Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ke wannan 'yar Sarki ki yi sani cewa yanzu ne zamu tunkari masifar da tafi duk wacce ta same mu a baya don haka zan iya rasa rayuwata ku ma za ku iya rasa taku. Kafin mu je zan yi miki tambaya ta karshe ina so ki fada mini iyakar gaskiyarki, Shin idan na gama biya muku bukatarku za ku cika alkawarinki a gare ni? Shin da gaske ne za ki kai ni inda kika boye wasikar masoyiyata?" Lokacin da Rahila ta ji wadannan tambayoyi sai idanunta suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo mata sannan ta ce, "Na rantse da darajar gemun mahaifina zan zamo mai cika alkawari a gare ka kuma lallai zan kai ka inda wasiyyar masoyiyarka Rashmin take." 396 TASKARNOVELS.COM.NG Da jin haka sai farin ciki ya lulluɓe Aljani Maruful Dauwaz ya mayar da su Rahila izuwa kan kafadarsa sannan ya fito daga cikin sakon da suka buya ya ci gaba da tafiya yana neman ɓangaren da gidan Gimbiya Ramlatul Siyam yake. Duk inda yake wucewa Dakaru ne tsibi-tsibi, da zarar ya ga ana kallonsa sai hankalinsa ya tashi don gudun kada a gano cewa shi ba Hadimin gidan ba ne. ***** Al'amarin sadauki Najwar kuwa, lokacin da ya bace daga fadar Sarki Nashmir bai bayyana a ko ina ba sai kofar gidan Gimbiya Ramlatul Siyam. 397 TASKARNOVELS.COM.NG Koda masu gadin gidan suka gan shi sai suka bude masa kofar gidan da sauri ya kunna kai ciki. Najwar bai isa inda turakar Gimbiya take ba sai bayan ya yi tafiyar rabin sa'a. Ya so ace ya isa turakar da wuri ta hanyar amfani da karfin sihirinsa amma da yake sihirin tsafi ba ya tasiri a gidan Gimbiya Ramlatul Siyam dole ya hakura ya yi wannan doguwar tafiya. Shi kansa ya san cewa bai isa ya je ya dauko Gimbiya ba da karfin sihiri ko da karfin dantse, sai dai idan Gimbiyar ce da kanta ta amince ta biyo shi. Ko ina a cikin gidan Dakaru ne na tsaro, manyamanyan sadaukan aljanu da bil'dama masu yawan gaske, yadda komai jarumtakar mutum ko aljan idan suka yi masa rubdugu dole ne suami nasara a kansa. Lokacin da Najwar ya iso tsakiyar turakar Gimbiya Ramlatul Siyam sai aka tsayar da shi 398 TASKARNOVELS.COM.NG anan domin anan ne iyakarsa bai isa ya matsa gaba ba. Babu wanda yake wuce wannan wuri ya isa har cikin turakar Gimbiya face Sarki Nashmir da kansa. Koda aka tsaida Najwar sai kuwa ya tsaya cak batare da wata gardama ba sannan ya ce, aje a gaya wa Gimbiya cewa Sárki ne ya ba shi sako ya kawo mata. Nan da nan aka je aka sanar da ita. Sai ta ce a komo a gaya masa cewar ya bayar da sakon a kai mata. Ya yin da Najwar ya ji haka sai ya ce aje a gaya mata cewa sako ne na sirri kuma Sarki ya ce lallai kada kowa ya ji wannan sako. Koda Gimbiya ta ji haka sai ta mike zumbur! 399 TASKARNOVELS.COM.NG Cikin tashin hankali ta taho izuwa inda Najwar yake. Tana isowa kuwa ta iske Najwar a tsaye yana tsumayenta. A wannan lokaci Gimbiya ta tsala ado na gaban kwatance har kyawunta ya ninka na kullum. Koda Najwar ya ga Gimbiya a cikin wannan ado ai ya rude ya dimauce, bai san sa'adda ya kama dalalar da yawu daga bakinsa ba (Ka ji maye). Ita kanta Gimbiya sai da ta gane halin da ya shiga har ta kyalkyale da dariya. Daga can sai ta hade fuska ta dubi gaba dayan Dakarun da hadiman da ke falon ta ce su kauce su ba su wuri. Nan take kuwa aka watse aka bar su su biyu rak. A sannan ne ta yi masa nuni da wata kujera ya zauna, ita ma sai ta zauna bisa wata luntsumemiyar kujera da ke fuskantar tasa. 400 TASKARNOVELS.COM.NG Ta dube shi cikin wani irin murmushi mai taushi wanda ya sake dimauta shi sannan ta ce, Ya kai Sarkin yaki ina mai sanar da kai cewa fiye da hekaru goma baya na sani cewa kana matukar so na kuma kana begena dare da rana. Kai kuwa kan wanne dalili ka dorawa kanka jarabar sona alhalin ka san cewa wutsiyar Rakumi ta yi nesa da kasa?" Koda jin wannan batu sai hankalin Najwar ya gunzuma ya cika da tsananin mamaki ya dubi Gimbiya a firgice ya ce, "Ke kuwa ya a ka yi kika san wannan al'amari alhalin ban taɓa nuna miki so ba kuma ban taɓa furtawa wani ba?" Sa'adda Ramlatul Siyam ta ji wannan tambaya sai ta bushe da dariya sannan ta ce, mahaifina ne ya sanar da ni hakan. Ina tabbatar maka da cewa ya san duk halin da kake ciki kuma ya sanar da ni akan na yi hankali da kai. 401 TASKARNOVELS.COM.NG Yanzu wane sako ne tafe da kai, kuma yaya aka yi ka sami wannan sako daga mahaifina alhalin sa'adda ya bar gida kai ma ba ka nan ya tura ka yaki?" Koda jin wannan tambaya sai hankalin Najwar ya kara dugunzuma domin ya san cewa ba shi da wata gamsasshiyar amsa wacce zai iya kare kansa. Can kawai sai ya bushe da dariya ya "Babu wani sako daga mahaifinki, yanzu na zo ne na fitar da ke daga cikin gidan nan naki domin naj na aureki da karfin tsiya kuma a daren yau zan yi wa mahaifinki juyin mulki na hau kan karagarsa. Koda jin wannan batu sai Gimbiya Ramlatul Siyam ta bushe da dariya, ta yi ta dariyar kamar za ta daina ba. Daga can kuma sai ta murtuke fuska ta ce, Kifi na ganinka mai Jar Koma! Ka yi ban kuskure da kake tunanin za ka iya fitar da ni 402 TASKARNOVELS.COM.NG daga cikin wannan gida nawa. Ina tabbatar maka da cewa, koda babu wadannan miliyoyin Dakaru da ke kare ni ,ni kadai na ishe ka, domin Barewa ba ta gudu danta ya yi rarrafe ba, Idan kuma kana shakka jarraba ka gani.........." Kafin Ramlatul Siyam ta gama rufe bakinta tuni sadauki Najwar ya tunkaro ta kai tsaye. Ita uwa ko gezau ba ta yi ba har ya iso gare ta. Koda ya kai mata cafka da hannunsa sai ta goce ya cafki iska. Kafin ya yi wani yunkuri ta tama hannun nasa ta murde, kuma ta sa kafarta guda ta do ki bayansa, Saboda karfin dukan sai da ya yi sama ya gwara fuskarsa a jikin bango sannan ya fado kasa. Najwar ya mike tsaye zumbur cikin tsananin mamaki! Kawai sai ya ji danshi akan hancinsa da bakinsa, yana shafarsu sai ya ga jini. Al'amarin da ya matukar fusatashi ke nan ya 403 TASKARNOVELS.COM.NG gyara tsayuwarsa yana mai dunkule hannayensa. Koda ganin hakan sai ita ma Ramlatul Siyam ta mike tsaye ta gyara tata tsayuwar gami da dunkule hannunta ta ce, "Yau zan nuna maka cewa, na sha Jarumtaka a nonon uwata, kuma na gaji SADAUKANTAKA a jinin mahaifina. Kafin Najwar ya ce wani abu tuni Ramlatul Siyam ta dako wawan tsalle ta dira a gabansa. Nan take suka ruguntsume da azababben yaki, suka rinka kai wa juna SARA DA SUKA cikin tsananin zafin nama, juriya, naci da jarumtaka. Karar haduwar takubbansu da ihunsu ne ya sa Dakarun tsaron Gimbiya suka rugo izuwa cikin turakar da suke fafatawa. Koda suka ga ana tafka matsanaicin yaki tsakanin Gimbiya da Najwar sai suka yunkura 404 TASKARNOVELS.COM.NG za su kai wa Gimbiya Ramlatul Siyam dauki, sai ta daka musu tsawa ta hanacsu. Bisa dole suka tsaya suka yi cirko-cirko suka zama 'yan kallo. AL'AMARIN su Aljani Maruful Dauwaz kuwa, sai da suka daɗe suna yawo da bilinbituwa a cikin gidan sarautar sannan suka hango gidan Gimbiya Ramlatul Siyam. Tun daga nesa suka fahimci cewar ba lafiya ba, domin Dakarun aljanun da ke shawagi a saman gidan sun yi kaimi a wajen kewaya gidan kamar za su afka cikin gidan. Haka ya sa su ma dakarun bil'adaman da ke zagaye da gidan suka kasance. Kash! Rashin sani ya fi dare duhu! Aljani Maruful Dauwaz bai san cewa sihirin tsafi ba ya 405 TASKARNOVELS.COM.NG tasiri a wajen dakarun da ke tsaron gidan Gimbiya Ramlatul Siyam ba, saboda haka lokacin da ya durfafi gidan a cikin siffarsa ta ainahi, wato ta Aljani, ai kuwa sai suka yi caa! A kansa suka kawo masa miyagun hare-hare masu gaggawar tsinke numfashi. In ba don Maruful Dauwaz yana da tsananin bakin zafin nama ba da tuni sun daddatsa shi gunduwa-gunduwa. Cikin tsananin zafin nama ya daka tsalle ya bar inda yake, makaman Dakarun suka karci kasa, kasar wajen ta daddare. Nan fa Aljani Maruful Dauwaz ya zare takobinsa ya fada cikin miliyoyin Dakarun aka ruguntsume da azababben matsanaicin yaki. Ita ma Rahila sai ta zare takobinta ta taya Aljani Maruful Dauwaz yakin, amma da ta ga yakin ya fi karfinta, wato yawan Dakarun ya wuce misali, kuma sihirin tsafi ba ya tasiri a kansu ba ta isa 406 TASKARNOVELS.COM.NG ta ci gaba da yakar Dakarun ba sai ta yi wuf ta suri Sarki Laffaru suka daka tsalle suka shige cikin kunnen Aljani Maruful Dauwaz suka yi lamo kamar babu su a wajen. Shi kuwa Aljani Maruful Dauwaz sai ya zama kamar shaidani a tsakiyar Dakarun. In yai sama sai Dakarun aljanu su yanyame shi ya kasa tsinana komai. Idan ya sako kasa kuwa sai Dakarun bil'adama su yi masa rubdugu. Nan fa hankalinsa ya dugunzuma ainun musamman da ya fahimci cewar wadannan Dakarun yaki masu tsaron Gimbiya Ramlatul Siyam sun sami horon yaki na musamman kuma su sihirin tsafinsu yana tasiri, amma duk wanda ya zo gare su nasa sihirin tsafin ba zai yi tasiri a kansu ba. Aljani Maruful Dauwaz ya ji ya yi nadama matuka da ya kawo kansa wannan wuri domin bai ga ta yadda zai iya guduwa ba bare ya iya ci 407 TASKARNOVELS.COM.NG gaba da yakin har ya sami nasarar hallakar da Dakarun ya shiga cikin gidan Gimbiya Ramlatul Siyam. Ko shakka ba ya yi idan aka ci gaba da wannan bakin gumurzu a haka har izuwa wani lokaci mai dan tsawo tabbas zai gaji, kuma da zarar ya gajin za a sami nasarar hallaka shi. Koda Maruful Dauwaz ya zo nan a zancen zucinsa sai ya tuno da Rahila da Sarki Laffaru da ke kan kafadarsa. Bisa mamaki sai ya ji ko motsinsu ba ya ji akansa. Al'amarin da ya kara dugunzuma hankalinsa ke nan, ya zata ko tun sa'adda aka fara wannan gumurzu suka faɗo kasa daga kansa aka mutsittsike su. Nan fa ya raba hankalinsa biyu, wato ya ci gaba da yakin kuma yana dira a kasa yana dube-dube ko zai ga su Rahila, saboda idan har tabbatar da cewa an kashe su bai ga amfanin wannan yaki da yake yi ba tunda da ma saboda su yake yakin domin idan anyi nasara su cika masa alkawarin da ke tsakaninsu. 408 TASKARNOVELS.COM.NG Koda ya fara hakan sai Dakarun na sama da na kasa suka sake yi masa rubdugu suka rinka kai masa SARA DA SUKA gami da naushi da bugu ta ko ina. Kaico! Idan aka yanka Kazar wuya to ba makawa sai an fige ta. Lokacin da Dakarun suka kara ZAGE DANTSE akan Aljani Maruful Dauwaz sai ya zamana cewa da kyar yake iya kare sara da sukan da suke kawo masa, sai dai yana iya kare naushi da bugu, su ma ba duka ba, domin akwai lokacin da wani basamuden Aljani ya gabza masa wawan naushi a baki. Ta ke hakorinsa guda yai fitar burgu tare da wani gudan jini. Nan take Aljani Maruful Dauwaz ya ga taurarin wuya a idanunsa ya fara gani dishi-dishi, ya shiga cikin wani irin mugun hali mai kama da fitar haiyaci. A sannan ne wani katon jarumin Aljani mai nacin tsiya ya sami nasarar dankara masa sara a 409 TASKARNOVELS.COM.NG gadon bayansa. Take gadon bayan ya dare, Aljani Maruful Dauwaz ya kwarara uban ihu yai katantanwa a sama har sau uku ya rikito kasa ya baje a bisa turba cikin halin suma. A daidai wannan lokaci ne Rahila da Sarki Laffaru suka gangaro daga cikin kunnensa za su fado kasa, sai Rahila tayi wuf ta kamo jelar wani Aljani ta wurkila sama sau biyar kuma ta cafo Sarki Laffaru da hannu daya ta dada jefa shi a cikin kunnen Aljani Maruful Dauwaz ya kule a ciki. Ita kuma sai ta ci gaba da yakar Dakarun aljanun na sama da na kasa tana shawagi akan Maruful Dauwaz tana hana sauran Dakarun samun nasarar karasa kashe Maruful Dauwaz. Rahila tana wannan yaki ne da dukkan karfinta cikin tsananin fusata domin ta san cewa idan ta bari aka hallaka Aljani Maruful Dauwaz, to fa 410 TASKARNOVELS.COM.NG komai ya dagule domin dayansu ba zai tsira da rayuwarsa ba, kuma dukkan burinsu ya rushe. Ita kanta Rahila ta yi matukar mamakin irin wannan bajinta da take yi a cikin miliyoyin Dakarun na aljanu da mutané. To amma fa ta san cewa karshen tikatiki, tik! A kodayaushe komai zai iya faruwa a gare ta tunda dai ta kasa koda kashe Badakkare daya daga cikin Dakarun. kuma ga shi Dakarun ba sa gajiya kamar ma kara samun karfi da kuzari suke. Ai kuwa ana dada kara samun wani dan lokaci sai ita ma Rahila ta fara gajiya, Dakarun bil'adaman da ke kasa suka fara yin tamaula da ita. Kafin a jima sun kumbura ma ta fuska kuma sun hada ma ta jini da majina., in ba don ma tana da tsananin karfin dantse ba da matukar juriya da tuni sun daddatsa ta gunduwa-gunduwa. 411 TASKARNOVELS.COM.NG Ai kuwa ba ta ankara ba sai ji ta yi an dankara mata sara sau uku a lokaci guda. Saran farko a bayan kafarta ta hagu. Na biyu a kafadarta ta dama. Na ukun kuwa a gefen cikinta. Ko ina sai da jini yai feshi. Rahila ta kurma uban ihu ta fadi kasa rikica ko shurawa ba ta yi ba. A daidai fuskar Aljani Maruful dauwaz ta fado. Iskar da ta haifar ce ta sa Maruful Dauwaz ya farfado daga dogon suman da ya yi. Yana bude idanunsa ya yi arba da Rahila kwance a gabansa kamar gawa. A daidai wannan lokaci ne Dakaru suka sake tasowa za su afkawa Maruful Dauwaz su yi gutsin-gutsin da sassan jikinsa. Cikin bakin zafin nama mara misaltuwa Maruful Dauwaz yai wuf! ya sure Rahila ya jefa ta cikin kunnenesa ta kule a ciki tamkar an jefe guga cikin rijiya, sannan ya daka wawan tsalle a ya ci gaba da saran Dakarun yana naushi da bugunsu duk a lokaci guda, kuma yana kwarara ihu mai tsananin firgitarwa. 412 TASKARNOVELS.COM.NG Tsananin karfin ihun nasa ne ya sa Dakarun suka fara firgita, bisa dole suka rinka buďa masa hanya yana durfafar kofar gidan. Babu abin da zai bai wa mutum mamaki face yadda Maruful Dauwaz ke wannan yaki cikin tsananin fushi, juriya da naci duk da cewar jini na zuba a gadon bayansa, kuma jiri na dibarsa. Kokarinsa shi ne ya dangana da jikin kofar gidan ya ɓalla ta da karfin tsiya. Koda Dakarun suka gane nufin Maruful Dauwaz sai su ma suka kara zage dantse suna kara yi masa rubdugu amma sai suka kasa kai shi kasa domin fatali yake yi da su da karfin tsiya yana yin gaba. Su kansu Dakarun sun yi matukar mamaki domin ba su taɓa ganin sadauki mai bakin naci irin nasa ba, domin dan karamin yanka ko sara ma baya sa shi ya je kas, sai dai kawai ka ji yana ihu sakamakon zafi da zogin da yake ji. 413 TASKARNOVELS.COM.NG (SANNU MAURUFUL DAUWAZ,NSADAUKIN SADAUKAI BABBAN MASOYI GA MARIGAYIYA RASHMIN) ************ A can cikin turakar Gimbiya Ramlatul Siyam kuwa, fadan da ake yi tsakanin sadauki Najwar da Gimbiya Ramlatul Siyam ya yi tsamari ainun, domin kowannensu ya gane kurensa. Duk da cewar sun kasa koda lakutar jikin juna amma kowanensu ya gabzawa kowa naushi da bugu. Najwar ya yi matukar mamakin yadda aka yi Ramlatul Siyam ta kasance gagarumar jaruma Amma da ya tuna sadaukantakar mahaifiyarta sai ya daina mamaki. Lokacin da suka shafe sa'a uku suna kwarmazuwa babu wanda ya sami nasarar kai wani kasa sai duk suka ja da baya bisa dole suka tsaya suna haki kamar Zakaru. A sannan ne wadannan Dakaru da suka shigo turakar suka 414 TASKARNOVELS.COM.NG sake yunkurawa za su afkawa Najwar amma sai Ramlatul Siyam ta sake hana su suka ja da baya. Koda ganin haka sai sadauki Najwar ya bushe da dariya sannan ya maida takobinsa cikin kufe sannan ya gyara tsayuwarsa yana mai dunkule hannayensa biyu ya ce, "Tunda dai mun kasa cutar da juna da makami ai sai mu fid da raini da karfin dantse kawai". Koda jin wannan batu sai jikin Ramlatul Siyam ya yi sanyi kamar ba za ta amince ba. Daga can kuma sai ta kwalla ihu ta rugo gare shi suka kacame da sabon masifaffen yaki. Tabbas Ramlatul Siyam ta yi ganganci domin kwarewarta da sanin makama ba ta kai rabin ta Najwar ba tunda shi ya saba da karo da mazaje iri-iri hatta mahaifin nata ma da kyar yake samunnasara a kansa bare ita da jarumtakar ta ma ba ta kai ta mahaifin na ta ba. 415 TASKARNOVELS.COM.NG Koda suka fara kai wa juna naushi da bugu sai Najwar yai wuf ya kama hannayen Ramlatul Siyam ya murde su izuwa bayanta ya daure hannayen da wata igiyar tsafi cikin zafin nama sannan yai sauri ya dora wata wuka akan wuyanta ya dakawa Dakarun da ke cikin turakar tsawa ya ce, Su dare su ba shi hanya ko kuma ya yanka ta! Ba shiri Dakarun suka dare suka ba shi hanya ya nufi kofar fita yana waige-waige da kallon Dakarun don kada wani daga cikinsu ya shammacecshi, yana mai ingiza Ramlatul Siyam yana kuma daɗa rike hannayenta da karfi yana harde kafafunta don kada ita ma ta shammacecshi da kafar tata. Koda suka iso daf da kofar fita sai kawai suka ga an doko kofar da karfin tsiya. Take kofar ta fado ciki ta fadi kasa rikica, sai ga Aljani Maruful Dauwaz ya baiyana dauke da jaruma Rahila. Shi da Rahilan duk jikinsu ya yi kaca-kaca da jini har suna layi kamar za su fadi kasa. 416 TASKARNOVELS.COM.NG Koda Najwar ya yi arba da su sai ya cika da tsananin mamaki domin bai taɓa ganin mahalukin da aka kulle a cikin wannan kurkuku har ya samu damar fita sai su. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin Sadauki Najwar da kuma Aljani Maruful Dauwaz. Daga can sai Najwar ya tuntsure da dariya ya dubi Maruful Dauwaz ya ce, "Ku ba ni hanya na wuce ko kuma na sa a karasa hallaka ku. Kun san dai na fi karfinku tunda na kara da ku kun gani." Koda jin wannan batu sai Rahila ta dakawa Najwar tsawa ta ce, "Ai tsakaninmu da kai yanzu babu yarda ko bin umarni tunda mun gane cewa kai mayaudari ne kuma maci amana. Tunda har ka ci amanar Sarkinka to babu wanda ba za ka ci amanarsa ba. Ka sani cewa mun baro kasashenmu da komai namu domin mu mallaki Gimbiya Ramlatul 417 TASKARNOVELS.COM.NG Siyam, kuma mun sha bakar wahala har mun kusa rasa rayuwarmu. Babu irin bala'in da ba mu haɗu da shi ba bisa wannan TAFARKI. Shin kana zaton cewa akwai wani abu da zai iya firgita a yanzu? Bama kai ba, ko Sarkinka ne muka yi fito-na-fito da shi a wannan lokaci ba za mu gudu ba bare mu janye bisa abin da ke gabanmu. Kawai ka ba mu Gimbiya Ramlatul Siyam idan ba haka ba kuwa sai dai mu ci gaba da yaki mai rabo ka dauka." Gama fadin hakan ke da wuya sai suka ga an watso Dakaru daga cikin turakar sun baje a kasa matattu kimanin su dubi dari da doriya, sannan kuma suka ji an ci gaba da mummunan yaki a can wajen gidan. Ihun mazaje da karar haduwar makamai sun cika dodon kunne. 418 TASKARNOVELS.COM.NG Ashe zuri'ar su Aljani Barukul Masnur ne suka kawo wa sadauki Najwar dauki domin sun gaji da zaman jiransa a can fada. Wohoho! Nan fa gidan Gimbiya Ramlatul Siyam ya daďa hargitsewa, cikinsa da wajensa aka ci gaba da azababben yaki. Maruful Dauwaz da Rahila suka afkawa Najwar suna kokarin kwatar Gimbiya Ramlatul Siyam daga hannunsa, amma sai suka kasa. Su Aljani Barukul Masnur kuwa, sai suka rabu zuwa kaso biyu, kaso daya suka tari Dakarun da ke kofar gidan Gimbiya, kaso daya kuma suka tari Dakarun da ke ciki aka ci gaba da BAKIN ARTABU. Nan fa aka rinka ragargaza maza, kasuwar cinikin daukar rayuka ta baje kolinta. Sassan jiki na aljan da na bil'adama ya dinga yawo a sararin samaniya. 419 TASKARNOVELS.COM.NG Jini kuwa ya rinka feshi da fantsama ya wanke gaba dayan ginin gidan ciki da waje kai kace sabon shafe aka yi da shi. Sai da Najwar ya sumar da Maruful Dauwaz da Rahila sau bakwai-bakwai, amma saboda naci da zarar sun farfado sai ka ga sun tashi an ci gaba da yaki da su. Babu yadda Najwar bai yi ba akan ya fice da Gimbiya daga cikin wannan gida nata amma abu ya gagara domin koda ya bazar da su Maruful Dauwaz sun zube kasa sumammu da ya tunkari bakin kofar fita sai ka ga Dakarun da ke tsaronta sun sake yi masa rubdugu sun hana shi sakat. Hakika a wannan lokaci sai da Rahila da Maruful Dauwaz suka gane kurensu kuma suka jiyo kamshin mutuwa. Duk su biyun babu wanda bai sami raunika a jikinsa ba sana da guda arba'in. 420 TASKARNOVELS.COM.NG Lokacin da su Merful Dauwaz suka yi suma na bakwai ne, Najwar ya zare wadansu gajerun wukake biyu daga jikinsa da nufin ya fafe cikinsu Maruful Dauwaz. Koda Gimbiya Ramlatul Siyam ta ga abin da te shirin faruwa sai ta daga kafarta ta gaban fuskarta ta doki fuskar Najwar. Cikin gigicewa yai tsalle sama da baya. Kafin ya duro kasa sai ita ma ta daka tsalle sama ta tare shi ta zare wata wukar a jikinta ta soka masa ita a makoshinsa. Najwar ya kurma uban ihu a lokacin da jini yai tsartuwa daga cikin makoshinsa, suka rikito kasa tare. Najwar ya baje a kasa yana kakarin mutuwa. A dai-dai wannan lokaci ne Dakarun da ke tsaron Gimbiya suka gama kashe gaba dayan zuri'ar su Aljani Barukul Masnur. Sai ga shi babban cikin Dakarun gidan ya shigo rike da kan Aljani Barukul Masnur a hannunsa jini na 421 TASKARNOVELS.COM.NG ďiga a jikin kan, yai nuni da kan izuwa ga Gimbiya Ramlatul Siyam kuma ya risina ya ce, "Ya shugabata mun gama da dukkan maciya amanar mahaifinki". Gimbiya Ramlatul Siyam ta yi murmushi ta ce, Ni ma na gama da shugabansu ga shi a kwance zai mutu". Ramlatul Siyam ta yi nuni da sadauki Najwar wanda ke kwance a kas male-male a cikin jini har a sannan bai daina kakarin mutuwa ba. Ramlatul Siyam ta tofa wa Najwar yawu a fuska ta ce, "Wannan shi ne sakamakon maci amana irinka!" A dai-dai waunan lokacie Rahila da Aljani Maruful Dauwaz suka furtado suna numfashi sama-sama kuma suna gani dishi-dishi. Koda 422 TASKARNOVELS.COM.NG ganin haka sai shugaban Dakarun gidan ya yunkura zai karasa kashe su Maruful Dauwaz amma sai Ramlatul Siyam ta daka masa tswa ya dakata. Shugaban Dakarun ya dubi Ramlatul Siyam cikin tsananin mamaki ya ce, "Haba ya shugabata, saboda me za ki hana ni hallaka su alhalin sun kasance manyan abokan gaba waɗanda suka zo domin su sace ki su raba ki da mahaifinki kuma su raba ki da wannan daula da kike ciki wacce babu inda za ki sami irinta a wannan duniya?" Sa'adda shugaban Dakarun ya zo nan a zancensa sai ya ga Gimbiya Ramlatul Siyam ta sunkui da kanta kas ta yi shiru. Nan take idanunta suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo mata sannan ta dago da kanta ta ce, "Ai tuni na rabu da mahaifina domin ba zai taɓa dawowa ba, tun ranar da ya bar gida na san cewa mun yi bankwanan karshe ba za mu sake saduwa ba har abada. 423 TASKARNOVELS.COM.NG Hakika lokaci ya yi da zan bar ku domin na je na fuskanci rayuwata ta gaba domin ita ce kaddarata, tabbataccen al'amarin da ba zai shafu ba. Daga yau gabadayan Hadiman da ke cikin Wannan gida kun sami 'yancin kanku, kowannenku yana da damar tafiya inda yake so a cikin wannan duniya domin ya fara sabuwar rayuwa. tabbas wannan masarauta sai dai a tuna da ita a tarihi amma ta ruguje ke nan. Idan kun so za ku iya nada sabon Sarki daga cikinku wanda zai ci gaba da jagorantarku". Koda gama fadin haka sai Ramlatul Siyam ta sa aka shiga yi wa Rahila da Aljani Maruful Dauwaz magani domin a ceto rayuwarsu. A daidai wannan lokaci ne Sarki Laffaru ya fito daga cikin kunnen Aljani Maruful Dauwaz. Koda yai arba da miliyoyin gawarwakin da ke cikin 424 TASKARNOVELS.COM.NG falon kuma ya ga Gimbiya Ramlatul Siyam tsaye a gabansa ga su Maruful Dauwaz a kwance ikin mugun yanayi mai kama da suma ko Imutuwa sai ya firgita ainun ya yunkura zai koma cikin kunnen Aljani Maruful Dauwaz. Caraf! Sai Gimbiya Ramlatul Siyam ta cafo hannunsa tana mai yi masa murmushi ta ce, "Haba ya kai mijina na gobe tsoron me kuma za ka ji alhalin komai ya zo karshe, burinka na daf da cika". Koda jin wannan batu sai Sarki Laffaru ya yanke jiki ya gangaro daga kan Aljani Maruful Dauwaz a sume saboda tsananin mamaki da farin ciki. Bai farfado ba sai bayan sa'a uku. ( yasin Laffaru ya cika ďan sa'a) Yana farfaɗowa ya ga Aljani Maruful Dauwaz zaune daf da shi yana ta faman shara kuka.Ba komai ne ya sa Maruful Dauwaz yin wannan kuka ba face ganin Rahila a cikin mugun yanayi 425 TASKARNOVELS.COM.NG saboda Likitoci sun taru a kanta suna iya yinsu amma har a sannan tana numfashi sama- sama. Su kansu Likitocin guiwoyinsu sun yi sanyi sun sallama cewar abu ne mawuyaci ta yi nisan kwana ko kuwa ta rayu. Maruful Dauwaz ya ci gaba da rusa kuka kamar ba zai daina ba saboda ya san cewa idan Rahila ta mutu shi ke nan ba zai ga wasiyyar masoyiyarsa ba marigayiya Gimbiya Rashmin. Babban abin bakin cikin ma shi ne, Rahila ba ta iya koda bude bakinta ma bare ta yi magana ta gaya masa inda ta ɓoye wannan wasiyya ta masoyiyarsa Bayan Maruful Dauwaz ya dade yana kuka, sai Gimbiya Ramlatul Siyam da Sarki Laffaru suka kamu da tsananin tausayinsa suka shiga rarrashinsa har Ramlatul Siyam ta kwantar masa da hankali. tana cewa, ya yi hakuri babu mamaki nan da wani lokaci ta iya bude bakinta har ta yi magana". 426 TASKARNOVELS.COM.NG Cikin alamun karayar zuci Aljani Maruful Dauwaz ya share hawayen idanunsa ya dubi Gimbiya Ramlatul Siyam ya ce, "Ya ke wannan yar Sarki, ki yi sani cewa ni kam na cire rai da rayuwar Rahila, don haka rayuwata ba ta da wani sauran amfani a doron kasa.Ki sani cewa na yi matukar mamaki da kika hana a kashe mu. Shin za ki iya gaya mana dalilin da yasa kika hana a kashe mu har kika sa aka ceto rayuwarmu? Wannan ita ce kadai alfarmar da nake nema a wajenki kafin na yi sallama da wannan duniya". Lokacin da Gimbiya Ramlatul Siyam ta ji wannan tambaya daga bakin Aljani Maruful Dauwaz sai hawaye ya zubo ma ta ta ce, "Ya kai Sarkin sadaukan aljanu, ka yi sani cewa ni a rayuwata tun ina yarinya karama duk abin da zai same ni sai an nuna min shi a mafarkina. 427 TASKARNOVELS.COM.NG Kuma duk mafarkin da na yi sai ya tabbata a gaske. Fiye da shekaru biyar baya da suka shude na gani a cikin mafarkina cewar Daular Mulkin Mahaifina za ta rushe kuma zai bar gida don tafiya neman wani mashi da ake kira Galilu Harus. Idan ya tafi neman wannan mashi ba zai dawo ba, a can zai mutu wajen fafatawa da wanda ke rike da mashin. Ba

Chapter 15 of 18