Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
haka dai su jarumi Damzur suka cigaba da sa ido akan Aryala har cikinta ya tsufa ya cika wata tara.A ranar da nakuda tazowa Aryala ne akayi abin mamaki da baza'a taba mancewa dashi ba domin a ranar ne kauyen gaba daya ya sauya hadari ya gangamo alhalin lokacin bazarane bana damina ba,aka rinka tsala ruwan sama tamkar da bakin kwarya,kuma a ranar ne dabbobin daji suka firgice suka shigo cikin gari suka cudanya da mutane ba tare da son cutar dasu ba. A ranar ne jama'a sukayi ta hako zinare,lu'u lu'u a ko ina cikin kauyen daga sauran kauyukan dake makwabtaka dasu domin wannan bakon jaririn dan baiwa da aka haifa. Daga wannan rana Aryala taci gaba da rainon jaririnta,jarumi damzur da barde husum kuwa sai sukayi wata katuwar gona suka kama noma a cikinta inda suka sami albarkar noman suka zamo babu tamkarsu a harkar noma a kauyen gaba daya. Sannu a hankali jaririn Aryala yacigaba da girma ai kuwa yana cika shekara shida a duniya sai Damzur da Barde Husum suka fara koya masa yaki. Lallai barewa batayi gudu ba danta yayi rarrafe,aikuwa shekara shidan ne wannan yaro wanda ake kira da suna Goga ya rinka yin gagarumar jarumtaka wacce ta ninka wadda mahaifiyarsa tayi sau goma domin tun a sannan yake iya fada da karti arba'in ya kaisu kas saboda tsananin karfin damtsensa da iya yakinsa. Lokacin kuwa da ya cika shekara goma shi kadai yake shiga daji yayi farautar yan fashi komai yawansu sai yazo da kawunansu ya lodosu akan dokinsa yazo dasu cikin kauyen,saidai kawai mutane suyita al'ajabin wannan jarumtakar tasa.A wannan lokaci ne aka samasa suna Jarumi Sha Yaki ba don komai akasa masa wannan suna ba sai saboda yana iya shafe kwana uku yana yin yaki batare daya gaji ba. Wata rana ya dawo daga yin farauta a daji sai kawai yaji mahaifiyarsa dasu jarumi damzue suna hirar abinda ya faru tun kan a haifeshi don haka saiya labe ™AbbAs AbdUlkAdIr hAdA hAdA™ yana sauraransu a sannan ne yaji tarihin yadda aka sami cikinsa da yadda bakin cikin hakan yasa ta hakura da kasarta da mulkinta.Koda jin wannan labari sai hawaye ya zubowa Goga Sha Yaki yaji ya tsani sarki Uzaima da dukkanin sarakunan dake waccen nahiyar ma,take ya dauki alwashin cewa saiya kawar da dukkanin sarakunan ya kafa sabuwar daula tasa da karfin tsiya...... Koda Yarima yazo daidai nan a labarinsa sai kawai ya fahimci asuba tayi,al'amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan nan take ya katse labarin dayake baiwa su Nauwara yace kowa ya tashi ayi alwala domin gabatar da sallar asuba. Koda jin haka sai kowa ya cika da mamakim yadda akayi har asuba tayi basu sani ba saboda dadin labarin da yake basu. SHIN SU YARIMA YAZID ZASU ISA KOGON HAJRUL ASWAD A RAYE SU DAUKO WASIKAR JINI? WANE IRIN MUGAYEN MASIFU ZASU HADU DASU AKAN HANYA KAFIN SU ISA CAN? TSAKANIN WAZIRI RIDWAN DA YARIMA ZAINUR WAYE ZAI GAJI SARAUTAR? INA LABARIN SARAUNIYA LAZWARA? SHIN ITAMA ZA'AYI WANNAN TAFIYA TARE DA ITA? MENENE DALILIN DA YASA LOKACIN DA GIMBIYA NAUWARA DA YARIMA YAZID SUNA GANIN JUNA SAI ZUCIYOYINSU SUKA BUGA DA KARFI? Godiya ta musamman Ga Allah (SWT)Madaukakin Sarki,Mai Rahama Mai jin Kai daya bani ikon Kammala "Wasikar Jini" 1-6. kuma zamu cigaba da 7 insha Allahu ina neman goyon bayan ku 100% kamar yadda nake tare daku da fatan bazakuban kunyaba ta wajen comment da like and share.. Littafi Na Bakwai (7) Part Â. . Yauwa wa BAYAN SU YARIMA YAZID SUN IDAR DA SALLAR ASUBA ANYI ADDU'A AN SHAFA A CIKIN WANNAN KOGON DUTSE.Sai Yarima Zainur ya dubi sarkin yaki Haiman tace yakai Abbana yanzu zamuyi bankwana daku anan ni da Yazid mu tafi izuwa can kogon Harul Aswad in yaso kai da uwata da gimbiya Naurawa da dakarunka sai ku cigaba da zaman jiranmu har Allah ya dawo damu domin kuwa rayuwarku zata zama a cikin mummunan hadari idan har kuka fita daga cikin wannan kogon dutse saboda na tabbatar da cewa a yanzu haka Waziri Ridwan da dakarunsa nan nan suna farautarmu. Kafin Zainur ya gama rufe bakinsa tuni Sarkin yaki Haiman ya tari numfashinsa yana mai cewa haba yakai dana saboda wane dalilin zaka hanani yin wannan gagarumar tafiya wacce ko mutum mutuwa yayi a sanadinta tamkar shahada ce yayi tunda akan nufin daukaka KALMAR ALLAH muke. Ka tuna cewa na sami lafiyar jikina tamkar ban taba yin wani ciwo ba.Ka tuna da yakin da mukayi da wadannan dakarun sumame yadda Allah ya bamu sa'a akansu a cikin kankanin lokaci. Dan haka ni yanzu babu abinda nake shakka ko nake tsoro face ubangijin musulunci. Dani da matata da dukkan wadannan hadimai nawa da kuma gimbiya Nauwara duk sun sallama rayuwarsu domin daukaka kalmar Allah saboda haka kawai muyi tafiya tare gaba dayanmu. Wuya bata kisa kuma dole sai ansha wuyar sannan akan sha dadi,wannan tafiya da zamuyi itace kadai babbar madogarar da zamuyi amfani da ita wajen jaddada addinin gaskiya a wannan nahiya gaba daya. Koda sarkin yaki Haiman yazo nan a jawabinsa sai gimbiya Nauwara taji wani irin gagarumin farin ciki ya lullubeta bisa jin cewa tare da ita za'ayi wannan tafiya dik da cewa tasan halin data baro mahaifinta a kan gangarar mutuwa. Tuni itama a cikin zuciyarta ta yanke kaunar sake saduwa da mahaifin nata tunda tasan cewa bashi da niyar karbar addinin gaskiya bare ya sami dace da samin babban rabo a wajen Allah. Ba tare da wata gardama ba shima Yarima Yazid ya amince da suyi wannan tafiya tare gaba dayansu.Nan da nan kowa ya kimtsa suka hau dawakansu suka fita daga cikin wannan kogon dutse suka nausa izuwa cikin daji. Saida sukayi tafiya mai tsawo batare da sun hadu da komai ba har rana tayi sosai.Yazid ya shawarci Yarima Zainur dasu yada zango a wannan wuri ayi sallar azahar kuma a ci abinci in yaso a cigaba da tafiya. Batare da wata gardama ba kuwa ya amince da wannan shawara.Bayan an idar da sallah an fara cin abinci ne kwatsam sai yarima Yazid ya cire hannunsa daga cin abincin ya mike tsaye zumbur ya kurawa gabas idanu.Al'amarin daya razana kowa kenan a wurin kuma yasa yarima Zainur ma ya tsaya ga barin cin abincin ya mike ya dubi Yazid cikin kaduwa da mamaki yace,yakai Abokina lafiya kuwa naga ka daina cin abincin ka mike tsaye zumbur haka? Me yasa ka kura idanunka izuwa gabashin wanann daji? Sa'adda Yarima Yazid yaji wannan tambaya sai yayi ajiyar zuciya yace inaji a jikina cewar a koyaushe za'a iya kawo mana hari na MAMAYAR BAZATO daga gabashin wannan dajin. Zuciyata tana gaya min cewa akwai abokan gaba a bayanmu masu farautarmu kuma nan da lokaci kankani zasu riskemu anan. Koda jin wannan batu sai Yarima Zainur yayi dariya yace waishin a mafarki aka nuna maka wannan al'amari ko kuwa hasashen kawai kakeyi? Yazid ya dubi Zainur fuskarsa a murtuke babu alamar raha ko wasa yace ba mafarki nake yi ba kuma ba almara bace.Yau da gobe ce tasa na kiyasta faruwar hakan.kuma ni Allah hore mini baiwa irin wannan tahin abinda zai faru tun kafin ya farun. Koda jin haka sai sarkin yaki Haiman ya dubi Yarima Zainur yace yakai dana ka sani cewa nima nayi imani da abinda yarima Yazid ya fada dan haka ya zama wajibi mu dauki matakin gaggawa. Yakai Yazid yanzu menene abinyi?Yazid yayi ajiyar numfashi sannan ya dubi Haiman yace maza kasa a kwashe komai namu daga nan aboye acan gaba kadan amma abar tantuna kamar guda uku. Mu duka zamu ja da baya mu buya a cikin duhuwoyi amma mu zagaye wannan sansani muna masu dana KWARI DA BAKA. Kafin nan zamu haka kasa mu binne tarkuna kamar guda dubu kuma zamu daddaura mugayen tarkuna a saman jikin bishiyoyi suma kamar guda dubu. Cikin kaduwa da mamaki Haiman ya dubi Yarima Yazid yace ta yaya kake zaton cewa zamu iya kammala wannan aiki a cikin kankanin lokaci kuma a tunaninka makiyan da suke biye damu suna da yawan da har sai munyi musu wadannan mugayen tarkuna haka? Yazid ya gyada kai yace kwarai kuwa makiyan dake binmu sun ninkamu yawa sannan kuma sun fitowa ne da gagarumin shiri domin su hallakamu kuma su rabamu da wannan taswira ta zuwa kogon Hajarul Aswad.Lallai idan mukai gaba da gaba dasu sai sun karar damu gaba dayanmu.Hakan ma da zamuyi yan dabaru ne mu dana musu tarkuna na bazato ba iya karar dasu zamuyi ba,amma zamuyi matukar razana su har su karaya su ja da baya,mu kuma sai musan wata sabuwar dabarar da zamuyi musu. Illa haka zamuyi ta fafatawa dasu har mu isa kogin Hajarul Aswad.Abinda nasani kawai shine yayi da tafiyar ta nutsa damu dasu duk rayuwarmu tana cikin hadari sai mai yawan rai zai kai labari.Abinda nake so daku shine musa aranku cewa ubangijin gaskiya na tare damu kuma shine kadai zai kare mu daga dukkan abin ki.Ya bamu nasara bisa abinda mukasa a gabanmu.Koda gama fadin haka sai Yarima Yazid ya zabi mutum ashirin daga cikin yaran sarkin yaki suka tafi izuwa cikin daji da gudu sukaje suka saro rassan bishiyoyi akazo aka fikesu.Wasu aka binne su a karkashin kasa wasu aka tabesu aka daddaure su a saman bishiyoyi cikin duhuwar ganyaye.Saidai su Yarima Yazid suka shafe kusan sa'a daya da rabi suna wannan aiki,kuma duk sa'adda Yazid yake ™Abbas Abdulkadir hada hada™ kokarin hada tarko sai yaga Gimbiya Nauwara ma tana kwaikwayon abinda yakeyi kuma sai gashi tana yinsa mai kyau da inganci kamar tasan yadda akeyi. Al'amarin daya daure mai kai kenan ya bashi mamaki.Da zarar Nauwara taga zata hada idanu da Yarima Yazid sai tayi sauri ta kau da kanta saboda ta tsare darajarta da kimarta ta 'ya mace kuma yar sarki.Ba komai ne yasa hakan ba face ta fahimci cewa tabbas zuciyarta ta kamu da son wanann kyakkyawan saurayi ma'abocin kyau da kwarjini amma sai tayi alkawari da zuciyarta cewar ba zata nuna masa sirirn zuciyarta ba face ya fara tuna mata da kansa. Tabbas rashin sani yafi dare duhu.Inda Nauwara tasan waye Yazid a bangaren kunya da kuma danne SIRRIN ZUCIYArsa da batayi gangancin yanke wannan hukuncin ba. Bayan an kammala kafa tarkuna a cikin karkashin kasa da saman bishiyoyi kuma dukkan kayayyakinsu an kaisu can gaban sansanin an boye sai aka bar tantuna uku kawai kuma akayi mutum mutumi na dakaru guda shida kacal aka tsaida su a kusurwoyin sansanin hudu. Kai har wuta aka kunna a tsakiyar sansanin aka ajiye dakaru na mutum mutumi guda hudu a zaune sun kewaye wutar alamar cewa dumi sukeji saboda dama a na cikin lokacin matsanancin sanyi ne.Gama yin hakan keda wuya sai su Yarima Yazid suka bar wajen gaba dayansu sukaje suka biye dawakansu kuma suka hau saman bishiyoyi suka zazzauna bayan kowannensu ya lullube jikinsa da ganyaye gaba daya,idanunsu ne kadai a waje kuma tazarar dake tsakaninsu da sansanin batafi kamu talatin ba ya zamana cewa a saman sun yiwa sansanin KAWANYA. Haka dai su yarima Yazid suka cigaba da lampo akan bishiyoyi kamar birirrika, abu kamar wasa har saida rana ta fadi ko motsin wani abu basu ji ba ko a cikin dajin kuma basu hango wata runduna ba mai zuwa. Al'amarin da yasa zuciyar kowa ta karaya kenan kuma guiwarsu tayi sanyi.Kuma duk suna rike da kwari da baka.Sai Nauwara ta sauke bakanta kasa ta cire kibiyar ta mayar da ita cikin kuttun kibiyoyin dake goye a bayanta kuma ta shimfida bayanta akan reshen bishiyar ta kishingida tana mai duban Zainur cikin alamun karayar zuciya tace yakai dan uwana ina ganin cewa wancan abokin naka tunanin banza yayi kawai har da yake tunanin cewa makiya zasu biyo bayanmu,banda abin sama shiga ba duba yakeyi ba kuma ba tsafi ba,akan wane dalili zuciyarsa zata raya masa cewa ana biye damu.Koda jin wannan jawabi sai Yarima Zainur ya bata rai ya dubeta cikin alamun fishi yace idan kowa a sansanin nan namu bai yarda da abokina ba ni na yarda dashi dari bisa dari tunda dai nasan cewa baiyi imani da komai ba face Allah to nima na gasgasta duk maganarsa kuma duk irin umarnin daya bani zan bishi.Kada kiyi garaje a cikin wannan al'amari ki zamo mai hakuri da zuba idanu,lallai zaki sha mamaki. Gama fadin hakan keda wuya kuwa sai suka jiyo sukuwar dawakai daga nesa a bangaren gabas,cikin hanzari kowa ya dana kwari da bakansa ya tabe,dama Yarima Yazid da sarkin yaki Haiman sun gayawa kowa cewa kada kowa yayi wani yunkuri face sun bayar da inkiya. Sannu a hankali sautin gudun dawakan ya rinka karuwa wanda har yasa kasar dajin gaba daya ta fara rawa sai kace miliyoyin kofatun dawakai ne ke sukuwa.In badon zuciya irin ta musulunci ba da tuni su Yarima Yazid sun firgita sun zubar da makamansu sun falfala da gudu domin tsira da rayukansu. Ai kuwa koda rundunar ta matso kusa hatta sarkin Yaki Haiman saida zuciyarsa ta buga da karfi bisa hango sarki Marwatu da Waziri Ridwan akan gaba cikin gagarumar shigar yaki ga dubban daruruwan miyagun dakaru a bayansu masu tsananin kwarjini da ban tsoro tamkar sa ci babu kuma dukkaninsu suna dauke da muggan MAKAMAN YAKI sai ihu suke gami da kururuwa suna karawa dawakansu kaimi tamkar zasu tashi sama. Koda ganin wannan BAKAR RUNDUNA sai Yarima Yazid ya fara yiwa Allah kirari a cikin zuciyarsa yana ambaton sunayensa tsarkaka bisa neman taimakonsa.Kamar sarkin yaki Haiman,Zainur da gimbiya Nauwara sun san abinda yarima Yazid keyi sai suma suka kama kiran sunan Allah a cikin zukatansu suna masu neman tallafinsa. Hakika duk wanda ya dogara da Allah to Allah zai iya masa duk abinda ya gagareshi,nan take su Sarkin Yaki Haiman sukaji dukkan tsoro ya kau daga cikin zukatansu sannan kuma sai sukaji wani irin gagarumin karfi ya shiga jikinsu. Saida ya rage saura baifi taku goma ba tsakanin wannan runduna da sansanin nasu yarima Yazid sai sarki Marwatu ya tuna cewa sunyi ganganci da basu tsaya ba. Sun tabbata da cewa babu wani tuggun da ake shirya musu a farko amma sai yayi tunanin cewa an shirya musu,nan take sarki Marwatu ya wangame bakinsa ya bude muryarsa da karfi yana mai bayar da umarnin a tsayar da dawakai kada a fada cikin sansanin amma ina BAKIN ALKALAMI YA BUSHE.Saboda ihun dakarun nasu da karar kofatun dawakansu dake kartar kasa ya danne sautin muryar tasa kuma ga kura ta turnuke sama da kasa kowa baya shaida kowa sosai. Wohoho. AJALI idan yayi kira dole ne a amsa,ai kuwa wadannan dubbunan daruruwan dakaru na fadawa cikin sansanin sai ruwan kibiyoyi gami da fikakkun rassan bishiyoyi suka rinka soke su har dawakansu ma suka rinka zubewa kasa MATATTU.Koda na baya sukaga yadda na gabansu ke ta zubewa kasa tamkar ana sassabe a hona sai suka firgita ainun suka kada linzamin dawakansu suka juyo da baya,amma sai suka rinka jin ruwan kibiyoyi da fikokin rassa na barar dasu kasa.Daga can kuma sai kasa ta rinka riftawa dasu suka rinka fadawa cikin ramuka,fikakkun rassa na tsire su suna mutuwa.Nanfa dakarun suka dada dimaucewa domin bala'i yakai bala'i saidai kaga jini na tsartuwa da feshi dakaru na rusa ihu da kururuwa suna zube kasa matattu ™Abbas Abdulkadir hada hada™ Sama da kasa,gabas da yamma,kudu da arewa ruwan kibiyoyi suke sha ba kakkautawa.Koda mutum ya sami nasarar fita daga cikin sansanin saidai kawai yaji kasa ta rufta dashi ya hallaka.Saida aka shafe kusan sa'a daya da rabi ana wannan ruwan kibiyoyi da fikakkun itatuwa dakarun su sarki Marwatu nata mutuwa tamkar ana karkado busasshen fure daga jikin bishiyoyi ya zamana cewa kimanun kaso daya da rabi na dakarun sun hallaka.Da kyar da sidin goshi Waziri Ridwan da sarki Marwatu suka tsira da rayukansu amma saida kowannensu ya sami mugun rauni a jikinsa,shida waziri Ridwan a damtsen hannunsa na dama kibiya ta soke shi ta hudashi ta faso bayan hannun.Saboda tsananin zafi da zugin da yaji sai ya kasa zare kibiyar,ga jini nata zuba amma a haka ya rinka rarrafe da rub da ciki ya samu ya ruga cikin daji ya buya a cikin duhuwar bishiyoyi.Shima sarki Marwatu da sauran dakarun nasa haka suka samu da kyar suka isa inda waziri Ridwan yake kowannensu dauke da mugun rauni.Shi Sarki Marwatu ma a cinyar ta hagu kibiya ta soke shi ya fadi kasa sai janyoshi akayi a kasa a wulakance aka tserar da rayuwarsa da kyar. .Sai bayan su sarki Marwatu sun iso cikin wannan duhuwar ciyayi ne suka sami nutsuwa suka kafa sansani kuma suka zagaye sansanin da dakaru don tabbatar da tsaro.A sannan ne aka shiga yiwa masu rauni magani,sarki Marwatu da Waziri Ridwan kuwa saida likita ya basu wani maganin bacci mai karfi suka bingire sannan aka iya cire musu kibiyoyin dake jikinsu aka sa musu magani.Duk su biyun babu wanda ya farfado sai bayan sa'a uku a firgice duk su biyun suka farfado suka mike zaune a cikin tantin da suke kwance. Koda suka kalli junansu kuma suka tuno da irin mummunar barnar da'akayiwa dakarunsu acan sansanin su yarima Yazid kuma suka dubi raunikan dake jikinsu sai suka kamu da tsananin bakin ciki zukatansu suka kama tafarfasa kamar zasu kone. A cikin hadin baki kowannensu ya wangame baki ya kwarara uban ihu na bakin ciki mai tsananin firgitarwa take sautin ihun nasu ya cika dajin gaba daya da amsa kuwa,daga cam sai sarki Marwatu ya dubi Waziri Ridwan cikin tsananin fishi da takaici da bakin ciki yace,yaya akayi wadannan abokan gaba sukayi mana irin wannan muguwar mamaya?Menene dalilin da yasa basirarmu ta toshe har muka afka musu cikin gaggawa haka ba tare da munyi tunani da nazari ba? Waishin menene dalilin da yasa sihirinmu na tsafi yaki tasiri akansu. Lokacin da waziri Ridwan yaji wadannan tambayoyo daga bakin sarki Marwatu saiya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubi Marwatu cikin alamun nutsuwa yace yakai abokina kayi sani cewa ahalin yanzu yarima Zainur ya hadu da wani takadirin aboki wanda ya kasance ma'abocin ADDININ MUSULUNCI waishi Yarima Yazid.Karfin sihirin tsafin Yarima Yazid ne yasa muka kasa samun nasara akansu.Idan har muna son mu mallaki wannan taswirar ta zuwa dajin Hajarul Aswad dole ne mu kashe wannan bakon jarumi kafin su riga mu zuwa can kogon na Hajarul Aswad,karfin damtse,iya yaki ko sihirin tsafi ba zasu sa mu sami nasara ba akan wannan takadirin bakon jarumi amma kowannen dan adam yana da lago kuma yana da rauni dole ne muyi amfani da rauninsu da lagonsu kafin mu sami nasara akansu. Koda jin wannan batu sai Sarki Marwatu yayi ajiyar zuciya yace ta yaya zamu gano rauninsu da lagonsu,kayi sani cewa nayi mummunan bakin ciki bisa ganin yadda su Yarima Zainur suka kashe mini dubunnan daruruwan dakaruna da kuma yadda muka sha bakar wahala a wannan YAKIN SUNKURU da sukayi mana,ni yanzu babban burina shine mu rama abinda sukayi mana naga jinin jama'arsu ya zuba da yawa akan kasa su kuma mu kamasu a raye muyi ta gana musu azaba mafi radadi a doron kasa har ta zamo sanadin ajalinsu. Ta yaya kake ganin wannan bukata zata biya? Koda jin wannan tambaya sai Waziri Ridwan ya bushe da dariya mugunta lokaci guda kuma ya murtuke fuskarsa yace ka bani kwana uku rak zanyi tunani a kan hakan. Tab kuji Mugayen azzalumai wanda zuciyarsu ta kekeshe da zalunci.Bayan defeat din da akayi musu duk sun manta da yadda suka tsira da kyar har Sarki Marwatu ana jansa da a kasa domin a tsirar da rayuwarsa. Lallai sun cika azzalumai.Bari in dakata anan: Dafatan littafin yayi so karku bani kunya. Like, comment and share necessarily WASIKAR JINI!!! Littafi Na Bakwai (7) Part B. . ZANYI TUNANI AKAN HAKAN. KODA JIN HAKA SAI MARWATU YA ZAZZARO IDANU YACE YANZU KANA NUFIN KACE BA ZAMU CIGABA DA BINSU BA HAR SAI BAYAN KWANA UKU? Ai kuwa zasu iya bamu tazarar da ba zamu iya cimmu su ba.Waziri Ridwan yayi dan guntun murmushi yace kwantar da hankalinka abokina ai ba daina binsu zamuyi ba kuma duk tazarar da zasu bamu zamu iya riskarsu a cikin kankanin lokaci. Abu mai mahimmanci shine mu karbe wannan taswirar dake hannunsu kafin su isa can kogon Na Hajarul Aswad,ina mai tabbatar maka da cewa su kansu yanzu basu san inda suka dosa ba daman basu fara amfani da taswirar ba amma tabbas tunda sunga sun sami wannan gagarumar nasara akanmu zasu iya fara amfani da ita a gobe. Ai dama taswirar zata fara aikine a karkashin wancan daji da sukayi mana wannan mummunar barna,ina mai yi maka alkawari cewa kafin su isa karshen wannan daji zamu kashe dukkanin dakarunsu su kuma zamu kama su a hannu muyi yadda muka so dasu. Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube sarki Marwatu yace na yarda da kai abokina domin nasan halinka tun muna yara babu abinda zaka sa a gabanka ya gagareka,lallai kana da mutukar sa'a da rabo. Koda jin haka sai suka bushe da dariya a tare suna masu rungume junansu. Wannan shine abinda ya faru a tsakanin sarki Marwatu da Waziri Ridwan bayan sun kaiwa su yarima Zainur harin bazato domin suyi musu kisan farat daya amma sai akayi KAIKAYI KOMA KAN MASHEKIYA. * A Can sansanin su yarima Yazid kuwa bayan kura ta lafa abokan gaba sun gudu sai kowa ya fito daga cikin maboyarsa aka kama yin kabbara saboda farin cikin nasarar da akayi a wannan yaki.Nan take yarima Zainur ya rungume yar uwarsa Gimbiya Nauwara shi kuma sarkin yaki Haiman saiya rungume yarima Yazid yana mai yi masa godiya dasa masa albarka. Haiman ya janye jikinsa daga cikin na Yazid ya kama hannunsa ya jashi izuwa kan wani dutse suka zauna a lokacin da Zainur da Nauwara suka juyo suka zuba musu ido.Koda Yazid ya hada ido da Nauwara sai yayi sauri ya sunkui da kansa kas don kada ta fuskanci cewa akwai wani abu a ransa game da ita.Tabbas yarima Yazid yaji son Nauwara a cikin zuciyarsa kawai tsananin dauriya ce da kawaici tasa ya danne zuciyarta sa kuma ya kasa furtawa ko nuna abinda ke cikin ran nasa. Sarkin yaki Haiman ya dubi Yazid a cikin nutsuwa yace yakai wannan gwarzon jarumi mai dumbin hikima da basira kayi sani cewa yau shekara ashirin da biyar kenan ina ruke da mukamin sarkin yaki,kuma na halacci yakoki a kalla guda talatin da uku amma ban taba ganin yakin da ya bani tsananin mamaki da al'ajabi irin wannan da mukayi yau ba. Ka tuna cewa gaba dayanmu bamu kai mutum dari uku ba amma sai gashi mun sami nasara akan mutane sama da dubu dari biyar.Ban tava ganin tugu da dabarar yaki ba irin wannan dakayi mana,in badon kai musulmi bane nima haka da sai nace ba mu bane mukayi yaki su Waziri Ridwan ba Aljanu ne suka yake su. Koda jin wannan batu sai yarima Yazid yayi yar guntuwar dariya sannan yace ai dama shi aikin Allah haka yake kada kayi mamakin cewa akwai sa hannun mala'ikun Allah a cikin wannan gumurzu da mukayi musamman idan kayi la'akari da tsananin yawan wadannan abokan gaba,ya kamata a ce tun a farkon fara yakin duk makaman da muka tanada sun kare amma sai gashi ana cigaba dayi musu ruwan kibiyoyi da fikokin itatuwa duk yawan nasu sai gashi ya zama na banza,ina mai tabbatar maka da cewa idan har bawa zai tsare dokokin Allah kuma ya sallama komai nasa a gareshi to inda duniyar nan kaf zata taru tofa baza'a iya cutar dashi ba,amma yayin da mutum daya jal a cikin miliyoyin musulmai ya aikata wani zunubi to fishin Allah zai iya sauka akan gaba daya al'umma,bisa wannan dalili ne nake son ka dada tara jama'ar nan taku kaja musu kunne ka shaida musu cewa su kiyaye duk irin dokokin dake cikin addinin musulunci kamar yadda a kullum nake zaiyana musu kuma mu ruke gaskiya dasu,kada su rude su sabi ubangiji. Koda yarima Yazid yazo nan sai sarkin yaki Haiman yace tabbas zan shaida musu kamar yadda ka umarceni. Ina da tambaya guda daya a wajenka yanzu menene abinyi a garemu? Zamu kwana ne anan wurin sai gobe mu cigaba da tafiya ko kuwa yanzun nan zamu cigaba da tafiyar.Lokacin da yarima Yazid yaji wannan tambaya sai yayi shiru ya sunkui da kansa kasa yana tunanin har izuwa tsawon yan dakiku,daga can kuma saiya daga kai ya dubi Haiman yace masu iya magana sunce zama waje daya tsautsayi ne inji kifi tunda a koyaushe za'a iya kawo farmaki. Duk da cewa mun kashe da yawan wadannan abokan gaba kuma mun raunana da yawansu zasu iya fusata su sake kawo mana wani harin na bazato domin daukar fansa. Kai koda ma basu kawo mana harin ba zasu iya turo yan leken asirinsu domin suga halin da muke ciki sanann su san irin harin daya dace su kawo mana. Shi yaki dan zamba ne da yaudara don haka yanzu ma dole me sake yaudararsu zamu bar sansaninmu kamar yadda yake ba zamu cire tantuna ba zamu kara yawan dakarun tsaro na mutum mutumi kuma mu kunna fitilu da daddare tamkar muna nan a cikin sansanin hakanne zai bamu damar mu sake nausawa cikin daji har mu isa karshen wannan daji da muke ciki inda taswirar Dajin Hajarul Aswad zata fara aiki. Idan Allah ya taimake mu har daren ya shude abokan gaba basu gano cewa bama cikin sansanin nan ba to tabbas zamu basu tazarar da ba zasu iya riskarmu ba har mu isa can kogon Hajarul Aswad mu dauko wasikar jini. Koda jin wannan hikima sai murna ta kama sarkin yaki Haiman nan take kuwa ya kira dakarunsa ya sasu suka sake hada mutum mutumi kimanin guda ashirin aka sake zubasu a cikin sansanin,daga nan kuma aka... *Abbas Abdulkadir Hada Hada* kunna fitilun wuta tsirarru suka kewaye sansanin saboda kada fitilun su yawa su haska mutum mutumin tun daga nesa a gane cewa ba dakaru bane na gaske,gama wannan shirin keda wuya sai su yarima Yazid suka hada nasu inasu suka bar wannan wuri suka nausa cikin daji. Saida suka shafe sa'a bakwai suna tafiya basu riske dajin ba har ya zamana cewa kowa ya kosa a sannan ne yarima Yazid ya dubi sarkin yaki Haiman yace ya kamatu mu yada zango anan saboda na fuskanci cewar jama'a sun gaji kuma gashi yamma tayi magriba zata iya riskarmu nan da cikar sa'a guda,zaifi kyau muyi sallah muci abinci in yaso mu yanke shawarar abinda ya kamata muyi walau cigaba da tafiya ko kwana anan.Koda jin wannan batu sai sarkin yaki Haiman yayi murmushi yace yakai Yazid ai duk abinda kazo dashi dashi za'ayi aiki saboda kaine jagoran wannan tafiya a yanzu.Yazid yayi murmushi yace yaza ayi kace nine jagoran wannan tafiya alhalin a cikin nahiyarku muke kun fini sanin duk inda muka dosa kuma kun fini sanin sirrikan wadannan dazuzzuka naku. Haiman ya numfasa yace gaskiya ne abinda ka fada amma ai ni ba dan kai ba yanzu tuni gaba dayanmu nan mun hallaka don dayanmu bazai tsira ba daga sharrin abokan gaba. Nan take aka shiga kafa tantuna ana shirya musu shimfidu domin a zauna a huta. A wannan lokaci ne wasu daga cikin dakarun suka sami damar cin abinci. Nanfa kowa ma ya shiga kimtsa cikinsa ita kuwa gimbiya Nauwara sai ta koma gefe daya tayi tagumi ta fada tunani mai zurfi. Ba komai take tunani ba face halin data baro mahaifinta wanda tasan cewa abune mayuwaci su sake ganin fuskokin juna,nan ta aiyana a ranta cewa tuni ma waziri Ridwan da sarki Marwatu sun riske su har cikin fada sun kashe su. Koda gama aiyana hakan sai nan take idanunta suka ciko da kwalla suka fara zubar da hawaye.A daidai wannan lokaci ne yarima Zainur yazo gareta rike da wani akushi cike da abinci,Zainur ya zauna daf da Nauwara ya dubeta yace ga abinci nan kici don na tabbatar da cewa akwai yunwa a jikinki? Koda jin haka sai Nauwara ta dago kai ta dubeshi idanunta sharkaf da hawaye tace bana sha'awar naci abinci saboda ina cikin mugun bakin ciki,nan take hankalin Zainur ya dugunzuma ainu ya dubeta cikin tsananin alamun damuwa yace haba ya yar uwata ke kuwa menene ya jefaki cikin bakin ciki haka alhalin kowa anan yana farin ciki da wannan nasara da

Chapter 12 of 15