Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wani sauti danaji yana fitowa daga cikin dakinku,ni sunana Yarima Zainur da ga waziri Ridwan,kai kuma waye? Koda jin wannan tambaya sai yarima yazid yayi murmushi yace sunana Yazid kuma na fito ne daga can nahiyar dake gabashin wannan nahiya taku,ba wani abu bane yasa nazoyin fatauci wannan gari naku ba face na sami labarin cewa kuna da arzikin ma'adanan kasa mai yawa,mu kuma abubuwan da muke karanci kenan a can nahiyar tamu. Koda jin wannan batu sai yarima zainur ya jinjina kai a lokacin da yayi masa wani irin kallo na rashin yarda sannan yace,inason mu zauna ni da kai mu tattauna wadansu maganganu masu muhimmanci a sirrance,cikin mamaki yarima yazid ya dubi yarima zainur amma sai yayi shiru bai nuna amincewarsa ko rashin amincewarsa ba akan batun su zauna su tattauna,nan take sarkin kasuwa yasa aka je aka dauko kujeru guda biyu aka kawo wa zainur da yazid aka ajiye musu a gefe daya sannan aka kori mutane kowa ya koma cikin gidansa ya kullo kofa. Ardadu kadai aka bari a tsaye a bayan yarima yazid,kafin su fara tattaunawa sai yarima zainur ya dubi Ardadu da kyau ya kare masa kallo yai nazarinsa sannan ya dubi yazid yace,duk dana lura cewa wannan mutum dake tare dakai hadiminka ne babba,ban yarda dashi ba don haka inason ya matsa can gefe daya muyi sirrinmu. Cikin mamaki Yazid ya dubi zainur sannan ya dubi Ardadu yayi masa inkiya take Ardadu ya matsa gaba can nesa da su yana mai bata rai. Yazid ya dubi zainur cikin nutsuwa yace yakai yarima kai kuwa menene dalilin dayasa kace baka yarda da wancen hadimin nawa ba? Koda jin wannan tambaya sai yarima zainur yayi murmushi yace ai wannan hadimi naka tsohon danfashi ne wanda ake kira da suna Ardadu,babu wanda yasan iyakar adadin rayukan da suka salwanta a dalilin Ardadu da kuma dinbin dukiyar da aka rasa, shi mutumin kirki a fuska ma ana ganeshi,yanzu gashi kaima da kanka ka datse masa hannunsa duk da cewar ya zama babban hadiminka. Koda zainur yazo nan a jawabinsa sai yarima yazid ya cika da tsananin mamaki ya kurawa zainur idanu yace,dakata yarima shin kana yin tsafi ne? Indai ba tsafi kakeyi ba babu yadda za'ayi kasan duk wadannan al'amura da suka faru a bayan idanunka. Dajin haka sai yarima zainur ya bushe da dariya sannan yace bana tsafi amma ina da tsananin bincike bisa abubuwan da suke faruwa a wannan nahiyar tamu ciki da wajenta,duk wani babban takadari inada labarinsa harma taswirarsa an zana an kawo mini,kaga kenan bai kamata kayi mamaki ba akan bayanin danayi maka na shugaban yan fashi Ardadu,abinda nakeso dakai yanzu shine ka fada mini gaskiyar wanene kai? Kuma menene ya kawowa wannan birni namu? Koda jin wannan batu sai yarima yazid ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan yace zan fadi koma iyakar gaskiya a kaina amma kaima kayi alkawari cewa zaka fada min gaskiya akan duk lamarinka. Yarima zainur yace na dauki alkawarin zan fada maka iyakar gaskiyar badon koma ba sai don saboda naga alamar cewa kai mutum ne mai gaskiya maza ka bayyana min gaskiyar matsayinka a birninku. Yarima Yazid ya gyara zama yace sunana Yarima Yazid da ga sarki Arsanal na birnin Haurul ba komai ne ya kawo ni kasar ku ba face neman wata Wasikar jini, ba don komai nake neman wannan wasikar ba sai domin na nemawa mahaifina da kasata kubuta daga sharrin sarkinku,akwai dukiya mai yawa ta sarki aiyuba a garinmu wacce ake juyata bisa ka'idar za'a bashi riba duk shekara wannan shekarar yanfashi sun kawo mana harin bazato sun kwashe gaba dayan dukiyar kuma bamu da yadda zamuyi mu iya biyanta bisa wannan dalili ne muka shiga bincike har muka gano cewar babu wata hanya da zamu iya kare kanmu daga barazanar sarkinku face mun rabashi da WASIKAR JINI wacce itace +Abbas Abdulkadir Hada Hada+ madogararsa akan karfin sihirinsa da karfin mulkinsa,idan har bamu rabashi da wannan wasika ta jini ba lallai zai turo dakarunsa su shafe birninmu su kuma kame jama'ar duka a matsayin bayi ko kuma ya jefemu cikin wata masifar mai tsananin. Koda Yarima Yazo nan a zancensa sai yarima zainur ya cika da tsananin mamaki amma saiya bushe da dariya,al'amarin daya baiwa yarima yazid mamaki kenan,zainur yace yakai wannan dan sarki kayi sani cewa kazo da wani babban al'amari wanda ni kaina a yanzu na kasa fahimtar abin a rayuwata sama akan wannan batu na wasikar jini,bisa binciken da nayi akan kasarku ta haurul kuna yin wani addini ne wanda ake kira musulunci kuma kunyi imani da cewa ubangijinku shine mai iko akan komai da kowa idan har kunyi imani na gaskiya akan wannan ubangiji naku me yasa ba zaku rokeshi ba akan ya shiga tsakaninku da sarkinmu tunda kun yarda cewa zai iya magance komai. Yarima Yazid yace tabbas abinda ka fada gaskiya ne amma ka sani cewa ubangijinmu mai adalci ne kuma baya zalunci bamu karbi dukiyar sarkinku ba sai bisa ka'idar cewa zamu bashi kaso daya jak cikin kaso uku na ribar da aka samu a shekara. Ga shekara ta zagayo bamu bashi ba,kaga kenan mun karya alkawari don haka muna jin kunyar mu kai karar sarkinku wajen ubangijinmu kuma tsoransa ya hanamu muke mu sanar dashi gaskiyar abinda ya faru,koma yu dace yayi mana afuwa. Sa'adda Yarima Yazid yazo nan a zancensa sai yarima zainur yai ajiyar zuciya sannan yace tabbas addininku akwai adalci a cikinsa tunda har bakwa son cutar da wani akan gaskiyarsa to amma ka sani cewa ina bukatar na sake ganin karfin addinin naku da ubangijinku domin ina ganin cewa shine kadai zai iya fitar damu gaba daya daga cikin matsalar da muke ciki,ko kuna cikin fargabar sarkinmu ni kuma ina cikin fargabar mahaifina wanda idan harya hau kan karahar mulkin kasar nan shike nan kasashen duniya ma gaba daya sun shiga uku dimin zaluncinsa zai tumbatsa ya kwarara izuwa dukkan nahiyoyin duniya. Koda jin wannan batu sai yarima yazid ya jinjina kai yace aikuwa indai hakane ashe ba karamin jihadi zanyi ba na tsaya har anan birnin naku naga na taimaka mun hana mahaifinka samun damar da yakeso ya samu,amma inaso kayi mini bayani ta yaya mahaifinka zai samu wannan babbar dama? Nan take Yarima Zainur ya kwashe labarin duk abinda ya faru tundaga ranar daga ranar daya fita farauta daji har yaje birnin Arnan daji ya sadu da sarauniya Lazwara kawo izuwa zaman da yayi da gimbiya nauwara da duk bayanin datayi masa akan WASIKAR JINI. Koda yarima zainur ya gama baiwa yarima yazid wannan labari sai yazid ya cika da tsanani mamaki ya rasa ma abinda zaice masa can sai yarima yazid ya dubi zainur yace nidai yanzu ba zan komawa birninmu face da labarin mai dadi wanda zai kwantar da hankalin mahaifina da sauran mutane kasarmu don haka yanzu inason ka bani shawara bisa abinda zai fisheni. Koda jin wannan batu sai yarima zainur yayi shiru yana tunani har izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma saiya dago kai ya dubi Yazid yace daga yau mun zama abokai na aminci nidakai don haka inason ka cigaba da sauraro har izuwa lokacin dazan tafi neman WASIKAR JINI domin mu tafi tare kuma kamar yadda na gaya maka dazu inason ka nuna mini isa da ikon ubangijinka domin na gani ko zan iya dogara dashi na sami biyan bukata ta,zaka cigaba da zama ne a cikin wannan birni namu akan matsayinka na babban bafatake daga wata nahiya da wannan furuci nakeyi maka sallama sai mun sake haduwa a karo na biyu,na barka lafiya,koda gama fadin hakan sai yarima zainur ya juya da baya ya bar cikin kasuwar,cikin hanzari Ardadu ya ruga izuwa wajen yarima yazid ya risina cikin biyayya yace ya shugabana ina fatan dai yanzu ka samo mana labarin inda wasikar jini take? Cikin alamun fushi yarima yazid yadubi Ardadu yace,waya gaya maka cewar ana samu komai a saukake sai ansha wuya sannan akan sha dadi,yazid na gama fadin hakan sai ya juya ya koma cikin wannan gida,a lokacin ne sarkin kasuwa ya ruga da gudu ya iskace cikin gidan kuma ya risina a gareshi cikin matukar biyayya kamar zai yi masa sujjada yace ya shugabana kayi hakuri bisa katse maka barcinka da yarima yazo yayi kuma lallai gobe da sassafe zansa magina su gyara wannan matattakalar benen data rushe. Koda jin wannan batu sai yarima yazid yayi murmushi a lokacin da Ardadu ya karaso bayansa ya dubi sarkin kasuwa yace ai dama ba barci nakeyi ba sa'adda yarima ya shigo cikin gidannan kuma yakin da mukayi bisa rashin sani ne amma ai yanzu mun fahimci junanmu,yana gama fadin hakan sai ya taka rusasshiyar matattakalar benen ya haye sama kuma ya shige cikin dakin barcin nasa Ardadu na biye dashi. Da shigarsu cikin dakin sai yazid da Ardadu suka kwanta domin suyi barci amma sai Yarima Yazid yaji idanunsa sun kekashe ba komai ne ya janyo hakan ba face mamaki bisa ganin yadda ya fafata kazamin yaki da yarima zainur ya kasa samun nasara akansa alhalin ba sa'ansa bane a shekaru ya bashi kusan tazarar shekara biyar zuwa shida,abinda ya kara bashi mamaki mashine labarin gimbiya Lazwara dayaji sarauniyar arnan daji wacce ma tafi yarima zainur karfi da iya yaki.To waishin ma yaya akayi ta sami irin wannan gagarumin karfi da kuma gagarumin horon.Nan take Yazid ya aiyana a ransa yace duk ranar da yarima zainur ya sami damar zuwa daukar horon yaki a wajen gimbiya Lazwara lallai tare zasuje domin yaga irin jarumtakarta kuma yasa ido domin shima ya koyi irin yanayin yakin nata. Haka dai Yarima Yazid yacigaba da tunanin gami da sake sake cikin zuciyarsa har barci ya saceshi bai sani ba. Al'amarin sarkin yaki Haiman kuwa lokacin +Abbas Abdulkadir hada hada+ daya isa gidan sarki sai aka shigar dashi har cikin kuryar turakar sarki yana shiga ya iske sarki aiyuba tare da gimbiya nauwara a zaune a cikin wani irin yanayi mara kyau domin duk su biyun idanunsu sunyi jawur alamar cewa sun hade suna kuka.Koda ganin hakan sai hankalin haiman ya dugunzuma ainun domin abinda yake tsoron faruwa ga dukkan alamu shine yake shirin faruwar. Haiman ya durkusa kasa bisa guiwarsa guda yana mai sunkui da kansa kas ya kwashi gaisuwa. Sarki Aiyuba ya masa gaisuwar sannan ya umarceshi daya zauna akan daya daga cikin kujerun na alfarma.Cikin sanyin jiki haiman ya mike tsaye yaje kan kujerar ya zauna sannan ya gaida gimbiya Nauwara ta amsa ba tare data dubeshi ba a lokacin da wani siririn hawaye guda daya ya gangaro akan kumatunta. Sarki aiyuba ya fuskanci sarkin yaki haiman cikin nutsuwa sannan yace yakai haiman inaso ka sani cewa a duk fadin kasata kaine mutum na uku wanda na yarda dashi nayi imani cewar bazaku taba cutar dani ba,mutum na farko shine 'yata wato gimbiya nauwara,mutum na biyu shine danka yarima zainur sai kuma kai na uku kaga kenan na aminta da danka ainun fite dakai kanka saboda wata babbar hujja wacce bazan iya gaya maka ita ba yanzu,amma ita ba yanzu amma indai kana raye nan gaba zakaga hujjar da idanunka. Ba wani abu bane yasa na kirawo ka nan ba yanzu har cikin turakata face domin na sanar dakai cewa kwanakina a duniya sun kusanto karshe don haka ba lallai bane nan gaba na haura sama da kwanaki sittin ba araye. Koda jin wannan batu sai idanun sarki yaki haiman suka zazzaro kuma hankalinsa ya dugunzuma ainun cikin alamun tsananin firgici ya dubi sarki aiyuba a lokacin da zuciyarsa ke dukan uku uku yace haba ya shugabana yaya gaka a raye kuma cikin koshin lafiya zaune daram a gabana amma kana cewa bazaka haura kwana sittin ba nan gaba shin wani ciwo ne ya kamaka ko kuwa kashe kanka zakayi.? Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa sarki aiyuba yayi shiru kamar bazaice komai ba yana mai sunkuyar da kansa kasa daga can kuma sai ya dago kansa ya dubi haiman yace babban likitane na gidan sarautar nan yaci amanata ya zuba mini guba a cikin maganin daya saba bani,inasha yanzu haka guba taci karfin jikina kuma nayi bincike a cikin hallar tsafina na gano cewa a cikin kwanakin da basu wuce sittin ba wannan ciwo zai zamo sanadin ajalina. Koda sarki aiyuba yazo nan a zancensa sai haiman ya sake cika da tsananin mamaki bakinsa na rawa ya dubi sarki aiyuba yace ya shugabana ta yaya babban likita ya aikata wannan babban laifi yayi babbar cin amana alhalin shine likitan kakanka da kuma mahaifinka ne? Koda jin wannan tambaya sai sarki aiyuba ya fashe da kuka yace ni kaina nayi matukar mamaki bisa yadda akayi babban likita yaci amanata amma danayi bincike saina gano cewa ba laifin sa bane dan uwana waziri ridwan ne ya kama iyalansa a sirrance ya boyesu a inda babu wani daya sani yace dashi koya zuba mini guba a cikin maganina ko kuma ya kashe gaba dayan iyalin nasa saboda su gomasha daya wanda suka hada da matansa biyu da kuma 'ya'yansa, nasa an nemo iyalan babban likita an mayar dasu amma shi babban likitan nasa an kaishi Sijiil Mausara an kulleshi tunda yafi son rayuwar iyalansa akan tawa. Koda jin wannan batu sai hawayen tausayi ya zubowa sarkin haiman yace ya shugabana ai gwara a kashe babban likita dadai kasa akaishi cikin wannan mugun kurkuku wanda in aka shigeshi ba'a fitowa face an zama gawa,to shi kuma waziri wane hukunci ka yanke masa bisa wannan babban laifi daya aikata na kokarin hallaka? Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya sake zubowa sarki aiyuba a karo na biyu yace kanason na kashe dan uwana guda daya tilo daya rage mini a duniya ne? Wanna shine abin kunya kuma abin gori na karshe wanda zan barwa tarihin gidanmu bazan yiwa waziri hukuncin komai ba amma inaso a bayan mutuwa ta na dasa masa bakin cikin dazai zamo sanadin ajalinsa kuma ya rasa komai da kowa,bazan taba samu wannan nasara ba face da taimakonka. Cikin alamun kaduwa sarkin yaki haiman ya dubi sarki aiyuba yace ta yaya zan iya taimakonka a cikin wannan al'amari? Sarki aiyuba ya mike tsaye daga kan kujerar da yake zaune ya kama hannun gimbiya nauwara yaja ya kawota gaba haiman ya dubeshi yace idan harka tsare lafiyar gimbiya da ranta a lokacin da ciwo ya kwantar dani,lallai zan cika burina akan abokan gabata yakai masoyina,nan da kamar sati biyu ciwon dake cikina zai tashi ainun harya kaini ga kwanciya asannan nakeson na tura yarima zainur izuwa can inda wasikar jini take. A wannan lokaci ne dan uwana ma waziri ridwan zai bazama neman wannan wasikar kuma a sannan ne zaiyi kokarin sawa a kashe yata nauwara,inason ka zamo mai tsaron lafiyar yata na musamman tun daga lokacin da yarima zainur ya tafi neman wasikar jini har izuwa lokacin da zai dawo cikin wannan birnin namu,wannan shine alkawarin da nakeso ka daukar mini kuma shine kadai abinda zaka iya sakamini dashi bisa duk irin abubuwan alherin danayi maka a tsawon zamana da kai. Cikin matukar mamaki sarkin yaki haiman ya dubi sarki aiyuba yace ta yaya zan fika iya tsaron lafiyar yarka alhalin duk fadin duniyar nan babu wanda ya fika karfin sihirin tsafi? Koda jin wannan tambaya sai sarki aiyuba ya sake zubar da hawaye a karo na uku sannan yace ai sirrin wannan sihirin tsafi na wasikar jini shine duk ranar da maishi ya kwanta jinya to ya daina iya cigaba da sarrafa sihirin kenan face ta warke sumul. A yanzu zan baka taswirar hanyar da za'abi aje inda aka adana WASIKAR JINI daga na birnin zuwa inda wasikar jini take tafiya ce ta kwana goma sha bakwai,izuwa wani kogon dutse boyayye... . WASIKAR JINI!!! Littafi Na Uku (3) Part C . Izuwa wani kogon dutse boyayya daka cikin wadansu manyan tsaunika dake cikin dajin Hajarul Aswad,fiye da shekara dari uku baya babu wani mahaluki daya sake shiga cikin wannan kogon dutse face ni don haka wanda duk ya sake ya samun nasarar shiga cikinsa a raye cikin koshin lafiya har kuma ya gano a inda wannan kogo yake mai lakani da Gulsul Bamhari ya shiga cikinsa lallai aishine zaiga wasikar jini ya karantata kuma shi zai hau karagar mulkina, yakai haiman kayi sani cewa tsananin karfin damtse kona sihirin tsafi bazaisa mutum ya sami nasarar keta cikin dajin hajarul aswad lafiya ba face tsananin sa'arsa da kuma kyan zuciyarsa amma akwai inda karfin damtse da iya yakin zai iya taimakon mutum,bisa wannan dalili ne nakeson ka jadddadawa yarima zainur lallai yaje ya nemi sarauniya lazwara mai mulkin birnin arnan daji ta kara masa ilmin yaki kafin ya tafi izuwa dajin hajarul aswad.Koda gama fadin haka sai sarki aiyuba yaje ya bude wata kara,ar akwatin zinare da karfin sihirinsa na tsafi,itadai wannan akwati a shafe take bata da murfi ko mukulli kuma babu wata huda ko kofa a jikinta amma sai gashi sarki aiyuba ya budeta tamkar an tsaga tsakiyar kabewa. Nan take ya zabura ya zura hannunsa cikin akwatin ya dauko wata tsohuwar fatar dabba jimammiya,koda ya warware fatar saiga taswirar hanyoyin da za'abi aje dajin hajrul aswad a jikinta.Nan take sarki aiyuba ya mikawa sarkin yaki haiman wannan fatar sannan yace yakai amintaccen sarkin yaki na ka tabbatar da cewa ka dankawa yarima zainur wannan fata a sirrance ba tare da wani ya gani ba,amma kada ka bashi sai a ranar dana kwanta jinyar wannan cuta,kada ka kuskura ka bari wani yaga wannan fata a hannunka kafin ka dankawa zainur koda kuwa matarka ce ka kasance tare da wannan fata a jikinka dare da rana har izuwa lokacin da zaka dankawa zainur ita. Koda sarki aiyuba yazo daidai nan a zancensa sai sarkin yaki haiman yayi sauri ya soka wannan fata a cikin can kasan aljihun wandonsa sannan ya dubi sarkin cikin alamun mamaki yace ya shugabana naji kace akwai inda karfin damtse da iya yaki zaiyi amfani a cikin dajin aswad kuma a sanina da kai sam baka da wani karfin damtse kuma baka taba rike takobi ba bare ma ace ka iya yaki to yaya akayi ka kare kanka a cikin daji hajrul aswad a lokacin da kaje wurin da karfi da iya yaki yake da amfani,? koda jin wannan tambaya sai sarki aiyuba yayi murmushi na karfin hali kuma nan take hawaye ya zubo masa yace mahafinka shine yayi mini rakiya izuwa dajin hajrul aswad kuma shine ya ceci rayuwata a wannan wuri a sannan banfi shekara goma sha ba a duniya kuma yana kuma yana kan matsayin sarkin yakin ubana.Tun ina da shekara shida a duniya mahaifinka ya daukarwa mahaifina alkawarin kare lafiyata da rayuwata bisa wannan dalili ne ya sallama rayuwarsa don kare tawa.Shin baka taba jin tarihin yadda mahaifinka ya rasa rayuwarsa bane? Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa sarkin yaki haiman yace tabbas uwata ta gaya mini cewa mahaifina ya mutu a cikin gagarumar jarumtaka a tsakiyar maridai yana fafata kazamin yaki amma bata taba gaya mini a inda ya mutu ba da kuma sanadin daya kaishi wurin. Koda jin wannan batu sai sarki aiyuba da gimbiya nauwara suka kamu da tsananin tausayin sarkin yaki haiman suka kama zubar masa da hawaye. Sarki aiyuba ya rungume haiman a kirjinsa yace tabbas nine na baiwa mahaifiyarka labarin duk abinda ya faru garemu nida mahaifinka cikin dajin hajrul aswad sakamakon halaccin da mahaifinka yayi mini na sallama wata dukiya mai tarin yawa a gareshi wacce ni kaina bansan iyakar adadinta ba. Mahaifiyarka ce kadai tasan a inda wannan dukiya take kuma itace kadai zata iya dibarta sai kuma kai nan gaba idan har ta dankata a hannunka. Koda jin wannan batu sai sarkin yaki haiman ya cika da tsananin mamaki saboda koda wasa mahaifiyarsa bata tabayi masa batun wannan dukiya ba kuma gashi tsufa ya kamata ainun harma ta makance saboda tsufan kuma ko tafiya bata iyayi sosai face da taimakon dogara sanda.Kai magana ma da kyar takeyi.To waishin mahaifiyar tawa mugunta tayi mini kenan ta boye mini wannan sirri ko kuwa ta kwashe dukiyar ne ta karar da ita ban sani ba? Amsar da haiman ya kasa baiwa kansa kenan,kamar sarki aiyuba yasan abinda yake aiyanawa a cikin ransa sai kawai ya dafa kafadarsa yace dubeshi yace ko yau mahaifiyarka ta fadi ta mutu sai ka gaji wannan dukiya wacce na baiwa mahaifinka saboda sirrin dukiyar nan na jikin wannan sanda wacce mahaifiyarka ke dogarawa yayin mikewa tsaye ko yin tafiya kuma kasancewa kai da bakinka ka gaya mata cewa ko a bayan ranta babu abinda kakeso a tare da ita dare da rana face wanna sanda ta hannunta saboda kayi imani cewa sandarce kadai zata iya debe maka kewarta. Koda sarkin aiyuba yazo nan a zancensa sai sarki yaki haiman ya kamu da tsananin mamaki gami da tsananin farin ciki domin ko a mafarki bai taba zaton cewa iyayensa sun mallaki wani abu ba mai daraja a rayuwarsa,shi zatonsa kawai sun rayu ne cikin bautar gidan sarautar kawai shima kuma gashi zai mutu a cikinta a banza. Sarki aiyuba ya dubi haiman yace yakai sarkin yaki ka sani cewa muna da makiya da yawa a wannan nahiya kuma gashi bazan nisan kwana ba saboda haka kai da yarima zainur ne kadai zaku iya kare kasar nan daga kowace irin masifa idan har ridwan ne ya zamo sarki to kai da zainur ku kare gimbiya nauwara da talakawa ta hakane kadai zaku iya tabbatar da adalci a nahiyar nan,kuma sarki ridwan babu yadda za'ayi ya iya cutar daku,kada ka taba tunanin cewa zaka raka yarima izuwa dajin hajrul aswad kaidai kawai ka ™Abbas Abdulkadir hada hada ™ zauna tare da mahaifiyarka dare da rana har izuwa lokacin dasu yarima zasu dawo daga neman WASIKAR JINI. Lokacin da sarki aiyuba yazo nan a zancensa sai sarkin yaki haiman ya rude kuma ya rikice yace ya shugabana ka gaya mini cewa duk wanda ya karanta wasikar jini ya sami sirrikan tsafi irin naku kuma ya zamana gagarabadau a wannan duniya ma gaba daya to amma gashi kana cewa koda Ridwan ya zama sarki babu yadda zaiyi damu nida yarima ta yaya hakan zata kasance? Koda jin wannan tambaya sai sarki aiyuba yayi murmushi yace akwai wani babban sirri na biyu wanda zan sanar dakai shi yanzu,wannan sanda wacce ke hannun mahaifiyarka tana da irin sirrin da wasikar jini kedashi amma babu wanda zai iya sarrafata har ya iya amfani da sihirinta face wanda ya kasance jinin wannan gidan sarauta,kaga kenan babu wanda zai amfani wannnan sanda face yarima zainur wanda ya kasance tamkar dan cikinka tunda kai da matarka ne kuka raine shi kum a hannunku ya girma,sannan akwai kauna da shakuwa mai yawa a tsakaninku,tunda dai baku da wani da a duniya face shin don kun mallaka masa wannan sanda ina ganin cewa babu wata matsala.Koda sarkin yaji wannan batu sai ya dan gyara murya gami dayin tari yace nidai babban burina shine a bayan mutuwa gimbiya nauwara ta cigaba da rike matsayinta na galadima a majalisar kasar nan domin ta hakane kadai zata zama tamkar itace ke mulkin kasar,shi kuwa dan uwana Ridwan zai zamo tamakr gunki koda kuwa shine akan karagar mulki,yanzu zan sanar dakai wani babban sirri na biyu wanda ko ita kanta gimbiya bata sani ba kuma bana son ta sami saidai bayan raina. SHIN SARKI YAKI HAIMAN ZAI IYA RIKE AMANAR GIMBIYA NAUWARA? WANE SIRRI NE SARKI ZAI SANAR DA SARKIN YAKI HAIMAN WANDA HAR BAYASO GIMBIYA NAUWARA TA SANI? SHIN TSAKANIN YARIMA ZAINUR DA MAHAIFINSA WAYE ZAI SAMU NASARAR DAUKAR WASIKAR JINI? WACE IRIN BAKAR WAHALA ZASU SHA KAFIN ISAR SU DAJIN HAJARUL ASWAD? WANE IRIN TAIMAKO YARIMA YAZID ZAI BAIWA YARIMA ZAINUR? SHIN ZASU KASANCE CIKIN ABOTA NE KO KUWA? YAUSHE NE SARKI AIYUBA ZAI MUTU KUMA MAI ZAI FARU BAYAN MUTUWARSA? Mu hadu a littafi na hudu(4) domin jin cigaban WASIKAR JINI!!! Littafi Na Hudu (4) Part A . KODA Nauwara taji wannan batu saita fashe da kuka ta dubi sarki Aiyuba tace yanzu dama akwai wani sirri wanda zaka iya boye minishi? Sa'adda sarki Aiyuba yaji wannan batu sai hawaye ya zubo masa sannan ya kamo Nauwara ya rungumeta a kirjinsa yace ya yata sanin wannan sirri a gareki yanzu bashi da wani amfani domin bazai haifar da komai ba a gareki face damuwa da tunanin mara tukewa.Sarki Aiyuba na gama fadin hakan saiya janye jikinsa daga cikin na gimbiya nauwara ya tafi izuwa ga sarkin yaki haiman yayi masa rada a kunne sannan ya sallama shi ya fice daga cikin turakar yana mai waigen sarki yana zubar da hawaye saboda gani yake kamar ba zasu sake ganin juna ba,fitarsa keda wuya sai sarki aiyuba ya kama hannun gimbiya nauwara ya jata suka tafi izuwa kan doguwar kujera suka zauna sannan ya dubeta idanunsa cike da kwallah yace ya yata kiyi sani cewa yanzu zaman farin ciki a tsakanina dake na iya tsawin sati biyu ne kacal don haka abinda kike son ki gaya mini ki fadeshi a cikin wadannan kwanaki domin da zarar sati biyu sun cika ko magana bazan iya ba,duk da cewa ina iya kallonki dajin duk abinda zaki fada. Koda jin wannan batu sai gimbiya nauwara ta fada kan kirjin sarki aiyuba ta fashe da matsanancin kuka na bakin ciki shi kuma saiya shiga rarrashinta yana mai bata baki. . Lokacin da yarima Zainur ya baro kasuwa ya dawo gida asuba ta kusayi,a wannan lokaci ya gaji ainun kuma ga tsananin barci a cikin idanunsa,kai tsaye ya shige cikin gidan sarki yaki haiman da nufin ya wuce izuwa dakinsa ya kwanta.Yana shiga cikin harabar gidan sai zuciyarsa ta buga da karfi yaja ya tsaya cak a waje daya cikin tsananin mamaki,ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin mahaifinsa na jini tsaye a gabansa fuskarsa cike da annuri wato waziri Ridwan. Cikin hanzari waziri ridwan ya taho ga yarima zainur ya rungumeshi yana mai nuna tsananin farin cikinsa bisa ganinsa amma sai yarima zainur ya janye jikinsa daga cikin nasa da sauri ya dubeshi cikin kaduwa da matukar mamaki yace yakai abbana meya kawo ka nan gidan a irin wannan lokaci? Koda jin wannan tambaya sai waziri ridwan yayi murmushi yace yanzu don uba yazo ganin dansa sai ya zamo abin tuhuma? Yana gama fadin hakan sai idanunsa suka ciko da kwallah ya dubi zainur cikin nutsuwa yace kai dana kayi sani cewa nayi matukar nadama bisa yadda nayi watsi dakai tun tuni ban jakaa jikina ba har na bari wasu suka rabeka tamkar sun haifeka. Koda waziri ridwan yazo nan a zancensa saiya durkusa kasa bisa guiwoyinsa a lokacin da hawaye ya zubo masa ya kama hannun zainur ya rike yace kayi mini aikin gafara yakai dana,kayi sani cewa dani da mahaifiyarka duk munyi nadamar nisantarka damu kayi don haka yanzu nazo ne na daukeka mu tafi gida daga yau zaka ga gata da kulawa irin wanda babu wani da daya samesu a garin nan gaba daya face gimbiya nauwara. Koda waziri ridwan yazo nan a zancensa sai yarima zainur ya kyalkyale da dariya,al'amarin dayai matukar razana waziri ridwan kenan ya cika da mamaki. Lokaci guda zainur ya fincike hannayensa daga cikin na ridwan yaja da baya yana mai murtuke fuska ya dubi ridwan din a fusace yace meyasa kai da mahaifiyar tawa baku nuna mini so da kulawa ba a tsawon shekaru goma sha shida da suka gabata ba,lallai banza bata kai zomo kasuwa duk yadda akayi akwai wata bukata da kuke da ita a wajena shi yasa yanzu kazo kana nema na. Nan take hawaye ya zubowa Yarima Zainur yace tun daga kuruciyata kawo iyanzu ban san wani abu waishi soyayya ta iyayen da suka haifi da ba abinda zan iya fada kawai shine mahaifiyata ta shayar dani,kai kuma ka ciyar dani ka tufatar dani izuwa tsawon shekara shida amma daga sannan sarkin yaki da matarsa ne suka cigaba da rukeni a matsayin dansu kawo i yanzu,ya zakuyi da irin shakuwar dake tsanani na dasu? Tayaya kuke zaton cewa zaku iyarabani dasu dare daya? Koda Yarima zainur yazo nan a zancensa sai waziri ridwan ya fashe da kuka yace yakai dana kayi sani cewa babu yadda za'ayi hannun mutum

Chapter 6 of 15