ya sa dabbobin suke tsorata da
shi.
Lokacin da Laffaru ya gaji da yawo a cikin dajin
har ya ji kishirwa ta kama shi sai ya je karkashin
wata doguwar bishiya ya zauna sannan ya fidda
dan guzurin abincinsa ya fara ci. Abin da bai
sani ba shi ne, ashe akwai abin da ya fito nema
akan wannan bishiya da ya zauna a karkashinta.
460
TASKARNOVELS.COM.NG
Wani murtukeken rikakken Zaki ne kwance
akan bishiyar yana barci. Zakin bai dade da
cinye wata barewa ba da ya make.
Bayan ya ci ya koshi kuma ya je ya sha ruwa sai
ya zo ya hau can saman bishiyar ya kwanta.
Yana kwanciya kuwa sai barci ya sace shi. Da
yake barcin nasa bai yi nisa ba ko munshari bai
fara ba.
Koda Laffaru ya fara cin abincin sai sautin
taunarsa ya sa Zakin ya farka. Ai kuwa yana
lekawa kasa ya yi arba da Laffaru sai ya kwarara
uban gurnani mai tsananin firgitarwa.
Gurnanin nasa ya cika dajin gaba daya da amsa
kuwwa. Hatta Maruful Dauwaz da Ramlatul
Siyam da ke can tsakiyar dajin sai da suka jiyo
wannan ruri na Zaki.
461
TASKARNOVELS.COM.NG
Cikin tsananin farin ciki Ramlatul Siyam ta daka
tsalle ta fada kan Aljani Maruful Dauwaz tana
mai cewa, "Na sami miji!"
Bisa mamaki sai ta ga Maruful Dauwaz ya
sunkui da kansa kas cikin alamun karayar
zuciya sannan ya ce, "Wannan rurin Zakin da
kika jiyo ba na fitar rai ba ne, ruri ne na
tsoratarwa.
Tabbas Laffaru ya yi MUGUN GAMO da murjejen
Zaki kuma rikakken gaske domin sai zakin da ya
haura shekaru talatin a duniya shi ne yake irin
wannan ruri".
Koda jin wannan batu sai hankalin
Ramlatu!Siyam ya dugunzuma ainun ta ji kamar
ta ruga da gudu izuwa cikin dajin domin ta kai
wa Laffaru dauki amma sai ta dake.
462
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da wannan Zaki ya yi wannan ruri sai
Laffaru ya mike zumbur a matukar tsorace
domin ya gudu, ai kuwa sai Zakin ya duro a
kansa ya turmusheshi a kas suka kama kokawa
suna mirgine- mirgine.
Zakin ya fara kokarin ya kafa hakoransa akan
makoshin Laffaru shi kuwa sai ya dage iya
karfinsa yana gabzawa Zakin naushi suka ci
gaba da turmutsutsu da birgima a kas.
Nan da nan Zakin ya karkarce jikin Laffaru da
faratan hannayensa da na kafafunsa. Albarkacin
mirginawar da suke yi ne shi ma Zakin fuskarsa
ta rinka gwaruwa a jikin duwatsu da bishiyoyi
har ya sami raunika, jini ya cika fuskar tasa.
Ai kuwa suna cikin birgima a kasan ne da
mirginawa suka fado izuwa asan wani rami
wanda ruwan kogi ne ke azababben gudu a
cikinsa. Suna fadowa cikin ruwan sai
kowannensu kansa ya bugu akan duwatsu duk
463
TASKARNOVELS.COM.NG
suka suma. Igiyar ruwa ta tafi da su izuwa can
gaɓar kogi tayi watsi da su.
Sai da iska ta bugesu sannan Laffaru ya fara
farfadowa. Koda ya yunkura domin ya mike
tsaye sai ya ji ya kasa saboda ji ya yi kamar ba
shi da kafar dama.
Koda ya dubi kafar tasa sai ya ga ta karkarce
kuma ta kumbura suntum! Nan take ya gane
cewa karyewa ya yi. Al'amarin da ya matukar
dugunzuma hankalinsa ke nan.
Kwatsam! Sai wannan Zaki ya farfado daga
dogon suman da ya yi. Ai kuwa yana bude
idanunsa ya yi arba da Laffaru zaune a gabansa
sai ya daka tsalle gami da wangame bakinsa zai
afka masa.
Cikin tsananin zafin nama Laffaru ya cisgo wata
'yar karamar bishiya da ke daf da shi yai sama
464
TASKARNOVELS.COM.NG
ya tari Zakin. Bisa sa'a kuwa sai tsinin reshen
bishiyar ya shige cikin hancin Zakin ya bullutso
ta wuyansa.
Suna fadowa kasa shi da Zakin sai Zakin ya
kama matagungun da shure-shuren mutuwa. Sai
da Zakin ya dade yana shure-shure sannan ya
mutu.
Nan fa tashi ya gagari Laffaru. Dole ya ci gaba da
zama a bakin wannan koramar da wanan
karamar bishiya wacce ya kashe Zakin da ita ya
samu ya kakkarya rassanta ya gyara karayar
tasa ya daure kafar a jikin rassan da taimakon
tsumman rigar jikinsa da ya yayyage. Sai da ya
kwana uku yana jinyar kafar tasa a bakin
wannan kogi ya zamanacewa, ba shi da abincin
ci sai danyen naman wannan Zaki da ya kashe,
har ma Zakin ya rube ya fara tsutsa amma a
haka yake cin naman nasa don kada yunwa ta
kashe shi, tunda babup kyastu a wajen wanda
zai kunna wuta ya gasa naman. Ruwan wannan
kogi kuwa shi ne ya zamo ruwan shan sa.
465
TASKARNOVELS.COM.NG
Al'amarin Ramlatul Siyam da Aljani Maruful
Dauwaz kuwa, koda suka ga rana tafadi dare ya
yi Laffaru bai dawo ba sai hankalinsu ya
dugunzuma ainun suka aiyana a ransu cewa ya
mutu.
Koda kwana uku suka shude sai suka kara
sallamawa.
Abin da ya kara dugunzuma hankalinsu shi ne a
wannan rana ne Rahila ta ci gaba da aman jini
ba kakkautawa, ga shi sun diga mata wannan
maganin barci amma ta kasa yin barcin sai
numfashinta ne ke ci gaba da sarkewa.
Koda ganin halin da Rahila ta shiga sai Maruful
Dauwaz ya fara kuka domin ya san cewa
karshen burinsa ya zo.
466
TASKARNOVELS.COM.NG
Kwatsam! ba zato ba tsammani sai suka ga
mutum ya tunkaro su yana dogara ice da
hannunsa na dama, hannunsa na hagu kuwa na
rike da wani katon kan Zaki.
Koda mutumin ya matso kusa sai suka shaida
shi. Ba wani ba ne face Sarki Laffaru.Cikin
tsananin farin ciki Ramlatul Siyam ta mike
zumbur! ta ruga wajen Laffaru ta rungume shi
tana cewa, "Ka zama mijina na zama matarka".
A daidai wannan lokaci ne suka ji Maruful
Dauwaz ya fashe da matsanaicin kuka.
A firgice suka juyo suka dube shi sai suka ga
ashe Rahila ce ta mutu akan hannayensa.
Ai kuwa sai su ma suka durkushe kasa suka
fashe da matsanaicin kuka. Sai da Laffaru,
Ramlatul Siyam da Aljani Maruful Dauwaz suka
467
TASKARNOVELS.COM.NG
shafe sa'a biyar suna kuka da bakin ciki sannan
suka haka kabari suka binne Rahila.
A sannan ne Aljani Maruful Dauwaz ya dago kai
ya dubi Sarki Laffaru da Ramlatul Siyam a
lokacin da hawaye ke zubowa kan kumatunsa
daki- daki ya ce, "Ya ku abokan tafiya, ku yi sani
cewa lokacin rabuwa ta da ku ya yi, tabbas in ba
don ina da sauran alkawari guda daya ba da
yanzu take a gabanku zan kashe kaina.
Alkawarin da ya rage mini kuwa shi ne na
komawa kofar kogon Darul Iksina domin na
gani idan sauran abokan tafiyarku na nan a
raye.
Alfarma daya zan iya yi musu na karanta
wadannan dalasimai na tsafi na bude kofar
kogon.
468
TASKARNOVELS.COM.NG
Lallai idan akwai wanda yai rai a cikinsu a
sannan ne zai iya fitowa ni kuma sai na dauke
shi na maida shi kasarsa".
Koda jin wannan batu sai Laffaru da Ramlatul
Siyam suka kara kamuwa da tsananin tausayin
Aljani Maruful Dauwaz. Ramlatul Siyam ta dube
shi ta ce, "Ya kai Sarkin sadaukai na duniya, ka
yi sani cewa har abada duniya ba za ta manta da
kai ba domin ka yi jarumtakar da babu wanda
ya taɓa irinta.
Kai ne ka fara shiga wajen da ya gagari kowa a
duniya, kuma kai ne ka dauko ni daga cikin
fadar mahaifina wajen da ya fi ko ina karfin
tsaro a duniya. Bai kamata a ce gwarzon mayaki
kamarka ya yi mutuwar banza ba.
Na sani cewa bayan ka je kogon Darul Iksina
babu abin da za ka sake yi face ka kashe kanka.
Ina mai rokonka alfarma guda daya.
469
TASKARNOVELS.COM.NG
Ina son a ranar da na haihu ka zo ka ga 'yata ka
dauke ta da hannayenka masu albarka ka sa
mata albarka domin ina son anan gaba ta yi
alfahari da cewa Sarkin sadaukan duniya ya
dauke ta da hannayensa.
Ina tabbatar maka da cewa sai na sassaka
gunkinka a lokacin da kake dauke da jaririyata
domin ya zamo abin tunawa da kai a gare mu
har abada. Kuma lallai za mu bar tarihinka a
rubuce yadda jama'ar kowanne zamani za su
riske shi kamar yadda aka samu kadan daga
cikin tarihin naka a kundin tarihi na Birnin
Lairuf wato garin su Gimbiya Rahila. Sa'adda
Ramlatul Siyam ta zo nan a zancenta sai hawaye
ya kara zubowa Aljani Maruful Dauwaz ya ce,
"Hakika babu wata alfarma da za ki nema a
wajena na ki yi miki don haka na yi miki
alkawari lallai zan dawo gare ku a ranar da kika
haihu."
Koda gama fadin hakan sai Aljani Maruful
Dauwaz ya buɗe fuka-fukansa ya tashi sama a
hankali yana kallon su Ramlatul Siyam su ma
470
TASKARNOVELS.COM.NG
suna kallonsa suna hawaye shi ma yana hawaye
har ya luluka a cikin gajimare ya ɓace musu da
gani.
Maruful Dauwaz ya ci gaba da tsala gudu a
sararin samaniya ba sassauci yana mai tunkarar
tsibirin da kogon Darul Iksina yake. Ai kuwa a
cikin sa'a biyu da rabi jal ya iso bakin wannan
kogi wanda kogon na Darul Iksina ke kansa.
Aljani Maruful Dauwaz na sauka a bakin gabar
kogin sai ya dubi gabas da yamma, kudu da
arewa ya ga wayam babu wata halitta mai
numfashi a wajen, koda kuwa tsuntsu guda daya
ko kwari, kuma ba a jin sautin komai face na
iskar da ke kadawa a cikin dajin.
Nan take Aljani Maruful Dauwaz ya tuna tsawon
shekarun da ya yi a cikin kogon Darul Iksina
saboda bakin cikin mutuwar masoyiyarsa, ya
tuna cewa shiga yanzu ba shi da kowa a duniya
domin duk zuri'arsa ma sun kare.
471
TASKARNOVELS.COM.NG
Abin da yai masa saura kawai shi ne wannan
wasiyya wacce masoyiyarsa ta bar masa kuma
ga shi wadda ta san inda wasiyyar take ta mutu
sai ya fashe da matsanaicin kuka.
Sai da Aljani Maruful Dauwaz ya shafe rabin sa'a
yana wannan kuka sannan ya dubi kogon Darul
Iksina ya bude bakinsa ya karanta wadannan
dalasimai na tsafi. Faruwar hakan ke da wuya
sai kofar kogon ta bude da kanta.
Aljani Maruful Dauwaz ya kura idanu izuwa
cikin kofar amma sai ya ji shiru bai ji motsin
tafiya ba kuma bai hango kowa ba.
Tsawon kusan wata rabin sa'ar bai ga wani ya
fito ba sai ya fid da rai ya aiyana a ransa cewa
gabadayan abokan tafiyar su Laffaru sun mutu a
cikin kogon na Darul Iksina.
472
TASKARNOVELS.COM.NG
Aljani Maruful Dauwaz ya yunkura domin ya
tashi sama sai kawai ya jiyo sautin tafiya daga
can cikin kogon Darul Iksina.
Cikin tsananin murna ya dakata ya sake zuba
idanu izuwa cikin kogon. Sannu a hankali sautin
tafiyar ya rinka karuwa har ya yi arba da masu
fitowar.
Ba wasu ba ne face Shaharan, Zarina, Shadira,
Imran, Lumaira da mahaifiyar Haiman.
Dukkaninsu da kyar suke tafiya. Zarina ta goyo
mahaifiyar Imran a bayanta, ita kuma Shadira
tana rike da hannun makauniya Lumaira. Imran
da Shaharan kuwa sun rike kafadun junansu
suna dingishi.
Koda su Imran suka hango Aljani
MarufulDauwaz a can bakin gaɓar kogin sai
473
TASKARNOVELS.COM.NG
suka firgita ainun suka ji kamar su koma cikin
kogon na Darul Iksina domin ba su taɓa ganin
Aljani mai matukar kwarjini da ban tsoro ba
kamarsa.
Amma da suka tuna cewa ba su san wanda ya
bude musu kofar kogon ba har suka fito sai suka
aiyana a ransu cewa lallai wannan Aljani ne ya
bude kofar kogon.
Yayin da Aljani Maruful Dauwaz ya fahimci
cewar sun tsorata da shi sai ya dube su cikin
murmushi ya ce, "Ya ku wadannan ZARATAN
JARUMAI ababan alfahari ku yi sani cewa ni ba
wani bane face Aljani Maruful Dauwaz."
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lulluɓe su
Imran suka yafuto Aljani Maruful Dauwaz da
hannayensu suna masu yi masa nuni da ya zo ya
dauke su. Nan take kuwa Aljani Maruful Dauwaz
ya ketare kogin ya sauka a gabansu.
474
TASKARNOVELS.COM.NG
Ba tare da fargabar komai ba su duka suka hau
kan Aljani Maruful Dauwaz suka zauna shi kuma
sai ya bude fuka-fukansa ya tashi da su sama
yana mai tsala gudu a cikin gajimare.
Suna cikin tafiyar ne ya ba su labarin duk abin
da ya faru tsakaninsa da su Laffaru tun daga
lokacin da suka riske shi a cikin a cikin kogon
Darul Iksina kawo izuwa sa'adda ya dauke su
suka tafi izuwa fadar Sarki Nashmir suka yi
wannan yake-yake, har daga karshe Rahila ta
mutu ba tare da ta sanar da shi inda
wasiyyarmasoyiyarsa take ba, da kuma dajin da
ya baro Ramlatul Siyam da Sarki Laffaru inda za
su ci gaba da rayuwarsu ta zaman aure."
Koda Aljani Maruful Dauwaz ya gama bai wa su
Imran labari, sai suka cika da tsananin bakin
ciki da tausayi suka fashe da kuka gabadayansu.
A sannan ne kuma ya yi musu albishir da cewa,
Boka Muzaffar da Sarki Nashmir sun kashe
475
TASKARNOVELS.COM.NG
junansu amma mashin Galilul Haras ya koma
hannun Sharlis. Haka kuma ya tabbatar musu da
cewa daya bayan daya sai ya mayar da
kowannensu kasarsa.
Koda jin wannan labari sai suka kamu da
tsananin farin ciki. Amma da suka tuna cewa
lokacin rabuwarsu ya zo gaba daya sai suka ci
gaba da kuka saboda sabo da shakuwar da suka
yi.
Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin Aljani
Maruful Dauwaz, da su jarumi Imran, jaruman
da su ne kadai suka tsira da rayuwersu a cikin
kogon Darul Iksina bayan sun fid da rai ga tsira
da rayuwa.
*****
476
TASKARNOVELS.COM.NG
AL'AMARIN Sharlis kuwa, lokacin da ta ga ta
mallaki mashin Gul Haras sai ta cika da tsananin
farin ciki ta koma Birnin Kufa.
Tana isa gida ta iske danta Sarki Shaddadu a
zaune cikin matukar damuwa saboda rashin
ganinta. Koda ta baiyana a gabansa rike da
mashin Galilul Haras sai ya mike zumbur! Ya
ruga gare ta suka rungume juna cikin tsananin
farin ciki.
Nan take ta ba shi labarin darajar mashin Galilul
Haras ta tabbatar masa da cewa, za ta koya
masa yadda ake sarrafa Mashin amma sai bayan
ya girma ya mallaki hankalin kansa don kada
kuruciya tasa ya je ya yi wani abin da bai dace
ba.
Daga wannan rana Sharlisa ta ci gaba da koya
wa Shaddad yaki dare da rana ya zamana cewa
jarumtakarsa kullum karuwa take yi.
477
TASKARNOVELS.COM.NG
Wani lokacin tausayinsa ne yake kama ta idan ta
ga irin bakar wahalar da yake sha wajen karɓar
horon yaki, har ma ya kan suma sai dai Sharlis
ta ji kwallah ta zo mata saboda tsananin
tausayinsa amma duk da haka ba ta daina ba shi
horon ba.
Ba komai ne yasa Sharlisa take bai wa Shaddad
wannan horo mai tsanani ba face saboda ta yi
bincike ta gano cewa Sarki Laffaru ya auri
Gimbiya Ramlatul Siyam kuma suna nan a cikin
wani daji suna zaman rayuwar aure. Babu
yadda Sharlisa ba ta yi ba domin ta shiga dajin
Rauful Mausur amma abu ya gagara. Sau goma
sha daya tana yin gagarumin shiri ta je har
bakin dajin domin ta shiga amma sai ta kasa,
bisa dole ta hakura ta koma da baya.
A cikin binciken da ta yi ne ta ga cewa lallai
Sarki Laffaru da Gimbiya Ramlatul Siyam za su
haifi 'ya mace kyakkyawar da babu kamarta a
duk duniya, kuma za ta taso da gagarumar
jarumtaka irin wacce babu wani jarumi mai
irinta.
478
TASKARNOVELS.COM.NG
Babu wanda zai iya tararta da fada ko yaki face
danta Shaddadu. Shi kansa Shaddadun ba zai iya
hallaka ta ba face yai amfani da mashin Galilul
Haras.
Lokacin da ta daďa zurfafawa a cikin binciken
nata ne, sai ta gano cewa babban abin da zai
janyo rashin nasarar Shaddadu akan 'yar Sarki
Laffaru shi ne SOYAYYA.
Ko shakka babu in dai ya yi arba da 'yar Sarki
Laffaru sai ya kamu da tsananin sonta, in kuwa
ya kamu da tsananin sonta ba zai iya kashe ta
ba.
Koda Sharlisa ta gano wannan al'amari sai ta
rinka cusawa Shaddad kiyayyar mata a
zuciyarsa, ta rinka nuna masa cewa sharrin
mata ya fi na bakin kumurci.
479
TASKARNOVELS.COM.NG
A haka Shaddad ya taso da tsananin kiyayyar
mata, ya zamana cewa ya tsane su ainun komai
kyan mace ba ta birge shi.
Kai hatta sha'awa ma irin wacce kowanne da
namiji ke yi wa mace sai da Sharlis ta cire wa
Shaddad ita da karfin sihiri, a matsayin ba za ta
dawo masa da sha'awar ba sai bayan ya kashe
'yar da Laffaru ya haifa sannan ya kamo
Laffarun ye kawo mata shi sun gana masa
muguwar azaba tsawon kwanaki sannan su yi
masa kisan gilla.
A kwana a tashi, sai jarumi Shaddad ya cika
shekaru ashirin da daya a duniya. A sannan ne
kirar jikinsa ta ginu sosai, kai da ganinsa ka ga
gawurtaccen jarumi saboda murdewar da jikin
nasa ya yi da kuma tarin kwanji da jijiyoyi.
Ga shi Allah Ya yi masa tsananin kyan fuska da
kyan surar jiki. Karfin dantsensa kuwa ya wuce
a misalta saboda komai girman bishiya idan ya
480
TASKARNOVELS.COM.NG
naushe ta da hannu daya take ta ke tunɓukowa
daga cikin kasa ta fadi kasa.
Kuma komai yawan mayaka shi kadai yana iya
tarwatsa su ya kashe na kashewa, masu sauran
kwana su gudu. Idan kuwa yana yaki zai iya
kwana da yini bai gaji ba
A ranar da Shaddad ya cika shekara shirin da
daya ne, Sharlis ta kimtsa shi ta damka masa
mashin Galilul Haras sannan ta gargade shi akan
kada ya yi amfani da mashin face ya gamu da
'yar Sarki Laffaru.
Koda jin haka sai Shaddadu ya dubi
mahaifiyarsa Sharlis cikin tsananin damuwa ya
ce, 'Ya ke Ummina yanzu ya za a yi na gane
wannan babbar mikiya tawa alhalin ban santa
ba, kuma ban taɓa ganin irin fuskarta ba?
481
TASKARNOVELS.COM.NG
Ke da kanki ma kin yi iya bincike a cikin tsafi
domin ki ga fuskarta amma abu ya gagara
saboda tana cikin dajin da ba a iya ganin komai".
Sa'adda Shaddadu ya zo nan a zancensa sai
Sharlis tayi ajiyar zuciya har kwalla ta zo ma ta a
cikin idanunta, sannan ta yi murmushi ta ce,
"Kada ka damu ya kai dana, yanzu-yanzu zan ba
ka wata layar tsafi. Duk Macen da ka hadu da ita
in dai ka ga tana da jarumtaka gami da tsananin
kyau da zarar ka kara layar a jikinta za ka ga
layar ta sauya launi daga baka zuwa ja jawur.
Kana ganin haka ka yake ta da mashin Galilul
Haras ka hallaka ta.
A jikin wata sarka da ke wuyanta za ka ga hoton
dajin da mahaifinta yake. Ka cire sarkar ka tafi
da ita har can inda mahaifin nata yake ka kamo
shi ka kawo shi wajena domin mu cika burinmu
a kansa."
482
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda gama fadin hakan sai Sharlisa ta rungume
Shaddadu ta fashe da kuka saboda ba ta son
rabuwa da shi koda na tsawon dakika daya.
Al'amarin da ya karya zuciyar Shaddad ke nan
shi ma ya kama kuka. Sai da suka dade a
kankame da una sannan suka yi bankwana ta ba
shi Tsuntsunta na tsafi, ya hau kan tsuntsun ya
zauna.
Nan take tsuntsun ya bude fuka-fukansa ya
tashi da shi sama. Sharlisa ta daga kanta sama
tana kallonsu har sai da suka kule a cikin
gajimare sannan ta sauke kanta a lokacin da
hawaye ya zubo mata ta wuce kai tsaye izuwa
fada ta zauna akan karagar mulki aka ci gaba da
tafiyar da harkokin mulki kamar yadda aka
saba, wato ta rikewa Shadaddu karagar mulki
kafin ya dawo.
*******
483
TASKARNOVELS.COM.NG
A can dajin Rauful Mausur kuwa, Gimbiya
Ramlatul Siyam da mijinta Laffaru sun ci gaba
da rayuwa cikin matukar farin ciki da kwanciyar
hankali har tsawon watanni.
A sannan ne Ramlatul Siyam ta sami juna biyu,
al'amarin da ya jefa Laffaru cikin tsananin farin
ciki ke nan ya ci gaba da kulada Ramlatul Siyam
ainun har cikin na ta ya tsufa.
A ranar da cikin ya cika wata tara ciť nakuda ta
zo wa Ramlatul Siyam ta fara ihu da shureshure. Nan fa Laffaru ya dimauce ya rasa abin da
zai yi domin bai san ma yadda zai taimaka mata
ba ta haihun. Ana cikin haka ne kwatsam! Suka
ga Aljeni Maruful Dauwaz ya baiyana.
Nan take Maruful Dauwaz ya rinka umartar
Laffaru bisa yadda zai taimakawa Ramlatu
Siyam, shi kuwa sai ya himmatu yana mai bin
umarnin.
484
TASKARNOVELS.COM.NG
Duk da haka sai da ta shafe sa'a biyar tana
nakudar sannan ta haifo santaleliyar jaririya
mai tsananin kyau na ban al'ajabi. Aljani Marufl
Dauwaz ne da kansa yaje ya wanke jaririyar.
Koda ya dubi fuskarta sai ya ga a duniya bai
taɓa ganin mai tsananin kama da masoyiyarsa
Gimbiya Rashmin sama da wanann jaririya ba.
Nan take ya ji ya kamu da tsananin son jaririyar
kuma yaji kamar an yaye masa dukkan bakin
cikinsa naduniya. Nan take ya rungume jaririyar
a kirinsa ya fashe da kukan farin ciki.
(BARKA DA DAWOWA SADAUKIN SADAUKAI
BABBAN MASOYI GA GIMBIYA RASHMIN)
Daga wannan rana Aljani Maruful Dauwaz ya
zauna tare da su Sarki Laffaru a cikin dajin
Rauful Masnur ya taya su rainon jaririyarsu.
485
TASKARNOVELS.COM.NG
Da aka kwana bakwai sai aka radawa jaririyar
suna ZIYA'UL HAK.
Haka dai Laffaru, Ramlatul Siyam da Aljani
Maruful Dauwaz suka ci gaba da renon Ziya'ul
Hak har ta fara girma ta shekara bakwai a
duniya.
A wannan lokaci Ziya'ul Hak ta shaku ainun da
Aljani Maruful Dauwaz fiye da ma iyayenta
domin kodayaushe tana tare da shi dare da
rana. Sau tari sai ta yi barci a kan kirjin Maruful
Dauwaz sannan Ramlatul Siyam take zuwa ta
dauke ta ta kai ta cikin tanti ta kwantar da ita.
Lokacin da Ziya'ul Hak ta cika shekara bakwai
ne Aljani Maruful Dauwaz ya fara koya mata
yaki da kansa kuma ya dinga ba ta horon fada.
486
TASKARNOVELS.COM.NG
Kullum sai ya ba ta horon sau uku. Nan da nan
Ziya'ul Hak ta taso da gagarumar jarumtaka.
Tun ba ta fi shekara tara ba ta ke fita farauta
daji ita kadai ta kaso manyan dabbobin daji, sai
dai ka ga ta ratayo Zaki ko Damisa a kafadarta ta
zo gida da shi.
Shi kansa Aljani Maruful Dauwaz sai da ya cika
da tsananin mamaki bisa ganin irin tsananin
jarumtakar Ziya'ul Hak.
Babu abin da ya fi ba shi mamaki face karfin
gudunta, domin shi kansa da suka kasa tsere a
kasa, kasa wuce ta ya yi, nan take ta ba shi
tazara mai yawan gaske.
Sa'adda Ziya'ul Hak ta shekara goma sha takwas
a duniya sai karfin dantsen nata ya wuce gaban
misali, shi kansa Aljani Maruful Dauwaz idan
yana yaki da ita da kyar yake iya kare hareharenta. Akwai lokacin da ta doki kirjinsa da
kafarta guda sai da ya fadi can gefe guda ya ji
487
TASKARNOVELS.COM.NG
kamar janye shi aka yi da majajjawa aka kwala
shi a kasa.
Tun daga ranar ya dada sallamawa
jarumtakarta, domin in ban da Aljani
Sharkamuza da sadauki Najwar ba, to babu
wanda ya taɓa yi masa irin wannan duka sai
Ziya'ul Hak.
A ranar da Ziya'ul Hak ta cika shekara goma sha
takwas ne Aljani Maruful Dauwaz ya kira
Laffaru da Gimbiya Ramlatul Siyam gefe daya
suka kadaita ya shaida musu cewa jiya ya fita
daga cikin wannan daji na Rauful Masnur ya yi
rangadi a cikin daji na gaba.
Anan ne ya yi bincike ya gano cewa Shaddadu
ya girma ya zama gawurtaccen jarumi kuma
Sharlisa ta mallaka masa mashin Galilul Haras
ya fito farautar Ziya'ul Hak domin ya kashe ta
sannan ya zo har nan dajin Rauful Masnur ya
kama Sarki Laffari".
488
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan labari sai hankalin Laffaru da
na Ramlatul Siyam ya dugunzuma ainun.
Ramlatul Siyam ta fara zubar da hawaye ta ce,
"Yanzu ya za a yi mu yi maganin faruwar
wannanal'amari?"
Aljani Maruful Dauwaz ya yi ajiyar zuciya
sannan ya ce, "Hanya daya ce za mu bi mu yi
maganin wannan matsala.
Dole ne ita ma Ziya'ul Hak ta yi shiri ta tafi
farautar jarumi Shaddadu domin ta hallaka shi,
amma fa idan yana tare da Mashin Galilul Haras
ba ta isa ta iya yi masa komai ba, amma tunda
shi yaro ne ai mun fi shi wayo da dabara.
Ni zan yi wa Ziya'ul Hak rakiya a cikin wannan
tafiya domin na zamo mai ba ta kariya da
489
TASKARNOVELS.COM.NG
shawarwari akan yadda za mu sami nasara akan
Shaddadu koda kuwa zan rasa rayuwa ta.
Ku sani cewa wanzuwar Ziya'ul Hak a doron
kasa shi ne abin da ya hana ni kashe kaina,
saboda ta dauke mini kewar masoyiyata.
Yanzu sai ku shirya mana wannan tafiya ku yi
bankwana da ita."
Nan take Ramlatul Siyam ta kirawo Ziya'ul Hak
ta sanar da ita duk abin da ake ciki.
Ba tare da ɓata lokaci ba Ziya'ul Hak ta yi
bankwana da iyayenta tana kuka su ma suna
kuka suka rabu suna masu yi mata fatan nasara.
Nan take Ziya'ul Hak ta hau kan bayan Aljani
Maruful Dauwaz shi kuma ya bude fuka-fukansa
490
TASKARNOVELS.COM.NG
ya tashi da ita sama suka luluka a cikin
gajimare!
A nan muka kawo karshen littafin MAZAN JIYA
na uku (3)
*****************
WANNE IRIN BAKIN GUMURZU ZA A YI IDAN
JARUMI SHADDADU DA JARUMA ZIYAUL HAK
HAR SUKA HADU?
SHIN SHARLISA ZA TA CIKA BURINTA AKAN
SARKI LAFFARU?
YAYA KARSHEN RAYUWAR JARUMI SHADDAD
ZA TA KASANCE?
SHIN ZAI YI SOYAYYA KUWA A RAYUWARSA?
491
TASKARNOVELS.COM.NG
YAUSHE NE ZA A JI LABARIN SADAUKI HULKAS
NA BIRNIN ROMANIYA WANDA SHI NE CIKON
JARUMI NA UKU DAGA CIKIN MAZAN JIYA?
Mu hadu a littafin MAZAN JIYA 4 (Kashi na
hudu) don jin ci gaban wannan kasaitaccen
labari mai matukar kayatarwa.
Muna neman afuwa ga makaranta bisa tsayin
labari, hakan ya faru ne sakamakon tsayin da
hikayar take da shi.
Daga mai debe muku kewa a kullum da ko
yaushe.
ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI
(The King of Adventure Story)
492
TASKARNOVELS.COM.NG
Ni Maiboko, ina rokon makaranta wannan
gawurtaccen littafin, da mu yi kokari mu
tasirantu da kyawawan dabi'un da suka siffantu
a cikin wannan hikayar.
Mu kalli dalilan da suka sa Maruful Dauwaz ya
yi nisan kwana sannan kuma yake samun
nasara a kan duk abin da ya sa a gabansa,
sabanin gagarumar nadama da tashin hankalin
da sarki Lafaru yake a ciki
Rayuwar aljani Maruful Dauwaz abar nazari ce
da kwaikwayo duk da ta kasance a cikin hikaya
ne.
Aljani Maruful Dauwaz, yana daga cikin dalilan
da suka sa nake wannan posting ďin.
A karshe, yiwuwar cigaba da littafi na huďu na
alakanta hakan da lissafin lokaci.
493
TASKARNOVELS.COM.NG
494
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 18