Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya rube yasa makami ya sare abinsa da hannunsa,tundai munyi nadama bisa wannan kuskure da muka tafka ai ya kamata ka yafe mana ka sani cewa har abada mune iyayenka na jini baka isa ka canja mu ba duk inda ka wuce za'a nuna ka ace kai dana ne babu wanda ya isa ya kankare wannan. Kafin waziri ridwan ya gama rufe bakinsa tuni yarima zainur ya tari numfashinsa da kakkaurar murya yana mai cewa kada ka kara cewa kai ubana ne na jini babu wani uba na gari wanda zai kyamaci dan daya haifa a cikinsa face idan wannan da bai kasance jininsa ba,laifin me nayi muku kaida mahaifiyata har da zaku tsaneni kuki bani irin soyayyar daya dace? shin saboda kawai ra'ayina ya bambanta da naku ne? Shin saboda ku babu abinda kukeso a duniya sama da kudi,mulki da zalunci? Koda Yarima Zainur yazo nan a zancensa sai ya fashe da matsanancinkuka na bakin ciki.Waziri ridwan ya matso gaba zainur yakai hannayensa da nufin ya janyo shi izuwa kirjinsa ya rungumeshi amma sai yaji an kirawo sunansa.Yana jin muryar wanda ya kirawo shin saiya juya da sauri sukayi arba. Ba wani bane yake shigowa cikin gidan face sarkin yakin haiman,cikin sauri haiman ya karaso gaban waziri ridwan ya zube kasa bisa guiwoyinsa ya kwashi gaisuwa sannan ya mike tsaye cikin girmamawa kansa a sunkuye saboda biyayya yace ya shugabana lafiya kuwa naga kazo gidana a wannan lokaci na daf da ketowar alfijir? Ai kama ta yayi ka turo a kirawo ni idan kana da wata bukata a gareni.Koda jin wannan batu sai waziri ridwan yayi murmushi yace ai wajen dana nazo ba wajenka ba amma kaima inason mu gana cikin sirri,kodajin ™Abbas Abdulkadir Hada-Hada™ haka sai sarkin yaki ya dubi yarima zainur yace dashi ya tafi izuwa cikin dakinsa. Ba tare da wata gardama ba zainur ya juya ya tafi izuwa bangaren da dakinsa yake shi kuma haiman saiya wuce gaba izuwa falonsa sai suka zauna bisa kujerun,take wani hadimi ya kawo wa waizir ridwan ruwan shayi a kofi ya ajiye bisa teburin dake gabansa shi kuma haiman sai yayiwa waziri tayin shayin. Waziri Ridwan ya murtuke fuska ya dubi haiman a fusace yace ba shan shayi bane ya kawo ni gidanka nazo ne domin nayi maka wadansu tambayoyi,lallai inason ka bani amsoshinsu bisa gaskiya kuma sakamakon dazai biyo baya dama ce babba a gareka,tambaya ta farko a gareka itace me sarki ya gaya maka a cikin wannan dare na yau sa'adda ya gaiyaceka har cikin kuryar turakarsa? Tambaya ta biyu itace me ka sani dangane da babban abin dogaron sarki wato wasikar jini,kuma a ina aka boyeta? Tambaya ta uku wacce itace ta karshe inason ka gaya mini wasiyar da sarki yabar maka akan yarsa gimbiya nauwara tunda ya tabbatar da cewa kwanakin numfashinsa yazo karshe. Take sarkin yaki haiman ya mike tsaye yaje ya dauko takobinsa wacce ke rataye a jikin bango wannan ya durkusa a gaban waziri ridwan bisa guiwoyinsa kansa na sunkuye ya mika masa takobin da hannayensa biyu yace ya shugabana ga takobi na ka kasheni da ita domin hakan zai fiye mini sauki akan na bayyana maka sirrin dake tsakanina da sarki. Ka tuna cewa yau sama da shekaru arba'in kenan kai ma ina rufe sirrinka bisa duk irin tuggu da makircin da kake shiryawa sarki don mallake karagarsa ta mulki amma ban taba gayawa sarki laifinka ba,daidai da rana daya sarki yana yawan tambayata akan sirrinkanka amma ko sau daya ban yarda na sanar dashi komai ba duk abinda kaga ya sani akanka to ta hanyar karfin sihirin tsafinsa ya sani ai kuwa tunda har ban tona sirrinka ba a gareshi lallao shima bazan iya tona nasa sirrin ba a gareka,duk ku biyun shugabanni nane kuma kamar yadda ya zamo sarki kaima zaka iya zama sarki,ta yaya zaka iya yadda dani a lokacin da ka zamo sarki tunda kasan cewa bani da sirri zan iya tona maka asiri wata rana. Koda sarkin yaki haiman yazo nan a zancensa sai jikin waziri ridwan yayi sanyi kuma ransa ya baci ainun,zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone,nan take jikin ridwan ya kama tsuma ya fisge takobin daga hannun haiman ya zareta daga cikin kufen ya dagata sama da nufin ya sareshi amma saiya kasa don haka sai ya maida ita cikin kufen ya jefawa haiman abarsa yace ka rabani da dana,kuma kaki taimaka mini na hau karagar mulkin kasar nan a saukake,to ka sani cewa nasan babu abinda sarki ke so face dana zainur ya sami karagar mulki ina mai tabbatar maka da cewa muddin ina numfashi a doron kasa zainur bazai hau kan wannan karaga ba nine zan hauta don haka daga yau bani da babban makiyi a doron kasa sama da zainur kuma nine ajalinsa. Koda jin wannan batu sai idanun sarkin yaki suka zazzaro ya dubi waziri ridwan cikin alamun tsananin mamaki da tsoro yace haba yakai waziri shin ka mantane cewa zainur ne kadai danka a duniya yanzu kana nufin kace kafi kaunar duniya akan danka? Waziri ridwan ta gyada kai yace kwarai kuwa akan wannan karagar mulki na kashe uwata da ubana amma gashi ban samu ba don haka na gaba ma zan iya kashe dana domin na sameta a duniyar nan kaf babu wani abu dayafi wannan karagar mulki daraja a wajena amma a yanzu na gane cwa mutum uku ne manyan abokan gabata masu son rabani da wannan karaga kuma ba wadansu bane face kai,zainur da kuma gimbiya nauwara,muddin ku ukun nan kuna raye koda na hau kan karagar mulkin kasar nan bazan iya aiwatar da komai ba face na kawar daku. Na sani cewa zan iya kashe ka yanzu a cikin wannan daki naka tunda na fika karfin damtse,iya yaki da karfin sihirin tsafi,amma idan na aikata hakan sarki zai iya wargazamini dukkan shirina,nasan sarki yasan cewa nine na sa aka sa masa guba a cikin maganinsa yasha,kuma na tabbatar da cewa bazai wuce nanda wata biyu ba a raye a doron kasa,matsalata kawai shine rashin sanin inda wasikar jini take,tabbas a yanzu ko kai ko yarima zainur dayanku yasan a inda wasikar jini take amma nasan cewa ko kasheku zanyi ba zaku gaya mini ba,babu komai zansa ido sosai a kanku naga ta yarda zaku tafi izuwa inda wasikar jini take batare da kun sani ba. Koda gama fadin hakan sai waziri ridwan ya juya ya fice daga cikin yabar sarkin yaki a durkushe a kasa cikin tsananin tashin hankali da dimaucewa domin bai san abinda ya kamata yayi ba. washe gari da safe har yarima zainur ya gama kalaci tare da sarkin yaki da matarsa,sarkin yaki baice dashi komai ba,sai bayan sarkin yaki ya gama shiri tsaf zai tafi fada saiga yarima zainur ya fito cikin shiri zai tafi waniwani,cikin mamaki haiman ya dubi zainur yace ina zakaje yanzu da sassafe haka kuma gashi kayi shigar farauta? Batare da boye masa komai ba zainur ya risina ga haiman cikin biyayya yace zanje kasuwa ne domin nagana da wani bakon bafatake daga nan kuma idan da sauran lokaci inason na leka daji domin yin farauta. Koda jin wannan batu sai Haiman ya jinjina kai sannan yace,abinda zan gaya maka shine ka kula da kanka kuma duk inda zakaje da duk abinda zakayi ka tabbatar da cewar babu mai biye dakai don ganin sirrinka. Sa'adda zainur yaji wannan batu sai yayi murmushi yace nagode abbana har zainur ya juya zai fice daga cikin gidan sai ya juyo yace yakai abbana waishin jiya da daddare kiran me sarki yayi maka ne? Koda jin wannan batu sai sarkin yaki haiman ya murtuke fuska yace babu ruwanka da al'amuran dake tsakanina da sarki kamar yadda babu ruwana da naka al'amuran da kake kullawa asirrance. Gama fadin hakan ke ™Abbas Abdulkadir hada hada™ da wuya sai haiman ya dagawa wani hadiminsa hannu ya kawo masa dokinsa yahau ya fice daga cikin gidan,shima yarima zainur saiya ruga izuwa inda nasa dokin yake ya kama yahau,ya fice da gudu daga cikin gidan ya nausa izuwa cikin gari yana mai bin hanyar dazata kaishi izuwa kasuwa. Lokacin da yarima zainur yayi nisa ga barin gidan yazo wani wuri inda babu mutane sosai inda yake daidaikun gidaje ne sai kawai yaga wani narkeken kato tsaye a gabansa cikin shigar arnan daji.Katon ya risina ga yarima zainur ya kwashi gaisuwa sannan yace ya shugabana sarauniya tace ta aikoni gareka tace lallai intafi dakai gareta yanzu,koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube yarima zainur musamman da yaji cewa a yau zai sake ganin kyakkyawar fuskar sarauniya lazwara amma daya tuno da yanason yaje ga bakonsa Yarima Yazid ayanzu sai ya duni wannan manzo cikin murmushi yace naji dadi da sarauniyarka ta cika alkawari amma idan da hali inason ka rakani izuwa kasuwa yanzu domin naga wani bako nawa.Manzo sarauniya lazwara ya gyada kai yace ai bazan iya sake tsayuwa ba anan koda tsawon dakika arba'in bisa umarnin gimbiya saidai kayi hakuri,kuma abinda nakeso dakai shine yanzu kabi wannan hanya ka fara yin gaba ni kuma zan tsaya na tabbatar da babu wata matsala domin na fuskanci kamar cewa akwai masu binka a baya. Gama fadin hakan keda wuya sai sukaji motsi akan duhuwar ciyayi koda suka nufi wajen sukaji an fita da gudu suka kasa tsere yabar yarima zainur tsaye a wajen sai bayan lokaci mai dan tsawo sannan manzo ya dawo yace sun bace ni banga ko su waye ba,ya shugabana saika kula da kyau domin akwai masu sa ido akan al'amuranka,yana gama fadin hakan sai ya ruga da gudu a kasa da kafafunsa tamkar akan iska yake gudun.cikn sauri yarima zainur ya zuburi dokinsa da gudu ya bishi amma saboda karfin gudun manzon sai gashi dokin zainur ya kasa cimmasa,al'amarin dayai matukar baiwa yarima zainur mamaki kenan domin bai taba ganin mutumin da yafi doki gudu ba sai yau. Nan take ya gane cewa lallai wannan manzo da lazwara ta aiko shine mafi dacewa dayin wannan aiki,haka dai wannan manzo da yarima zainur sukayi ta sakin gudu a cikin daji suna ketawa ta cikin kwazazzabai,duhuwoyi kai wani lokacin ma har takan wadansu duwatsun suka bi inda sai kwararren masanin daji ne zai iyabi,amma sai gashi wannan manzo yana ta ratsa duk da cewa ko takalmi babu a kafarsa. Dan wata kaya kuwa take yake bi takanta tamkar sawun kafarsa na karfe ne,wata barauniyar hanya suka biyo ba waccen hanyar daya sani bace wacce sukabi sukazo birnin arnan daji ko rabin sa'a basu shafe ba suka iso birnin na arnan daji. Da isowarsu sukaga gaba dayan jama'ar birnin mazansu da matansu,yara da manyan sun taru sunyi dandazo a cikin wani babban fili sunyi kawanya ga dukkan alamu dai wani abu akeyi a tsakiyar filin suke kallo,tun daga nesa aka hango manzon sarauniya ya dawo sai aka busa wani katon kaho. Take hankalin kowa ya dawo izuwa bakin kofar shigowa birnin kuma jama'ar suka dare a tsakiya aka baiwa manzo da dokin zainur hanya suka kunno kai,nan take zainur ya hango wadansu zakakuran mayaka guda biyu suna ta fafata kazamin yaki mai tsananin ban tsoro domin kowannensu yana neman ran abokin fadan nasa ne. Sudai wadannan jarumai biyu sune mafi girma da kira ta sadaukantaka a gaba daya mazajen dake cikin birnin na arnan daji,kuma komai jarumtakar mutum idan yayi arba da wadannan jarumai biyiu dole ne ya tsorata don yasan cewa karo dasu ba wasa bane saboda kai da ganinsu kasan cewa suna da matukar karfin damtse idan kuwa kaga yadda suke yaki da tsananin zafin nama gami da jarumtaka ta ban al'ajabi dole ne a sallama musu,acan gefe daya kuma bisa wani gini mai tudu sai yarima zainur ya hango sarauniya lazwara zaune ta harde kafa daya bisa kan daya ga kuyanginta sama dasu dari a kewaye da ita,daf da ita kuma dakaru ne dauke da makamai sama dasu su dubu uku.duk inda yarima zainur ya hanga sai yaga dakarun birnin rututu. A tsaitsaye tamkar yaki zasu fita,babban abinda yafi bashi mamaki shine tsananin yawan dakarun sarauniya lazwara wanda indai lissafi za'ayi sun ninka dakarun nasu birnin sau goma,to waishin me yasa sarauniya lazwara batayi amfani da wannan dama ba ta yakemu ta dawo damu karkashin mulkinta? Amsar da yarima zainur ya kasa baiwa kansa kenan,abinda dai bai sani ba shine yawa mayaka bashine nasarar yaki ba,hanyoyin da akebi a samu nasara a yaki suna da yawan gaske.lokacin da manzo da yarima suka ratso ta tsakiyar yan kallo suka wuce wadannan jaruman gasa masu fafata yaki sai suka tunkari inda sarauniya lazwara ke zauna koda lazwara ta hangosu sai fuskarta ta fadada da murmushi ya mike tsaye daga kan kujerar da take zaune ta sauko kasan ginin da take bisa tari yarima zainur ta ruke dokin nasa tana mai yi masa barka da zuwa. Al'amarin dayai matukar baiwa gaba dayan jama'ar mamaki kenan domin wannan ne karo na farko da akaga sarauniya lazwara ta taso da kanta ta taryi wani bako.Yarima zainur ya sauko daga kan dokin nasa sannan ya risina ga Lazwara ya kwashi gaisuwa,lazwara ta karbi gaisuwar tace lale marhaban da zainur dan waziri ridwan biyoni muje izuwa cikin fadata domin mu zauna mu kulla yarjejeniya.Cikin mamaki yarima zainur ya budi baki da nufin cewa wani abu amma sai lazwara ta tari numfashinsa tace ka cika gaggawa ai bai kamata kayi mini wani korafi ba,kamata yayi ka tsaya kaji abubuwan da zanzo maka dasu.Tana gama fadin hakan saita juya ta nufi wani katon tsauni wanda akayi masa kofar shiga ta farin karfe dakaru shida na take mata baya,batare da fargabar komai ba kuwa yarima zainur ya bita a baya. ™Abbas Abdulkadir hada hada™ koda suka shiga cikin tsaunin sai ka yarima zainur ya daure kuma ya zama kamar wani dan kauye ya kama kalle kalle da waige waige ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin yadda aka kawata wannan fada wacce ko fadar sarki aiyuba bazata fita komai ba,duk da cewa a cikin kogon tsauni akayi wannan fada amma ko ina a haskake yake yadda ko allura ce ta fadi kasa sai ido ya ganta. Girman wannan fada ya ninka ta fadar sarki aiyuba sau uku ga fadi da tsawon gaske amma ko ina a shimfide yake da wani koren kilishi mai tudun gaske gami da tsananin laushi domin lokacin da yarima zainur ya dora kafarsa guda akai saida da tsoro ya shigeshi don ya zata lumewa zaiyi.An zuba kujeru na alfarma masu yawa, wadansu suka yiwa fadar kyau,karshen fadar an girke wata katuwar karagar mulki ta karfen zinare wacce akayi mata siffar tsuntsun dawisu. Dakaru sama da dubu goma ne suka kewaya wannan fada sannan kuma ga bayi,kuyangi da hadimai nansu da yawa suna ta aiyukansu kaca kaca a cikin fadar.Koda shigowar sarauniya lazwara cikin wannan bada sai gaba dayan mutanen dake ciki suka tsaya cak a inda suke suka daina motsi tamkar gumaka saboda biyayya harsaida lazwara taja yarima zainur izuwa can saman gini mai tudu inda karagar mulkin take,suka zauna tare sannan hadiman suka ci gaba da harkokinsu kai kace ruhinsu aka zare kuma aka dawo musu dashi.Nan take aka kawowa yarima zainur abinci da abinsha na alfarma sama da kala da dari bisa faranta ake jere a gabansa har da yayan itatuwa iri iri har dama irin wanda idanunsa basu taba gani ba,kuma harshensa bai taba dandanawa ba. Nanfa mamaki ya turnuke yarima zainur ya tambayi kansa a cikin zuciyar yace ta yaya wadannan arnan daji suka sami wannan gagarumar daula alhalin suna rayuwa a cikin wannan kungurmin daji kuma ko wata suturar kirki basa sawa face fatun dabbobin daji,amsar da yarima zainur ya kasa baiwa kansa kenan. Nan take lazwara tayiwa zainur tayin abincin suka kama ci tare saida suka ci suka sha sukayi hani'an sannan lazwara ta dubi yarima zainur cikin nutsuwa tace yakai yarima zainur yaudai gashi na cika alkawari na turo anzo dakai dangane da bukatarka ta son koyon yaki a wajena. Na amince zan koya ma amma bisa sharadi uku, sharadi na farko shine dolene ka fara jarraba jarumtakarka akan jaruman nan nawa guda biyu wadanda ka gansu a can kofar wannan fada tawa suna artabu.Idan har ka sami nasarar kaisu kas ko ka sami nasarar hallakasu a sannan ne zan fara koya maka irin nawa horon yakin badon komai ba sai saboda nina fisu karfi da iya yaki sau uku kuma babu wanda zai iya jure irin horon yakina face yafi wadancan jarumai biyu karfi da iya yaki. Sharadi na biyu shine bayan na koya maka yaki ka tafi izuwa dajin hajarul aswad ka sami nasarar karanta WASIKAR JINI idan ka zamo sarki zaka sadar da harkokin kasuwanci a tsakanin birnina da naka,ma'ana zaka bude mana kofar birninka mu rinka shiga muma zamu bude muku kofar birninmu ku rinka shiga kuma za'a yarda aure ya rinka faruwa a tsakanin mutanenmu da naku, sharadi na karshe zakayi alkawari a rubuce cewar har abada birninku bazai taba yin yunkurin kawo mana harin sumame ba domin maishe damu karkashin ikonku Lokacin da sarauniya lazwara tazo nan a zancenta sai hankalin yarima zainur ya dugunzuma ainun ya dubeta cikin alamun firgici da tsananin damuwa yace haba yake wannan sarauniya saboda me zaki shimfida mini wadannan sharuda haka masu tsananin tsauri,tabbas ko makaho ne ya shafi ni sannan ya shafi wadancan jaruman biyu naki yasan cewa bazan iya samun nasarar yaki ba akansu ba domin kuwa ance alamar karfi tana ga mai kiba,dangane da sharadi na biyu kuwa dana uku ki tuna fa cewa fiye da shekaru dari baya da suka shude babu wani sarki wanda ya taba jarraba yin kasuwanci da ku koya hada zuri'a daku kuma babu sarkin daya taba daukar muku alkawarin cewar bzai nemi birnin ku ba akan ya dawo karkashinsa,akan wane dalili kike son ni na karya tsohon tarihi wanda iyayena da kakannina akansu suka gushe. A gaskiya kinzo mini da babban al'amari wanda yafi gaban hankalina da tunani na saboda haka ina bukatar naje nayi shawara. Koda jin wannan batu sai sarauniya lazwara ta kyalkyale da dariya daga can kuma saita murtuke fuska ta dubi zainur tace bazan hanaka kaje kayi shawara ba,amma kasani cewa kwana goma sha hudu ne kacal a gabanka ka koyi wannan horon yaki wanda dole saika sameshi sannan zaka iya ratsawa cikin dajin da zakaje ka sadu da wasikar jini,har ka sami damar karantata in ba haka ba kuwa har abada wanna dama ta wuce ka,na baka kwana uku rak kaje kayi shawara ka dawo gareni amma fa idan ka haura kwana ukun shike nan damarka ta wuce. Koda gama fadin hakan sai sarauniya lazwara ta dubi wannan manzo wanda yazo da yarima zainur tace yakai saidur maza ka yiwa yarima jagora ya koma izuwa cikin birninsu na latul harus amma kabi dashi ta cikin boyayyiyar hanya ta uku. Saidur ya risina ga sarauniya lazwara yace an gama ya shugabata,nan take saidur ya nufi kofar fita daga fadar shi kuma yarima zainur saiya mike tsaye da sauri yabi saidur a baya yana waigen sarauniya lazwara yanayi mata wani irin kallo wanda ta kasa ne ma'anarsa shin kallo ne na soyayya ko kuwa kallo ne na takaici bisa zabin data bashi.Koda taga ta kasa baiwa kanta amsar wannan tambaya sai itama ta maida masa martanin kallo mai dauke da alamar tambaya wanda ya jefashi cikin rudani da wasi wasi. Har yarima zainur ya kusan isa bakin kofar fita daga fadar sai sarauniya lazwara ta kira sunasa cikin matukar mamaki ya tsaya cak ya waigo yana sauraron karasowarta a lokacin data durfafi inda yake,da isowarta daf dashi saita dubeshi tace idan ka isa wajen abokinka bakon bafatake Wanda yazo daga birnin Haural kace dashi inayi masa barka da zuwa kuma shima ina gaiyatarsa izuwa nan fadata a lokacin da zaka dawo tunda shima yana sha'awar ganin irin jarumtaka ta da iya yakina amma ka gaya masa cewa duk abinda yake zaton zai faru bashinezai faruba. Koda sarauniya lazwara tazo nan a bayaninta sai Yarima Zainur ya cika da tsananin mamaki Kuma ya tsorata ainun da al'amarinta.. WASIKAR JINI!!! Littafi Na Hudu (4) Part B . Kuma ya tsorata ainun da al'amarinta ya gamsu cewa lallai Lazwara ta cika gagarumar matsafiya tunda gashi tasan abinda bata nan ya faru. Nan dai yarima zainur ya juya ya fice daga cikin fadar jikinsa a sanyaye kamar wanda ruwa yaci,yana fitowa ya hango saidur ya nausa cikin daji yana mai bin wata sabuwar hanya,cikin gaggawa zainur ya kama dokinsa yahau,ya zubureshi da gudu har yaje ya riske saidur. Saidur ya dubi zainur yace wannan hanyar da zamubi doki bazai iya bin taba,ina mai shawartarka dakabar dokinka anan idan har kana bukatarsa in ka sake dawowa ka dauki abinka. Har zainur yayi niyar yaki yadda da wannan shawara ta saidur sai wata zuciyar tace dashi ai kuwa masu iya magana sunce da dan gari akan ci gari. Tunda har saidur ya bani wannan shawara kama tayayi nayi aiki da ita tunda shi ya fini sanin hanyar kuma nasan cewa shi baya bukatar doki tunda yafi doki gudu da juriyar tafiya a daji. Nan take ya tsaida dokin nasa ya sauko daga kansa kuma ya korashi da baya ya koma izuwa birninsu saidur. Koda ganin haka sai saidur ya falfala da azababben gudu izuwa cikin dajin. Aikuwa sai zainur shima ya take masa baya ya mai tsala gudu iya karfinsa,in badon ya kasance tsohon mzfarauci ba wanda ya saba gudu a cikin daji yayin yin farauta da cikin dakiku kadan saidur zai bace masa da gani. Duk da hakan ma saida ya bashi tazara maiyawa yayi masa fintinkau. Inda ya rinka samun matsala mashine ya cikin wadansu kogunan duwatsu ya rinka bi dashi wanda mutum bazai taba zaton cewa suna bullewa ba,kai wani kogon dutsen ma baya bullewa saidai kaga munyi nutso a cikin kogin dake cikinsa mun fito ta cikin wani babban kogo sannan muci gaba da iyo a cikinsa harmu fita mu cigaba da gudu mu sake fadawa cikin wani kogon,kai a wannan rana dai nasha bakar wahala domin saida muka shafe sa'a uku cur muna tayin wannan uban gudu a daji kuma muna ratsawa ta cikin kogunan duwatsu da kogi kai kace gudun ceton ranmu muke, saida na gaji likis na rinka haki kamar raina zai fita kuma ban kasa daina hango saidur ba har muka iso iyakar birnin arnan daji. A wannan lokaci ne na durkushe kasa bisa guiwoyina ina ta fama hakin kamar raina zai fita gashi makwogarona ya bushe saboda tsananin kishirwa,shi kuwa gogan naka saidur ko alamar gajiya ma babu a tare dashi,kuma babu wani haki da yakeyi,kawai sai ya dubeni cikin murmushi ya cire battarsa ta ruwan ya miko mini,cikin hanzari na fisge battar daga hannunsa na budeta na kafa abakina na kama kwalkwalar ruwan har saidai nayi gatsa sannan na sauke kaina kasa na mikawa saidur battarsa.Yana karbar battar saiya risina a gareni yace na barka lafiya yarima sai gani na biyu idan ka dawo birnin mu.Yana gama fadin hakan ya juya da baya ya falfala da wannan azababben gudu nasa tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya kafin kace wani abu tuni ya bace mini da gani. A sannan ne fana dawo cikin hayyacina sosai har na tsaya ina mamakin yadda akayi ma har na iya bin bayan saidur da gudu har yazamana cewa bai bace mini ba alhalin gudun nasa tamkar walkiya ne.Saida na shafe yan dakiku zaune a kas ina haki da hutawa sannan na mike tsaye na cigaba da tafiya ina mai tunkarar cikin birnin latul harus kai tsaye na durfafi kasuwa ina isa gidan da yarima yazid yake sai na iskeshi tare da abokin tafiyarsa Ardadu a tsaye a kofar gidan suna shirin su yawata a cikin kasuwar domin su sayi irin kayayyakin da suke bukata. Tun daga nesa Yarima Zainur ya kwalawa yarima yazid kira,sai yarima yazid ya waigo cikin farin cki ya taryeshi cikin alamun murna yazid ya dubi zainur yace yakai abokina kayi sani cewa tunda muka rabu ka barni a cikin zulumi da wasi wasi domin gani nakeyi kamar ba zaka sake dawowa gareni ba,kuma sai na fara tunanin cewa duk yadda ake ciki ka zagaye ka tafi izuwa birnin sarauniya lazwara ba tare da kazo ka gayyace ni ba mun tafi tare bisa wannan dalili ne zuciyata asare kuma guiwoyina sukayi sanyi na aiyana a raina cewa shikenan duk burina da shirina ya ruguje bazan taba samun abinda ya baroni da kasarmu ba. Lokacin da yarima yazid yazo nan a zancensa sai yarima zainur ya dubeshi yayi murmushi sannan ya zaiyane masa duk abinda ya faru a gareshi tun daga lokacin da suka rabu kawo iyanzu,koda jin wannan al'amari sai hankalin yarima yazid ya dugunzuma ainun ya dubi zainur cikin alamun tsananin damuwa yace kai yanzu dawa zakayi shawara bisa wannan sharadi da sarauniya lazwara tazo maka dashi? Zainur ya gyada kai yace babu wanda zanyi shawara dashi face kai. Cikin matukar mamaki yazid yace saboda me zakayi shawara dani alhalin kana da makusanta kuma aminai ai kamata yayi kaje kayi shawara da sarkin yaki ko kuma gimbiya nauwara amma bani ba,kai gimbiya nauwara ce ma tafi cancanta da baka shawara tunda itace ta fara sanar dakai duk sirrin dake cikin wannan al'amari. Koda jin haka sai Yarima zainur ya kada kai yace gimbiya nauwara ba zata iya taimaka mini ba kamar yadda na gaya maka da farko cewar inason ka dada gamsar dani akan addininka da ubangijinka,saboda haka inaso mu ajiye batu neman taimakon gimbiya lazwara a cikin tafiyar da zamuyi izuwa inda wasikar jini take,me zai hana mu dogara da ubangijinka akan ya bamu kariya idan harnaga irin karfin ubangijinka da kuma isarsa a cikin wannan tafiya mai mugun hadari da zamuyi lallai zan karbi addinin naka tunda gabannin ma mu isa inda WASIKAR JINI take, koda yarima zainur yazo nan a zancensa sai farin ciki ya lullube yarima yazid yace na amince da wannan shiri naka kuma ina mai tabbatar maka da cewa ubangijina bazai bani kunya ba lallai zaka sha mamaki kuma zakaga abubuwan al'ajabi da idanunka yanzu inda matsalar take shine ya za'ayi musan hanyar daya kamata mubi don zuwa inda WASIKAR JINI take? koda jin wannan tambaya sai yarima zainur yaja dogon numfashi ya ajiye sannan ya dubi yazid yace kafin nanda cikar sati biyu zamu sani,yazid yace yaya akayi kasan cewa zamu sani din kafin cikar sati biyu? Wanda ya sanar dani batu WASIKAR JINI shine ya sanar dani hakan amma fa ina zargin cewa sarkin yaki haiman ya san komai akan WASIKAR JINI amma bansan dalilin da yasa yake boye mini ba,kuma ina mai tabbatar maka da cewa wadanda suka san batun WASIKAR JINI A garin nan kaf basu wuce mutum biyar ba daga ni sai nauwara,sai sarki da kuma mahaifina waziri ridwan.koda jin wannan batu sai yarima yazid ya jinjina kai ya dubi zainur yace abinda nakeso dakai shine ka kula da kanka sosai domin mahaifinka zai iya sa ido sosai akanka kai da sarkin yaki haiman kuma duk yadda zaiyi yasan duk halin da kuke ciki sai yayi ba don komai ba sai don yasan hanyar dazai bi ya rigaku zuwa inda WASIKAR JINI take. Zainur ya numfasa yace tabbas sarkin yaki yayi mini nuni da hakan,ma yanzu dai mubar wannan magana haka muje na raka ku cikin kasuwa don na fuskanci cewar so kuke kuje kuyi siyayya. Yazid yayi murmushi yace wannan gaskiya ne. Nan take yarima yazid ya yafito Ardadu da hannu ya taho garesu kafin Ardadu ya riske su tun sun kara gaba inda zainur ya dubi yazid yace yakai abokina inason fa ka sani cewa hali zanen dutse ne don haka bana jin cewa Ardadu zai ajiye dukkan miyagun halayensa gaba daya kuma bana fidda ran cewa wata ran zai iya cin amanarka don haka jansa a jikinka abune mai hadari. Naso ace tun sa'adda kukayi gamuwar farko ka aika dashi barzahu domin barin mugun iri kamarsa a doron kasa ba karamin ganganci bane, WASIKAR JINI!!! Littafi Na Hudu (4) Part C . Naso ace tun sa'adda kukayi gamuwar farko ka aika dashi barzahu domin barin mugun iri kamarsa a doron kasa

Chapter 7 of 15