Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
juya suka fice tare daga cikin dakin girkin ya kaishi inda suka saba zama suci abinci kan wani madaidaicin tebur.Bayan sun zauna sai Haiman ya zubawa zainur abinci kuma ya zuba masa ruwa a kofi yayi masa nuni dayaci abinci ba tare da gardamar komai ba kuwa zainur ya kama cin abincin hannu baka hannu kwarya har saida yaci ya koshi yayi gyatsa sannan Haiman ya dubeshi cikin nutsuwa yace,menene ya faru gareka jiya a daji sa'adda ka fita farauta? Koda jin wannan tambaya sai Yarima Zainur ya kawo gwauron numfashi ya ajiye ya kwashe labarin duk abinda ya faru gareshi a daji ya labarta masa tun daga lokacin daya harbo wannan tsuntsu ya gasa domin yaci kawo izuwan wadannan arnan daji suka wulakanta masa namansa har yakai su gayin yaki ya korasu har cikin birninsu inda sarauniya Lazara ta taka masa birki har sukayi wadannan maganganu shi da ita.Koda zaiyanu ya gama bashi wannan labari sai hankalin Sarki yaki Haiman ya dugunzuma ainun yayi shiru yana mai sunkui da kansa kas,al'amarin daya firgita jarumi zainur kenan kuma ya jefashi cikin rudani da wasi-wasi daga can sai Haiman ya daga kai ya dubi zainur cikin alamun tausayawa da damuwa yace,ya shugabana kayi sani cewa kasar nan nan gaba zata iya shiga cikin rudani da rikici na siyasa kuma ba kowane zai haddasa suba face mahaifinka waziri ridwan tabbas za'a zubar da jini mai yawa kuma za'ayi asarar miliyoyin rayuka da dukiya amma kai kadaine zaka iya hana faruwar hakan.Koda jin wannan batu sai idanun zainur suka zazzaro ya dubi haiman cikin alamun mamaki da firgici yace ya yaya zan iya tsayar da mahaifina akan kudirinsa alhalin yafini sanin tuggun duniya kuma yasan hanyar da zaibi ya yi maganin duk wanda yake ganin cewa zai iya kawo masa matsala. Sarkin Yaki Haiman ya gyada kai yace tabbas abinda ka fada gaskiya ne domin a duk fadin kasar nan ma sarki ne kadai baya shakkar waziri ridwan saboda ya fishi duk abinda yake takama dashi inason ka sani cewa waziri ya kasance kasaitaccen matsafi kuma gawurtaccen mayaki amma kuma a fagen yaki ko farcen kafar sarki bai kai ba ni kaina da nake kan wannan matsayi na sarkin yakin kasar nan waziri ridwan yafini karfin damtse da iya yaki idan har sarki aiyuba ya riga waziri ridwan mutuwa sai kowa ya shiga uku a kasar nan muddin baka yiwa tufkar hanci ba,hanyar da zaka yiwa tufkar hanci kuwa dayace dole ne ka cigaba da koyon yaki domin ka zamo zarton jarumin da babu kamarsa a wannan nahiya kamar yadda sarauniya lazwara ta baka shawara idan har kanason kakai kan wannan matsayi tofa saidai kaje ka koyi yakin a wajen sarauniya lazwara ko wajen sarki marwatu domin sune kadai suke da horon yaki na ban al'ajabi wanda suka samu a wajen iyayensu.Bayan kahau wannan matsayi na zarton jarumin da babu kamarsa dole ne kuma ka zamo mai tsaron lafiyar gimbiya nauwara domin taci gaba da zama akan matsayi +Abbas Abdulikadir hada hada+ na gadalimar wannan masarauta tamu donta haka ne kadai zaka iya kare kasar nan da jama'armu daga sarrin mahaifinka idan har kuma ba zaka iya zama mai tsaron lafiyar gimbiya ba dole ne ka nemi karagar mulkin kamar yadda mahaifinka ke nemanta ruwa a jallo domin ka tserar da komai da kowa na kasarnan. Sa'adda sarkin yaki haiman yazo nan a zancensa sai ran yarima zainur ya baci har idanunsa suka ciko da kwalla ya dubi sarki yaki yace,yanzu kana nufin kace dani na daura damar yin gaba kenan da mahaifina mu zama makiyan juna? Haiman ya gyada kai yace tabbas abinda nake nufi kenan kodai ka zabi kasarka da jama'arka ko kuma ka zabi mahaifinka ka sani cewa a yanzu babu abinda mahaifinka zai iyayi amma kasani cewa duk ranar da babu sarki aiyuba komai zai iya faruwa ina mai tabbatar maka da cewa wannan shawarar da nazo maka da ita yanzu itace babban burin sarki kuma komai dadewa da kansa zai kirawoka ya baiyana maka ita. Koda gama fadin hakan sai sarki yaki Haiman ya mike tsaye ya koma cikin turakarsa ya janyo kofa shi kuwa zainur a kan wannan tebur nacin abincin asuba ta riskeshi saboda kasa yin barci yayi saboda fargaba,mamaki da tunanin abubuwan da haiman ya gaya masa,tabbas hankalinsa ya dugunzuma ainun kuma har saida hawaye ya zubo masa. ******************************* Acan birnin Hairan kuwa lokacin da manzon ya dawo daga birnin Latus Harus tare da abinci mai yawa da kuma dinare niki niki a cikin buhunhuna sai farin ciki ya baibaye sarki marwatu da gaba dayan jama'ar kasar bisa ganin wannan waraka datazo musu ta fita daga talauci saboda tsananin farin ciki ma tun kafin tawagar manzo ta iso cikin garin sarki marwatu da manyan fadawansa sukayi hawa sukaje suka taro su kuma suka rakasu aka dawo izuwa cikin fada,nanfa gari ya rude da shewa,kade kade da bushe bushe na farin ciki.Bayan sarki Marwatu ya zauna akan karagar mulkinsa fadawansa sun zauna kowa ya nutsu sai sarki marwatu ya bayar da umarni a karanta amsar wasikar da sarki aiyuba ya aiko masa da ita.Nan take kuwa magatakarda ya cika aikinsa tun kafin a gama karanta wasikar ran sarki marwatu ya baci jikinsa ya kama karkarwa kuma zuciyarsa ta fara tafarfasa kamar zata kone nan take yaji kamar yasa amayarwa da sarki aiyuba gaba dayan dukiyarsa amma daya tuna da halin da kasarsa ke ciki na fatara,yunwa da talauci sai ya kasa.Nan take sarki Marwatu ya dubi manzon yace gaya mini duk abinda ya faru a lokacin da kajewa da sarki aiyuba wasikata fadarsa. Nan take kuwa manzo yayi cikakken bayani kamar yadda abinda ya wakana,koda sarki marwatu yaji irin shawarar da gimbiya nauwara ta baiwa mahaifinta sai yaji nan take ya tsaneta ainun kamar yadda ya tsani mutuwarsa kuma ya kudire a ransa cewa komai daren dadewa sai ya hallaka gimbiya nauwara saboda ya fuskanci cewar itace zata iya gadon mahaifinta taci gaba da samun fifiko akan gaba dayan sarakunan dake nahiyar amma abin tambaya anan shine ta yaya zai iya kasheta a sirrance ba tare da mahaifinta ya san cewa shine ya kasheta ba? Babu irin binciken da sarki marwatu baiyi ba a cikin hallarar tsafi akan yadda zai murkushe kasar latul harus ya mallake arzikin da suke dashi kuma ya kawar da sarki aiyuba ya mallake irin sihirin tsafinsa amma abu ya gagara saboda duk sa'adda yayi irin wannan binciken babu abinda yake gani face mutuwarsa.Bayan sarki marwatu yayi dogon tunani da nazari akan wannan sharadi da sarki aiyuba ya gindaya masa akan dukiyar da aka bashi aro saiya bushe da dariyar mugunta,nan take yasa aka shiga rarraba kayan abincin da aka kawo izuwa birane da kauyukan kasar sannan kuma ya aika aka gaiyato masa masana kasa da noma sukazo suka kama aiki gadan-gadan sannan kuma aka bude hanyar ruwa daga teku ya ratso izuwa dukkanin garuruwan kasar don gabatar da noman rani aka baiwa manoma rance jar da iri mai kyau suma suka kama aiki baji ba gani,aikuwa kafin shekara ta zagayo sai gashi birnin Hairan ya bunkasa akan harkokin noma da kasuwanci,arziki ya yalwata a hannun jama'a,fatara da talauci sukayi kaura tamkar ba'a taba shiga cikin yanayi mara kyau ba,kai saidai takai cewa a gaba nahiyar ma in banda birnin latul harus babu wani birnin da yafi birnin hairan girman kasuwa da daukakarta da kuma karfin arziki nanfa sarki marwatu ya shagala a cikin wadata da dukiya,hatta fadarsa ta mulki sai da aka rusheta aka gina irin ta sarki aiyuba aka kashe mata dukiya mai dumbin yawa.A ranar da shekara ta zagayo ne wasikar sarki aiyuba ta dawo ga sarki marwatu a karo na biyu wacce ta kunshi bukatar kudin da aka rantawa kasar hairan da kuma dakaso daya cikin kaso ukun ribar da aka samu acikin harkokin noman da akayi. Koda sarki marwatu yaji abinda wasikar ta kunsa saiya bushe da dariya nan take yasa aka rubu amsar wasikar inda ya bukaci ayi masa alfarmar karin lokaci na wata shida.Sa'adda aka kawowa sarki aiyuba amsar wasikar yaji alfarmar da sarki marwatu ya nema sai shima ya kyalkyale da dariya,a wannan lokaci fadar ta cika makil,gimbiya nauwara na zaune daf dashi a damansa a can gefe daya kuma sauran fadawansa ne su waziri ridwab a zazzaune sai muzurai sukeyi domin suji hukuncin da sarki zai yanke. Kwatsam sai sukaga sarki ya dubi gimbiya nauwara cikin murmushi yace masu iya magana sunce ta inda aka hau tanan ake sauka saboda haka yanzu wacce shwara zaki bani kamar yadda kika shawarceni a lokacin dana amince na bashi wannan taimako? Maimakon gimbiya nauwara ta bude baki tace wani abu sai ta mike tsam daga kan kujerarta taje har daf da sarki aiyuba tayi masa rada a kunne,take sarki aiyuba ya tuntsire da dariya yayi ta kyakyatawa kamar bazai daina ba,al'amarin daya razana kowa kenan a fadar banda ita kanta nauwara da kuma sarkin yaki Haiman.... Nima dai ganin wannan dariya tasa na razana na tsaya. WASIKAR JINI!!! Littafi Na Biyu (2) Part B . Banda ita kanta Nauwara da kuma sarkin yaki haiman. Daga wannan rana sarki aiyuba bai sakeyin batun dukiyar daya aikawa sarki marwatu ba har watanni shidan daya diba suka cika kai har ma wata shekarar ma ta sake zagayowa bai aiko masa ba kuma baice kala ba,al'amarin da yasa sarki marwatu ya saki jikinsa kenan saboda zatonsa sarki aiyuba ya hakura gaba daya da wannan dukiyar tasa yabar masa ita. Nanfa sarki marwatu yacigaba da bushasha abinsa ya rinka facaka da dukiya son ransa kai kace rijiyoyin dinare ne dashi. Kwatsam rana daya sai aka wayi gari a birnin Hairan wannan ruwan kogi da janyo izuwa cikin birnin ya kafe,fari ya afkowa gonakai ya zamana cewa kwari sun cinye gaba dayan amfanin gona duk fataken kasar kuwa sai suka durkushe basu tsira daga sharrin en fashi akan hanyoyinsu ba,bakin fatake kuwa masu kawo ziyarar ciniki a birnin sai suka dauke kafa nanfa ungulu ta koma gidanta na tsamiya ya zamana cewa mutanen kasar sun fara gudun hijira izuwa kasashen dake makwabtaka,da masifa takai masifa saida shi kansa sarki marwatu da iyalinsa suka fara fuskantar matsalar yunwa ba shiri sarki marwatu ya debi ragowar yar dukiyar data rage a hannun sa ta dinare buhu dari uku yayi shiri ya tunkari birnin latul harus. Bayan tafiyar kwana goma sha daya ne cif sarki marwatu ya iso birnin latul harus da safe a lokacin rana ta dan hudo,a wannan lokacin sarki aiyuba na zaune a fada gimbiya nauwara na zaune a damansa sai ga wani hadiminsa ya shigo da sauri ya zube kasa yana mai yiwa su sarki marwatu iso,koda akaji cewar sarki marwatu ne yazo sai kowa ya cika da tsananin mamaki ba tare da nuna wata damuwa ba sarki aiyuba ya bada izini akaje aka shigo da sarki marwatu da jama'arsa da kuma yar dukiyar dazo da ita.Kai tsaye sarki marwatu ya durfafi inda karagar sarki aiyuba take kansa a sunkuye,koda dakarun sarki aiyuba suka ga sarki marwatu na kara kusanto sarkin su sai suka yunkura suka zare takubba zasu tareshi amma sai sarki aiyuba ya daga musu hannu yana mai hanasu. Fuskarsa cike da murmushi dakarun suka mayar da takubbansu cikin kufe amma sai suka zubawa sarki marwatu idanu ba tare dasun daga hannuwansa akan kufen takobinsu ba,kuma sarkin yaki haiman ne akan gaba daf da sarki aiyuba ya kurawa sarki marwatu idanu yana jira ya gani kozai yi wani mugun nufi.Koda ya rage saura baifi taku biyar ba a tsakanin sarki marwatu da sarki aiyuba sai sarki marwatu ya tsaya cak sannan ya durkusa kasa bisa guiwoyinsa biyu a lokacin da hawayen takaici ya zubo masa sannan ya budi baki batare da ya iya daga kansa ya dubi sarki aiyuba ba yace ya kai sarkin sarakai kuma dodon sarakunan wannan nahiya kayi mini aikin gafara bisa cin amanarka danayi da kuma karya alkawarin danayi maka tsawon shekaru biyu,na tuba na bika kuma ina mai rokonka alfarma guda daya kuma ta karshe koda laifin danayi kisane hukuncinsa ina mai rokonka daka tausayawa jama'ar kasata ka dawo musu da arzikinsu na noma da kasuwancinsu kuma ka dauke musu farin daya addabi gonakinsu ni nasan cewa kayi amfani ne da karfin sihirinka na tsafi wajen jefamu a cikin wannan masifar. Koda sarki marwatu yazo nan a jawabinsa sai sarki aiyuba ya tuntsire da dariyar mugunta yayi ta kyakyatawa kamar ba zai daina ba,daga can kuma sai sarki aiyuba ya murtuke fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya dubi sarki marwatu cikin alamun tsananin takaici har kwallah ta cika masa idanu yace,yakai wannan sarki ma'abocin kaskanta a gabanmu kayi sani cewa laifinka yakai na hallaka ka yanzu take ba don komai basai saboda nasan cewa a duniya babu abinda ka tsana sama dani da kuma 'yata gimbiya nauwara kuma babu abinda kake so sama daka mallake wannan kasa tawa da duk arzikin cikinta amma saboda wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa shi yasa ka hakura bisa dole nasani cewa duk ranar da babu ni sai kayi yunkurin cika burinka akan 'yata da kasata don haka nima inanan ina shiri akan hanyar dazan bi na baiwa 'yata kariya a bayan na shude,na yarda zanyi maka alfarmar daka nema akan mutanen kasarka amma bisa sharadi guda sharadin kuwa shine dolene ka zabi wata gaba daga jikinka wacce baka sonta nasa ayanke maka ita wannan shine kadai abinda zai fanshi laifinka da kuma jama'arka. Koda sarki aiyuba yazo nan a zancensa sai hankalin kowa a cikin fadar ya dugunzuma aka cika da mamaki ita kuwa gimbiya nauwara dariyar farinciki ta kama kyalkyalawa a lokacin dashi sarki marwatu ya firgice kuma ya dimauce bai san sa'adda ya sake zubewa kasa a gaban sarki aiyuba yana mai yi masa sujjada yace,haba ya shugabana saboda me kakeson ka wulakanta sarki mai cikakkiyar daraja kamata kamai dashi masaki? Nikam na zabi ka kasheni dadai ka nakastani akn wannan bukata tawa.Ka tuna fa cewa ni gwarzon jarumi ne mai tarwatsa maza a filin daga dadai ace na rasa wani bangare a jikina akaron banza gwara ace a filin yaki ne na rasa kaina ko kafata ko hannuna domin zan mutu a cikin alfaharin cewa ni namiji ne kuma jarumi abin kwatance,dajin wannan batu sai sarki aiyuba ya bushe da dariya sannan yace dukkan sarki na kwarai kasarsa da al'ummarsa shine abinda yafiso,shin kasan irin tsananin wuyar da iyayena da kakannina suka sha kafin su sami nasarar gina wannan kasa tamu,shin kasan irin rayukan da suka salwantar da irin dukiyar da suka salwantar kafin su samo ilmin sihirin tsafin dana gada yanzu harna iya baiwa kasar tsaro na musamman? To ka sani rai da jiki ba abakin komai suke ba wajen kafa tubalin ginin kasa,idan har kanason ka gina kasarka ta sami kafuwa ta har abada dole sai jikinka ya zuba akan kasa wannan ce kadai +Abbas Abdulkadir Hada Hada+ hujjar da zata tabbatar da soyayyarka ta gaskiya akan kasarka da al'ummarka kai nake jira wane bangare na jikinka kakeso mu cire don samu biyan bukatarka a wajena? Lokacin sa sarki aiyuba yazo nan a zancensa sai sarki marwatu ya mike tsaye fuskarsa a murtuke ya mikar da hannunsa na hagu ya dubi sarki aiyuba yace na sallama hannuna na hagu domin gina kasata da al'ummata.koda jin wannan batu sai sarki aiyuba ya tuntsire da dariyar murna lokaci guda kuma ya turbune fuskar tasa ya dubi sarkin yaki haiman,take haiman ya risina cikin biyayya yace an gama ya shugabana.Yana gama fadin hakan sai ya zare takobinsa mai tsananin kaifi gayawa jini ya durfafi sarki marwatu. Adaidai wannan lokaci ne tsirarun dakarun sarki marwatu suka zube kasa suna kuka suka kama rokansa akan kada ya bayar da hannunsa a sare shi kuwa sai yayi biris ko kallonsu baiyi ba yabar hannunsa na hagu a mike sauran jama'ar dake cikin fadar kuwa sai kowa yayi tsuru tsuru ana mamaki da tausayin sarki marwatu sarkin yaki haiman ya tsaya daf da sarki marwatu ba bayansa ya daga takobinsa sama zai fille masa hannun kenan sai kawai akaji tsawa daga bakin kofar shigowa ana mai cewa a dakata. Take kowa ya dubi bakin kofar domin aga wanda ya bayar da wannan umarni,ba wani bane face Yarima Zainur Dan waziri ridwan ya tunkaro fadar kai tsaye ba tare da shakkar komai ba a lokacin da mahaifin nasa ya bishi da harara gami da kallon takaici. Yarima Zainur ya iso har gaban karagar mulki sannan ya zube kasa gaban sarki aiyuba ya kwashi gaisuwa,zainur ya daga kai ya dubi sarki cikin girmamawa yace,ya shugabana a matsayina na jinin wannan masarauta ina mai nemawa sarki marwatu sassauci akan wannan hukunci da aka yanke masa ya shugaban badon komai nake nema masa wannan sasauci ba sai saboda dalila gudu biyu,dalili na farko shine nasan cewa kai adali ne kuma mai tausayi,sarkin da ba'a taba neman wata alfarma a wajensa an rasa ba inhar masu neman alfarmar sun kasance masu bautar abin bautarmu,afuwarka bata yankewa komai rintsi a tarihin sarakunan kasar nan,kaine kadai sarki daya shekara arba'in akan mulki ba tare da anyi yaki ba ko sau daya,ya shugabana wannan hukunci da kake shirin yankewa akan sarki marwatu zai iya zama sanadin barkewar yaki a tsakaninmu da sauran sarakunan dake nahiyar nan saboda kaine sarki na farko daya taba wulakanta sarki a bainar taro cikin fadarsa,kodda mune zamu sami nasarar yaki akan sauran sarakuna aisai munyi asara mai yawa, dalili na biyu shine ya shugabana a kullum anason sarki yazamo mai rage makiyansa kada ya zamo mai karasu sarki marwatu tsohon makiyinmu ne kuma gaba ce data samo asali tun iyaye da kakanni wannan sassauci da zaka yi masa zai janyo karin martabarka a idon duniya kuma a idon makiya. Lokacin da yarima zainur yazo nan a jawabinsa sai jikin sarki aiyuba yayi sanyi matuka su kuwa sauran jama'arsa dake fadar sai suka cika da tsananin mamakin yarima zainur bisa basirarsa da hangen nesansa da kuma wannan kundumbala dayayi wacce ko mahaifinsa sai yaji tsoron yinta don kada fishin sarki ya tabbata akansa saboda ko kadan sarki aiyuba ya tsani wanda zaiyi masa shishshigi akan harkokinsa na mulki. Waziri ridwan bai san sa'adda ya kama murmushin farin ciki ba saboda ko kadan baya son a taba sarki marwatu sakamakon cewar tsohon abokinsa ne tun kuruciya tun sa'adda mahaifinsu sarki da ya gushe yake kai ziyara wajen mahaifin sarki marwatu a wannan lokacin shi sarki aiyuba ba'a zuwa dashi ko ina anata koyar dashi sha'anin mulki a gida saboda sani cewa shine zai gaji karaga baya ga wannan dalili waziri ridwan da sarki marwatu sun shirya a sirrance cewar duk ranar da sarki aiyuba ya mutu marwatu zai taimakawa ridwan ta kowane hali ya zama sarki mai cikakken iko kuma a kawar da gimbiya nauwara Sarki aiyuba saiya dago kai ya dubi yarima zainur cikin alamun tsananin takaici wanda har saida ya haddasa cikar kwalla a cikin idanunsa yace,yakai dana kayi sani cewa a iya sanina dakai baka taba neman alfarma ba awajena sai yau,kash inda kasan abinda zai faru nan gaba da baka nemawa sarki marwatu wannan alfarma ba tabbas bazan iya bada maka kasa a fuska ba saboda ina matukar jin kunyarka fiye da yadda nake ganin girman kowa a wannan fada,lallai bazan janye alkawari naba akan sarki marwatu na zubar da jininsa a matsayin fansa akan laifin dayayi mini,amma a maimakon hannunsa na dama da zamu yanke inason a yanke mini babban dan yatsansa na hannun hagu. Koda jin wannan batu sai hankalin sarki marwatu ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe ya yunkura da nufin ya juya da baya ya tsere amma sai sarki aiyuba ya nunashi da sandar hannunsa ta mulki take marwatu ya sulale kasa sumamme a lokacin da guntulallen dan yatsansa ya fada kan tafin sarki aiyuba Koda sarki aiyuba yaga dan yatsan sarki marwatu akan tafin hannunsa sai ya kyalkyale da dariyar farin ciki kuma ya mike tsaye daga kan karagar mulkinsa ya shige cikin gidan sarautar yana mai mutukar murna,a wannan lokacinne waziri ridwan yasa aka dauke sarki marwatu da sauri aka tafi dashi gidansa inda likita ya shiga yi masa aiki. Al'amarin gimbiya nauwara kuwa lokacin da fada ta watse kowa ya kama gabansa sai ta taho wajen yarima zainur ta dubeshi tace,inason ka biyo ni yanzu domin muje muyu wata magana mai muhimmanci,a cikin alamun mamaki da biyayya zainur ya risina a gareta yace ya shugabata yanzu har inada wata daraja da zaki tattauna muhimmiyar magana dani? Koda jin haka sai gimbiya nauwara tayi murmushi tace,ai darajar taka ma ta wuce haka yadda kake zato domin inda baka da ita da babu yadda za'ayi yau sarki ya saurareka har ya +Abbas Abdulkadir hada hada+ karbi alfarmar daka nema.Koda gama fadin hakan sai gimbiya nauwara ta juya ta nufi wani bangare na dabam na gidan sarautar cikin sauri yarima zainur ya bita a baya basu tsaya a ko ina ba sai cikin wani kasaitaccen lambu.Bayan sun shiga cikin lambun sun zauna sai kuyangi suka kawo musu ruwan inibi a cikin tambula da kofuna guda biyu akan faranti suka ajiye a gabansu har daya daga cikin kuyangin ta yunkura zata zuba musu ruwan ibinin da hannunta sai nauwara ta hanata ta sallamesu suka fice daga cikin lambun suna waigenta cikin alamun tsananin mamaki saboda yaune karo na farko da suka taba ganin gimbiya nauwara ta kebe da wani da namiji a cikin gidan sarautar harma tana shirin shayar dashi ruwan inibi da hannunta,shi kansa yarima zainur abinda ya daure masa kai yayi matukar bashi mamaki amma sai ya dake. Bayan nauwara ta zuba ruwan inibi a cikin kofuna gida biyu sai ta mikawa zainur kofin guda ita kuma ta dauki dayan saida kowannensu ya kurbi ruwan inibin sau uku sannan nauwara tayi gyaran murya ta dubeshi cikin murmushi tace,Yakai dan uwana waishin yaya kake ganin zaka iya kwatanta jarumtakar sarauniya lazwara akan taka? Koda jin wannan tambaya sai zuciyar yarima zainur ta buda da karfin gaske ya dubi nauwara cikin alamun tsananin mamaki yace,yaya kikasan cewa nasan sarauniya lazwara? Nauwara tayi murmushi tace shin ka manta ne cewa a nahiyar nan kaf babu matsafi kamar mahaifina?To kasani cewa duk abinda ya faru a gareka a cikin daji sa'adda ka fita farauta na gani a cikin madubin tsafina,tabbas na yava da irin jarumtakarka amma kuma da naga yadda sarauniya lazwara tayi maka duka daya ta kaika kas cikin galabaita sai jikina yayi sanyi kuma na kara tabbatar da maganar da mahaifina ya sanar dani akanka, mahaifina ya gaya mini cewa kaine kadai mutumin da zai iya barwa amanata a hannunka bayan mutuwarsa amma kuma ba zaka iya rike amanar ba face ka kara samin horon yaki ninkin wanda kake dashi kuma sai ka nemo WASIKAR JINI ta zame maka jagora a dukkan harkokinka. Lokacin da gimbiya Nauwara tazo nan a zancenta sai yarima zainur ya sake cika da tsananin mamaki yace,meye kuma wasikar jini? Nauwara tayi murmushi gami da gyara zama sannan tace wasikar jini wata wasika ce ta musamman wacce aka rubuta da tauwadar jini ta mutane tara su dai wadannan mutane tara sune asalin mutanen da suka fara zama a birnin nan namu na latul harus kuma sa'ilin da kakannimu a wannan masarauta babu komai a cikin wannan wasikar mai shafi dari daya face sirrika guda uku,sirri na farko shine gaba dayan dukiyar dake karkashin kasa wannan nahiya gaba dayanta,sirri na biyu shine duk wanda ya karance wasikar sai ya zama sarki a birnin latul harus,sirri na uku wanda shine na karshe wanda duk ya karance wannan wasikar jini saiya samu irin sirrikan tsafin da mahaifina ke dasu,a bayan mutuwar mahaifina kai da waziri ridwanne zaku bazama neman wasikar don haka ne nake son kai kayi nasarar ganinta da karantata kafin shi. Ka sani idan ya rigaka ganin wannan wasika shikenan karshen farin ciki da zaman lafiya yazo kenan a birnin namu ,amma idan kaine ka rigashi za'a cigaba da zaman lafiya da yalwar arziki har izuwa sa'adda danka zai gajeka babu wanda zai iya ganin wannan wasikar ta jini har ya iya karantata face ya kasance jinin sarautar nan gidan,bazaka iya zuwa inda wasikar jini take ba face kafi sarauniya lazwara karfi da iya yaki,in ba haka ba kuwa mahaifinka waziri ridwan zai kasheka da hannunsa don kawai biyan bukatarsa. Lokacin da gimbiya Nauwara tazo nan a zancenta sai hankalin yarima zainur ya dugunzuma ainun har hawaye ya zubo masa bai san sa'adda ya takarkare ba ya kwarara uban ihu kuma ya fashe da matsanancin kuka,da kyar nauwara ta rarrashe shi tace hakuri zakayi yakai dan uwana domin haka kaddararka ta kasance ka zama babban makiyin mahaifinka,ina mai shawartarka daka guntse bakinka kada ka kuskura bari mahaifinka yasan wannan al'amari tun yanzu domin idan ya sami tun yanzu zai kasheka kuma ka zauna a cikin shirin komawa birnin arnan daji domin ci gaba da karbar horon yaki a wajen sarauniya lazwara nida kaina zan raka ka mu nemi wannan alfarma kuma na tabbatar da cewa ba zata ki ba. koda zainur yaji wannan batu sai yayi shiru ya kurawa Nauwara idanu ba tare da yace komai ba. WASIKAR JINI!!! Littafi Na Biyu (2) Part C . Koda Zainur yaji wannan batu sai yayi shiru ya kurawa Nauwara idanu ba tare dayace komai ba. *** *** *** Al'amarin su Ardadu da Yarima Yazid kuwa lokacin da suka cigaba da tafiyarsu kasar Lahul Harus,tunda suka taho babu abinda yake dakatar dasu face sallah da cin abinci kuma sun kwashe kwanaki uku akan hanya suna wannan tafiya,saida sukayi nisa sosai sai suka hangi wasu matafiya a can gaba dasu sun nufo hanyar daga gani sunje kasar latus harus ne sunci kasuwa hanyar ta biyo dasu.Koda ganinsu sai Ardadu ya cika da tsananin farinciki domin ya gaji da tafiyar kasar da suke gashi Yarima Yazid sauri ne dashi tafiya suke kamar masu gudu gudu sauri sauri dan haka ne baya korafi,idan an tsaya yin sallah domin ya gwammace ayi ta sallah da wannan tafiya,sosai ya gaji.Dan haka sai ya dubi Yarima yace,ya shugabana wai mai ya hana muka fito ba tare damun samun dawakai ba,mun hau domin rage mana nisan tafiya,kana sane da cewa tafiyar da doki zaiyi ta yini daya itace wadda mu zamu yita a kwana uku,kaga kenan da akan doki muke tafe da tuni yau kwananmu tara kenan akan hanya. Koda Yarima Yazid yaji wannan batu sai yayi murmushi yace ai tafiyar kasa tafi dadi,dalili kuwa baka dauke da nauyi face nauyin kanka da ace yanzu da doki muke tafe da tuni mun takura shi kuma yanda mu kanmu bamu da yawan guzuri shima zai kasance bashi da guzuri,kaga kenan da tuni yanzu yunwa ta addabeshi a uzurinsa da banasa ba,kaga yanzu mu zamu iya jakuri ba kamar shi ba yadda yake dabba. koda jin wannan batu daga Yazid sai Ardadu yayi shiru daga bisani yace maganarka gaskiya ce amma kuma aishi dokin dama anyishi dan ya taimakawa bani adama,in hakane kuwa koda ya mutu wajen bauta mana kamar yayi jahadi ne,dan haka inason kayi hakuri da abinda zai faru yanzu domin ya zama dole mu samu dawakan da zasu rage mana nisan tafiya sannan mu samu karin guzuri.Dajin haka sai yarima ya dakata ya nunashi da yatsa yace bana bukata in kuwa ka kuskura ka kwace abin wani rabuwarmu tazo.Ardadu dajin haka sai yaja bakinsa yayi shiru badan ya hakura ba,tabbas ko baiyi kwacen doki ba sai yayi na dukiya,koda Ardadu yayi wannan tunanin saiya dubi Yazid yace todai ya kamata mu tsaya anan mu yada zango ni yanzu na fara gajiya baya ga haka ina jin bawali.Koda Yazid ya dubi sama sai ya fuskanci rana tayi haske sosai lokacin sallar azahar ya nufo take ya aminta da batun ardadu duk da cewar bai yarda dashi ba.Adaidai wannan lokaci shima Yazid ya dauki salkarsa na ruwa ya nufi can bayan wani dutse dan yayi bawali shi kuwa Ardadu sai ya tafi can yamma da inda Yazid ya nufa cikin sauri sauri ya nufi cikin daji ya rinka gudu. Shi kuwa Yazid sai ya fito daga inda ya nufo har ya samu guri ya kwanta bai jima da kwanciya ba lokacin sallah yayi koda yayi alwala ardadu bai dawo ba dan haka sai ya dan jirashi dansuyi jam'i amma shiru ganin kada lokaci

Chapter 4 of 15