Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba karamin ganganci bane, sa'adda yarima yazid yaji wannan batu sai yayi murmushi yace tabbas abinda ka fada gaskiya ne amma inaso ka sani cewa a halin yanzu Ardadu yana cin albarkacin wata babbar rigane daya sanya wacce ita ce take bashi kariya daga gareni,ba wata riga bace wacce Ardadu ya sanya ba face addinin musulunci daya karba,muddin yana yin abubuwan da Allah ya wajabta masa bani da ikon kashe ko cutar dashi face ya kauce daga kan hanyar tafarkin gaskiya abinda nasani kawai shine indai bashi da rabo a cikin wannan addini na gaskiya tofa watarana saiya saba dokar Allah wacce zata bani damar na kawar dashi don haka shine zai zabawa kansa abinda zai fishsheshi. Nan take dai su biyun sukayi shiru basu sake cewa uffan ba sukaci gaba da kutsawa cikin kasuwar kuma adaidai wannan lokaci ne ardadu ya iso daf dasu suka cigaba da tafiya tare su ukun. . Al'amarin Sarkin Yaki Haiman kuwa lokacin daya baro gidansa bisa doki da nufin ya tunkari fadar saiyabi wata hanya wacce bama ita ya saba bi ba,ita dai wannan hanya yankece ta bayan gari dole ne mutum ya ratsa ta gefen wani daji sannan ya dawo kan hanyar cikin garin Hanya ce mai sauri wadda nan da nan zata kai mutum izuwa gidan sarautar birnin latul harus cikin kankanin lokaci. Koda sarkin yaki ya iso tsakiyar dajin dake wannan hanya saiyaji alamun motsi a cikin duhuwoyin dake zagaye da tsakiyar hanyar da yake kai,abinka da tsohon mayaki wanda yasan shirin abokan gaba kuma yasan duk irin tuggin da ake amfani dashi wajen harin sumame sai yayi sauri yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak ya baza idanunsa da kunnuwansa izuwa cikin duhuwoyin tsawon yan dakiku bai sake jin motsin komai ba,kwatsam saiga wata barewa ta fito da gudu daga cikin ciyayi ta nausa yamma ta kasa tsere da wata damisa,koda ganin hakan sai sarkin yaki yayi murmushi kuma ya saki jikinsa yaci gaba da tafiya abinsa cikin kwanciyar hankali. Kash rashin sani yafi dare duhu ashe a can gaba kadan wasu dakarun sumame ne a kwance cikin duhuwar bishiyoyi suna sanye da korayen tufafi wadanda kalarsu ta saje data ciyawar wajen kuma duk sun rufe fuskokinsu idanunsu kadai ake gani suna dauke mugayen makamai boye a jikinsu. Adadin wadannan dakaru sunkai dubu kuma sun kware ainun a iya yaki.Saida sarkin yaki haiman ya karaso tsakiyar wadannan dakarun sumamen sannan suka mike tsaye a tare sukayi masa kawayanya nanfa aka fara kallon kallo a tsakaninsa dasu.A sannan ne shugaban dakarun wani dogo mai kirar sadaukai ya ratso ta tsakiyarsu ya iso kusa da sarkin yaki suka karewa juna kallo sannan shugaban dakarun sumamen ya tuntsire da dariya.Lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa ya nuna haiman da dan yatsa ya daka masa tsawa yace yakai haiman idan kanason ka tsira da rayuwarka ka bamu abinda muke bukata yanzu take. Koda jin wannan batu sai sarkin yaki haiman ya bushe da dariya sannan ya dubi shugaban dakarun yace amma dai kai ka cika wawa mara tunani in banda hankalinka ya gushe ta yaya kake zaton zaka iya bani tsoro da batun mutuwa,shin ka mantane cewa nine wanda ya siyar da rayuwarsa sau babu adadi ya shiga tsakiyar abokan gaba yana sara da suka,bansan iyakar adadin rayukan da takobina ta dauka ba,zuciyata ta dade da kekashewa ga barin tsoron ganin zubar da jini,ai MAKASHIN MAZA MAZA KAN KARSHI. . idan ku yan fashi ne masu neman abinci ku fadi ko nawa kuke so zan iya baku amma idan wani abu kuke nema wanda zakuyi amfani dashi wajen cuta da kasata ko al'ummata tofa bazaku samu ba saidai koni koku wani ya zama gawa anan wurin. Koda jin wannan batu sai ran shugaban dakarun ya baci ya dakawa haiman tsawa yace kai dakata haka ba cacar baki ce ta kawo mu ba ko bata lokaci abinda muke so ka bamu shine taswirar hanyar zuwa inda WASIKAR JINI take wacce sarki Aiyuba ya baka,bamu wannan taswirar yanzu yanzu ko kuma mu kashe ka mu dauka daga jikinka. Sa'adda shugaban dakarun yazo nan a zancensa sai sarkin yaki haiman ya kamu da tsananin mamaki bisa yadda akayi wadannan dakarun sumame suka san abinda ya faru tsakaninsa da sarki alhalin a sirrance sukayi komai a cikin turakarsa kuma gimbiya nauwata ce kadai a wajen sannan yana da tabbacin cewa babu yadda za'ayi nauwara ta tonawa mahaifinta asiri tunda tamkar ta tonawa kanta ne,saboda makiyanta ta baiwa makamin da zasu iya hallakata dashi ne. Lokacin da sarkin yaki haiman yazo nan a tunaninsa sai ya fusata ainun zuciyarsa ta kama tafarfsa kamar zata kone kawai saiya zare takobinsa ya dubi shugaban dakarun sumamen cikin tsananin fushi ya daka masa tsawa yace kai tsohon makiri karen farautar azzalumai kayi sani cewa daku da wanda ya turoku tsakanina daku sai kisa. Kafin shugaban dakarun ya budi baki yace wani abu tuni haiman ya dako tsalle sama daga kan dokinsa ya kaiwa shugaban dakarun mummunan sara a wuya da nufin ya cire masa kai,cikin bakin zafin nama shugaban dakarun ya sunkuya ya kaucewa saran amma duk da haka saida kafin takobin ya shaftare wani bangare na rawanin daya rufe fuskarsa dashi. Take rawanin ya kwance ya fadi gefe amma sai haiman yaga cewa bakuwar fuska ce wadda bai taba gani ba a cikin birnin latul harus,al'amarin daya tabbatar masa da cewa lallai wadannan dakaru hayarsu aka dauko. Nan take sauren dakarun sukayi caa akan sarkin yaki da nufin suyi masa rubdugu su sassara shi amma sai ya zame musu alakakai ya rinka tarwatsasu da karfin tsiya yana kare dukkanin harinsu kuma ya kawo musu sara da suka ta sama da kasa gefe da gefe. Wani irin salon fada haiman ya rinkayi ya zamana cewa yana katantanwa a sama da kasan dakarun kuma ya hada da gabza musu naushi da bugu amma saboda kwarewar dakarun a iya yaki gami da tsananin nacinsu da taurin zuciya sai gashi suna shanye duk irin dukan da yake musu duk da cewa yana hada musu jini da majina kuma yana saran sassan jikinsu jini na zuba amma basu fasa kara matsarsana suna kai masu mugayen hare hare. Shi kuwa shugaban wadannan mugayen dakaru sai kawai ya koma gefe daya yaja tunga ya zuba ido domin yaga iyakar jarumtakar haiman da iyakar juriyarsa. Wohoho manyan jarumai sune wadanda suka saba dayin karo da maza komai yawansu kuma sune wadanda basusan tsoro ba sannan komai wuya komai tsanani basa gudu a filin daga saidai a gudu a barsu ko kuma a ci karfinsu a kashe su a wajen. Saida aka shafe sa'a uku cur ana bakin artabu tsakanin sarkin yaki haiman da wadannan dakaru ya zamana cewa ya kashe mutum dari uku da arba'in a cikinsu amma shi baije kasa ba mma fa anyi masa manyan raunika gudu uku a jikinsa har jiri ya fara dibarsa sakamakon jininsa dake zuba amma saboda bakin naci irin nasa yaki yaje kasa da zarar dakarun sun yunkura masa sai kaga shima ya afka musu yaci gaba da yakarsu cikin gagarumin karfi tamkar a sannan ne ya fara yaki.... Nima ganin wannan gumurzu yasa na tsaya kallo... WASIKAR JINI!!! Littafi Na Hudu (4) Part D . Tamkar a sannan ne ya fara yakin.Al'amarin daya fara tsorata ragowar dakarun kenan suka fara ja da baya musamman da sukaga cewa gawarwakin yan uwansu fa karuwa sukayi ba raguwa ba.A hakan dai aka cigaba da wannan yaki har Haiman ya sake samun nasarar kashe mutum dari biyu da ashirin da uku ba tare da an sakeyi masa rauni ko daya ba,al'amarin daya fusata shugaban dakarun kenan ainun ya dakawa yaran nasa tsawa yana mai umartarsu dasu ja da baya su bashi wuri.Nan take kuwa su duka sukaja da baya shugaban dakarun ya zare takobinsa sannan ya kama rigar jikinsa da hannu daya ya yageta koda Haiman yaga tsananin girmansa da kuma tarin kwarjininsa gami da murdewar jikin nasa sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi domin ya tabbatar da cewar a yadda ya jigata dinnan kuma jini ke zuba a jikinsa bazai iya hallaka wannan basamuden kato ba,amma kuma daya tuna cewa wannan yaki fa da yakeyi yaki ne na ceton kasarsa da al'ummarsa dama gaba dayan mutanen duniya daga sharrin azzalumai sai yaji dukkan tsoro ya kau daga zuciyarsa nan take yayi wuf shima ya yade rigar jikinsa ya daure raunin da yafi zubar da jini a jikinsa don tsaida jini,sannan ya gyara tsayuwarsa yana mai fuskantar shugaban dakarun suka fara kallon kallo,kwatsam sai suka rugo da gudu izuwa kan juna suka ruguntsume da sabon azababben yaki. Wohoho!Masifa ba'a sa mata rana duk sa'adda karfi ya hadu da karfi tofa bala'i yazo kenan kuma sai mai rabon ganin badi shine zaikai labari. Lokacin da wadannan zaratan jarumai biyu suka kacame da masifaffen yaki suka wanzu suna masu kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin bakin zafin nama da juriya da jarumtaka ta ban al'ajabi sai suka dimautar da duk dakarun dake wajen,kuma suka tashi hankalin duk wani abu mai rai dake cikin dajin domin babu shiri tsuntsaye suka kama yin kaura suna barin shekarsu. kananun dabbobi kuwa suka kama guje guje suna fadawa cikin ramukansu suna buya,ba komai ne ya haddasa hakan ba face bishiyoyin dake wajen ma basu tsira daga sharrin kaifin takubban jaruman biyu ba domin duk sa'adda dayansu ya kaiwa dayan sara da zarar ya goce ya sami bishiya saidai kaga bishiya ta rabe gida biyu komai girmanta haka ma idan naushi ya kawo ya sami bishiya komai girman saita jijjigo daga cikin kasanta ta fadi kasa. Nanfa suka tayar da kura dajin gaba daya yai fururu,su kuwa sauran dakarun sumamen da suka dimauce suka firgita bisa ganin wannan mugun bakin artabu da akeyi da shugabansu basu san sa'adda suka rinka cika wandunsu da iska ba suna neman wajen buya,saida aka shafe sa'a daya da rabi ana wannan fafatawa dayansu bai sami nasarar cutar da daya ba,ba shiri kowannensu yaja da baya sukayi cirko cirko suna haki da kallon juna kamar zakaru,damar da suka samu kenan suka dan huta kuma suka shiga tunanin dabarar da zasuyi domin su sami nasara.Ashe kowannensu dabara daya ce tazo masa ta sauya salon fadan,aikuwa sai suka yunkura suka tasowa junansu cikin mugun nufi lokaci guda. Suna haduwa suka kacame da masifaffen yaki amma wannan karon sai suka hada da kaiwa juna naushi da bugu da hannu da kafa,faruwar hakan keda wuya sai yakin ya sauya yanayi domin a sannan sarkin yaki Haiman ya gane kuskurensa saboda shugaban dakarun ya fishi karfin damtse nesa ba kusa ba,idan Haiman ya jurewa shugaban dakarun naushi biyar a lokaci guda sai kaga ya shanye duka amma da zarar shi kuma yayi masa naushi daya sai shugaban dakarun ya yarda takobin hannunsa yacigaba da gabzawa haiman naushi a fuska da ciki har sai haiman ya yarda takobin nasa kuma ya rinka faduwa kasa jini na tsartuwa abakinsa. Saida shugaban dakarun ya yiwa Haiman laga laga yaga ko kyakkyawan motsi bayayi sannan yazo kansa ya tsaya ya zura hannunsa cikin aljihun rigarsa ya fiddo wannan fata mai dauke da taswirar dajin Hajarul Aswad. Cikin tsananin farin ciki shugaban dakarun ya bushe da dariyar farin ciki,kawai sai ya zaro wata katuwar wuka daga kugunsa ya daga sama zai kirbawa Haiman a kirjin,kawai sai yaji an ruke hannunsa ta baya wani irin riko mai tsauri da zafin gaske har yaji kamar hannun nasa zai karye.Ba shiri ya saki wukar dake hannunsa ya juya da kyar. Ba wani ya gani ba ruke da hannunsa face Sarauniya Lazwara koda yaga ashe ma yarinya ce ta ruke masa hannun nasa saiya firgita ainun yayi zaton cewa aljana ce ta rukeshi don haka saiya sume a tsaye nan take ta saki hannun nasa ya sulale kasa,duk wannan abu dake faruwa Haiman baya cikin haiyacinsa baima san wanda ke tsaye akansa ba.Saida sarauniya Lazwara ta gama dinke raunikan dake jikin sarkin yaki haiman ta shafa masa magani sannan ya farfado daga dogon suman da yayi ya dawo cikin haiyacinsa sosai,koda ya bude idanunsa yayi arba da sarauniya Lazwara zaune a gabansa sai shima ya firgita yadan ja da baya,koda ta fahimci cewar ya tsorata da ganinta saitayi murmushi ta dubeshi tace kwantar dahankalinka yakai sarkin yakin birnin Latul Harus ashe har zaka kasa shaidani don mun rabu tsawon shekaru takwas kacal,nice fa sarauniya Lazwara.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke haiman ya yunkuro da kyar ya gyara zamansa yana mai jingina bayansa a jikin wata bishiya sannan ya dubi Lazwara yace godiya a gareki ya shugabata tabbas kin ceci rayuwata data dukkan al'ummar dake wannan nahiya gaba daya,caraf sai Lazwara ta tari numfashinsa tace basai kayi mini bayanin komai ba domin babu abinda ban sani ba,ina zaune a can cikin birnina cikin turakata na ganka a cikin madubin tsafina kanayin yaki da wadannan abokan gaba,koda naga sunci karfinka zasu hallaka ka sai nayi amfani da karfin sihirin tsafina na baiyana anan na ceci rayuwarka,yanzu ga abinda yaso ya kwata a hannunka.Nan take Lazwara ta mikawa Haiman wannan fata mai dauke da taswirar hanyar zuwa dajin Hajarul Aswad ya karba sannan tace ka sake adana wannan fata da kyau domin wanda yake farautarta yafi wuta zafi,kuma yafi annoba masifa,kuma yafi kowane irin ciwo radadi da zugi zan cigaba da baka kariya da taimako gwargwadon iyawata har izuwa ranar da zaka yadda kuka shirya kai da sarki Aiyuba amma idan ka koma gida ka sadu da danka Yarima Zainur ka gaya masa nace lallai ya saki reshe ya kama ganye,tunda ya hada kai da wannan bafatake domin bazai taba kaishi ga nasara ba saidai hallaka. Ka gaya masa cewar har yanzu lokaci bai kure ba yana da sauran dama da zaizo har fadata ya karbi taimakona bisa ka'idar dana shimfida masa. Koda gama fadin hakan sai sarauniya Lazwara ta bace tamkar bata taba wanzuwa ba a wajen,cikin karfin hali sarkin yaki haiman ya mike tsaye yabar wajen yaje inda dokinsa yake yana dingishi da kyar ya kama dokin ya haye kansa sannan ya sakar masa linzami ya tunkari hanyar gidan sarki... SHIN SARKIN YAKI ZAI IYA TSARE WANNAN TASWIRA HAR IZUWA LOKACIN DA ZAI DANKATA A HANNUN YARIMA ZAINUR? TSAKANIN WAZIRI RIDWAN DA YARIMA ZAINUR WAYE ZAI ZAMA SARKI BIRNIN LATUL HARUS? WACE IRIN BAKAR WAHALA YARIMA ZAINUR DA WAZIRI RIDWAN ZASU SHA A CIKIN DAJIN HAJARUL ASWAD? SHIN ZAINUR ZAI CANZA SHAWARA YA KOMA WAJEN SARAUNIYA LAZWARA? WANE IRIN TAIMAKO YARIMA YAZID ZAI BAIWA YARIMA ZAINUR A CIKIN TAFIYARSU TA ZUWA DAJIN HAJARUL ASWAD? YAUSHE NE SARKI AIYUBA ZAI MUTU KUMA ME ZAI FARU BAYAN MUTUWARSA TASA? WASIKAR JINI!!! Littafi Na Biyar (5) Part A . WAZIRI Ridwan na zaune cikin kujerar turakarsa tare da matarsa Gimbiya Ra'isa suna cikin matukar farinciki tana shayar dashi ruwan barasa yana ta faman kyalkyala dariyar murna sai ta tari numfashinsa tace,yakai mijina waishin meye tabbacinka cewa wadannan dakarun sojan haya zasu iya hallaka sarkin yaki su karbo maka wannan taswira ta zuwa Dajin Hajrul Aswad? Koda jin wannan tambaya sai waziri ridwan yayi murmushi yace yake Ra'isa nasan iyakar jarumtakar sarkin yaki haiman kuma nasan ta wadannan dakarun sojan haya don haka ko kada bani da shakka akan nasararsu a kansa.Ina mai tabbatar miki da cewa daga yanzu a koyaushe zaki iya ganin an kawo min wannan taswirar.Gama fadin haka keda wuya sai babban hadimin waziri ridwan yazo bakin kofar turakar yayi gyaran murya yace ya shugabana ga bakonka na dazu da safe ya dawo.Koda jin haka sai waziri Ridwan ya mike tsaye zumbur cikin dimbin farinciki ya dubi Ra'isa yace ai dama na gaya miki bari naje na karbo taswirar ki gani. Kai tsaye waziri ridwan ya bude kofa ya fice daga cikin turakar ya isa can babban falo inda yake ganawa da dukkan bakinsa.Yana shigowa falon sai zuciyarsa ta buga da karfi ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin shugaban dakarun sojan hayar nan a tsaye kansa a sunkuye cikin alamun rashin nasara kuma babu taswira zuwa dajin Hajrul Aswad a hannunsa.Koda ganin waziri Ridwan sai shugaban dakarun ya zube kasa bisa guiwoyinsa ba tare da ya dago da kansa ba ya budi baki yace ya shugabana ka yafe min mun kasa cika wannan aiki.Koda jin wannan batu sai ran waziri ridwan ya baci zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone kuma jikinsa ya kama tsuma kamar wanda ake sokawa allura,bai san sa'adda yasa kafarsa ba ya doki kirjin shugaban dakarun. Duk da girman shugaban dakarun saida ya fadi kasa. Cikin tsananin fushi Waziri Ridwan yace ta yaya kuka kasa samun nasara akan haiman alhalin na tabbatar da cewa kun fishi karfin damtse da juriyar yaki? Yanzu kana nufin kace kenan duk makudan kudaden dana baku sun zama a banza kenan? Koda jin wannan tambaya sai shugaban dakarun ya yunkura da sauri ya mike zaune ya dubi waziri ridwan yace,ya shugabana hakika na sami nasara akan sarkin yaki haiman domin saida nayi masa laga laga na sumar dashi kuma take na ciro taswirar zuwa dajin hajarul aswad a jikinsa amma faruwar hakan keda wuya sai naji an cafke hannuna ta baya anyi mini wani irin mugun riko wanda naji kamar hannun zai ruburbushe.Koda na juya na kalli wanda yayi mini wannan ruko sainaga ashe wata yarinya ce ma karama wacce shekarunta ba zasu haura sha ba.Take na gane cewa aljana ce bansan sa'adda na sulale kasa sumamme ba. Koda jin wannan batu sai waziri ridwan ya kwarara uban ihu cikin tsananin takaici. Al'amarin da yasa gaba dayan mutanen dake cikin gidan nasa suka firgice kenan suka fita daga haiyacinsu. Waziri Ridwan ya dubi shugaban dakarun a fusace yace kai shasha ba aljana bace sarauniya Lazwara ce mai mulkin birnin arnan daji.Itace daya babbar abokiyar gabata ta biyu wacce take son taga bayana kuma a shirye take ta taimakawa su yarima zainur su rigani mallakar wasikar jini. Koda jin wannan batu sai shugaban dakarun yace ya shugaban ka bani dama ta biyu ina mai tabbar maka da cewa a lokacin abinda bai wuce kwanaki goma ba lallai zan kawo maka wannan taswira idan kuma na kasa zan dawo maka da dukkan kudadenka daka bamu.Koda jin wannan batu sai waziri ridwan ya bushe da dariyar farinciki yace idan kuwa ka kawo mini wannan taswira a cikin kwanakin daka fada zan sake baka kudi ninkin wadanda na baka kuma nayi maka alkawarin cewar idan na zama sarkin kasar na sai farin ciki ya lullubeka. Shugaban dakarun sojan hayan wanda ake kira da suna Uraidu Bin Hamsar ya mike tsaye zumbur yana mai dora tafin hannunsa na dama bisa kirjinsa yace,na rantse da darajar gemun ubana zanje nayi gagarumin shiri don cika wannan aiki naka,kuma ina mai tabbatar maka da cewa lallai nan da cikar kwana goma zanzo maka da wannan taswira ta kowanne hali.Koda gama fadin hakan sai sadauki Uraidu ya mike tsaye ya fice daga cikin falon shi kuwa waziri ridwan saiya bishi da kallo yana mai kyakyata dariyar farinciki tamkar wasikar jini ce ta fado hannunsa. . Al'amarin su Yarima Zainur kuwa lokacin da suka kutsa cikin kasuwa su uku suka gama siyayyar da zasuyi sai suka shiga wata rumfa suka zauna domin su huta kuma suci abinci saboda a wannan lokaci rana ta take kuma duk su ukun sun kamu da yunwa.Nan take yarima yazid yasa hannu a cikin aljihunsa domin dauko kudi ya baiwa Ardadu yaje ya siyo musu abinci amma sai yarima Zainur yayi wuf ya ruke hannunsa yace,Haba yaza ayi bako ya ciyar da dan gari ai nike da hakkin ciyar daku. Koda gama fadin hakan sai yarima zainur yasa hannu cikin aljihunsa ya fiddo da kudi ya bawa Ardadu.Cikin hanzari ardadu ya karbi kudin ya nausa cikin kasuwa domin siyo irin abincin da suka umarceshi da siya. Saida Ardadu yadan bata lokaci kadan yana yawo a cikin kasuwar sannan yaga shagon siyar da irin abincin dasu yarima zainur ke bukata,cikin hanzari ya shiga shagon ya bayar da kudin aka bashi.koda ya fito daga cikin shagon da niyar ya koma can tsakiyar kasuwa inda su yarima yazid suke sai yaga wadansu samudawan karti su hudu sun sha gabansa. Koda Ardadu ya karewa dakarun kallo sama da kasa yaga cewa sun cika zaratan dakaru masu tarwatsa maza a filin daga ya tabbatar da cewar ba zai iya dasu ba sai ya dubesu yace,me kuke bukata daga gareni? Koda jin wannan tambaya sai babban cikinsu ya daka masa tsawa yace Kai Ardadu shin arziki kake nema ko tsiya? To indai arziki kake nema kazo muje wajen shugabanmu ka gana dashi.Koda jin wannan batu sai Ardadu ya dubi katon cikin zakuwa yace maza ka kaini wajen shugaban naku.Nan take dakarun suka wuce gaba yana biye dasu sukayi wani bangare daban na kasuwar har suka isa wani katon gida,kai tsaye kartin hudu suka shige cikin gidan mai surkuki Ardadu na biye dasu amma zuciyarsa sai daka take duk da cewa shi mutum ne wanda ya saba zama a daji yana tare ayari na fatake yanayi musu fashi. Ba komai ne yasa tsoro ya darsu a cikin zuciyarsa Ardadu ba face ganin samudawan dakarun dake cikin wannan gida dauke da miyagun makaman yaki kuma da ganinsu kasan cewa baki ne ba yan garin bane,kuma yadda ya shigo cikinsu shi kadai din nan idan suka so zasu iya cinyeshi danye ba tare da wani sami koda tsoka daya ba. Haka dai aka cigaba da tafiya da Ardadu har aka iso wani daki dake can karshne gidan sannan aka bude musu kofa suka shiga,suna shiga yayi arba da wani murgujejen katon mutum zaune bisa wata babbar kujera ta alfarma yana shan giya ga kuma gasasshen rago a gabansa wadansu mata sunyi shigar banza guda biyu suna yanko naman suna sa masa a baki yana ci yana rungume su yana kyalkyala dariya.Koda katon yaga an shigo da Ardadu sai ya daga hannunsa yabada wata inkiya .Nan take kowa ya fice daga cikin dakin ya zamana cewa an barsu su biyu kacal a cikin dakin wato dagashi sai Ardadu. Kawai sai murgujejen katon mutumin ya dubi Ardadu cikin murmushi yace lale marhaban da tsohon dodon fatake na dajin Aryas, Ardadu bin Kaumar. Sunana Uraidu bin Hamsar. Koda Uraidu yazo nan a zancensa sai Ardadu ya dubeshi cikin kaduwa da mamaki yace yaya akayi kasan ni? Uraidu yayi murmushi a karo na biyu yace ai na dade da saninka domin kuwa sana'armu daya ce wato fashi a daji daga bayane tun kafin ka hadu da yarima yazid nima tawa likkafar tacigaba na hadu da waziri Ridwan na wannan birnin da muke ciki ya daukeni akan makudan kudaden da ban taba tara kamarsu ba a tsawon shekaru goma sha daya dana keyin fashi a cikin dazuzzukan dake can nahiyarmu. Abinda na kasa ganewa akanka yanzu shine mece ce ribarka da kake bin yarima yazid? Mutumin da baya iya baka koda kyautar dinare goma. Baya iya tsinana maka komai face kyautar abinda zaka ci da yar suturar da zaka sanya.Akan wane dalili zaka yarda a rude ka da wani sabon addini wanda babu komai a cikinsa face talauci? Koda Uraidu yazo nan a zancensa saiya mike tsaye yaje ya dauko wata katuwar jakar fata ya cirota ta dira a gaban Ardadu ya dubeshi yace bude wannan jakar kaga abin dake ciki.Cikin hanzari gama da rawar jiki Ardadu ya bude jakar,koda yayi arba da abin dake ciki saiya dimauce idanunsa suka zazzaro kuma gaba dayan jikinsa ya kama rawa,ba komai ya gani ba a cikin jakar face tarin lu'u lu'u,tunda yazo duniya da duk tsawon shekarun daya shafe yana harkar fashi a daji bai taba ganin dukiya a cure lokaci guda mai yawan wanann ba. Koda Uraidu ya lura da cewa wannan dukiya ta ruda Ardadu sai farin ciki ya kamashi ya sake dubansa yace wannan dukiya somin tabi a gareka,muddin zaka bi umarninmu kayi abinda muke so zaka sami dukiyar da har ka mutu ba zakayi talauci ba,kai bama yayanka ba hatta tattaba kunnenka sai sun mutu sunbar abin daka tara.Kasancewar akwai taswirar zuwa dajin Hajarul Aswad a wajen sarki yaki haiman marikin yarima zainur abokin maigidanka yarima yazid.Muna son kasan duk hanyar da zakabi ka sato mana wannan taswira a cikin kwanakin da basu wuce tara ba.Indai ka sami wannan nasara kawai jakar lu'u lu'u irin wannan guda dari da suke jiranka. Koda jin wannan albishir sai Ardadu ya dimauce kuma ya firgice nan take Ardadu ya zube kasa a gaban Uraidu yace na rantse da darajar iyayena ko zan rasa rayuwata saina kawo maka wannan taswira a cikin kwanaki taran daka umarceni. Uraidu ya bushe da dariyar murna yace yanzu saika dauki wannan jakar lu'u lu'u kaje can inda zaka boye kayanka sannan ka koma inda su yarima zainur suke ka kaimusu abincin da suka bukata amma ka sani cewa cin amanata ko yaudara a bakacin ranka yake. Koda jin wannan batu sai Ardadu ya risina ga Uraidu yace har abada bazan yi gangancin cin amanarka ba domin kuwa ni a rayuwata kudi suna gaba da komai ko wannan addini na yarima yazid dana karba na karbeshi ne bisa sa ran cewa zanyi amfani da shi wajen samun abin duniya amma kuma naga alamun cewa hakina bazai cimma ruwa ba ashe kune silar cika wannan babban buri na rayuwata ban sani ba. Ardadu na gama fadin hakan saiya sunkuya ya dauki wannan jakar luu luu ya sabata a kafadarsa ya dubi Uraidu yace lallai ko ta yaya zan kawo maka wannan taswira a cikin kwananki tara kamar yadda ka bukata.Koda gama fadin hakan sai Ardadu ya sake sunkuyawa ya dauki akushin daya siyowa su yarima zainur abinci ya fice da sauri. Fitarsa keda wuya saiya tafi izuwa gidan sarkin kasuwa akayi masa iso kafin Ardadu ya isa gidan sarki kasuwa saida yayi ta canja hanyoyi yana badda bami kuma yana ta waige waige domin ya tabbatar da cewa babu mai binsa a baya a matsayinsa na tsohon masanin tuggu. Abinda Ardadu ya aiyana a ransa shine su Uraidu zasu iya yaudararsa anan gana su kwace duk abinda suka bashi,lokacin da Ardadu ya isa gidan sarkin kasuwa ya kadaita dashi saiya gaya masa cewa babban hadimi ne na yarima Yazid kuma babu wanda hankalinsa ya kwanta dashi daya ajiye musu hajarsu face shi don haka ne suka kawo masa wannan haja domin ya ajiye musu sai ranar da zasu bar gari zasu zo su karba.Koda jin wannan batu sai sarkin kasuwa yayi murmushi yace yau shekarata arbain da daya kenan ina kan wannan matsayi nawa na sarkin kasuwa kuma duk abinda aka kawo mini ajiya ™Abbas Abdulkadir Hada Hada™ za'a dawo a riskeshi kamar yadda ka bani indai inayin son zuciya ta da ban kawo iyanzu ba akan matsayina. Da izinin ubangijina abin bautata zaka dawo ka iske ajiyarka lafiya kalau saidai sharadi guda daya,sharadin kuwa shine duk bayan kwana guda zaka bani ladan dinare hudu na lada ajiya sannan kuma ina son ka gaya mini wanda zai iya wakiltarka yazo ya karbi wannan dukiya idan har kai baka sami dawowar karbarta ba idan na sanshi a fuska shikenan idan kuma bansanshi ba sai ka gaya mini siffofinsa da kamaninsa. Koda sarkin kasuwa yazo nan a zancensa sai hankalin Ardadu ya dugunzuma ya rasa bainda ke masa dadi saboda yasan cewa bashi da wanda zai iya turowa ya wakilceshi akan wannnan dukiya kuma idan yace bashi da wakilin sarkin kasuwa zai iya zarginsa akan cewa akwai rashin gaskiya akan wannan dukiya.Koda Ardadu yaga bashi da wata mafita sai yasa hannu a cikin aljihun rigarsa ya dauko wani tsohon hatiminsa wanda ya saba amfani dashi lokacin da yake kan matsayin shugaban yan fashi ya mikawa sarkin kasuwa yace duk wanda yazo gareka da irin wannan hatimi to ka dauki wannan dukiya ka bashi. Nan take sarki kasuwa ya karbi hatimin sukayi sallama da Ardadu ya tafi. Acan tsakiyar kasuwa kuwa lokacin dasu yarima yazid suka ga cewa Ardadu ya dade sosai bai dawo daga siyo abinci da suka aikeshi ba sai mamaki ya kamasu. Yarima Zainur ya dubi Yarima Yazid yace anya kuwa lafiya wannan yaron naka ya dade haka bai dawo ba? Ina ganin cewa zaifi kyau mubi bayansa tunda bamu sani ba ko makiyanmu ne suka kai masa hari.Koda jin wannan batu sai

Chapter 8 of 15