Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yarima yazid ya numfasa yace nayi hakane saboda na nunawa duniya cewa tafarkin da kuke kai ba shine tafarkin gaskiya ba,tabbas kuna cikin bata mabayyani yanzu gashi ka kamu da cutar da kowa yake ganin cewa babu yadda za'ayi ka warke harka tsira da rayuwarka,kwana da kwanaki kana kwance kamar gawa ba ci ba sha,ba magana,ba motsi da bude ido saboda bakin sihirin dake jikinka amma gashi yanzu farat daya da taimakon ubangijina na tasheka zaune harma ka iya budar baki kayi magana alhalin kana jiran mutuwarka ne nan da cikar kwanaki kadan. Shin wannan bai isa yasa kayi imani cewa babu abin bautawa da gaskiya ba face ubangijin musulunci? Koda yarima yazid yazo nan a jawabinsa sai sarki Aiyuba ya bushe da dariya. Al'amarin daya baiwa su gimbiya nauwara tsananin mamaki kenan,sarki Aiyuba ya sake yunkurawa da kyar ya mike zaune batare da an taimaka masa ba sannan ya dubi yarima yazid yace,kai yazid yanzu kai kana ganin cewa zaka iya kareni daga kaddarar da ababan bautarmu suka shirya a kaina,kabar ganin cewa ka tasheni a yanzu har na iya magana da motsi,ina mai tabbatar maka da cewa ruhina yana can a dajin Hajrul Aswad a hannun ababan bautarmu,kuma ajikin wasikar jini,idan har kanason ka ceci rayuwata to saidai kaje ka yaki dukkan allolinmu dake cikin kogon dajin hajrul aswad ka kashe su su dari tara da casa'in da tara,sannan kuma ka kone WASIKAR JINI yadda har abada ba zata sake yin tasiri ba. Ina mai tabbatar maka da cewa idan ka nufi dajin hajrul Aswad da wannan manufa saika hadu da mugayen masifun da zasu shallake tunaninka,kuma babu yadda za'ayi ka iya tsira daga wannan masifu bare har ka iya isa kogon Hajrul Aswad ka kashe allolinmu ka kone wasikar jini. Baya ga wannan kayi sani cewa ko masifar da zaka fuskanta daga dan uwana waziri Ridwan wanda yake son ya gaje wannan karagar mulki tawa ta isheka domin bazai taba bari ka sami nasara ba. Lokacin da sarki Aiyuba yazo nan a jawabinsa sai yarima yazid yayi murmushi a karo na biyu sannan yace,naji yarka tace kabar mata wasiyar zainur yayi amfani da duk shawarar dana bashi me yasa kayi imani da hakan alhalin kuma yanzu gashi ka kasayin imani da abinda zan iya aikatawa? Koda jin wannan tambaya sai jikin sarki Aiyuba yayi sanyi ya sunkui da kansa kas sannan yace nayi hakane saboda ni na fison na mutu akan tafarkin da iyayena da kakannina suka mutu amma ina sha'awar 'yata ta mutu akan naka tafarkin. Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa gimbiya Nauwara ta dubi sarki Aiyuba tace haba yakai Abbana ashe yanzu baka so ka cigaba da rayuwa tare da ni hat kaga 'ya'yanka da jikokinka? Koda jin haka sai hawaye ya zubowa sarki Aiyuba yace yake 'yata kiyi sani cewa na dade da cire wannan buri daga cikin rayuwata saboda tuni na bayar da jini na ga ababen bautarmu kuma nasan cewa bazan kai lokacin da zakiyi aure ba. Koda jin haka sai Yarima Yazid ya tari numfashin sarki aiyuba yace yanzu idan na tafi izuwa dajin hajrul aswad na tsallake duk masifun dake kan hanyar naje na hallaka ababan dogaronku kuma na kone wasikar jini na dawo nan gareka a raye cikin koshin lafiya kuma kaima na iske ka araye zaka karbi addinina kayi imani da ubangijin musulunci? Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa sarki aiyuba yace,yakai wannan dan sarki kayi sani cewa a zuri'ar mu babu abinda yafi alkawari muhimmanci don iyayena shekaru arba'in da uku da suka shude abinda nake nufi shine tun ina da shekara bakwai a duniya na yiwa mahaifina alkawarin cewa zan rike addininsu da al'adarsu,kuma zan mutu akan tafarkinsu,ko a yanzu a cikin zuciyata nasan cewa addininka shine addinin gaskia,kuma koda kaje ka samo wannan nasara ka dawo ka riskeni a raye cikin koshin lafiya bazan karbi addininka ba. Lallai saina mutu akan addinina don cika alkawari ga mahaifina da kakannina,amma ina mai umartar 'yata gimbiya nauwara data karbi addininka saboda a kawo karsehn wannan bakin addinin namu da kuma bakar al'ada. Kayi sani cewa ban san iyakar rayukan dana dauka ba don cika umarnin allolinmu da biyan bukatunsu,bansan iya adadin jama'ar dana zalunta ba,ko don saboda wannan babban dalili dana dauka a doron kasa,lallai inason na mutu akan tafarkina domin shine kadai horon daya dace dani. Yake 'yata na sani cewa daga kuruciyarki kawo i yanzu baki taba kashe koda kwaro ba da hannunki,baki taba zaluntar wani bil'adam ba don haka ne nayi miki sha'awar shiga wannan addini mai adalci saboda ya dace dake kuma inason anan gaba keda zuri'arki kuyi rayuwa mai inganci wacce zaku amfaneta duniya da lahira.Koda gama fadin hakan sai sarki aiyuba ya kamo hannun yarima yazid sannan ya kamo na gimbiya nauwara ya hada waje guda ya dubi yazid yace daga yau na sauke nauyin dana dorawa dan'uwan nauwara wato zainur na dorashi akanka yakai yazid Bin Arsanal,na bar maka amanar 'yata,lallai ka shigar da ita cikin addininka mai tsari kuma ka shafe addinina da makiyana daga doron kasa,wannan ce kadai hanyar da zaka iyabi ka yada naka addinin a wannan nahiya gaba daya.Wannan shine kalamaina na karshe a gareku ina maiyi muku fatan sa'a da nasara amma tabbas ni kam tawa ta kare,lallai bazaku dawo ku riskeni a raye ba. Koda gama fadin hakan sai gimbiya nauwara ta rungume sarki aiyuba ta fashe da matsanancin kuka,shima saiya kama kukan a lokacin da tausayinsu ya turnuke yazid,zainur da sauran hadimai suma suka kama zubar da hawaye. Bayan sarki aiyuba da gimbiya nauwara sun dan jima a kankame da juna sai ya cire jikinsa daga cikin nata sannan ya dubeta a lokacin da hawaye ya zubo masa yace,daga yau gidan nan ya haramta a gareni har sai bayan kun dawo daga dajin Hajrul Aswad a cikin nasara.A sannan zaki iya hawa karagar mulki.Koda gama fadin hakan sai sarki Aiyuba ya koma kan gadonsa ya kwanta yana mai yiwa Gimbiya Nauwara kallon karshe a lokacin data kura masa idanu tana zubar da hawaye.Nan Yarima Zainur ya kamo hannunta ya jata suka fice daga cikin turakar sarki tana waigensa shima yana zubar da hawaye. SHIN SU YARIMA YAZID ZASU ISA KOGON DAJIN HAJRUL ASWAD A RAYE SU DAUKO WASIKAR JINI? WANE IRIN MUGAYEN MASIFU ZASU HADU DASU AKAN HANYA KAFIN SU ISA CAN? TSAKANIN WAZIRI RIDWAN DA YARIMA ZAINUR WAYE ZAI GAJI SARAUTAR? INA LABARIN SARAUNIYA LAZWARA? SHIN ITAMA ZA'AYI WANNAN TAFIYA NE TARE DA ITA? MENENE DALILIN DA YASA LOKACIN DA GIMBIYA NAUWARA DA YARIMA YAZID SUNA GANIN JUNA SAI ZUCIYOYINSU SUKA BUGA DA KARFI? INA LABARIN ARDADU KUWA? WAISHIN KUWA INA SARKI MARWATU? Mu Hadu A Wasikar Jini Littafi Na Shida domin jin cigaban wannan kasaitaccen labari. WASIKAR JINI!!! Littafi Na Shida (6) Part A . Al'amarin Ardadu kuwa lokacin daya isa wannan gida inda su barde Uraidu suke dauke da taswirar zuwa dajin Hajrul Aswad cikin tsananin farin ciki bisa sanin cewa shi kam ya gama arziki na duniya bashi ba talauci,sai aka bude masa kofar gidan ya shige ya isa har can ciki inda barde Uraidu ke zaune.Koda barde Uraidu yaga Ardadu ya shigo fuskarsa cike da annuri sai shima farin ciki ya lullubeshu saboda ya san cewa ya samu nasara. Cikin zakuwa Uraidu ya taso daga kan kujerar da yake zaune ya tari Ardadu yace ina abindana umarceka da samowa,shin ka dace? Koda jin wannan tambaya sai Ardadu yayi murmushi sannan kuma ya murtuke fuska yace ta yaya zan mika maka wannan abu mai daraja alhalin banga cikon alkawarinmu ba. Koda jin haka sai barde Uraidu ya bushe da dariya sannan ya dubi wadansu dakaru nasa.Nan take dakarun suka shiga cikin wani daki suka fito da wadansu manyan akwatuna guda hudu na karfe.Koda aka bude akwatunan saigasu cike taf da lu'u lu'u,koda ganin wannan dukiya sai Ardadu ya zaro taswirar daga cikin aljihunsa ya nunawa barde Uraidu,sannan yayi wuf ya dauko wata fililar wuta ya rike ya dubi Uraidu yace idan kukayi wani yunkuri na yaudarata zan kone wannan taswira yanzu take,abinda nakeso daku shine yanzu mu fita waje a dora wadannan akwatuna bisa keken doki a bani sannan na danka muku wannan taswirar. Koda Ardadu yazo nan a zancensa sai Barde Uraidu ya bushe da dariya sannan ya dubi Ardadu yace hakika ka burgeni domin ka nuna mana cewa kai tsohon macucine wanda yasan kan tuggu,ka sani cewa saboda muhimmancin wannan taswira dake hannunka ko kuda banson ya sauka a kanta saboda haka a shirye nake nabi dukkan umarninka. Nan take Uraidu yasa aka dauko wadannan akwatuna na kudade aka lodasu akan keken dokin saida Ardadu yaga ya hau kan keken dokin ya zauna sannan ya wurgawa Uraidu wannan taswira ya cafe shi kuma ya zaburi keken dokin da gudu ya tafi a cikin dimbin farin ciki. Tafiyarsa keda wuya sai barde Uraidu ya bushe da dariyar mugunta yace shasha kawai ai hanyar kashe makahon kare yawa gareta. Ka dauki ajalinka ka tafi dashi baka sani ba.Gama fadin hakan keda wuya sai uraidu ya koma cikin wannan gida yayi shiga ta badda kama sannan ya fito aka kawo masa doki yahau ya zabureshi da gudu ya nufi gidan waziri ridwan. Ta cikin wata barauniyar hanya Uraidu yabi ya nufi gidan waziri ridwan,hanya ce ta bayan gari inda babu mutane kuma babu wanda yasan da wannan hanya face shi kansa Waziri Ridwan sai kuma wanda ya yarjewa. Waziri Ridwan ya kirkiri wannan hanya ne saboda aiwatar da al'amarunsa na sirri ba tare da wani ya gani ba. Ta cikin wani bututun karfe dake cikin karkashin kasa Uraidu yabi da dokinsa sai gashi ya fito tsakiyar gidan waziri ridwan bisa dokinsa.Da fitowarsa sai wani hadiminsa ya ruga gareshi ya ruke masa dokin ya sauka sannan ya durfafi turakar waziri ridwan tamkar cikin gidansa yake shiga. Waziri Ridwan na zaune a cikin kuryar turakarsa yana nazari a cikin madubin tsafinsa saiga Uraidu ya shigo fuskarsa cike da annuri koda waziri ya hangoshi sai shima ya mike tsaye zumbur ya tareshi cikin murna, Take Uraidu ya zube kasa bisa guiwoyinsa yayi gaisuwa sannan yasa hannu a cikin aljihunsa ya dauko wannan taswira wacce aka zanata a kan fatar damisa ya mika masa.Cikin tsananin farin ciki Ridwan ya karbi taswirar ya dubata da kyau kawai sai ya bushe da dariyar farinciki sannan ya dubi Uraidu yace tabbas ka cika aikinka daidai don haka yanzu zan cika alkawarina a gareka,kaje ga sarkin gida akwai rijiya guda goma a cikin gidan nan wadanda ke cike da zinare da lu'u lu'u kaje kaida yaranka ku yashe wannan rijiyoyi kuyi gaba da abin ciki rabonku ne.Koda jin wannan bishara sai barde Uraidu ya kamu da tsananin farin ciki ya sake zubewa kasa yana godiya sannan ya mike tsaye zumbur ya ruga waje da gudu. Uraidu na fita kuwa sai yayi kicibus da sarkin gida kawai sai sarkin gida ya kama hannunsa ya jashi izuwa wani daki ya nuna masa wadannan rijiyoyi na zinare da lu'u lu'u.Koda ganin wannan dukiya sai Uraidu ya dimauce ya kama kyalkyala dariyar farin ciki tamkar mahaukaci sabon shiga kuma ya kama sintiri a tsakanin rijiyoyin yana lekasu. Daman masu iya magana sunce zama waje daya tsautsayi ne kuma a bari ya huce shi ke kawo asara ko rabon wani.Lokacin da barde uraidu ya tsaya bata lokaci a can dakin da rijiyoyin dukiya suke shi kuma waziri ridwan na ruke da taswirar nan yana kara nazarinta a hankali cikin nutsuwa kawai sai yaga ashe babu inda ya nuna ainihin kogon Hajrul Aswad,daya sake nazarin taswirar da kyau saiyaga ashe taswirar ta wani dajin daban ce wanda ba a cikin nahiyar yake ba. Nan take zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone kawai saiya mike tsaye zumbur ya ruga waje ya nufi dakin da wannan rijiyoyi suke.Adaidai wannan lokaci ne barde Uraidu ya fito daga cikin dakin a guje domin yaje ya kirawo yaransa su jide dukiyar kawai sai yayi karo da waziri ridwan,cikin bakin zafin nama waziri ridwan ya zaro wata sharbebiyar wuka ya lumawa Uraidu a ciki. Take wukar ta bullo ta gadon bayansa amma saboda jarumtaka sai barde Uraidu ya bangaje waziri Ridwan ya fadi,jini yayi tsartuwa a lokacin da jiri ya debeshi ya juya ya dubi ridwan ya bude baki da kyar yace,ya shugabana saboda me zaka kasheni alhalin na cika aikinka kamar yadda kake bukata? Koda jin wannan tambaya sai waziri ridwan ya mike a fusace yace kai shashasha aikinka bai cika ba.Kawai sai waziri ya cillawa uraidu wannan taswira yace duba da kyau kagani sarkin yaki yaudararka yayi bai baka taswirar ta gaskiya ba wannan jabuce.An gaya maka ™Abbas Abdulkadir Hada Hada™ ana cin dukiyata ne a saukake? Ka sani nayi asarar miliyoyin dinare akan wannan aiki tun daga farkonshi kuma a yanzu kana son nayi asara ninkin ta farko? Koda jin wannan batu sai barde Uraidu ya bushe da dariya cikin karfin hali,al'amarin dayai matukar baiwa waziri ridwan mamaki kenan. Uraidu ya fadi kasa yana kakarin mutuwa amma duk da haka saiya bude baki da kyar yace yakai waziri Ridwan shin ka mantane da dimbin dukiyar da kashe a baya a kokarin karbe wannan karagar mulki daga hannun dan uwanka saboda hassadarka da zaluncinka har izuwa yanzu ka kasa samun wannan nasara kuma baka daina asarar miliyoyin kudade ba. To kasani mutum yana mutuwa da burinsa,nafi shekara talatin ina fashi da sata,ina kashe mutane don kawai na tara dukiyar da zata isheni iya rayuwata amma saboda haramtacciyar hanya nakebi ta tara dukiyar batayi mini albarka ba bare burina ya cika. Tabbas hanyar da kabi don cika burinka ka ninka tawa sau dubu a rashin tsafta don haka ba zaka taba samun nasara ba,lallai da wannan bakin burin naka zaka mutu. Koda jin wannan batu sai waziri ridwan ya zare takobinsa ya nufo uraidu ya fusace shi kuwa Uraidu sai yacigaba da kyalkyala masa dariya har saida yazo daf dashi ya daga takobin sama ya fille masa kai,take kan Uraidu yayi sama ya fado kasa tum amma kuma dariyace akan fuskar har a sannan, cikin tsananin fushi waziri ridwan ya kwalawa wadansu dakarun sojan haya kira su dari biyu da ashirin a cikin shiga ta bakaken tufafi suka fito da gudu daga cikin wani babban daki na gidan suka zo suka zube a gabansa su suka suna masu sunkuyar da kawunansu kas. Sudai wadannan dakarun sojan haya sun ninka dakarun uraidu sau biyu a girma,kwarjini da iya yaki kuma suna dauke da muggan makaman yaki irin wanda ma ba a saba gani ba. Take waziri ridwan ya dubi wadannan dakaru yace na umarceku dakuje gidan sarkin yaki haiman a daren yau ku kashe duk mai numfashi dake gidan,sannan ku nemo wannan taswirar ta dajin Hajrul Aswad ku kawo mini.Koda jin wannan batu sai gaba dayan dakarun suka amsa cikin hada murya sukace an gama ya shugaba. Wannan shine abinda ya faru a gidan waziri ridwan bayan barde Uraidu yakai masa jabun taswirar dajin Hajrul Aswad * Al'amarin Barde Ardadu kuwa lokacin daya tafi da dukiya a cikin keken dokin yana mai matukar farin ciki sai yayi ta kyalkyala dariya domin ji yake kamar yafi kowa a duniya samun sa'a da nasara,kai tsaye ya nufi gidan sarki kasuwa domin karbar waccan dukiya ta farko wacce ya bayar da ita ajiya.Yana zuwa kuwa aka bude masa kofar gidan ya kunna kai ciki,bisa sa'a kuwa sai ya iske sarkin kasuwa zaune a harabar gidan bisa shimfida,jama'a sun kewayeshi ana tattaunawa akan harkokin kasuwanci mafi akasarin jama'ar dake wajen fatake ne.Koda sarkin kasuwa yaga Ardadu ya shigo sai ya mike tsaye daga kan shimfidarsa ya tareshi suka gaisa.Sarkin kasuwa ya juya ya dubi wadansu hadimansa dake tsaye a gefe guda yace dasu suje su dauko jakar mai kala kaza a cikin daki kaza.Nan take hadiman suka ruga izuwa cikin gidan don cika umarnin cikin mamaki da farin ciki Ardadu ya dubi sarkin kasuwa yace nawa zan biyaka bisa wannan ajiya da kayi mini? Koda jin wannan tambaya sai sarkin kasuwa yayi murmushi yace ai duk abinda kayi niya shi zaka bayar idan ma kaga zaka takura to zaka iya bari sai wani lokacin. Koda jin wannan batu sai mamaki ya kara turnuke Ardadu ya gane cewa lallai sarkin kasuwa bai bude ajiyar daya kawo masa ba yaga abinda ke ciki,kawai sai ya tambayi kansa a cikin zuciya yace dama ashe akwai irin wadannan mutane a duniya masu amana haka? Kafin ya baiwa kansa amsa sai ga wadannan hadiman sun fito dauke da ajiyar Ardadu.Take aka sanya jakar cikin keken dokin bisa wadannan akwatunan dinare- dinare. Ardadu ya shafa dukkan aljihun jikinsa yaji ko sisi don haka sai yasa hannun ya bude wannan jakar kudi kadan ya zura hannunsa cikin domin ya dauko dinare guda uku kacal ya baiwa sarkin kasuwa a matsayin ladan ajiyarsa. Kash rashin sani yafi dare duhu, inda Ardadu yasan abinda zai biyo baya da bai cusa hannunsa a cikin wannan jakar kudi ba.Ashe tun ranar da uraidu ya bashi wannan jakar acan kasanta akwai wani karamin bakin maciji mai mugun dafi,macijin najin hannun Ardadu ya shure shi saiya dankara masa sara bai san sa'adda ya kurma uban ihu ba,shida jakar kudin suka fado kasa,kudin suka tarwatse macijin ya yunkura zai gusa sai wani daga cikin dakarun sarkin kasuwa ya dankara masa sara ya baje a kasa matacce,shi kuwa Ardadu saiya kama karkarwa kamar wanda aka tsoma a cikin ruwan kankara,idanunsa suka wurkila kuma saiga farar da dafara na fitowa ta cikin bakinsa,kafin sarkin kasuwa da yaransa su baiwa Ardadu wani taimako tuni rai yayi halinsa ya zama gawa. Cikin tsananin mamaki sarkin kusuwa ya dubi gawar Ardadu sannan ya dubi makudan kudaden da suka tarwatse a kasa daga cikin wannan jaka ya dubi yaransa yace yanzu dama ashe kudi ne haka a cikin wannan jaka wannan mutumin ya kawo mini ajiya ban sani ba. Koda jin wannan batu sai babban hadimin sarkin kasuwa yayi ajiyar zuciya ya shugabana ai bana fidda tsammani cewa wadannan akwatunan guda hudu ma dake cikin keken doki kudi ne a ciki,shin baka san ko wanene wannan mutum bane? To ba wani bane face mashahurim danfashin nan daya gagari fatake wato Ardadu. Koda jin haka sai tsoro ya kama sarkin kasuwa yasa aka bude wadannan akwatuna gudu hudu sai gasu cike da dinare da lu'u lu'u,nanfa kowa ya dada firgita ainun a wajen. Babu abinda ma yafi firgita sarkin kasuwa face ganin tambarin waziri ridwan daga cikin akwatunan kudin.Nan fa sarkin kasuwa ya sake dimaucewa fiye da ko yaushe jikinsa ya ™Abbas Abdulkadir hada hada™ kama tsuma ya dubi babban hadiminsa cikin alamun tsoro da firgici yace,tabbas muna cikin mummunan hadari wannan dukiyar dai ga dukkan alamu ta waziri ridwan ce kuma ina ganin cewa satota akayi saboda nasa halin waziri ridwan babu mutumin dazai iya amincewa ya bashi wannan dimbin dukiya domin a juya masa ita. Yanzu me ya kamata muyi? Shin zamu dauki wannan dukiya ne mu mayar da ita ga waziri ko kuwa zamu ajiye tane har sai anyi cigiyarta? Koda jin wannan tambaya sai babban hadimin ya numfasa yace ba zamu mayar da wannan dukiya baga waziri ba kuma ba zamu ajiyeta ba anan gidan shawarar da zan bayar itace mu kwashe wannan dukiya mu kaita gidan sarki mu dankata a hannun gimbiya nauwara tunda a halin yanzu itace mai kula da harkokin kudade na kasar nan. Koda jin wannan shawara sai hankalin sarkin kasuwa ya kwanta nan take ya bada umarni aka tafi da dukiyar izuwa gidan sarki, gawar Ardadu kuwa sai aka dauketa a sirrance akaje aka boye saida dare ya raba sannan aka je aka jefata a ruwan teku kifaye da sauran halittun ruwa suka sami rabonsu. Ohh Allah ka kiyashemu da yin mummunan karshe, hakika duk mutumin da yasa kwadayin duniya a ransa gami da cin zali da cuta to da wuya karshensa yayi kyau,wannan shine yanda karshen munafuki Ardadu ya kasance,saidai kuma ya mutu musulmi don haka babu wanda yasan sakamakonsa a wajen Allah duk da cewa kuwa ya karbi musulinci ne da zuciya biyu, * Al'amarin su Yarima zainur kuwa lokacin dasuka baro gidan sarki tare da gimbiya nauwara bisa dawakai da nufin su koma gidan sarkin yaki haiman sai sukayi kicibus da sarkin yaki a cikin keken doki tare da dukkan hadimansa da kuma dakarun dake tsaron gidansa. Cikin kaduwa da alamun tsananin mamaki yarima zainur ya sauko daga kan dokinsa yazo gaban keken dokin ya dubi haiman yace yakai abbana ina dalilin fitowarka daga gida alhalin kana bukatar ka kwanta kayi jinyar raunikan dake jikinka,kuma ina ka nufa daga nan? Kafin haiman ya budi baki yace komai saiya dubi gimbiya nauwara da yarima yazid ya yafuto su da hannu. Take suma suka sauko daga kan dawakansu sukazo gareshi a sannanne haiman ya dubesu su ukun yace dani daku duk rayuwarmu na cikin mummunan hadari.Nan take ya kwashe labarin duk abinda ya faru tsakaninsa da Ardadu bayan fitarsu ya zaiyane sannan yace dole ne daganan mubar cikin garin nan kuma mu nemi inda zan buya nayi jinyar jikina,kema gimbiya ba zaki bi su yarima izuwa wannan tafiya mai mugun hadari ba dole ne ki zauna tare dani har izuwa lokacin da zasu dawo. Ina mai tabbatar muku da cewa dazarar waziri ridwan ya gano cewa jabun taswira Ardadu ya bashi zai turo a kashe mu kuma a caje gidana gaba daya don neman ta gaskiyar. Ko da gama fadin hakan sai sarkin yaki haiman ya zura hannunsa a cikin aljihun wandonsa ya fiddo wannan taswirar ya dankawa yarima zainur a hannunsa yace ga amanar sarki na dankata a hannunka kamar yadda ya bukata.Yanzu saimuyi sauri mubar cikin garin nan tun kafin makiya suzo su riskemu, koda jin wannan batu sai su yarima suka juya da baya cikin hanzari suka nufi hanyar data nufi wajen gari suna masu sakarwa dawakansu linzami,aikuwa sai dawakan haiman da jama'arsa ma suka rufa musu baya. WASIKAR JINI Littafi Na Shida (6) Part B . Aikuwa sai dawakan Haiman da jama'arsa ma suka rufa musu baya. * A can Gidan Waziri Ridwan kuwa duk da cewa ya kirawo wadannan dakarun sumame ya basu umarnin sukai hari izuwa gidan sarkin yaki da daddare sai yaji yakasa samun sukuni da kwanciyar hankali nanfa ya kama kai kawo yana tunani iri iri. Daga can sai kawai ya shiga can cikin turakarsa yayi gagarumar shigar yaki cikin batar da kama sannan ya kirawo wani hadiminsa yace dashi yayi sauri ya tafi izuwa cikin daji inda dakarunsa na sumame sukayi kwanton bauna ya gaya musu cewa su rarrabu kaso kaso a cikin dajin kuma su zuba ido sosai domin a koyaushe zasu iya ganin makiyansu su yarima zainur,da zarar an gansu a kashe su a dauko masa taswirar dajin hajrul Aswad. Koda jin wannan umarni sai badakaren ya risina yace an gama ya shugabana.Nan take hadimin ya rugo ya kama doki yahau ya fice daga cikin gidan da sauri. * Acan birnin sarki Marwatu kuwa tuni yan leken asiri sun kaiwa sarki marwatu labarin cewa sarki Aiyuba ya kwanta cutar ajali har takai cewa ma baya ci baya sha,kuma baya iya yin komai da kansa saidai a kwantar a tayat. Koda jin wannan labari sai farinciki ya lullube sarki marwatu take ya aiyana a ransa cewa batun biyan bashinsa yasha ruwa kuma lokacin da zai rama cin fuskar da sarki Aiyuba yayi masa yayi. Nan take yasa aka shirya dakarun yaki na mutum dubu dari uku ya jagorancesu suka kama hanyar da zata kaisu birnin sarki aiyuba. Haka dai wannan runduna taci gaba da tafiya ba sassauci dare da rana har saida suka iso dajin karshe wanda daga shi sai cikin birnin sarki aiyuba sannan suka yada zango. Bayan sun kafa sansani sai sarki marwatu ya tashi wani kwararren badakare dan leken asiri ya turashi izuwa cikin garin domin ya gano halin da ake ciki. Dama bokan sarki marwatu ya shaida masa cewa nan da cikar sati biyu sarki aiyuba zai fadi ya mutu.Idan har yana son yaci garin da yaki to lallai ya afkawa garin a ranar da sarki aiyuba ya mutu kada ya bari a kara koda kwana daya. A ranar da bokan ya gayawa sarki marwatu wannan labari sarki aiyuba ya shafe kwana uku a kwance yana jinya yanzu kuma sarki marwatu ya shafe kwana biyar cif yana yin wannan tafiya,yanzu kenan saura kwana shida sarki aiyuba ya mutu. * Lokacin dasu Yarima Zainur suka durfafi cikin dajin suka kama tafiya saida suka shafe yan sa'o'i suna tafiya dama yarima yazid ne akan gaba,kawai sai akaga yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak. Nan take kowa ya tsayar da nasa dokin akayi tsit a lokacin da yarima yazid ya kama raba idanunsa yana kallon gabas da yamma kudu da arewa,kawai sai ya juyo ya dubi gaba dayan abokan tafiyarsa yayi musu inkiya suyi shiru,kuma kada wanda ya motsa daga inda yake. Nan take yarima yazid ya shiga karanta wadansu addu'o'i na musamman,faruwar hakan keda wuya saiga wata runduna ta mayakan sumame su da yawa sunzo sun gifta ta gabansu bisa dawakai a sukwane dauke da muggan makamai suna ta waige waige da kalle kalle. Nanfa su sarkin yaki suka firgita ainun domin sunsan cewa ko ba'a gwada ba linzami yafi karfin bakin kaza,tabbas cikin dakiku kadan idan wadannan dakarun sumame sukayi musu rufdugu zasu gama dasu komai irin kokarin da zasuyi kuwa saboda ido ba mudu bane yasan koma kuma da ganin kura kasan zata ci mutum. Ba zato ba tsammani sai su sarkin yaki haiman sukaga Allah bai baiwa wadannan dakaru ikon ganinsu ba duk da cewa gasu sunzo daf dasu,wani lokacin ma har bangaren su sukeyi amma basu gansu ba.Haka dai wadannan dakarun sumame suka gaji da neme neme da dube dube suka gaji sukabar yankin wajen gaba daya. A sannan ne yarima yazid ya hango wani kogon dutse a can gabansu nan take ya bayar da umarni aka karasa can. Ba tare da wata gardana ba kuwa daga dayansu suka durfafi wannan kogon dutse. Da isarsu sai sukaga yazid ya tsaya a bakin kofar kogon bayan ya shiga cikinsa ya duba ko ina ya tabbatar da cewar babu wani abu mai cutarwa a cikinsa saida kowa ya gama shiga cikin kogon sannan yarima yazid ya tofa wata addu'a ta musamman a kofar kogon sannan shima ya shiga. Bayan kowa ya zauna ana hutawa kuma an dauko guzurin abinci anci ansha,sai sarkin yaki haiman ya yunkura da kyar ya mike tsaye yana mai dogara sanda ya taho inda yarima yazid ke zaune ya zauna kusa dashi suka fuskanci juna sannan yace yakai wannan dan ssarki kayi sani cewa tabbas yau naga abin al'ajabi a tare dakai kuma zuciyata ta karkata izuwa ga wannan addini naka,na sani cewa inada karfin sihirin tsafi daidai gwargwado amma sihirin wadancan dakarun sumamen da suka fito farautarmu ya ninka nawa sau goma,amma sai gashi sunzo har gabanmu kuma sun kasa ganinmu. Ina ganin haka na gamsu cewa ba kowa bane ya bamu kariya face ubangijinka saboda naga lokacin da kake ta karanta wadansu addu'oi a cikin ranka na neman tsari. Sa'adda haiman yazo nan a zancensa sai farin ciki ya kama yarima yazid yace tabbas nayi murna da Allah ya nufeka da fahimtar hakan,to ka sani cewa muddin muna cikin wannan kogon dutse babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da ya isa ya shigo har nan ya cutar damu,kai hatta dabbobi da kwari ma ba zasu iya zuwa kusa da mu ba. Albarkacin addu'ar dana karanta na tofa a bakin wannan kogo. Kafin yarima yazid ya gama rufe bakinsa kuwa saiga wani AYARI na kuraye kimanin su arba'in sun fito farautar abinda zasuci,kallo daya zaka yiwa kurayen ka gane cwa suna cikin tsananin yunwa domin sai zazzaro harsunansu suke suna lasar duwatsu da kasa kuma suna dalalar da yawu. Koda kurayen suka hango alamun mutane a cikin kogon da su yarima yazid ke ciki sai suka ruga da gudu domin su kawar da yunwar su suna kar ™Abbas Abdulkadir Hada Hada™ tar kasa da faratan kafafunsu tamkar sunci babu.Koda suka iso daf da bakin kofar kogon dutsen sai sukayi turjiya suka kasa shiga ciki suka kama koke koke sunaja da baya.Ba komai ne ya haddasa hakan ba face ji da sukayi

Chapter 10 of 15