Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels  WASIKAR JINI!!! Littafi na Daya (1) Part A A wani zamani can baya mai tsawo daya shude a cikin daular kasashen larabawa anyi wani shararren sarki mai suna Aiyuba Ibinin Silhar.Masana hasashe da masu bincike na wannan zamani sun tabbatar dacewa babu wani sarki a duniya kaf wanda yakai sarki Aiyuba tarin dukiya da kuma karfin sihirin tsafi,saidai kash,ko kadan bai kasance sadauki ba ko jarumi mai karfin damtse da iya yaki,amma saboda wannan dukiya daya tara da kuma karfin sihirin tsafi sai ya zamo dodo ga dukkan sarakunan dake nahiyar ya zamana cewa duk tsoronsa sukeji.Komai yawan dakarun yakin sarki da kuma jarumtakarsu indai sukace zasu yaki sarki Aiyuba saidai su sha kashi.Sarki Aiyuba yana da matar aure guda daya rak mai suna Hufaira wacce sukayi auren saurayi da budurwa tun kafin ya zamo sarki wato ya gaji karagar mulki a wajen mahaifinsa kuma kafin ya tara dukiya taban al'ajabi.Allah bai bawa sarki Aiyuba haihuwa ba saida ya shekara daya akan karagar mulki a sannan idanunsa suka bude akan fadada harkokinsa na kasuwanci izuwa ko ina a cikin duniya,ya zamana cewa duk bangaren da mutum yaje a duniya walau kasar larabawa,turawa da bakaken fara da kuma bangaren kasar Hindu da birnin Sin sai yaga gonaki,gidaje,da rumfuna Na kasuwa anan na sarki Aiyuba Ibn Silhar.Kuma gaba dayan fatakensa suna amfani da wani hatimi guda daya mai taswirar rakumi da takobi a jikin kowacce irin haja tasa sai kaga wannan hatimi. Dukkanin yaransa masu sarrafa duniya suna tsananin tsoronsa kuma suna adana masa dukiyar domin idan ka kuskura kaci amanarsa tofa ka rinka ganin masifu kenan iri iri na cututtuka masu azaba,kuma ka rinka shiga bala'i iri iri kenan har sai kazo gabansa ka kawo wannan dukiya kuma ka tuba sannan zaka samu kanka. Wani babban hali na kirki a tare da sarki Aiyuba shine ko kadan baya wasa da hakkin yaransa yana biyansu ladan aikinsu kamar yadda ya kamata,kuma indai ka shekara guda kana yi masa bauta kaima ka fita daga sahun talakawa saidai a saka ka a sahun attajirai. A shekarar farko daya hau karagar mulki ne Matarsa Hufaira ta haifar masa 'ya mace kyakkyawa ta gaban kwatance mai sunaNuwaira,koda yake sarki Aiyuba yaso ace 'da namiji ya samu domin ya gaje shi amma duk da haka saida yayi farin ciki ainun kuma saida aka shafe kwana saba'in kullum sai anyi walimar ta farin cikin samun wannan 'ya.Attajiran sarakai da matsafa saida sukazo daga kowanne bangare na duniya suka halacci wannan biki na murnar haihuwar gimbiya Nuwaira.Batun maroka kuwa duk wanda ya sami damar shiga gidan sarautar sarki Aiyuba kakarsa ta yanke saka domin shi da talauci sunyi hannun riga.Da yawan marokan haukacewa sukayi saboda ganin irin tsananin dukiyar da suka samu wacce bama suba hatta jikokinsu da tattaba kunnensu sai sunci albarkaci,wasu kuwa kuka suka kamayi domin basu san ta yadda zasu iya diban dukiyar ba su tafi da ita,bisa dole komai hadamar maroki yabar wata dukiya ya kwashi iya wadda ya iya diba.Yan fashi kuwa dake kan hanyoyin zuwa birnin Lailatun Harus wato birnin sarki Aiyuba basu taba samun ganima ba a rayuwarsu irin ta shekarar da aka haifi Gimbiya Nuwaira,wasu ma da yawansu sanadin daina yin fashin su kenan. Bayan an kwana saba'in ana walimar murnar haihuwar ta gimbiya Nuwaira sai baki suka watse suka koma izuwa kasashensu,a lokacin ne fa labarin Gimbiya Nuwaira dana mahaifinta ya sake yaduwa da fantsama a ko'ina cikin duniya,sunayensu ya zamo abin kwantace,daukak arsu ta shafe duk wani mai sharafi a zamanin. Wani babban abin mamaki da yake daurewa mutane kai dangane da sarki Aiyuba shine babu wanda yasan a inda yake tara dukiyarsa ko yake boyeta, Amma duk sa'adda yaso yayi amfani da dinare ko lu'u lu'u ko makamancin su kawai zaice aje guri kaza ne a dauko,ana zuwa kuwa za'a ga dukiyar koda yawanta yakai cikin gari guda,kuma koda an san cewa babu komai a wajen,mafi yawan wuraren dayake cewa aje a debo dukiyar ma wulakantattun wurare ne marasa daraka inda babu tsaro kamar kududdufai ko inda ake tara shara. Haka dai arzikin sarki Aiyuba yaci gaba da habaka ya zamana cewa kullum a cikin gyara birninsa yake da gine gine na kawa da kasaita har saida takai cewa a duniya kaf babu wata kasa data kai tasa kyawu,tsaruwa da kawa,fadarsa kuwa aljanar duniya ake kiranta domin komai na cikinta da lu'u lu'u aka yishi. Lokacin da gimbiya Nuwaira takai shekara bakwai a duniya sai kyawunta ya ninka nada,al'amarin da yasa iyayenta suka kara son ta kenan ainun fiye da koyaushe.'Yayan masu fada a ji kuwa tun daga sannan suka fara kamun kafa ta neman aurenta saboda matsayin ubanta da kuma kyawunta,amma sai sarki Aiyuba yayi biris da bukatarsu komai irin dangantakar dake tsakaninsa da iyayensu kuwa,wannan shine abu na farko daya fara jefa hassada a zukatan sarakunan dake nahiyar suka fara tsanar sarki Aiyuba. A yamma da birnin Lailatul Harus wato birnin sarki Aiyuba akwai wata kasa mai suna Hirama,sarkin dake mulkin kasar Hirama ya kasance gagarumin sadauki mayaki mai tarwatsa maza a filin daga,ana kiransa da suna Murwatu,shima matsapi ne na gaske,amma bai kama farcen kafar sarki Aiyuba ba,domin ya taba jarraba karfin tsafinsa akan na sarki Aiyuba yaji ba dadi,harma saida ya durkusa bisa gwiwoyinsa a gaban sarki Aiyuba ya nemi gafara don kada ya rasa rayuwarsa. Al'amarin ya faru ne a wata shekara da akayi fari a kasar Hirama ya zamana cewa yunwa,fatara da talauci ya addabi mutanen kasar har takai cewa kananun yara da masu rauni suna mutuwa.Lokacin da al'amarin yayi tsamari ainun sai sarki Marwatu yasa aka rubuta wasika ya tashi manzo izuwa ga sarki Aiyuba a cikin wasi kar ya nemi taimakon abinci mai yawa gami da aron kudade masu yawa domin ya bunkasa harkar noma a kasar tasa,dama babbar matsalar kasar itace kasarsu bata da dadin noma sai masana kasa sunzo sunyi mata aiki sannan kuma suna da karancin ruwa,dole ne a buda hanyoyin ruwa daga kasashen ketare su shigo,kuma a nemi iri mai kyau na shuka. Sarki Marwatu ya dauki alkawarin cewa bayan ya shekara guda zai dawo da duk kudin da aka ara masa kuma zai bayar da riba kaso guda cikin uku. Lokacin da wannan wasika ta riski sarki Aiyuba yana zaune akan karagar Mulki a fadarsa ana tafiyar da harkokin mulki,ga Gimbiya Nauwara zaune a cinyarsa kumaga fadawansa da sauran jama'ar gari sun kewayeshi. A tsakiyar fadar wadansu kyawawan 'yan mata ne su bakwai suna ta tikar rawa anayi musu kida don debe kewa. A wannan lokacin sarki Aiyuba yana cikin nishadi da walwala don daka dubeshi kasan cewa farin ciki ya cika zuciyarsa.Bayan magatakarda ya gama karanta wasikar sarki Marwatu sai sarki Aiyuba ya tuntsire da dariya irin tasu ta sarakai masu jin izza sannan ya dubi 'yarsa Gimbiya Nauwara yace,'yata kinji bukatar da sarki Marwatu yazo mini da ita,shin kin amince na taimaka masa ko kuwa na rabu dashi? Kisani cewa duk wannan dukiya dana tara a duniya badan kowa na tara taba sai domin ki,kece kadai kike da ikon fadin abinda za'ayi da ita.Koda fadawan sarki Aiyuba da sauran jama'arsa sukaji wannan batu sai suka cika da mamaki sukayi zaton ma ko sarki Aiyuba ya sami dan tabin kwakwalwa ne domin basu ga dalilin da zaiyi wani abu da dukiyarsa sai ya tambayi 'yarsa wacce ta kasance yarinya karama 'yar shekara bakwai.A lokacin da gimbiya taji tambayar da mahaifinta yayi mata saita yi murmushi sannan ta dubi sarki tace,yakai Abbana kayi sani cewa kana daarzikin da zaka iya ciyar da gaba dayan kasashen dake nahiyar nan tamu kuma ka wadatar dasu da arzikin da zasu tsira daga talauci to amma nafi so kayi taimako a inda ya dace abinda nake nufi shine wannan sarki Marwatu yana daga cikin wannan sarki Marwatu yana daga cikin irin sarakunan da sukayi maka girman kai, baya daga cikin sarakunan da suke zuwa gaisheka duk shekara duk wani abu na farin ciki idan ya sameka baya zuwa ya tayaka sai yanzu da bukatarsa ta taso sannan zai nemi taimakonka. To kasani cewa bazamuki taimakonsa ba,kasa akai masa abinci mai yawan gaske kuma a bashi kudade masu yawa wadanda zasu isheshi ya gyara harkar noma amma bisa sharadin zai biyaka kuma ya biya ka riba bayan cikar shekara guda kamar yadda ya sharadanta da kansa.In har ya karya wannan alkawari to duk abinda ya biyo baya kada ya zargo kowa face kansa. Baya ga wanann inaso ka gaya masa a cikin amsar wasikarsa cewa kai mai arziki ne kuma attajir uban sarakai inda ma ya nemi kyauta da an bashi amma rashin biyayyarsa ce ta sanya a bashi aro. Koda Gimbiya Nauwara tazo nan a zancentsa sai gaba dayan mutanen dake fadar suka cika da tsananin mamaki bisa yadda akayi Nauwara ta zamo yarinya mai kaifin hankali da tunani haka, shi kuwa sarki Aiyuba sai ya kamu da tsananin farin ciki ya dubi 'yan majalisa yace,kunga wannan yarinyar dole ne ta kasance a cikinku domin ko babu ni zata iya baku shawarwari akan harkokin mulki wadanda zasu amfane ku su amfani kasa gaba daya,kuma duk abinda ya taso na kudi zata taimaka muku dashi,saboda zata gaji duk dukiyarta bisa wannan dalili daga yau dinnan na mika matsayin Galadima a hannun Gimbiya Nauwara tunda shine matsayi na kula da duk harkokin kasuwancinmu da sarrafa kudaden kasa,koda jin wannan batu sai idanun Galami suka zazzaro hankalinsa ya dugunzuma kuma ransa ya baci.Ya dubi sarki Aiyuba cikin alamun tsananin damuwa a lokacin dayai sauri ya durkusa a gabansa zai fashe da kuka yace,Haba yakai dan uwana ya za'ayi kace gimbiya ce zata karbi matsayina alhalin shekarunta basu kai ta ruke wannan mukamin ba kuma idan ta karbi wannan mukami ni kuma wane matsayi zan rike a wannan majalisa ko kuwa so kake na karayin kasa ne? Koda jin wannan batu sai sarki ya mike tsaye daga kan karagarsa ta mulki ya sauko har kasa inda galadima ke durkushe ya kama kafadunsa ya tashe shi tsaye ya dubeshi cikin murmushi yace,Yakai galadima kayi sani cewa har abada bazan taba wulakantaka ko kaskantar dakai ba saboda kaine kadai dan uwana na jini daya rage a wannan duniya,a kan wane dalili zaka damu da mukami a cikin wannan fada alhalin ko yanzu na fadi na mutu kaine zaka gaji karagata,tunda babu yadda za'ayi gimbiya tayi mulki bisa dokar wannan masarauta tamu? Idan kana kwadayin dukiyar da take kai kawo ne a ofishinka na kasuwanci idan ka zama sarki komai na hannunka,ka sani cewa gimbiya babbar gudunmawa zata bayar a gareka kuma da babban taimako na kudi ko nawa ake bukata tunda arzikin da zan barmata ya ninka duk arzikin dake cikin kasashen nan na nahiyoyinmu sau goma,daga yau ka koma matsayin wazirina tunda ka sani cewa tunda na hau mulki kujerar wazirci babu kowa a kanta,koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube galadima ya kama godiya kamar bazai daina ba,amma yana hada idanu da gimbiya Nauwara sai ya murtuke fuska kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwarsa,ita kuwa saita risina a gareshi kuma ta tayashi murna bisa samun wannan sabon mukami na waziri. Nantake sarki Aiyuba yasa aka rubuta wasikar da sarki Marwatu ya aiko da ita kuma akayi bayani a cikinta kamar yadda Gimbiya Nauwara ta bukata,daga nan sai aka shirya buhunhunan abinci a kalla miliyan uku bisa keken shanu da rakuma gami da buhunhunan dinare duba arba'in bisa rakiyar dakaru dubu dari aka baiwa manzo na sarki Marwatu suka kama hanya suka durfafi birnin Hirama.......... Dafatan littafin yayi.? Kasancewar korape-korapen da najima ina samu akan cewa ayi wani littapin yaki nikuma banida lokaci daman kun sani, wannan dinma nayi rubutun ne tun 2015 yana ajiye shiyasa nace to ko akwai wanda basu karanta ba wasu kuma zasu so sake karantawa... Ina patan zaku bani hadin kanku mu gudu tare mu zira tare. WASIKAR JINI!!! Littafi Na Daya (1) Part B . Aka baiwa wannan manzo na sarki Marwatu suka kama hanya suka durfafi birnin Hirama. Al'amarin waziri Ridwan bin Silhar kuwa lokacin da fada ta watsa sai ya tafi izuwa gidansa cikin tsananin farinciki tamkar an mallaka masa duniyar gaba daya nan take yasa aka shirya walima ta musamman ya gaiyaci duk manyan abokansa na birnin da kauye. Washe gari kuwa gidansa ya cika makil ya batse da jama'a maza da mata,ba'a fara walimar ba sai bayan anje fada an gama bikin nadashi,babban abinda ya bakantawa waziri Ridwan rai shine ba sarki ne ya nada masa rawani ba na wazirci,Gimbiya Nauwara ce ta wakilci sarki kuma tun a fada yaga komai ya sauya na irin ikonsa da karfinsa akan harkokin arziki na kasa.Hatta dukiyar da ake ajiyewa a Baitul Mali a gabansa mai kula da dukiyar yazo gaban gimbiya da lissafin komai kuma yayi bata bayanin yadda ake sarrafa dukiyar bisa tsarin tsohon galadima,koda ta fahimci cewa tsari ne nason kai da son zuciya,domin akwai wadansu kudade da suke shiga aljihun galadima a banza maimakon su rinka zuwa hannun talakawa mabukata,sai ta dubi ma'ajin baitul Malin tace,yau zan canja tsarin komai na dukiyar dake cikin baitul Mali kuma zan kirawoka na baka komai a rubuce bisa yadda nakeson a rinka tafiyar dashi. Koda waziri yaji wannan jawabi na gimbiya sai zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone kuma yaji ya sake tsanar gimbiya fiye da ko yaushe,ba komai ne ya janyo hakan ba face ya san cewa da zarar gimbiya ta sauya tsarin komai na dukiyar baitul mali shike nan ya daina samun kudade masu yawan gaske wadanda dasu ne yake sharholiyarsa a garin yake yin duk abinda yaso har ma ake shakkarsa. Da farko attajiran garin sun dauke cewa sarki Aiyuba ne yake baiwa dan uwansa Ridwan kudade shi yasa yake tafiyar da rayuwar mai mugun tsada a gidansa da harkokinsa,amma a yanzu da aka sauke shi daga matsayinsa na mai kula da bailtu mali sai komai ya sauya ya kasa cigaba da bushasha kamar yadda ya saba duk da ci gaba daya samu a majalisa ba baya ba. Bayan an dawo daga fada an fara walima mutane maza da mata,sarakai da attajirai,da masu fada aji suna ta ciye ciye da shaye shaye a cikin babban falon gidan Waziri Ridwan amma shi mai gaiyatar babu shi a wajen sai matarsa Gimbiya Ra'isa wacce itace take karbar baki tana sawa ana kaisu inda ya kamata su zauna,koda Ra'isa taga an shafe kusan rabin sa'a da fara walimar amma mijinta bai gama shirin ba ya fito daga cikin turakarsa sai ta tafi izuwa turakar tasa da sauri.Tana shiga sai ta iske shi a zaune bisa kujera ya kifa kansa akan tebur yana ta sheshshekar kuka,al'amarin daya dugunzuma hankalinta kenan ta ruga gareshi ta dago da kansa suka dubi juna tace,Haba yakai Abul Zainur yaya zaka zauna anan kana kuka alhalin yau rana ce ta farin ciki bisa babban mukamin daka samu,ga masoyanka can fa sun taru a falo ana tayaka murna.Koda jin wannan batu sai waziri Ridwan ya kyalkyale da mahaukaciyar dariya,al'amarin daya firgita Ra'isa kenan ta danja da baya ta kura masa idanu kawai.Take Ridwan ya tsuke bakinsa ga barin yin dariyar ya dubeta cikin yanayi na bakin ciki a lokacin da hawaye ya zubo masa yace,Yake matata kiyi sani cewa dan uwana sarki Aiyuba ba matsayi ya kara mini ba tauyeni yayi domin wannan kujera ta waziri daidai take da ajiye ice ko dutse abinda bashi da rai wanda bazai iyayin ko motsin komai ba,kin sani cewa bani da wani buri a wannan duniya face na zamo gagarumin attajiri wanda babu kamarsa a duniya a tarin dukiya dajin dadin komai na barwa duniya abin tarihin da baza'a taba mancewa dashi ba. A da nayi tunanin cewa da zarar dan uwana sarki Aiyuba ya mutu zan cika wannan buri nawa tunda ni kadai nake da gadon duk abinda ya mallaka amma a yanzu daya sami haihuwa sai dukkan burina ya ruguje tunda gimbiya Nauwara zata gaje dukiyar ce wacce a halin yanzu babu wani mahaluki a doron kasa daya mallaki a dadinta.bani da ikon batar da gimbiya Nauwara ko na kashe ta domin duk abinda zan aikata a boye sai ya gani da karfin sihirinsa na tsafi. Babban abin bakin cikina shine na fuskanci cewa wannan matsayi na galadima da sarki ya rabani dashi yafi kowanne mukami daraja da muhimmanci akasar hatta karagar sarki kuwa... Dalilin da yasa na fada miki haka shine gaba daya harkokin kudi na kasar yana cikin wannan matsayi haka kuma galadima shine da jan ragama ta zabin sarki kuma shine mai baiwa sarki shawara akan harkokin mulki,kinga kenan ko na hau kan karagar mulki gimbiya Nauwara ce mai jagorantar mutane a fakaice idan tayi aure ta sami haihuwar 'da namiji,danta zai iya zama sarki kinga kenan a karshe nida duk iyalina zamu tashi a tutar babu,ki tuna cewa a yanzu danmu Yarima Zainur da shekaru biyu kadai ya girmi Gimbiya Nauwara,yaushe ne shima zai girma kuma yaushe ne nima zan hau karagar mulkin kasar nan har ya gajeni? Koda Waziri Ridwan yazo nan a zancensa sai ya fashe da kuka,al'amarin daya karya zuciyar Ra'isa kenan taji ta kamu da tsananin tausayinsa don haka sai ta rungumeshi ta shiga rarrashinsa tana cewa, Ka kwantar da hankalinka yakai Mijina kayi sani cewa komai nisan jifa kasa zai fado tunda idan babu mutuwa ai akwai tsufa da cuta,da sannu lokaci zaizo wanda sarki Aiyuba yanaji yana gani daukakarsa ko ikonsa zasu dakushe kuma ko yana so ko baya so dole ne ya mutu yabar wannan karagar mulki da dukiya daya tara a hannunka tunda dai yanzu ya fara tsufa kuma 'yar nan tasa yarinya ce karama kaine kadai shakikinsa idan bai danka amanarsa a hannunka ba saidai ya barta a hannun bare wanda zai sami banza ya kwashe tsuntsu daga sama gasasshe. Koda Ra'isa tazo nan a zancenta sai fuskar Ridwan ta fadada da murmushi take yaji wani irin farin ciki ya lullube shi,kawai sai ya dubi Ra'isa cikin murya yana cewa yake matata hakika ba karamin hangen nesa kikayi ba yanzu domin na tsaya na yi nazari naga cewa duk abinda kika fada gaskiya ne,kuma banga hanyar da sarki Aiyuba zai iya tsallake duk wadannan abubuwa da kika fada ba,koda jin haka sai duk su biyun suka kyalkyale da dariyar mugunta sukayi ta dariyar kamar bazasu daina ba. . YARIMA ZAINUR ya taso a cikin wani irin hali wanda yasha bambam dana mahaifinsa waziri Ridwan domin shi ko kadan bashi da son abin duniya kuma harkokin sarauta ma basa gabansa, a rayuwarsa babu abinda yakeso sama da farauta da kuma jarumtaka bisa wannan dalili ne ya mannanewa sarkin yakin birini wanda ake kira Haiman bin Husein ya rinka bashi horon yaki kuma suka rinka fita farauta daji tare. Saida takai cewa dare da rana Yarima Zainur na tare da sarkin yaki Haiman,kai watarana ma a gidan sarkin yaki yake kwana,da yake matar sarkin yaki bata taba haihuwa ba sai taji ta kaunaci yarima zainur tamkar dan data haifa a cikinta,kuma ta rinka kyautata masa ainun,Al'amarin daya janyo Yarima Zainur ya shaku da Lahisa kenan ainun da kuma mijinta Haiman har yaji yafi kaunarsu a kan iyayensa,sabida ra'ayinsu yazo daidai da irin nasa na rashin damuwa da duniya sabanin iyayensa wanda babu abinda suke so sama dasu tara dukiya mai yawan tsiya kuma su shagala a cikin jin dadi suyi facala da warwasawa. Hakance tasa Yarima Zainur yaji yafison yayi rayuwarsa a gidan sarkin yaki Haiman.Nan da nan kuwa Yarima Zainur ya taso da hazaka a bangaren iya yaki da farauta har ya zamana cewa shi kansa sarkin yaki yana mamakin irin baiwar da Allah ya yiwa Zainur, sadaukantaka tun yana yaro karami da tsananin jure wahalar karbar horo ko kuma wahalar daji ya shafe lokaci mai tsawo na jure gudu,yunwa da kishirwa gami da taurin kai,kafewar zuciya da tsananin rashin tsoro. Lokacin da Yarima Zainur ya cika shekara goma sha hudu sai ya fara yin abubuwan al'ajabi wadanda sukasa nan danan labarinsa ya bazu ko'ina a nahiyar domin a wannan lokaci ne ya shiga wani daji dake yamma da birnin Lailatul Hawas wanda a cikin sane wadansu arnan daji suka kafa sansaninsu.Ance yawan arnan dajin yakai miliyan uku da doriya,kuma sunfi shekara dari da wani abu a wannan daji,amma babu wani abu a wannan daji,amma babu wani sarki daya taba tunanin ya murkushe su su zama bayinsa ko kuma ya rinka karbar haraji a hannunsu,gashi dai ana harkokon kasuwanci dasu na cinikayyar fatun dabbobi da sauran kayayyaki amma kuma babu wata kyakyawar alaka a tsakaninsu da mutanen birnin Lailatus Hurus walau ta aure ko ta zumunci haka zalika duk mutumin daya sake ya shiga cikin iyakarsu yayi farauta koya debo wani amfanin gona kona daji to kuwa bazai fito a raye ba saidai gawarsa ta dawo amma sai gashi Jarumi Zainur ya karya wannan alkadari nasu. Abinda ya faru ne a wata safiya sa'adda jarumi Zainur ya shiga daji domin yin farauta a wannan lokaci yana sanye da wata tsangalalliyar rigar fata iya cibiyarsa mai yankakken hannu,wandon jikinsa na fata ne dogo kuma matsatstse,takalman dake kafarsa ma na fata ne masu madauri iya gwiwa yana ruke da wata baka babba mai kyau da daraja kuma ya rataya kuttun kibiyoyo a bayansa. A gefen cinyarsa ta hagu da dama akwai wadansu gajerun adduna guda biyu a daure kuma a cikin kufensu da yake Allah ya yiwa Yarima Zainur kira mai kyau gashi dogo kuma mai matsakaicin kaurin jiki ga tarin gwanji kuma a murde yake duk wanda ya ganshi a wannan lokaci sai ya burgeshi kuma sai yayi masa kwarjini.Saida yarima Zainur ya shafe kusan sa'a hudu a cikin dajin yana farauta amma bai hadu da wata dabbar kirki ba face kananun dabbobin daji kamar zomaye da tsuntsaye,al'amarin daya bata masa rai kenan domin a rayuwarsa babu abinda yakeso idan ya shiga farauta face ya hadu da babbar dabba irin su zaki,kura,damisa da sauransu wadanda zai fafata dasu ya murkushe su da karfin tsiya ya kashe sannan ya murkushe su da karfin tsiya ya kashe sannan ya fede su ya kwashe abubuwan dake da amfani a jikinsu yakai su kasuwa ya siyar.Wani lokacin kuma dabbar da ranta zai daureta ramau ya sabota a kafadarsa ya shiga da ita cikin gari saidai kaga jama'a nata binsa du....ana mamakin irin wannan tsananin jarumtaka tasa. Sa'adda Yarima Zainur ya shafe kusan sa'a hudu yana farauta ya sami nasarar harbo wani tsuntsi daga sama koda tsuntsun ya fado kasa matacce sai murna ta kama Zainur saboda dama a wannan lokaci ya fara jin yunwa nan take Zainur ya fige tsuntsun tas sannan ya shiga hada wuta ya fara gashi,shi dai wannan tsuntsun kato ne mai tsoka sosai,kuma namansa yana da matukar dadi da tsada a kasuwa koda tsuntsun ya fara gasuwa yana digar maiko sai Yarima Zainur yaji alamin takun sawaye a bayansa,cikin hanzari ya mike tsaye ya zare addunansa guda biyu yana mai gyara tsayuwa dif sai yaji shiru wato takun sawun ya dauke tamkar daukewar ruwan sama.Zainur ya cigaba da tsayuwa a inda yake batare daya motsa ba,kwatsam sai yaga wadansu arnan daji sama dasu dari bakwai suna fitowa gaba dayansu kawai sai babbansu wani narkeken kato abin kwatance ya tunkari inda wannan tsuntsu na Zainur yake,kawai sai ya dauke tsuntsun ya yagi cinya guda ya kuma ci,al'amarin daya fusata yarima Zainur kenan ya dakawa narkeken katon tsawa yace dashi ya aje masa namansa kada ya cinye.Koda jin haka sai katon ya dubi sauran yan uwansa ya tuntsire da dariyar mugunta maimakon ma ya ci gaba da cin naman tsuntsun sai ya jefa naman cikin wani bakin ruwan tabo ya tattakeshi da kafafunsa kuma ya cigaba da kyalkyalawa Zainur dariyar mugunta. A wannan lokaci ne fa jikin Yarima Zainur ya kama tsuma kamar maijin sanyi zuciyarsa kuwa ta kara tafarfasa kamar zata kone,kwatsam ba zato ba tsammani sai arnan dajin sukaga Zainur ya daka tsalle sama daga inda yake tsaye tamkar an cilloshi daga cikin BAKA,kafin wani daga cikin arnan dajin yayi wani yunkuri tuni Zaiyanu yasa addarsa ya sare wuyan wannan kato wanda ya bata masa naman daya gasa,take kan katon yayi sama a lokacin da jini yayi feshi daga cikin dungulmin wuyan ya bata wasu daga cikin yan uwansa.Koda ganin abinda ya faru sai ragowar arnan dajin suka afkawa yarima Zainur gaba dayansu sukayi masa rundugu da niyar suyi gutsun gutsun da sassan jikinsa. Kaico tsautsayi ba'a sa masa rana kuma ita masifa a kwance take duk wanda ya tsokanota akansa takan kare,koda Yarima Zainur yaga wadannan miyagun arnan daji masu naci kamar suci babu sun afko masa gaba dayansu sai ya durkushe kasa yayi wata irin katantanwa yana mai zabtare musu kafafu a lokaci guda kuma ya doki kasa da hannunsa guda yayi tsalle a sama kai kadan ya fafe cikin da yawansu da addunansa biyu,sai gashi ya tarwatsa su da karfin tsiya,ai kuwa sai ya sami dama ya rinka kutsawa ta cikinsu yana sara da suka cikin wani irin bakin zafin nama tamkar jikinsa bana jini da tsoka bane,duk inda yasa gabansa saidai kaga maza na zubewa kasa kamar ana sassabe a gona. Babu abinda

Chapter 1 of 15