ci gaba da wannan
dauki ba dadi har tsawon sa'a daya da rabi, a
sannan ne suka iso tsakiyar dajin.
Koda Tsuntsayen suka ga su Imran na neman
tsira daga sharrinsu, sai suka taru gaba dayansu
suka yi musu kawanya kuma suka yi musu
103
TASKARNOVELS.COM.NG
rubdugu aka ruguntsume da sabon azababben
yaki mai tsananin firgitarwa da tashin hankali,
domin kuwa, su tsuntsayen suna yakin ne da
dukkan karfinsu don ayi ta, ta kare, su ma su
Imran sun jajirce iyakar iyawarsu don kare
kansu.
Koda aka dan jima ana wannan bakin artabu sai
al'amura suka sauya, saboda jaruman sun fara
gajiya. Hatta gimbiya Rahila ma ta gaji ainun har
wani tsuntsu ya cafi kugunta da 'yan yatsunsa
biyu ya yunkura zai yi sama da ita ke nan sai
sadauki Imran ya do ki tsakiyar kansa da sanda.
Tsuntsun ya rikirkice, kuma ya yi wani uban
ruri sakamakon tsananin zafi da zogin da ya ji,
babu shiri ya saki Rahila ta fado kasa a matukar
galabaice, saboda kugun na ta ma da ya danka
da yatsun kafarsa ya yi ma ta rauni har ta kasa
mikewa ta ci gaba da gudu. Koda ganin halin da
Rahila ta shiga sai boka Muzaffar yai wuf ya
sure ta ya goya ta a bayansa ya ci gaba da gudu,
kuma aka ci gaba da gumurzun a haka.
104
TASKARNOVELS.COM.NG
Kaico! Tsautsayi ba a sa masa rana. Ita kuwa
masifa, idan ta zo babu makawa sai ta afku, sai
dai a dauki dakon hakuri dole.
Lokacin da aka sake dan jimawa a cikin wannan
hali sai ya zamana cewa kayan karfen da ke jikin
kowa wanda ke dan ba su kariya duka ya
kekkece babu mai sauran amfani, kowa sai ya
fara gajiya, ya Zamana cewa mugayen
tsuntsayen sun rutsa jaruman a waje daya sun
kasa ci gaba da gudu, don haka sai suka ci gaba
da kai musu mugayen hare-hare. Tun suna
karewa da mai da martani har ya zamana cewa
sun kasa mai da martanin, sai dai kare kai.
Tafiya gaba-gaba dai sai kare kai din ma ya
gagara.
Wayyo! A wannan lokaci ne fa Tsuntsayen suka
fara yiwa jaruman mugayen rauni. Sarki Laffaru
ne ya fara kifewa kasa yana mai kwarara uban
ihu sa'adda wadansu tsuntsaye biyu suka yi
masa rubdugun sara da faratan kafafunsu a
lokaci guda.
105
TASKARNOVELS.COM.NG
Saran farko a kirjinsa aka lafta masa har jini yai
feshi, sara na biyu kuwa a gadon bayansa ne
lafcece. Jarumi Shaharan da ke ta guje-guje da
zulle- zulle a tsakankanin Tsuntsayen sai shi ma
wani tsuntsu ya fake shi ya make shi a fuska.
Saboda karfin makuwar sai da yai katantanwa a
sama sau uku sannan ya baje a kasa sumamme.
Gimbiya Rahila da Zarina kuwa, wani tsuntsu ne
yai musu kwaf daya da fuka-fukansa, su ma dai
suka yi ďaiďai a kasa ko kyakkyawan motsi ba
su kara yi ba. Haiman, Shadira da boka Muzaffar
kuwa, a kafafunsu aka laf-lafta musu sara, suka
yi tsugunnon dole suna kwarara ihu sakamakon
tsananin zogi da radadin da suka ji.
Nan take jini ya rinka zuba a jikinsu, kuma jiri
ya debe su suka kwanta a kas bisa dole suka
rungumi Raddara kawai suna jiran su ji
mutuwarsu domin babu abinda za su iya
tsinanawa don kare kansu.
106
TASKARNOVELS.COM.NG
Lumaira mahaifiyar Imran da Sarkin Farisa
kuwa, tuni duk sun suma, ba don samun rauni
ba, sai saboda tsananin firgita bisa ganin
wannan gagarumar masifa da suka tsinci kansu
a ciki wacce tafi karfin jaruman da ke kokarin
kare lafiyarsu.
Nan dai ya zamana cewa babu sauran jarumi
guda daya da ke tsaye a cikinsu face sadauki
Imran, shi ma albarkacin iya sarrafa wannan
sanda da ke hannunsa ne yasa ya kai labari.
Koda Tsuntsayen suka ga saura jarumi Imran
shi kadai a tsaye yana fafatawa da su, sai suka ja
da baya gaba dayansu suka tsaitsaya a sama
cak! Cikin iska kamar hadin baki, kai kace
hutawa suke. A lokacin ne shi ma jarumi Imran
ya tsaya cak! Ya gyara tsayuwa rike da sandarsa
gamgam da hannu biyu, yayin da jini ke
satatowa ta kan gefen hannunsa na hagu
sakamakon wani lafcecen yanka da ke kan
kafadarsa.
107
TASKARNOVELS.COM.NG
Imran ya dudi gabadayan jarumai abokan
tafiyarsa ya gansu gabadaya a kwance a kas
cikin mugu hali kamar ma wasunsu sun mutu,
domin babu alamar rai a jikinsu.
A sannan ne ya tuno da mahaifiyarsa, wacce ke
goye a bayansa, kawai sai ya kira sunanta, ai
kuwasai ya ji shiru. Cikin firgici! Ya taɓo kanta
da hannunsa guda, sai yaji kan ya langabe
alamar babu rai a tare da ita.
Cikin gagarumin fushi Imran ya takarkare ya
kwarara uban ihu ya falfala da matsanaicin
gudu izuwa kan wadannan Tsuntsayen da
dukkan fushinsa da karfinsa da nufin a yi ta, ta
kare ko shi ko su!
Ai kuwa su ma Tsuntsayen sai suka taso masa
gaba dayansu suna yin wannan ruri mai iya
kurmantar da bil'Adama, amma shi bai ma san
suna yi ba.
108
TASKARNOVELS.COM.NG
Kafin ya hade da Tsuntsayen tuni ya daka
wawan tsalle sama tamkar an cilla shi daga cikin
baka ya tari Tsuntsayen ya hau dukansu da
sandarsa a cikin bakin zafin nama da dukkan
iyakar karfin dantsensa.
Bisa tsautsayi kuwa sai ya sami daya daga
cikinsu Tsuntsayen a ido. Nan take idon
tsuntsun ya fashe, ya sulalo kasa. Ji ka ke tim!
kamar giwa ta fadi, don har sai sa dakasa ta yi
girgiza. Tsuntsun ya baje matacce a kas ko
shurawa bai yi ba.
Koda Imran ya ga ya sami wannan nasa ta gano
lagon Tsuntsayen sai ya ci gaba da dukan
idanun Tsuntsayen da sandarsa. Ai kuwa sai ga
shi yana karkaɗosu kasa suna mutuwa.
Babu abin da zai yi matukar burge mutum a
wannan gumurzu face yadda Imran yake daka
tsalle sama tamkar fuka-fukai ne a jikinsa, wato
109
TASKARNOVELS.COM.NG
a sama yaci gaba da gumurzun da Tsuntsayen.
Wani lokacin ma sai dai ka ga yana tattaka
Tsuntsayen tamkar yana taka matattakalar
bene. Abinka da Sarkin yawa ya fi Sarkin karfi, a
hakan ne wasu Tsuntsayen suka rinka kai masa
sara da suka.
Wani loakcin ka ga sun same shi jini na tsartuwa
da feshi a jikinsa yana kwarara uban ihu, amma
saboda bakin naci da dakewar zuciya da juriya
shi ma bai fasa ragargazar su ba.
Abin da ya ayyana a ransa shi ne, koda
wadannan Tsuntsayen za su kashe shi sai ya
tabbatar da cewa shi ma ya yi musu muguwar
бarna da yawansu tun da dai ya gano lagonsu.
Haka dai aka ci gaba da wannan mummunan
artabu tsakanin jarumi Imran da mugayen
tsuntsayen har izuwa tsawon sa'a guda, ya
zamana cewa ya kashe fiye da kaso biyu cikin
110
TASKARNOVELS.COM.NG
ukunsu, amma fa a wannan lokaci ya gaji ainun,
har ba ya iya yin tsalle sama a kasa yake yakin.
Wani lokacin ma idan suka make shi sai ya baje
a kasa kamar ya mutu, amma da zarra sun yi
caa! a kansa za su yagalgala shi sai su ga ya mike
zumbur! Ya ci gaba da ragargazar su tamkar ma
a sannan ya fara yakin. Kai wani lokacin ma har
lambo yake yi wa tsuntsayen ya yi kamar ya
mutu, sai dai kawai su ga ya sake mikewa ya ci
gaba da kashe su.
Su kansu wadannan mugayen Tsuntsayen a iya
wanzuwarsu a cikin wannan daji ba su taɓa
haduwa da takadarin bil'Adama mai taurin rai
ba kamar Imran.
Koda Tsuntsayen suka ga Imran ya yi musu
gagarumár ɓarna, kuma ga shi sun kasa kashe
shi sai suka karaya, suka dauka cewa ba za su
iya kashe shi ba, don haka ba shiri su duka suka
111
TASKARNOVELS.COM.NG
yi sama suka luluka izuwa can kololuwar sama,
suka bar nahiyar dajin gaba daya.
A dai-dai wannan lokaci ne Imran ya kama layi
da tangadi kamar wanda ya sha giya ya bugu,
sakamakon jinin da ke zuba a cikin sassan
jikinsa. Bai ma san sa'adda sandarsa ta suбuce
daga hannunsa ba.
Tabbas a wannan lokaci inda Tsuntsayen na
kusa da salin-alin za su sa masa wawa su cinye
shi, ko ruburbushin jikinsa ma ba za su rage ba,
domin ba zai iya kare kansa da komai ba,
saboda dukkan karfinsa ya kare.
Inda Tsuntsayen sun san cewa haka za ta faru
da tabbas basu gudu ba! Nan take Imran ya kife
kasa sumamme. In da ace akwai mutum tsaye a
filin da aka yi wannan bakin gumurzu da dole ya
ce kowa ya mutu, domin babu wanda yake
numfashi daga cikin su Imran.
112
TASKARNOVELS.COM.NG
Wajen gaba daya ya yi kaca-kaca da jini da kuma
gawarwakin wadannan tauntsaye abin ba kyan
gani. Sai bayan kusan sa'a biyu lokacin da wata
irin iska mai tsananin sanyin gaske ta fara
kadawa sannan jaruna Shadira ta farfado ita
kadai.
Tana bude idanunta ta ji gaba daya jikinta yai
ma ta nauyi tamkar an danne ta da katon dutse,
don haka sai ta kasa mikewa tsaye. Koda ta dubi
filin yakin ta ga gabadayan abokan tafiyarta a
kwance babu mai numfashi, sai ta fashe da kuka,
domin a zatonta kowa ya mutu babu sauran mai
rai.
Nan fa ta fara jan jiki tana tafiya a hankali da
kyar har ta isa inda jarumi Imran ke kwance.
Shadira ta dago da kan Imran ta ga baya motsi,
kuma babu alamar numfashi a jikinsa, sai kawai
ta rungume kansa a kirjinta ta dada fashewa da
matsanaicin kuka na bakin ciki.
113
TASKARNOVELS.COM.NG
Ruwan hawayenta da ke zuba akan fuskara ne
ye zamo sanadin farfadowarsa daga dogon
suman da yayi. Nan take Shadira ta ji Imran ya
rike kafadarta da hannunsa guda.
Koda ta ji haka ta gane cewa bai mutu ba sal ta
bushe da dariya ta sake rungume shi a kirjinta
cikin tsananin farin ciki. Shi ma sai ya kama
dariyar murna. Sai da suka daďe a kankame da
juna suna ta dariya kamar ba za su saki juna ba.
Bayan sun dawo cikin haiyacinsu ne duk su
biyun suka dubi sauran abokan tafiyarsu, suka
ga cewa har yanzu fa su biyu ne rak! Suka mike,
sai hankalinsu ya dugunzuma ainun.
Imran ya dubi Shadira a lokacin da hawaye ya
subuto masa, ya ce, "Yanzu mu biyu ne rak ke
nan muka tsira da rayuwarmu a wannan daji?"
Koda jin wannan tambaya sai ita ma hawaye ya
zubo ma ta ta ce, "Haka dai yanayi ya nuna,
amma zai fi kyau mu tashi mu duba kowa, babu
mamaki akwai sauran mai rai, domin kaicma na
fitar da rai da kai, amma kuma sai ga shi ka
mike".
114
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan batu sai Imran yaji ya sami
kwarin zuciya gami da farin ciki. Kawai sai ya
yunkura ya mike tsaye da kyar yana tangadi
kamar ba zai iya taku daya ba. A haka ya nufi
inda sauran abokan tafiyar ke kwance yana
harde kafafu kamar zai fadi, domin har a sannan
bai daina jin jiri ba.
Ita kuwa Shadira sai ta sake yunkurawa domin
ta mike tsaye amma sai ta kasa.
Imran ya je kan kowa daya bayan daya ya
girgizavsu amma har ya gama duba su duka bai
ga mai alamar rai ba.
Koda ganin haka sai ya durkushe kasa bisa
guiwoyinsa ya fashe da kukan bakin ciki. Koda
Shadira ta hango halin da yake ciki sai ta ci gaba
da jan ciki har ta riske shi sannan ta kwanta
akan kirjinsa ta ci gaba da tayavshi kukan.
Da ma Imran mahaifiyarsa ce wadda ya duba
daga karshe don haka, yana kankame da ita
115
TASKARNOVELS.COM.NG
yana ta kuka, a lokacin da ya ji ya tsani kansa,
kuma ya tsani duniyar gaba daya. Bayan sun yi
kuka har sun gaji sai Shadira ta dago da kanta
daga kan kirjinsa ta dube shi ta ce, "Ya kai
masoyina, wai shin yanzu mene ne amfanin
rayuwarmu a doron kasa? Na rasa dan uwana
Masnur, kai skuma ka rasa mahaifiyarka.
Dukkan burinmu na duniya ya yanke. Yanzu ga
shi abokan tafiyarmu kaf ďinsu sun mutu. Mene
ne amfanin zuwanmu kogon Darul Iksina tunda
wadanda za mu je dominisu babu su?
Sa'adda Shadira ta zo nan a jawabinta sai Imran
ya sake fashewa da matsanaicin kuka, ya ce,
"Hakika rayuwarmu ba ta da wani amfani,
gwara ma ace mu ma duk mun mutu" Koda jin
wannan batu sai Shadira ta yi murmushi ta ce
"Ai kuwa ni yanzu farin cikin da ya rage mini a
nan duniya kawai shi ne, na mutu akan kirjinka,
ko ba komai na mutu tare da masoyina na biyu
wanda na so shi fiye da komai. Ka sani cewa in
ban da dan uwana Masnur da na rasa babu
wanda zuciyata ta aminta da shi kuma take
kauna da gaskiya sama da kai! Koda jin haka sai
hawayen farin ciki ya zubowa Imran daga can
116
TASKARNOVELS.COM.NG
kuma sai ya ce, ba shakka kin zo da shawara to
amma ta yaya za mu mutu a tare ba tare da
ďaya ya riga ďaya mutuwa ba?
Shadira ta, mu nausa cikin daji watakila mu
haďu da wata muguwar dabbar, sai mu sallama
mata kanmu ta cinye mu ko kuma mu nemi
katon tsauni mu hau karshensa sai mu
rukunkume juna mu sallamo kasa bisa duwatsu
mu hallaka. Koda jin haka sai Imran ya ce,
"Tabbas kin zo da shawara mafi kyau".
Nan take Imran ya ajiye mahaifiyarsa a gefe
daya ya kura mata idanu sa'adda hawaye ya ci
gaba da shatata bisa kan kumatunsa har izuwa
tsawon 'yan dakiku, sannan ya ce, "Ya ke
Ummina ki gafarce ni, hakika zan mutu da
tsananin bakin ciki bisa rashin samun nasarar
cika burin zuciyata.
Na so a ce na mutu akan hannunki domin na
nemi gafararki bisa abin da na kasa cikawa,
117
TASKARNOVELS.COM.NG
amma idan har akwai wata rayuwar bayan
wannan na yi miki alkawari sai na cika miki
burinki.. Haka dai Imran ya ci gaba da surutai
barkatai ba tsari.
Koda Shadira ta fuskaci alamun yana neman
zautuwa sai ta yunkura da kyar ta kama
hannayensa suka mike tsaye tare ta jan shi suka
kama dingishi suna tafiya har suka yi dan nisa
da wajen.
Ai kuwa nan take suka yi arba da wani rami mai
zurfin gaske a gabansu. Kawai sai suka dubi
juna suka yi murmushi. Ba tare da jiran komai
ba suka durfafi wannan rami ko kallon gabansu
ba sa yi, sai kallon fuskokinsu suna yi wa juna
murmushin karshe.
Saura taku uku kacal tsakaninsu da ramin sai
kawai Imran ya ji an kwala masa kiran. Cikin
dimauta da razani ya juyo baya. Koda ya ga
wanda ya kira sunan nasa sai ya cika da
118
TASKARNOVELS.COM.NG
tsananin mamaki gami da farin ciki mara
misaltuwa. Ba wani ya hango ba face
mahaifiyarsa tana rarrafe ta tunkaro su kuma
hawaye na zuba daga idanunta.
Nan take Imran ya ruga da gudu izuwa gare ta
ya sure ta ya rungumeta a kirjinsa. Shi da ita
suka bushe da dariyar murna, ya kama
sumbatar ko ina a fuskarta yana mai cewa, Ashe
ba ki mutu ba ya Ummana, ashe ba ki mutu ba"
Mahaifiyar tasa ta rike fuskarsa da hannayenta
biyu ta ce, "Ya za a yi na mutu alhalin kana raye
a doron kasa, kuma akwai alkawari a
tsakaninmu?
Ya kai dana, kayi sani cewa na dade ina
mafarkin cewa burinmu ya cika, ina tabbatar
maka da cewa ban taɓa yin mafarki bai tabbata
ba. Lallai ina ji a jikina cewa, komai wuya, komai
rintsi sai na sami lafiya na taka kafafuna ka gani
da idanunka. Koda mahaifiyar Imran ta zo nan a
zancenta sai Imran ya sake rungume ta a
kirjinsa ya fashe da kukan farin ciki, tana mai
tayavshi kukan.
119
TASKARNOVELS.COM.NG
Jaruma Shadira da ke tsaye a can bayansu tana
kallonsu cikin tsananin murna sai ta taho gare
su ita ma ta rungume su ta taya su kukan farin
cikin.
Ba zato ba tsammani sai suka ji motsi yai yawa a
bayansu. Koda suka waigo sai suka ga ashe
sauran abokan tafiyar su ne suka farfado daga
dogon suman da suka yi daya bayan daya. Cikin
tsananin farin ciki suka karaso gare su suna
tashinsu zaune.
Nan fa aka shiga taimakon juna. Masu manyan
raunika a jikinsu aka rinka dinke musu raunin,
raunin da za a sa masa magani aka sa masa
maganin.
Zarina ce ta dinkewa Shaharan manyan raunika
guda biyu da ke jikinsa da hannunta, ita kuma
dan uwanta Sarkin Farisa ya dinke nata raunin
da kansa.
120
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da Zarina ke dinkewa Shaharan
rauninsa ne Sarkin Farisa ya lura da cewa
Zarina da Shaharan suna satar kallon juna suna
murmushi, don haka sai ya gane cewa lallai
akwai soyayya mai karfi a tsakaninsu.
A iya sanin da Sarkin Farisa ya yi wa Zarina ba
ta taɓa koda taɓa wani da namiji ba face shi,
kuma bai taɓa ganin ta yi wa wani murmushi ba
sai shi, amma yau gavshi ta damu bisa ranin da
ke jikin Shaharan har ta yi masa magani da
hannunta, kuma tana yi masa murmushi.
Koda Zarina ta ga cewa dan uwanta ya fuskanci
tana son Shaharan sai kunya ta kama ta kuma
hankalinta ya dugunzuma, domin ta karya
alkawarin da ta dauka cewa ba za ta yi aure ko
soyayya ba face ta samowa dan uwanta maganin
cutar da ke jikinsabCikin tsananin takaici da
damuwa Zarina ta mike tsaye tsam! daga gaban
jarumi Shaharan ta koma can gefe daya ta yi
tagumi a yayin da idanunta suka ciko da kwalla
tana mai bakin cikin saba alkawarin da ta yi.
121
TASKARNOVELS.COM.NG
A can gefe daya kuwa, gimbiya Rahila ce take sa
wa Sarki Laffaru magani akan raunikan da ke
jikinsa, ita kuma boka Muzaffar na sanya mata.
Shi kuma aljani Marhabul Zaurus ne yake sa
masa maganin. Abin da ya daurewa kowa kai a
wajen shi ne aljani Marhabul Zaurus ya fi kowa
samun yawan raunika a jikinsa a wannan bakin
gumurzu da aka yi a daji na uku, amma kuma
yafi kowa jure raunikan kuma da kansa ya yi wa
kansa magani.
Dokin Shaharan kuwa, shi kadai ne bai sami
rauni ko daya ba sakamakon kariyar da aljani
Marhabul Zaurus ya ba shi, ya lulluɓe shi da
dukkan fuka-fukansa, don haka duk harin da
aka kawowa dokin akan Marhabul Zaurus yake
karewa.
Lokacin da Sarkin Farisa ya ga 'yar uwarsa
Zarina ta koma can gefe daya ta zauna sai ya
dubi jarumi Shaharan ya ce, "Ya kai ma'abocin
122
TASKARNOVELS.COM.NG
gudu, ka yi sani cewa kai ne saurayi na farko da
'yar uwata ta nunawa soyayya a duniya.
A dalilin son da samari ke yi mata, da yawansu
sun hallaka bisa kamuwa da cutar begenta a
zukatansu. A tunanina, har abada babu wani
mahaluki da zai iya bai wa 'yar uwata farin ciki
face ni kaina, amma yanzu na karyata kaina
kuma na yi imani cewa kai za ka iya ba ta
dukkan farin cikin rayuwa.
Na sani cewa ka dade kana begen 'yar Sarkin
garinku a cikin zuciyarka, kuma ka baro kasarku
ne domin ka yi gasar tseren doki ta neman
auren 'yar Sakin naku.
Ina mai tabbatar maka da cewa 'yar uwata tafi
'yar Sarkinku kyau, ta fita karfin mulki da arziki.
Ina ji a jikina cewa abu ne mawuyaci na rayu a
cikin wannan tafiya tamu har burina ya cika,
wato samo mini maganin cutar da ta addabe ni
123
TASKARNOVELS.COM.NG
ta hana ni yin aure. Bisa wannan dalili daga yau
na ba ka amanar 'yar uwata.
Idan har rai ya yi halinsa ina son ka aure ta
domin ka debe mata kewa ta tunda kaivne za ka
iya ba ta farin cikin da take samu daga gare ni.
Ka sota, So na hakika, irin wanda dan uwa ke yi
wa dan uwansa, ba wai So irin wanda saurayi ke
yi wa budurwa ba.
Idan da hali ka So ta kamar yadda na ga
mahaifiyar imran ke son danta Imran." Sa'adda
sarkin Farisa ya zo nan a jawabinsa sai
tausayinsa ya kama jarumi Shaharan har
hawaye ya subuto masa nan take suka rungume
juna. Shaharan ya ce, "Ni kuwa na yi maka
alkawari lallai zan rike 'yar uwarka bisa amana
da soyayya mara misaltuwa. Koda jin haka sai
Sarkin Farisa ya kara Kankame Shaharan a
kirjinsa yana mai yi masa godiya.
124
TASKARNOVELS.COM.NG
Bayan gimbiya Rahila ta gama sa wa Sarki
Lafaru magani sai ya dube ta cikin mamaki ya
ce, "Ya ke wannan ma'abociyar kyawu da
jarumtaka, ke kuwa me ya sa kike nuna kauna
da damuwa a gare ni?" Koda jin wannan
tambaya sai Rahila ta bushe da dariya.
Al'amarin da ya bai wa Lafaru da boka Muzaffar
mamaki ke nan. Rahila ta hade fuskarta sannan
ta ce, "Shin ka manta ne cewa dukkan burina na
duniya ya ta'allaka ne akanka? Kamar ydda naka
ya ta'allaka akan auren gimbiya Ramlatul Siyam.
Dole ne na fara nuna maka kauna tun a yanzu
domin ta kowanne hali sai na aure ka sannan
burina zai cika. Ni yanzu babbar matsalata shi
ne, ba ni da tabbacin za mu isa can kogon Darul
Iksina gabadayanmu nan a raye, domin na
karaya bisa irin yanayin da muka tsinci kanmu a
ciki.
Da farko dai na san cewa gaba dayanmu nan
babu mai jarumtakata amma sai ga shi na kasa
tsinana komai a cikin wannan daji na uku da
muka shigo. Ko shakka ba na yi jarumi Imran ne
125
TASKARNOVELS.COM.NG
ya kashe tsuntsayen nan kuma bai isa ya kashe
su ba gaba daya ina kyautata zaton dai guduwa
suka yi da suka ga barnar de yake musu ta yı
yawa. Ku tuna cewa yanzu fa saura mugayen
dazuzzuka guda biyu a gabanmu kuma masifar
da ke cikinsu ta fi wacce muka wuce a baya."
Koda Lahira ta zo nan a zancenta sai jikin kowa
yai sanyi kuma hankali ya dugunzuma aka yi tsit
ana tunanin zuci. Tsawon 'yan dakiku dayansu
bai ce uffan ba.
Daga can sai sarki Laffaru ya dubi boka
Muzaffar ya ce, "Ya kai abin dogaronmu wai
shin yanzu idan muka ratsa ta cikin wadannan
dazuzzuka biyu muka wuce lafiya, ya ya batun
shiga cikin kogon Darul Iksina ya ke? Shin babu
wata matsala da za mu fuskanta a cikinsa?"
Koda boka Muzaffar ya ji wannan tambaya sai
yai ajiyar zuciya sannan ya ce, "Ni kam dukkan
ilimina ya tsaya iya nan ban san ma yadda za mu
iya shiga cikin kogon Darul lksina ba kuma ban
san irin matakan tsaron da ke cikinsa ba".
126
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan batu sai ran sarki Laffaru ya
ya dubi boka Muzaffar a fusace ya ce, "Ashe kai
wawa ne ba ka san ciwon kanka ba! Yanzu kai
da ba ka ma san yadda za mu shiga cikin kogon
Darul Iksina ba amma ka debo mu muka sha
wannan bakar wahala?"
Kafin sarki Laffaru ya gama rufe bakinsa boka
Muzaffar ya daka masa tsawa wacce ta firgita
shi ainun ya ji kamar an kaɗa hantar cikinsa.
Boka Muzaffar ya ce, "Ai kaine babban wawa
wanda rashin hangen nesansa ya jefa shi a cikin
bala'i.
Ai wanda yake cikin ruwa ko bakin takobi masa
kamawa zai yi. Shin ka manta da bala'in da kake
ciki ne na abokiyar gabarka Sharlis? Ai da ka
zauna ka jira ranar da ɗanta zai girma ya yi
maka gisan gilla ya haye kan mulkinka da
dukiyarka gwara ka taho neman maganin
wannan barna koda kuwa ba za ka samu ba. Ka
127
TASKARNOVELS.COM.NG
tuna cewa rai ba a bakin komai yake ba muddin
akwai biyan bukata. Sai da Sharlisa ta sai da
rayuwarta ta sha bakar wahala tun tana yarinya
karama har ta girma sannan ta sami nasarar
hawa kan tafarkin daukar fansa a kanka. Saboda
me kai yanzu ba za ka sallama rayuwarka ba
don ganin ka kubuta daga sharrinta?
Gabadayan abokan tafiyar nan tamu sun
sallama rayuwarsu ne don cika burin
zuciyoyinsu, ga shi har daya daga cikinsu ta rasa
dan uwanta, dukkan burinta ya rushe, amma
duk da haka ba ta fasa ci gaba da yin wannan
tafiya ba. Ai ko ba komai mun ajiye abin tarihi
wanda babu wani mahaluki da ya
taba yinsa, koda kuwa a iya nan tafiyarmu ta
yanke. Lokacin da boka Muzaffar ya zo nan a
jawabinsa sai sarki Laffaru ya shiga taitayinsa
har ya bai wa Laffaru hakuri. Al'amarin da ya
janyo jikin kowa ya yi sanyi ke nan.
Boka Laffaru ya ce, "Ya zama wajibi mu zauna
anan har tsawon mako biyu domin mu yi jinyar
128
TASKARNOVELS.COM.NG
jikinmu sosai kafin mu shiga daji na biyar
saboda idan muka yi gangancin ci gaba da tafiya
a haka, cikin kankanin lokaci mu duka zamu
hallaka". Nan take kowa ya aminta da wannan
shawara ta boka Muzaffar. Ba tare da ɓata lokaci
ba suka kafa tantuna sannan aka ci abinci.
Bayan kowa ya huta sai suka shiga janye
gawarwakin wadannan tsuntsaye suna jefa su a
cikin ramin nan mai zurfi don kada su dame su
da doyi, kuma kananan tsuntsaye masu cin
mushe su adabbe su a wajen.
Suna gama watsa tsuntsayen a cikin ramin sai
suka kunna wuta suka jefa a cikin ramin. Nan
take gaba dayan gawar tsuntsayen ta kama ci da
wuta.
Haka dai su Imran suka ci gaba da zama a cikin
wannan daji suna jinyar kansu har tsawon mako
biyu amam kullum a tsorace suke domin gani
129
TASKARNOVELS.COM.NG
suke kamar ko yaushe ragowar wadannan
tsuntsayen za su iya
kawo musu MAMAYAR BAZATO.
Ai kuwa tsuntsayen sun sha zuwa su yi shawagi
a samansu amma wani Iko na Allah ko sau daya
tsuntsayen ba su yi yunkurin kai musu hari ba.
Daga karshe ma sai tsuntsayen suka ɓace ɓat
tamkar ba su taɓa wanzuwa ba a dajin.
A ranar da kwanaki goma sha hudu suka cika ne
kowa ya ji ya sami karfin jikinsa sai dai tabon
raunika kawai a jikinsu. Nan fa suka yi shiri
kowa ya kimtsa sannan aljani Marhabul Zaurus
su duka ya tashi da su sama aka ci gaba da taifya
suka durfafi daji na hudu wanda ke dauke da
muggan dabbobin daji iri-iri masu matukar
hadari
Da isowarsu farkon dajin sai aljani Marhabul
Zaurus ya saki fuka-fukansa ya sauko kas ya
tsaya cak bai motsa ba. Kowa sai ya noke ya ki
130
TASKARNOVELS.COM.NG
saukowa daga kan aljani Marabul Zaurus aka
kama kallon- kallo.
Al'amarin da ya sa boka Muzaffar ya bushe da
dariya ke nan ya ce, "Me kuke tsoro kowa ya
kasa sauka kasa? Ba a sami wanda ya iya amsa
masa wannan tambaya ba. Koda ganin haka sai
boka Muzaffar ya sauka kas sannan ya dubi
gimbiya zarina ya ce, "Gaishe ki ya mai ilimin
daji ki yi sani cewa yau ne ranarki domin muna
bakin daji na huďu da ke dauke da mugayen
dabbobi. Ke kaɗai ce za ki iya kuбutar damu a
cikin wannan daji don haka sai ki sauko ki yi
mana jagora har mu isa karshen dajin".
Koda jin wannan batu sai Zarina ta yunkura za
ta sauko kas. Cikin hanzari sarkin Farisa ya ruko
ta dube ta cikin alamun firgici da tashin hankali
a lokacin da idanunsa suka ciko da kwallah ya
ce, "Ya ke 'yar uwata ki yi sani cewa a halin
yanzu zuciyata tana bugawa da karfi kuma ina ji
a jikina cewa in dai muka shiga cikin wannan
daji karshen zamanmu tare ya zo. Ni kam na
hakura da wannan buri da ke gabanmu saboda
131
TASKARNOVELS.COM.NG
haka mu yanke wannan tafiya tamu daga nan
mu zauna anan mu jira mu ga abin da hali zai yi
ko abokan tafiya za su isa can kogon Darul
Iksina su dawo lafiya. Idan kuma ba su dawo ba
sai mu juya da baya mu koma kasarmu. Gwara
mu koma gida mu ci gaba da rayuwarmu a cikin
mulkinmu muna
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 18