Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya kure sai ya tada sallar har saida yayi raka'a biyu sannan ardadu ya fito da hannunsa rike da wandonsa alamar yana daure mazarin wandon.Nan ya zauna yayi alwala kamr yanda Yazid ya koyar dashi,da yake Yazid basa kan hanya har wadannan mahaya sukazo suka wuce yazid bai lura ba haka suma basu lura dashi ba. Bayan sun kammala sallah sai Yazid ya dubi ardadu yace wai ina kaje ka dade haka? Dajin haka sai Ardadu ya danyi murmushi yace ai cikina ne ya murda dan har saida na kosa da tsugunno. Yarima ya dubeshi sosai cikin rashin yarda yace ban yarda dakai ba yakai ardadu ka sanar dani gaskiya. Ardadu yayi murmushi yace wacce gaskiya kuma ai batun boye boye ni dakai ta kau bazanyi sata ba bazanyi cuta ba haka bazan ci zarafin kowa ba,wannan shine alkawarin dake tsakanin nidakai kuma bazan saba maka ba. Koda jin haka sai Yazid ya danyi shiru yace idan ka saba fa wane hukunci zan dauka akanka? Ardadu dajin haka sai shima yadan yi shiru gami da duban Yazid da murmushin yake yace,ka hakura da tafiya dani kamar yanda kaso hakura a baya. Ni bazan hakura da tafiya dakai ba domin ka zamo wani jigo na wannan tafiya,hukuncin dazan dauka daishine idan harka saba to babu shakka yaki zamu sakeyi dakai sabo wanda babu wanda zai rabamu saidai mutuwa. Koda Ardadu yaji wannan batu sai gabansa ya fadi take ya dubi Yarima Yace a'a gaskiya a wannan ba hukunci bane yakai shugabana kadai samu wani. Yarima Yazid ya girgiza kai yace ba shawara na nema daga gareka ba babu abinda zai hana haka face ka kadaita zuciyarka da aikata sabawa mahaliccinka. Ardadu yayi shiru yana tunani daga bisani ya dago kai ya dubi Yazid yace amma...sai yayi shiru da bakinsa Yazid bai damu da tambayarsa abinda yayi niyar fada ba sai suka cigaba da tafiya,basuyi nisa da tafiyar ba sai Yazif ya dubi ardadu yace,menene labarin WASIKAR JINI? koda jin wannan tambaya sai Ardadu ya fadada murmushinsa domin tun dazu abinda yakeson yaji Yarima ya tambayeshi kenan,amma yayi shiru yayi biris,nan take ya gyara baki yace,WASIKAR JINI wata wasika ce da aka samar da ita ta hanyar yin tawada da jinin wasu manyan jarumai da suka shude su tara a cikin kasar latul harus,itadai wannan wasika da itane ya jawo habbakar arzikin kasar latul harus kuma da ita ne sarki aiyuba yake takama domin shi kadai ne ya samu ikon karantata saidai ayanzu akwai waziri ridwan da kuma dansa Zainur suna nan suna shirye shiryen neman wannan wasikar su karantata.Idan har waziri ridwan ya karanta wannan wasikar to birnin latus harus zai wargaje,zama lafiyarsa zai bankwana tashe tashen hankula zasu tsaya kaida fata a cikin birnin wanda mu barayi wannan itace damar da muke nema domin muyi +Abbas Abdulkadir hada hada+.wadaka.Koda Yarima Yazid yaji wannan batu saiya daka masa tsawa da cewa kai ka manta a wane matsayi kake yanzu da kake kiran kanka da barawo? Koda jin wannan batu sai Ardadu ya tsuke bakinsa sannan yace tuba nake ya shugabana ina amfani ne da shirinmu na baya.Yazid yayi shiru yace ina saurarenka.Nan take Ardadu yacigaba da sanar dashi in kuwa har yarima zainur ne ya samu damar mallakar wannan wasikar har ya karanta ta to birnin Lahul harus zai kasance cikin zaman lafiya da lumana. Koda Yarima yaji wannan batu sai Ya dubi Ardadu yace idan ni ne kuma na mallaketa? Dajinwannan batu sai Ardadu ya tuntsure da dariya saida yayi ta isheshi sannan ya dubi yazid tace ai ko a mafarki bana jin zaka iya mallakar wannan wasikar domin kuwa yarima Zainur da mahaifinsa sune kadai suke da damar da zasu iya daukar wannan wasikar harsu karantata kai kuwa baka da karfin da zaka gwabza dasu har ka hanasu dauka, idan kuwa a misali ka dauki wannan wasikar to baka da damar yin aiki da ita domin kuwa bazata taba yin amfani a gareka ba domin baka kasance jinin sarautar kasar latul harus ba. Koda jin wannan batu sai Yarima Yazid shima ya tuntsire da dariya wannan dariya ita ta saka Ardadu shiga tsananin mamaki ya dubi yazid yace ya shugaba na ina dalilin wannan dariya ahalin da nake sanar dakai mummunan al'amari. Dajin haka sai Yarima Yazid yayi murmushi yace ba komai ne ya bani dariya saida kake sanar dani wahalar mallakar wani abu daga cikin kasar mushrikai matsafa,meye abin wahalar raba arne da makami? Da zuwa nan a batun Yazid sai Ardadu tace ai kuwa wannan arne ba karamin takadir bane domin kuwa dukkaninsu sun fika kyakyawar hanyar da zata kaisu ga samun wannan wasikar domin kuwa shi yarima zainur zai samu taimako daga wata kankanuwar yarinya dake dajin dake makwobtaka dasu,shi kuma waziri ridwan zai samu taimako ne daga tsafi da kuma amininsa sarki Marwatu,kai kuma naga baka da wani taimako daya wuce nawa ni kuwa bani da karfin dazan iya kallon wannan zarata da niyar yin yaki dasu. Dajin haka sai Yazid ya daga yatsansa daya ya nuna sama yace hakika babu abin bauta face UBANGIJIN MUSULUNCI ni ko kai babu abin dogaro a cikin wannan tafiyar ubangijin daya haliccemu ya halicci duniya da duk wani abu da yake cikinta shi zai bani ikon daukar wannan wasika kuma ba burina na karantata ba burina na hana azzalumai yin aiki da ita dan haka muje zuwa. Koda gama fadin hakan sai yarima yayi gaba shi kuma Ardadu ya bishi a baya har suka isa wani guri da dawakai guda biyu suke tare da tarin dukiya a gefe ga abinci. Da ganin wannan dukita sai Yarima ya dauke kai shi kuwa Ardadu sai ya dubi Yazid yace ya shugabana ina dalili zaka dauke kai daga kyauta da ubangijin musulunci ya bamu,lallai wannan kyauta ce daga gareshi domin kawo mana dauki a bisa tafiyarmu. Yazid ya dubeshi yace bata haka ubangijinmu yace mu nema ba,wannan dukiyar wani ce ba tamu ba dan haka kada ka kuskura ka taba su kazo mu cigaba da tafiyarmu. Koda jin wannan sai Ardadu yace kada kayi haka yakai Yazid wannan dukiya da dawakai bana kowa bane face na wadannan mahayan da suka nufo mu ni na ruke su suka bani kaga kuwa idan har muka tafi muka barsu anan zasu mutu su bushe ko barayi su sace su dan haka kazo mu tafi dasu. Dajin wannan batu sai Yarima Yazid ya dakata ya nufi Ardadu ya zare gatari da takobin da suke jikinsa ya mike masa daya yace babu abinda zai rabani da kai sai mutuwa yakai wannan mayaudari macuci maha'inci. Koda fadar haka sai yaja da baya ya tsaya yana jiran Ardadu amma ardadu ko motsi baiyi ba ganin haka yasa Yazid ya daka tsalle ya nufeshi. YAUSHE NE SARKI AIYUBA ZAI FADI YA MUTU? TSAKANIN YARIMA ZAINUR DA WAZIRI RIDWAN DA KUMA YARIMA YAZID WAYE SAI SAMI NASARAR GANIN WASIKAR JINI? WANE MATAKI SARKI MARWATU ZAI DAUKA IDAN YA FARFADO DAGA SUMA DA YAYI YAGA AN GUNTULE MASA BABBAN DAN YATSANSA NA HAGU? SHIN WANE IRIN BAKIN YAKI ZA'A KWAFSA TSAKAKIN ARDADU DA YARIMA YAZID? Mu hadu a WASIKAR JINI littafi na uku don jin cigaban wannan labari. Ina mai baku hakuri na rashjin jina jiya da kukayi saka makon rashin chaji a wayana. Da patan zakumin uzuri, in Allah yakaimu anjima da dare ina dauke da cigaban littapin ammana sai naga masuso da yawa. WASIKAR JINI!!! Littafi Na Uku (3) Part A . Lokacin da Yarima Yazid ya dako tsalle sama ya kaiwa Ardadu Mugun sara da addarsa sai Ardadu yai sauri ya kare saran don ceton rayuwarsa amma sai Yazid yasa kafarsa ta dama ya doki cikin Ardadu. Take cikin nasa ya kulle ya fadi kasa yana murkusu gami da kuma kallon wuya a lokacin da numfashinsa ya kama sarkewa kamar zai mutu.Har Yarima Yazid ya sake daga addarsa sama zai fille kan Ardadu cikin tsananin fishi sai kuma ya fasa,cikin sanyin jiki Yazid ya ajiye addarsa sannan ya dubi Ardadu cikin alamun tsananin takaici yace abinda ya hanani kasheka yanzu abu daya ne kuma ba wani abu bane face kai musulmi ne.Babu wata hujja da zatasa musulmi ya kashe dan'uwansa musulmi face ya aikata zunnubin daya cancanki kisa. Ayanzu kai ka aikata laifin sata don haka hukuncin laifin sata zan maka yanzu. Kafin Ardadu ya budi baki yace wani abu tuni Yarima Yazid ya shammace shi ya sare wuyan hannunsa na hagu,nan take Ardadu ya kwala uban ihu lokacin da hannun nasa ya guntule kuma jini yai tsartuwa kawai sai Ardadu ya sulale kasa sumamme. Lokacin da Ardadu fardado daga suman da yayi saiya tsinci kansa akan doki guda,doki na tafiya dashi a gefensa kuma Yarima Yazid ne bisa wani dokin.Suna hada idanu sai Yarima Yazid yayi masa murmushi yace,yakai Ardadu ina tayaka murna bisa sauke nauyin zunubin dake kanka na sata,ka sani cewa idan ka sake yin sata zan sake sare daya hannun naka lafiyayye ka zamo cikakken kuturu mara yatsu goma.Kana gani dai yanzu ka rasa yatsu biyar saboda haka sai ka kiyaye,koda jin wannan batu sai hawayen takaici ya zubowa Ardadu yace,yanzu ashe har hukuncin sata yakai matsayin a yankewa mutum hannu? Yarima Yazid yace kwarai kuwa ai sata babban laifi ne a addinin musulunci saboda ayi nuni da haka ne akayi wannan hukunci mai tsauri.Koda gama fadin hakan sai Yarima Yazid yai shiru bai kara cewa komai ba,shi kuwa Ardadu banda kukan zuciya da tsananin bakin ciki babu abinda yake fama dashi a cikin ransa. Haka dai suka cigaba da tafiya ba sassauci suna masu durfafo birnin latul harus domin gano a inda wasikar jini take. Acan cikin birni na latul harus kuwa lokacin da sarki marwatu ya farfado daga suma da yayi sakamakon babban dan yatsansa na hagu da sarki Aiyuba ya guntule masa sai ya mike zaune zumbur kamar wanda ya farka daga mafarki mai ban tsoro ya kama waige waige gami da duban dakin da yake ciki a lokacin da yake kokarin tunani domin ya gano waishin abindake faruwa a gareshi mafarki ne ko kuwa gaske ne kwatsam sai yaji an turo kofar dakin an shigo.Ba wani bane ba ya shigo face Waziri Ridwan fuskarsa cike da annuri nan take sarki marwatu yayi dogon ajiiyar zuciya ya dawo cikin haiyacinsa kuma a lokacin ne ya tuno da duk abinda ya faru tsakaninsa da sarki Aiyuba a fada,cikin firgici ya daga hannunsa na hagu,koda yaga babban dan yatsansa na hagun a guntule sai ya takarkare ya kurma uban ihu.A lokaci guda kuma ya fashe da kukan bakin ciki,koda ganin haka sai waziri ridwan ya zauna akan gefen gadon da sarki marwatu yake ya dafa kafadarsa yace kwantar da hankalina yakai abokina kayi sani cewa kada mage ba yanka bane,tabbas yanzu sarki aiyuba ya sami lagonka tunda ya rabaka da gaba daya sirrikanka na tsafi kuma ya wulakantaka ya tozarta darajarka a gaban mutane amma ka sani cewa lokaci zaizo wanda zakayi ramuwar gayya. Na sani cewa bazaka iya daukar fansa ba akan sarki aiyuba amma zaka iya dauka akan 'yarsa gimbiya Nauwara kuma ina mai tabbatar maka da cewa wannan lokaci yana daf da zuwa,sa'adda waziri ridwan yazo nan a zancensa sai sarki marwatu ya dubeshi cikin alamun kaduwa da tsananin mamaki yace yakai tsohon abokina menene hujjarka ta cewa wannan lokaci yana daf da zuwa? Koda jin wannan tambaya sai waziri ridwan ya kyalkyale da dariyar mugunta lokaci guda kuma saiya turbune fuska yace bincike ya nuna mana cewa sarki aiyuba na dauke da cutar ciwon zuciya kuma ba komai bane ya haddasa masa wannan ciwo ba face bakin cikin sani cewa 'yarsa gimbiya Nauwara bazata taba gadar karagar mulkinsa ba.tabbas sarki aiyuba yaso ace 'da namiji ya haifa ba mace ba,na sami labarin wannan cuta tasane daga bakin babban likitansa wanda ya aminta dashi dari bisa dari abinda bai sani bashine a duniya bashi da makiyin da yafi wannan likita nasa saboda maganin ma da yake bashi yana sha yana karawa cutar karfi a hankali ba tare da ya ankara ba.Koda jin wannan batu sai mamaki ya kara turnuke sarki Marwatu yace yakai abokina menene ya haddasa kiyayya tsakanin sarki aiyuba da wannan liktan nasa harda yake yi masa wannan mugun tanadi? Koda jin wannan tambaya sai waziri Ridwan ta sake bushewa da dariyar mugunta a karo na biyu sannan yace ai labarin ne mai tsawo kayi hakuri Zan baka wannan labari nan gaba idan lokacin daya dace ka sani yayi,abinda nakeso dakai yanzu shine kayi shiri ka koma izuwa kasarka ka cigaba da tafiyar da harkokin mulkinka kamar yadda ka saba kada ka kuskura ka nunawa talakawanka gajiyawarka harsu gane cewa yanzu baka da karfin sihirin tsafi,ka sani cewa kowa yana tsoronka a kasar taka ko dan saboda karfin damtsenka da iya yakinka,ka cigaba da hakuri har izuwa lokacin da hakanmu zai cimma ruwa,da zarar sarki aiyuba ya fadi zan aiko kazo cikin gaggawa domin musami damar cika burinmu.Koda jin wannan batu sai sarki Marwatu ya dubi waziri ridwan cikin alamun mamaki yace bangane abinda kake nufi ba,zaka kirani bayan ya fadi,kana nufin da zarar ya kwanta rashin lafiya ko kuwa da zarar ya mutu? waziri Ridwan yayi ajiyar zuciya yace ai da zarar ya kwanta rashin lafiya a lokacin da ciwo yayi tsanani zanyi wata gagarumar ta fiya neman wasikar jini,dole saina sami wasikar jini na karantata sannan zan iya hawa karagar mulkin kasar nan,a halin yanzu duk duniya babu wani mahaluki wanda ya isa ya iya karanta wannan wasikar jini har ya iya zama sarki a wannan kasa tamu kuma ya mallaki wannan dukiya mai tsananin yawa ta sarki aiyuba face ni da dana yarima zainur,amma duk yadda zanyi saina tabbatar da cewa hannu na ya riga na dana kaiwa kan wasikar jini. Koda jin haka sai sarki marwatu ya jinjina kai cikin alamun mamaki yace to waishin yanzu kenan kai da danka zaku iya zama ABOKAN GABA. Waziri Ridwan ya turbune fuska yace kwarai kuwa kuma idan harna gama yana nema ya zarce mini matsala zan iya kawar dashi.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke sarki marwatu yace haba yakai abokina yarima zainur nefa dakai danka a duniya. Waziri Ridwan yayi dan guntun murmushi yace nasan da haka aini a wajena dashi da babu duk dayane tunda tsakanina dash babu wata shakuwa kuma yafi kaunar makiyana fiye dani. Sarki marwatu ya gyada kai a lokacin daya mike tsaye yace babu matsala zan zauna a cikin sauraron jin sakonka kuma ina mai tabbatar maka da cewa zan baka dukkan gudunmawa wajen ganin burinka ya cika amma ka zamo mai cika alkawari a gareni. Waziri Ridwan yayi 'yar gajeriyar dariya yace kada ka damu yakai abokina lallai zaka sameni mai cika alkawari shin yanzu kana da wata bukata da kakeson a biya maka kafin ka tafi izuwa birninka? Sarki marwatu yayi ajiyar numfashi yace kwarai kuwa inada bukata guda daya inason ka turo mini sarkin makera na garin nan akwai abinda nakeson ya kera mini kafin na bar garin nan naku.Koda jin wannan batu sai waziri ridwan yayi murmushi yace nasan abinda kakeso a kera maka kuma kayi babbar dabara domin ta hakane kadai zaka kawar da tunanin mutane akan abinda ya sami babban dan yatsanka na hagu ka tafi izuwa masaukin naka yanzu nan zan turo maka sarki makera.Gama fadin hakan keda wuya sai sarki marwatu yayi murmushi sannan ya juya ya fice daga cikin turakar. Lokacin da sarki ya isa masaukinsa sai dakarun dake tsaron masaukin suka tareshi da albishir na cewa sarkin makera na zaune a cikin falonsa yana jiransa.Cikin tsananin mamaki sarki marwatu ya jinjina kai kawai saiya kunna kai cikin babbar turakar yana murmushi yana shiga kuwa yayi arba da sarkin makera zaune akasa bisa kilishin dakin. koda sarkin makera ya ga sarki marwatu tsaye a kansa sai ya zube kasa wanwar ya kwashi gaisuwa sannan yace ya shugabana na amsa kiranka me kake bukata daga gareni? Sarki marwatu yayi murmushi yace yakai sarkin makera kayi sani cewa ina da bukatar ka kera mini hannu na karfe wanda zan sanyashi akan hannuna na hagu kuma na iya sarrafashi ba tare da ido ya gane cewa na sanya hannun ba. Koda jin wannan batu sai sarki makera ya jinjina kai yayi shiru tsawon yan dakiku kadan sannan ya dubi sarki marwatu cikin biyayya yace ya shugabana wannan aiki ne mai wahala wanda ba'a taba yin irinsa ba kuma zaici kudade masu yawa. Kodajin haka sai sarki marwatu yayi murmushi yace kudi ba matsala bane ko nawa ne ake bukata zan bayar,matsala itace tsawon kwana nawa zaka iya kammala wannan aikin? Sarkin makera yayi dan nazari sannan yace zan iya kammala wannan aiki a cikin sati daya da kwana biyar. Koda jin haka sai sarki marwatu ya kyalkyale da dariya sannan ya fiddo jakar kudi cike da lu'u lu'u ya yafewa sarkin makera ita batare daya kirga iya adadin lu'ulu"un dake ciki ba yace,ga wannan kaje ka fara aiki idan basu isa ba ka aiko na kara maka. Hannun sarki makera na rawa ya dauki jakar lu'ulu'u ya kama godiya kamar zai yiwa sarki marwatu sujjada ya mike tsaye yana mai cewa ya shugabana ai wannan kudi ya isa a kammala komai. Nan take sarki marwatu ya sallami sarkin makera ya tafi shi kuwa marwatu saiya zauna a turakar yayi tagumi yana mai fadawa cikin dogon tunani na bakin ciki da takaici, ba komai ne yaje fa sarki marwatu cikin wannan hali ba face jin batun wasikar jini.Ada ba komai sarki marwatu ke shirin yiba face yaudara gami da cin amanar abokinsa waziri ridwan,abinda ya aiyana aransa shine da zarar sarki aiyuba ya fadi ya mutu zai kawo harin bazata ya kama birnin da karfin tsiya kuma ya dare kan karagar mulkin sarki aiyuba,yanzu da yaji cewa bazai iya hawa karagar sarki aiyuba ba face ya karance wasikar jini kuma ya kasance jinin sarautar latul harus sai murna ta koma ciki kuma ya kamu da tsananin bakin ciki.Nanfa zuciyarsa ta kama sake sake ta kulla wannan ta kwance wance har sai da lokacin bari yayi,wato dare ya raba sosai amma sarki marwatu bai sami mafita ba ko shawara wacce zata fishshe shi,bisa dole sarki marwatu ya hakura da tunanin komai ya mike tsaye ya shiga cikin turakar ya kwanta kwanciyarsa keda wuya kuwa sai ya kama barci harda munshari. Al'amarin Yarima Zainur kuwa lokacin daya rabu da gimbiya Nauwara sai hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe a rayuwarsa,ba komai ne ya tayar masa da hankali ba face jin batu cewa shida mahaifinsa zasu zamo abokan gaba akan neman mulki,nanfa yarima zainur ya fara tunanin hanyar dazaibi ya hana faruwar wannan gaba amma daya nutsu a cikin tunanin nasa saiya gane cewa babu makawa sai wannan gaba ta kullu tunda daishi yana kishin kasar da kuma jama'arsu,shi kuwa waziri ridwan akan biyan bukatarsa zai iya siyar da kasar gaba daya,to waishin yanzu wane hukunci ya kamata na yanke? Shin idan lokacin tafiya neman wasikar jini yayi zan hana mahaifina yin tafiyar ne ko kuwa zan bar mu hadu acan wajen neman WASIKAR JINI ne in yaso muyi yaki dayanmu ya kashe daya. Koda Yarina Zainur yazo a zancensa zucinsa sai hawaye ya zubo +Abbas Abdulkadir Hada Hada+ masa nan take ya fashe da matsanancin kuka a wannan lokaci yana cikin kuryar dakin sane na gidan sarkin yaki haiman kuma a sannan dare ya raba sosai,yana cikin wannan hali ne kwatsam yaji an turo kofar dakin nasa a firgice bisa rashin tsammani ya dago kasan yaga wanda ya shigo ba wani bane face sarkin yaki haiman fuskarsa cike da alamun tausayawa a gareshi kuma idanunsa sun ciko da kwalla.Maimakon sarkin yaki ya budi baki yace dashi wani abu sai kawai ya zauna a gefen gadon nasa ya janyo shi izuwa kan kirjinsa ya rungumoshi sannan ya shiga rarrashinsa yana mai cewa,yakai dana kayi sani cewa ita kaddara ta riga fata babu yadda za'ayi wani ya iya sauya maka kaddararka nasan duk abinda yake damunka a yanzu amma shawara daya zan baka shawarata kuwa ba komai bane face ka tsaya kayi tunani da nazari a bisa duk irin hukuncin daya kamata ka yankewa kanka,lallai kada kasa son rai dason zuciya a cikin al'amuranka duk abinda zai cutar da kasarka da kuma mutanenka ka gujeshi wanda duk kasan cewa zai taimaki kasarka da jama'arka kuwa ka rumgumeshi ka soshi,koda yin hakan zai zamo sanadin rasa rayuwarka kasani cewa bana nufin ka cutar da wani naka saboda ganin ka cimma naka burin amma fa idan nine a matsayinka zan iya hakura da komai da kowa nawa don kare kasata da jama'ata saboda yin hakan shike nuni da shugaban dazai yi adalci. Lokacin da sarkin yaki Haiman yazo nan a zancensa sai mamaki ya turnuke yarima zainur kuma ya kamu da tsananin bakin ciki har idanunsa suka ciko da kwallah hawaye ya subuto masa ya dubeshi yace ya shugabana yanzu ashe duk kasan da wannan al'amari tuntuni amma baka sanar dani ba? Koda jin wannan batu sai shima sarki yakin idanunsa suka ciko da kwalla yace ka gafarceni yakai yarima hakika bazan iya sanar dakai wannan sirri ba saboda sarki ya gargadeni akan kada na sanar dakai din kuma ina mai tabbatar maka da cewa duk fadin garin nan mutum hudu ne kacal suka san wannan sirri daga sarki,sai waziri,sai gimbiya nauwara sannan kuma ni.Gama fadin hakan keda wuya saiga wani hadimin sarkin yaki haiman yazo kofar dakin da suke yayi gyaran murya,koda jin hakan sai sarkin yaki haiman ya fito da sauri ya dubi hadimin yace menene? hadimin ya risina cikin girmamawa yace ya shugabana ai sarki ne ya aiko yanzun nan yace a gaya maka cewa lallai ka hanzarta kaje gareshi,cikin kaduwa da mamaki sarkin yaki ya dubi hadimin yace lafiya kuwa sarki zai turo ayi kirana a cikin wannan tsohon daren? Ko harin bazata aka kawo mana?Hadimin yace a'a inda hari aka kawo da yanzu kaji an busa kahon yaki,dajin haka sarkin yaki bai tsaya bata wani lokaci ba sauya ruga izuwa inda bargar dawakai take yaje ya kwance doki da kansa ya daura masa sirdi yahau kuma ya zabureshi da gudu ya fice daga cikin gidan sarautar. Al'amarin Yarima Zainur kuwa lokacin daya sarkin yaki ya fice daga cikin gidan shima saiya fito daga cikim gidan ya nausa izuwa cikin gari ba tare da sanin ma inda ya dosa ba gashi dai dare ya raba garin tsit baka jin sautin komai face haushin karnuka da kuma sautin iska dake kadawa.Tsananin bakin ciki ne yasa Yarima Zainur ya kama tafiya a kasa da kafafunsa ba tare da sanin inda ya dosa ba yana tafe kamar mahaukaci sabon shiga yana kuka,duk da cewa yarima zainur bashi da wata shakuwa tsakaninsa da mahaifinsa saiyaji ya kamu da tsananin bakin ciki bisa jin cewar zai zamo abokin gabar mahaifin nasa,haka dai zainur yaci gaba da tafiya har ya durfafi kasuwa kai tsaye.Kasuwar tayi tsit tamkar babu mutum daya mai numfashi a cikinta alhalin kuwa akwai gidajen haya a cikin kasuwar inda baki ke kwana.Gaba daya gidajen dake cikin wannan kasuwa na hayane kuma mafi yawansu suna da bene.Lokacin da Yarima Zainur yazo giftawa ta tsakiyar kasuwar sai ya jiyo sautin muryar wani mutum acan saman bene ta cikin wata taga har zainur ya dangota tagar sai ya dawo da baya ya tsaya kuma ya kasa kunne domin yaji abinda mutumin yake fada,tunda yarima zainur yazo duniya bai taba jin sauti mai dadi wanda kunnuwansa keji ba a yanzu ba,sauti ne kamar na waka ko kuma karatu cikin wadansu irin kalmoni na hikima a daraja,nan take yarima zainur yaji wadannan kalmomi sun ratsa zuciyarsa don haka sai yaji babu abinda yakeso sama da ganin mutumin da wadannan kalmoni ke fita daga bakinsa,bisa wannan dalili ne yarima zainur ya durfafi kofar gidan da yake jiyo sautin karatun domin ya shiga kuma ya hau harkan saman benen,da zuwa sai yasa hannunsa ashe kofar a bude take don haka saiya kunna kai ciki ba tare da shakkat komai ba.Ashe ba wani bane yake wannan karatun face Yarima Yazid kuma karatun alkur'ani yakeyi da farko ya fara karatun ne a cikin zuciyarsa amma a lokacin da shaukin karatun ya debeshi sai ya manta da cewa a cikin kasar kafurai yake don haka baisan yana karatun ba a fili kuma duk da cewar muryarsa akasa take saida ta fito waje ta cikin tagar dakin saboda kasancewar dare ya raba. A wannan lokaci Yarima Zayid na zaune ne akan wani farin buzu ya tankwashe kafafunsa kuma yana rike da littafin alkur'ani a hannunsa wanda yake karantawa,a gefensa na dama kuma daf dashi takobinsa ce ajiye a kas,agefen hagunsa kuwa Ardadu ne kwance akan shimfida yana ta fama sharar barcinsa harda minshari.Dama a can kofar gidan su Yarima Yazid suka daure dawakan nan nasu wanda Ardadu ya sato. Lokacin da Yarima Zainur ya turo kofar gidan ya shigo saida wadannan dawakai guda biyu suka dan tsorata sukayi haniniya.Jin haniniyar tasune yasa Yarima Zainur ya dora hannunsa guda akan kufen takobinsa domin a zatonsa barayi ne suka kawo ziyarar bazato.Koda Zainur ya shigo cikin gidan saiya wuce kai tsaye izuwa kan matattakar benen ya fara hawanta domin ya isa wannan daki inda yake jiyo sautin karatun kuma karar takun sawun same akan matattakalar na cigaba da cika kunne amma ko a jikinsa,saida ya taka matattakalar karshe ya dora hannunsa akan kofar dakin da nufin ya turata sai kawai yaji hucin saran takobi a daidai kunnensa.Cikin bakin zafin nama Yarima Zainur ya sunkuya takobin Yazid ta sari iska amma kafin yayi wani yunkuri tuni Yazid ya sake kawo masa wani saran a ciki da nufin ya tsargeshi gida biyu,aikuwa in badon Zainur ya daka tsalle yabar wajen ba da saidai wani bashi ba. Aikuwa sai takobin ta dara matattakalar suka rikito kasa tare,karar rugujewar matattakalar benen tasa Ardadu da sauran mutanen dake cikin gidan suka farka daga barci a gigice.Koda Zainur da Yazid suka fado kasa daga kan matattakalar benen sai sukayi wuf suka mike tsaye zumbur ba shiri.Shima Yarima Zainur ya zaro takobinsa domin ya kare kansa,nanfa suka kacame da azababben yaki ya zamana suna kaiwa junansu sara da suka cikin tsanamin zafin nama, juriya da bajinta. WASIKAR JININ!!! Littafi Na Uku (3) Part B . Cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta,nanfa suka banko kofar gidan ta karye suka fado wajen gidan suka dada mikewa tsaye zumbur suka cigaba da bakin artabu kowannensu yana yin wannan yaki ne iya karfinsa da ransa da jikinsa. A tunanin Yarima Yazid yana yaki ne da rikakken dan fashi wanda ya saba kaiwa fatake hari,shi kuwa Yarima Zainur sai ya dauka cewar yana yaki ne da dan leken asiri daga wata kasar koma wannan karatu da yaji wadansu dalamisai ne na tsafi ake karanta su domin a cutar da birninsu. Lokacin da aka cigaba da wannan mamakin yaki tsakanin Yarima Zainur da Yarima Yaizd sai mutane sukayi ta firfitowa daga cikin gidaje suna kallon ikon Allah amma a tsorace,adaidai wannan lokaci ne Ardadu ma ya fito da gudu daga cikin gidan shima ya saje a cikin yan kallo yana baiwa idanunsa abinci. Saida Yarima Zainur da Yarima Yazid suka shafe sama da rabin sa'a suna bakin artabu mai tsananin ban tsoro da tashin hankali ba tare da dayansu ya sami nasarar koda lakutar jikin daya ba,kwatsam sai kowannensu ya samu nasarar dora tsinin takobinsa akan wuyan dan uwansa amma sai suka ki cutar da juna suka tsaya suna kallon kallo,sannan ne ma suka lura da cewa sun tara yan kallo.Koda sarkin kasuwa ya kyallar ido yaga ashe da yarima zainur akeyin wannan gumurzu da kuma bako yarima yazid saiya ruga da gudu yace yakai Yarima menene ya hada ka fada da fatakenmu haka? Koda jin wannan batu sai jikin zainur dana yazid yayi sanyi, yazid ya dubi zainur cikin biyayya a lokacin daya sauke takobinsa daga kan wuyan zainur yace ka gafarceni ya shugabana kayi sani cewa na yake kane saboda ina zaton ko dan fashi ne yake kokarin shigowa dakinmu. Koda jin haka sai Yarima Zainur yayi murmushi shima ya sauke takobinsa daga kan wuyan Yazid ya dubeshi yace nima nayi zaton ko kai dan leken asiri ne daga wata kasar mai shirin cutar da kasar nan sakamakon

Chapter 5 of 15