kayan tana wasa da yatsun hannunta cikin matsanancin faduwar gaba ."
?aukar kayan mommy tayi ta ajiye akan ?aramin table din dake gabanta ta sake kamo hannunta "duk da haka babu farinciki a tare dake kisna ,sam ban ji dadin ganinki haka ba, idan akwai abinda ke damunki ki fa?a min ni mahaifiyarki ce Karki boye min komai tayi maganar tana kallonta . shiru kisna tayi tana kallon momy zuciyarta na dokawa da matsanancin karfi "nayi iyakar kokarina dan naga kin kasance tare da muradi dan ina da tabbaci akanshi, na yarda dashi dari bisa dari na yarda zai baki kulawa da soyayya kamar yadda kika fa?a cewar yana baki nasan zai yi fiyye da haka komai zai faru zai rikeki amana ba zai wulakantaki ba amman ina son Ki fa?a min idan kina fuskantar wata matsala atare dashi ?.
wani sabon shiru ne ya sake biyowa baya kisna ta sunkuyar da kanta kasa tana kukan zuci dana zahiri "idan kuma duk abinda na lissafa baki samu ba agurinsa kuma bazaki iya fadawa mahaifiyarki damuwarki ba shikenan , ki qara hakuri ki jajurce kafin zuwan nawal ,muddin kika yi hakuri ina da tabbacin muradi zai kula da lamarinki cike da dimbin soyayyarsa "nasan zaki iya janyo hankalinsa saboda kina da komai na jan hankalin d'a namiji ,ki d'aurewa zuciyarki sannan naji dadin yadda ki kisan ki boye sirrin mijinki duk da nasan Aliyu bai sonki amman kika masa kyakkyawan yabo da kyautatawa "ta k'arasa maganar hawaye na turereniyar zubowa daga cikin idanunta dingar hawayen mahaifiyarta yasa ta d'ago nata idon a gigice dake cike da hawaye "dan Allah mommy Karki yi min hasarar hawayenki , karki zubar da hawaye akaina, ki rufa min asiri mumy na dade ina sanyaki zubar da hawaye , a yanzu kuma babu abinda nake bukatar gani atare dake sai farinciki da murmushi akan fuskarki".
Mommy ta tsura mata ido kawai tana kallonta da nazarinta cike da tausayawa ,ko rantsuwa tayi baza tayi kaffara ba tasan diyarta na cikin matsanancin damuwa , girgiza mata kai kisna tayi alamun ta daina kuka "you are great mother for my life ," kisa Ido kiga Ikon Allah momy bazan sake yin wani abu da zai sake sakaki cikin damuwa ba ,zan yi abinda nasan za kiyi alfahari dani , sannan bazan boye miki ba saboda ke mahaifiyata ce ko babu komai zaki taya ni a addu'a akan mijina ,ina ?an fuskarta wasu matsaloli ka?an daga garesa wanda nake tunanin nan kusa zanyi maganin komai da ikon Allah".
"inshallahu zaki yi nasara akan shi , Allah zai karkato miki da hankalinsa ya mallaka miki zuciyarsa ya soki fiyye da kowa a duniya ". Allah yasa momy har dake kenan ? ta fadi haka tana murmushi mai gauraye da kuka , mommy tayi dariya tana dungure mata kai "ai na fahimceki ba tun yau ba kina adawa da soyayyarmu da Aliyu ".
"kai momy "
"kai momy ko gaskiya maza tashi kije ki kira min muradi yazo yanzu ina son ganinsa "okay mom ".ta mike da sauri ta nufi kofar fita, ta bu?e kofar ta mayar ta rufe ta juya da sauri domin zuwa isar da sakon momy kawai ta jita a saman faffad'an kirjin mutun sun yi karo dashi , kamshi daddad'an turarensa ne yasa ta fahimci shine , a matukar tsaroce ta d'ago da sauri tare da yin baya gudun jin saukar mari aiko kafarta ?aya ta gurd'e kasancewar takalmi mai dan tsini ke sanye a kafafunta ta bude baki zata saki qara yayi saurin tarota gabad'aya ta zubo jikinsa ,bai san yadda akayi ba sai ji yayi bakinsu ya ha?e guri ?aya batare daya shiryawa hakan ba tare da zagaye kugunta da hannuwansa duka."
saurin dauke numfashi yayi cikin wani irin yanayin da shi kadai yasan manufarsa , yayinda duk wani gashi dake kwance a jikinsu ya mike tsaye yrrrrrrrr tattare da jin shaukin juna , wani irin bugawa zuciyarsu ke yi a lokaci ?aya ,zaro ido tayi hankalinta yayi bala'in tashi tayi saurin runtse idanuwanta saboda bazata iya jurar kallon cikin kwayar idanunshi ba ,dan tasan kuskurenta ne ya janyo faruwar hakan har gashi ta janyo ya aikata abinda bai shirya ba ."
a hankali ya zare bakinsa cikin nata ya tsaida ita bisa kafafunta amman ta kasa tsayuwa ta sake runtse idanunta gam ta zube a jikinsa ta kwanta lamo tana sakin numfashi sama sama ,jinta makale a tattausan jikinsa tana sha?ar kanshin turarensa yasa ta dinga jinta wani irin gabadaya ilahirin jikinta ya dauki shocking kamar wacce aka junata da wutar lantarki shima hakan ce ta kasance dashi ,a hankali suke sha?ar numfashi juna , ya cire bakinsa yana runtse idanunshi muryarsa a kasalance yace "ki tsaya bisa kafafunki mana , tayi kokarin tsayawa kamar yadda yace amman ta kasa "bazan iya ba zafi nake ji a kafata tayi maganar kamar mai rera kuka a tare suka bude idanunsu , shiru suka yi tsaye suna kallon kwayar idanun juna zuciyarsu na mummunar baguwa da karfi , ta dinga zukar kamshin turarensa wanda a duk sanda zai numfasa sai kamshin turarensa ya kai wa hancinta ziyara ,bata jin zata damu da hukunci da zai biyo baya ita dai taji dadi wannan moment din daya kasance atsakaninsu ,Kuma tayi farinciki kasancewarsu tare , ta sake lumshe idanunta tana jin ina ma su kasance haka muddin rai ."
A hankali ta bu?e idanunta fesss Akanshi take idanunsu ya sarke cikin juna wani irin suka dinga ji ajikinsu kallon juna suke ko kifta ido basa yi, kusan minti biyar suka ?auka tsaye suna kallon kwayar idanun juna batare da kiftawa ba sannan babu wanda yayi yunkurin cewa wani abu , dukkaninsu babu wanda numfashinsa bai fita da sauri saboda tsintar kansu acikin wannan yanayin ,duk da basu sha bakin juna ba sun dandin miyon juna kad'an kwayar idanunsa take kallo bata san haka take bala'in sonshi ba sai yanzu da taji hannunsa zagaye da kungunta lura da hakan da yayi ne ya hanzarta zare hannuwansa dake jikinta yana kallonta a kaskance .numfashi ta sauke tana gyara tsayuwarta tare dingisa kafarta ta makale da bango tana saita natsuwarta muryarta cike da in ina tace "ammm uhmn mo...mommy ce ke kiranka ".
Numfashi ya fesar da kyar yayi taku biyu batare daya ce mata qala ba illa ya tattara miyon bakinsa ya zubar a gabanta sannan ya d'aura hannunsa akan handle din k'ofa ya murd'a ya shiga d'akin da sauri ta sauke naunauyen ajiyar zuciya "wahhhhhyyo Allah zubar da miyon bakinsa yayi ? ta furta hkn a fili cikin tsananin tashin hankali tare da runtse idanunta sai ga hawaye sharrrrrrr sun zubo akan kuncinta , zafi goma da ashirin ga raunin kafarta ga bakinciki abinda Aliyu yayi , zullumi da rashin madafar dafawa ne yasa ta durkushe agurin tana cigaba da matso ruwan hawaye "Allah yasani tana matukar qaunar ya Aliyu musamman yanzu da take hango soyayyar nawal acikin kwayar idanunshi ,sai dai komai runtse zatai kokari ta rushe wannan qaunar da yake mata ta dawo zazzafan kiyayya da tsana mai tsanani da irin sirrin da Allah ya bata.. ".
A natse ya janyo karamar stood gaban momy ya zauna yana fuskantarta bayan yayi sallama ta bashi umarnin shigowa "gani mamana me kike bukata ki fadi min duk abinda kike so".ya fada yana karewa fuskarta kallo ganin kamar yanayinta da idanunta ya sauya ya sake yin kusanta kanshi da ita "mai ya sameki mamana is like ma Kamar kinyi kuka menene ya saki kuka plz Ki fa?a min banason ganinki cikin damuwa ?." Duk ya rude ya dimauce ya riko hannuwanta cikin nashi kamar zai yi kuka baya son ganinta cikin damuwa bare kuma ace a gidansa ta samu damuwar "Kwantar da hankalinka muradi babu komai ,ba kuka nayi ba "ta fada muryarta na rawa ,shiru tayi kafin daga baya ta numfasa sannan ta kira ainihin sunansa kamar zatayi wani kukan "Aliyu......" ..Gabadaya ya tattara hankalinsa da natsuwarsa gareta cike da tsantsar biyayya ya amsa da "na'am momy ." yana da kyau ku sake bawa junanku dama domin samun zaman lafiya a tsakaninku , nasan kana da zuciya mai kyau sannan kana da kafiya akan duk wanda yayi maka laifi ".tayi maganar hawaye na sake zubo mata "no no mommy why dan Allah me yasa zaki min haka bakisan zubar hawayenki babban tashin hankali bane gareni "? Ta sake matso wasu hawayen hankalinsa ya sake tashi ya rike hannunta gam jikinsa na rawa "ya Allah ya furta momy Kinsan fa babu abinda na tsana a rayuwata kamar zubar hawayenki ya kai yatsan hannunsa yana ?auke mata hawaye dake gangaro mata "Ka barni nayi kuka muradi ya girgiza mata kai alamun karta yi masa haka " ni nasan abinda ke sani kuka Aliyu , ni dai zan cigaba da neman alfarma agurinka kayi hakuri da kisna a rayuwa , ina son ganinku tare muddin rai saboda ina kyautata zaton zata fi samu farinciki da kwanciyar hankali agurinka fiyye da kowani namiji da zata kasance a karkashinsa ,a da ma ka tsaya ka kular min daita da iyakacin karfinka ina ga yanzu da take karkashin ikon ka ,nasan halin kisna sosai tunda ta sheida min da bakinta cewar tana sonka da dukkanin rayuwarta nasan iyakar gaskiyarta ta fa?a min saboda bata karya ".
shiru ne ya ziyarci dakin na kusan minti goma babu wanda ya sake cewa komai daga Aliyu har momy kafin daga baya ta cigaba da magana muryarta a raunane "bazan takuraka akan dole sai ka so kisna ba haka bazan dakatar da aurenka da nawal ba saboda na d'aukeka kamar dan dana haifa ne da cikina kamar yadda ka d'aukeni matsayin uwa," ka amince da kisna ka duba lamarinta dan Allah ta zamo abokiyar rayuwarka ta har abada ka bata farinciki ..... ".tana gama fadar haka ta mike tsaye jikinta na rawa ta nufi kofar fita idanunta basu gane mata kisna dake raku'be manne da bango ba saboda yanayin da take ciki ,dan kusan idanunta sun rufe ya biyo bayanta da sauri yana kiran sunanta ,"momy momy !!! bata tsaya akoina ba sai a bakin kofar d'akin da zata zauna kamar yadda kisna ta bukata, da sauri ya k'arasa inda mukulin dakin yake ya dauko ya bude mata ta shiga d'akin tsaf sai kamshi ke tashi saboda kisna ta gyara ko'ina ta zauna a bakin gado tana sauke numfashi shima ya zauna kusa daita "dan Allah mommy kiyi hakuri ina iyakacin bakin kokarina babu abinda ....."
"na sani Aliyu ba sai ka fa?a min komai ba jeka ka huta Allah yayi muku albarka " zaro ido yayi yace "haba momuy yaushe rabon muga juna da zaki koreni tun yanzu duka karfe nawa yanzu momy ? ".
shiru tayi ta kasa cewa komai illa girgiza masa kai datai a hankali abubuwa suka dinga dawo mata daki daki da suka faru a baya idan bata manta kalmanta na karshe garesa ba itace da kanta tace "aliyu duk randa kasamu damar auren kisna a rayuwarka duk abinda kayi mata na tozarci bazan damu ba sannan bazan yi magana akai ba, bazan d'aga ido na kalleka nace saboda me ka mata ba ka aureta ko dan ka gallaza mata .........."
runtse idanunta tayi "to mai yasa yanzu ta damu saboda taga kisna cikin damuwa bayan tasan muradi bazai taba wasa da kalamanta ba "?
"Bai kamata ki damu ba umarninki muradi yake aiwatarwa ,muryarta a sanyaye tace " tashi kaje d'ana ma ha?u gobe idan Allah yasa muna da yawanci rai ta k'arasa maganar tare da gyara zamanta zuwa kwanciya ."
Jiki a sanyaye Aliyu ya mike ya bar dakin zuwa nashi dakin ya zauna a bakin gado ya harde kafafunsa guri daya yana girgizawa yayinda hannuwansa ke kan gado , ya runtse idanunshi gam yana tunanin maganganun mommy gareshi "to ko kisna ta fa?a mata halin da yake mata ne "?"No yasan bazata fa?a ba tunda ko ranar ma yaji abinda take fa?a mata yasan bazatai abinda tasan momy zataji yaushinsa ba ,bai tashi daga zaunen da yake ba sai da lokacin Sallah magarib yayi ya mike yaje yayi alwala yayi Sallah ya dawo parlou'n kasa ya zauna ya hard'e kafafunsa yana kallon kisna da yaranta .
Duk inda ta dingisa kafarta yaranta na makale daita kamar zata gudu ta barsu suna zuba mata shirmen su na yara , sosai abun ya bashi haushi dan ko kallon inda yake yaran basu yi ba ,ya lura sun fi son uwarsu dashi aryan ne yafi makale mata ta kalleshi tana murmushin karfin hali"babana kuje gurin papa mana na karasa aikin da nake "a tare suka makale kafada alamun bazasu ba "kuje mana ta fada a ?an tsawace take aryan ya fashe da kuka shima areef kamar jira yake ya fara "momy zaki sake guduwa ki bar mu ko inji cewar aryan ? Take jikinta yayi sanyi Ta kamosu jikinta "Babu inda zani muna tare kunji 'yan albarka ,tare ma zamu kwana yau kaji babana maza ku share hawayenku duk yadda tayi su tafi gurin Aliyu ki sukayi ,dan haka ta hakura ta barsu makale daita, ta cigaba da aikinta shi kuwa haushi yasa ya mike ya koma daki yana jan tsaki ..."
a natse ta turo kofar d'akin ta shigo hannunta rike da tire d'auke da cup da plet tana dingisa kafarta kad'an , ta karaso gabansa ta janyo stood ta ajiye masa "ga coffer da cake nayi tunanin zaka bukata"? a hankali ya bude idanunshi akanta yana kallonta katin daga baya ya girgiza mata kai alamun " a'a . "mamanka tace na dinga kulawa da kai fa ,na kuma mata alkawarin zan baka kulawa har sai kace ya isa , dan Allah kasha kaji mijina cake din yayi dadi sosai ."
shiru yayi yana kallon karamin bakinta da take motsa shi a hankali , ta kamo laulausan tafin hannunsa cikin nata wani irin zirrrrrrrrr suka ji atare take zuciyarsu ya shiga dokawa da sauri sauri "wannan shine natural reaction nasan kaji irin abinda naji yanzu kou ? yayi shiru yaki cewa komai sai dai har lokacin idanunsa na kanta , ta numfasa kana ta cigaba da magana a natse " babu macen da zata soka a yanzu fiyye da yadda nake maka , i love You so much ya Aliyu do you love me "? Tayi masa tambayar tana tsare shi da narkakkun idanunta Shiru yayi ya kasa furta mata uffan "ya aliyu ka bawa zukantamu damar kusancin da junansu nasan cikin lokaci kankani zasu fahimci juna , ina son ka soni tun daga karkashin kasan zuciyarka ba dan wata darajar kowa ba, idan ka cigaba da kina acikin zuciyarka kuwa zuciyata zata iya kamuwa da wani mumnunar ciwo wanda zai fi karfin kowa a karshe kuyi asarata ."
"tana bukatar ya sota yanzu bayan abubuwan data masa, ita da ta kasa fahimtarsa a lokacin daya fi bu?atar hakan daga gareta inji cewar wani bangare na zuciyarsa ,yayinda wankakkiyar zuciyarsa tace "kana da taurin kai aliyu kana da bakar zuciya kuma wannan dalili zai sa ka karshe rayuwarka kana cutar da kanka ,ya kamata ka bata dama ta biyu kamar yadda ta bukata ka tsaya da kyau ka fahimceta ka dawo daita cikin zuciyarka ka manta matsalolin da sukai ta faruwa a baya , ka sha wuya sosai akanta yanzu ne lokacin da zakaji dadin rayuwa daita ka amince da kisna a karo na biyu "."Dakata Aliyu kisna bata sonka karya take maka saboda zuciyarta ta saba da son mutane dabam dabam yanzu duk ka manta irin abinda ta maka "?
"Bari kaji abinda zan fa?a maka kisna ba kai take so ba ya'yan dake tsakaninku take so tana son taga sun rayu tare da mahaifinsu , kayi tunani da kyau saboda ya'yanta tanace maka ba saboda komai ba, bata damu da kai ba karka yarda da duk wani nadamarta karya take maka wannan makaryaciya zuciya gareta, karka yarda daita , karka amince da maganarta". wannan tunanin da zuciyarsa tayi yasa a hankali ya zare hannunsa daga cikin nata ya yarfe baya jin zai iya sonta a rayuwarsa zai dai kyautata zamansa daita, ita kanta momy bata takura akan lallai sai ya sota dole ba.. "
Mikewa tsaye Aliyu yayi zuciyarsa na bugawa sosai tamkar zata fito waje ya juya mata baya hade da rungume hannuwansa a saman fadaddan qirjinsa ,jiki a sanyaye ta mike itama ta tsaya a bayansa zuciyarta na rawa, harumta ta aro ta sanyawa jikinta sannan ta bu?e bakinta da kyar tace "dan Allah kayi hakuri mu samu zaman lafiya har zuwa sanda mommy zata wuce bana son ta fahimci wani abu a tsakaninmu "ya juyo a hankali qirjinsu ya ha?e da juna jin tudun dukiyar fulaninta yasa yayi saurin runtse idaunshi yana sake jin wani sauyi a sansar jikinsa ta ja baya da sauri wanda sauran ka?an ta fadi kasa yayi saurin tarota ya matseta gam da kafad'unsa batare da yatsun hannuwnsa ya ta?a jikinta ba, idanu suka tsurawa junansu suna jin wani iri feelings a sansar jikinsu, motsin shigowa d'akin ne yasa tayi saurin matsawa baya tana dingisa kafarta tare da juyowa tana kallon kofar shigowa , aryan da areef ne suke rige rigen kokarin shigowa d'akin suna dariya, suna ganinsu tsaye suka turo ?aramin bakinsu ."
" hannuwansa duka ya miko masu alamun suzo gurinsa amman suka ki zuwa suka tsaya suna kallon uwarsu "kuje gurin papa mana kun tsaya kuna kallona ". sake turo ?aramin bakinsu suka yi , murmushi ta sakar musu dan tasan abinda yasa suka bata rai bai wuce fushi sukai akan ta barosu a parloun suna cin abinci su kadai ba dan duk sanda sukai mata haka da fuska alamun sunyi fushi ne."
a tare kisna da Aliyu suka soma motsa kafafunsu domin isa inda suke tsaye ,a tare suka karasa suka durkusa daidai tsayinsu ,Aliyu ya rike hannu aryan yayinda kisna ta d'aura hannuta akan areef "menene kuke fushi yau fa ranar farinciki ne zaku kwana tare da papa da mommy"yes amman me yasa kika tafi kika bar mu mu kadai a parlou'n kika dawo nan "?
"Muje kuyi wanka ku kwanta kunji yarana " ta share tambayar da aryan yayi mata dan bata san amsar da zata ba dan nata ba "no mommy sai kin fa?a mana abinda kike yi a gurin papa kika barmu a parloun mu kadai "shiiiii ta d'aura hannunta a bakinsa " kana son rigima fa ...... " Saurin katseta yayi ta hanyar cewa " no mumy you most tell us what are doing here with papa "areef stop talking nonsense to your mum " "not arif is aryan ta fa?a tana mike wa tsaye da kyar rike da hannu areef wanda ya kasance shiru shiru suka nufi bayi shiru yayi yana kallon gefen tafin kafanta da take kokarin barin gurin ,Idanunshi taji yana yawo a sansar jikinta wanda ya haddasa mata jin faduwar gaba mai tsanani ."
Ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa yana runtse idanunshi " ya kamata zuwa wannan lokacin yana gane yaransa ko dan surutun aryan , dan aryan yafi areef surutu sosai shi areef shiru shiru ne kamarsa ba kamar aryan ba wanda ya dauko surutun samir "ka daina yiwa momynka irin wannan tambayar babu kyau yara masu yin irin wannan tambayar suna dawowa lized .
saurin zaro ido waje aryan yayi cikin tsananin tsoro yana hura hanci tamkar mutumin dake durkushe a gabansa , "no bazan sake ba dan bana son na dawo lized yayi maganar yana Bata fuska kamar zayi kuka , shiru aryan yayi na second biyu sannan yace " to papa idan ni na zama lized shi kuma areef fa me zai zama ? "Bazai zama komai ba tunda shi baya da surutu irin naka ha?e rai aryan yayi Sosai kamar sanda yake yaro ,komai nashi suka dauko sai abinda bazaa rasa ba da suka dauko na mahaifiyarsu , babu ta yadda za'a gansu ace ba ya'yansa bane, ko makaho ya shafa zai tabbatar da ya'yansa ne "papa ka daina cewa ina da surutu areef ne mai surutu Aliyu ya girgiza masa kai alamun a'a "Allah papa areef ne he used to trouble me ask gramma murmushi aliyu yayi yana shafa sumar kanshi cikin tsananin farinciki.
suna tsaye tazo ta wucesu still tana dingisa kafa bayan kamar minti goma ta dawo d'akin hannunta rike da kayan baccinsu da hoda..
wanka tayiwa aryan kmr yadda tayiwa areef ta fito rike da hannunsa ta goge masu jiki ta shafa musu hoda ta sanya masu kayan bacci wando da riga farare sol masu matukar kyau taja hannunsu zuwa dakin mommy aryan da aref suka ja suka coge alamun basu zuwa ko'ina , ta tsaya tana Kallonsu daya bayan daya "dont you said we are going to sleep with you and papa "Shiru tayi ta rasa abinda zata ce masu ,bayan kamar minti biyar ta sake Jan hannunsu har tayi taku biyu dasu , muryarsa mai da?in sauraro da tsinka jijiyoyin jiki taji ya shiga cikin kunneta"Ki barsu su kwana anan tunda kin shiryawa hakan ,idan aka san baza'a yiwa yara abu ba kar a fa?a musu karya dan zasu ?auka dabi'a ce mai kyau yayi maganar yana ?alle mabalin rigarsa kamar ba daga bakinsa maganar ta fito ba ."
Ba tace masa komai ba saboda tasan yin karya ba halinta bane ,ta karasa bakin gado ta d'auko daya daga cikin bargon da suke kwanciya akai zata shimfida musu a kasa yace "no Ki kwantar dasu akan gado ke kuma ki kwanta a kasa ta cikin mirrow yaga yaran gabad'aya sun koma gurinta tare da dage kafada aryan ne yace "ni tare da momy nah zan kwanta kema momy zaki kwana damu ko"?
"Yes my boy amman mubi dokar papa ko" "shegen iyayin tsiya ta fada musu zasu kwana tare daita saboda tasan dole sai da ita zasu kwana guri daya nasan ta fadi haka ne dan ta samu damar shige min " ya fadi haka a kasan ransa yana tabe baki ."
Cup din coffer data kawo masa ya d'auka ya kurba ka?an sannan ya shiga bayi domin yin wanka , koda ya fito daga wanka tuni ta kwantar dasu ta dawo gurinsa tayi kasa da muryarta "ka bari na kwanta tare dasu da zarar sunyi bacci zan dawo kasa na kwanta , kallo daya yayi mata tare da kawar da kanshi gefe ya dauki turare ya feshi jikinsa da bayan kunnenshi ya bude wardrobe ya dauki fararen kayan bacci ya zira ya dauki laptop d'insa ya dawo kan kujera ya zauna ya ajiye laptop din a gabansa ya bude ya kunna ya soma duba sakonnin fan's d'insa dana kasuwancinsa .."
Kusan minti goma tana kwance tare da yaranta suna bata labarin shirme , ita kuma tana shafa kansu tana jin sanyi aranta "wa?an nan yaran wata rana sune garkuwa a gareta a gidan Aliyu ,idan zamansu da Aliyu ya cigaba a yadda suke yanzu tasan ?a?anta bazasu lamunta ba ,bazasu bari ya cigaba da wulakantata ba wa?an nan yara sune jigon rayuwarta a gidansa kuma sune qadarorinta , kwantowa suka yi gbdy ajikinta suna wasa da jelar gashinta ta rungumesu gaba-daya ajikinta tana lallabasu dan suyi bacci da kyar ta samu bacci ya d'aukesu ta mike ta sauko daga kan gadon tayi shimfida a kasa ta ajiye pillow ta dan saci kallon inda yake zaune sai faman aikin danne danne yake akan system yana hamma murmushi tayi ta karaso garesa ta tsaya tana kallonsa "shuold I offer you a coffee again "?
"No ya" furta batare daya d'ago ba ta juya jiki a sanyaye ta kasan idanunshi yaga har lokacin tana dingisa kafarta ?aya gyaran murya yayi ta juyo da sauri ta tsaya "janyo table din can kizo nan " ya fada kanshi na kan system
Ta sake juyawa tayi tare ta janyo kujera kamar yadda yace "ki zauna mana kin wani tsaya min akai" zama tayi idanunta na kanshi ya matsar da laptop d'in gabansa yasa ?afarsa daya ya tura table din da take zaune akai baya ka?an sannan ya mike ya d'auko man zafi ya dawo ya zauna yana fuskantarta tare da kamo kafarta mai ciwo kallonsa tayi a matukar firgice jikinta na daukar rawa dan ba ?aramin zafi kashin bayan kofar ke mata ba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 21