Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kamar zasu babbake saboda wani irin azababben hucin zafi dake fesowa daga cikin kogon dutsen. Ba shiri kurayen suka juya da baya da gudu suka nausa wani bangaren daban na dajin. Adaidai wannan lokaci ne su haiman sukayi doguwar ajiyar numfashi suka dawo cikin hayyacinsu. A sannan ne haiman ya dubi yarima yazid yace tabbas yanzu nayi imani da cewa babu wani ubangiji wanda ya cancanci a bauta masa face ubangijin musulunci don haka a shirye nake yanzu na karbi wannan addinin mai daraja. Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube yarima yazid har ya budi baki zaice wani abu kawai sai yaga yarima zainur,gimbiya nauwara, da dukkan hadiman sarkin yaki sunzo gabansa sun durkusa sun dubeshi cikin hadin baki suna masu cewa muma munyi imani da wannan addini naka. Take Yarima yazid yaji hawaye ya zubo masa saboda farin ciki,ba tare da bata lokaci ba ya biya musu kalmar shahada suka maimaita amma sai yazid ya lura da wani hadimi gudu daya wanda ya tsuke bakinsa yaki biya kalmar shahadar.Yazid yayi shiru bai tonawa hadimin asiri ba, amma sai ya aiyana a ransa cewa lallai zaisa ido a kansa tunda bai sani ba ko ya biya kalmar shahadar ne a cikin zuciyarsa bai biyata a fili ba tunda shi imani a zuci yake ba a baki ba. . Kaico!Allah ka shiga tsakaninmu da munafiki domin kuwa sharrin munafuki yafi na barawo takaici da bakin ciki domin shi munafuki tamkar haske yake yana jikinka yana morarka amma kuma yana yi maka babbar illah. Ashe wannan munafukin hadimi yaron waziri Ridwan ne kuma yafi shekaru goma sha biyar yana bauta a gidan sarkin yaki kuma da gaiya waziri ridwan yasa aka siyarwa da haiman shi a matsayin maraya saboda yasan cewa haiman baya ajiye bawan da ba maraya ba a gidansa,kuma tun wannan bawa yana yaro yake zuwa gidan waziri ridwan a sirrance yana kai sirrin gidan haiman bisa duk abubuwan da yake shiryawa. WASIKAR JINI Littafi Na Shida (6) Part C . Yana kai sirrin Haiman bisa duk abubuwan da yake shiryawa. A tsawon wadannan shekaru sarkin yaki haiman yana matukar mamakin yadda waziri yake sanin abubuwa nasa dayawa na sirri,amma sai yayi zaton cewa da karfin sihirinsa na tsafi ne yake sani bai san cewa yana da munafuki a jikinsa ba. Lokacin da wannan munafikin bawa ya fito daga cikin kogon dutse sai ya falfala da gudu ya tunkari hanyar da zata kaishi cikin gari,yana cikin gudunne yayi kicibus da wadannan dakarun sumame na sojan haya sunyi masa kawanya ba tare da fargabar komai ba saiya dubesu yayi musu wata inkiya. Koda ganin haka sai suka sauke makaman dake hannunsu kasa. Shugaban su ya dubi bawan yace meye labari? Waishin a ina kuka buya muka nemeku sama da kasa a cikin wannan dajin muka rasa. Koda jin wannan tambaya sai bawan yace ai wani takadirin bako ne ya bamu kariya da irin sihirinsa muna can baya cikin wani kogon dutse kuzo muje na kaiku wajen ku shiga ku hallaka su. Nan take bawan ya juya da baya da gudu su kuwa dakarun sumamen suka rufa masa baya cikin murna da mugun nufi. Koda bawan da dakarun sumamen suka iso bakin wannan kogon dutse sai suka yi turjiyar dole bisa jin wannan hucin zafi mai tsananin gaske. Hatta shi kansa bawan wanda dazun nan ya fito daga cikin kogon sai ya kasa komawa. Al'amarin dayayi matukar baiwa dakarun sumamen mamaki kenan suka rasa dabarar da zasuyi su shiga cikin kogon dutsen. Koda ganin haka sai shugaban dakarun sumamen ya bada izini aka dawo baya kadan aka tsaya akayi cirko cirko. A sannan ne shugaban dakarun ya dubi sauran yaransa yace mu tsaya a nan harsu gaji da buyan su fito ai duk tsiyadai ba zasuyi ta zama a ciki ba har abada. Idan yunwa bata fito dasu ba kishirwa zata fito dasu. Haka dai dakarun sumamen suka zuba ido akan kofar kogon dutsen suna rike da makamansu kawai jira suke suga wani ya fito daga cikin kogon dutsen su rafkeshi amma har gari ya waye babu wanda ya fito,asalima su yarima yazid basu san abindake faruwa ba a kofar kogon dutsen,domin barcinsu suke ta sharawa tamkar suna cikin ainihin gidajensu na kwana. Saida asuba tayi yarima yazid ya tashi kowa domin ayi alwala ayi sallah sannan suka hango rundunar dakarun sumamen acan bakin kofar kogon dutsen,nanfa hankalin kowa ya dugunzuma banda na yarima yazid. Koda yazid yaga haka saiya dubesu haiman a fusace yace ashe imaninku mai rauni ne ban sani ba,shin kun mantane da cewa tun jiya Allah ya nuna muku ikonsa ya hana kuraye ma'abota jin yunwa shigowa cikin wannan kogon dutse ya kareku daga sharrinsu? Koda jin wannan batu sai jikin kowa yayi sanyi suka kama yin istigfari,yarima yazid yayi gyaran murya sannan yace yanzu zamuyi alwala mu gabatar da sallah sannan mu roki Allah akan ya bamu sa'a akan wadannan abokan gaba kuma ya karemu daga sharrinsu,da izinin Allah zakuga abin al'ajabi. Koda gama fadin hakan sai kowa ya kama yin alwala sannan yarima yazid yawuce gaba yayi jasu,bayan an idar da sallah sai akayi addua'a kamar yadda yazid ya fada. Ana gama shafa adduar sai kawai akaga sarkin yaki haiman ya mike tsaye zumbur kamar bai taba ciwo ba ya zare takobinsa yana mai cewa duk wanda yayi imani da Allah ya biyoni mu afkawa wadannan abokan gaba. Nan take yarima yazid,zainur gimbiya nauwara da sauran gaba dayan hadiman haiman ma suka zare takubbansu suka kwala kabbara suka ruga waje da gudu, aikuwa suna haduwa da dakarun sumamen sai aka ruguntsume da azababben yaki mai tsananin ban tsoro da ban al'ajabi domin nan take su yarima yazid suka zamewa dakarun sumamen alakakai sukayi ta ragargazarsu. Duk inda suka sa gabansu saidai kaga mazaje na zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona cikin abinda bai wuce rabin sa'a ba su yazid suka kashe kaso biyu a cikin kaso ukun dakarun. Koda dakarun sumamen suka lura da irin mummunar barnar da akayi musu sai tsurarun suka cika wandonsu da iska suka ruga izuwa cikin daji a dimauce domin su tsira da rayuwarsu. Nan take su yarima zainur sukayi kabbara suka kuma yi godiya ga Allah bisa wannan gagarumar nasara daya basu. A cikin wannan kogon dutse su yarima yazid suka kara yada zango har wani daren yayi da niyar cewa gobe da sassafe zasuyi shiri su cigaba da tafiya don riskar dajin hajrul Aswad yake inda wasikar jini take. * Al'amarin waziri Ridwan tunda ya tura manzo izuwa ga wadannan dakarun nasa na sumame dake cikin daji sai ya zuba idanu domin yaga dawowar manzon yazo masa da labari mai dadi amma sai yaji shiru kamar maye yaci shirwa. Al'amarin daya dugunzuma hankalinsa kenan ya kasa zama ko tsayuwa bis wannan dalili ne ya kama dokinsa a cikin daren yahau ya fice daga cikin birnin shi kadai ya tasamma cikin daji.Koda yazo wannan daji na karshe wanda dagashi sai birnin nasu sai kawai ya hango sansanin dakarun yaki daga can nesa kada. Al'amarin dayayi matukar bashi mamaki kenan domin shi kadai a saninsa babu wata kasa a nahiyar wacce ta isa ta kawo musu harin bazato,nan take zuciyar waziri ridwan ta baci kuma zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone don haka saiya tunkari wannan sansani na mayaka batare da shakkar komai ba. Ai kuwa yana matsawa kusa dasu sai dubunnan dakaru suka taso masa akayi masa kawanya daga masu mashi sai masu takubba.A sannan ne waziri ridwan ya hango tutar birnin sarki marwatu a cikin sansanin. Koda ganin tutar saiya kyalkyale da dariyar farin ciki ya kwalawa sarki marwatu kira yace yakai abokina sarki marwatu maza ka fito ka taryi abokinka ridwan. Sarki marwatu na cikin tantinsa a kwance yana barci yaji kamar a mafarki ana kiransa. Aikuwa saiya farka a razane koda kunnuwansa suka jiyo sautin muryar ™Abbas Abdulkadir Hada Hada™ waziri ridwan saiya mike zumbur ya ruga waje da gudu,ridwan na hango marwatu saiya sauko kasa daga kan dokinsa shima ya ruga gareshi suka rungume juna cikin tsananin farin ciki. Nan take sarki Marwatu ya kama hannun ridwan ya jashi izuwa cikin tantinsa aka kawo musu giya da nama suka fara ci,a sannan ne waziri ridwan ya dubi sarki marwatu a cikin wani irin kallo na rashin yarda yace shin har yanzu kana kan burinka ne nason ganin ka mallake kasata ko kuwa so kake kawai ka rama wulakancin da dan uwana yayi maka? Koda jin wannan tambaya sai sarki marwatu ya bushe da dariya sannan yace ai labari na samu cewa zaki ya kwanta shi yasa na gaggauta kawo ziyara domin na debi rabona kafin sauran dabbobin daji su dasa masa wawaso. Dajin wannan batu sai waziri ridqwan ya sake bushewa da dariya a karo nabiyu sannan ya turbune fuskarsa yace dubeshi cikin tsananin fushi yace yakai abokina ni dakai KAR TA SAN KAR ne,na sani cewa baka yafiya amma duk da haka nasan kuma ka dade da burin ganin ka mallaki birnina.To ka sani cewa ko dan uwana ya mutu yau babu wanda ya isa ya hau kan karagar mulkinsa face wanda ya mallaki wasikar jini ya karanceta ka sani cewa a halin yanzu makiyana sun fito domin zuwa kogon hajrul aswad inda wasikar jini take. Nayi iya bincikena na kasa gane inda wannan kogon yake kuma taswirar zuwa wajen tana hannun sarkin yaki haiman. Inason ka taimaka mini mu bazama farautar sarkin yaki a cikin dajin nan domin mu kamashi mu kashe kuma mu dauki taswirar,nayi maka alkawarin idan muka sami wannan nasara zamu raba wannan kasa tawa biyu ka dauki kaso daya. Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube sarki marwatu ya rumgume waziri ridwan suka kama kyalkyala dariyar mugunta da murna suka ci gaba da kora ruwan giya suna ciskar naman kazan dake gabansu. * A can kuma kogon dutse kuwa da dare yayi sai su gimbiya nauwara suka kasa barci saboda fargabar gagarumar tafiyar dake gabansu da kuma sanin hadarin dake cikinta.Koda Yarima Yazid ya fahimci halin da suke ciki saiya dubesu yace yaku yan uwana ku kwantar da hankalinku ku sani cewa ba'a zama wani a banza dole sai an sha wuya. Inda kunsan labarin sarki Uzaima da Sarauniya Aryala da ko kadan baku damu kanku ba. Koda jin haka sai nauwara ta dubeshi tace wacece kuma sarauniya Aryala? Yarima yazid yace ga kadan daga cikin labarinta. °°°°°°A.A Hada Hada°°°°°° SARKI UZAIMA na zaune bisa wata kujera ta alfarma a tsakiyar turakarsa ta barci ya caba ado saiga shugaban dakarunsa ya shigo tare da sarauniya Aryala,koda ganinsu sai sarki Uzaima ya mike cikin tsananin farinciki ya taho garesu yana mai yiwa Aryala barka da zuwa kuma ya bude hannayensa da nufin ya rungumeta.Kawai sai Aryala ta daga kotar takobinta guda ta tokare kirjinsa da ita tace babu wani da' namiji daya taba rungumata face mahaifina, kana son karya wannan alkadari nawa ne? Koda jin wannan batu sai sarki Uzaima yayi murmushi sannan ya juyawa Aryala baya ya nufi inda wani teburi yake mai dauke da tambula na ruwan inibi ya fara zuba ruwan inibin a cikin kofuna biyu yana mai cewa haba tauraruwar taurari shin kin manta ne cewa kece kika fara karya alkadarina na jarumtaka a duniya har kika kaini kasa? Menene idan na rungumeki a matsayin matar dazan aura? Koda jin wannan batu sai sarauniya Aryala ta bushe da dariya tace hakika wannan mafarki naka yana da kamar wuya ko kuma ince yayi daidai da tatsuniyar yara mara kan gado. Bincike ya nuna cewa har nabar duniya babu wani 'da namiji dazai zama mijina saboda me kake son wahalar da kanka a banza? Sarki Uzaima yayi dan guntun murmushi a lokacin daya juyo ya taho gareta rike da kofuna biyu na inibin na gilashi cike kowanne da ruwan inibi ya mika mata guda ta rike. Bata sha ba shi kuma sai ya kurbi nasa sannan ya dubeta cikin tsawa yace kamar yadda kike yin mafarki zaki iya sauya alkadarinki haka nima nake mafarkin sauya nawa,na gani a cikin madubin tsafina cewa ba zakiyi aure ba amma hakan baya yana nufin cewar ba zaki iya samun haihuwa da wani ba. A takaice na gane cewa nine wanda zaki sami juna biyu dashi,babu makawa sai wannan kaddara ta faru,mai zai hana tun yanzu ki kare darajarki da kimarki ki aureni domin 'danmu yayi alfahari da cewar an haifeshi akan tafarkin aure mai daraja tsakanin sarki da sarauniya. Kapin sarki Uzaima ya gama rufe bakinsa tuni sarauniya Aryala ta tari numfashin tana mai daka masa tsawa tace kada ka sakeyi min batun aure,shin kana ganin cewa zaka iya yi mini fyade ne? Sarki Uzaima ya gyada kansa cikin murmushi yace ai bakin rijiya ba wajne wasan makaho bane,ni kaina nasan cewa bazan iyayi miki fyade ba da karfin tsiya amma ki sani cewa maso abinka ya fika dabara wannan shine dalilin da yasa na hana dakaruna shigowa nan kuma na rantse da gemun iyayena ba zaki fita daga cikin turakar tawa ba face na sanki 'ya mace,kuma bada karfin tsiya bukatata zata biya ba,sirrin yana jikin wannan kofin da kika rike a hannunki a jikin kofin an shafa wani sinadari wanda tuni ya shiga dukkan kofofin fatar jikinki,nan da cikar yan dakiku kadan zaki rasa gaba daya karfin jikinki ko tsayawa ba zaki iyayi ba kina ji kina gani zan sarrafaki yadda duk nake so. Koda jin wannan batu sai sarauniya Aryala tayi jifa da kofin dake hannunta ta kama goge tafin hannunta a jikin rigarta. Da ganin haka sai sarki Uzaima ya kyalkyale da dariya ya dubeta yace wannan shine ihu bayan hari,ai BAKIN ALKALAMI ya riga ya bushe. Cikin tsananin fishi Aryala ta zare tagwayen takubbanta ta yunkura da nufin ta afka masa kawai sai ta kame a inda take domin ji tayi kamar an zare gaba dayan lakar dake jikinta,jim kadan kuma saita bingire kasa ta baje. ™Abbas Abdulkadir Hada Hada™ A lokacin da taji ta kasa koda motsa dan yatsanta guda,sarki Uzaima ya dubeta ya sake kyalkyalewa da dariya a karo na biyu sannan yazo kanta ya durkusa yace yake abar KAUNATA,abar BEGE NA kiyi sani cewa a wannan duniya kaf yanzu babu abinda nake SO sama dake,inda zaki bani gurbi a cikin zuciyarki kuma ki zabeni a matsayin mijinki na aure da kin sami cikar dukkan burinki na duniya,to amma kaddara ta riga fata,ni ma babu yadda zanyi dole ne na kau da batun aure a tsakaninmu muddin inason na cika nawa babban burin na samun magaji. Koda gama fadin hakan sai sarki Uzaima ya ajiye kofin inibin dake hannunsa yasa hannayensa biyu ya dauki sarauniya Aryala yaje ya shimfideta akan gadonsa,koda ya fara cire maballan rigar jikinsa sai yaga ta kura masa idanu hawaye na zubo mata. Nan take yaji ya kamu da tsananin tausayint amma daya tuna burin dake gabansa sai kawai yaci gaba da kokarinsa har saida hakansa ya cimma ruwa. Hawaye bai daina shatata ba daga cikin idanuwan Aryala har Uzaima ya kammala abinda zaiyi,a sannan ne ya kura mata idanu yace,ki gafarceni yake MASOYIYA ta,daga yau zan kula dake a matsayin matata a cikin wannan babban gidan sarauta nawa,kuma na baki dukkan jin dadin rayuwa da duniya har izuwa lokacin da zaki sami rabo daga gareni wato juna biyu,zan kula da lafiyarki yadda ko kuda bazan bari ba ya taba lafiyarki. * A can bakin kofar turakar sarki Uzaima kuwa lokacin da Barde Husum yaga sarauniya Aryala ta dade bata fito daga cikin turakar sarki Uzaima ba sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya kama hannun Jarumi Damzur ya jashi izuwa gefe daya ya dubeshi yace yakai Damzur ka yi sani cewa tabbas akwai wani abu dake faruwa wanda ba daidai bane,nasan halin Aryala mutumce wadda batayin magana mai tsawo,tunda har kaga ta dade haka da yawa bata fito ba daga cikin turakar sarki Uzaima lallai ba lafiya ba. Koda jin wannan batu sai nan take idanun Jarumi Damzur suka kada sukayi jawur,zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone,kawai sai ya dubi Husum yace maza kaida dakarunka ku taimaka mini zan fasa dakarun dake gabanmu da karfin tsiya na shiga har can cikin turakar Sarki Uzaima,amma dole ne mutum daya ya biyoni ciki domin ya taimaka mini wajen dauko sarauniya koda zamu risketa a cikin mugun yanayi,zanyi kokarina naga mun gudu da ita daga cikin gidan sarautar nan mun mayar da ita can birnin Nurul Ansar,wannan shine aikina kuma shine alkawarin dana daukar mata. Koda jin wannan shawara sai barde Husum yace an gama ya shugabana,nan take duk su biyun suka zare takubbansu suka afkawa dakarun dake gabansu suka hausu da SARA da SUKA,koda ganin haka sai sauran yan uwansu dakaru suka kawo dauki.Nanfa wuri ya yamutse,ihun mazaje da karafkiyar karafa ya cika gidan sarautar gaba daya,dakarun sarki Uzaima dake kan katanga rike da KWARI da BAKA sai suka dimauce suka rinka sakin harbi ta ko ina,al'amarin daya janyo suke rinka kashe yan uwansu suma kenan basu lura ba. Wannan itace damar dasu jarumi Damzur suka samu suka tarwatswa dakarun dake bakin kofar turakar da karfin tsiya suka kunna kai cikin suna masu falfala azababben gudu. Sarki Uzaima nacan a gaban sarauniya Aryala yanayi mata sambatu sai ya jiyo ihun mazaje da karafkiyar karafa acan wajen turakarsa a firgice ya mike tsaye zumnur ya ruga izuwa inda takobinsa da garkuwarsa suke domin ya dauko su daga jikin bangon da suke rataye amma kafin hannunsa yakai kansu tuni Jarumi Damzur ya dako tsalle a sama ya doki gadon bayan sarki uzaima.Sarki uzaima yayi sama fuskarsa ta gwaru da bangon dakin ya fado kasa sumamme,cikin hanzari Jarumi Damzur ya dauki sarauniya Aryala ya sabata a gadon bayansa ya sake rugowa waje har ya dawo inda ake gumurzu,da karfin tsiya yaci gaba da tarwatsa dakarun sarki uzaima yana saransu da sukarsu. Barde Husam na taimaka masa amma saboda tsananin yawan dakarun guda dubu biyu da dari bakwai ya rage sauransu dari uku da biyu kacal. A haka dai suka ci gaba da azababben yaki har tsawon dakiku masu yawa,da kyar da sidin goshi gami da dabarun yaki suka iso har farpajiyar gidan sarautar suka tasamma inda bargar dawakai suke,a sannan ne fa dakarun sarki Uzaima suka sake tuttudowa da yawan gaske tamkar daga cikin kasa suke fitowa sukayi musu rubdugu... . waye zai iya tuna mana sunan extract din labarin da yazid yake baiwa su gimbiya nauwara? WASIKAR JINI!!! Littafi Na Shida (6) Part D . Suka sake tuttudowa da yawan gaske tamkar daga cikin kasa suke fitowa sukayi musu rubdugu.. . Wohoho! Idan Jarumi ya cika jarumi tofa ba'a ganin jarumtakarsa sai idan yaga mutuwa muraran a lokacin da zuciyarsa ke dauke da babban buri,burin su jarumi Damzur shine su sami damar guduwa da sarauniya Aryala daga cikin gidan sarautar kafin sarki Uzaima ya farfado daga dogon suman da yayi,don haka sai suka cigaba dayin yakin da dukkan karfinsu ya zamana cewa duk inda suka sa gabansu saidai kaga maza na zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona. Kaico a wannan lokaci ne aka kashe ragowar yan uwansu dakaru mutum dari uku ya zamana saura su biyu kacal suma din babu wanda ba'ayi masa rauni ba sama da guda biyar a jikinsa ba. Gashi dai jini na zuba a jikinsu amma basu fasa tarwatsa dakarun ba,a haka suka isa inda dawakai suke suka haye kansu suka zaburesu da gudu ana harbo musu kibiyoyi da masu,su kansu sun gama sallamawa cewa mutuwa zasuyi tunda babu yadda za'ayi dawakansu su iya shallake doguwar katangar gidan sarautar amma ba zato ba tsammani sai sukaga dawakan nasu sun daka tsalle sun shallake katangun kuma sunci gaba da gudu suna masu nauwasa cikin daji,a guje aka bude kofar gidan sarautar dakarun suka biyo bayansu a guje domin su cimmasu. Adaidai wannan lokaci ne sarki Uzaimana ya farfado daga dogon suman da yayi koda ya bude idanunsa ya dubi ko ina a cikin turakar yaga babu sarauniya Aryala saiya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa nan take ya mike tsaye zumbur ya dauko kayan yakinsa ya ruga izuwa waje yana isowa filin gidan sarautar yayi arba da gawarwakin dakarunsa dana su sarauniya Aryala,sai ya tambayi ina sarauniya Arayala take. Nan fa aka gaya masa cewa an kashe mata dakarunta gaba dayansu amma shugaban dakarun nata da mataimakinsa sun sami nasarar saceta akan doki sun gudu amma anbi sawunsu. Koda jin haka sai sarki Uzaima ya sake kwarara uban ihu ya ruga izuwa cikin bargar dawakansa ya kamo wani farin ingarman dokinsa ya haye kansa ya zabureshi da gudu yabi sawun dakarun da sukabi su jarumi Damzur. Lokacin da su Jarumi Damzur suka nausa cikin daji da sarauniya Aryala bisa doki suna tsala gudu sai suka cigaba da sakarwa dawakansu linzami kamar zasu tashi sama,kai da gani kasan cewa gudun ceton ransu sukeyi kodai su tsira ko kuma su hallaka. Duk wannan abu dake faruwa har a sannan sarauniya Aryala bataji karfin jikinta ya dawo ba. Duk irin azababben gudun da sukeyi sai da suka rinko jiyo sautin sawayen dawakan dakarun da suka biyo su,ashe dawakan dasu jarumi Damzur suka hau na musamman ne wadanda suka sami horon gudu da tsallake gine gine masu tsawo. Tunda safe aka fara wannan tseren guda har saida rana ta fadi ya zamana cewa su Jarumi Damzur sun baiwa dakarun sarki Uzaima tazara mai yawa kuma har sun fita daga cikin iyakar kasar sannan dakarun suka hakura suka daina binsu suka juya da baya. Ai kuwa suna juyawar sukayi cikibus da sarki Uzaima a sukwane bisa farin dokinsa,yana ganinsu yaja linzamin dokin yayi turjiya yana mai daga kafafunsa sama gami da haniniya,koda sarki Uzaima ya dubi gaba dayan dakarun yaga basa tare da sarauniya Aryala saiya kurma uban ihu ya zare takobinsa yahau dakarunsa da sara saboda tsananin fishi ba shiri dakarun suka tarwatse suka bazama izuwa cikin daji suna neman wajen buya don tsira da rayuwarsu. * Al'amarin su Jarumi Damzur kuwa basu daina gudu akan dokin ba har saida suka tabbatar da cewa sunyi nisa ga barin iyakar birnin Kisra sun shiga cikin yankin dazuzzukan birnin kisra sannan suka tsaida dawakansu suka fado kasa daga kan dawakansu a matukar galabaice tamkar ransu zai fita. Da kyar suka yiwa kansu magani suka dinke raunikan dake jikinsu.Sarauniya Aryala kuwa bata dawo cikin haiyacinta ba gami da samun karfin jikinta har saida sanyin asuba ya kada a sannan ta farka daga barci. Koda ta bude idanunta ta tsinci kanta a cikin daji kuma taga jarumi Damzur da Barde Husum zaune a gabanta saita takarkare ta kurma uban ihu sannan ta fashe da matsanancin kuka da kyar su jarumi damzur suka rarrasheta tayi shiru sannan jarumi damzur ya dubeta yace ya shugabata ina dalilin wannan kuka naki? Aryala tasa hannu ta share hawayenta sannan tace sarki Uzaima ya kawar da Budurcina ya karya alkadarina. Koda jin haka sai jarumi Damzur da Barde Husum suka kamu da tsananin bakin ciki har idanuwansu suka ciko da kwallah.Aryala ta cigaba da magana cikin sheshsheka tana mai cewa yanzu da wane ido zan kalli mahaifina wanda ke kwance cikin jinyar rashin lafiya yana son yaga dawo wata gida cikin nasara dauke da dukiya mai yawa. Da wane idanu zan kalli jama'ata alhalin na kasa kare kaina bare na kare rayuwarsu da mutuncinsu,ku kanku gashi nasa kunsha bakar wahalar da kuka kusa rasa rayukanku,ni kan yanzu rayuwar duniya ta fita daga raina gwara ma ku taimaka mini ku kashe ni idan kuka ki kashe ni to lallai zan kashe kaina. Koda sarauniya Aryala tazo nan a zancenta sai jarumi Damzur da barde Husam suka fashe da kuka suka shiga rokonta akan ta janye wannan manufa tata kuma sukayita bata baki akan ta hakura ta yarda su maida ita birnin nurul ansar,duk da cewa sarauniya Aryala tana son ta koma gida ta iske mahaifinta a raye amma sai bakin cikin abinda ya sameta yasa taji bata son sake saduwa dashi. Da kyar da sidin goshi dai su jarumi Damzur suka shawo kan sarauniya Aryala ta amince akan a cigaba da tafiya don isa birnin nurul ansar. Nan da nan suka cigaba da tafiya ba sassauci ya zamana cewa basa yada zango komai dare komai rana face sun gaji likis ko kuma duhu yayi yawa,cikin sa'a suka shafe kwana ™Abbas Abdulkadir Hada Hada™ tara suna tafiya batare da sun hadu da wani mugun abuba sannan suka iso birnin nurul ansar.Tun daga nesa suka hango an sauke tutar masarautar daga kan kofar birnin,zuciyoyinsu suka buga da karfin gaske a wannan lokaci sarauniya Aryala na bisa doki Jarumi Damzur na kasa yana jan dokin nata shi kuma Barde Husum na biye dasu bisa daya dokin,kawai sai sarauniya Aryala taja linzamin dokin nata ta tsaya cak ta dubi barde Husam tace babu lafiya a kasata kodai mahaifina ya rasu ko kuma ancimu da yaki. Ka ruga cikin birnin ka gano abin dake faruwa. Koda jin wannan umarni sai jarumi Husum ya sakarwa dokinsa kaimi ya nufi cikin birnin nurul ansar. Jim kadan saiga barde Husum ya dawo garesu jikinsa a sanyaye kuma kansa a sunkuye,koda ya iso daf dasu ya dago kansa sai sukaga idanunsa sunyi sharkaf da hawaye take sarauniya Aryala ta kwalawa mahaifinta kira ta fashe da matsanancin kuka,saida Aryala ta shafe sama da sa'a daya da rabi tana kuka sannan ta nutsu ta dubi su jarumi Damzur tace tunda har ban dawo gida na iske mahaifina a raye ba bana bukatar sarautan idan a cikinku akwai mai sha'awar yaje ya karbi karagata yanzu anan zanyi rubutu kuma na buga hatimina bisa shaidar cewa na bashi karagar tawa. koda jin wannan batu sai jarumi Damzur da Barde Husum suka fashe da kuka,jarumi damzur ya dubeta yace yake jarumar jarumai kiyi sani cewa banga amfanin rayuwata ba muddin bana tare dake saboda kece kika tsamoni daga cikin mummunar rayuwa kika mayar dani mutum,nasan menene adalci da soyayya alhalin adacan babu abinda nasani face zalunci da kiyayya. Bani da abinda zan saka miki dashi face nayi bauta a karkashinki har izuwa karshen rayuwata. Shima barde Husum saiya dubi sarauniya Aryala yace tun ina yaro karami iyayena suka mutu mahaifinki ne ya reneni tamkar dan cikinsa kuma yasa aka koyar dani horon yaki har na zama babba a cikin dakarunsa,shine ya bani macen dana aura tazo ta mutu a lokacin haihuwarta ta farko kuma shine ya bani gida da dukiya mai yawa,bai taba neman wata alfarma a wajena ba sai sau daya alfarmar kuwa itace kafin mu baro birninmu ya rokeni akan na kula dake kuma na tsare lafiyarki da rayuwarki har izuwa karshen rayuwata. Dame zan sakawa mahaifinki bisa abinda yayi mini a rayuwa face na cika alkawarin baki tsaro.Lallai ina tare dake har izuwa karshen rayuwata. Koda Barde Husum yazo nan a zancensa sai sarauniya Aryala ta sauko daga kan dokinta ta rungumesu duk su biyun ta fashe da kuka gaba dayansu saida suka jima a kankame da juna sannan suka janye jikinsu daga cikin nata suka dorata akan doki suka kauce daga kan hanyar da zata kaisu birnin nurul ansar suka nausa cikin daji batare da sanin inda ma suka dosa ba.Haka dai su sarauniya Aryala suka cigaba da tafiya har saida suka shafe sati uku suna tafiya sannan suka iso wani kauye dake cikin wata nahiya daban da tasu,suna sauka a bakin wannan kauye sai sarauniya Aryala ta kamu da tsananin rashin lafiya ya zamana cewa zazzabi mai zafi ya rufeta kuma ta rinkayin kumallo.Nanfa hankalinsu ya dugunzuma suka karasa cikin wannan kauye da sauri suka biya kudi aka kaisu gidan wata likita. Koda aka kwantar da Aryala a cikin wata bukka likitar tazo ta dubata saita dubi su jarumi Damzur cikin murmushi tace ai ba wani abu bane ya samu yar uwarku,ta sami juna biyu ne. Koda jin wannan batu sai Aryala ta kurma uban ihu kuma ta mike tsaye zumbur kamar mahaukaciya ta rarumo wuka zata daba a cikinta. Da kyar jarumi Damzur da barde Husum suka riketa suka kwace wukar dake hannunta. Nanfa ta fashe musu da matsanancin kuka na bakin ciki.Daga wannnan rana Aryala ta tsani kanta kuma ta tsani juna biyun da take dauke dashi,babu abinda batayi ba don ta lalata juna biyun datake dauke dashi amma sai abu ya faskara

Chapter 11 of 15