Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sukayi dakin da sukajiyo ihun shaheeda suna shiga nanma sukayi mutuwar tsaye dakyar suka Hana najip dukansu anahaka Amjad yashigo da yan sanda yace yihakuri Yaya najip ga yansanda Nan zasubima hakkinka gaba dayansu akahada kansu da sauran abokan holewar tasu lokacin da zaashige dasu alhaji yace kutsaya yadaga Kai yakalli karima yacemata nasakeki saki uku abin da kikaimin Allah yasakamin yabimin hakki karima tadada sakin wanni kukan tace Dan Allah kayi hakuri karkamin haka Alhaji yace Daman Ni narasa tayaya na aureki yarcikina dake kinzo kin koranmin uwar yarana kinrabani da ita najip shima yakalli shaheeda yace kema nasakeki saki uku ga takardar results dinku da Dr yakawo dukanku kuna da ciki muna tayaku murna ke shaheeda kema kinsani zamana dake baabin da yataba shiga tsakanina dake Kuma da macan bani na aurokiba mummy ce yau naso ace tananan tagani da idanta abin da yafaru kekuma karima aje akaiwa hauwa'u jika gida tayi raino danwannan batarbiyar malam bace kinzubar da tarbiyir gidanku da mutuncin gidanku yansanda sukaja mota sukatafi dasu jiki amace suka dawo gida yasimee kuka kawai take se rarrashinta sukeyi Su najib atare sukace daddy yaushe zamuje wajan mommy mudau kota yace yanzu yamma tayi mubari gobe da safe dukanmu semu tafi sukace Allah yakaimu alhaji yace nifa mamakin tafiyar hajiya naja'atu kyauye nake Kuma kunce dakaina nakaita sukace eh daddy nansaka bashi labarin yanda akayi Alhaji hawaye kawai yakeyi daki alhaji yashege yakulle kansa yazauna Yana ta kuka WASHE GARI DA SASSAFe Alhaji da yaransa gaba daya sukadau hanyar zuwa grin bawo sun Isa lafiya sunkusa zuwa gidan su hajiya naja'atu sukaga wata Mata zani daban Riga daban mayafima haka takalmin yatsinke andaureshi da leda da kara akanta tana tafiya dakyar yasimee tace Allah sarki su Yaya kuga wata Mata dakara akanta mansur yace kyauye kenan inaga kobata da yarane take daukowa da kanta sukace Allah sarki Alhaji najinsu bece komaiba shi damuwa tayimasa yawa azuciya suna garasawa kofar gidan suka finfito zasu shiga kenan sukaga wannan matar da suka shige da Kara akai tazo itama zatashiga gidan Amjad yace lah kunga matar da muka shige ahanya itama Ashe Nan zatazo sukace waya gayamaka yace gatanan tataho zata shiga kubari tafara shiga tukunna semu shiga tazo shiga tana daga Kai takallesu kawai seji sukayi takira sunansu cikin kuka tayar da Karan dake kanta baki suka saki suna kallan ikwan Allah atare sukace wacece wannan kamar mommy tace nice Baku ganeniba ko tadada fashewa da kuka dagudu suka rungumeta Alhaji shima kukan yakeyi suna shiga cikin gida marka tajiyo kokekoke dagudu tafito daga daki tana tambayar lafiya dantajiyo Harda kukan hajiya tsayawa tayi cikin jinkunya yauga ga mijin hajiya naja'atu da yaranta sunzo wajanta hajiya cikin kukan murna takalli Marka tace matar baba Kinga ikwan Allah miji yau yazo wajan matarsa gayara suma sunzo ganin mahaifiyarsu marka takasa magana sabo da kunyar da takamata Hajiya tajasu tace kozo muje dakina sunashiga darawar jiki takade musu tabarmar da take kwana akai tace kuzauna cikin mamaki suka hada baki sukace mommy dagaske kike nanne dakinki dakike kwana tace eh menene sukace to Ina katifar da kike kwanciya akai cikin hawaye tanuna musu tabarmar da ta shinfida musu basusan lokacin da suka dada fashewa da kukaba sabo da tausayin mahaifiyarsu da sukeji aransu alhaji kuka shima kawai yakeyi dukunyar kanshi yakeji yau matarsace uwar yaransa abar kaunarsa itace cikin wannan halin adalilinsa sanadiyar auran da yakara Hajiya tace ku zauna fari a i ebo muku ruwa sukace aa mommy zauna kihuta atare su najip suka gaisheta cikin farin ciki taamsa tadaga Kai takalli alhaji tace sannu da zuwa Ina wuni kanshi asunkuye yakasa amsawa shikunyarta yakeji dasukaga haka mansir yaimusu Ido sutashi sufita suka tashi suka ce mubari muleka waje muga ko tsohunnan yadawo mugaisa semu shigo dashi tare sukai sauri suka fice Ita hajiya azuciyarta tinani takeyi ko haryanzu kamar Dane tace dama danake fes yakini bare yanzu kanta asunkuye se hawaye takeyi sejitai alhaji ya rungumeta yace naja'atu kiyafemin Dan Allah duni najamiki halin da kike ciki tace bakomai alhaji Ni alheri hakan ya zamemin karka damu Nima kayafemin kusan nice silar komai Sallamar babanta dasu yasimee sukaji dasauri alhaji ya amsa harkasa alhaji ya gaisheshi cikin fara'a yaamsa su Amjad se tsokanar kakansu sukeyi Malam bukar baban hajiya yace jikokina sungirma naji dadin ganinsu nayi mamaki dasuka ganeni Atare su najip sukace haba tsoho Kuna kama da mommy fa aidole muganeka Nan alhaji yaimasa bayanin Sunzo tafiya da hajiya naja'atu baban hajiya yace to dama tini tagama karbar maganinta tawarke tinda tazo basu tashiba yace Amma kwana zakuyi alhaji yace yau zamu tafi baba ai zamudawo kwana zamuyi inmunzo yace ga yaranan yanzu sunsan garin ,zakaringa ganinsu akai akai marka tinda tashige daki Bata Kara fitowaba sabo da kunya dakansa malam yace Wai inana markane Hajiya tace tana daki yakwalla Mata Kira tafito Kai asukunye Nan su yasimee suka hau tsokanarta haba tsohuwa daga ganinmu seki shige daki kobakiyi murnar ganin jikokinkin nakiba tace haba aa nayi murna Daman yanzu zanfito mugaisa . itadai hajiya dariya kawai takeyi Hajiya tace Bari naje nashirya naimaza naje nai sallama da malamarmu dasauri yaran sukace mamala Kuma taidariya tace eh Se yamma suka taho bayan alhaji yacikasu da abin arziki marka dukunya takama ta su najip da zasu taho sukabata kudi sukace tsohuwa gashi ajajari bakihar kunne se murna take akunyace take nunawa hajiya tai dariya tace inaruwana keda jikokinkiki nansuka rabu cikin farin ciki suka dawo gida Bayan sundawo da kwana biyu hajiya naja'atu tahuta suke mata bayanin abin da yafaru bakaramin tashin hankali tashigaba da Al ajabin abin da su shaheeda sukayi Nan take cewa najip yayafe Mata yaje yanemo Yar gidan mutunci a auramasa baruwanta da arziki tace yanzu nagane meye duniya nagane da rajar Dan adan badan komaiba wannan abin da yafaru Dani yazamemin alheri arayuwata Nan take fada musu rayuwar da tayi akyauye sunji tausayina sosai Harda kuka Tace yanzu inasu karima suke Nan suke fada Mata haryanzu suna wajan yan sanda Hajiya tace Amjad kar ayihaka asakesu sukoma wajan iyayansu shaheeda da karima iyayansu koba komai kawayenane itakuma karima kodan mutuncin mahaifinta Nan Amjad yakira abokinsa dansandan da maganar take ahannunsa yace yasakesu sutafi gida zasuje gida ayimaganar yacemasa to Alhaji da lokacin yafito daga daki duyanajin hirar da sukeyi yace hajiya kishirke keda najip muje gidan su karima Hajiya tace to sukafito zuwa gidan su karima lokacin karima tadawo gida agala baice seda tazo gida takarbi kudi gurin malam tabame motar da yakawota lokacin malam nakofar gida shima yatsorata dayaga karima tambayarta yake meyafaru sekuka take taki magana anahaka sega motar su hajiya naja'atu tatsaya akofar gidan dagudu karima tashiga cikin gida tana kuka lokacin yan gidan duka sunanan sunata Hira atsakar gida sukaga karima tashigo da gudu tana kuka atare sukahau tambayarta meyake faruwa se sallamar hajiya naja'atu sukaji umma da tafito daga daki nantarude tana rawar baki tana nuna hajiya naja'atu da hannu tace naja'atu kece hajiya tai dariya tace hauwa'u kenan nice umma tayi mutuwar tsaye Mami tacemata hajiya karaso sannu da zuwa malam da su alhaji atare suka shigo suma Nan umma da karima suka Kara rudewa umma tarasa meyake faruwa malam yace alhaji kuzauna gawaje bayan sunzauna su Adam suka gaigaishesu Nan malam yafara magana yace alhaji abin da yasa nacema mushigo cikin gida sabo da iyalina duka sunanan Kuma inaso kaimin bayanin meyake faruwa agabansu Nan alhaji yayiwa su malam bayanin abin da yafaru tindaga farko harkarshe karima nagefe tamakure waje daya sekuka take bakaramin tashin hankali suka shigaba gaba dayansu sunkasa cewa komai kowa ya girgiza da maganar Nan alhaji yakecewa ga takardar sakinta tin alokacin nasaketa saki uku umma jiki yamutu sezarzare Ido take Alhaji yace malam muzamu koma sewani lokacin akunyace malam yafito yaraka su alhaji malam yaitaba alhaji hakuri Bayan suntafi malam yashigo gida Yana shigowa yanemi waje yazauna yafashe da kuka hauwa'u kuncuceni keda karima Malam yadafe kirjinshi Yana tatari yakasa karasa maganar da yakeyi nanan su Mami suka rude suka yokansa dagudu suna Kiran sunanshi New writer's Hakan Take *Husba'ahfama* 😍❀🀩 *'YAR kwalliya*β€πŸ’‹ πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ’„πŸ’… *HEEDAYA* πŸ’…πŸ’„ *( I KIRARI)* πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  Written by *husba'ahfama* *IG officiall_husba'ahfama* Facebook *Real Husba'ahfama* Follow me on Wattpad *@Real Husba'ahfama* 60-61 Sunakiran sunanshi malam lokaci guda yafita haiyacinsa dagudu suka daukeshi zuwa asibiti likitoci suntaru akansan danceto rayuwarshi Lokacin da malam ya farfado sesannu iyalinsa sukemasa idanshi arufe hawayene kawai yakefita a idanunshi yaki yaimusu magana Nan Dr yashigo yace yana bukatar hutu abarshi yahuta kowa yafita abar mutum daya awajansa Umma da kareema sunkasa binsu asibiti agida akabarsu suna fita umma tayo kan kareema tarufeta da duka dukanta take idanta yarufe kareema kincuceni kingama dani nashiga uku Ni hauwa'u yazanyi dakaina da wannan abin kunyar da kikajamin dawana idan zankalli yan gidannan musamman hafsa da heedaya uwa uba Kuma mahaifinki kinsan in yawarke bazamuji tadadiba agidannan narufamiki asiri nanemomiki gidan da Zaki huta gashi kinjawa kanki kinfito daga gidan tadada fashewa da kuka tace oni hauwa'u yaunice akakawowa cikin shege gida wlh kozaki mutu se anzubar da cikinnan Dan wannan abin kunyar yamin yawa heedaya da itace yadace tashigo da cikin shege gida Bata shigo da shiba seke da kike da aure waiyo Allah Ni hauwa'u kareema kincuceni kingama dani du gatan da na nunamiki abinda Zaki sakamin dashi kenan Kareema nishi kawai takeyi tana fitar da numfashi dakyar kukanma takasa damuwa da danasani sunmata yawa azuciya ga azaba da jikinta yakemata Atsakargida umma tabar kareema tashiga daki kuka kawai take rusawa tarasa tinanin da zatayi Lokacin Mami da heedaya suka shigo sunbar mazan a asibiti sunyi sallama bawanda ya amsa nansukaga kareema akwance da sauri sukayo kanta heedaya nakuka tace anty kareema mekike anan kishiga daki kowankama bakiyiba Bari nadora Miki ruwan wanka heedaya ce tahada Mata ruwan wanka takaimata tayi wankan Nan heedaya tace anty kareema meyasa kika jamana abin kunya Kika zubarmana da mutuncin gidanmu kinjamana taban da bazetaba gogewaba a idan mutane kinjefa Abba awani hali yanzu kinsan halin da mukataho muka barshi a asibiti kinsanme likitoci sukace akanshi Kareema tace kuyi hakuri heedaya wlh shirrin shedanne niyanzu bansan dawana idan zankalli Abba ba Dan Allah heedaya karkubari Abba yakoreni Dan Allah kutayani bashi hakuri tadada fashewa da kuka Mami najinsu itama hawaye take tayi azuciya Mami tace Allah kenan danhaka bakyau kanajawa danwani alkaba i inkayi kanka yake dawowa hauwa'u baabin da bakiceba akan heedaya gashi Allah yakareta seakan yarki abin yakoma Allah kadada shiryamana zuria karabasu da shirrin zamani Heedaya takalli Mami tace Mami tinani. Mekikeyi Mami take bakomai heedaya kamata kirakata daki Wai kareema Ina hauwa'u tace tana daki Mami tace au dama tananan tabarki atsakargida awannan halin Heedaya da kareema nashiga dakin umma ta dakamusu muguwar tsawa Umma take kebakar muna fuka karnaga kafarku anan hardawani rikota burunku keda uwarki yacika kunmata asiri tadauko abin kunya kekuma kareema wawuya harkinmanta suwaye heedaya da hafsa kika saki jiki dasu to in bakisaniba murnasuke azuciyarsu danhaka kikoma wajansu bazaki kwanarmi adakiba nabarwa hafsa me Kareema tace Dan Allah umma kiyi hakuri karkimin haka karki gujeni awannan halin da nakeciki koma meye dasu umma susuka temakamin daki fa kikashige gashi kogurin Abba kinki zuwa Kuma kojikinsa kinki tambaya Kuma mumuka jamasa halin da yakeciki ayanzu Umma tace shikenan wlh dagaskene sun aikaceki sun juyarmiki da kwakwalwa toseki koma wajansu barikuga mezanmuku karku fitarmin daga daki da sauri heedaya tadada kama kareema takaita dakin Mami sunashiga kareema tanemi waje takwanta tarasa meyake Mata Dadi du maganar da umma takeyi Mami najinta taimata shuru itama daki tashige tasamu kareema nata kuka heedaya na rarrashinta Nan Mami tahau yimata nasiha har hankalinta yakwanta taishuru Su alhaji da sukabar gidansu kareema katsaye gidansu shaheeda suka wuce sukasamu manaifan shaheeda suka yimusu bayanin abin da yafaru Nan Babar shaheeda tahau borin kunya tana cewa bahalin yarta bane Nan baban shaheeda yadaka Mata tsawa yace nasan zaarina yanda Kika Bata tarbiyaarta kituna komainisan jifa kasa zedawo kisani Allah yakubutar Dani daga sihirinki nayi shurune kawai nabarki azaman azirin dakikemin Yana tasiri ajikina koke hajiya naja'atu kinsan komai wani lokacinma har nasiha kike Mata yan uwana nane sukadage da addu'a da magani Nan alhaji ibirahim gadara yabashi hakuri suka yimusu sallama baban shaheeda yaba najip hakuri akan abin da yafaru Nan yarakasu har mota Baban shaheeda nakomawa gida Yace shaheeda banga lefinki sosaiba kowana hali Kika shiga mahaifiyarki ce taja miki Nan ya daga Kai yace asabe asirin da kikaimin yakarye Kuma yanzu kullin inacikin azikar danhaka kokinyi wani sihirin baabin da zesameni insha Allah danhaka zanmiki albishir nafarko nadade da Kara aure harta haihu yanzu Haka dawani tsohon cikin ajikinta jikinta Sekuma albishir na karshe kije nasakeki saki daya Kuma adalci daya zanmiki kizauna agidannan keda yarki bazan korekiba darajar haihuwar da mukai dake nabarki agidana tintini duwani abunawa me mahimmanci nadaukeshi nakaishi gidan da matata take aciki Dan Haka Kinga tafiyata Sabo da tsabar rudanin da hajiya asabe Babar shaheeda take ciki yanke jiki tayi tafadi ko motsi batayi shaheeda batasan lokacin data kwalla ihuba mommy kitashi Dan Allah daddy kayi hakuri kar kaimana Haka daddy Kojuyowa beyiba yana kuka azuciyarshi yace zandawo wajanki shaheeda sekingane menene duniya tukunna se babarki tayi nadamar abinda take aikatawa yashiga mota yai tafiyarshi BAYAN kWANA UKU Ansallami malam daga asibiti alhamdulillah yasamu sauki tinda akakai malam asibiti umma da kareema basujeba su Mami ne suke tazarya haryau da aka sallameshi umma nadaki sejitayi ana sallama Harda muryar malam Nan umma tadora hannu aka tace nashiga uku shikenan malam yadawo yasamu sauki wlh yau baze barmuba seyadau mataki akanmu Malam Yana shiga dakinsa bayan yahuta yakira iyalinsa duka kowa yazo Amma Ban da umma da kareema Nan malam yace su hauwa'u basa nanne Adam yace sunan Abba Malam yace jeka Kirasu Kuma kagaya musu karsu Dade inba hakaba ransu zebaci Adam nashiga cikin umma yafara Kara Nan Adam ya gayamata sakwan malam yaleka dakin Mami yakira kareema tinda malam yadawo umma take zaryar bandaki gudawa takeyi Kiran da malam yaimusa yanzu cikin yadada rudewa jiki amace umma tashiga da sallama abakinta kowa yaamsa Mata Amma ban da malam kareema da tashigo kanta asunkuye tamakure guri daya Nan malam yaigaran muyar kowa yaishuru Yana sauraran mezece New writer's Hakan take *Husba'ahfama* 😍❀🀩 *'YAR kwalliya* β€πŸ’‹ πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ’„πŸ’… *HEEDAYA* πŸ’…πŸ’„ *(I KIRARI)* πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  Written by *husba'ahfama* *IG officiall_husba'ahfama* Facebook *Real Husba'ahfama* Follow me on Wattpad *@Real Husba'ahfama* GABADAi GABADAI GIDAN BARDEπŸ‘πŸ‘Œ Allah🀲 yakareku Allah 🀲yadada daukakaku anakinku Allah nasanku🀣kunza ciwan Ido sehakuri🀣bayanda zaaidaku hm Dan adanπŸ€”abin tsoro Allah 🀲kadada karemu daga sharrin masu sharri Ameeen summa ameeen WANNAN SHAFIN NAKUNE GIDAN BARDE Nasadaukar da shi gareku Ina kaunarku sosaiβ€πŸ˜πŸ˜˜πŸ‘Œda sosai Allah ya kareminku 😘❀ 62-63 Malam yace bakomai bane yasa nataraku anan se akan abin da kareema tajawa gidannan tazubar Mana da kimar gidannan da mutuncina dakomai Ni yau Yar Dana Haifa ta aikata wannan badalar balefin kowa bane hauwa'u lefinkine danhaka tare Zan hukuntaku Kinga ikwan Allah hauwa'u ba abin da bakiceba akan heedaya Amma segashi duabin da kikafada Akan kareema ya faru ita heedaya Allah yakareta Danhaka seyazama darasi awajanki Yar makaranta budurwa batadauko cikin shegeba takawo gidan ubanta se Wanda Bata zuwa Kuma matar sure ita tadauko cikin shege takawo gida doka tafarko banyarda kodawasa kokuma kinasane kiyi yunkuri zubarwa da kareema cikin jikinta wlh wlh inhar haka tafaru hukuncin da zan yanke Miki konace muku bazakuji da dadiba Dan wlh hardaureku senayi dasauri umma da kareema suka daga Kai suka kalli malam sukaga bawasa afuskarshi maganar da yake fada dagaske yake zeaikata dasauri suka sunkuyar da kansu Malam yacigaba da cewa sedoka tabiyu kafinnan kafin dare kugaugauta barmin gida duwani Abu da kukasan nakune kukwashe inhar kukakai dare agidannan zanmuku korar wulakanci Wanda Baku taba zatan zanmukuba umma tafashe da kuka shikenan malam inka koremu inazamu kasan komai wajanwa zandosa adangi Dan Allah Dan annabi malam kayi hakuri kayafe Mana sharrin shedanne kusa baki su Adam kunaji zaakori uwarku kunki magana Dan ubanki kareema kibashi hakuri tadada fashewa dakuka su Adam zasu bawa malam hakuri yaimaza yadaga musu hannu yace baruwanki duwanda yai magana ranshi zemugun baci kareema in Banda kuka baabin da take tace Dan Allah Abba kayi hakuri nagane kuskurena kayafemin Dan Allah karka koremu wlh bazan karaba yadaka Mata tsawa yace karna karaJin muryarki bazanmiki bakiba Allah yashiryeki kutashi kubani waje wannan shine hukuncin da nayanke Kuma kisani hauwa'u wannan lokacin kowa kikakira bazantaba saurararshiba yakalli su heedaya yace kutashi kotafi Allah yaimuku albarka dujikinsu amace sukatashi sukabar dakin se Mami datakasa tashi umma nagefe tana ta kuka tadaga Kai takalli Mami tace kinkisa baki sabo da kinamurna zanbarmiki gidan ko Mami tace nibana murna Dan zakibar gidannan insha allahu bainda zaku malam yace hauwa'u kitashi kibarmin gidana kafin raina yakara baci dasauri tatashi tabar dakin tana kuka Mami takalli malam tace haba malam inrai yabaci hankali ake nemowa Dan Allah kayi hakuri yanzu inka koresu inazasu da wannan cikin kaga mundada tonawa kanmu asiri insukabar gidan hannunka baya rubewa kayanke kayar kayi hakuri Dan girman Allah kayafe musu kabarsu da wannan kaddarar da tasamesu yace hafsa bazaki ganeba kema kinsan nadade inahakuri da hauwa'u dufitinar da takeyi agidannan nasani kawai inashurune kozata gane gaskiya tinda taki ganewa Dole tabarmin gidana sujecan suraini cikin Amma baanan gidanba kema karna batamiki ranki kitashi kibani waje zanhuta Dole Mami tabashi waje takoma daki tasamu su Adam jiki mace tashiga ta zauna su heedaya sukace Mami yanzu meye abinyi ran Abba yabaci sosai wlh baze sauraremuba munsan kema kinbashi hakuri yakiyarda Mami tace mubari yahuce kafin dare semu dada bashi hakuri Sukace to Allah yasa yasauraremu Umma da kareema Banda kuka baabin da sukeyi adaki umma tace shikenan kareema Kinga abin da kikija Mana yanzu wajanwa zamudosa dawannan abin kunyar Koda danatafi lokacin Yana rashin lafiyarnan dannasan kina gidan alhaji zakisa yasayamin gidan da,zan zauna shiyasa Amma yanzufa wanake dashi bani dakowa mahaifana sunrasu saura yan uwana sumakuma bawani shirimuke dasuba kiga abin kurya da Kika jamana gaban su hafsa Kuma kinsan makiyanmune su basa kaunarmu gasharadin da yakafa karna kiramasa kowa yanzu yazanyi sekitashi muhada Kaya yanzu ko yankunne da sarkarki na daham zamu Saida baze sayamana gidaba sedai mukama haya ita kareema taki cewa komai hawayene kefita daga idanta Mami ce takira aminin malam awaya Dan Allah yazo wata matsalace take faruwa dasauri malam lawan yazo gidan bayan sungaigaisa yake tambayar Ina umma Nan Mami tace Daman akantane muka kiraka katayamu bawa malam hakuri malam lawan yace meyake faruwa Kuma Nan Mami tafada Masa hukuncin da malam ya yanke Amma Bata fadamasa abin da kareema taaikataba Aminin malam yace haba habakaikuwa Dan uwana aminina wannan hukuncin da kayanke yayi tsauri da yawa yanzu insuntafi Ina kakeso suje Dan Allah kayi hakuri kabasu dama takarshe nanemi wannan alfarmar takarshe akansu yace Wai Ina hauwa'u ne tazo itama Mami ce taje takirata tazo Nan yadada mata.fada yace tadada bawa malam hakuri Kuma Dan Allah kartakuma dakyar malam ya hakura bayan malam lawan yatafi Nan malam yace dokar da zandada samuku nafarko maganar zubar da ciki korashin lfy kareema tayi akaje asibiti akaduba akace waniabu Tasha daniyar zubar da ciki nariga nafada Miki abin da zanmuku Kuma daga yau bani bake ki harkarki naitawa kina zaunane darajar yaranki da aminina dawasa naji wata fitina tatashi agidannan niji da sahannunki wlh sekin barmin gidana har abada Nan tadaga Kai tana kallan malam taga tsanarta karara a idansa batasan lokacin da tadada fashewa da kukaba tace insha Allah baabin da zefaru nagode yace Kuma naji korar da kikayiwa kareema daga dakinki baki isaba dolane takoma dakinki tinda yarkice kije kitayata rainan cikin Kuma tahaifo kiraini jikanki seyanzu Zaki sakarwa hafsa ita yanzu tinda tadauko abin kunya keinkina da kunya Zaki kora kareema dakin hafsa keda kike da tarbiya Kika iya koyarda ita ai bakyakaita dakin da zata lalaceba tinda baabin da baki fadaba akan hafsa da yaranta musamman heedaya yanzu Dan Allah bakiji kunyarsuba jiki amace tatashi tatafi daki tanafitar da hawaye Bikin heedaya nata matsowa su Mami se shiryeshirye akeyi Wanda zaabawa heedaya koyazo bawata hirar arziki bace take shiga tsakaninsu kawai tana fitane danbiyaiyar mahaifinta Amma bawai Dan tana sansaba tana fitane Danta farantawa mahaifinta Rai SAURA sATI DAYA BIKIN HEEDAYA Sukawayi gari da rasuwar mijin da zata aura sanadiyar ciwanciki lokaci daya kafin akaishi asibiti Allah yakarbi ransa bakaramin tashin hankali mahaifan yaran sukashigaba da labarin rasuwar yazowa su heedaya da mahaifanta bakaramin tashan hankali suma suka shigaba hankalinsu yatashi sosai ko heedaya mutuwar ta girgizata Mami tace kekuma heedaya kandarar da tasameki kenan in har lokacin auranki yazo sewata kandarar dazo tashige taciki Allah ya jikan yaran kekuma Allah yaimiki zabin alheri tace ameeen Mami Ali dasu Adam adakin Mami suna hira heedaya sukaga tadaga Kai sama tana ta murmushi Adam yace ikwan Allah heedaya tinanin mekike Haka Harda murmushi tace wlh Yaya waniabu natuna yace meneneshi tace tinani nayi tinda Wanda Zan aura yarasu shikenan yanzu Abba zekyaleni nacigaba da karatuna kaga daganan har Allah ya kawomin Wanda nakeso yace hm heedaya kenan waiharkin manta Abba baya magana biyu inyafadi Abu seyacika to wlh kidena murna dakuma wannan tinanin tinda kikaga haryanzu bece komaiba kumayau saura kwana uku bikin da Allah yanufa yaran nadarai wani ikwan Allah ranar sadakar bakwansa shine ranar daurin auranku dayana raye kijira kiga me Abba zeyi ranar kedai kawai muyita addu'a Allah yaimiki zabin alheri allah yafimu sanin meyake faruwa Nan jikin heedaya yamutu gaba daya ali yace wlh Yaya dazu Abba yana waya damasu yimata Kayan daki suna fadamasa sungama dasauri heedaya tace Dan Allah mekaji yace Kuma Yace aa nibangama jinsuba nashigo gida Rana Bata karya sedai uwar Diya taji kunya yaune sadakar bakwan yaran da zaa aurawa heedaya akofar gidansu heedaya akayi sadakar bakwan mutane suntaro sosai bayan angama addu'a gawanda yarasu har mutane sunfara tashi akai sanarwa kowa yakoma yazauna akwai daurin aure Andaura auran heedaya Akan sadaki nera dubu dari buyu dakyar malam yayarda da sadakin da akawo cewa yayi kudin sunyi yawa mahaifin yaran ne yace kudin basuyi yawaba ayi hakuri akarba Haka sukainiyar bayarwa su aganinsuma yayi kadan Dan karsu bada dayawane ace yayi yawa shine sukaba da dubu dari buyu Su mami dasu heedaya suna daga cikin gida sukajiyo sanarwar daurin auran heedaya kowa yayi mamakin sunan angwan da akakira da sunan mijin heedaya bakaramin kaduwa su Mami sukayiba harta kareema da umma dasukaji sunan angwan Dana mahaifin angwan sungirgiza dajin sunan Heedaya tadada kasa kunne taji sunan Wanda akekira taji shidinne mijin da aka auramata Nan kunnanta yajiyo Mata hakane wani irin ihu heedaya ta kurma tafadi kasa sumarmami New writer's Hakan Take *Husba'ahfama*😍❀🀩 *'YAR kwalliya*β€πŸ’‹ πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  πŸ’„πŸ’… *HEEDAYA* πŸ’…πŸ’„ *(I KIRARI)* πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘  *IG officiall_husba'ahfama* Facebook *Real Husba'ahfama* Follow me on Wattpad *@Real Husba'ahfama* 64-65 Dagudu su Mami sukayo kanta arude Mami tace kubani ruwa anabata tayaiyafamata taja dogon numfashi tabude Ido ahankali takalli Mami tace

Chapter 13 of 21