Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tsaye da 74 TASKARNOVELS.COM.NG kyar ya zo kan yaro Masnur ya daga hannunsa guda sannan ya kara hancinsa a dai-dai nasa ya ji babu alamar numfashi, ya dora kunnensa a kirjin Masnur, nan ma ya ji babu alamar numfashi, sai ya dago kai ya dubi abokan tafiya daya bayan daya cikin yanayin karayar zuciya yana mai musu nuni da yaro Masnur ya mutu. Nan take kowa ya fara kuka, masu kwalla na yi, masu zubar da hawaye na zubarwa.. Ana cikin wannan hali ne jaruma Shadira ta farfado sosai, ai kuwa sai ta mike zaune zumbur! ta shafa bayanta, koda ta ji babu yaro Masnur sai ta mike tsaye zumbur! tana waigewaige tana neman dan uwanta Masnur ta fara kwala masa kira. A wannan lokaci MAsnur na kwance a bayan boka Muzaffar ba ta ganshi ba. Ganin zubar hawaye ne akan fuskokin abokan tafiyar ta ta yasa jikinta yai sanyi. Kawai sai ta dubi boka Muzaffar ta ce, "Ina dan uwana?" Muzaffar ya kasa ba ta amsa, kawai sai ya share hawayen idanunsa ya koma gefe daya, Shadira ta yi arba 75 TASKARNOVELS.COM.NG da gawar Masnur a kwance idanunsa a bude kamar zai yi ma ta magana, har a sannan jini na kwarara daga kan tsakiyar kansa. Shadira ta tunkaro inda gawar ke kwance çikin tsananin tsoro, har jikinta na makyarkyata. Koda ta iso daf da gawar ta dubi tsakiyar kan Masnur sai ta ga ashe kan ya kusan darewa ma gida biyu har tana ganin kwakwalwarsa. Nan take Shadira ta kwarara uban ihu sannan ta durkushe-kasa bisa guiwoyinta ta ciccibi gawar Masnur ta rungume ta a kirjinta ta fashe da matsanancin kuka tana mai kurma ihu. Al'amarin da ya jefa kowa cikin tsananin tausayi da bakin ciki kenan aka ci gaba da kuka kamar ba za a daina ba. Komai rashin imanin mutum idan ya ga yadda Shadira ke wannan uban kuka da bakin ciki bisa rashin dan uwanta dole ne ya kamu da tsananin tausayinta. Bayan Shadira ta dade a kankame da gawar dan uwanta yaro Masnur tana kuka sai kuma ta 76 TASKARNOVELS.COM.NG shiga sambatu cikin rera waka mai dauke da kalmomin ban tausayi masu karya zuciya tana mai cewa: "Ina amfanin rayuwa idan babu masoyi? Duniya ki rike jin dadinki Kuma ki rike kayan kawar da ke cikinki. "Domin ba ki da abin da zai kawar mini da bakin cikin zuciyata" "Ke mutuwa ashe ke matsoraciya ce? Ki fito fili ki tare ni idan kin isa, yau sai na ga bayanki!" Lokacin da su sadauki Haiman suka ji irin wannan sambatu da Shadira ke yi sai suka daďa kamuwa da tsananin tausayinta. Nan take Lumaira ta saki Haiman ta je wajen Shadira ta rungume ta ta baya ta shiga rarrashinta, amma a banza, kamar ma daďa zuga ta ta yi, sai Shadira ta sake fashewa da matsanaicin kuka tana mai dada kankame gawar ďan'uwanta Masnur, kuma ta ci gaba da sambatu. 77 TASKARNOVELS.COM.NG Har aka gama sa wa kowa magani a rauninsa Shadira ba ta saki gawar Masnur ba, kuma ba ta daina kuka da sambatu ba. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin kowa ke nan a wajen. Koda ganin haka sai boka Muzaffar ya kira dukkanin jaruman, wato Haiman, Imran, Zarina da Shaharan suka koma gefe daya domin su tattauna akan al'amarin jaruma Shadira Boka Muzaffar ya dubi jaruman a nutse, ya ce, "Ya ku abokan tafiya, ku yi sani cewa na kira ku ne izuwa nan domin mu yi shawara bisa halin da abokiyar tafiyarmu ta shiga. Idan muka kyale ta ba mu raba ta da gawar dan uwanta ba ta ci gaba da wannan sambatu za ta iya haukacewa. Ma'ana ta rasa hankalinta gabadaya, idan kuma muka ce za mu rabu da ita anan tabbas za ta iya kashe kanta tunda ba ta da sauran buri da farin ciki a rayuwarta. Haka kuma ba za ta yarda ta bi mu ba mu ci gaba da wannan tafiya tare da ita tunda burinta ya yanke. Yanzu mene ne 78 TASKARNOVELS.COM.NG shawararku bisa abin da ya kamata mu yi a kanta?" Sa'adda boka Muzaffar ya zo nan a zancensa sai hankalin kowa ya kara dugunzuma aka rasa wanda zai ce kala, kuma suka kara kamuwa da tsananin tausayin Shadira. Bayan shudewar 'yan dakiku masu tsawo, sai sarki Laffaru yai gyaran murya ya ce, "Ni ina ganin cewa ba mu da wani zabi wanda ya fi kawai mu tafi mu bar ta a nan ita da gawar dan uwanta, domin idan ma muka tafi da ita matsala za ta zame mana, ba za ta iya taɓuka komai a cikin tafiyar ba, sai dai ma ta daďa karya mana zuciya". Koda jin wannan batu sai gimbiya Zarina ta fusata, ta daka wa Sarki Laffaru tsawa ta ce, "Ai dama kai tsohon azzalumi ne, ba ka san irin ciwon da masoyi yake ji ba yayin da ya rasa masoyinsa, shi ya sa ka raba Sharlis da iyayenta, ka lalata rayuwarta, gavshi kuma kaicma yanzu rayuwarka ta shiga mugun hadarin da ba ka da tabbacin kubuta. Wato yanzu mun gama cin moriyar ganga kenan kana son mu yar da 79 TASKARNOVELS.COM.NG kwauranta? Sai da Shadira ta gama sallama rayuwarta ta ceto tamu sannan kake son mu yi mata butulci mu tafi mu bar ta a lokacin da bacta da kowa, ba ta da sauran buri." Zarina ta dubi boka Muzaffar ta ce, "Ba za mu bar Shadira a nan ba. Yanzu sai mu lallaɓa ta mu karbe gawar daga hannunta mu binne shi sannan mu ci gaba da wannan tafiya bayan mun yi jinyar jikku nan mu ta a kallah kwanaki bakwai. Koda jin wannan batu sai kowa ya aminta. Nan take Zarina da Lumaira suka je wajen Shadira suka shiga rarrashinta a kan ta ba su gawar yaro Masnur domin a binne shi amma sai taki. Koda ta ga sun matsa ma ta sai tacyi wuf ta goya gawar a bayanta ta daure ta tamau sannan ta dana kibiyoyi akan bakanta ta tsira su ta ce, "Duk wanda ya ce, "Zai raba ni da dan uwana a cikinku sai na kashe shi!" 80 TASKARNOVELS.COM.NG Cikin alamun tsoro Zarina da Lumaira suka bar wajenta suka koma can inda su boka Muzaffar ke zaune. Nan fa aka rasa wanda zai je ya karbi gawar a hannunta. Da ma tunda aka fara wannan rikici sadauki Imran bai ce uffan ba. Kawai sai ya dubi mahaifiyarsa ya ce, "Zan je na karbi gawar wannan yaro daga hannun 'yar uwarsa na binne shi". Koda jin haka, sai mahaifiyar Imran ta firgita ainun ta rike hannayensa ta ce, "Kada ka je gare ta ta kashe ka a banza". Imran ya yi murmushi ya ce, "Koda ta rasa hankalinta ba za ta kashe ni ba. Ki zuba ido kawai ki ga abin da zai faru". Yana gama fadin hakan sai ya mike tsaye ya nufi inda Shadira ke tsaye goye da gawar yaro Masnur ya durfafe ta kai tsaye ba tare da shakkar komai ba, amma ya kura mata idanu 81 TASKARNOVELS.COM.NG cikin alamun tausayawa, har kwalla ta ciko a idanunsa. Lokacin da Shadira ta ga Imran ya durfafo ta kuma ta tabbatar da cewa so yake ya karɓe gawar Masnur daga gare ta sai ta ritsa shi da bakanta ta saita shi, kuma ta tabe bakan, amma sai hannunta ya kama karkarwa ta kasa harbinsa, ita ma ta kura masa idanu kawai ba tare da ta sauke bakan nata kasa ba. Imran ya ci gaba da tunkararta ba tare da jin tsoron komai ba. Al'amarin da ya bai wa kowa mamaki kenan aka ci gaba da kallonsu kawai domin a ga abin da zai faru. Yayin da ya rage saura bai fi taku uku ba kacal tsakanin jaruma Shadira da Imran sai ta dan sauke bakanta ta saki harbi daf da kafarsa ta daka masa tsawa ta ce, "Kada ka kara kusanto ni. Wannan shi ne kashedin karshe a gare ka!" Imran ya yi murmushi kawai ya ci gaba da tunkaro ta, ita kuma ta dada daga kwarinta ta saita shi kuma ta taɓe kwarin iya karfinta. A 82 TASKARNOVELS.COM.NG wannan lokaci ne mahaifiyar Imran ta fashe da kuka saboda ganin za a kashe danta a banza. Har Imran ya zo daf da Shadira yadda baka ce kawai a tsakaninsu amma ta kasa harbinsa kawai sai ya sa hannunsa ya ture Bakan nata sannan ya buďe hannayensa a lokacin da hawayen tausayi ya zubo masa. Nan take Shadira ta yi jifa da bakanta ta rungume shi tana mai sake fashewa da kuka, ta kankameshi a jikinta. Imran ya janye jikinsa daga cikin nata suka fuskanci juna sosai ya ce, "Ya ke abar bege da tunanina tun farkon haduwarmu, ki yi sani cewa tsananin tausayinki bisa wannan babban rashi da kika yi yanzu ya sa na karya alkawarin da na yi wa mahaifiyata a baya cewar ba zan yi soyayya ba sai bayan ta sami lafiya. Hakika na kamu da tsananin tausayinki da na ga kin rasa dan uwanki wanda kike so fiye da komai a duniya, sannan sai na kwatanta rashin a kaina na ce inda ni ne na rasa mahaifiyata lallai zan ďimauce fiye da yadda kika ďimauce. Daga yau 83 TASKARNOVELS.COM.NG na yi alkawarin zan ba ki soyayya ta gaskiya gami da kulawa irin wacce kika bai wa dan uwanki Masnur domin na debe miki kewar rashinsa. Ina son ki rungumi kaddara. Ki sani cewa gabadayanmu nan babu wanda ya fi karfin ya tsinci kansa a cikin irin halin da kika shiga. Yanzu sai ki bani gawar Masnur domin mu binneshi". Sa'adda Imran ya zo nan a zancensa sai Shadira ta sake rungume shi ta fashe da sabon kuka na murna da bakin ciki. Lokacin da mahaifiyar Imran ta ji abin da danta Imran ya fada wa Shadira sai farin ciki ya lulluɓe ta ta ji kamar an ba ta kyautar mulkin duniya, domin ďanta ya samu soyayyar gaskiya. Haka dai suka taru suka haka kabari suka sanya yaro Masnur a ciki suka bizne koda Shadira lallai da gaske ta rasa ďan uwanta har abada sai ta kara fashewa da kuka ta rungume Imran. Haka dai Imran ya cigaba da rarrashinta har gari ya waye ba tare da sun runtsa ba. Bayan cikar kwanaki bakwai sai kowa ya kimtsa ya yi 84 TASKARNOVELS.COM.NG shiri domin a cigaba da tafiya. Lokacin da jaruma Shadira ta ga za ta bar kabarin dan uwanta Masnur kuma abu ne mawuyaci ta sake ganin kabarin sai ta fashe da kuka ta fada kan kabarin tana sumbatarsa. Al'amarin da ya karya zuciyar gabaďayan abokan tafiyar kenan, saboda kowa ya san cewa shi ma zai iya rasa masoyinsa nan gaba a cikin tafiyar. Su duka sai suka kama kuka. Hatta gimbiya Rahila, boka Muzaffar da Sarki Laffaru wadanda ba su da 'yan uwa ko masoya a cikin wannan tafiya, ba su san sa'adda suka fara kuka ba. Da kyar Imran ya samu ya bambare Shadira daga kan kabarin dan uwanta Masnur, ya ja ta suka je suka hau kan aljani Marhabul Zaurus suka zauna. Cikin gaggawa sauran abokan tafiyar ma suka hawo suka zazzauna sannan Marhabul Zaurus ya bude fuka-fukansa ya tashi sama ya luluka izuwa cikin gajimare yana mai tsala gudu suka durfafi dajin na uku 85 TASKARNOVELS.COM.NG Bayan an sami kamar sa'a uku ana tafiya a sama ba tare da kowa ya ce kala ba, sakamakon alhinin mutuwar da aka yi, sai aljani Marhabul Zaurus yai gyaran murya sannan ya juyo da kansa ya dubi boka Muzaffar cikin alamun tsoro ya ce, "Ya shugabana ka yi sani cewa tun yanzu zuciyata ta fara bugawa da karfi saboda tsoro, domin nan da cikar sa'a biyu rak za mu riski wannan daji na uku mai dauke da miyagun manya-manyan tsuntsaye. Ka sani cewa aljanu ma komai girmansu da karfinsu suna shakkar waďannan tsuntsaye saboda karfin sihiri ba ya tasiri a kansu, kuma suna da gagarumin karfi na gaban kwatance domin da yatsu biyu kacal suke surar giwa su yi sama da ita komai girmanta. Kuma duk abin da suka karta da faratan kafafunsu to fa ko dutse ne sai ya farfashe. Daya daga cikinsu yana iya cinye rabin giwa ya baiwa 'ya'yansa rabin su cinye Suna da tsananin yawan gaske yadda ko a birni guda suka yiwa rubdugu za su iya hallaka komai da kowa a cikin 86 TASKARNOVELS.COM.NG kankanin lokaci. Anya kuwa za mu iya tsallake sharrin wadannan tsuntsaye?" Koda jin wannan tambaya sai boka Muzaffar ya sunkui da kansa kas yai shiru bai ce komai ba, saboda ba shi da wani bayani mai gamasarwa. Daga can sai yai ajiyar zuciya ya kira sunan aljani Marhabul Zaurus ya ce, babu abin da zan iya cewa akan wannan tambaya da ka yi mini, abin da na sani kawai shi ne muna sa rai da samun nasara. Gama fadin haka sai boka Muzaffar ya tsuke bakinsa yai shiru bai kara cewa uffan ba. Haka dai aka ci gaba da tafiyar amma duk wanda ka duba sai ka ga akwai alamun tsoro a yanayin fuskarsa. Hakika gaba dayan wadannan matafiya a gigice suke da shiga wannan daji na uku inda za a yi karo da wadannan masifaffun tsuntsaye . Babban abin da ya fara karya musu zuciya shi ne, ganin yadda jaruma Shadira ta rasa dan uwanta a daji na biyu don haka kowa ya san 87 TASKARNOVELS.COM.NG cewa komai zai iya faruwa gare shi a cikin wannan tafiya babu mai tabbacin zai gama lafiya. Bayan shudewar sa'a biyu cif, Sai suka iso wannan daji na uku. Tun daga baya-baya aljani Marhabul Zaurus ya saki fuka-fukansa ya sauko lasa ba tare da ya karbi izinin saukowa ba. Al'amarin da ya fusata boka Muzaffar ke nan ya dube shi ya ce, Waye ya ba ka izinin ka sauko da mu kasa tun gabannin mu iso farkon daji na ukun? Koda jin wannan tambaya sai aljani Marhabul Zaurus ya risina cikin biyayya ya ce, "Ya shugabana ka yafe ni kuma ka sani cewa, na yi haka ne domin mu sake yin cikakken shiri na shiga wannan daji na uku, saboda idan muka shige shi kai tsaye, wadannan mugayen tsuntsaye za su iya yi mana rubdugu a lokaci guda su gama da mu. 88 TASKARNOVELS.COM.NG Ina tabbatar muku da cewa karfinmu da makaman mu ba za su cece mu ba daga harin tsuntsayen sai dai sa'a da jajircewa! Lokacin da aljani Marhabul Zaurus ya zo nan a jawabinsa sai jikin kowa yai sanyi, kuma hankalin kowa ya kara dugunzuma, ban da na Shadira, domin ko kadan babu alamar tsoro a tare da ita, mutuwar ma nemanta take. Kai in ba don son Imran da ke yawo a zuciyarta ba da tuni ta kashe kanta ma, domin ba ta ga amfanin rayuwarta ba a doron kasa. Nan take kowa ya sauko kasa daga kan aljani Marhabul Zaurus. Shaharan da dokinsa ne suka sauka daga karshe. Shaharan ya ja dokinsa a hankali izuwa cikin wadansu ciyayi, ya sake shi ya kama kiwo abinsa a lokacin da ya kurawa dokin idanu yana 89 TASKARNOVELS.COM.NG kallon mugayen raunikan da ke jikin dokin, ga shi dama ba shi da lafiya, ko tafiya baya yi. Nan take kwallah ta zovwa Shaharan domin a duniya babu abin da yake so sama da wannan doki, ko kuda ba ya son ya taɓacshi, amma yanzu gacshi duk ďinki ne kaca-kaca a jikinsa. Bayan kowa ya zauna an dan huta, sai aka shiga tattaunawa bisa irin shirin da ya kamata a yi, don shiga cikin wannan daji. Boka Muzaffar ya ce, "Abu na farko dai, kun ga su wadannan tsuntsaye ba sa jin sara da suka, kuma komai nauyin abu suna iya surarsa da 'yan yatsun kafafunsu su yi sama da shi, kuma duk abin da suka sura bai isa ya iya kubcewa daga hannunsu ba, saboda haka duk yadda za mu yi ka da mu kuskura mu bar tsuntsayen nan su dauki daya daga cikinmu ta kowane hali".Sa'adda boka Muzaffar yaczo nan a jawabinsa sai kowa yai shiru yana tunani. Daga 90 TASKARNOVELS.COM.NG can sai jarumi Haiman yai gyaran murya ya ce, "To shin su wadannan tsuntsaye a gaba dayan jikinsu babu inda KAIFI DA TSINI zai yi tasiri?" Da jin wannan tambaya sai boka Muzaffar ya yi shiru yana tunani, daga can sai ya ce, "Fiye da shekaru dari bakwai baya ba a taɓa samun mahalukin da ya ratsa ta cikin wadannan dazuzzuka biyar ba, ya koma gida a raye bare aji daga bakinsa cewa wadannan tsuntsaye suna da lago. A duniya babu abun da za a ce ba zai yiwu ba, saboda haka babu mamaki mu ne waɗanda za su gano lagon wadannan tsuntsaye. Ni dai a yanzu shawarar da zan bayar ita ce, mu rufe jikinmu da kayan yaki na karfe yadda koda tsuntsayen sun kawo mana sara da suka da faratan kafafunsu sai dai su sami karafunan ba dai jikinmu ba". 91 TASKARNOVELS.COM.NG Koda jin wannan batu sai sarki Lafaru ya dubi boka Muzaffar a fusace ya ce, "Me ya sa tun kafin mu baro garuruwanmu ba ka sanar damu wannan al'amari mun yi tanadi ba? Yanzu a ina za mu sami kayan yaki na karfe wadanda za mu rufe jikinmu da su?' Koda jin wannan batu sai boka Muzaffarya ya bushe da dariya, lokaci guda kuma ya murtuke fuska sannan ya ce, "To ai in ban da abinka mene ne amfanin sihirin tsafin da muka mallaka?" Kafin wani daga cikinsu ya kara cewa wani abu tuni boka Muzaffar ya rintse idanunsa ya fara karanta dalasiman tsafi. Sai da ya shafe dakiku dari biyu da ashirin yana karanta dalasiman tsafin a fili, yana gamawa kuwa sai kowa ya tsinci kansa a cikin kayan yaki na karfe. Hatta mahaifiyar Imran, Sarkin Farisa, Lumaira da dokin Shaharan kuwa. Sai ya zamana gaba dayan jikinsa a rufe yake da sulken karfe. 92 TASKARNOVELS.COM.NG Kai bama dokin Shaharan ba, hatta aljani Marhabul Zaurus jikinsa ya lullube da kayan yaki, hatta katon kansa kuwa, idanunsa, bakinsa da kunnuwansa ne kadai a waje. Koda kowa ya tsinci kansa a cikin wannan kayan yaki sai suka cika da murna saboda a tunaninsu sun tsira daga sharrin wadannan mugayen tsuntsayce. Abin da bacsu sani ba shi ne, wannan kariya ba zavta hana tsuntsayen cutar da su ba. A wannan lokaci jaruma Shadira na zaune ita kadai a gefe daya bisa kan wani dutse ta daga kanta sama tana tunani. Ba komai take tunani ba face irin abubuwan da suka faru a baya tsakaninta da dan uwanta marigayi yaro Masnur. Musamman a irin lokutan da suke wasan 'yar birin-birin, da sa'adda suke cin abinci tare da kuma lokacin da take yi masa wanka ta yi masa ado. Kai hatta kwanciyar barci 93 TASKARNOVELS.COM.NG kullum akan kirjinta Masnur ke bacci, ba ya yarda ya gusa daga kusa da ita. Sa'adda Shadira ta zo dai-dai nan a tunaninta sai zuciyarta ta karye, ta fashe da kuka. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin kowa ke nan. Cikin sauri jarumi Imran ya je gare ta ya zauna daf da ita, sannan ya sa hannunsa ya share hawayen da ke zuba a fuskarta ya ce, "Ya ke abar kaunata, na sani cewa kin yi babban rashi wanda har abada ba za ki taba mantawa da shi ba, amma saboda me ni ba zan maye miki gurbin dan uwanki ba? Daga yau ina son ki daukeni a matsayin dan uwa, uwa, uba, uwa, kuma babban masoyi wanda babu kamarsa. Na rantse da darajar kaunar da nake yi wa mahaifiyata zan soki kamar yadda kowacce uwa ke son danta, kuma kamar yadda dan uwa ke son dan uwansa na jini. Sannan zan sallama rayuwata don kare taki". 94 TASKARNOVELS.COM.NG Koda jaruma Shadiara ta ji wannan batu sai ta rungume Imran tana mai cewa, "Ina yi maka fatan cika wannan alkawari.Tabbas idan alkawarinka ya cika za ka maye mini gurbin dan uwana da na rasa". A can gefe daya kuwa, Shaharan na satar kallon gimbiya Zarina, amma bai san cewa tana kallonsa ba da wutsiyar idonta, kuma dan uwanta ma Sarkin Farisa yana lura da abin da ke faruwa a tsakanin nasu. Nan take Sarkin Farisa yai murmushi a lokacin da ya dubi 'yar uwar tasa ya ce, "Ya ke 'yar uwata, ni kuwa ina son na nemi wata alfarma guda daya rak a wajenki". Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Zarina ta ce, "Yanzu dama ashe akwai wata bukata da kake da ita amma tuntuni baka furta mini ita ba? Sarkin Farisa ya numfasa, "A'a a yanzu ne bukatar ta zo mini". 95 TASKARNOVELS.COM.NG Zarina ta ce, "Ina sauraronka, in dai abu ne mai yiwuwa a duniyar nan, kuma ina da ikon yi sai na yi maka shi. Sarkin Farisa yai shiru kamar ba zai ce komai ba, daga can kuma sai ya dubi Zarina ya ce, "A duniya babu mutumin da nake tausayawa face wanda ya jarabtu da son wani, amma wanda yake so din ya ki karɓar soyayyar tasa. Me zai hana ki yi wa sadauki Shaharan murmushi koda sau daya ne rak domin ya sau nutsuwa da saukin radadi da zogi na begenki a cikin zuciyarsa? Tabbas ya kamu da tsananin sonki, kuma so ba na wasa ba. Koda jin wannan batu sai Zarina ta haɗa fuska ta ce, "Haba ya kai dan uwana, ka sani cewa na yi alkawarin cewar bá zan yi aure ko soyayya ba face na ga kai ma ka warke, kuma ka sami masoyiya wadda za ka aura. Lallai ina nan a kan wnanan alkawari nawa, babu abin da zai sa na karya shi face mutuwa. Ka yi hakuri ya kai dan uwana, ba zan iya yin wannan abu da ka umarce ni da yi ba". 96 TASKARNOVELS.COM.NG Boka Muzaffar da Sarki Laffaru kuwa, a wannan lokaci suna zaune a can gefe daya kusa da gimbiya Rahila suma suna tasu hirar dabam. Duk sa'adda Rahila ta dago kai sai ta ga Sarki Laffaru ya kura ma ta idanu ko kiftawa baya yi. Abin da ya ba ta haushi ke nan, kuma ya ba ta mamaki. Ta ce a cikin zuciyarta, "Wai shin me Sarki Laffaru yake ci ne na baka na zuba? Kuma mene ne ya burge shi a tare da ni, shi da yake kan tafarkin auren gimbiya Ramlatul Siyam 'yar Sarkin birnin Hindu wacce ban fi ta kyau ba, kuma mahaifinta yafi mahaifina arziki da daukaka a duniya? Koda yake, ai shi mutum ne mai son mata da yawa. Ni kam babu ruwana da duk matsalarsa, burina kawai shi ne na biya tawa bukatar".Rahila na cikin wannan tunanin ne ta ji boka Muzaffar ya ce, "A tashi a ci gaba da tafiya". 97 TASKARNOVELS.COM.NG Nan take kuwa aka mike aka durfafi cikin daji na uku. Imran ne akan gaba goye da mahaifiyarsa, Shadira na biye da shi daf da daf, sannan jarumi Haiman goye da matarsa Lumaira, sai Zarina goye da Sarkin Farisa, sai Raliila, sannan boka Muzaffar da Sarki Laffaru. Al'ajani Marhabul Zaurus ne na karshe. Al'amarin da ya ke fusata boka Muzaffar ke nan, saboda yana mamakin yadda aljani Marhabul Zaurus yafi dukkan sauran abokan tafiyar tsoro, a matsayinsa na ljani mai shirgegiyar halitta, amma duk ta zama ta banza. Koda shigar su Imran cikin wannan daji na uku sai suka fara daga kawunansu sama suna kallekalle don su ga ta inda wadannan mugayen tsuntsaye za su kawo musu farmaki, da ma kowa ya zare makaminsa yana dube-dube da waige-waige gami da kallon sama ta kowanne ɓangare. 98 TASKARNOVELS.COM.NG Sai da suka yi doguwar tafiya a cikin dajin, amma ko motsin Tsuntsayen ba su ji ba. Al'amarin da ya matukar basu mamaki ke nan, har sarki Laffaru ya dubi boka Muzaffar ya ce, "Anya kuwa mun shigo cikin dajin da mugayen Tsuntsayen nan suke?" Kafin boka Muzaffar ya budi baki ya ce wani abu sai kwatsam! Suka ji kasar dajin gaba daya ta kama girgirza tana darewa. Al'amarin da ya firgita su ke nan. Nan take ramuka suka rinka budewa, sai ga wadannan mugayen Tsuntsayen suna bullutsowa sama daga cikin ramukan tamkar an tashi matattu a makabarta. Kafin su Imran su yi wani yunkuri sama da Tsuntsaye dubu dari sun yi musu kawanya babu ta inda za su iya ratsawa su wuce. 99 TASKARNOVELS.COM.NG Daga can kololuwar sama kuma sai ga wata runduna guda ta wadannan tsuntsaye suna tsala gudu sun durfafo su. Nan fa cikin kowa ya duri ruwa, hankalin kowa ya dugunzuma ainun, domin sun san cewa suna cikin bakin hadari. Tabbas rayuwarsu tana a tsakanin MUTUWA DA RAYUWA. (Zuwa ga makaranta. Ina so mu sani cewa, salon da Madakin Gini ya bi wajen wahalar da jaruman yana da alaka da kwarjinin kogon DARUL IKSINA ne. Ana so a tabbatar mana da cewa, hakika waďannan dazuka sun cika gagarabadau ababan misali) Kafin tsuntsayen saman su iso sai na kasan suka fara marmatsowa domin su afka musu. Koda ganin abin da ke shirin afkuwa sai Imran ya buɗe muryarsa da karfin tsiya ya ce, Ku biyo ni a baya, duk inda ku ka ga na yi ku bi ni. 100 TASKARNOVELS.COM.NG Ai kuwa yana gama fadin haka sai ya falfala da azababben gudu ya tunkari tsuntsayen da ke gabansa ya ratsa ta cikinsu da karfin tsiya ya rufe su da duka da sandarsa, sai ga shi ya tarwatsa su da karfin tsiya ya sama musu hanya, suka ci gaba da gudu. Amma sai Tsuntsayen suka biyo su a guje aka ruguntsume da masifaffen yaki. Su Imran suna gudu suna juyowa suna kare harin tsuntsayen da makamansu. Duk sa'adda makamansu suka hadu da kafafun Tsuntsayen sai dai ka ga tartsatsin wuta ya tashi kamar karfe da karfe ne suka haďu. A daidai wannan lokacin ne wadancan Tsuntsayen da ke tahowa daga sama suka iso suka lullube saman su Imran, yakin ya kara tsamari ainun. Duk da cewa su Imran suna tsala gudu suna ketawa ta cikin bishiyoyi amma Tsuntsayen ba su fasa bin su ta sama da kasa ba. Ko bishiya Tsuntsayen suka yi karo da ita, komai kaurin bishiyar sai dai ka ga ta karye ta fadi kasa sun wuce abinsu. Duk sa'adda tsuntsayen suka karci kayan karfen da ke jikin 101 TASKARNOVELS.COM.NG su Imran kuwa, sai dai ka ga kayan na darcwa tamkar takarda aka yanka da zabira. Wani lokacin ma faratan Tsuntsayen na kartar jikin jaruman bayan sun keta kayan jikin nasu. Sai dai ka ji suna ihu, jini na tsartuwa a jikinsu. Imran ne kawai Tsuntsayen ba su yiwa rauni ba, sai kuma gimbiya Rahila. Lokacin da jarumi Imran ya lura da halin da sauran abokan tafiyarsa ke ciki, wato waďannan tsuntsayen sun yi musu rauni, kuma suna kokarin surarsu, in ba don ma sun kasance jarumai ba masu juriya da naci da tuni tsuntsayen sun yi sama da su. Abin da ya fi dugunzuma hankalin su Imran shi ne, ganin yadda KAIFI DA TSINI ba ya tasiri a jikin tsuntsayen, har ta kai cewa ma takubbansu sun fara dakushewa. Nan take Imran ya fusata ainun, ya ci gaba da dukan tsuntsayen da sandarsa kuma a kai ya fi dukansu, sai dai ka ga sun fado kasa, amma 102 TASKARNOVELS.COM.NG kuma sai su sake mikewa zumbur! Su yi sama su ci gaba da kawo hari. Imran sai ya sauya salon yaki, ya rinka dawowa da baya yana kade tsuntsayen da sandarsa, don kubutar da sauran abokan tafiyarsa. Wato sai yai gaba kuma yai baya, amma duk da haka dai bai hana tsuntsayen ci gaba da kawo mugayen hare-hare ba. Duk wannan gumurzu da ake yi a cikin gudu ake yinsa. Sau tari idan Tsuntsayen suka kawo farmaki sai ka ga jaruman na faduwa kasa saboda karfin iskar fuka-fukan Tsuntsayen da kuma karfin harin nasu. Amma kuma sai ka ga jaruman sun yi wuf sun mike sun ci gaba da gudu kafin Tsuntsayen su cafke su duk da cewa kuwa sun yi musu rauni. Haka dai aka

Chapter 4 of 18