Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kwanciya yaji kumarinshi ya fara dawowa yanzu ya fara jin baiyi asarar zamowa mai kwazo ba sabanin a baya da yakeji tamkar shi ba kowan kowa bane a filin daga,duk irin kokarinsa na korar arnan daji da yanfashin da yakeyi sai yaji ya tashi a banza,amma yanzu da ibin Haisham ya fara nuna cewa suma zasu iya sai hankalinsa ya fara kwanciya.Ya tsurawa ibin Haisham idanuwa yana son jin abinda zaice takamar sarki Aiyuba. Ibn Haisham ya cigaba da cewa takamar sarki Aiyuba bai wuce rubutacciyar WASIKAR JINI ba.Wannan wasikar itace takamar sarki itace takamar duk wani mai neman daukaka a cikin wannan duniya.Bani da tarihin WASIKAR JINI amma ina da sani cewa itace karfin sihirin sarki Aiyuba itace takamarsa itace sirrin birninsa tabbas idan waninmu ya mallaki wannan WASIKAR JINI to babu shakka duk irin takamar sarki Aiyuba da bunkasarsa da wani kuri nashi sai ya saurara kuma sai yayi shayinka,dan haka kafin cikar wannan rana da tsufa bai riskeni ba sai naje kasar na samu wannan wasikar domin na dawo da ita cikin wannan al'umma tamu ta musulunci tabbas idan yayi bincike ya gano cewar wannan wasikar tana cikin wannan kasar,sai ya hakura da duk wani mugun nufi a garemu sannan kuma zamu juyashi yadda mukeso kamar yadda ya juya ragamarmu,inda ace wannan wasikar zata samu da basai mun sha wahala mun gwabza yaki dasu ba,da zarar sunji tana garemu hankulan baki daya nahiyar nan zai tashi kamar yadda aka maida mu makaskanta sai mun zo mun zama babu sama damu.Abin takaicin da kaico babu yanda zamuyi mu dauko wannan wasikar,amma da akwai samartaka a tare dani babu abindazai hana ni yin shiri na tunkari kasar Lautul Harus dan na dauko wannan wasikar. Koda jin wannan batu sai baki daya jama'ar dake gurin sukayi shiru suka nutsu suna kallon Ibn Haisham shi kuwa Yarima Yazif sai ya mike tsaye ya dubi kowa dake cikin fadar sannan ya tsayar da kansa ga kallon Ibn Haisham yace,zuciyata bata karaya,kuma ban fansar da rayuwata ga tsoron kafurai ba,zan iya duk abinda ya kamanayi dan fansar daukacin al'umma ta,yakai wannan babban malami ina mai tabbatar maka da cewa a shirye nake dana yi JIHADI dan haka na shirya yanzu haka danayi jihadi dan haka na shirya yanzu haka ka sanar dani labarin WASIKAR JINI nayi alkawari da yardar Allah ina nan tafe da ita a cikin kwanakin da suka rage mana. Koda jama'ar dake fadar sukaji wannan batu sai suka dinga kallon kallo suna masu mamakin yarima ba don komai ya cikasu ba face shi yarima tunda ya taso baya kaunar fita koda wajen kasar dukda ya kasance gagarumin sadauki bayason fita ko ina koda yan fashin sumame ne suka kawo hari zuwa cikin kasar da ya ratattakesu zuwa bakin ganuwar garin shikenan sai ya dawo bai taba takawa yabar cikin kasar ba tunda aka haifeahi kawo iyanzu bai san ko ina ba. Waziri ya dubi Yarima Yazid yace,yakai Yarima shin kasan inane kasar Latul Harus kasan kuwa hadarin da yake ciki ballantana kaje da zummar daukar abu mafi daraja daga garesu tabbas idan kayi wannan gangancin kamar kana kokarin neman tsayawar numfashinka ne, yakai Yarima kayi hakuri kayi zamanka anan domin mahaifinka yana halin MUTUWA KO RAYUWA ka duba halin da mahaifinka yake ciki mana,idan kayi la'akari da irin halin da yake ciki na mutuwa da rayuwa bai kamata ace kaima ka rasa rayuwarka a kasuwar daukar rai ba. Koda jin wannan sai Yarima ya sunkui da kai daga bisani ya daga kai yace,duk abinda zai faru rubutaccene daga Ubangijinmu,zamana a cikin wannan kasa tamu ta Haura bata da wani amfani inaso ka sani mahaifina yana cikin tsananin rashin lafiya wanda bazai samu kansa ba sai washe garin gobe inkuwa ya farka duk yanda akayi aka sanar dashi abu mara dadi babu shakkar likitansa ya tabbatar min da zai iya rasa rayuwarsa, dan haka ya zama dole koda rundunar mayakan kasar Latul Harus zasu tunkaromu na fita na tare su dan gudun kada su shigo cikin kasata har abbana ya farga da halin da ake ciki hankalinsa ya gushe zuciyarsa ta buga ya fadi ya mutu,dan haka ya zame min dole nayi wannan fita a yanzu. Koda Yarima Yayi wannan furucin sai ya fice daga cikin dakin taron bai zame ko ina ba sai a cikin gidansu koda ya isa sai ya riske mahaifiyarsa a zaune a kusa da mahaifinsa tana risgar kuka Yarima ya risina a kusa da ita duk abinda ya faru ya kwashe ya sanar mata.Koda jin haka sai ta dubeshi tace,kai kuwa ta yaya kake hangowa kanka nasara baya ga kaji irin hatsarin da yake cikin kasar sarki Aiyuba,yakai dana mafi soyuwa a raina wannan abu da kake kokarin yi tamkar kana neman tarar aradu ne.Koda jin wannan batu sai Yarima ya dubi umman tasa sannan ya nuna mata mahaifinsa dake kwance rai a hannun Allah yace,wannan Abba nane akwance mutuwa yau ko gobe,ya ummina kina sane da cewa idan Abbana ya farfado kafin cikar wa'adin da likita ya sanar damu ba tabbas sai rundunar sarki Aiyuba ra cika mana kasa ta batse ta yaya kunnuwan sarki zasu rufe daga jin sautin karar karafkiyar takubba,ta yaya kunnensa zai kange daga jin karar tafiyar kibiyoyi, ya ummina abinda nakeson sanar dake shine babu abu mafi masalaha face nayi tattaki zuwa kasar Latul Harus domin na nemo abinda zai zamo garkuwa a tsakaninmu da zaluncin sarki Aiyuba,babu abinda nake bukata daga gareki face ki samin albarka ya ummina inaji a jikina akwai alamar samun nasara a kudirina. Koda yazo nan sai tayi shiru daga bisani tace,yakai dana ya zama dole na barka kayi wannan tafiya domin hujjarka tafi tawa saidai duk da hakan idan ka tafi kana sane da cewa akwai kananun ayari ko dodannin da suke kawo bara a garemu,yanzu idan sukaji maganar tafiyarka kasan saisun addabemu da kawo hari,in kuwa zasu ci gaba da kawo hari to babu shakka sai wata rana kunnuwan mahaifinka yaji kuma kasan abinda yake wakana daga lalurarsa,dole zaiji kuma zuciyarsa zata iya bugawa domin kuwa duk cikin kasar nan babu maharbin da ya wuce kai haka zalika babu wanda ya iya yakin sunkuru kamar kai,kai kadaine zaka iya yin karo da arnan daji na tsawon kwana biyu ba tare da wani yaji ba,saidai da wannan nake maka bankwana domin tafiyarka tafi zamanka alheri.Koda jin wannan batu sai yayi murmushi ya kuma sumbaci Abbansa ya shiga dakinsa yayi shigarsa ta mafarauta ya fice daga cikin gidan. Wannan shine dalilin fitowar Yarima Yazid daga gida. Dan haka ya cigaba da nausawa babu ji babu gani ko waiwaye bayayi,bashi da fata face yaga yayi tsinke a cikin kasar Latul Harus. Yarima Yazid yana cikin wannan tafiya saidaya zo wata kwana da idan ya bita shike nan ya daina hango ganuwar birninsu ya daina hango sashin kasarsu gaba daya,koda zuwa wannan kwanar sai ya waiga koda waigawaesa sai gabansa ya fadi,hankalinsa ya dugunzuma ya shiga cikin tsananin tashin hankali,bai tsaya bata lokaci ba ya fito da KWARI DA BAKANsa dake sakale a kafadarsa ya danata a cikin mashi ya koma da baya cikin tsananin gudu tamkar zai tashi sama. MAI YARIMA YAZID YA HANGO? SHIN INA LABARIN YARIMA ZAINUR? SHIN YARIMA YAZID ZAI SAMU DAMAR MALLAKAR WASIKAR JINI? SHIN MECECE MA WASIKAR JINI? Domin jin duk wadannan tambayoyi sai mu tara a littafi na gaba don jin amsoshinsu. Yakuka ce dan naga kamar ma littapin bai mukuba dan bana kallon commnt din masu cewa suna so. WASIKAR JINI!!! Littafi Na Biyu (2) Part A . LOKACIN da Yarima Yazid ya juya rike da gwafarsa daya danata sai ya kasance yana wani gudu mai abin al'ajabi duk inda yayi taku kamar sau arba'in a kasa saiya daka tsalle sama ya tafi a cikin iska,dan haka kafin kace meye wannan ya kusanci kofar ganuwar birnin Haurul.Ba komai yasa Yarima Yazid yin wannan gudu ba face wata kura data taso ta tokare sararin samaniya,kurar ta toshe kofar garin ta hada gagarumin hadari a daidai kofar ganuwar birnin Haural,tsilli tsilli idanuwansa ya fara hango masa ayarin dakarun yan fashi sunkai kimanin dubu goma,kowannensu rike yake da makami mai barazana ga rayuwar dan adam. Lallai wadannan ayarin yan fashi sun isa abin tsoro da ja da baya,duk wata jarumtakla idan tayi tozalo da irin girman wadannan ayarin na yan fashi da kuma tarin mangara mangaran makamansu dole shakku ya shiga cikin zuciyarsa amma abin mamaki yadda Yarima ke cin uban gudu bashi da buri face ya isa garesu ya hanasu shiga cikin birninsu ko ta tsiya tsiya. Amma koda ya kusanto su sosai sai suka banke kofar birnin suka daga makamansu sukayi kuwa akan dakarun da suke tsoron kofa.Nan take suka murkushe su cikin kankanin lokaci suka kama rufe kofar birnin suka ci gaba da nausawa cikin garin. Koda Yarima ya hango sun rufe kofar birnin sai hankalinsa ya tashi ainun amma da fushinsa ya kara ninkuwa ya tabbatar idan ya tsaya kokarin bude kofar zasu iya isa cikin birnin har suyi barna,sai kawai ya daka wani uban tsalle ya tashi sama kamar tsuntsu,koda yayi sama sai ya fara saki mashin daya dana tun fara hangowarsa dasu. . Jarumi Yazid gwarzon jarumi ne masanin iya yaki da gwafa wannan dalili ne yasa yake iya tarwatsa dakarun duk yawansu domin idan yana harbi da kibiya bazakayi tsammani mutum ne yake tabewa ba yana sakinta saboda tsananin karfin tafiyar kibiyar,a duk sa'adda ya saki mashi ya fita daga cikin gwafa baya faduwa kasa face ya soke mutum biyar ko shida. Idan kuwa a kuskure yayi harbin sai wannan mashin ya soke mutum sama da goma.Dan haka tun daga sama suka fara jin ana musu ruwan kibiyoyi,kafin su ankara mazaje sama da arba'in sun zube kasa matattu ko shurawa basayi.Dakarun ayarin yan fashin suka ja tunga suna masu mamakin daga inda akeyi musu wannan dauki ba dadi,kafin su ankara sai ga jarumi Yazid ya dira bisa kafafunsa a gabansu,Yana dirga sai ya kara dame gwafarsa ya sake jikin iska kafin ta isa garesu ya kara sakin wasu guda biyu. Aikuwa sai yanfashin nan suka ci gaba da zubewa kasa matattu.Koda shugaban yanfashin yaga irin barnar da Yarima Yazid yake yiwa yaransa sai yayi wata hatsabiyar kara ya yunkura ya cire wani katon katari da yake rataye a kubin rigarsa ya dagashi sama ya jinjina asama yayi kuwa ga jama'arsa nan take su duka suka afka kan Yarima Yazid.Shi kuwa sai yaja da baya ya zuba masu har guda biyar a cikin gwafar ya dame ya sakar masu,nan yake ya rage wasu daga cikin masu tunkaro shi. A sannan ne ya daka tsalle sama ya nufi ayarin yan fashin babu takobi ko gatari a hannunsa,amma yana isa garesu ya tari wasu karata su biyar ya sunkuya ya kwashe kafafuwansu cikin bajinta sukayi sama suka zube a kasa. Makamansu sukayi kasa.Koda ganin haka sai ya dauki takobi gami da wani gatari yana daukar wannan ya rike katamau nan take ya shiga cikinsu ya fara kuntata musu,cikin tsananin bajinta ya fara sare kawunansu yana sare su da gatarin hannunsa. Wohoho idan kaji ana sa gudu ki gudu ne bai zoba,nan take Yarima Yazid ya kuntatasu ya rage musu yawa duk inda yasa gaba saidai yan fashin masu kumari da kai bara sun koma suna rike kugu gami da yin warwas a kasa. Wannan al'amarin ba karamin tada hankalin shugaban yan fashin yayi ba domin yasan cewa dama inhar zasu yi karo da Yazid to babu shakka sai ya zame musu matsala,yadda yaga Yazid yake girbar yaransa tamkar ya hori kansa sai ya fusata ganin idan har yabar Yazid yaci gaba da karo da yaransa to babu shakka zai karar dasu ya zamana sun kasance su kadai a filin gurin wanda hakan ba karamin asara bace a gareshi,babban dan fashi wanda ake tsoro da gudu ace Yarima ya kunyata shi ya kama shi a matsayin ribatacce. Koda ya kada gatarinsa sama sai yayi ihu ya nufi Yazid a yayin da Yarima Yazid yake ci gaba da ragewa yan fashin yawa.Cikin shammata wannan katon shugaban yan fashin ya doki Yazid ta baya,saboda karfin dukan daya yiawa Yazid saida Yazid ya tafi da karfi yayi tafiya mai nisa sannan ya zube kasa dukkanin makaman hannunshi suka zube kasa.Da kyar Yazid ya iya dagowa ya dubi shugaban yan fashin,shi kuwa shugaban yan fashin sai ya daka tsalle ya nufo Yazid da niyar ya turmusheshi. Koda Yazid yaga shugaban yan fashin da irin wannan manufa sai ya mirgina gefe shugaban yan fashin ya daki kasa.Saboda tsananin karfinsa saida kasar gurin ta rabe gida biyu.Harsai da kafarsa ta shiga cikin kasa.Da kyar ya cireta ya dubi Yazid da fushi.Koda Sukayi kallon kallo cikin tsananin fusata sai Yazid ya karkade rigarsa ta kuma tofar da yawu,acikin yawun daya tofar ya lura da jini,nan take hankalinshi ya duguzuma cikin tsananin bacin rai ya maida kallonsa ga shugaban yan fashin shi kuwa shugaban yan fashin sai ya kece da mahaukaciyar dariya saida yayi dariyar ta isheshi sannan ya dubi Yarima Yazid yace,Yaro man kaza da kana tunanin akwai wata rana da nasara zata gabato maka yayin da kayi gaba da gaba da Ardadu shin kana tunanin akwai ranar da zaka tsira a lokacin da aka bakantawa Ardadu mai karfin doki saba'in,to ka kuka da kanka,domin kayi gamo da katar yau hallaka zata cudanya da rayuwarka zan tsawaitar da numfashinka.Koda Ardadu shugaban yanfashin yazo nan a batunsa. +Abbas Abdulkadir Hada Hada+ sai Yarima Yazid yayi murmushi ya daga hannuwansa sama ya hada su guri guda ya murda suka bada wani sauti kararas,ya girgiza jikinsa domin ya samu kwarin jikinsa koda gama wannan murde murden sai ya dubi Ardadu yace,wannan duka cika bakine yakai wannan kazantaccen mushriki azzalumi inason kayi sani cewa kai kadai kayi kadan dana gwabza yaki dakai abinda nake da muradi dakai shine kayi umarni da ragowar mutanen ayarinka domin kuyi dandazo zuwa gareni kuyi yaki dani mafi tsananin kwarewarku da hakane nake da kwarin gwiwar tunkararku amma sam kai kayi kadan nayi yaki dakai. Koda Ardadu yaji wannan mummunan lafazi daga bakin Yarima Yazid sai ya fusata cikin tsananin fushi yayi kansa cikin bakin kuduri. Koda ya iso gareshi sai ya daga gatarinsa yakai masa wawan sara babu ba gani sara Ardadu yake kaiwa Yazid amma yazid yana kauwacewa saran harsaida Ardadu yakai sara kusan sau tamanin da uku,a sannan ne yayi nasarar gogar Yarima Yazid da gatarinsa a dokin bayansa amma kuma kafin ya kara kai wani yunkuri tuni Yazid ya fusata yayi tsalle ya saka hannunsa ya kirbawa Ardadu naushi a fuska.Idanuwan Ardadu suka rufe cikin tsananin jin radadin zafi,ai kuwa sai ya kama dube dube dan kada Yarima ya shammaceshi ya kara gabza masa wani bahagon naushi,Kafin idanuwansa su bude Yazid ya kara daka tsalle sama ya dokeshi a kirji,duk irin girman da Ardadu yake dashi sai gashi saboda tsabar karfin dukan da Yazid yayi masa ya tashi sama tamkar wanda aka dauke shi da kugiya bai zame ko ina ba sai cikin dakarunsa.Da sauri ya taso cikin tsananin bacin rai ya dawo ga Yazid kafin ya karaso Yazid ya nufoshi yana isa gareshi ya kaucewa wani wawan naushi da Addaru ya kawo masa naushin yabi iska kafin Ardadu yayi mamakin rashin dalilin rashin sa'ar dayai sai Yazid ya kwashe kafafunsa yayi sama ya fado kasa yana fadowa Yazid ya take masa kirji.Nan idanuwan Ardadu suka zazzaro sukyi kuru kuru ya kasa daga kafar Yazid sai uban haki da nemo dauki yake,koda yaga cewar idan ya jima a haka zai iya asarar rayuwarsa sai ya daka wata tsawa ga dakarunsa nan take suka nufo Yazid da niyar su kamashi su cinyeshi danye.Kafin su karasa sai Yarima ya daga Ardadu yayi wulli dashi izuwa garesu. Koda sukaga shugabansu a sama yana reto sai suka yi yunkurin su tareshi amma koda yazo garesu sai suka kasa tareshi wanda suka nufeshi dan kai masa dauki duk saida suka karkaye saboda nauyinsa da kuma karfin dukan da Yazid yayi masa.Koda ganin haka sai suka ruga ga Yarima cikin fushi da dacin rai suna ihu suna kururuwa dauke da makamansu a hannunsa.Kafin kace meyewa wannan tuni gurin ya kara ya mutsewa cikin tsananin kwarewa da iya salon yaki Yazid ya dinga gididdibasu yana sokarsu tare da naushi da bugu da kafa da hannu.Aikuwa sunyi matukar tsananin danasanin tunkarar Yazid domin a tunaninsu akwai ayarin aljanun da suke kawo masa taimako saboda duka daya yake yiwa mutum sai kaga ya baje kasa ko shurawa bayayi.Cikin Azama kuma tamkar ba dan adam ba. Lokacin da akayi sa'a biyu a na wannan gumurzu sai gurin ya rage yawan kazaman yan fashin ya zamana bai wuce mutum goma ba daga shi sai ragowar ayarin su tara sai shugabansu da yake kwance sharkaf.Koda Yarima Yazid ya dakawa ragowar wadannan ayarin da suke rage a tsakiyar filin tsawa sai suka razana suka zube kasa ko shurawa basuyi ba,wannan ihun daya daka shine ya farkar da shugaban Ayarin koda mikewarsa saiya dubi Yarima Yazid yaga wayam filin gurin babu koda mutum daya a cikin ayarinsa.Ganin wannan mummunar barnar da Yazid yayi masa sai tsoro da fargaba ya shiga zuciyarsa nan take ya yanke shawarar yin sulhu da Yarima.Koda Yarima Ya dako tsalle ya dirga a gabansa sai yace,to uban dawa meye sauranka? Ina kuma kokarin naka na iska,idan har ka isa kai namiji ne inason kayi yaki dani hannuwanka na masu rike da takubbai biyu,ni kuma zan zauna batare da makami ko garkuwa ba,na kuma rantse da girman Allah sai nayi maka KISAN GILLAH.Koda zuwa nan a cikin batun Yazid sai Ardadu ya zube kasa cikin risinawa yace,ya shugabana kayi mini rai ko ba a gwadaba linzami yafi karfin bakin kaza,na hakura kuma nayi mubaya'a a gareka zan ta bauta a gareka har lokacin daka yantar dani.Koda Yarima yaji wannan batu sai yayi murmushi ya dubi Ardadu yace bazan taba aminci dakai ba saidai zanyi maka gargadi gami dayi maka katanga da cikin wannan kasa,idan har na kara jin waninku ya kusanto cikin birninmu mai tarin albarka to zai dandani mutuwa mafi daci,dan haka ka kwashe kaskantattun dakarunka ka wuce dasu zuwa matsugunarku.Koda jin wannan batu sai Ardadu ya kara risina yace,ya shugabana kayi sani wadannan ayari nawa tuni azabarka tayi sanadin wanzuwarsu zuwa kiyama inason ka aminta dani na zamo bawa wanda zaiyi maka rakiya a cikin wannan tafiya taka,babu duk abinda zaka bukata ba tare dana samo makashi ba,dan haka kayi aminci dani yakai wannan sadauki mai tarin jumurda. Dajin wannan sai Yarima Yazid ya daka masa tsawa yace kayi abinda na umarceka inason kuma ka sani ruwa da wuta bazasu taba yin shiri ba,dan haka ka fice daga wannan yanki gaba daya.Koda gama fadar haka sai Yarima ya tunkari kofar birnin da zummar ya fice,koda Ardadu yaga Yarima ya wuce ya barsa anan tsaye sai yayi sauri yabi Yarima da gudu yana isa gabansa saiya zube yace,wannan damar ita kadai zaka bani ta maidani mutumin arziki na daina sata da fashi Yakai Yarima,in har ka tafi ka kyale ni zan iya hada kai da wasu rukuni na yan fashin da suke zaune a cikin wannan yankin na cigaba da aikata mummunar sana'armu dako a cikin addininmu ba abune mai kyau ba,ni kuwa har inna kasance cikin duniya to zan kas +Abbas Abdulkadir hada hada+ ance cikin dauwamar bakin ciki da radadin yanda ka tozartani,ka wulakantani,ta yaya zan goge wannan tabon dakayi min a gaban makiyana abokana sana'ata na tabbata sai sun gorantamin domin har a ranar da aka haifeka saida muka shigo cikin birnin nan mukayi sata amma dan abin kunya yau gashi ina mai kaskanta a gareka tabbas idan ban zamo hadiminka kaicona yakai Yarima da wannan kadai zan tsira daga gorin dazan fuskanta daga yan uwana dan haka ina mai neman alfarmarka daka tafi dani. Koda Ardadu yazo nan a batunsa sai Yarima ya kada kai yayi gaba ba tare daya kara duban Ardadu ba.Ardadu koda yaga haka sai ya daga murya da karfi yace,ina da labarin WASIKAR JINI sannan inada labarin yanda zaka mallaki WASIKAR JINI,Inhar kanason kasamu wadannan labari to tabbas inada amfani a cikin wannan tafiya taka,domin a karkaf wannan kasa babu wanda yasan cikakken labarinta faceni. Koda Yarima Yazid yaji wannan batu sai ya tsaya cak ya waigo ya dubi Ardadu cikin sanyin jiki,tabbas inhar yana da labarin WASIKAR JINI ya zama dole yayi tafiyar nan dashi,domin shi babu abinda ya sani dangane da WASIKAR JINI kai hatta birnin Latus Harus bai san ta inda zaibi ba,koda yin wannan tunanin sai ya dubi Ardadu yace,In har kanason tafiya dani sai ka zamo mai addini irin nawa sannan sai ka cire cuta da yaudara da kwace a cikin zuciyarka in har zaka karbi addinina ka kuma cire wadannan abubuwa dana lissafa maka a shirye nake da nayi tafiya dakai. Koda Ardadu yaji wannan batu sai yayi murmushi yace,na amince zan karbi addininka anan take sannan zan daina yaudara da cuta,amma bazan daina kwace ba domin kuwa muddin akace na daina kwace ba abinda zamu ci a wannan tafiyar tamu sai ya gagaremu sannan zamu shiga cikin Birnin Latus Harus ba tare da komai ba,hakan kuma na nufin kaskantarmu saboda ita wannan kasar babu talaka haka duk bakon daya shiga kasar da talauci to babu shakka zamu shiga muna kaskantattu wanda ko kallo bazamu ishe su ba,in har ka amince zanyi kwace har na tara dukiya mai yawa muci musha mu kuma shiga kasar Latul Harus da yalwar arziki yanda jama'ar kasar zasu daraja mu da kimantamu. Dajin wannan daga Ardadu sai Yarima ya girgiza kai yace, ban yarda ba ka yarda da Allah ka yarda da cewar shine mai yin komai ba waninsa ba,in har ka aminta mu tafi in kuma baka aminta ba ba zan tafi dakai ba. Da Ardadu yaga Yazid da gaske yake inhar bai aminta ba ba tafiyar za'ayi dashi ba sai ya yarda ya bari cewa aransa tundashi kwararre ne wajen kwace zai iya yin kwace ba tareda sanin Yazid ba dan haka sai yace,na amince mu tafi. Nan take Yazid ya musuluntar dashi suka dauki hanyar tafiya basu jima da barin gurin ba saiga dakaru sama da mutum dari uku sun nufo bakin ganuwar bisa wani daya kubuta yaje ya sanar da abinda ke faruwa a nan bakin ganuwar.Koda bayyanarsu gurin sai mamaki ya kamasu ganin gurin babu wani sadauki mai rai kowa da kowa yayi warwas a kas ko shurawa basayi da kyar suka samu wani wanda yake iya daga kansa.Koda shugaban dakarun ya hango wannan sai ya isa gareshi yana isa ya dago kansa cikin fushi yace,yakai wannan DAN TA'ADDA ina dalilin faruwar haka a gareku alhalin munsan bamu turo kowa ba dan ya tareku ta yaya akai haka ta faru a gareku? Koda jin wannan tambaya sai wannan danfashi cikin nishi sama sama da kyar ya motsa baki yace,ba kowa bane yayi mana wannan illar face Yarima Yazid kuma a yanzu haka shugabanmu ya bishi rakiyar inda ya nufa.Koda wannan shugaban dakarun yaji wannan batu sai ya cika da mamaki ainun ya mike tsaye kai tsaye yayi umarni da wasu daga cikin dakarun dasu kama ragowar dakarun suje su haka rami a binnesu.Take sai shi kuma ya koma cikin garin ya nemi waziri ya zaiyane masa duk abinda ya faru. Duk wanda yaji wannan batu sai mamaki ya cikashi nandai suka hadu suka kara yiwa Yarima fatan Allah ya dawo dashi lafiya ya kuma bashi sa'ar samun abinda ya tafi nema dan kubuta daga sharrin sarki Aiyuba. *** *** *** ACAN kuma kasar Latus Harus lokacin da Yarima Zainur ya isa cikin birnin sai ya wuce kai tsaye izuwa gidan SARKIN YAKI Haiman yana shiga cikin gidan sai ya iske Haima tare da matarsa Lahisa zaune a fargajiyar gidan suna cin abincin dare cikin nishadi da hira suna ta kyalkyala dariya,koda suka ga Jarumi Zainur ya dawo daga farauta hannunsa wayam ko zomo babu sai suka mike tsaye zumbur cikin firgici da mamaki saboda hakan bata taba faruwa ba.Zainur bai taba dawowa gida ba cikin latti haka bayan magriba kuma bai taba tafiya farauta ya dawo zakai ba face ya sabo katuwar dabbar daji a kafadarsa,sannan kuma fuskarsa babu annuri ko kadan domin kallo daya mutum zaiyi masa ya gane cewa yana cikin matsanancin bakin ciki da damuwa. Kai tsaye Zainur ya wuce izuwa cikin dakinsa kansa a sunkuye ko duban inda su Haiman baiyi ba bare ya tsaya ya gaishe su kamar yadda ya saba,kawai sai ji sukayi ya banke kofar dakin nasa da karfi ta kulle.Cikin alamun tsananin mamaki Haiman da Lahisa suka dubi junansu kawai sai Lahisa ta mike tsaye da nufin ta tafi dakin Zainur din ta tambayeshi abinda ke damunsa,amma sai Haiman yai wuf ya ruko hannunta yamai da ita zaune sannan ya dubeta cikin nutsuwa yace, Mune gaba dashi ko shine gaba damu? Ai ko wani ne ya bata masa rai bai kamata ya huce akanmu ba haka kuma idan wani abune yake damunsa kamata yayi yasanar damu ko zamu iya magance masa,ki rabu dashi kawai idan abin ya isheshi da kansa zaizo yayi mana bayani. Sa'adda Haiman yazo nan a jawabinsa sai Lahisa tayi ajiyar zuciya cikin alamun damuwa tace,aini babbar damuwata itace akwai alamun yunwa a tare dashi domin bakinsa +Abbas Abdulikadir Hada Hada+ ma a bushe yake kuma da sassafe ya fita ko kalaci baiyi ba.Koda jin haka sai sarki Yaki Haiman yayi murmushi yace ai bari ba shegiya bace idan haihuwa bata sa anyi biki ba ai mutuwa tasa ayi,koda gama fadin hakan sai Haiman ya cigaba da cin abinsa ko alamar wata damuwa babu a tare dashi yana gama cin abincin sai ya mike tsaye ya shiga cikin turakarsa yayi kwanciyarsa. Saida dare ya raba Yarima Zainur na zaune a cikin dakinsa cikin tsananin bakin ciki da tunani ba komaine ya jefashi cikin wannan hali ba face takaicin yadda yarinya karama ta fishi karfi da jarumtaka alhalin shi yana ganin yadda yake dakawa manyan mazaje gumba a hannu,waishin sarkin yaki ne bai koyar dashi irin horon daya kamata bane ko kuwa malamin daya koyar da Gimbiya Lazwara yafi malamin Haiman iya yaki? Amsar da Yarima Zainur ya kasa baiwa kansa kenan a can wani bangaren yaji yana fama da begen Lazwara domin dduk sa'adda ya rufe idanuwansa sai ya rinka ganin fuskarta wani lokacin kuma sai yayi ta tuno da duka abinda ya faru tsakaninsa da ita. Lokacin da dare ya raba sosai sai yunwa ta addabi yarima zainur kuma tunanin gimbiya lazwara ya ishe shi har shi kansa abin ya bashi mamaki domin gani yayi in dai kyaune lazwara take takama dashi gimbiya nauwara ta ninkata amma ko sau daya bai taba jin zuciyarsa na tunaninta ba domin ya dauketa a matsayin yar uwarsa tamkar uwa daya uba daya suke duk dacewar yasan akwai aure a tsakaninsu. Babban dalilin dayasa zainur baya son ya rabi gimbiya nauwara shine saboda harkar sarauta ko kadan zainur baya son mulki kuma bayason sarki aiyuba yayi zargin cewa yana da sha'awar karagar mulki.Shi kuwa sarki aiyuba yayi matukar mamaki bisa yadda yaga jarumi zainur yake gudunsu shi da yarsa da yadda kuma ya sadaukar da rayuwarsa a kan farauta da koyan yaki babu yanda sarki aiyuba baiyu ba akan ya janyo yarima zainur izuwa jikinsa amma sai zainur ya zuke yama daina zuwa fada da duk inda zai hadu da sarki ko gimbiya nauwara wani iko na Allah kuma ita gimbiya nauwara tana matukar kaunar zainur domin jininta da nasa sun hadu amma kaunace irin ta yan uwantaka. Lokacin da yunwa ta ishe jarumi zainur yaji ya kasa barci da sukuni saiya mike tsaye cikin sanda yaje ya bude kofar dakin nasa a hankali yadda baza aji motsin saba sannan ya fice kai tsaye zainur ya wuce izuwa cikin dakin girki yana shiga sai ya kama bude tukwane domin ya debi abincin dazaici. Ba zato ba tsammani sai yaga gaba dayan tukwanen abincin ya kare cikin alamun karayar zuciya da matukar damuwa zainur ya juya da nufin ya fice daga dakin girkin amma sai yayi kicibus da sarki yaki Haiman tsaye kuma ruke da kwanon abincin yana yi masa murmushi kawai sai Haiman yayi masa murmushi kaiwa sai haiman ya yafito zainur da hannu ya

Chapter 3 of 15