Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zai baiwa mutum mamaki face yadda Zainur ke sara ta gaba da baya kuma sama da kasa kai kace iskace ke sarrafa hannayensa ba wai shike sarrafa su ba da kansa,nanfa arnan daji suka shiga uku suka rasa yadda akayi wannan karamin yaro yake gasa musu gyada a hannu.Saida aka shafe sa'a biyu cif ana wannan bakin artabu Zainur yana ragargazar arnan dajin amma an rasa mutum daya dazai sami nasarar koda lakutar jikinsa,koda arnan dajin sukaga irin mummunar barnar da yarima Zainur yayi musu domin ya kashe sama da kaso daya cikin kaso ukunsu kuma ko alamar gajiya babu a tare dashi sai suka fara cika wandunansu da iska suka juya da baya da gudu izuwa cikin jeji domin su tserar da rayuwarsu.Har Yarima Zainur ya fasa binsu amma daya juya ya dubi inda aka jefa wannan tsuntsu daya gasa cikin tabo aka tattakeshi sai ransa ya baci ya falfala da gudu yabi bayan arnan dajin duk wanda ya riska saikaga yayi masa falan daya, wohoho!ai koda arnan dajin suka waigo sukaga Zainur ya taso su a gaba yana dadayi musu barna sai suka kara ZAGE DAMTSEn gudun nasu nanfa aka kasa uban tsere na GUDUN CETON RAI! sai gashi SA GUDU YA KORI KI GUDU,haka dai akaci gaba da yin wannan tseren gudu baji ba gani,abinda zai baka mamaki kuma ya baka kunya shine wai yaro ne matashi dan shekaru goma sha shi kadai ya koro karti majiyan karfi sama dasu dari uku.Wannan karon dai da kyar Zainur ya sami nasarar riskar mutum hudu ya rafke har akayi gudu na tsawon sa'a guda cur,kwatsam sai Yarima Zainur yaga gaba dayan arnan dajin daya biyosu da gudu sun tsaya cak,kuma sun juyo sun fuskance shi suna haki ba tare da wata alama ta tsoro ba,koda ganin haka sai shima ya tsaya cak a inda yake saboda yasan cewa banza bata kai zomo kasuwa kuma ruwa baya tsamin banza,adaidai wannan lokaci ne Zainur ya lura da cewa ai sun shigo cikin yankin garin arnan dajin domin yana iya hango gidajensu tsilli tsilli a cikin dajin kuma yana iya hango matayensu da 'ya'yansu da yayyansu suna firfitowa daga cikin gidajen nasu daya bayan daya tamkar daman sunsan da abinda yake faruwa.Ko kuma abinda yake shirin faruwa,babu zato babu tsammani sai Zainur yaji motsin wani abu a samansa cikin iska kamar kibiya aka harbo,kafin ya daga kansa sama yaga ko meye tuni an doki kirjinsa.Saboda karfin dukan da akai masa shima saida yai sama kamar majaujawa aka jujjuya sannan aka janye shi.Bayansa ya maku da wata bishiya sannan ya fado kasa a galabaice yana aman jini da tari. A fusace Zainur ya daga kansa da zummar ganin wanda yayi masa wannan duka,koda yayi arba da wanda yai masa wannan dukan sai ya kidime kuma ya kamu da tsananin mamaki.Ba wani bane face kyakyawar yarinya wacce batafi shekara tara a duniya ba.Tana sanye da sutura irin ta wannan arnan dajin,amma a kanta akwai hular sarauta ta zinare kuma gadon bayanta ta rataya wata sharbebiyar takobi. Kawai sai Zainur yaga yarinyar tana kallonsa cikin murmushi kuma tana yafito shi da hannun cikin nuna alamun cewa ya taho suyi yaki.Cikin tsananin fushi da kunar rai Zainur ya mike tsaye zumbur yana ware hannunsa biyu masu rike da adduna kuma jini na zuba daga jikin addunan.Bai jira wata wata ba ya ruga da gudu izuwa wajen yarinyar yana mai kwarara uban ihu gami da daga addunan nashi sama cikin mugun nufi.Koda ganin haka sai itama yarinyar ta zaro sharbebiyar takobinta daga cikin kufenta ta falfalo da gudu ta nufi wajen da yake.Kodaya rage baifi taku uku su hadu dashi ba sai ta daka wani uban tsalle sama takai masa wawan sara a kai.Cikin zafin nama Zainur yai amfani da dukan karfinsa da zummar kare saran data kai masa amma duk da haka bai samu nasarar kare saran data kai masa ba saida saran nata ya zabtare wani bari na bakin gashin kansa.A haka ta shallake shi ta dirga a bayanshi bata gama dirga ba tasa kafa ta baya ta daki gadon bayansa.Zainur ya tafi ya fadi a kasa har saida bakinsa ya fashe jini yana zuba,amma sai yai zumbur ya tashi yana gyara jikinsa ya kuma gyara tsayuwarsa. A wannan lokacin yarinyar ta kuma kyalkyalewa da dariya shi kuma sai ransa ya kuma baci saboda ganin gashin kasan iska tana daukarshi tana yawo dashi,yakai hannunsa ya shafa lebensa yaga jini yake zuba.Hakan yasa ya yunkura zai taso mata,ganin haka yasa ta dakatar dashi ta kalle shi cikin murmushi da kallon raini tace masa.... Marbass Dan Aunty WASIKAR JINI!!! Littafi Na Daya (1) Part C . Cikin murmushi da kallon raini tace masa,Haba dan saurayi dakata mana shin fifikon nasara dana samu akanka bata isheka ba har kasan cewar nafika karfi na kuma fika iya yaki. Da inason na kashe ka da tuni nayi fata fata da namanka.Ka sani cewa ka aikata mummunan laifi daya kamata na kasheka tunda ka kashe min dakaru masu tarin yawa a cikin wannan daji kuma ka karyan dokata ta shigowa cikin wannan daji ayi farauta. Yakai Zainur dan waziri Ridwan kayi sani cewa nice Gimbiya Lazwara sarauniyar wannan garin da kake ciki kuma na gaji sarauta ne a wajen mahaifina fiye da shekara dari iyayena da kakanni na suke zaune anan babu wani sarki daga birninku daya taba tunanin ya yakemu ko kuma ya cutar damu.Amma kuma na gani a cikin madubin tsafina bayan mutuwar sarki Aiyuba na yanzu wato mahaifin Gimbiya Nauwara a lokacin yaki zai barke tsakanin mu daku, amma kuma na kasa gano barin dazai samu nasara a tsakaninmu. Babu shakka zamu zama Abokan Gaba tsakaninmu na tsiya-tsiya saboda ra'ayinka ya banbanta ainun dana mahaifinka.Sabo da kai baka damu da duniya ba kuma baka kaunar zalunci kuma baka son raini.Dan haka babu shakka bayan mutuwar sarki Aiyuba mutum daya daga cikin biyu dole zaiyi sarautar birnin Lailatul Harus kuma a cikin biyun kodai kai ko kuma mahaifinka.Idan kaine ka zama nasan ba zaka yakemu ba amma kuma idan mahaifinka ya zama babu makawa sai ya yakemu babu makawa kaine kadai zaka iya takawa mahaifinka burki,ko ka zamu masa matsala akan wulakancin da yakeson yayi mana.Wannan shine babban dalilin da yasa nayi maka rai a yanzu,yakai Yarima Zainur ina mai baka sharawa dakaje ka karawa kanka ilmin yaki da fada domin akwai babban aiki a gabanka nan gaba wanda ba zaka iya dashi ba.Da wannan furuci nake yi maka sallama sai watarana idan da rai da rabon zamu sake saduwa inba a filin yaki ba.Koda gama fadin hakan sai sarauniya Lazwara ta juya da nufin ta koma cikin birninta ta cikin wata babbar kofa,amma sai Yarima Zainur yayi wuf ya kira sunanta,ta waigo sannan ya durkusa kasa bisa guiwoyinsa cikin alamun biyayya kansa na sunkuye yace,Ya shugabata kafin mu rabu inason na nemi wata alfarma guda daya a wajenki inason ki bani dama na sake kawo miki ziyara domin nayi maki wadansu tambayoyi gami da neman wata bukata guda daya.Koda jin wannan batu sai Sarauniya Lazwara ta bushe da dariya sannan tace,ai dama nasan sai ka nemi alfarma a wajena a gaskiya a yanzu bazan iya saurarinka ba saidai kaje ka cigana da jirana,bayan nayi tunani da nazari idan naga ya dace na saurareka zakaga manzo daga gareni.Tana gama fadin hakan sai ta juya da sauri ta shige cikin birnin nata.Zainur yaga gabzawa arnan dajin masu kirar mutanen farko sunsha gabansa bisa dole ya hakura ya juya da baya ya nausa cikin dajin da gudu zuciyarsa cike da sake sake gami da dinbin al'ajabi ya nufi birnun Latul Harus. *** *** *** Tafiya yake cikin sassarfa yana ratsawa ta tsakakkaniyar duwatsu da suka yawaita a cikin daular tasu ta Hindu,kayan jikinsa irin yanayin suturun mutanen sin,kansa daure yaje da wani jan kyalle,bayansa rataye da wata kufai na masu,babu takobi a jikinsa sai wata rantsantsiyar gwafa duka rataye a bayansa.Takalminsa na fatar bauna,sadauki Yazid daya fito daga kasar Haural,cike da tsananin fushi mai tarin yawa,baiko waigawa bayansa domin idan ya juya ya dubi ganuwar birninsu sai yaji tamkar ya koma da baya ya fasa wannan tafiya tasa dan haka ya kautar da karkatar kansa ga barin kallon bayansa yayi gaba abinsa. Hankalinsa yayi gaba wajen nufar Birnin Latu Hurus inda sarki Aiyuba ke mulki ba komai yake jagorantar Yarima Yazid zuwa wannan birnin ba face zuwa neman WASIKAR JINI,da saurinsa yake takawa domin sanin cewa samun wannan wasika shine kadai abinda zai zamo masa yayewar masifar da take addabar yankinsu da kuma tsira daga masifar sark Aiyuba duk da cewar tunkarar kasar yake dan neman WASIKAR JINI ba saukekken lamari bane. Babu abinda yake tayar da hankalin Yazid face cutar data kama mahaifinsa bisa jin irin asarar da yayi wacce kuma bazata kawo zaman lafiya a yankinsu ba,dan haka ya kara azama,shidai wannan yanki na Haurul yana can ne a karshen yankin kasar Sin inda sarki Aiyuba baki daya yake mulka.Masifu da bala'i da yake addabar birnin shi ya haddasa musu fari da yunwa,kishirwa gami da farmakin arnan daji,da kuma dodonni da suke kawo musu bara a kowane karshen shekara. Tsananin takaicin wannan masifa itace ta sawa sarki ya kasance cikin tsananin cuta har ya zamana abinci saidai a bashi ruwa ma haka,wannan saida kyar yake iya sha,saboda irin jiki da yake fama dashi. Akwai arziki a cikin kasar Haural fiye da kima,wannan dalili ne yasa a koda yaushe barayi,yan fashi suke yin shigowar bazata cikin kasuwar garin suyi fashi su kashe na kashewa su kuma yi fyade ga matayensu,haka arnan daji idan sunso mugunta saisu farwa wannan yanki su ragargajesu su kwashe abinda zasu kwasa su gudu. A kwana uku da suka wuce,akwai wasu mahayan yan fashi sukayi shigowar sumame cikin birnin Haural cikin dare basu zame ko'ina ba sai cikin kasuwar garin.koda suka shiga cikin kasuwar sai suka farwa runfuna suka dinga kwasar kayan al'umma ciki kuwa harda kayan da ake karbowa daga kasar Latul Harus ake siyarwa kuma duk kayan sarki ne yake karbowa daga can din ya zuba a kasuwa idan an siyar a kaiwa sarki Aiyuba dukiyar da aka tara masa. Daga cikin kasashen da suke kasuwanci da sarki Aiyuba,kasar Haural suna daga na daya wadanda suka siyar masa da hajoji,kayan abinci da sauarn nau'ikan abubuwa da suke karbowa daga kasar sarki Aiyuba.Saidai duk wannan wawash kayan da kasar Haural suke sarki Aiyuba baya daga musu kafa duk sa'adda akayi lissafi aka samu akasi batare da dukiyar shi ta cika ba,sai an samu matsala domin sai yayi musu bure ya zare musu ido ya nuna cewar zai iya yaki dasu idan har basu nemo masa cikon dukiyarsa ba.Wannan dalili ne yasa a koda yaushe idan kasar Haural sukayi lissafi idan zasu fitar da dukiyar sarki Aiyuba idan suka lissafa sukaga babu cikon kudinsa to idan hankalinsu yayi dubu sai ya dugunzuma saboda tsananin tsoransa da sukeji.Sannan su zauna suyi kama kama su hada dukiyoyin attajiran kasar su hada masa dukiyarsa saboda gudun masifarsa. Da haka suke tsira daga azabar sarki Aiyuba kuma babu dalilin da yasa yaki jinin ya tausaya musu face sun banbanta a addini,shi yana bautar gunki su kuma suna bautar Allah(SWT).Wannan dalili ne yasa baya daga musu kafa baya jin kansu ko tausaya musu dalili dayane ma yasa yake basu kaya,dalilin kuwa shine suna tara masa dukiya a bagas.Koda yan harin sumamen yan fashin suka ragargaji kasuwar birnin suka kwashe dukiya sannan suka shiga babban ofis din ma'adanar dukiyar kasar ta cikin kasuwar suka kwashe komai sai suka haye dawakansu suka fice daga cikin kasar.Lokacin da gari ya waye,wasu dakarin da suke tsaron kasuwar suka nufo gidan sarki cikin tsananin dimauta hankulansu duka a tashe,cikin tsananin firgici koda zuwa sai suka yi cirko cirko suna sauraren fitowar sarki,jim kadan saiga sarki ya fito hankalinsa a tashe domin tun kafin zuwansu ya riga ya gama sanin abinda ya faru tun da akayi sallamar sallar asuba. Koda zuwa gabansu sai sarkin kasuwa ya duka gabansa cikin tsananin tashin hankali ya fara zubar da hawaye kafin yace komai.Sarki ya dubeshi cikin damuwa da dimauta yace,yakai sarki kasuwa abinda nakeson ji daga gareka yanzu shine ina babban ofishinmu inda ake adanawa sarki Aiyuba dukiyarsa da muka fitar aka tanada ana jiran ranar dazai aiko a basa kayansa,ina fatan dai ace a cikin wannan dukiya da take cikin babban ofishin kasuwa ba'a taba ta ba,in har wannan dukiya bata samu tabuwa ba to babu shakka mun tsira daga azabar rikicin dazamu fuskanta,in har kuwa Allah yasa dukiyar sarki Aiyuba bata tabu ba to duk irin asarar da mukayi saimu rungumi kaddarar Allah,in kuwa dukiyarsa ta tabo to saimu ce inna lillahi wa'innna ilahiraji'un,domin kuwa wannan babbar masifar tafi dukkan irin masifun da suke kawo mana barazana a cikin wannan yanki namu. Koda sarki Arsanal yazo nan a jawabinsa sai sarkin kasuwa ya dubi sarki cikin tsnanin damuwa daga bisani kuma saiya fashe da kuka,Al'amarin daya dugunzuma hankalin sarki kenan,yayi matukar tashi cikin tsananin firgici yace,mai ya faru yakai Zanur inason kayi maza ka sanar dani abinda ya faru.Zanur najin haka saiya goge hawayen fuskarsa cikin tsananin dimauta yace,ya shugabana hakika wadannan yan sumamen sunyi mana babbar illa ko kwatankwacin irinta ba'a taba yi mana ba,domin kuwa babu abinda suka bari daga dukiyar kasar nan kama zuwa dukiyar sarki Aiyuba da sauran kayansa da suka rage,kama da sauran hajojinsa.Duka wadannan yan sumame babu abinda suka bari yakai sarki mai iko da daraja. Fadar hakan keda wuya sai zuciyar sarki Arsanal ta buga take ya sulale kasa sharaf.Cikin azama aka daga shi aka shiga dashi cikin gidan aka kwantar dashi bisa shimfidarsa ana masa fifita, Matarsa da dansa Yazid suka nufo cikin turakar tasa a dimauce cikin tashin hankali,koda isowarsu sai sukayi arba da sarki a kwance baya iya motsawa wannan al'amari shiya kara dugunzuma hankalinsu kenan,sukayi sauri suka isa gareshi matarsa Barira ta durkusa idanunta dauke da hawaye tace,ya mai gidana mai ya sameka ka shiga cikin wannan hali? Yakai Mijina uban Yazid ka daure ka tashi gamu gareka,Yakai Abu Yazid ka daure ka tashi. Yazid ya risina ya kama hannun mahaifinsa yace,Ya abbana shin menene ya saka cikin halin suma alhakin yanzun nan ka fita cikin koshin lafiyarka,babu ko damuwa a tare dakai,yakai Abbana kada wani fushi yayi tasiri a zuciyarsa har yakai gamun rasaka,kayi juriya da dukkanin fitinar data razana maka zuciya.Allah (SWT) shine mai yayewa kuma ina mai rantsuwa da ubangijin musulunci duk irin abinda ya raunana maka zuciya zanyi iyakar nawa kokarin danna kawar maka dashi.Koda kuwa masiface kwatankwacin masifar dodannin da suke kawo mana hari a duk karshen shekara ya abbana kayi dauriya ka tashi. Jin wannan alwashi da Yazid yake dauka yasa sarkin kasuwa matsawa kusa dashi cikin tsananin tausayawa ya dafa kafadar Yazid yace,ya shugaba kayi hakuri kabi sannu a hankali domin shugabana yana cikin tashin hankali da buguwar zuciya ta haifar masa,abinda ya kamata kayi hakuri ka koma gefe ka zauna yanzun nan an tura likita yazo domin ya duba lafiyarsa. Lokacin da Yazid yaji wannan batu saiya waigo a hankali ya dubi sarkin kasuwa cikin ladabi da biyayya yace,yakai sarkin Kasuwa sanar dani meye yasa mahaifna zuciyarsa ta bugu harya kasance cikin tashin hankali ya shiga hali irin wannan? Koda jin wannan batu sai sarki Kasuwa ya rike hannun Yarima Yazid ya kuma jashi gefe guda daga cikin babbar turakar sarki,ana cikin haka ne saiga likitan sarki ya shigo da yar akwatunsa da take dauke da magunguna.Wannan al'amari ne yasa shi mahaifiyar Yazid ta baro gurin mijinta ta dawo gasu yazid da sarkin kasuwa a yayinda yake shirin fara labarta masa abinda ya faru. Sarkin kasuwa yayi gyaran murya cikin kallon Yazid da muryarsa mai nutsuwa da kwantar da hankali ga mai sauraro yace,abinda ya faru shine,adaren yau yan fashin sumame sunyi gangami wanda basu taba yin kamarsa ba haka zalika sun shiga cikin kasuwar garin nan sun kwashe duk wata dukiya da kayayyakin abinci da suke kasuwa,basu bar komai ba.Wani abin takaici bayan da suka gama satar tasu,sai suka dinga bankawa cikin gidajen da suke makota da kasuwa suna kama mataye sunayi musu fyade suna kuma kashe duk wanda yayi niyaryi musu katanga daga abinda suke aikatawa,tun a talatainin dare suka bayyana basu suka bar cikin kasar nan ba saida alfijir ya keto lokacin da aka fara kiran assalatu.Yakai Yarima wannan labari daya riski sarki shine abinda ya bakanta masa rai har yasa zuciyarsa ta buga. Koda sarkin kasuwa yazo nan a cikin batunsa sai hankalin Yazid ya dugunzuma cikin zuciyarsa ya fara tasbihi yana kiran sunan Allah,iyakar bacin zuciya zuciyarsa ta baci hankalinsa ya dugunzuma ainun.Domin lokaci guda jikinsa ya fara rawa naman jikinsa yahau karkarwa tamkar wanda ake sassara masa jiki.Duk irin sanyi da yake ratsa turaka sai ya zamana Yarima Yazid gumi ne kawai ke karyo masa. Barira kuwa kuka ta kamayi saboda tsananin firgici daga bisani tayi ajiyar zuciya ta dubi sarkin kasuwa tace,yanzu kenan dukiyar sarki Aiyuba duka har da ita suka wawashe? Sarkin Kasuwa ya jinjina kai ya amsa mata da cewa ai babu abinda suka bari a babban ofishin kasuwa komai sun wawashe hatta ragowar kayansa da sukayi kwantai basu bari ba sun tafi dasu.Nan take ta sunkuyar da kanta tasa bakin zanenta ciki ta toshe bakinta dan kada sautin kukanta ya cika daki.A hankali take furtawa shikenan mun shiga uku,mun lalace,shikenan sai mun dandana azabar sarki Aiyuba domin kuwa bazai taba yafe mana ba. Yazid cikin tsananin mamaki ya dubi ummansa ya durkusa gabanta yace,ya ummin waye sarki Aiyuba? Kuma mai zai sa mu dandana azabarsa dan dukiyarsa ta salwanta shin baisan kaddara ba? Ummansa ta girgiza kai cikin tarin takaici tace,Sarki Aiyuba yasan kaddara kuma yana da tsananin kirki yana kyautatawa al'uma domin abinsa bai rufe masa ido ba,saidai duk wannan kyautatawar dason taimakon al'ummar yanayinsa ne akan kafurai wadanda suke bautawa gunki,ko kuma suke tsafi, baya afuwa ga duk wanda ya kasance yana addini irin namu,baya kaunar musulunci da musulmai,kuma wannan abu har idan yaje kunnensa bazai damu ba da asarar da yayi ba,sai dimbin farinciki saboda ya samu hanyar dazai kuntata mana ya samu hanyar dazai tozartamu,tabbas idan har ba karbar addininsa mukayi ba babu shakka ko wanda yake cikin kada saiya fimu jin dadin rayuwa ko kuma wanda ya kasance cikin karkashin ruwa yana neman taimako. Dajin wannan batu sai Yarima Yazid yayi shiru yana tunanin tabbas yasan labarin sarki Aiyuba yana ganin shagunansa a kasuwar garinsu,kuma yanaji a yawan lokaci idan an tashi lissafin dukiyarsa mahaifinsa hankalinsa kan tashi ainun.Nan da nan ya shiga cikin damuwa ya kuma fara neman hanyar dazai magance wannan matsala tunda duk rintsi duk tsanani sai ya fitar da kasarsu daga cikin masifar sarki Aiyuba koda zai rasa rayuwarsa ne saidai hanyar dazai bi ya magance hakan ne bai santa inda zai biba. Muryar likitan da yake duba lafiyar sarki sukaji su dukan suka waiga gareshi,suka zuba masa idanu cikin firgici ba komai ne ya jefasu cikin firgici ba face ganin yanda alamun damuwa karara suka baiyana a fuskar likitan,da sauri Yazid,Barira da sarkin kasuwa suka nufi inda likitan yake zaune kusa da sarki da yake shimfide akan gadonsa na alfarma.Koda zuwa gabansa sai Yazid cikin kagauta ya dubi likitan yace,yakai babban amintaccen likitan abbana shine meye yake damun abbana? Koda likitan yaji Yazid da wannan tambaya sai ya dago kai ya dubeshi sannan ya sauke ajiyar zuciya yace,tabbas sarki ya samu tabuwa a cikin zuciyarsa wanda ta haddasu bisa faduwa da gabansa yayi,ta yiyu sarki yayi gamo da wani abu ne mai ban tsoro ko kuma akwai abinda ya sameshi wanda ya firgitashi ainun,dan haka yanzu abinda nake bukata shine abarshi ya samu hutu,na tsawon kwanaki arba'in a cikin wadannan kwanaki sarki zai fardado a kwana biyu rak,amma koda ya farfado zai kasance cikin yanayin mantuwa har tsawan wadannan kwanaki. Abin kiyayewa a cikin wadannan kwanki shine kada wani mahaluki ya sake ya sanar dashi wata magana da zata tada hankalinsa in har kuwa aka tunatar dashi to babu mamaki idan zuciyarsa ta kara bugawa ayi asararshi baki daya. Dan haka sai a kiyaye da wannan in Allah yaso zai samu sauki a cikin wannan kwanaki kuma a kwana arba'in din tunaninsa zai dawo.Koda likita ya gama yin wannan jawabi sai hankalin Yazid ya kara dugunzuma musamman da yaji anacewa idan aka kara tunatar da sarki wani abu zai bata masa rai zai iya asararsa.Nan danan ya dubi likitan yace,Ya likitan mahaifina kamar wacce magana da wacce magana ne ya kamata akadaita kunnensa dasu? Koda likitan yaji wannan tambaya sai ya dubi Yazid yace,ai duk wani abu da akasan bana dadi bane kada a sake ayi masa maganar domin kuwa yin hakan zaisai danasani ta hau kanmu domin tabbas za'a iya rasa sarki. Yazid yayi shiru yana nazari.Ana cikin haka saiga waziri da galadima duk sun shigo cikin turakar hankulansu a tashe saboda tsananin firgici har faduwa sukeyi saboda tsananin firgici.Koda isowarsu sai Yazid da mahaifiyarsa suka duka suka kwashi gaisuwa saboda tsananin tashin hankalin da suke ciki basu ma samu damar amsa gaisuwar ba,Barira ta fice daga cikin turakar shima likitan ya tafi bayan yayiwa su waziri bayanin irin abinda yake damun sarki. Waziri ya dubi galadima cikin damuwa yace,hakika tashin hankali ya tabbata a garemu wanda kuma bamu da mafita face ubangiji ya samar mana mafita,masifar sarki Aiyuba lallai saita tabbata a kanmu domin dama bashi da wani buri face yaga mun dakusar masa da dukiya,Gashi yanzu saura kwanaki goma sha biyar ayi wannan lissafin duka dukiyarsa anyi asararta. Hudijam masifa bata da rana sai a lokacin data tabbata,yakai Galadima ga sarkinmu rai a hannun Allah,mene dabara? . En uwa masu karatu ku basu shawara me yaka mata suyi? . Sai amin apuwa na rashin jina da wuri da patan za a karbi uzurina. WASIKAR JINI!!! Littafi Na Daya (1) Part D . Yakai Galadima ga sarkinmu yanzu rai hannun Allah,menene dabara? Koda jin haka sai galadima ya gyara murya ya nutsu sannan tafe,babu dabara babu karfi saina ubangijin musulunci ai bamu da abinda yafi face mu mika ragamarmu ga Allah domin kuwa shine kadai zai iya cetonmu. Waziri ya girgiza kai gami da gyara zama ya dubi sarki dake kwance bai masan sunayi ba,ya maida kansa ga kallon Yazid daya zuba musu ido cikin tsananin tashin hankali sannan ya maida kansa ga galadima yace,hakika maganarka gaskiya ce babu wanda zamu mika lamuranmu face Allah da ya halicce mu,saidai kuma ko ubangiji ya horemu da muyi yunkuri wajen kare kanmu daga dukkan masifar datake naman kawo barazana a garemu,wanda wannan hubbasa din da zamuyi shi zaisa Allah yaji kanmu da rahma ya taimakemu,amma muna kwance mu dinga tunanin taimako daga gareshi tamkar mun kasance lusaray ne. Galadima ya danyi shiru daga bisani ya dubi waziri yace,maganarka kaima gaskiya ce,ya zama dole muyi hubbasa domin kare kanmu daga irin masifar da zata tunkaro mu anan da kwanaki sha biyar masu zuwa,saidai abin tunanin anan shine fitinar da zata tunkaro mu ba irin fitinar da suka saba kawo mana farmaki bane da zamuyi yan dabaru mu korasu,inason ka sani shi sarki Aiyuba matsafi ne,baya ga haka kuma ya mallaki dumbin mayaka marasa iyaka,da idan ya turo mana kaso daya daga cikin kaso dari na dakarunsa sai sun cinye namanmu danye,bare nasan mugunta ta sarki Aiyuba domin ya tozartamu sai ya turo mana fiye da kaso goma,yanzu idan ya turo mana kaso goma daga cikin kaso na adawansa yaya kake tsammani zamu karke dasu.Koda waziri yaji wannan batu saiyayi shiru kawai domin maganar da galadima ya fadi gaskiya ce,dan haka sai ya gyara murya yace,abinda ya kamata yanzu ayi shela ana neman kowa a fada gobe dan aji shawarwarin kowa akan abinda zai kawo mana sauki daga cikin masifar da zata tunkaromu. Da wannan shawarar ta waziri suka dasa aya,washe gari da safe bayan an zauna a fada waziri ya wakilci sarki bisa girmansa da kuma jin maganarsa da ake a cikin kasar,ya fara bayani kamar yanda suka farashi da galadima har kawo karshen tattaunawarsu.Koda waziri ya gama kawo musu tattaunawar da sukayi shida galadima sai ya dora da cewa duk wanda yake da wata shawara zai iya kawo tasa domin dai a samu a tsira daga masifar da zata addabemu.Waziri yayi shiru na tsawan lokaci batare da kowa yace komai ba kowanne dake cikin fadar gabansa ne kawai yake faduwa.Domin tun lokacin da labari ya iske kowa an sace dukiyar sarki Aiyuba sai hankalinsu ya dugunzuma ya kuma kasa kwanciya da kyar aka samu wani attajiri wanda ake kira da suna Ishalu.Koda mikewar ishalu sai ya gurfana a tsakiyar taron yace,tabbas muna cikin tashin hankali da hali na tsaka mai wuya,abinda nake nufi anan shine muna cikin tashin hankalin da bamu da tabbacin fita daga cikinsa sai yanda hali yayi,ni a tawa shawarar ina ganin a samu mahayi ayi rubutu na wasika zuwaga sarki Aiyuba a shaida masa ga abinda ya samu dukiyarsa yayi mana hakuri ya karo mana kaya idan shekara ta zagayo sai mu biyashi rabin abinda zamu bashi a wannan shekara sannan mu bashi na shekarar da ake baki daya,inyaso wata shekarar ma sai ayi hakan,kunga kenanan mun jefi tsuntsu biyu da hogi daya,mun bi yasa kuma mun cigaba da cinikayya dashi sabanin yaji wannan batu ta sama,nasan halin sarki Aiyuba zai iya yin hawa da dakarunsa yazo ya wulakantamu.Koda wannan attajiri yazo nan a jawabinsa sai galadima ya mike tsaye yace,yakai Ishalu wannan shawara taka sam batayi ba,in baka manta ba,akwai yarjejeniya a tsakaninmu da sarki Aiyuba na rashin yin afuwa akan duk abinda ya samu dukiyarsa,kada ka manta sarki Aiyuba ya kwulla wannan kasuwanci damu ne bisa yahudawa da suka umarce dayayi hakan suka kuma kimtsa masa ta yanda zai ci galaba akanmu idan an kwulla wannan kasuwanci,kayi sani cewa sarki Aiyuba bai kulla wannan kasuwanci damu ba dan samun ribarmu ko dan samun cigabanmu ba. Ya kulla wannan kasuwanci ne dandai kawai yaci zarafinmu ya tozartamu ba dan komai ba duk a cikin nahiyarsa mu kadai ne kasar da mukeyin addinin musulunci,kuma yayi iyakarsa kokarinsa akan ya dakatar damu daga bautar Allah amma hakan ya gagara,tabbas idan aka tashi dan aike zuwa kasar Lautul Harus tabbas kafin cikar kwanaki hudu sai mashuna sunyi zaman dirshen a cikin kahonhunan zuciyoyinmu tabbasa sai jini ya gauraye da kasar wannan birni na Haural,in gar bamu kasance mu kafirta ba munbi abinda suke bautawa dan haka wannan shawarar taka sama bama kaunarta wata kwatankwacinta duk wanda zai kawo shawara ya zamana ya kawota daidai da fahimtarmu. Koda galadima ya koma ya zauna sai dukkan jama'ar da suke garin sukayi shiru babu wanda ya kare cewa kala har aka wuce dakika biyar sai daga can wani shehin malami da ake kira da suna Ibini Haisham ya mike tsaye cikin fararen tufafi kansa da rawani,koda mikewarsa sai yayi gyaran murya ya dubi daukacin jama'r da suke zaune yace,hakika zuciyarmu tayi rauni kwarai da gaske zuciyoyinmu sun cika da shakkun wasu zindikai kafurai masu bautar wanin Allah,lallai daga cikin hasashen karshen duniya wannan yana daga ciki yaku jama'ar musulmai kuyi sani cewa duk irin takamar da sarki Aiyuba yake ba da koma yake takama ba face sihiri,sihirin kuma baikai ayar Allah ba,ina mai son kuyi sani cewar bazaranar yawan dakaru da sarki Aiyuba yakeyi akanmu basu isayin komai akanmu ba face mun barsu duk irin yawansu da tarin bataliyarsu basu isa suyi nasara akanmu ba saida ikon Allah,lallai akwai bukatar jajircewa mu shirya kanmu kafin zuwan wannan rana kamar yadda kuka sani idan ranar da akai wannan lissafi ta cika ba a kaiwa sarki Aiyuba dukiyarsa ba babu makawa washe garin ranar inuwar gagaruman sadaukai zasu cika mana birni,zasu yi mana rumfa da masu zasu haskaka mana rayuwa da kaifin takubbansu,tabbas hakan gaskiya ne domin babu abinda zai hana faruwar hakan tunda dama abinda suke jira ya samu kenan.To idan haka ne mai zai hana muma muyi shiri mu fito mu kare kanmu daga saukar kibiyoyinsu da garkuwoyinmu,mai zaisa mu fito mu kare haskakamu dazasuyi da takubbansu mai zai hana mu zubar musu da jini kamar yadda zasu zubar nama,idan har muka tashi tsaye da addu'a da jajurcewa Allah daya haliccemu zai bamu sa'a akansu to wai ma menene takamar sarki Aiyuba? Ibn Haisham yayi ajiyar zuciya,Yarima Yazid ya zuba masa ido tunda aka fara wannan batu sai yanzu ne yaga abinda yake da bukatar ji,nan da nan hankalinsa ya fara

Chapter 2 of 15