ya firgita da ya ga wannan kwarangwal domin iya tsawon rayuwarsa a duniya bai taba ganin halitta mai girma kamarsa ba, don shi kansa ya fi shi tsawo a tsaye sau hudu. Sarki Laffaru ya zare takobinsa ya kwankwashi kashin kwarangwal din, kawai sai ya jinjina kai 331 TASKARNOVELS.COM.NG ya ce, "Wannan kwarangwal din ya fi shekaru dubu uku da mutuwa a cikin wannakogo". Cikin mamaki Rahila ta dubi Sarki Laffaru ta ce, Kai kuwa yaya aka yi ka san wannan ilimi?". Laffaru ya yi murmushi ya ce, "Ai lokacin da nake da karfin sihirin tsafina na yi bincike matuka akan wannan fanni na sanin dadewar abu a duniya, don haka na sami ilimi mai yawa akan hakan". Gama fadin hakan ke da wuya sai Aljani Maruful Dauwaz ya dauki gawar wannan kwarangwal daga kan gadon icen yai jifa da ita izuwa jikin kogon dutse ta rugurguje sannan ya sake kade kurar da ke jikin fatar buzun da aka shimfida. Akan buzun ya kwanta akan gadon yana mai cewa, "Ni kam na sami wajen kwanciyata ku ma sai ku nemi naku. Lallai a cikin wannan kogo za mu yi jinyarmu tsawon mako biyu. Hankalina ya kwanta da wannan kogo domin ko wani mugun 332 TASKARNOVELS.COM.NG abun ne ya zo mana in dai muna cikin nan zai yi wuya ya iya hallaka mu cikin sauri". Gama fadin hakan ke da wuya sai Maruful Dauwa ya rufe idanunsa, nan take barci ya dauke shi sakamakon tsananin wahalar da ya sha a bakin gumurzun da ya yi da Aljani Sharkamuza. Kash! Rashin sani ya fi dare duhu! Inda Aljani Maruful Dauwaz ya san abin da zai faru da bai kwanta akan wannan gadon ice har bacci ya dauke shi ba. Domin kuwa, yin barcinsa ke da wuya Aljani Barukul Masrur ya sauka a dajin dauke da sadauki Najwar suka duro a daida inda aka yi wannan bakin gumurzu tsakanin su Aljani Sharkamuza da su Aljani Maruful Dauwaz. Ai kuwa suna dira suka yi arba da gawar Aljani Sharkamua. Koda suka ga irin kisan da aka yi masa, wato suka ga zururun rami ta cikin idonsa 333 TASKARNOVELS.COM.NG guda har bayan keyarsa sai suka cika da mamaki kuma zuciyarsu ta kama tafarfasa kamar za ta kone. Nan take Aljani Barukul Masnur ya shaki numfashi sannan ya dubi sadauki Najwar ya ce, "Ya shugabana na ji kamshin bil'adama guda biyu a cikin wannan daji da kuma kanshin Aljani dan uwana guda daya". Koda jin haka sai sadauki Najwar yai murmushin mugunta ya ce, "Abin da nake so da kai shi ka tashi sama ba can kololuwa ba ka dinga kaďa fuka-fukanka a hankali yadda ba za a ji motsinka ba har mu gano inda su Maruful Dauwaz suke. Sai dai kawai mu yi musu MAMAYAR BAZATO! Aljani Barukul Masnur ya yi dariya ya ce "Hakika ka zo da shawara mai kyau ya shugabana". Gama fadin hakan ke da wuya Barukul Masnur ya bude fuka-fukansa ya yi sama yana mai daďa 334 TASKARNOVELS.COM.NG bude kofofin hancinsa domin ya jiyo kamshin su Maruful Dauwaz ya gano a inda suke. A cikin kogon dutse kuwa, lokacin da Rahila da Sarki Laffaru suka ga Aljani Maruful Dauwaz ya kama barci har da yin munshari mai nauyi sai su ma su Rahila suka

Chapter 12 of 18