Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jigata ainun amma taki hakura sai cigaba da fadan takeyi. Ana cikin wannan hali ne halittar ta shammaci Yazid ta jefa jelarta guda izuwa kan Nauwara ta kanannade ta ta dagata sama. Koda ganin haka sai jikin Yazid ya yi sanyi ya ja da baya. Koda ganin haka sai halittar ta bushe da mahaukaciyar dariya mai kama da rurin tsohon zaki sannan ta dubi Yazid ta bude baki a karo na farko tayi magana tace,yakai wannan shaidanin bil'adama kayi sani cewa yau shekarata arba'in da daya a cikin wannan kogin kankara ina gadin wannan daji na Hajarul Aswad babu wani mahaluki daya isa ya ratsa ta cikin kogin nan walau mutum ko aljan har ya iso nan karshen gabar batare dana hallaka shi ba. Komai yawan runduna kota mutane kota aljanu saina karkashe su na karar dasu sun zama gawawarwaki amma sai gashi ka tsalleke wannan kogi kuma na kasa kashe ka.Yanzu gashi na sami nasarar dankar abokiyar tafiyarka wacce tayi dogon suma sakamkon naushi daya danayi mata dazu,to ka sani cewa har yanzu tana raye ba mutuwa tayi ba,amma idan kana son ta cigaba da rayuwa saidai ka tsaya cak a inda kake na matso gareka na kashe ka batare da kayi yunkurin kare kanka ba. Da zarar kayi wani yunkuri na kare kanka ko cutar dani kuwa zan matse jikin abokiyar tafiyar taka na kakkarya duk kasusuwan jikinta. Koda jin wannan batu sai hankalin yarima Yazid ya dugunzuma ainun ya rasa abinda zaiyi take ya tuna amanar da yarima Zainur ya bashi akan Nauwara sannan kuma nan take yaji sonta ya sake kwarara a zuciyarsa fiye da ko yaushe,kawai saiya tsaya cak yace na yarda kizo ki kashe ni amma na rokeki bayan kin kashe ni ki kyale Nauwara kada ki taba lafiyarta Koda jin haka sai Halittar ta bushe da dariya tace aini burina kawai shine na kashe ka kuma na hana kowa tsalle wannan kogi saboda idanban kashe ka ba ka karya lagona kuma ka rusa tarihin jarumtakata da kwarjini,ina maiyi maka alkawari cewa lallai bayan na kashe ka zan sauke abokiyar tafiyarka kasa amma dole sai dai ta koma da baya ba zata wuce gaba don tunkarar kogon Hajarul Aswad ba. Koda jin haka sai yazid yace na amince da hakan,kawai saiya saki jikinsa ya fara kiran sunayen ALLAH a cikin zuciyarsa yana mai neman taimakon Allah. Ita kuwa halittar sai ta cigaba da durfafoshi tana kyakyala dariyar mugunta,ashe duk wannan abu dake faruwa tsakanin Yazid da wannan macijiyar Nauwara ta dade da farfadowa daga dogon suman da tayi amma saboda tana kanannade a cikin jelar halittar a sama babu abinda zata iyayi.Koda Nauwara taga yadda Yazid ya sallama rayuwarsa domin ceto tata sai taji ta kara kamuwa da tsananin sonsa fiye da ko yaushe kuma sai ta kura masa idanu tana mai zubar da hawaye saboda tasan cewa lallai wannan shine gani na karshe da takeyi masa.Nan dai halittar ta cigaba da kyalkyala dariyar farin ciki tana mai kara tunkarar Yazid.Koda ya rage saura baifi taku biyar ba a tsakanin Halittar da yarima Yazid sai halittar ta daka tsalle sama da nufin ta sokawa Yazid faratan hannayenta biyu a makoshinsa.kwatsam ba zato ba tsammani sai Yazid yaga halittar ta sandare a sama tamkar gunki ta fado kasa tim matacciya ko shurawa batayi ba sakamakon wata takobi data soketa a kunnenta na dama ta faso cikin kunnenta na hagu. Sa'adda jini ya kama tsiri daga cikin kunnen hagun. Koda Yazid yayi arba da wanda ke ruke da takobin sai ya jada baya cikin kaduwa da mamaki,ba wani bane ba ruke da takobin data tsire wannan halittar face Sarauniya Lazwara. Yazid ya dunkule hannyensa biyu yana mai nuna alamun yin fada da Lazwara wacce ita kuma fuskarta a cike take da annuri gami da murmushi a wanann lokaci ne Nauwara ta zaro jikinta daga cikin jelar matacciyar halittar tasha gaban Yazid wato ta shiga tsakaninsa da sarauniya Lazwara ta dubeshi.... Wash littafin da dadi yake dan napiku san karan tashi..mu hadu gobe WASIKAR JINI!!! Littafi Na Takwas (8) Part B. . TA SHIGA TSAKANINSA DA SARAUNIYA LAZWARA TA DUBESHI TACE WANNAN MAI MULKI KUMA ABOKIYA CE A GAREMU,ITA CE SARAUNIYA LAZWARA MAI MULKIN BIRNIN ARNAN DAJI BIRNIN DAKE MAKWABTAKA DA BIRNINMU. Koda jin wannan batu sai Yarima Yazid ya dan saki jikinsa yayiwa Lazwara dan guntun murmushi kawai sai ya dubi Nauwara yace maza ki zo mu koma can sansanin abokan tafiyarmu domin zasu kasance a cikin zulumi da fargabar rashin ganinmu. Koda jin wannan batu sai sarauniya Lazwara ta dubi Yazid a fusace tace haba malam kai wane irin mutum ne yaya na ceci rayuwarka data abokiyar tafiyarka daga hannun wannan azzalumar halitta amma ko gode mini vakayi ba zaka dauke gimbiya ku tafi ku barni. Koda jin wannan batu sai Yazid ya juyo ya dubi Lazwara cikin nutsuwa yace ai ba kece kika ceci rayuwata ba ubangijina ne ya cece ni domin lokacin danaga bani da wata dabara da zan iya kubutar da rayuwar Nauwara saina kama kiransa a cikin zuciyata ina mai neman taimakonsa shi kuma saiya amsa rokona ya turo baiwarsa wato ke kika ceci rayuwarmu gaba daya. Koda jin haka sai sarauniya Lazwara tace ta yaya ubangijinka zai turo ni na cece rayuwarka alhalin ni bashi nake bautawa ba? Yazid yayi murmushi yace ai dake da abinda kike bauwata da duk wata halitta dake cikin sammai da kassai ubangiji nane ya halicce su. Shine sarki Guda daya wanda bashi da abokin taraiya bai haifa ba kuma ba a haife shi ba,yana nan a ko ina kuma yana ji yana ganin komai da kowa fiye da yadda kusancin ruhi da gangar jiki yake,idan baki amince da duk abinda na gaya miki ba ki cigaba da binmu a cikin wannan tafiya da sannu zaki ga karfin ubangijina da idanunki kiyi imani dashi. Koda gama fadin hakan sai Yarima Yazid yaja gimbiya Nauwara suka nufi hanyar da zata mayar dasu can sansaninsu da gudu,ita kuwa sarauniya Lazwara sai ta tsaya tana tunani da wasu wasi akan abinda ya kamata tayi. Koda taga Yazid sunyi nisa sai itama ta falfala da gudu ta riske su suka cigaba da gudun tare. Tun kafin su karaso sansanin daga can nesa hankalinsu ya dugunzuma su ukun sakamakon hango wani irin hayakin wuta a sama yayi tsiri ba kyan gani. Koda hango wannan hayaki sai zukatun su Nauwara suka buga da karfi suka kara kaimin gudunsu tun akan hanya suka fara yin tuntube da gawarwakin jama'arsu. Aikuwa sai Nauwara da Yazid suka fara zubar da hawaye bisa ganin yadda aka yiwa jama'ar tasu KISAN GILLAH duk da sun san cewa shahada sukayi. Cikin dimauta Yazid da Nauwara suka kara karfin gudunsu Yazid na kwalawa Haiman da matarsa kira ita kuma Nauwara tana kwalawa dan uwanta Zainur kira amma sai sukaji shiru basu amsa ba. Al'amarin daya kara dugunzuma hankalinsu kenan,nanfa suka cigaba da ganin gawarwakin dakarunsu har suka iso sansanin nasu inda suka iske shi a kone duk tantunansu da komai nasu kuma ko ina gawarwaki ne da jini male male a kasa. Bama su Nauwara ba hatta sarauniya Lazwara bata san sa'adda idanunta suka ciko da kwalla ba ta fara zubar da hawayen tausayi sakamakon ganin irin kisan gillar da akayi yiwa jama'ar su Nauwara. Kusa kowace gawa saida akayi gunduwa gunduwa da ita. Saida suka dubo ko ina a sansanin amma basu ga gawar sarkin yaki ba data matarsa da kuma ta yarima Zainur. Al'amarin da yayi matukar kara dugunzuma hankalinsu kenan suka cigaba da kuka ba sassauci saida suka jima suna kukan sannan suka dawo cikin hayyacinsu.kawai sai Yazid ya mike tsaye a fusace ya dubi Nauwara a lokacin daya dauki takobi da garkuwarsa yace zo mu tafi can sansanin abokan gaba domin daukar fansa,na tabbata sun kashe Haiman,Zainur da matar Haiman. Caraf sai sarauniya Lazwara tace Haiman da matarsa da kuma Yarima Zainur basu mutu ba,su kadai ne suka tsira da rayuwarsu a wannan harin sumame da abokan gaba suka kawo musu,amma sun kama su sun tafi dasu izuwa can sansanin nasu wajen sarki Marwatu da Waziri Ridwan domin a raye suke bukatarsu. Koda jin haka sai Yazid da Nauwara suka sake fusata Nauwara ta dubi Yazid tace zo muyi sauri muje can sansanin abokan gaba ayita ta kare komu ko su. Dajin wannan batu sai sarauniya Lazwara ta bushe da dariya sannan ta murtuke fuskarta tace ta yaya kike zaton cewa ku biyu rak zaku iya yakar sama da mutum dubu dari uku da doriya? Ina mai tabbatar miki da cewa idan kuka kai kanku sansaninsu waziri Ridwan tamkar sun sayar da rayukanku ne wai shin ma kun fito ne domin ku dauki fansa ko kuwa domin kuje kogon Hajarul Aswad ku dauko wasikar jini ku koneta domin ku ceto rayuwar al'ummar wannan nahiya? Ku sani cewa su Waziri Ridwan ba zasu kashe Haiman da Zainur ba saboda suna son suyi garkuwa ne dasu domin ku fanshe su da wannan taswira ta zuwa kogon Hajarul Aswad. Idan kuka kuskura kuka basu wannan taswirar to ba zasu baku su yarima Zainur ba zasu kashe su ne kuma su kashe ku,sannan suje su dauko wasikar jni su cigaba da yin mulkin zalunci a wannan nahiya. Lokacin da sarauniya Lazwara tazo nan a zancensa sai jikin Yazid dana Nauwara yayi sanyi sukayi shiru suna tunani. Daga can sai Yazid ya dago kai ya dubeta yace to wai ke menene dalilin da yasa kika biyo mu nan har kika taimake mu? Shin kema so kike ki yaudare mu ki sace wannan taswirar daga hannunmu domin ki mallaki wasikar jini ko kuwa kina da wata manufa ne daban wacce bamu sani ba? Koda jin wannan tambaya sai sarauniya Lazwara taja dogon numfashi sannan ta zauna a kasa dirshan ta dubi Yazid cikin nutsuwa tace sama da shekaru hamsin baya tun kafin a haifeni jama'ata basu taba shiga harkokin wata kasa ba a wannan nahiya. Muna zaman lafiya da kowane sarki amma bincike ya tabbatar mana da cewa muddin waziri Ridwan ko sarki *Abbas Abdulkadir Hada Hada* Marwatu dayansu ya mallaki wasikar jini saiya yake mu ya kawar damu daga doron kasa yadda har abada ba za'a sake tunawa damu ba. Kuma ashe ya zama dole na fito na kare birnina da jama'ata. Tabbas ni daku akan aiki guda muke,kafin Lazwara ta gama rufe bakinta tuni Yazid ya tari numfashinta yana mai cewa na yarda muna kan aiki guda amma ba tafarki iri guda ba,mu muna kan tafarkin addinin musulunci ne ke kuwa kina kan tafarkin tsafi.Yanzu wace shawara zaki iya bamu dangane da wannan al'amari kuma menene matsayinki bayan mun sami nasarar dauko wasikar jini mun koneta,shin zaki karbi addinmu ne ko kuwa zaki koma kasarko ne ku cigaba da addininku na tsafi ke da jama'arki? Sa'adda Lazwara taji wadannan tambayoyi guda biyu sai tayi gyaran murya tace sai yanzu kayi mini tambaya mai daraja. Da farko dai inaso ku sani cewa babu wani mugun nufi a cikin zuciyata ko son kai a kan wasikar jini,fata na kawai shine akawar da zalunci a wannan nahiya a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali.Abu na biyu kuma shine zan zuba ido naga iya karfin abin bautarku daga nan zuwa isarmu kogon Hajarul Aswad idan har naga kun iya dauko wasikar jini da taimakonsa lallai nima zan karfi addinin naku. Ina mai tabbatar muku da cewa nan da ko yaushe zamu iya gani manzo daga sansanin abokan gaba zaizo ne da sakon cewa idan kuna son rayuwar Haiman da matarsa da Zainur to kuje kukai wasikar jini.Koda jin wannan batu sai hankalin Yazid dana Nauwara ya kara dugunzuma ainu, Nauwara ta dubi Lazwara tace wace amsa ya kamata mu basu ko kuwa zamu bi manzon nasu ne mukai Taswirar wasikar jinin. Sarauniya Lazwara ta girgiza kai tace a'a ba zamubi manzon ba sako zamu bashi kamar yadda suka aiko.Abinda zaku gayawa manzon shine ya koma ya gayawa iyayen gidansa cewa ba zaku bayar da taswirar ba sai acan tsakiyar dajin da kogon Hajarul Aswad yake. Wannan wata babbar hikima ce nayi muku sai a nan gaba zaku fahimci hakan kuma ku gargade su a kan cewa idan suka kuskura suka taba lafiyarsu Haiman to a bakacin Taswirar. Har Yarima Yazid ya bude baki zai tambayi Sarauniya Lazwara ko wace irin hikima take nufi da cewar sai a tsakiya dajin Hajarul Aswad zasu bayar da wannan taswirar sai kawai suka jiyo sukuwar doki an durfafo wannan konan nan sansanin nasu,suna dago da kawunansu su ukun sukga ashe kuwa maganar Lazwara ce ta tabbata wato manzo ne daga sansanin abokan gaba. Jim kadan sai ga manzon ya iso daf dasu yana mai jan linzamin dokinsa,take dokin yayi turjiya ya risina a gaban gimbiya Nauwara ya kwashi gaisuwa.Tana hada idanu da manzon taga ashe babban hadimin waziri Ridwan ne wanda ake kira da suna Ubaiyu bin Marwas.Ubaiyu ya dago kai ya dubi Nauwara yace ya shugabata mai girma Waziri Ridwan yace na shaida muku cewa sarkin yaki Haiman da matarsa da kuma Yarima Zainur na hannunsu a can sansanin sarki Marwatu idan har kuna son ku fanshi rayuwarsu to kuje ku kai musu taswirar zuwa kogon Hajarul Aswad in ba haka ba kuwa zasu kure muku gudu su kashe ku kamar yadda suka kashe sauran jama'arku. Koda Ubaiyu yazo nan a jawabinsa sai gimbiya Nauwara ta kyalkyale da dariya. Al'amarin daya baiwa Ubaiyu mamaki kenan yace haba gimbiya yaya keda kike cikin wannan hali zakiyi dariya,shin bakya kishin dan uwanki ne bakya son ya tsira da rayuwarsa? Nauwara tayi murmushi tace ai idan ma kuka kashe dan uwana da sarkin yaki farin ciki zanyi saboda sun sami shahada kuma zasu sami babban rabo da sakamako na gidan Aljanna. Ka koma ka sanar da iyayen gidanka cewa ba zamu basu wannan taswirar ba sai a tsakiyar dajin Hajarul Aswad. Koda jin wannan batu sai idanun Ubaiyu suka zazzaro yace haba ranki ya dade kiyi tunani dai,caraf sai sarauniya Lazwara ta tari nunfashin Ubaiyu tana mai daka masa tsawa gami da zare takobinta tace maza kabar wajen nan ko nasa takobina na sare kanka. Kawai kaje ka isar da sakon da aka baka. Koda jin haka sai jikin Ubaiyu ya kama kyarma cikin hanzari ya kama dokinsa ya haye ya juya da baya ya zabureshi da gudu su kuwa sai suka bishi da kallo har saida ya bace musu da gani. Faruwar hakan keda wuya sai sarauniya Lazwara ta dubi Yazid da Nauwara tace ku tashi mu ruga da gudu izuwa cikin dajin nan muyi sauri mu isa can tsakiyar dajin Hajarul Aswad kafin abokan gabar nan su zo su riske mu domin Ubaiyu na sanar dasu sakon ki zasu biyo bayanmu. Ba tare da wata gardama ba kuwa sai Nauwara da Yazid suka mike tsaye suka falfala da gudu,itama sarauniya Lazwara saita bisu a gujen,nan da nan tazo ta tsere musu ta basu tazara mai yawan gaske domin wani irin gudu takeyi na ban al'ajabi har tashi takeyi sama kamar tsuntsuwa kai da gani kasan cewa aikin sihirin tsafi ne. Koda ganin haka sai shima Yarima Yazid ya kama yin wata addu'a ta musamman ai kuwa nan da nan karfin gudunsa ya karu shida na nauwara.Nan da nan suka zo suka wuce sarauniya Lazwara kafin ta ankara sun bata rata mai yawan gaske. Nanfa Lazwara ta kara zage damtse iyakar iyawarta duk dalasimanta na tsafi babu wanda bata ambata ba domin ta wuce su amma sai ta kasa. Al'amarin dayayi matukar girgiza ta kenan yasa ta firgita da al'amarin ma'abota addinin musulunci kenan.Saida suka shafe sa'a uku da rabi suna wannan gudu suna ta gifta bishiyoyi har ta cikin koramai suke bi suna taka ruwa tamkar akan kasa suke tafiya. Wannan shine abinda ya faru ga su Yarima Yazid bayan su sarki Marwatu sun kaiwa sansaninsu harin bazato sun kashe gaba dayan dakarun nasu. * A can kuma sansanin su sarki Marwatu kuwa tun daga lokacin da suka ci yaki a sansanin su sa yarima Zainur sai suka kamo sarkin yaki Haiman da matarsa da kuma Yarima Zainur suka jefasu cikin wani keji a ka dora *Abbas Abdulkadir Hada Hada* kejin akan keken shanu aka rinka wulakanta su akan hanya ana wahalar dasu.Har aka iso sansanin ko ruwa ba'a basu sun sha ba kuma ana isa aka fito dasu daga cikin kejin aka daure su a cikin rana ba'a kwance su ba saida rana ta fadi aka kwashe su kamar tsumma saboda tsananin jigata ta yunwa da kishirwa bisa wannan dalili suka fita daga haiyacinsu. Bayan an mayar dasu cikin keji an kulle ne aka kawo musu ruwa makurwa uku uku kadai aka basu gami da abinci loma uku uku kadai aka basu. An basu wannan abinci da ruwa ne don kawai kada su mutu,lokacin da suka danci wannan abinci ne suka dawo cikin hayyacinsu sai matar Haiman ta dubeshi a lokacin da hawaye ya zubo mata tace,yakai mijina yanzu shike nan mu tamu ta kare kenan an kashe gaba dayan dakarunmu daga mu mu ukun nan sai Yazid da Nauwara ne kadai muka rage muma din kuma ga dukkan alamu mutuwar zamuyi. Koda jin wannan batu sai Haiman ya kamo matarsa ya rungumeta a kirjinsa yace yake matata ina so ki sani cewa wuya bata kisa kuma ko mutuwa mukayi akan wannan tafarki bamu da wata asara domin shahada ce mukayi. Ni ina ji a jikina wadannan makiyan Allah ba zasu taba samun nasarar mallakar wannan wasikar jini ba. Caraf sai Yarima Zainur ya tari numfashin Haiman yace tabbas abinda ka fadi gaskiya ne yakai Abbana kuma zamu cigaba da addu'ar Allah ya kare mu daga sharrin su waziri Ridwan kuma ya bamu sa'a akansu mu kawar dasu da zalunci mu kafa addinin Allah a wannan nahiya. Su Haiman na cikin wannan zance ne waziri Ridwan da sarki Marwatu suka taho garesu suna kyalkyala musu dariyar mugunta,da isowarsu daf da bakin kejin sai waziri Ridwan ya zura hannunsa cikin kejin ya cafi makoshin Zainur yace kai yaro kayi asara,a baya sarkin yaki da sarki Aiyuba sun gagareni kuma sun jima suna kunsa mini bakin ciki,sun kare dukkan hanyoyin cigaba rayuwata kuma lokaci yayi da zan dauki fansa akanka. Tunda shi tasa ta kare gashi can kwance akan gangar mutuwa,a yau dinnan abokinka Yazid da gimbiya Nauwara zasu kawo mana Taswirar zuwa kogon Hajarul Aswad,mun yaudare su da cewa zamu basu ku a maimakon taswirar suna shigowa cikin wannan tanti zamuyi musu kofar rago mu hallaka su mu dauke taswirar sannan kuma muyi muku kisan gilla. Tabbas na tabbata da cewa ba zasu iya tafiya su barku ba dole ne suzo suyi kokarin ceton rayuwarku.Koda gama fadin haka sai Ridwan ya saki makoshin Zainur ya dubi sarki Marwatu suka bushe da dariyar mugunta tare suna cikin kyalkyala dariyar ne sarkin yaki Haiman ya tari numfashinsu yana mai daka musu tsawa yace,ku tsofaffun azzalumai kuyi sani cewa rana da yawa ta barawo ce rana daya jal ta mai kaya. Tabbas kun dade kuna sheka ayarku a doron kasa kuna zalunci kuna tara dukiya ta gurbatacciyar hanya,babu mai iya taka muku birki sai Mahaifin Gimbiya Nauwara.Yau sarki ya fadi amma kuyi tunani da hankalinku da kwakwalwarku an sami jarumi ma'abocin addinin musulunci wanda shine zai kawo karshenku. Ina mai tabbatar muku da cewa sakon da manzonku zai dawo dashi saiya girgiza ku,kowannenku sai hantar cikinsa ta kada. Kafin sarkin yaki Haiman ya gama rufe bakinsa kuwa sai sukaji sukuwar doki an nufo sansanin,cikin hanzari waziri Ridwan da sarki Marwatu suka waiga baya sai sukaga ashe manzo Ubaiyu ne ya dawo. A guje Ubaiyu ya ratso cikin sansanin da doki,da isowarsa sai yaja tunga a gaban su sarki Marwatu ya sauko da sauri daga kan dokin ya zube kasa gabansu sannan ya dago kai ya zaiyane sakon dasu yarima Yazid suka bashi cewar ba zasu zo wannan sansani ba kuma ba zasu bayar da taswirar ba face a tsakiyar dajin Hajarul Aswad. WASIKAR JINI!!! Littafi Na Takwas (8) Part C. . FACE A TSAKIYAR DAJIN HAJARUL ASWAD. KODA JIN WANNAN BATU SAI RAN SARKI MARWATU DANA WAZIRI RIDWAN YA BACI,ZUCIYOYINSU SUKA KAMA TAFARFASA KAMAR ZASU KONE,CIKIN FISHI SARKI MARWATU YA DUBI RIDWAN YANA MAI ZARE TAKOBINSA YACE,tunda dai sun hanamu taswirar zuwa dajin hajarul Aswad banga amfanin fursunonin da muke tsare dasu ba kawai mu kashe su. Waziri Ridwan yayi sauri yasha gaban sarki Marwatu ya dubeshi cikin matukar damuwa yace a'a idan muka kashe su yarima Zainur yanzu har abada ba zamu sami wannan taswirar ba bare mu mallaki wasikar jini zo kaji wata magana. Nan take Ridwan ya kama hannun sarki Marwatu ya jashi izuwa can gefe daya suka tattauna sukayi kuskus na tsawon yan dakiku suna gama tattaunawa ne suka tara gaba dayan mayakansu suka basu umarnin a fara shirin cigaba da tafiya kuma a shirya makaman yaki. Nan take kuwa aka shiga debo takubba,mashi da kibiyoyi aka shiga wasa su ana rarrabawa mayaka kai kace YAKIN DUNIYA za'a tafi. Koda Zainur ya ga yadda dubunnan daruruwan dakaru keta kai kawo a cikin sansanin suna ta shirye shiryen yaki sai nan take idanunsa suka ciko da kwallah har hawaye ya zubo masa. Al'amarin daya baiwa Haiman da matarsa mamaki kenan Haiman ya dubi Zainur cikin alamun kaduwa yace yakai dana ina dalilin zubar da wannan hawaye naka? Zainur yasa hannu ya share hawayensa sannan ya dubi Haiman cikin nutsuwa yace yakai abbana kaga wadannan dubunnan daruruwan dakarun da yawansu magidanta ne,suna da mata,'ya'ya da yan uwa kuma dukkaninsu jama'ar birnin mu ne amma dayansu ba zai tsira da rayuwarsa ba duk mutuwa zasuyi a cikin dajin hajarul Aswad. Kaga kenan matayensu zasu zama zawarawa,yayansu kuma zasu zama marayu,basu da ikon gudun shigowa nan dajin saboda tsoron waziri ridwan,haka suma dakarun yakin da sarki Marwatu ya taho da su daga kasarsa zasu mutu a cikin jahilci batare da sun amfani addinin gaskiya ba sun dandani dadinsa da kuma rahamar dake cikinsa. Koda Zainur yazo nan a zancensa sai jikin Haiman dana matarsa yayi sanyi suka kurawa dakarun yakin idanu suna masu jin tausayinsu.Kafin cikar sa'a daya an gama shiri tsaf an kwashe komai a sansanin an zaburi dawakai da gudu an durfafi hanyar da zata kaisu izuwa dajin hajarul aswad. Idan mutum yaga wannan falfala azababben gudu kuma yaga yawansu dole ya firgita yayi zaton cewa karshen duniya ne yazo. * A can cikin dajin hajarul aswad kuwa lokacin da sarauniya Lazwara,Yarima Yazid da gimbiya Nauwara suka falfala da azababben gudu izuwa cikin dajin Hajarul Aswad suka shafe sa'o'i suna gudun batare da sun gaji ba sai suka iso wani katon fili wanda ke cike da wata irin ciyawa mai taushi tamkar kilishi aka shimfida gaba daya a wannan gaili. A zagaye yake da wadansu irin dogayen bishiyoyi tamkar babu hanyar da mutum zai iya bi ya wuce. Da isowarsu wannan wuri sai sarauniya Lazwara ta kwalawa Yazid kira suka tsaya da Nauwara.Lazwara ta karaso garesu tana haki data kalli Yazid da Nauwara taga ko haki basayi kuma babu alamar gajiya a tare dasu duk da wannan tsananin gudu da suka sha sai ta kamu da tsananin mamaki amma saita basar ta dubi Yazid tace,nanne tsakiyar dajin Hajarul Aswad, anan ya kamata mu tsaya mu tunkari su sarki Marwatu ayita ta kare,idan mun sami nasarar kashe su mu karasa kogon hajarul aswad mu dauko wasikar jini idan kuma sune suka sami nasarar kashe mu sune zasu je su dauko wasikar jini su mallaketa su cigaba da yin mulkinsu na zalunci,ina mai tabbatar muku da cewa gaba dayan masifun dake cikin wannan dajin anan wurin suke kuma kowacce masifa daya ta ninka ta waccan halittar dana kashe a cikin kogin kankara sau uku babu abinda zai kwace mu anan face tsananin sa'a da kuma iya yakinmu da juriyarmu amma badai karfin sihiri ba. Caraf sai yarima Yazid ya tari numfashin sarauniya Lazwara yace ni dana san cewar ubangijina zai bamu kariya ke kuma sai mu gani idan tsafinki zai kareki idan kuma baki da tabbacin hakan to ki karbi addininmu yanzu take nayi miki alkawarin babu abinda zai sameki,koda jin wannan batu sai Sarauniya Lazwara ta kyakyale da dariya tace ai inda tun farko ban yarda da kaina ba bazan yarda na biyo bayanku ba har na iso nan.Lallai inda babu kasa anan ake gardamar kokawa,nidai burina shine na rayu har izuwa lokacin da za'a zo dasu yarima Zainur nan kuma naga wadanda zasu sami nasarar dauko wasikar jini tsakanin su sarki marwatu da mu. Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Nauwara da Yazid saboda basu san dalilin da yasa sarauniya Lazwara take son taga isowar Yarima Zainur wannan wuri ba. Har Nauwara ta bude baki zata tambayeta dalilin sai kawai sukaji kasa ta kama girgiza,kafin dayansu yayi wani yunkuri saiga wadansu irin samudawan dodanni suna faso kasar suna fitowa su dayawa ba adadi suka yiwa su yarima Yazid kawanya sai gashi su Yazid sun zama yan mini mini tamkar an ajiye yan tsaki uku a tsakiyar dubunnan kaji. Sudai wadannan dodanni suna da matukar tsawo gami da kaurin jiki kuma fuskokinsu nada matukar muni da ban tsoro idanuwansu jajaye ne tamkar dan buda aka gasa a cikin wuta.Jikinsu gaba daya a murde yake cike da kwanji da jijiyoyi tamkar duwatsu aka cure gaba dayan wadannan dodanni suna ruke da wani irin gabjejen sungumin itace mai dauke da wani irin tsini cako cako mai yawa a samansa.Duk da tsananin jarumtaka irinta yarima Yazid saida ya firgita bisa ganin wadannan dodanni da kuma yawansu amma daya tuna cewa yana tafarkin daukaka kalmar Allah ne sai dukkan tsoro ya kau daga cikin zuciyarsa. Kawai saiya zare takobinsa ya gyara tsayuwarsa yana jira yaga dodon dazai fara kawo masa +Abbas Abdulkadir Hada Hada* Hari.Itama Sarauniya Lazwara saita zare takobinta ta gyara tsayuwarsa.Gimbiya Nauwara kuwa kasa zare tata takobin tayi saboda tsoro ta koma bayan yarima Yazid ta tsaya jikinta na karkarwa. Koda Yazid yaga yadda Nauwara ta tsorata ainun da ganin wadannan dodanni sai yayi mata rada a kunne yace ki tsuguna kasa kuma kada ki kuskura ki motsa daga nan wajen daidai da taku goma. Gama fadin hakan keda wuya sai dodannin suka afkawa Yazid da sarauniya Lazwara aka ruguntsume da azababben yaki,ai kuwa ana fara wannan yaki ne Yazid da Lazwara suka raina kansu kuma suka san cewa sun gamu da gamonsu. Sudai wadannan dodannin basa jin sara da suka a jikinsu domin duk sa'adda takubbansu Yazid da Lazwara ya hadu da jikinsu saidai kaji wata irin kara na tashi tamkar karfe da karfe ne suka hadu kuma tarwatsin wuta ne ke tashi. Haka kuma basa jin naushi da bugu domin da zarar su Yazid sun naushe su hannunsu ne sagewa suji kamar dutse suka nausa. Bugu da kari dodannin suna da matukar zafin nama domin kafin su Yazid su kai musu hari guda su sun kai musu uku nan da nan suka kuntata Yazid da Lazwara suka fara galabaitar dasu,wani abin mamaki shine babu wani dodo daya kaiwa Nauwara hari a inda take tsugune amma jikinta sai karkarwa yake tana kallon gumurzun da akeyi cikin tsananin tsoro da tashin hankali. Ashe Yazid ya karanta wata addu'a ta musamman ya tofa adaidai wurin da Nauwara ta tsuguna. Ana cikin wannan mugun artabu ne wani dodo ya shammaci sarauniya Lazwara ya gabza mata wani wawan naushi a fuska,saboda karfin naushin saida tayi katantanwa a tsaye sau uku a lokacin da gudan jini ya furzo daga bakinta ta langwabe zata fadi kasa sumammiya. Koda ganin haka sai yarima Yazid ya dimauce bai san sa'adda ya kwala kabbara da karfi ba ya cafo Lazwara da hannu daya ya goyata a bayansa kuma ya afkawa dodannin da mugun sara da suka cikin bakin zafin nama na gaban kwatance a lokacin da yaji wani irin gagarumi karfi ya shige shi,ai kuwa sai gashi takobinsa na daddatsa dodanni duk tsananin yawan dodanni sai ya zamana banza domin an rasa wanda zai iya koda lakutar jikin Yazid kuma sai kutsawa ta cikinsu yake yana bazar dasu,sassan jikinsu ya rinka shawagi a sama yana zubowa kasa jini jikinsu ya rinka tsartuwa da fantsama. Wohoho.. idan kaji ana ki gudu to sa gudu ne bai zo ba. Koda sukaga irin mummunar barnar da yazid keyi musu kuma suka tabbatar da cewa

Chapter 14 of 15