Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba zasu iya kasheshi ba sai suka ruga izuwa cikin ramukan da suka fito.Ramukan suka rufe kansu tamkar basu taba wanzuwa ba a wajen sai gawarwakin yan uwansu kawai a kwance rututu a filin daji. Adaidai wannan lokaci ne Yazid ya sauke Lazwara daga bayansa a kasa. Koda ya ga har yanzu a sume take bata farfado ba sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya dimauce bai san sa'adda ya fisge battar ruwa ba a jikin Nauwara ya budeta ya zazzage ruwan akan fuskar Lazwara,faruwar hakan keda wuya sai Lazwara ta farfado tana mai jan dogon numfashi. Koda ta bude idanunta taga dubunnan gawarwakin dodannin zube a kasa kuma ta dubi yarima Yazid taga takobinsa da duk jikinsa ya rine da jini sai kawai ta bude baki tace nayi imani da ubangijin musulunci wanda ya baka karfin da ka kashe wadannan dodanni,ina ragowar dodannin suke? Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Yazid da Nauwara,yazid ya dubi Lazwara yace bazan baki amsar tambayarki ba sai bayan na shigar dake cikin addinina,nan take yazid ya biyawa Lazwara kalmar shahada ta maimaita sannan ya dubeta yace ragowar daodannin sun koma cikin ramukan da suka fito. Koda jin haka sai Lazwara ta mike tsaye tace zasu sake fitowa don haka mu zauna a cikin shiri. Gama fadin hakan keda wuya sai suka jiyo sukuwar gubu daruruwan dawakai an durfafosu suna daga kai sukaga ashe su sarki marwatu ne suka taho cikin shigar yaki,akan gaba kejin dake dauke dasu Haiman ne bisa wani keken doki. Wannan runduna tun daga nesa ta fara razana,ba komai ne ya razana su ba face hango gawarwakin wadannan dodanni da kuma hango Yazid face face a cikin jini takobinsa ma ta rine da jini. Koda ya rage saura baifi taku ashirin ba tsakanin rundunar su sarki marwatu da su Yazid sai rundunar tayi turjiya suka tsaya cak aka fara kallon kallo har saida kura ta lafa sannan waziri ridwan ya dubi yazid,lazwara da nauwara yace yaku abokan gaba gamu mun iso tsakiyar dajin hajarul aswad dauke da yan uwanku idan kuma kuka ki bamu wannan taswirar dayanku bazai tsira da rayuwarsa ba,ku dubi kanku sannan ku dubemu kun sancewa ko ba'a gwada ba linzami yafi karfin baki kaza, kai Yazid kabar ganin cewa ka kashe wadannan dodanni kai kadai to mu ba dodanni bane mutane ne wadanda sunfi aljani ma hatsabibanci da jarumtaka. Koda waziri ridwan yazo nan a jawabinsa sai Sarauniya Lazwara tayi caraf ta tari numfashinsa tace kai tsohon azzalumi kayi sani cewa kunyi babban kuskure da ganganci da kuka kawo kanku nan dajin domin baku isa ku iya ketare nan wajen ba a raye bare har ku isa kogon hajarul aswad ku dauko wasikar jini. Gaba dayanku sai kun zama gawa.Koda jin wannan batu sai waziri ridwan ya bushe da dariya yace ke yarinya kiyi sani cewa kowa ya rigaka kwana dole ne ya riga ka tashi,duk masifun dake cikin dajin nan munsan dasu kuma mun dauki mataki a kansu. Caraf sai sarauniya Lazwara ta sake tarar numfashin ridwan tace na yarda kun san masifun amma ai sani daban haduwa daban,idan kuna ganin cewa zaku iya dasu gasu nan ku jaraba mu gani. Tana gama fadin hakan saita juya ya dubi yarima Yazid tayi masa wata inkiya shi kuma saiya kwala kabbara ya naushi kasa da hannunsa guda take ramukan dodannin nan suka bude dodannin sukayi fitar burgu daga cikin karkashin *Abbas Abdulkadir Hada Hada* kasa,maimakon dodannin su afkawa su Yazid sai suka juya da gudu suka afkawa su sarki Marwatu aka ruguntsume da masifaffen yaki. Kaico ananfa KASUWAR CINIKIN DAUKAR RAYUKA ta bude,dodannin suka rinka ragargazar dakarun su sarki Marwatu suna yi musu mugun kisan gilla,abinda ya daurewa kowa kai a wajen shine ko dodo daya bai nufi inda kejin dasu Haiman yake ba kuma ta cikin dodannin Yazid ya kutsa yaje ya sare kubar da aka kulle kejin kofar ta bude ya fito dasu Haiman daga ciki ya tafi dasu can inda Nauwara da Lazwara ke tsaye. Koda Nauwara ta hango dan uwanta Yarima Zainur saita ruga gareshi ta rungumeshi cikin tsananin farin ciki,ita kuwa Lazwara sai taje gaban Zainur ta dubeshi cikin murmushi tace masoyina dama na kudurce a raina anan ne zan baiya maka SIRRIN ZUCIYA ta lallai tun a farkon haduwa ta dakai na kamu da tsananin sonka kuma a halin yanzu nima na karbi addinin Yazid shin kasa so na? Koda jin wannan tambaya sai Zainur yayi wuf ya janye jikinsa daga cikin na Nauwara ya dubi Lazwara cikin tsananin farin ciki yace nima tun a farkon haduwarmu na nutse a cikin KOGIN SON... Cikin sauri Nauwara ta rufe bakin Zainur da tafin Hannuta tace kabar sauran bayani saimunga yadda karshen wannan yaki zai kasance,nanfa duk su biyar din suka mayar da hankalinsu izuwa inda ake fafata wannan masifaffen yaki. Rabin sa'a aka shafe ana wannan yaki ya zamana cewa wadannan daodanni sun kashe gaba dayan dakarun sarki Marwatu,Sarki Marwatu da Waziri Ridwan ne kadai suka rage a raye kuma kowannensu ya sami mugayen raunika kimanin guda bakwai a jikinsa. Suma in badon tsananin karfin damtsensu ba da karfin Sihirinsu da tuni sun dade da mutuwa.Dodannin na shirin karasa kashe su sarki Marwatu da waziri Ridwan kenan sai Yazid ya daka musu tsawa take suka kame kam tamkar gumaka. Nan take Yazid ya fara kiran sunayen Allah tsakaka yana yi masa kirari,faruwar hakan keda wuya sai jikin dodannin gaba dayansu ya kama tsattsagewa suka ringa rugujewa suna zubewa kasa suna zama gari. Nan da nan dodannin suka hallaka gaba dayansu guda daya bai tsira da rayuwarsa ba. Sarki Marwatu da waziri Ridwan na ganin haka sai suka cika da tsananin al'ajabi gami da takaici,a wannan lokaci ko motsi ba zasu iyayi ba sakamakon jinin dake zuba a jikinsu kuma indai ba'a gaggauta dinke raunikan nasu an tsayar da jinin dake zuba ba na da wani lokaci zasu iya mutuwa. Koda Marwatu da Ridwan suka fahimci cewar lallai zasu hallaka idan ba'a taimake su ba suka kama rokan su Yarima Yazid dasu cecesu.Yarima Yazid ya matso daf dasu ya tsaya ya dubesu yace ina karfin mulkin naku kuma ina karfin damtsenku dana sihirin tsafinku,ku ceci rayuwarku mana da abubuwan da kuka dogara dasu,kun gani da idanunku ayau babu wani karfi wanda yafi na ubangijin musulunci. Kodon saboda dubunnan rayukan da kuka sa suka salwantar ba zamu ceci rayuwarku ba mutuwa ce kadai zata fanshe zunubanku a wannan doron kasa,ina mai tabbatar muku da cewa daga yau tsafi ya daina tasiri a wannan nahiya gaba daya kuma zalunci ya kau sai adalci a tsakanin masu mulki da talakawa. Yanzun nan zamu karasa kogon hajarul aswad mu kone duk abinda ke cikinsa sannan mu koma izuwa kasashenku mu kafa tutar addinin musulunci. Koda gama fadin hakan sai Yarima Yazid ya juya ya koma inda su Zainur ke tsaye suka rankaya gaba dayansu suka kara nausawa cikin dajin na hajarul aswad suka bar sarki marwatu da waziri ridwan suna murkususu suna kukan nadama gami da kakarin mutuwa. Kafin cikar dakika dari duk su biyun sun sandare sun zama gawarwaki. Kamar Yadda Yarima Yazid ya fada hakan al'amarin ya kasance wato sun isa har cikin kogon hajarul aswad suka dauko wasikar jini suka koneta faruwar hakan keda wuya kogon dutsen gaba daya ya kama rugurgujewa. A guje suka fito daga cikin kogon ba tare da dayansu ya hallaka ba. Lokacin da su Yarima Zainur suka dawo gida sun riske mahaifin Gimbiya Nauwara ya mutu don haka sunyi kuka da bakin cikin rashin karbar addinin gaskiya da baiyi ba. Nan take aka kafa tutar addinin musulunci a gidan sarautar sannan suka dunguma izuwa birnin sarauniya Lazwara nan take aka kaddamar da musulunci bayan nanne aka daura aure Yarima Zainur da Lazwara,Yarima Yazid da Nauwara sannan aka sake dawowa birnin su Nauwara aka baiwa Yarima Zainur sarautar garin wato ya gaji sarki Aiyuba. Shi kuma Yazid ya dauki matarsa Nauwara suka tafi can kasar su,komi ya dawo daidai yadda ya kamata,aka cigaba da zaman lafiya a cikin nahiyar da addinin irin na musulunci aka kautar da tsafi da bautar gumaka. . TAMMAT BI HAMDULILLAH!!! . ALHAMDULILLAH. Khairun Anillahul Wahidul Qahhar. A Nan Muka Kawo Karshen Wannan Littafi Mai Suna Wasikar Jini.Dafatan ya kayatar,nishadantar tare da wa'azantarwa. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 15 of 15