maganar kisna ta fito daga bayi gabanta ne ya shiga faduwa da karfi ko ba'a fa?a mata ba tasan da wacce yake magana "?"Karki damu zaki ganni nima ina son ganinki ta sake maimaitawa kanta na kanta kalmar , ta dawo kusa dashi ta durkusa bisa gwiwowinta tana kallonsa kasancewarta agurin bai sa ya katse kiran ba sai ma cigaba da wayarsa da yayi daga karshe yace" me too tasan duk yadda akayi kalmar i love You aka furta masa idanunta yayi raurau da hawaye "dan Allah kace ka yafe min laifin dana maka sannan ka sake bani dama Ina sonka Aliyu mai yasa bazaka soni ba "?
"Bani da ra'ayin sonki , ko yin wata muamula dake ,ki rayu dani cikin wannan rayuwar ko ki rabu dani ki auri wanda zuciyarki ta kafu akan soyayyarsa tun farko ba damuwata bace , wannan da kika ji muna waya daita sunanta nawal nasan kina da labarinta itace matar da zan aura sai ki shirya zama daita idan fa zaki iya idan bazaki iya kofar gidan Aliyu a bude take ". yana gama fadar haka ya juya mata baya ta mike tsaye hawaye ya gangarowa daga idanunta kafafunta take d'agawa a hankali tamkar bata da laka ajiki "nawal ta furta sunan a fili dan Allah karki shigo rayuwarmu nida mijina yanzu ma yaya aka kare ,nasan idan kin shigo ko kallona bazai ba , har ta hau kan step zance zuci take ta shiga Kitchen ta soma kwabin fulawa dan yi masa samosa haka ta dinga aikin tana zance zuci tana hawaye tamkar wata mahaukaciya sabuwar kamu ,hawayen idanunta yaki tsayawa bayan ta gama samosa ta dibo arish ta bere ta soya da kwai sannan ta d'aura ruwan zafi ."
Tana tsaye a kitchen ya sauko parloun kasa fitowarsa kenan daga bayi jikinsa sanye da gajeren wando baki da farin singlet ,wuyansa rataye da farin towel yana goge fuskarsa zuwa wuyansa , yayinda kafafunsa ke sanye da bakin silifas yana tafiya yana goge jikinsa , kai tsaye kofar Kitchen ya nufa dan ?aukar fury har ya kawo bakin kofa yaji sautin qarar dayan wayarsa dake ajiye a parlour tun jiya ,ya juyo ya dawo ya ?auki wayar ya manna a kunnen "hello Samir ya garin"? " da fatan komai lafiya ko ? lafiyata qalau na gaya maka fever ne kawai kuma anyi maganinta kaine aji farko fa ,daga can bangaren dady ya amshi wayar suka gaisa ya masa ya jiki "dan zazza?i ne kawai fa dady me yasa zai fa?a maka dan kawai ya tadda maka hankali "to ya saukin jikin "?"Yanzu lafiyata qalau inshallahu ma gobe zan fita zuwa office "okay naji dadin abinda kace ba damuwa za'a yi komai yadda ya dace samir ma zai shigo karshen wata tare da mummynku dole ayi tafiyar dashi gashi Samir din yace zaku je buga wasa spain ko ".?
"Eh haka ne dady ".
"to shikenan Allah yayi jagora idan kun dawo sai kuje hollond da Austaraliya ayi abinda ya dace "to shikenan dady sai anjima ya katse kiran ya shiga Kitchen kamshi ne ya bugi hancinsa ya zagayeta ya bu?e fridge ya ?auki abinda ya shigo dashi ya fita .."
shadaya da rabi na safe ta gama komai har da break fast ta gyara gidan ta hau sama tayi wanka dan zuwa lokacin tuni ya sauya kaya zuwa na gado wato kanana kaya zuwa wando da riga duk blue Black , tun ganiyar kuruciya bata sake ganinsa da manya kaya ba ,sai ranar daurin aurensu ,kuma tun daga lokacin bata sake ganinsa dashi ba, daga suit sai wondo da riga".
wardrobe ta bude inda ta jera kayanta ta tsaya tana karewa kayan kallo ta dauki doguwar riga ja wanda aka tsaga bangaren kafarta ?aya har zuwa cinyarta hannun riga daya dan tsiriri ne yayinda d'ayan hannun ya zamanto dogo ta taje gashinta ta fakashi a tsikiyar kanta tasa ribbon ta kama ta fito ta zuba masa chips da soyayyen kwai da tea Mai kauri ta kawo masa inda yake zaune yana danne danne a system ta ajiye "kayi break kasha magani " gyaran murya kawai yayi ya cigaba da abinda yake ta juya zata bar gurin "ummmmm ummmmm ummmmm yayi sound din Kamar Waka ta juyo da sauri tana murmushi "kana magana ne "?
Ya d'ago ya bar abinda yake ha?e da tsura mata idanunshi "tana da damuwa a rayuwarta , daman haka take shi bai sani ba , shi da yake daukarta mai mugun girman kai da taurin kai da rashin son shiga lamarin mutane, a she abun ba haka bane shegen rawar kai ne daita kamar farar kura da surutun tsiya , yatsun hannunta ta kamo ta soma wasa dashi tana kallonsa , kawar da kanshi yayi yana jan tsaki bai gama takaicinta ba yaji ta soma waka har da dan rawa ..,"
"Omo walai if them pont gun to my head say make I deny you I go tell them say lallai Ni be lie.
"I fit spen all of my money on you (oh ho)
"Speed a couple million you (yeah yeah )
"Give you loving tell you say e don do (yeye)
Special type of felling that I feel when am with .......
" Enough dan Allah Malama bana son hauka anan ya fada a tsawace yana watsa mata kallon banza " shiru tayi tana dubansa kamar ruwa ya cinyeta ganin ya hassale tace "kayi hakuri dan...... " jeki dan Allah banason hayaniya kin wani cika min kunne da banzar waka da wata muraryarki gangarin da bata dadin sauraro ,tsimi tsimi ta bar gun tana tabe baki ,yace " mahaukaciya kawai ji yadda take faman wangale baki kamar wata shasha ya yaja tsaki tare da maida kanshi a kan computer..
Tunda ta koma sama ta kwanta lamo tana tunanin rayuwa bata sake yunkurin saukowa kasa ba , sai misalin karfe hu?u na yamma , shima gabanta taji yana ta faman faduwa da bugawa ,ta sauko a natse take daga kafafunta , aiko idanunta suka ci karo da mugun abu ,dan kuwa wata matashiyar mace ta gani zaune a gefen mijinta ,sanye cikin doguwar riga blue black wacce aka yiwa aiki da zare milk colour a gaban rigar da hannun rigar , ta nad'e kanta da mayafi milk colour ,haka kafafunta sanye da takalmi blue black da ratsin milk colour , shekarunta zasu zarta nata a haihuwa, tana rike da yatsun hannun Aliyu cikin nata tana murzawa tare da yi masa sannu .
a hankali ta dinga takowa jiri na dibanta har ta karasa saukowa "Allah sarki my love sannu kaji Allah ya baka lafiya kaga da muyi aure bazan taba barinka kai kadai ba ,dole ina tare da kai a cikin wannan yanayin , kusan abinda tafi furta masa kenan ,yayinda kisna ke binsu da wani irin kallon mamaki "a gidan aurenta wannan film din ke faruwa ?" Take zuciyarta ta dinga tuttukin tana zafi da ciwo taji kamar taje ta rufeta da duka har sai taga bata mosti, sai dai sanin cewa bata da wani power agurinsa yasa ta d'auke Kanta akansu ta nufi kofar shiga kitchen zuciyarta na wani irin tsalle da rad'ad'i , tana gama shiga ta danne lip's d'inta na kasa da hakorinta da karfi tamkar zata fasa lebanta "ya Allah me ya kamata nayi yanzu "?"Na ?auki mataki akanta ne ko kuwa na hakura na kama girmana ?"Ki hakura ki kama girmanki kisna idan abu mai kyau tayi miki da sannu zata ga sakamako, idan ma akasin haka ne shima zata girbi abinda tayi tunda itama macece "mai yasa kika zo gidana ?" Ta sake furtawa a fili
"Mai yasa bazaki bari har sai kin kasance mata a garesa ba ?"
"Mai yasa na sauko? " da nayi zamana a sama da ban ha?u da wannan tashin hankalin ba , cikin sheshekar kuka take wa?an zantuttukan "mai yasa Aliyu ?kasan ina tsananin sonka dole zanji babu dadi a raina idan naganka tare da wata ". "mai yasa ka bata dama zuwa inda kake alhalin kasan kana da mata ?"Mai yasa zaka min haka Aliyu ?"Why! why!! why !!!do you this to me Aliyu ?".
"A cikin soyayyar da nake maka har yanzu ban bayyana maka rabi daga ciki ba, ka tausaya min kar zuciyata ta tarwatse akanka " na fita sonka da bukatarka , zan sadaukar maka da dukkanin farincikina , ka yarda dani dan Allah ka bani dama akwai sauran lokaci da zan gyara zamantakewar mu ,Aliyu duk abinda nayi maka ba yin kaina bane , zugar aunty afra ne gashi tasa na dasa kiyayyata acikin zuciyarka tun daga zamanin kuruciyata har zuwa auremu ,plz forgive me and forget what I did to you ,nasan kayi tsananin fushi dani ne shiyasa baka shayin aikata mummunar abu gareni ,sai dai bazan iya ?aukar zuwan wannan matar gurinka ba ,I will be able to handle this situation tana cikin wannan halin ya shigo kamar an jihosa bataji motsin shigowarsa ba sai tsayuwarsa a gabanta taji yana huci tamkar mayunwacin zaki"uban me kike yi ?
"Ko baki ga anyi bakuwa bane da zaki wani tsaya batawa kanki lokaci ki kawo mata wani abu ta sha ".
Tayi saurin gyada masa kai tana goge hawayen dake kwance akan kuncinta "da kyau kuka ba ?". ya fada yana kai hannunsa ya dago ha'barta Yana kallon cikin kwayar idanunta tayi saurin girgiza masa kai alamun "a'a ".
"uban meye wannan idan ba hawaye ba da zaki ?aryatani ?"Shine amman kayi hakuri bazan sake ba ta fada muryarta na rawa ya ingiza ta baya da iyakacin karfinsa tayi taga zata fa?a tayi saurin rike Kitchen cabinet ta tsaya bisa kafafunta tana sauke numfashi da kyar "haka nake so kullum nayita ganin zubarsu har zuwa sanda zuciyarki zata buga ki mutu ......".Ya karasa maganar yana sakar mata tsadadden
murmushinsa ,"minti a shirin na baki ki shirya mata abinda zata ci yayi baya ka?an yana kallon falon "my nawal mai zaki ci ?".....
Mmn Sudais
????????????
CUTAR DA KAI
????????
????????????
~TRUE LIFE STORY~
Free Page 7
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalmi, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga bukatar siyan ?aya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ..."????
Tambayar da yayiwa nawal yasa ta mike tsaye cike da yauki da rausaya ta soma takowa zuwa bakin kofar Kitchen din ,ta tsaya a gabansa tare da rungume hannuwanta duka a saman qirjinta ta tsura masa idanunta tana kare masa kallo ,ganinta tsaye a gabansa yasa kisna juyawa da sauri tana danne kukan dake shirin kufce mata dan babban abun kunya ne gareta ta bar nawal taga hawayenta ko damuwarta "me zaki ci a dafa miki my nawal ?". sautin muryarsa ta doki dodon kunnen kisna ,take zuciyarta ta cigaba da dokawar da take a tun sanda ya shigo kitchen din , cike da sihirtaccen kaunar da nawal take wa Aliyu ta sake matsowa jikinsa tamkar zata shige masa ta kai hannunta ?aya ta shafi gefen fuskarshi cikin shaukin son shi tare da jin dadin kulawarsa gareta "tabbas Aliyu na matukar sonta tunda har zai iya mata irin wannan karramawar a gidansa".
"i love You so much my love ta fa?a tana kashe masa idonta ?aya "I love you too my nawal ki fa?a min abinda kike son ci "?nawal ta saki murmushin jin dadi tace "my love karka takura min kanka da auntyna banason wahalar da....."
Aliyu bai barta ta k'arasa maganarta ba ya katse mata hanzari "nasan halinki da rashin son cin abinci just tell me what you ... .."
itama saurin katse shi tayi ta hanyar sakala hannunta cikin tafin hannunsa ta soma masa tafiyar tsutsa yayinda idanunta ke kanshi ta soma tafiya da baya da baya dashi , tana masa magana a shagwa'be .
"Cikina akoshe yake my love if not da zan so naci wani abu a gidanka kodan na sake faranta maka ". wani irin yanayi na zallar sha'awa ya tsinci kanshi ciki gabad'aya tsigar jikinsa ta mike gabadaya mazantakarsa ta motsa abunka ga lafiyayyen namiji ya sausauta muryarsa sosai kana yace"ok my nawal " .
a sukwane kisna ta juyo idanunta ya sauka a cikin na nawal sakamakon fuskarta na kallon kofar Kitchen , murmushin gefen baki kisna ta sakar mata tana mai danne abinda taji ya sauka a tsokar dake makale da qirjinta ,itama nawal din murmushin barikanci ta sakarwa kisna tana sake shigewa Aliyu kamar zata ratsa gangar jikinsa .
"Yau naga abinda yafi karfina , anya kuwa rayuwata zata d'aure a gidan nan idan wannan yarinyar ta shigo ? ta yiwa kanta tamvayar ha?e da kawar da fuskarta hawayen bakinciki na gangaro mata ."inna lillahi wa inna ilaihi rajiun kawai ta shiga furtawa tana maimatawa domin neman sausauci daga gurin Allah ..."
Nawal ta zaunar da Aliyu sannan ta zauna suna fuskantar juna ta matso da fuskarta sosai suna sha?ar numfashin juna bai an kara ba yaji saukan lip's d'inta akan lip's d'insa tana yawo dashi a daidai lokacin da kisna ta sake juyowa gabanta yayi wani irin mummunar fad'uwa ,ta dinga jin kamar zuciyarta zata kama da wuta, Gabadaya yanayinta ya sauya , numfashi ma da kyar take janyowa tana fitarwa zuciyarta na wani irin tuttukin bakincikin , ta ?auki wuka tana kallonsu "naje na tsoka mata wukar nan a kahon zuciya na kashe shegiya na huta ."No no karki yi haka wannan ai haukan kishi ne ,"to bari na d'aura ruwan zafi nayi mata wanka dashi ta soma ?o?arin kunna gas "kai shima wannan ba mafuta bane gara ki nemo abinda zaki mata cikin sauki ki korata ta sake maida idanunta akansu zuciyarta na wani irin zafi da ciwo ."
Aliyu na shirin kawar da fuskarshi yaji ta cafki bakinsa ta soma tsatsa kamar ta samu sweet , kisna tayi saurin runtse idanunta tare da yin kasa dafe da kirjinta dake tafarfasa tamkar an daura mata wuta , Aliyu ya kasa hana nawal aiwatar da abinda take so akanshi saboda feeling din da yake ji yana ratsa sansar jikinsa , batare daya ce mata uffan ba ta cigaba da sha bakinsa tana sauke numfashi dan wani irin sanyin dadi taji yana ratsata da kai wa kwalkwaluwarta sako na musamman ,wannan shine karo na farko da suka fara musanyawar yawu a tsakaninsu kuma kowanensu yaji sauyi na dabam ajikinsa shiru yayi ya cigaba da amsar sakon nawal bisa ra'ayinsa guda biyu na farko ragewa kanshi feeling , na biyu kuma dan ya sake tarwatsa zuciyar kisna tasan yana da martaba da darajan da za'a so shi......"
sai data tsotsi bakinsa sosai kafin daga baya ta saki tana sauke numfashi , shi kuwa komawa yayi ya jingina bayansa da kujera yana fidda numfashi "na matsu sosai my love , burina bai wuce mu kasance ma'aurata ba , yayi mata shiru yana lumshe mata ido dan shi kadai yasan yanayin daya tsinci kanshi a lokacin da take tsotsan bakinsa a hankali ya bude idanunshi akanta ya lura gabad'aya yanayinta ya sauya da gani da za'a wuce shan baki bazata hana ba ,shima ya kai zuciyarsa nesa ne bancin haka da yaso ya murza dukiyar fulaninta a tare suka sauke numfashi suna kallon juna yayinda kisna Ke kai sosai har da shesheka zuciyarta na zafi "mai yasa bazai soni ba ,bayan ina da duk abinda yake so ...?"Dan Allah ya Aliyu ka tausaya min wallahi zan kasance maka yadda kake so ,zan baka farinciki da kwantar maka da hankali ,zan kula da kai ,zan baka rayuwata hatta numfashina zan iya sadaukar maka dashi ka tausaya min ta karashe maganar tana wani irin kuka mai ban tausayi ".
bayan kamar minti biyar kisna ta goge hawayen dake kwance akan kuncinta ta fito a natse tamkar bata tare da wani damuwa hannunta rike da jug ?auke da ruwan sanyi ta ajiye a gaban nawal batare data kalli inda take ba hatta aliyun bata kalleshi ba ,ta juya a hankali tana taku tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta haye saman d'akinsu , zariya ta shiga yi a cikin d'akinta tana zance zuci kanta kamar zai tsage gida biyu tsabar bakinciki, kwakwaluwarta ta shiga cajin da tunanin neman mafuta ,dan dole tasan abunyi tun lokaci bai mure mata , idan ta bari wannan yar iskar matar nayi mata karuwanci a gida tun yanzu shinkenan zata rainata kuma kashinta ya bushe , tana tsaye ya shigo d'akin kallo ?aya yayi mata ya dauke kanshi aranshi yace "wahallaliyar banza kawai baki ga komai sai nayi nasanadin da zuciyarki ta buga ya soma cire kayan jikinsa ya ?auki towel ya taraya a wuyansa da alamun wanka zai shiga ,take ta sauke wani wahalallen numfashi , wani dadi ya lullu'beta ta samu damar da zata fattakar wannan yar iskar mata a gidanta ,yana gama shiga bayi ta fito daga d'akin ta kulle kofar ta bar key ajikin ta dawo parlou'n kasa inda nawal take zaune , wani irin mugun kallo mai ha?e da harara ta sakar nawal dake zaune kafarta ?aya akan ?aya tana girgizawa tana sake karewa falon kallo , gabanta ne yayi mummunar fad'uwa da ganin irin kallon da kisna tai mata , a hankali ta motsa bakinta "sannu da .......".Kisna tayi saurin katse mata hanzari ta hanyar d'aga mata hannu "sannun uwarki da ubanki zaki min amman dai ke anyi tsohuwar kilaki tsohuwar yar tasha ,jaka shasha ballagaza da bata san ciwon da darajan kanta ba , yanzu har rashin kamun kanki ya kai ki kwaso wa?an nan tsilla tsillan kafafun naki kamar na jemage ki zo gidan saurayi ? nawal ta cika da tsananin mamakin kisna ta bu?e baki zatai magana kisna ta sake d'aga mata hannu "dakata malama bana bukatar jin komai daga bakinki ,idan ki kayi ganganci bude wannan dan iskan bakin naki sai na lahira yafiki jin dadi dan sai zubar miki da ha?ora , maza maza second biyu kacal na baki ki tashi ki bar min gidana kafin na tura miki wannan abun a gidan kashinki dakikiya mai fuskar alade ta nunata da sekundireba ...........
"an gama yawon tazubar da karuwanci an rasa mashin shini shine za'a lekewa mijina ,na sake ganin wa?an kafafun naki masu kama dana jemage sai na lalata miki rayuwa , ai wallahi Allah ya taimakeki da kinci abincin gidana da kin tabbatarwa kanki mutuwa, domin guba zaki ci oya out ta kai hannu ta janyo wuyan rigarta ta soma tafiya daita bata tsaya a ko'ina ba sai a haraban gidan ta saida ita a jikin motarta "to be your first and last warning da zaki tako zuwa gidana a matsayinki na karuwa ,ki tabbatar da aure ne zai kawoki gidan nan ba karuwanci ba ta karasa maganar tana buga mata sikundireban hannuta a baki .
nawal ta saki ?ara mai sauti tare da rike bakinta cikin azaban zafi ta juya ta bu?e motarta ta shiga ta zauna zata maida murfin motar ta rufe ,kisna ta rike "bance karki fa?a masa ba ki fa?a masa dan girman Allah kiga yadda zanyi dake , wallahi sai kinga kudi kince kashi ne shashar tumakiya sannan kuma zaki iya cigaba da zuwa gidan bazan ce karki zo ."cikin rawar jiki nawal ta bar gidan tana zubar da hawaye "
kisna na ganin tafiyar motarta ta saki murmushin jin dadi "kadan kika gani wawiya ta juya da sauri taje ta bu?e kofar ta dawo parlou'n kasa ta zauna tana kallon tv qirjinta na bugawa da karfi a natse ya sauko falon yaga wayam babu nawal babu alamun , yace" ke ina yarinyar nan "?.
"Wacece haka ? Ta tambayesa tana hura hanci "Banason iskanci nasan kinsa wacce nake nufi yayi maganar a zafafe yana tsareta da idanunshi "to ni ina zansan inda take tayi maganar a shagwa'be mutumin dake zaman kansa har a tambayi inda yaje "wacece ke zaman kanta ? yayi maganar yana ?o?arin damkar makoshinta ta goce ha?e da mikewa tsaye tayi nesa dashi kirjinta na bugawa ..."Wallahi ki kiyayeni idan ba haka ba zan bata miki rai "to ni me na maka kodan ban da gata shi yasa kake min abinda kaga dama ? Ko Zaman daduro muke da kai ya dace ka gayyato budurwarka gidan nan har ma ku zauna kuna iskanci alhalin ga matarka sunanh a gidan ?
"Da wa kike wannan Maganar ya kara taku biyu zai cafkota ta buge hannunsa ta zura aguje "ni ka kyaleni karka dokeni bata tsaya a ko'ina ba sai a karshen step tana haki tana hura masa hanci ..."
"Zaki sani ne kuma zan kamaki cikin ruwan sanyi , zaki san baki da kunya dan wallahi sai na fasa bakin rashin kunya, kuma ki bari na kira nawal naji tace kin mata wani abu sai kin gane baki da wayo kamewa tayi guri daya ta rungume hannuwanta tana kallonsa tana fargaba, tasan idan nawal ta fada masa abinda tayi mata sai ya mata dukan mutuwa dan haka ta tsaya jira ya kirata taji yadda abun zai kaya ,idan taga dukan zai yi ta shige daki ta kulle ta barshi yayi kwanan falo .."
Tana kallonsa ya dauki wayarsa yana ?o?arin neman layin nawal kiran cochi dinsu ya shigo ya zauna yana amsa wayar " hello Mrs birsat kwana biyu bamuyi waya ba, ya kake ya kwana biyu ?". "yanzu kake nufi to shikenna ka dan bani lokaci zan kiraka back ..."ya katse kiran yana neman na Samir...
Bayan sun gama waya da Samir ya sake kiran mr birsat yayi masa bayani komai a natse sannan ya soma neman nawal ,tana ?auka yaji gabad'aya muryata ta sauya "me yasa kika wuce bayan nace ki jirani ?
"Kayi hakuri dan Allah na samu kiran gaugauwa ne "akwai kiran gaugauwan daya fi dokata mahimmanci? " kin fa san banason saba doka "kayi hakuri bazan sake ba yayi shiru yana kallon kisna dake tsaye tana kallonsa can yace "me yasa muryarki ya sauka kamar ma kuka kika yi ?"No babu komai fa wallahi mura ce ke son kamani Kuma nasha magani "ke dai ki fa?a min gaskiya idan akwai wani abu "babu komai ta fada a takaice tana danne kukanta duk yadda Aliyu yayi daita ta fada masa abinda ke damunta taki saboda taji tsoron gargadin kisna ..
******
Kwance yake akan gado hannunsa rungumeta da pillow yayinda idanunshi ke kallon celling d'akin, sosai yayi zurfi cikin tunani wayarsa ce ta ?auki qara ya kai hannunsa ya lalubo wayar yana dubawa sunan daya gani yasa ya ?an mike ya jingina bayansa da abun gado "assalamu alaikum "
"Wa'alaiki salam mummuy anyini lafiya "lafiya ya jikin naka jiya samir yake fa?a min baka da lafiya ? Cikin kwantar da murya yace "jiki alhamdulillah mumy naji sauki sosai "Allah ya qara sauki ka kular min da kanka fa ,ya amsa mata da "inshallahu mamana ya mutanen gidan ? "Duk muna lafiya ina ita kisna take ya d'ago ya kalli inda take kwance akan doguwar kujera idanunta na kallonsa, tun sanda daya ambaci sunan mummuy tayi shiru tana sauraronsa tana jin kamar tazo ta fixge wayar a hannunsa ta sake jin muryar mahaifiyarta ."
muryarsa a raunane yace" tayi bacci "okay inshallahu gobe zan kira ka ha?ani daita su aryan sun damu suna ina son magana daita "okay suna kusa ne yanzu ko sunyi bacci "?
"Ai tun takwas sukayi baccin dole ,ya gyara zamansa sosai yana son jin dalilin baccin "mai ya samesu mumy "? yayi maganar hankalinsa a matukar tashe " kasansu da kiriniya d'azu ne suna wasa a parlour daf da magariba sukai karo da juna , aryan ya fasa baki shi kuma areef goshi ,sai da muka dangana da asibiti shine fa muna dawowa sukai bacci
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 21