Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yarima yazid ya numfasa yace aini yadda nake tsoron Ardadu bana tsoron makiyan namu musamman tun daga lokacin dakayi mini karin bayani akansa,kasan sharrin wanda ke tare dakai yafi na wanda ke nesa dakai saboda shi yasan sirrinka.Cikin alamun mamaki zainur ya dubi yazid yace yanzu kana nufin kace dani duk da cewar ka yankewa ardadu hannunsa guda zai iya sake yi maka laifi ko kuma yaci amanarka? Yazid yace kwarai ma kuwa kasan ance ba'a yabon dan kuturu da yatsa har saiya girma sannan anan za'a fuskanci cewa abin duniya yafi komai muhimmanci a cikin zuciyarsa don haka yana da kyau mu zuba ido akan Ardadu. Yanzu dai tunda har yanzu bai dawo ba kawai mu tashi mu tafi ya iskemu a can masaukina.Gama fadin hakan keda wuya sai suka mike tsaye domin su tafi kawai sai suka hango Ardadu daga can nesa kadan ya durfafo su dauke da akushin abinci kuma fuskarsa cike da annuri.Koda ganin haka sai yarima zainur ya bude baki ba tare da ya kallo yazid bayace jikina ya bani cewar akwai wani mugun abu wanda wannan yaron naka ke shirin kullawa koma ya shirya shi domin bai kamata muga annuri akan fuskarsa ba alhalin ya bata mana rai bisa dadewar da yayi bai dawo ba. Sai mun fara samun ishash shen comment kafin mu kara yawan rubutu. WASIKAR JINI!!! Littafi Na Biyar (5) Part B . bai kamata muga annuri akan fuskarsa ba alhalin ya bata mana rai bisa dadewar da yayi bai dawo ba. Yarima Yazid yace nima dai naji hakan a jikina domin masu iya magana sunce ruwa baya tsamin banza. Lokacin da Ardadu ya iso gabansu yarima yazid saiya ajiye akushin a gabansu yana mai sunkui da kansa kas yace,ya shugabana ka yafeni bisa dadewar danayi ban dawo ba hakan ta faru ne sakamakon karancin irin abincin da kuka umarceni da siyowa a cikin wannan kasuwa.Koda jin haka sai yarima yazid yayi murmushi maimakon ya nuna fishinsa yace aini kaina nasan cewa hakan zata iya faru,yanzu dai sai mu zauna mu hanzarta cin wannan abinci kafin lokacin rufe kasuwa yayi domin rana na daf da faduwa. Ba tare da bata lokaci ba kuwa suka zauna sukaci wannan abinci su ukun,koda suka kare suka sha ruwa sai suka mike suka kama hanyar fita daga cikin kasuwa,suna cikin tafiya ne yarima zainur ya dubi yarima yazid yace yakai abokina inason yanzu mu wuce izuwa gidanmu ka kwana wajena,kuma na gabatar dakai a wajen mahaifina.Koda jin wannan batu sai yarima yazid ya dubi yarima zainur cikin mamaki yace haba yakai abokina me yasa kake son ka dorawa kanka wahala,ai kawai ka kyale mu mu karasa kwanakin da zamuyi a kasuwar nan tundai muma muna daf da barin garin.Yarima Zainur yace haba ai abin kunya ne a gareni ace na kasa baka masauki na barka a gidan haya cikin kasuwa alhalin yanzu ji nake kamar mun shafe shekaru masu yawa muna yin wannan abota,zanyi matukar bakin ciki idan har baka karbi wannan tayi nawa ba don haka yanzu zamu wuce ne izuwa masaukinku domin ku debo kayanku mu wuce izuwa can gidanmu. Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube Ardadu a cikin ransa bisa cewa komai zaizo masa cikin matukar sauki tunda dama baisan hanyar da zaibi ba ya sami damar kusantarsa ba,shi kuwa yarima yazid saiya nuna ko kadan baya son yaje ya kwana gidansu zainur saida zainur ya matsa masa. Haka dai suka karasa masaukinsu yazid,yarima zainur ya nemo mai amalanke aka kwaso kayansu gaba daya suka nufi gidan sarkin yaki haiman. Da isowarsu gidan sarkin yaki aka bude musu kofa suka shige ciki nan take zainur ya kirawo hadiman gidan suka kwashe kayansu yarima yazid aka tafi dasu izuwa dakinsa sannan yaja yazid da ardadu suka nufi cikin babban falo na gidan. Da shigarsu sai sukayi arba da sarkin yaki haiman kwance akan doguwar kujera likita na dinke raunika a jikinsa a gefe daya kuma matarsa ce a zaune ta hada kai da guiwa tana kuka.Cikin firgici da dimauce yarima zainur ya ruga inda haiman ke kwance ya kama hannunsa ya rike a lokacin da idanunsa suka ciko da kwallah yace yakai Abbana wanene yayi maka wannan danyen aiki,ka gaya mini ko waye naje na yakeshi.Koda jin wannan batu sai Haiman ya mike da kyar cikin matukar karfin hali ya dubi yarima yazid da ardadu sannan ya dafa kafadar yarima zainur yace haba yakai dana menene sabon labari don ka gannin a cikin wannan hali,wadansu dakarun sumame ne suka kawo min hari harna fafata ™Abbas Abdulkadir hada hada™ kazamin yaki dasu da kyar na tsira da rayuwata saboda karfinsu da kuma yawansu,amma basu sami damar kashe ni ba. Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa yarima zainur wani irin bakin ciki ya turnuke shi ya rungume haiman a kirjinsa yace yakai abbana gwara ace tsautsayin akaina ya faru.Lallai koma dadewa saina dauki fansa akan wannan mutane. Dajin haka sai haiman ya janye jikinsa daga cikin na zainur ya dubi yarima yazid da kyau sannan ya dubi Ardadu yace ina ka samo wadannan manyan baki haka? Koda jin wannan tambaya sai yarima zainur ya kwashe labarin yadda ya hadu da yarima yazid ya zainyanewa haiman ba tare daya boye masa komai ba. Koda jin wannan labari sai haiman ya dubi yazid cikin farin ciki yace tabbas muna da babban bako yau a gidannan, Ummul Zainur ai sai kije a fara shiryawa bakinmu abincin dare,kai kuma zainur saika kai abokin naka dakinka domin su huta. Ba tare da wata gardama ba kuwa sai matar haiman ta mike tsaye cikin murna ganin yadda haiman din ya sami karfin jikinsa harya iya mikewa zaune yake magana,ta tafi izuwa dakin girki domin ta fara shirya abincin dare suma hadiman gidan kowannensu ya shiga aiki na musamman domin karrama wannan baki. Bayan yarima zainur yakai yazid da ardadu dakinsa sun shirya kayayyakinsu saiya barsu a dakin ya koma can wajen haiman domin ya kara ganin yanayin jikinsa.Yana zuwa sai ya iske haiman ya sallami likita ya tafi kuma yana zaune yana shan wani ruwan magani a cikin kofi.Da shigowar zainur sai haiman ya dubeshi cikin alamun tsananin damuwa ya yafitoshi da hannu,cikin sauri da kaduwa zainur ya taho gareshi ya zauna daf dashi.Haiman ya dubeshi yace shin kasan sarauniya Lazwara? Koda jin wannan tambaya sai zuciyar yarima zainur ta buga da karfi ya sunkuyar da kansa kas yayi shiru kamar bazai ce komai ba amma daya tuna cewa bai taba yiwa haiman karya ba saiya dago kai ya dubeshi yace nasanta,haiman yayi ajiya zuciya yace itace ta ceci rayuwata daga hannun dakarun sumamen da suka kawo mini hari,kuma tace na gaya maka cewa kada ka dogara da abokinaka wato wannan bako da kazo mini dashi domin bazai iya taimakonka ba bisa abinda kasa a gabanka,lallai ka koma gareta kamar yadda kukayi alkawari domin ta karasa taimakon da tayi niya a gareka. Bana son komai dangane da abin dake tsakaninku ko abinda kake shirinyi ba amma dai kada kayi gaggawa a cikin dukkan sha'aninka ka tsaya kayi tunani mai kyau domin ka yankewa kanka hukuncin dazai amfaneka. Lokacin da sarkin yaki haiman yazo nan a cikin zancensa sai kan yarima zainur ya kara daurewa ya rasa ma abinda zaiyi. Daga can sai yayi ajiyar zuciyar ya dubi haiman yace yakai abbana kasha gaya mini cewa abinda babba ya hango yaro ko ya hau tsauni bazai hangoshi ba,yanzu a matsayinka na wanda ke gaba da ni wace shawara zaka iya bani akan wannan al'amari? Sa'adda haiman yaji wannan tambaya sai shima ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubi zainur cikin nutsuwa yace yakai dana kayi sani cewa wannan al'amari naka babbane kuma baya bukatar gaggawar yanke hukunci,ka sani cewa ina hada idanu da wannan abokin naka naji jikina ya bani cewa mutum ne mai daraja sosai wanda zai iya yin abin al'ajabin da ba'a taba zato ba.Na sani cewa itama sarauniya Lazwara tana da matukar amfani a garemu baki daya,kuma tana da abubuwan al'ajabi amma idan zaka iya auna wadanann mutane biyu a sikeli kaga wanda yafi nauyi a cikinsu saika sallama komai a gareshi,ko kuma kaje ka kwanta da wannan matsala a rana wanda duk kaga yazo maka a cikin mafarkinka a tsakanin yazid da sarauniya lazwara shi zaka mika wuyanka.Koda jin wannan batu sai yarima zainur yayi ajiyar zuciya yace nagode ya abbana lallai zanyi aiki da wannan shawara taka.Har zainur ya mike tsaye zai koma can dakinsa wajen su yarima yazid sai haiman ya ruko hannunsa ya zaunar dashi suka fuskanci juna yace dashi,kayi hankali da wannan bawa na yarima yazid domin akwai alamun butulci a cikin idanunsa gami dason abin duniya zai iya cin amanarku a ko yaushe don haka kusa ido akansa.Cikin alamun matukar mamaki zainur ya dubi haiman yace yakai abbana yaya akayi kasan wannan al'amari? Kasani cewa hatta yazid dani babu wanda ya yarda da wanann mutumin kuma ada can baya tsohon danfashi ne. Yarima Yazid shine yaci shi da yaki har yasa shi ya karbi addininsa amma duk da haka saida ya aikata laifin sama shi kuma ya yanke masa hannunsa guda a matsayin hukuncin satar.Koda jin wannan batu sai haiman yayi dan gutun murmushi yace ai kuwa shi hali zanen dutse ne idan wannan bawa yayi wasa sai yarima yazid ya sake yanke masa daya hannun nasa ya zama cikakken musaki.Nan dai yarima zainur ya mike tsaye ya koma can dakinsa yana zuwa ya iske yarima yazid da ardadu suna gabatar da sallar magriba don haka saiya koma gefe daya ya zuba musu idanu yana kallon yadda suka gabatar da ibadar tasu. Koda ya zuba ido yana kallonsu cikin nutsuwa yana nazarin yadda sukeyin ibadar sai yaji abin ya birgeshi matuka,ko da yarima yazid ya dago daga raka'ar farko ya fara ta biyu yana mai karanta suratul fatiha da suratul ikhlas sai yaji tsigar jikinsa ra tashi gaba daya,yanayin kalmomin na Al qur'ani sai suka saita tunaninsa saboda hikimar da yaji a cikinsu da kuma girmansu,take yaji a ransa cewa lallai akwai gaskiya da daukaka a cikin wannan addini. Lokacin da yarima yazid da ardadu suka idar da sallah suka jiyo sukaga zainur a zaune ya kura musu idanu kawai yana al'ajabi sai yarima yazid yayi murmushi a gareshi yace,yaya naga ka kura mana idanu ne tamkar baka taba ganinmu ba? Koda jin wannan tambaya sai yarima zainur yayi murmushi yace ai ba ku nake kallo ba ™Abbas Abdulkadir hada hada™ ibadar da kukeyi ce ta dauke mini hankalina na rantse da darajar iyayena da kakannina ban taba jin kalmomin dasu ka ratsa raina ba da zuciyata ba sama da wadanda naji ka ambata a cikin wannan ibada taka. Akwai hikima da daraja a cikinsu.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Yarima Yazid domin ya fahimci cewa zainur na daf da gane gaskiya tun kafin ma suyi gagarumar tafiyar dake gabansu,kawai sai yazid ya dafa kafadar zainur yace,ya kai abokina ai abinda kaji ma kadanne daga cikin kalmomi masu girma na ubangijin musulunci,da sannu zaka gasgata wannan addini nawa kuma ka gamsu cewa babu wani ubangiji daya cancanci a bauta masa face ubangijin musulunci.Koda yarima yazid yazo nan a zancensa sai yaga wani hadimin gidan ya shigo dakin dauke da abinci bisa faranti,take ya ajje ya fita. Fitarsa keda wuya sai Yarima Zainur ya dubi su Yazid yace ai sai kuzo kuci abinci.Koda jin haka sai Yazid ya dubi zainur cikin mamaki yace haba yaka abokina shin ka manta ne cewar da yammacin nan muka ci abinci a kasuwa saboda Ardadu bai kawo abincin da wuri ba. Zainur yayi murmushi yace ai na kawai ka cire hannayenka muci abinci duk da haka nasan baza'a rasa yunwa ba a jikin ka. Yazid ya sake yin murmushi ga yarima zainur yace aini ban taba cin abinci ba sama da loma uku tun daga kuruciyata kawo izuwa girmana saboda a tsarin addini na anason mutum ya raba cikinsa gida uku.Har Yarima Zainur ya bude baki da nufin ya tambaya yazid abinda yake nufi da raba cikinsa gida uku sai yaji wani hadimin gidan yazo bakin kofar dakin yace ga manzo daga gidan sarki a gareka. Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama yarima zainur domin shidai a saninsa ba'a taba aiko kiransa ba daga gidan sarki,don haka sai yayi zaton kodai wajen sarkin yaki haiman manzon yazo.Cikin sauri zainur ya fito daga cikin dakin ya riski manzon ya dubeshi yace waye ya aiko ka kuma wajen aka baka sako? Manzon ya risina cikin girmamawa yace ya shugabana mai girma galadima ce ta aikoni gareka tace lallai tanason ganinka yanzu. Koda jin haka sai zuciyar zainur ta buga da karfi ya dubi manzon cikin kaduwa yace ina fatan dai babu wani abu mara dadi daya faru a gidan sarki? Manzo yace mudai babu wani abu da muka gani ko muka ji ya faru komai na tafiya kamar yadda aka saba.Koda jin haka sai yarima zainur yayi ajiyar zuciya yace shike nan bari naje na fito mu tafi.Take zaimur ya koma cikin dakinsa da sauri ya kama shirin fita. Koda ganin haka sai yazid ya dubeshi yace yakai abokina shin zan iya yi maka rakiya? Har zainur yayi shiru kamar bazai amince da rakiyar tasa ba sai kuma ya dubeshi yace babu matsala ai tafiya mutum biyu tafi daya zo mu tafi.Cikin murna yarima yazid ya mike da sauri ya kimtsa suka fita batare da sunce da Ardadu uffan ba shima kuma da yake dama akwai mugun nufi a ransa sai yayi shiru baice dasu kala ba. Suna fita ya mike tsaye ya leke waje ta tagar dakin kawai sai ya hango yarima zainur ya tara gaba dayan hadiman gidan yana gaya musu wani abu,inda matsalar take shine baya iya jiyo abinda yake fada musu. Take Ardadu ya raya a ransa cewa an kara matakan tsaro ne a gidan.Nan fa hankalin Ardadu ya dugunzuma ainun saboda yasan cewa wannan itace babbar damar da yake da ita wacce zai iya sato wannan taswira daga jikin sarkin yaki haiman tunda gashi a cikin gidansa gashi kuma babu zainur da yazid a kusa,kuma shi kansa sarkin yaki a kwance yake cikin jinya bashi da wani karfin dazai iya kare kansa,don haka zai iya karbar taswirar da karfin tsiya dama tun da suka zo gidan yayi nazarin gaba dayan dakarun tsaron yaga gaba dayansu basufi su goma sha daya ba,su kuwa hadiman basufi su bakwai ba,don haka ya tabbatar da cewar a cikin abinda bazai wuce dakika dari biyu ba duk zai iya gamawa dasu,koda yasuyi masa rubdugi a matsayinsa na gwarzon mayakin daya saba tarwatsa ayarin guda ma a daji. Inda matsalar take shine idan har aka samu kuskure ya zamana cewa bai sami nasarar dauko wannan taswira ba tofa shikenan yayi biyu babu ma'ana bashi babu samun cikon wadancan makudan kudade wadanda Uraidu yayi masa alkawari kuma sam bashi da ikon cigaba da zama da yarima yazid bare ya sami dukiyar da yake sa ran samu nan gaba a cikin tafarkin addinin musulunci. Abinda Ardadu yake kwadayi a cikin addinin musulunci shine yarima yazid ya gaya masa cewa akwai lokacin da za'a tafi Jihadi a yaki manyan kafiran sarakunan nahiyar a sauke su daga kan karagarsu ta mulki da karfin tsiya.Dajin wannan albishir sai Ardadu ya aiyana a ransa cewa zaiyi amfani da wannan dama wajen sace dukiyoyin sarakunan da aka kashe yana zuwa yana boyeta a sirrance ba tare da an sani ba. Kaico!wanda duk zuciyarsa ta mutu akan son abin wani tofa mayuwaci ne ya gane gaskiya saboda imanisa ya raunana akan yarda da kaddara. Haka dai Ardadu ya cigaba da sake saken zuci yana tsaye a bakin tagar dakin yarima zainur har zainur da yazid suka hau dawakai sukabi manzon gidan sarki suka fice daga gida,suna fita sai yaga gaba dayan dakarun gidan sun taru a kofar shiga turakar sarkin yaki sun kama aikinsu na tsaro. Koda ganin haka sai ya gane cewa lallai har yanzu yarima yazid bai gama yarda dashi ba shi yasa aka gayawa dakarun gidan su kara tsaro.Kawai sai Ardadu ya bushe da dariyar mugunta lokaci guda kuma saiya turbune fuskarsa yace idan har na bari wannan dama ta wuceni na zama cikakken wawa. Koda gama fadin hakan sai Ardadu ya zare takobinsa ya fice daga cikin dakin Yarima Zainur ya nufi kofar turakar sarkin yaki gadan-gadan ba tare da shakkar komai ba,fuskarsa a murtuke kaida ganinsa kasan cewa babu imani a tare dashi,kawai so yake takobinsa tasha jini.. . Toofah Ardadu yaci Amana kuma ya tabe. WASIKAR JINI!!! Littafi Na Biyar (5) Part C . BABU Imani a tare dashi kawai so yake takobinsa tasha jini. Koda dakarun tsaron suka hango Ardadu ya nufosu rike da takobi tsirara sai suma suka zare takubbansu suka ruga izuwa gareshi,ai kuwa shima saiya rugo izuwa kansu cikin mugun nufi tuni ma ya gama aiyana yadda zaiyi musu kisan farat daya tunda basu fi su goma sha daya ba,saida ya rage saura baifi taku uku ba kacal su hadu sai sukaji an daka musu tsawa dasu da Ardadun duk sai suka tsaya cak suka dubi inda sautin tsawar ke fitowa wanda ya kasance daga wani bangare dabam na gidan ne ba daga wajen turakar sarki ba. Ba wani bane yayi wannan tsawa face sarkin yaki,a wannan lokaci sarkin yaki haiman na rike da wata sanda yana dogarata saboda rashin karfin jikinsa kuma babu wani makani a jikinsa.Kawai sai sarkin yaji ya dubi Ardadu yace yakai wannan tsohon kasurgumin dan fashi,Ardadu bin Aukas kada ka cutar da kowa a cikin wannan gida nawa,abinda nakeso dakai shine ka fada min abinda kake bukata na baka ka tafi salin alin,idan dukiya kake so ina da ita nau'i nau'i shin zinare kake bukata ko lu'u lu'u ko murjani,inada yakutu,zubar daji da farar tasa. Koda sarkin yaki yazo nan a zancensa sai Ardadu ya gyada kai yace bana bukatar ko dinare daya da abinda ya danganci dukiya.Abinda nake bukata kawai shine taswirar zuwa dajin hajrul aswad na sani cewa tana tare dakai idan har ka hanani wannan taswirar sai na kashe duk wani mahaluki dake cikin nan har kai da matarka. Koda jin wannan batu sai idanun sarkin yaki suka zazzaro ya dubi Ardadu cikin alamun tsananin tsoro yace yanzu babu wani abu da zaka iya karba maimakon wannan taswira,na sani cewa makiyanmu ne suka biyaka dukiya mai yawa domin kaci amanarmu ka sace wannan taswira ka kai musu,to ka sani cewa a shirye nake yanzu na baka gaba dayan dukiyar dake cikin gidannan domin ta zamo fansa a kan wannan taswira. Kafin sarkin yaki haiman ya gama rufe bakinsa tuni Ardadu ya tari numfashinsa yana mai daka masa tsawa yace baka da abinda zaka iya bani,ina mai umartarka daka hanzarta dauko wannan taswirar ka bani ko yanzun nan takobina tasha jinin kowa. Koda jin haka sai hawayen takaici ya zubowa sarkin yaki haiman cikin alamun tsananin bakin ciki ya zura hannu a cikin aljihunsa ya dauko taswirar ya mikawa Ardadu hannunsa na karkarwa.Ardadu ya fisge taswirar ya dubata sannan ya bushe da dariyar farin ciki,kawai saiya ruga inda bargar dawakai suke ya kwanto doki guda ya haye kuma ya zabureshi da gudu ya fice daga cikin gidan yana mai kyalkyale dariyar farin ciki. Al'amarin daya dugunzuma hankalin dakarun gidan kenan suka rugo izuwa gaban sarkin yaki haiman,shugabansu ya dubi sarkin yaki a cikin alamun tsananin damuwa yace haba ya shugabana saboda me zaka bari wannan tsohon azzalumi ya tafi da wannan abu mai matukar muhimmanci da yafi na rayuwarmu nan gaba dayanmu,shin banaji kace idan wannan taswira taje hannun azzalumai shike nan talakawa sun shiga UKUBA. Koda shugaban dakarun yazo nan a jawabinsa sai kawai sukaga sarkin yaki ya bushe da dariya.Al'amarin daya basu mamaki kenan gaba dayansu.Haiman ya dafa kafadar shugaban dakarun nasa yace kwantar da hankalin yakai Ukasha kayi sani cewa shi kuda ko a wajen kwadayi akan kamashi,tunda naga wannan tsohon danfashi tare dasu Yarima jiki na ya bani cewa saiya ci amanarsu. Duk da cewa na sami labarin ya karbi addinin wannan bako yarima yazid,ina ganinsa a cikin wannan gida nawa na dauki mataki a cikin raina kuma na kirkiri dabarar daya kamata nayi.koda haiman yazo nan a cikin zancensa saiya zura hannunsa a cikin aljihun wandon ya dauko wata taswirar wacce ta zama iri daya sak da wacce ya bawa Ardadu ya nunawa su Ukasha yace,wannan itace taswira ta gaskiya wadda na bawa Ardadu jabuce bazata kai makiyanmu izuwa hanyar gaskiya ba,yaku dakaruna daku da dukkan hadiman wannan gida nawa yau kusan shekaru ashirin kenan ina tare daku,gaba dayanku marayu ne kuma tunda kuruciyarku na deboku a yakokin dana fita na rikeku na raine ku tamkar 'ya'ya na bayan mutuwar iyayenku babu abinda na rage muku dashi a rayuwa. Duk da cewa asalinku bayi ne amma duk aikin da kukeyi mini biyanku nakeyi,na sani irin amincin dake tsakanina daku dakuma kaunar da muke yiwa juna,na sani cewa baku da wanda ya fini a wannan duniya tunda babu wanda ya taso tare dashi ya jibanci lamarinku face ni,bisa wannan dalili ne naki yarda na bari Ardadu ya yakeku domin zai iya hallaka kuko cutar da lafiyarka tunda nasan cewa yafi ku karfi da iya yaki,tunda ni bani da karfin dazan iya tararsa a yanzu,na sani cewa zaku iya rufe sirrina kuma har abada ba zakuci amanata ba shi yasa nake sanar daku dukkan wanann al'amarin.Ahalin yanzu kasar nan tamu tana cikin mugun hadari bisa tarkon makiya saboda a yanzu haka sarki ya kwanta ciwon AJALI,Kuma makiyansa so suke su karbe KARAGAR MULKInsa wannan taswira itace kadai ta hana su samun nasarar cika burinsu. Koda sarkin yaki haiman yazo nan a jawabinsa sai gaba dayan dakarun da hadiman suka rungume shi kuma suka fashe da kuka suna cewa ashirye muke mu sallama rayuwarmu domin ceto rayuwar jama'ar kasar nan,wannan shine abinda ya faru a gidan sarkin yaki haiman bayan fitarsu Yarima zainur da yarima Yazid izuwa gidan sarki. Al'amarin su yarima Yazid kuwa lokacin dasuka iso gidan sarki sai wannan manzo ya shiga bangaren gin gimbiya nauwara yayi musu iso,ba tare da bata wani lokaci ba kua sai aka shigar dasu har can cikin turakar tata suna shiga suka iske gombiya nauwara a zaune ta juya bayanta kanta a sunkuye.Koda taji motsin shigowarsu kuma ta gane cewa mutum biyu ne suka ™Abbas Abdulkadir Hada Hada™ shigo sai tayi sauri ta goge hawayen idanunta sannan ta waigo domin taga wanda yarima zainur yazo dashi. Koda ta waigo ta hada idanu da yarima yazid sai duk su biyun ita dashi zuciyoyinsu suka buga da karfin gaske. Al'amarin da babu wanda ya taba jin irinsa a cikinsu,da yake idanun nauwara sunyi jajur sakamakon kukan da tasha sai yarima zainur ya dubeta cikin alamun tsananin damuwa da firgici yace yake yar uwata menene ya faru gareki naga alamun kuka a idanunki?. Koda jin wannan tambaya sai zuciyar gimbiya nauwara ta karaya har hawaye ya subuto mata ba tare data ankara ba kawai sai ta dubi yarima zainur tace ahalin yanzu abbana ya kwanta cutar ajali kuma baya um baya um um saidai akwantar a tayar bai iya cin komai hatta ruwa saidai a dura masa a baki wani lokacin ma ana dura masa zaiyi amansa,kafin yakai ga wannan hali yabar min wasiyya guda cewar yabar amanata a hannunka kuma ya gaya mini cewa kai da sarkin yakine kadai zaku iya tsirar da rayuwata da kuma karagar mulkina. Baya ga wannan yace na gaya maka cewa kada ka bijirewa sabon abokinka dakayi kuma duk shawarar daya baka kayi aiki da ita,shin wannan saurayi dake gabana ma'abocin kwarjini shine sabon abokin naka? Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa yarima zainur ya kama hannun yarima yace tabbas wannan shine sabon abokina yarima yazid 'da ga sarki Arsanal na birnin haural yakai abokina wannan itace yar uwata gimbiya nauwara wacce na baka labari.Cikin alamun girmama nauwara da yazid suka gaisar dajuna sannan yarima zainur ya dubi gimbiya nauwara cikin alamun tausayawa yace yake yar uwata kiyi sani cewa ina bukatar naga sarki a yanzu saboda nasan cewa ganin karshe zanyi masa don abu ne mayuwaci naje na dawo daga tafiyar dake gabana na riske shi.Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa gimbiya nauwara tace kuzo muje izuwa turakar tasa,nan take gimbiya nauwara ta yunkura da nufin ta wuce gaba izuwa turakar sarki amma sai yarima yazid yayi wuf ya shige gabanta yana mai kama hannun zainur gami da jansa gaba.Batare daya waigo ya dubi nauwara ba sai yace kiyi hakuri yake gimbiya kiyi sani cewa ni a addinina mace bata shiga gaban namiji a yayin tafiya tunda dai zainur yasan inda zamuje babu matsala. Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama nauwara tace a cikin ranta wannan wane irin addini ne haka mai alkunya da kawaici. Nandai suka dugunzuma su ukun suka shiga cikin turakar sarki aiyuba. Sarki aiyuba na kwance bisa gadonsa na alfarma wadansu hadimansa sun kewaye shi anyi jugum tamkar ana zaman makoki,gashi dai sarki ba barci yake ba amma idanunsa a rufe suka kuma a rame,matuka sannan tunda ya kwanta wannan ciwo bai bude idanunsa ba inba don ma alamun numfashin akan kirjinsa ba da kawai zato za'ayi ya mutu.Da shigowar gimbiya nauwara tare dasu yarima yazid sai hadiman suka dare suka basu hanya suka iso har gaban sarki aiyuba,nan take nauwara ta zubar da hawaye sannan ta dubi yarima zainur tace,kaga halin da abbana yake ciki kuma lallai mutuwa zaiyi babu yadda za'ayi ya tashi daga wannan cuta,saboda yagaya mini cewa haka tsarin sirrin tsafinsa yake cewar da zarar yakai adadin shekarun dayakai yanzu akan karagar wannan ciwo zai riske shi,kuma ya gaya min cewa jinyar kwana gomasha hudu zaiyi kacal ajalinsa ya cika. Koda jin wannan batu yarima yazid yayi hailala yace kaico waya gaya miki cewa akwai wanda ya isa ya kashe bawa inba ubangijinsa ba? Kada kuyi imani da tsafi ko camfi domin karyane ba gaskiya ba ina mai tabbatar miki da cewa ubangijina zai iya tashin kafadun mahaifinki ko a yanzu take idan yaso. Koda jin wannan batu sai tsoro ya kama gimbiya nauwara,yarima zainur da dukkanin hadiman dake wajen,nauwara ta dubi yarima yazid cikin alamun fushi tace waye kai har da zaka tankawa tsafin mahaifina? Shin kanaso ne yanzunnan ka hallaka? To ka sani cewa shekara da shekaru tun iyaye da kakankin ban taba jin wanda ya aibata tsafin gidan nan ba sai kai. Koda jin wannan batu sai yarima yazid yayi murmushi yace tabbas daku da iyayenku da kakanninku tabbas kun dade a cikin bata mabaiyani,da izinin ubangijina zan nuna muku gaskiyar abinda nafada. Koda gama fadin haka sai yarima yazid ya tunkari gadon da sarki aiyuba ke kwance. Faruwar hakan keda wuya sai wata irin iska mai karfin gaske ta banko cikin dakin,wata katuwar bakar inuwa doguwa sankaleliya ta baiyana tana mai tsala wani irin kara mai ban tsoro wacce ta firgita su yarima zainur suka fadi kasa suna masu karkarwar jiki amma shi yarima yazid yana tsaye yana fuskantar inuwar.Koda inuwar ta taso masa zata afka masa saiya tofa mata addu'a kawai sai akaji inuwar ta sake kwala kara mai karfin gaske kuma ta fice da gudu ta cikin tagar daki. A sannan ne gagarumar iskar data addabi komai da kowa a cikin dakin ta dauke dif tamkar bata taba wanzuwa ba.Cikin tsananin mamaki nauwara,zainur da hadiman sarki suka mike tsaye suka kurawa yarima yazid idanu,nan take yazid ya karaso daf da sarki aiyuba wanda ke kwance kamar gawa,yasa hannunsa na dama ya dafa goshinsa yana mai karanta wata addu'a tare da tofa masa ita a dukkan sassan jikinsa.Faruwar hakan keda wuya sai idanun sarki aiyuba suka bude ya mike zumbur ya kama kumallon bakin jini. Al'amarin dayayi matukar baiwa su nauwara mamaki kenan kuma ya firgitasu,saida sarki aiyuba ya gama aman sai yayi ko kadan babu kwari a jikinsa don haka sai ya koma ya kwanta a lokacin daya kurawa yarima yazid idanu yana mai zubar da hawaye.A sannan ne ya bude bakinsa da kyar ya dubi yarima yazid yace me yasa kazo ka karya alkadarina? Mai yasa kake son karya tasirin daukakata da kuma gadon iyayena.? WASIKAR JINI!!! Littafi Na Biyar (5) Part D . KAKESON karya tasirin daukakata da kuma gadon iyayena. Koda jin wadannan tambayoyi sai

Chapter 9 of 15