Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
muka samu wacce bamu taba zato ba? Koda jin wannan tambaya sai Nauwara ta girgiza kai tace hakika nayi matukar farin ciki bisa wannan gagarumar nasara da muka samu amma duk sa'adda na tuno yadda karshen rayuwar mahaifina zata kasance sai bakin ciki ya turnuke ni na tsani wannan akida daya dauka ta iyayensa da kakaninsa.A kan wane dalili bazai karya alkawarin daya daukar musu ba ya karbi addinin musulunci yayi watsi da tsohon addininsu na bautar gumaka da tsafi,yanzu gashi ma lokaci ya kure babu mamaki tuni masu sarki Marwatu sun shiga garin sun ci shi da yaki,nasan cewa bazasu barshi a raye ba.Koda Gimbiya Nauwara tazo nan a zancenta saita fashe da kuka,al'amarin daya jefa yarima Zainur da kowa kenan cikin matukar tausayinta,zainur ya rungumeta a kirjinsa ya shiga rarrashinta yana mai bata baki har izuwa tsawon yan dakiku.Koda yaga taki ta daina kukan saiya janye jikinsa daga cikin nata ya mike tsaye ya tafi wajen yarima Yazid ya jashi izuwa gefe daya sannan ya dubeshi cikin alamun tsananin damuwa yace kai kadaine zaka iya kwantarwa da yar uwata hankalinta ta daina wannan kuka. Koda jin haka sai idanun yarima Yazid suka zazzaro ya dubi zainur cikin alamun firgici da mamaki yace yaya kai da kake dan uwanta na jini baka kwantar mata da hankali ba sai ni. Zainur yayi murmushi yace akwai dalilin da yasa na fadi hakan amma bazan gaya maka dalili ba a yanzu sai nan gaba,inaso ka sani cewa a duniya babu abinda Nauwara keso sama da farauta a cikin daji,inason a yanzu take ka gaiyaceta ku tafi farauta ku biyu rak izuwa cikin daji nasan zata ci duk abinda kuka farauto in ba haka ba kuwa saidai ta kwana da yunwa tana kukanta. Yayin da Yarima Yazid yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma yace shin baka san cewa a addinin musulunci haramun ne namiji ya kadaita da macen da bata kasance muharramarsa ba? Zainur yace nasan da haka amma ai addinin ya yarda da wata lalurar don kawar da wacce ta fita,bare ma na yarda da imaninka da kuma tsoron Allah,nasan ba zaka taba yin abinda bai dace ba ga yar uwata.Kada ka manta cewa shi kansa mahaifin namu cewa yayi ya danka amanar Nauwara a hannunka,ka biya mini wannan bukata dana nema a gareka domin ka ceto lafiyar Nauwara in ba so kake gobe da safe ta tashi da matsananciyar rashin lafiya ba. Koda jin wannan batu sai jikin Yarima Yazid yayi sanyi ya rasa abinda zaiyi kawai sai ya mike tsaye ya shiga cikin tantinsa ya dauko KWARI DA BAKAnsa gami da takobinsa kuma ya gyara damarsa.Koda ya fito daga cikin tantin sai yaga yarima Zainur tsaye a gabansa yana jiransa,kawai sai Zainur ya sanya hannu a cikin aljihun wandonsa ya dauko wannan taswirar ta zuwa kogon Hajarul Aswad ya mika masa yace idan baka tare dani sanaji kamar bazan iya kula da wannan taswira ba,ka ajiyeta a hannunka zanfi samun nutsuwa da kwanciyar hankali koda wani abu zai same mu anan inason kayi iya kokarinka ka isa kogon Hajarul Aswad ka dauko wannan wasikar jini ka koneta wannan ne kadai abinda zakayi ka jadda addinin ALLAH a nahiyar nan gaba dayan. Koda jin wannan batu sai Yazid ya dafa kafadar Zainur yayi murmushi yace yakai Abokina inason ka sani cewa duk abinda zan iyayi kaima zaka iya tunda munyi imani ne da abu guda.Duk wata gagarumar jarumtaka da zakaga nayi.... WASIKAR JINI!!! Littafi Na Bakwai (7) Part C. . DUK WATA GAGARUMAR JARUMTAKA DA ZAKA GA NAYI DA TAIMAKON ALLAH NAKE YINTA BAWAI TSAGWARON KARFIN DAMTSE NA BANE KO IYA YAKINA. Zainur ya maida masa da martanin murmushin yace nasan da haka amma na so ka sani cewa ko yan yatsun hannunka ka kalla akwai bambanci wani yafi wani girma to haka ma matsayi yake gami da baiwa. Kada ka manta cewa a baya na fafata yaki dakai,naga irin baiwar da Allah yayi maka ta jarumtaka da juriya da iya yaki,tabbas na gamsu da cewa ni ba sa'anka bane a wannan fanni haka kuma kana da ilmi mai yawa a addinin musulunci wanda ko rabinsa bani dashi don haka kafi ni sanin addu'oin daya kamata kayi a duk lokacin daka fuskanci wata hadari ko wata matsala,maza kaje ka sami yar uwata kuje kuyi wannan farauta ku dawo kafin magriba. Koda jin haka sai Yazid yayi murmushi ya karbi wannan taswirar yasa a cikin aljihunsa sannan ya nufi inda Nauwara ke zaune wacce kanta ke sunkuye hawaye na diga kan kyakkyawan kumatunta,kawai sai taji an kira sunanta da muryar da tasa zuciyarta ta buga da karfi. Cikin kaduwa da hanzari Nauwara ta dago kai taga yarima Yazid tsaye daf da ita amma fuskarsa na kallon gefe. Yazid ya bude baki yace shiga cikin tantinki ki dauko kayan farautarki domin ki rakani cikin daji. Koda jin wannan batu sai Nauwara taji wani irin gagarumin farin ciki ya baibayeta.Batare da bata wani lokaci ba Nauwara ta mike tsaye da sauri tana mai goge hawayenta ta fada cikin tantinta tamkar ma bata taba yin bakin ciki ba a rayuwarta. Cikin kankanin lokaci Nauwara ta gama shiri tsaf ta fito daga cikin tantin suka rankaya izuwa cikin daji Yazid nakan gaba tana biye dashi,sarkin yaki Haiman dasu yarima Zainur suka bisu da kallo kawai fuskokinsu cike da annuri,su kuwa ragowar dakaru mamaki ne ya kama su bisa ganin yadda yarima Zainur ya amincewa Yarima Yazid ya tafi da yar uwarsa izuwa cikin wannan mugun daji su biyu rak. Bayan kulewar Yazid da Nauwara ne sarkin yaki Haiman ya dubi Zainur cikin murmushi yace yakai dana hakika yau ne na dada tabbatar da cewa kana da basira gami da hangen nesa waishin yaya akayi ka gane cewa akwai soyayya tsakanin Yazid da yar uwarka Nauwara kuma menene dalilin da yasa kake son ka kulla shakuwa a tsakaninsu? Sa'adda Zainur yaji wadannan tambayoyi sai yayi murmushi gami da ajiyar zuciya a lokacin da mahaifiyarsa tazo garesu ta tsaya ta dubi Haiman tace ga abincinku can a cikin tanti na gama shirya muku ko kuwa sai kun gama tattaunawa a kan waccan MAKAUNIYAR SOYAYYA sannan zaku zo kuci abincin? Koda jin haka sai duk su biyun suka dubeta cikin matukar mamaki Haiman yace menene dalilin da yasa kika kira soyayyar tasu da matsayin makauniya? Dajin haka sai tayi murmushi tace ai duk soyayyar da ake yinta a cikin zuci a ka kasa baiyanata a fili makauniya ce kuma tana da hadarin gaske domin zata iya haifar da komai,na lura da Nauwara da Yazid tun a farkon wannan tafiya tamu ko wannnan su na satar kallon dan uwansa amma basa yarda su hada idanu don haka dayansu ya gane halin da kowanne ke ciki. A halin yanzu ba karamar dabara Zainur yayi ba daya hada su tafiya tare da samun kadaita. Idan gumu yayi gumu dole ne su baiyana gaskiya a fili koda kuwa bada furtawa bane saidai a aikace,wannan kadaitaka tasu zata haddasa saboda shakuwa kuma Nauwara zata karu da ilmin addini dana rayuwa koda kuwa rabin sa'a kacal zasuyi tare. Bani ba kuma ba kuba gaba dayan jama'ar dake cikin wannan sansani basu da wata shakka akan hada su da akayi waje guda domin an tabbatar da cewa Yazid bazai cutar da Nauwara ba kuma bazai bari wani abu ya cutar da ita ba,ina fatan wannan bayani danayi muku ya gamsar da ku ba sai kunci gaba da tattaunawa ba akan al'amarin nasu ba,sai ku taso muje cikin tantin kuci abinci. Tana gama fadin hakan saita juya da sauri ta nufi tantin cikin murna da mamaki Haiman da Zainur suke mike tsaye suna dariya suka bita a baya izuwa tantin. * Al'amarin Yarima Yazid da Gimbiya Nauwara kuwa tunda suka nausa cikin daji yana gaba tana biye dashi a baya suka kama farauta suna dube dube da hange hange ko zasu ga wata dabba ko wani tsuntsu su kai masa hari amma shiru kamar shirwa taci shirwa.Saida suka shafe kusan rabin sa'a a cikin wannan yanayi ba tare da dayansu ya ce uffan ba kuma sai taga dada kutsawa yake yi da ita cikin dajin ba tare da sanin inda ya dosa ba,gashi dajin yana da matukar kwarjini da ban tsoro,adaidai wannan lokaci ne Nauwara taji ta fara gajiya kuma kishirwa ta kamata. Nauwara ta shafa kugubnta taji babu battar ta ruwa ashe ta mantata a can cikin tantinta,ta dubi jikin Yazid wanda ke gaba taga shima babu battar ruwan a jikinsa.Nan take hankalinta ya dugunzuma bata san sa'adda ta ruga da gudu tasha gaban Yazid tana haki tace kai nifa na gaji kuma kishirwa ta kamani sosai yanzu a ina zan samu ruwan sha? Koda jin wannan tambaya sai Yazid yayi guntun murmushi a gareta a cikin zuciyarsa yana mai cewa ashe dai dole kanwar naki ce,na zata zaki cigaba da dauriya ne da nuna halin ko in kula din. Kamar Nauwara tasan zancen zucin da yakeyi saita dubeshi a fusace tace yaya ina tambayarka inda zan sami ruwan sha amma ka dubeni kana murmushi sai kace gonar auduga? Koda jin haka sai shima Yazid ya dubeta a fusace yace yaya zaki tambayi kaza hanyar rafi ai saidai ki tambayai agwagwa kisha labari ko kuwa kin manta ne cewa ni bako ne a wannan nahiyar,kefa yar gari ce a cikin dajin yakin kasarku,kece ya kamata ki fini sanin inda za'a je a sami ruwa a cikin wannan daji. Koda jin wannan batu sai Nauwara ta kyalkyale da dariya sannan tace ai zanice ta tarar da mu,muje domin kuwa *Abbas Abdulkadir Hada Hada* wannan ne karo na farko dana taba shigowa cikin wannan daji.Kai bama ni ba jama'a da yawa hatta manyan mafarauta,jaruman da suka yarda da kansu gami da shahararrun matsafa tsoron wannan daji sukeyi ba don komai ba sai kawai saboda ya makwabci dajin da kogon Hajarul Aswad yake,fiye da shekaru arba'in baya mafarauta da fatake ma basa yarda su iso farkon wannan daji ma bare su iso nan ma inda muke.Yazid ya gyada kai yace to ai shike nan saiki daure mu cigaba da lalube har sai mun gano inda ruwan yake.Yazid na gama fadin hakan sai ya cigaba da tafiya abinsa cikin matukar karfin hali Nauwara ta bishi a baya. Saida suka shafe rabin sa'a suna tafiya basu ga wata korama ba ko fadama,tun Nauwara nayin tafiyat da kuzarinta har saida ta fara sassarfa sannu a hankali ta kama yin tangadi kamar wacce tasha giya ta bugu a lokacin da labbanta suka bushe sukayi fari fat saboda tsabar kishirwa,shi kansa yarima Yazid din ba karamar juriya yayi ba daya cigaba da tafiya a hakan amma shima ji yayi kamrar ya zauna ya huta domin yaki yake ta faman yi tamkar ya dade yana gudu,duk bayan yan dakiku saiya juyo bayansa ya dubi Nauwara da zarar yaga halin da take ciki sai yaji ya kamu da matukar tausayinta. Suna cikin wannan hali ne yaji wuf karar faduwar wani abu a bayansa,cikin firgici da dimauta ya waigo bayan nasa da sauri ai kuwa sai yaga ashe Nauwara ce ta kife kasa da rub da ciki. A guje ya karaso gareta bai san sa'adda ya kama kafadunta ba ya juya da fuskarta kawai sai ganin idanunta a wurkile alamar cewa suma tayi,cikin bakin zafin nama da azababben gudu izuwa cikin dajin cikin dimautacewa wani lokacin idan yayi gabas baiga ruwa ba sai ya juya yayi yamma sannan ya dawo kudu da arewa da dai yaga babu ruwa a kusa kuma babu alamunsa sai yapara kiran sunayen Allah tsarkaka yanayi masa kirari da neman agajinsa.Allah maji rokon bawa fara yin wannan addua'a ta Yazid keda wuya saiya hango wata doguwar fadama wacce ruwanta daga kan saman wani dutse yake kwaranya cikin tsananin farin ciki Yazid ya rugwa da gudu izuwa inda fadamar take yana sabe da Nauwara a kafadarsa da zuwansa bakin fadamar bai tsaya bata wani lokaci ba saiya daka tsalle ya fada cikin fadamar gaba daya. Ai kuwa ruwa na shiga bakin Nauwara da jikinta saita farfado tana mai jan dogon numfashi amma sakamakon ruwan daya shiga cikinta da yawa sai numfashinta ya sake daukewa. A firgice Yazid ya fito da ita daga cikin fadamar ya shimfideta a kasa bakin koramar nanfa yayi arba da irin kyakkyawar surar jikin da Allah ya bata ya kai hannu da niyar danna cikinta kasa domin ruwa yafito amma saiya kasa saboda wannan ne karo na farko a rayuwarsa dazai taba jikin macen data kasance ba muharramarsa ba,Nauwara zata iya rasa rayuwarta sai yayi sauri ya shiga danna cikinta. Ai kuwa sai ga ruwa yana fitowa daga cikin bakin nata har ruwan ya gama fitowa Nauwara bata farfado ba kuma duk jikinta a sandare yake kamar gawa.Al'amarin daya dugunzuma hankalin Yazid kenan ya kara dimaucewa fiye da ko yaushe bai san sa'adda ya matse hancinta ba da hannunsa guda sannan yasa bakinsa a cikin nata ya hura mata iska. Faruwar hakan keda wuya sai numfashin Nauwara ya dawo ta mike zaune zumbur a firgice ta kama kalle kalle ko dataga yarima Yazid tsugune a gabanta kuma taji jikinta a jike sharkaf da ruwa saita dubeshi cikin alamun tsananin kunya da damuwa tace tsakaninka da Allah menene ya faru a gare ni? Na rokeka bisa girman Allah ka zaiyane mini iyakar gaskiya kada ka boye mini komai. Koda jin wannan batu sai zuciyar Yarima Yazid ta buga da karfi saboda ta daureshi da jijiyoyin jikinsa. A iya rayuwar Yazid bisa saninsa bai taba fadin karya ba bare kuma yanzu gashi an hadashi da girman Allah ance ya fadi duk abinda ya faru bisa gaskiya ba tare daya boye wani abu ba. Cikin hanzari Yazid ya juyawa Nauwara baya yace saboda me kike son kiji abinda ya faru gareki,kawai ki godewa Allah tunda dai kin tsira da rayuwarki.Nauwara ta gyada kai tace ai dukkan mai rai mamaci ne don haka bana tsoron mutuwa,fatana kawai Allah yasa na sami shahada a cikin wannan tafarki da muke kansa,saboda me baka son ka bani labarin duk abinda ya faru,kana jin kunya tane ko kuwa kayi wani abune ba daidai ba? Koda jin wadannan tambayoyi guda biyu sai ran Yarima Yazid ya baci ya dubi Nauwara cikin alamun fishi yace ai ita kunya alamace ta imani haka kuma ni dan adam ne ajizi don haka zan iyayin ba daidai ba amma zan faiyace miki duk abinda ya faru bisa gaskiya kamar yadda kika bukata domin ki sami nutsuwa a cikin ranki kuma ki cire dukkan zargi ko kokwanto a cikin ranki da zuciyarki. Batare da boye komai ba Yazid ya kwashe labarin duk abinda ya faru ya zaiyanewa Nauwara tun daga lokacin da kishirwa taci karfinta ta yanke jiki ta fadi kasa sumammiya kawo izuwa sa'adda ya tsomata a cikin wannan korama ta sake suma ya fito da ita ya ceto rayuwarta da kyar. Koda Nauwara ta gama jin wannan labari saita kyalkyale da dariya.Al'amarin dayayi matukar baiwa Yazid mamaki kenan kuma ya firgita ainun ya fara tunanin ko ta zautu ne har saida yaga tayi shiru ga barin dariyar ta dubeshi cikin nutsuwa sannan hankalinsa ya kwanta. Tsawon yan dakiku suna kallon juna dayansu baice uffan ba sai Nauwara tayi gyaran murya tace saboda me ka karya dokar Allah ka taba jikin macen daba muharramarka ba,ka sani cewa ni banda mahaifina da dan'uwana Zainur kaine namijin farko daya fara taba jikina gashi ma wai har bakinka ka...(uhmm Kunya).Nauwara ta kasa karasa bayaninta a lokacin da Yazid ya tari numfashinta yana mai daka mata tsawa yace mahaifinki ya bayar dake amana a gareni kuma na dauki *Abbas Abdulkadir Hada Hada* alkawarin kula dake da tsare rayuwarki da mutunci,idan kece zaki ki cika wannan alkawari? Nauwara tayi murmushi tace zan yarda da wannan hujja taka amma ba itace kadai ba akwai wata. Ka gaya mini gaskiya bisa tsoron Allah wanda yana jinmu kuma yana ganinmu,shin a cikin zuciyarka bakajin komai dangane dani. Koda jin wannan tambaya sai Yarima Yazid ya murtuke fuskarsa ya mike tsaye yana mai juya mata baya yace tashi mu koma can sansaninmu mu hakura da batun yin farauta tunda rana ta fadi magriba na daf dayi,yana gama fadin hakan saiya cigaba da tafiya.Nauwara ta mike tsaye zumbur ta ruga tasha gabansa ta tsayar dashi tace bazan koma sansaninmu ba face ka bani amsar tambayar da nayi maka. Yazid yace dole ne na koma tare dake tunda gadinki aka bani. To idan naki binka zaka kamani ne da karfin tsiya ka dora ni a kafadarka kamar yadda kayi mini sa'adda na suma,idan a wancan lokaci larura ce tasa ka taba jikina wannan lokacin kuma fa? Yazid yace wata lalurar ce tasa na aikata hakan,Kafin Yazid ya gama rufe bakinsa tuni Nauwara ta juya da baya cikin shammace ta falfala da gudun tsiya a cikin dajin,ai kuwa sai Yazid ya bita da sauri a guje yana kwala mata kira tamkar tseran gudu aka kasa tsakanin barawo da mai kaya. Karfin gudun Nauwara wanda har dan tashi sama yakeyi tana shallake kananun duwatsu wanda ke kasa da bishiyoyi. Kash rashin sani yafi dare duhu,inda Nauwara tasan cewa sunzo karshen dajin da suke ciki zasu afka cikin dajin kogon Hajarul Aswad yake ne da batayi gangancin yin wannan mugun wasa ba ga yarima Yazid. Nauwara na cikin falfala azababben gudu ne kawai taji ta fanjam ta fada cikin wani kogin kankara ga tsananin sanyi a cikinsa,domin tana fadawa ta kama karkarwar dari tururin sanyi ya fara fita daga cikin bakinta. Nan take ta firgita ta taso iziwa saman kogin ta fara iyo domin ta fito daga cikin a lokacin da Yazid ya rugo bakin kogin da gudu.Saura kiris Nauwara ta iso bakin gabar kogin sai kawai Yazid ya hango wata murtukekiyar jela ta wata halittar ruwa ta kanannade jikin Nauwara duka ta dagata sama zata makata izuwa kasan kogin. Daga inda Yazid yake ya daka uban tsalle sama yana mai kwala kabbara sai gashi a sama a guje tamkar daga cikin baka aka harboshi. Kafin jelar dabbar ta maka Nauwara izuwa cikin ruwan tuni yasa takobinsa ya sare kasan jelar dabbar kuma ya cafo kugun Nauwara da hannu daya suka sake fadowa kasa cikin kogin. Fadawarsu kasan ruwan keda wuya sai sukaga abin al'ajabin daya daure musu kai.Dabbar da Yazid ya sarewa jela ce ta taso sama daga karkashin kogin ta baiyana gaba dayan surar jikinta,ashe jela daya rak Yazid ya sare daga cikin jelolinta guda arba'in da daya. Ita dai wannan halitta siffar macijiya gareta amma kanta irin na mage ne saidai katone rafkeke mai girman gaske,bakinta wangameme ne tamkar an fafe dirom. Gaba daya jikinta daga kasan wuyanta zuwa jelarta,hannayenta na hagu da dama guda shida shida ne kuma yatsunta irin na birirai ne cike da zakwa zakwan farata,idanunta manya manya kuma jajaye ababan tsoro,kaurin jikinta kuwa yakai na karamar bishiyar kuka. Koda Yarima Yazid da Nauwara sukayi arba da wannan mummunar halitta a lokacin data wangame bakinta tayi wata irin kara mai karfin gaske wacce ta haddasa girgizar kasa a cikin dajin gaba dayansa sai Yazid da Nauwara suka firgita ainun hatta su yarima Zainur dake can wancan daji saida suka jiyo wannan kara suka razana. A daidai wannan lokaci ne Su Yarima Zainur sun fara yin alwala domin su gabatar da sallar magriba gashi har a sannan Yazid da Nauwara basu dawo ba.Koda sarkin yaki Haiman da Zainur da sauran dakaru suka jiyo wannan gagarumar kara ta dabbar da baza'a iya tantance taba sai kowa ya razana ainun amma saboda Sallah za'ayi sai Haiman yace a bari sai an idar da sallar sannan a tafi nemansu gimbiya Nauwara. . ME ZAI FARU TSAKANIN YARIMA YAZID DA KUMA GIMBIYA NAUWARA? SHIN SU SARKIN YAKI HAIMAN ZASU ZO HAR SU TAIMAKA MUSU? INA LABARIN SU WAZIRI RIDWAN DA SARKI MARWATU? SHIN YARIMA YAZID,YARIMA ZAINUR DA SARKIN YAKI HAIMAN ZASU IYA CIN NASARAR DAUKO WASIKAR JINI? TSAKANIN SU DA WAZIRI RIDWAN SU WAYE ZASU SAMU NASARA? Duk mai son jin wadannan amsoshi ya nemi Littafi na takwas (8) a kasuwa wanda shi zai zamo na karshe , inkuma naga masu so sunada yawa kamar 200 comment 100 like zan nacigaba da post muku inkuma kasa da hakane saidai kunema a kasuwa. END OF BOOK 7. WASIKAR JINI!!! Littafi Na Takwas (8) Part A. . NAN TAKE KUWA HAIMAN YA SHIGE GABA YAYI MUSU LIMANCI,BAYAN AN IDAR DA SALLAR ANYI ADDU'A SAI KOWA YA KIMTSA SUKA DEBI MAKAMANSU DA DUKKAN KAYANSU SUKAYI GABA. Tafiyar su yarima Zainur keda wuya bayan cikar rabin sa'a daidai saiga rundunar su sarki Marwatu sun baiyna,dukkaninsu a cikin shigar bakaken tufafi kuma a kasa suke babu mai doki guda daya,babu sarki Marwatu da Waziri Ridwan a cikin wadannan zuga sakamakon dole ne su kwanta suyi jinyar raunikan jikinsu. Daga nesa suka fara sanda harma a cikin rub da ciki suke tafiya suna jan jikinsu sai kace macizai. Sa'adda suka hango sansanin sukaga fitilo a kunne kuma ga dakarun tsaro a tsaitsaye sun yiwa sansanin kawanya,abinda basu sani ba shine babu kowa a cikin sansanin kuma dakarun da suke hangowa a tsaitsaye duk ba masu rai bane mutum mutumi ne dukkaninsu. Koda ya rage saura baifi taku ashirin ba tsakakanin dakarun sumamen da sansanin sai kawai suka fara harbo ruwan kibiyoyin wuta,nan da nan tantunan da aka kafa suka kama cin wuta,suma mutum mutumin dake tsaye suka rinka faduwa kasa suna ci da wuta,cikin kankanin lokaci komai dake cikin sansanin ya kone kurmus. Duk wannan abu dake faruwa dakarun sumamen na kwance a kasa cikin lambo jira suke kawai suji dakarunsu Zainur sun rugo daga cikin wutar sannan suma su taso su afka musu,amma sai sukaji shiru abin daya kara basu mamaki ma shine tunda suka harbo kibiyoyin wuta a cikin sansanin kawo izuwa sa'adda komai ya kone basu jiyo ihun koda mutum daya ba. Koda fuskantar hakan sai shugaban dakarun ya mike tsaye zumbur ya kura idanunsa da kyau izuwa cikin sansanin take ya gane cewa lallai makircin yaki aka nuna musu saboda ko mutum daya mai rai babu a cikin sansanin mutum mutumi ne kawai wadanda basu haura guda ashirin da wani abu ba kwance a kasa suna ci da wuta.Koda ganin haka sai shugaban dakarun sumamen ya kwarara uban ihu cikin tsananin bakin ciki.Al'amarin da yasa gaba dayan yaran nasa suka mike tsaye kenan suka dubi cikin sansanin. Koda suka fahimci abinda ke faruwa sai suma ransu ya baci nan take shugaban dakarun ya fiddo wani dan karamin madubin tsafi daga cikin aljihu ya shafe shi sai ga fuskar waziri Ridwan ta baiyana,kafin shugaban dakarun sumamen ya bude baki yace wani abu tuni Ridwan ya tari numfashinsa yana mai cewa kai shashashan banza,abokan gaba sun yaudare ku ne kamar yadda suka yaudare mu da farko,kai wane irin dakiki ne ashe ban gargadeka ba akan kada ku kai hari sai kun tabbatar da cewa abokan gabar na nan a cikin sansaninsu. To ka sani cewa tuni sun matsa gaba sun kafa wani sansanin kuma a yanzu haka wasu daga cikinsu sun bar sansanin sun tafi neman wannan bakon da gimbiya Nauwara wadanda su tuni sunyi nisa a cikin daji babu mamaki ma sun fada cikin daji da kogon Hajarul Aswad yake. Maza ku karaso sabon sansanin nasu ku kashe duk wani abu mai rai dake cikinsa karku bar ko kaza guda daya da rai.Ni da sarki Marwatu da sauran dakaru zamu riske ku a sansanin nan da zuwa gobe da safe. Koda gama fadin haka sai hoton fuskar waziri Ridwan ya bace daga kan madubin.cikin gaggawa shugaban dakarun sumamen da yaransa kimanin su dubu arba'in suka nausa da gudu izuwa cikin daji. Wani irin gudu sukeyi na ban al'ajabi saboda karfin sihirin tsafinsu domin har tashi sama suke suna dira a kan kololuwar dogayen bishiyoyi suna karawa gaba. * A can cikin kogon kankara kuwa lokacin da yarima Yazid da Gimbiya Nauwara sukayi arba da wannan katuwar mummunar halitta mai siffar macijiya dauke da kan mage,ga hannaye guda goma sha biyu gami da jelar guda arba'in da gutsiren daya wacce Yazid ya sare rabinta sai suka firgita ainun. Ba shiri Yazid ya tunkude Nauwara bayansa ya daka mata tsawa yana mai bata umarnin ta cigaba da iyo ta fice daga cikin kogin kankarar ta isa can daya gabar tasa. Koda halittar ta fahimci hakan sai ta tasam musu su biyun tana jeho musu hannayenta da jelunanta tana kawo musu mugun duka gami da sara da suka da kaifin faratan hannayenta. A karom farkon data kawowa Nauwara sara da farcen hannunta guda Nauwara ta yunkura cikin zafin nama ta zare takobinta ta kare saran ai kuwa sai kafin farcen nata ya raba takobin Nauwara gida biyu,kafin Nauwara tayi wani yunkuri tuni halittar ta gabza mata wawan naushi da jelarta guda a fuska. Saboda Karfin Naushin saida Nauwara tayi sama kuma tayi katantanwa sau uku a saman sa'adda jini yayi feshi daga bakinta ta fado kasa cikin kogin kankara a sume kuma ta fara lumewa izuwa karkashin kogin. Koda Yazid yaga abinda ya faru ga Nauwara sai ya fusata ainun bai san sa'adda ya kwala kabbara ba ya daka tsalle sama daga cikin kogin tamkar daga cikin baka aka cillo shi ya dankarawa halittar wawan sara a tsakiyar kanta.Nan take takobin tasa ta rabe gida biyu amma saboda karfin saran nasa saida halittar tayi wani uban ruri sakamakon tsananin zafi da zugin da taji ta fadi da baya cikin kogin tsundum tamkar daga sama aka jefo giwa. kafin halittar ta taso saman ruwan tuni Yazid yayi nutso kasa ya dauko Nauwara yayi ninkaya izuwa bakin gaba ya shimfideta a kasa amma ko alamar numfashi babu a tare da ita. Al'amarin dayayi matukar dugunzuma hankalinsa kenan ya fara kokarin dawo da numfashinta yana mai danna kirjinta. Kawai sai yaji tasowar wannan halittar daga karkashin kogin. A fusace Yazid ya juyo ya kura mata idanu.Halittar ta fito daga cikin ruwan tana tafiya sululu a kasa tamkar macijiya kuma ta tunkaro inda yake.Komai dakewar mutum gami da karfin zuciyarsa idan yaga wannan halittar yayin fitowarta daga cikin wannan kogi tana mai baiyana gaba dayan surarta dole ne ya *Abbas Abdulkadir hada hada* firgita.Cikin zafin nama Yazid ya mike tsaye zumbur ya shafa ko ina a jikinsa yaji babu makami ko guda daya kawai saiya dunkule hannayensa yana mai gyara tsayuwarsa sannan ya shiga karanta wadansu addu'o'i na musamman a cikin zuciyarsa a lokacin da halittar ta cigaba da durfafo shi. Koda ya fuskanci cewa halittar so take ta kawo musu cafka su biyun har da Nauwara wacce ke kwance tamkar gawa sai ya rugo da gudu izuwa kan halittar ya tareta suka ruguntsume da azababben yaki ya zamana cewa suna kaiwa junansu naushi da bugu,ita halittar tana kai masa duka da dukkan jelunanta amma sai gashi yana iya kade hannayen nata da jelunan nata cikin wani irin bakin zafin nama na gaban kwatance kuma yana mai da mata martani. Duk sa'adda ya sami nasarar naushin halittar ko ina a jikinta sai tayi baya a sama tamkar da majaujawa aka janyeta saboda karfin naushin nasa amma saboda naci irin nata sai kaga ta kuma tasowa sun cigaba da artabun.Kokarin halittar kawai shine ta samu ta kanannadeshi da jelarta guda amma ta kasa,shi kuma kokarin da yake shine ya samu damar naushinta a fuska ko a kanta saboda ya fuskanci cewa nan ne lagonta yake,domin sa'adda ya dankara mata saran nan a tsakiyar kanta saida idanunta suka wurkile tayi rabin suma ta lume kasa a cikin kogon kankarar amma saboda bakin naci tana farfadowa sai ta taso sama suka cigaba da artabu. Saida Yazid da wannan halitta suka shafe kusan rabin sa'a suna kwamarzuwa tana bugunsa yana bugunta ya zamana cewa kowannensu naji a jikinsa amma an rasa wanda zai sami nasara a cikinsu. Ita dai halittar tana ta zane masa sassan jikinsa da jelunanta amma ta kasa sukarsa ko yankansa da faratan hannayenta,shi kuma ya sami nasara yana ta gabza mata naushi a fuskarta har idonta guda ya kumbura subtum yana zubar da jini,kunnenta guda ya doshe ta daina ji dashi,ko ina a fuskar tata ya kumbura yayi luhu luhu gashi dai ta

Chapter 13 of 15