a hankali ya dinga masa nasiha mai ratsa jiki sai kusan shida na yamma suka bar gidan zuciyar Safiyya cunkushe da bakinciki duk abinda mijinta ya fa?a bata dauki komai ba , ita dai tasan Aliyu ya taho da diyar mutane ne ?an kawai ya cutar daita ".a mota tsokano maganar ta dinga yi dan nasir ya fa?a mata abinda ya faru tsakanin kisna da Aliyu amman yaki ,dan baya son tasan komai dangane da rayuwar Aliyu , ganin haka ta kudurta a ranta zata dawo musamman domin taji komai abakin kisna"
Ranar haka kisna ta kasance da zazza?i , ko falon bata sake fitowa ba , ya shigo d'akin kallo ?aya yayi mata ya fahimci zazza?i ne ke d'awainiyya daita "kin shigo daki dan bakin munafurci kin boye ,to ki bu?e kunnuwanki da kyau , duk abinda kika san nawa ne acikin gidan karki yi ganganci ta'bawa idan ba haka ba wallahi wallahi ......"
qarar wayarsa ce ta katseshi ya ?auka ya juya ya fita daga d'akin kunneshi manne da wayar har ya fita bata san ya fita ba wani sabon tashin hankali da faduwar gaba da wani irin tsoronsa ne suka d'arsu a zuciyarta "yanzu irin rayuwar da zata yi kenan "?
"a she Aliyu bai san darajan dan adam ba kamar yadda tai tsammanin ? " mutumin da kullum take wa kallon yafi kowani ?an adam kirki da nagarta a duniya shine yau yake kokarin kasheta da ranta ta share hawayen daya wanke mata fuska ta tashi ta soma ha?a kayanta a jaka tana cikin zubawa cikin jakarta ya shigo sai da gabanta yayi wani mumnunar faduwa da ganinsa , da sauri tayi jefa da kayan da yake hannunta sakamakon kallon da yayi mata ta matsa baya da sauri "kashina ya bushe ta furta hakan a kasan ranta " cikin matsananci mamaki yake kallonta "a kwana biyu kacal har ta gaji dashi ya furta a ransa dariyar mugunta na kokarin subuce masa yayi saurin had'iyewa yana watsa mata harara, tausayin kanta ya ka mata "a kwana biyu kacal har kin gaji da aliyunki kin soma nemanwa kanki mafuta ba ?"
"haba yarinya har yaushe daren yayi? "ai yanzu aka fara buga wasan ,ina irin naki wasan yake ?"yayi magana yana tsareta da idanushi tare da tsuke ?aramin bakinsa "Okay a she fa yanzu son Aliyu ake baza'a iya aikata komai ba , amman zan so ki fito da salon iskanci da kika iya kala kala sai mu buga wasan mugani cikin ni dake waye zai yi nasara ".
"babu abinda zanyi har kullum hakuri zan cigaba da baka saboda nasan ...... " yi min shiru munafukar Allah kawai hakurin ubanki zaki cigada da bani ? tayi saurin girgiza masa kai jikinta na rawa wallahi kika sake bude wannan rubabben bakin naki da zumar bani hakuri sai Kin dawo ball a gidan nan , dan na dinga kwallo da kanki kenan har sai kin mutu .."Tsit tayi tare da sunkuyar da kanta kasa tana sauke numfashi ,"mai mugun hali kawai ya fada yana fad'awa saman gadon ya talla'be kanshi da hannunwansa duka ya runtse idanunshi gam yana jan dogon tsaki ..."
Tun daga rana bata sake samun canji rayuwa daga Aliyu ba, tsananin yafi na wanda take ciki , kuskure ka?an duka da zagi ga azabar yunwar da yake mata, sai ya fita tun safe ya barta babu abinci , sai idan ta roki mai gadi ya taimaka mata dashi a rana sau daya take cin abinci , kafin kace me ta zabge tayi wata ?atuwar rama sai dogon hanci da wuya ,a qalla sai datayi sati biyu a kasar , sannan wata ranar lahadi yace ta shirya dan shiga kasuwa shima darajan nasir taci if not haka zai barta tayi rayuwar yunwa daga karshe ta mutu ya huta ..
yana zaune cikin motarsa kiran beaz 330 hannuwansa akan stearing , ganinsa cikin mota ya hana escout dinsa harama biyosa dan duk sanda yayi haka baya nufin yana da bukatar rakiyarsu , ta fito jikinta sanye cikin doguwar riga marun colour har kasa mai zanen fulawa milk colour tun daga wuyar rigar har zuwa shashin dukiyar fulaninta ,rigar tayi mata kyau sosai ,kafafunta sanye cikin flat shoe masu matukar kyau , babu kwalliya a fuskarta sai powder data dan shafa, ta shafawa lip's d'inta Whit lipstick
duk da ta rame sai dai hakan bai hana kyawun da Allah yayi mata fitowa ba ,ta fito haraban gidan tana taku a natse kamar koda yaushe ta bude murfin mota ta shiga cikin dari dari ta zauna batare da ta sa seatbelt ba , ya murza stearing din motar , take mai gadi ya bude musu makeken get din gidan suka fita .
a hankali motar ke gudu akan titi ta ?an juyo inda yake ta kallesa yayi kyau sosai , komai nashi irin nasu aryan ne babu abinda suka bari nasa , ya ?an juyo ya kalleta ya ?auke idanunshi yana jan tsaki "mayya kawai ji yadda ta kurawa mutu ido kamar zata cinye mutu ,burki yaja aiko gabad'aya ta gigice ta zubo jikinsa dole yasa ya tsaya ba dan ya shiryawa hakan ba yana kallonta , a fusace yace "kina hauka ne ,ki sanya seatbelt mana "am sorry ta fada tare da janyo seatbelt ta sanya tana kallon wani bangare "komai yayi kyau yake masa zan cigaba da hakuri da kai nasan wata rana zaka sauko ka soni ?"
Duk wani abun bukata a gida bangaren abinci babu wanda bai siyo ba sai daya cika bayan Boot d'insa sannan suka ?auki hanyar dawowa gida , akan hanyarsu tace "ina bukatar waya da sabon layi ina son nayi waya da mummy ".
banza yayi mata cikin haka taga wani guri da'ake siyar da waya da layin waya tace "yauwa dan Allah ka tsaya ka siya min , ya tsayar da motar kamar abun arziki yana gama tsayar da motar ya sauke mata yatsunsa biyar a fuskarta "shiga hankalinki baki isa kisani yin abinda banyi niyya ba, duk abinda kika ga nayi na gadama ne wawiya mara kamun kai kawai , kina wani hauka kamar tinkiya , ke din da bakowa bace , ba matsayi gareki a zuciyata ba ,dake da jaka daya kuke agurina , ya kai hannunsa ya murza stearing ya cigaba da tuki har suka karaso gida kuka take kamar wacce akace uwarta da ubanta sun mutu yana gama daidai tsayuwar motarsa ya bude boot ya fito ya shige ciki abunsa ya barta ..
yana zaune a parlou'n ta shigo fuskarta tayi jajur kwayar idanunta sunyi luhu luhu sun kod'e har ta kusan gifta shi ya hard'e kafarta tayi kasa luuuuuuuu zata fa?o jikinsa , bai san yadda akayi ya tarota ba aikuwa hannuwansa duka suka sauka akan dukiyar fulaninta wani irin shock yaji a gabad'aya jikinsa , idanuwanta ta tsura masa tana kallonsa a tsorace , hakan yasa yayi saurin cire hannunsa "ya'akayi hannuna ya kai jikinki "?
yayi maganar cikin ?acin rai zuciyarsa na wani iri zafi ,mikewa tsaye yayi jikinsa na rawa yana mata wani irin kaskantacce kallo mai razana duk wanda aka yiwa shi "ba tambayarki nayi ba kika min shiru" ya'akayi hanuna ya kai wannan banzar jikin naki "wallahi ban bansani ba nasan dai san zaka taimaka min ne hakan ta faru "
"meye shi hakan ya faru yanzu ? tayi saurin girgiza masa kai idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye ta samu guri zata zauna" uban wa zai kwaso miki kayan ?" ta kalleshi da sauri hawaye na zubo mata . "oh kina tunanin ni ne zan shigo miki da kayan bayan naje nayi wahala na siyo da kudina ?"
"bance ka shigo dashi ba amman dan Allah ka bawa mai gadi umarni ya shigo dashi jikina ciwo yake "ubanki da ciwon jiki dan Allah malama tashi kije ki kwaso ," sai na maidake kaskantacciyar baiwa a gidan nan , duk wata babbudewa da cikar iskar da kike takama dashi sai na sauke miki shi ,ya zira hannunsa cikin aljihun wandonsa ya zaro wayarsa ya soma danne danne .... ...."
Juyawa tayi jiki a matukar sanyaye ta koma haraban gidan ta k'arasa bayan motar ta bu?e ta soma fito da caton din monster fury energy, lamunsa ne yana bala'in son shi ya kusan carton goma , ta fito dashi ta kai kitchen ta dawo ta ?auki carton din ruwa shima guda goma ,sai kayayyakin amfani shikafa manja mangyada da dai sauransu , gabad'aya ta ha?a gumi tana cikin aikin Safiyya ta shigo gidan da sauri ta karaso gareta , ta dafa kafad'unta a tsorace ta juyo ganin Safiyya ta sauke naunauyen ajiyar zuciya tana fad'ad'a fuskarta da murmushi "
a she kice ?" ta gyada mata kai ",abinda zaki saka mai gadi ya shigar miki dashi shine kike yi da kanki ,"kai ai babu komai zan iya ai ne shiyasa "zaki iya ko wannan mugun mijin naki ya sakaki , kalli idanunki kamar ma duka yayi miki , kai bama kamar bane marinki yayi ko? "
"Karki damu dani plz mu shiga ciki ta ?auki wani kwali guda biyu muje ko "bari na tayaki safiya ta ?auki wani kwali tare suka shiga parlou'n basu iske Aliyu ba ya hau sama tare suka kwashe kaya sannan ta tayata ajiye komai a mazauninsa ,suna aikin Safiyya na zargin Aliyu"Allah yana sama yana kallon abinda Aliyu yake miki shi zai kwatar miki hakinki ,kuma inshallahu nan ba dadewa ba sai ya girbi abinda ya shuka ,mugu azalumi kawai ,kisna tayi dariya tace ayya Safiyya ki daina fadar haka babu abinda zai sameshi inshallahu , mijina mutumin kirki ne wallahi wannan abinda ya faru a tsakaninmu ki ?auka qaddarata ce haka , tayi tsaki "lallai yanzu har wani yabonsa kike ? "To ai bashi da laifi wallahi, bana ganin laifinsa hasalima zuciyata sake qaunarsa take "tab gaskiya zuciyarki bata miki adalci ba " ......
Har kusan shida Aliyu bai sauko ba, tare da Safiyya suka da dafa soyayyiyar taliya wacce taji salad garbage da carote da soyayyen nama kaza sai dataci sannan tayi mata sallama ta wuce.
bayan safiyya ta wuce ya sauko yana mika ha?e da salati ,ko kallon inda take bai yi ba , ya zauna ya dauki remut ya kunna tv ya janyo jakarsa ya fito da computer d'insa ya kunna ya soma duba sakonnin mutanen dake kaunarsa wasu yayi maida martani wasu kuma ya wuce , ganin haka yasa ta mike ta shiga kitchen ta dauko kular data zuba masa abincinsa , ta daura a tire da ruwa da fury ta dauko ta fito , ta ajiye akan table din da computer dinsa ke kai.
ya d'ago kyawawan idanunshi ya zuba mata yana kallonta, murumushi tayi masa mai narkar da zuciya tamkar ba ita ce ta gama cin azaba a hannunsa ba dumple d'inta ya lotsa hakan yasa ta ?ara kyau "kaci abinci sannan ka cigaba da aikin "baza'a ci ba , ki ?auke abincinki yanzu kafin nayi miki rashin mutunci "dan Allah ni da kaci idan ka gama ci sai ka min rashin mutunci ,kalli yadda ka rame kaima, kaki kwantar da hankalinka kaci abinci mai nauyi kullum daga cake sai snaks ...."
Ai ko gama rufe bakinta bata yi ba taji gabad'aya kular abinci ajikinta , a firgice take kallonsa tana kakkabe abincin , duk jikinta ya baci da taliya cigaba kakkabe jikinta tai Allah yasa abinci ya ?an sanyi "bana bukatar komai daga gareki ke ce mayar abinci gashin nan kiyita fama , duk ranar da kika sake min tayi abinciki da bai dadi ,dan nasa ba iyawa kika yi ba , yawon gantali bai bari an tsaya an koya ba , sai na kasheki da duka stupid Kawai mai kama da siffar maciji "...
"duk yawon gantalina dai da darajata ka ........"
Saurin katse maganarta tayi ta kwasa aguje saboda ?o?arin mikewa da yayi "da ki tsaya mana kiga yadda zanyi dake ?aramar mara kunya ? "Kuma wallahi ki dawo ki gyara gurin nan minti goma kacal na baki ,ya dauki computersa ya fita zuwa haraban gidan ya bu?e motarsa ya shiga ya cigaba da aikinsa ....
Bayan ta gama aikin gyara garin daya abinci ya 'bata d'aki ta koma tayi wanka ta sako wata doguwar riga milk colour kusan yanayinsu daya data safe data saka sai dai ita wannan mai karamin hannu ce ,kuma shara shara dan kana iya hango jikinta bata d'aure gashin kanta ba tabarshi ya zubo gadon bayanta ta koma parlou'n ta tsurawa tv ido wanda a zahiri ba kallon take ba hankalinta na gareshi ,
bai shigo parlou'n ba sai bayan isha'i , ?auke kanshi yayi ya hayewarsa sama ,yau ma bacci suka yi kamar yadda suka saba, tana kan gado yana kan kujera yayinda baccin nata ya kasance rabi da rabi tana yi tana bu?e idanunta akan shi ,shi kuwa tsakaninaa da Allah yake sharar baccinsa sai tayi kamar ta sauko ta kwanta ajikinsa sai zuciyarta ta gargadeta a haka har bacci bawon yayi awon gaba daita.."
*****
Washegari
Tsaye yake a gaban dress mirrow ,jikinsa sanye da rigar wanka yayinda hannunsa ke rike da towel , ya cire rigar wanka ya goge sumar kanshi da fuskarshi yabi jikinsa da lotion sannan ya feshe jikinsa da turaruka masu sanyi kanshi ya tsuke cikin suit baki masu matukar da tsada , ya da'ura agogon dimond a tsintsiyar hannunsa ,ya dauki culmb ya gyara sumar kanshi ,yana ?o?arin ?aukar briefcase dinsa ta shigo d'akin tana rausaya wanda ya zame mata jiki dan idan basaninta kayi tun asali ba ,zaka ?auka yanga take ,wata hadaddiyar riga ce har kasa ajikinta rigar tayi matukar yi mata kyau sosai kamar dan ita akayi , abunka ga farar mace sai rigar ta haskakata sai kamshi take zubawa " fuskarta ?auke da murmushi tace amincin Allah ya tabbata a gareka mijina barka da Safiyya ,ina ta sauri nazo na shiryaka shine har ka shirya ko ? " ta fad'i hakan tana kallonsa tabe baki yayi yana jan dogon tsaki yana tare da d'aga mata hannu yana mata gargadi sannan ya maida hankalinsa ga kofo ta kai hannu zata amshi briefcase din hannunsa "bana bukatar hauka plz yabi gefenta zai wuce , tabi bayansa da kallo "ka?an kadan dai tunda ka sauke ra'ayin barin wutan lantarki a kunne ka siyo kayan abinci yau gashi ka manta baka kulle kofa ba wata rana zaka canza tana cikin zance zuci ya dawo d'akin , gyaran murya taji har ta tsorata ", dauki abinda zaki ?auka zan kulle d'akina ....."
Mmn sudais
????????????
CUTAR DA KAI
????????
????????????
~TRUE LIFE STORY~
Free Page 4
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalmi, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ?aya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096,
yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ..."????
.....tsuru tsuru tayi kamar mara gaskiya tana kallonsa "ki fito mana saboda baki da manners kin wani tsareni da wadannan shegun idanuwan naki masu kama dana aku common get out ya fada a fusace kamar zai dauketa da mari , k'arasawa tayi inda hijab d'inta yake ta d'auka don gabatar da sallah ,dan bata san lokacin da zai ?auka ba kafin ya dawo gidan ."
cike da sanyi jiki take d'aga zara zaran yatsun kafafunta ta fito daga d'akin ta tsaya tana ci-gaba da kallonsa ,ya janyo kofar da karfi ya kulle ha?e da murd'a key "meye na wani tsayamin akai kamar kina bina bashi ? "dan Allah malama ki wuce banason ganin wannan banzar fuskar taki ,kin wani tsareni da ido kamar zaki cinyeni ko zaki cinye ni ne?" Yayi maganar a fusace yana zaro mata idanu ,Tayi saurin girgiza masa kai alamun "a'a "ko wani naga zai cinyeka ai sai inda karfina ya ..."...
"ya isa dan Allah malama bance ki qara da dogon sharhi ba dan bana bukatar jin komai daga gareki hasalima na tsani ganinki a kuda dani bare wannan shrgiyar muryarta ki ,yana gama fa?ar haka ya raba ta gefenta ya wuce yana d'aga kafafunsa kamar baya son taka kasa , wani sabon abin mamaki suna isa parlou'n kasa ya canza wuta kamar yadda ya saba a tun farkon zuwansu "bance karki yi changeover ba , kiyi duk yadda kike so jikinki ne zai gaya miki idan na dawo ,ya kama hanya ya fita yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa ."
Naunayen ajiyar zuciya ta sauke da karfi tana dafe goshinta "daman haka Aliyu yake ?" "daman zai iya rashin mutunci da rashin imani haka ?" shiru tayi tare da kwanciya akan doguwar kujera , ta shiga tunanin rayuwa idan akace mata akwai wata rana da zata zo rayuwarta ta dawo haka zata karyata ,sai gashi tazo mata fiyye da tunaninta, nasan halinsa tunda na zauna dashi ban ta?a samun matsala dashi ba ,bai ta?a aikata min laifin komai ba, yasan duk abinda zai yi ya faranta min rai , idan nace wannan abun baki ne ,to muradi zai ce bakinkirin ne , bai ta?a sa'bawa umarnina ba, duk abinda ya biyo baya daga gareki ne kisna , ba kuma zan lamunta ba ......" wannan shine maganganun mahaifiyarta a lokacin da zasu baro Nigeria .
ta sauke numfashi "zan d'aure mummy ,Kuma zan sanyawa zuciyata hakuri sannan zanyi ?o?arin na nasan yadda zan janyo hankalinsa gareni."
Shi kuwa Aliyu tunda ya bar gidan zuciyarsa a cukunshe take da bakinciki mara misaltuwa , ya kasa manta abinda tayi masa a baya "ka manta komai aliyu ko dan darajan iyayenta, sunyi maka komai arayuwa , mutun kan ci daraja wani nasa mai imani inji cewar wankakkiyar zuciyarsa "surukina kuma d'ana muradi , kai kasan halakar qaunar da take tsakanina da kai , ina sonka fiyye da komai a rayuwata ,ina rokon alfarmarka ka kasance tare da kisna muddin rai , kasan yadda nayi fama daita a can baya ,gashi a karo na biyu zata dawo hannunka , wannan abu bakaramin faranta min zuciyata yayi ba , bazan iya kwatanta maka farinciki da nake ciki ba , ada ta kasa fahimta komai ,amman a yanzu ta fahimci komai zaka ji dadin rayuwa daita, nasan kai mutun ne da d'aukaka ko matsayi bazai ta?a canzaka ba, ada tayi kuskure , a yanzu kuma tana son gyara kuskurenta na baya kayi hakuri ka bata dama " nasihan mahaifiyarsa kuma mahaifiyar kisna kenan gareshi har ya isa ma'aikata tunanin magangagun mummy ne ke yawo a cikin kwakwaluwarsa "
"Wunin ranar kwance tayi sa tana saka da warwara , sallah ne kawai ke taddaita, yamma nayi ta shiga Kitchen domin girka abinci dare , bubbud'e wundunan Kitchen din tayi domin taga hasken aiwatar da aikinta ,abincin da tasan yafi so shi tayi ?o?arin d'aurawa , tuwon shikafa da miyar wake "Yau mijina zai ji dadi abinda yake so zan girka masa tayi maganar a kasan zuciyarta , shiru tayi bayan ta d'and'ana miyar , jikinta yayi sanyi sosai saboda tuno baudadden halinsa da tayi, "ban sani ba ko zai ci abincin nan ko bazai ci ba ? " Tayiwa kanta tambayar ..
"komai nayi masa sai ya gwasaleni ya kama fa?a da zagina alhalin yasan banason daya daga ciki , ya zakiyi kisna haka zaki cigaba da hakuri dashi har zuwa sanda Allah zai sauko miki dashi , ta gama komai a tsanake ta shirya dinning ta shiga bayin dake manne da parloun tayi wanka ta sake maida kayan jikinta data cire tazo ta raku'be guri daya tana jiran dawowarsa ".
*****
Karfe takwas daidai ya shigo gidan a gajiye hannunsa rike da jakar laptop d'insa , ya zaro wayarsa ya kunna sannan ya d'aga idanunshi da suka koma ja , ya sauke akan abun canza wuta , ya canza haske ya haska gidan gabad'aya sannan ya soma daga kafafunsa da kyar saboda kanshi dake masa wani aza?a??en ciwo , ta mike da sauri ta karaso gurinsa "sannu da zuwa zata amsa jakar hannunsa ya watsa mata wani mugun kallo batare daya amsa mata sannu da zuwan data yi masa ba , ya wuceta ya ajiye jakar computer dinsa akan kujera dan akwai aikin da zai yi a daren , ya furzar da iska kana a hankali ya nufi step yana takawa ?aya bayan ?aya cikin izza tamkar wani jinin sarauta ."
tsayawa tayi cak tare da bin bayansa da kallo tana tunani abun yi "aliyu na tozartata dayawa yana wulakantata tamkar bai san daga inda ta fito ba ,ada can baya ba haka yake ba, ba haka tasan shi ba ,ta ina zata fara irin wannan rayuwar da yake muradi daita? bazata iya ba gaskiya ,dan haka duk yadda zatayi sai tayi ta shawo kanshi su zauna lafiya , sannan zata lalla'bashi yaci abincin data dafa masa koda kuwa zata samu tukuncin duka da mari ne daga garesa zata d'aure tayi iya kokarinta, bayansa ta biyo da hanzari koda ta shiga d'akin yana zaune a kan doguwar kujera ya rike kanshi dake sarawa da duka hannuwansa ,sosai zuciyarta ke bugawa da ganin yanayinsa ,ta karaso garesa ta kudurce aranta komai zai faru sai dai ya faru amman zata jure duk wata azaba daga garesa , tsugunawa tayi a gabansa ta zuba masa narkakkun idanunta tana jin zallar qaunarsa na ratsata "meke damunka aliyu ko baka da lafiya ne ?" tayi masa tambayar hawaye nabin kuncinta ji take duk duniya babu abinda take qauna sama dashi, ta kai hannu zata riko hannunsa yayi saurin fixge hannusa yana jan tsaki "karki ta?ani wai dan Allah me yasa kike son kawowa rayuwata hari ne alhalin kinsan bana son kusancimu tare ?" shiru tayi tana ci-gaba da kallon yadda yake motsa lip's d'insa " kamar baya son magana komai nashi a natse kuma a yangance , "Baka son kusancimu gashi kuma Allah ya had'amu tare ,kuma ina Sa rai mutuwa ce zata rabamu ......."
Mtsssss ya ja dogon tsaki yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa "wannan kuma damuwarki ce dan Allah ki fita daga d'akin nan banason damuwa kuma bana son Kallon fuskarki yana gama fadar haka ya mike ya soma cire kayan jikinsa yana ajiyewa a saman gado bata daddara ba ta dinga bin kayan daya bayan daya tana ?aukewa tare da kai su ma'ajinsu , ya saura daga shi sai boxcer ya janyo towel ya da'ura a wuyansa zai shiga bathorrom tayi saurin rungumeshi tsam ta baya "ka bar zuciyata da rashin sonta da bakayi dan Allah , ka daina hukuntani haka ya Aliyu ,ka tausaya min idan kana careles dani zuciyata zata iya bugawa".
"kece da kanki kika *CUTAR DA KANKI* "nasani wallahi nice, nasan nice , na *CUTAR DA KAINA* nasan ka d'and'ani damuwa mai yawa a tare dani , amman ka yafe min abinda nayi maka ,nasan nayi kuskure , dumin jikinsa ya ratsata tayi saurin runtse idanunta "jikinka da zafi ya Ali , "da alamun baka da lafiya , juyowa yayi tare daita ajikinsa suna fuskantar juna sannan ya zareta a jikinsa ya shige bathoroom batare daya bata amsar tambayarta ba ".
Bathtube ya shiga yai having shower ya dade yana sakarwa kanshi ruwa tukunna ya fito tana tsaye tana jiran fitowarsa , yana goge jikinsa ta karaso ta soma taya shi ",dakata dan Allah malama bana son kina ta'ba min jiki "amman da....."enough I don't want to hear anything from you ,cire hannuwanta tayi ta ajiye ?aramin towel a mazauninsa ta ja ta tsaya rungume da hannuwanta duka a qirji tana kallonsa yana goge ko'ina ajikinsa ya d'auko kayan shan iska ya saka farin wando da farar riga , ya fesa turare mai sanyi kamshi , ya zo ya wuceta ya sauko zuwa falon kasa ta sake biyo bayansa da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 21