zarar girma yazo musu zasu tattara su koma jaharsu su cigaba da rayuwa ..."
A wannan lokacin kamar yadda muka samu labari uncle haroon bai bi bayan iyayensa zuwa ilo ba acewarsa mai zai yi a kauye babu wuta babu network babu jin dadin rayuwa tsakaninsa da kauye sai dai kallo ya tattara ya bi wani abokinsa farhan zuwa jos ,duk sanda mommy taje ilo gurin mahaifiyarta dan kai mata ziyara ta dinga mata kuka kenan akan uncle haroon tare da bar mata wasiyya iri iri akanshi , "Idan garba da bature sun juya masa baya salaha karki juyawa d'anuwanki baya " ina son babakarami tamkar raina ,dan Allah kema ki so shi kamar yadda nake son shi ki janyosa jikinki ko bayan raina idan Allah yasa ya dawo kuka hajiya kayi keyi sosai wanda har yasa mommy kuka suka rungume juna gam suna kuka yayinda Alhaji sani yayi shiru yana Kallonsu cike da takaici da bakinciki dan duk tautaunawarsu yana shiga kunnuwansa , kuka suke kamar ransu zai fita , cike da zafin zuciya alhj sani ya tako zuwa inda suke rungume da juna ya fara magana cikin zafin zuciya yana cewa" momy karki kuskura ki ?auki maganar mahaifiyarki da mahimmancin da zai sai ki damu rayuwarki akan takwaran Alhaji dan ko ya dawo garemu bashi da muhalli acikin gidan nan, ban ciresa a cikin ya'yana ba amman na ciresa a cikin zuciyata dan bazan amshesa ba ,ba dai yana gudun zama damu bane saboda bamu da arziki yaje duniya ce gashi nan gata wanda bai zo ma tana jiransa "hajiya kayi ta zabura ta mike tsaye tana fuskantar shi cike da mamakin jin furucinsa sannan tace "saboda me zaka fadi haka alhalin d'anmu ne babakarami bashi da iyayen da suka fimu ",ana ki tunanin ba ai shi bai daukemu a matsayin iyaye ba , kafin kace me gurin ya hargitse da magana da rudani tsakanin hajiya kayi da Alhaji sani zuciyar hajiya kayi ta tsinci kanta cikin rashin natsuwa da jin hukuncin mijinta , ranar tamkar mutuwa akayiwa a gidan mommy da hajiya kayi babu abinda suke sai aikin zubar da hawaye yayinda shi kuwa a lokacin haroon yana can yawon duniya bashi wannan gari bashi wancan gari duk garin da yasan zai ji dadi zashi ,kullum kuma cikin samun sabbin abokai da yammata yake kuma har wannan lokaci mata basu daina kashe masa kudi ba , a hankali har ya shiga harkan neman mata da smoking kamar yadda momy ta samu labari mata na biyansa kudi dan ya kwana dasu , ranar kuwa momy tayi kuka tamkar ranta zai bar gangar jikinta bata fadawa kowa ba ranar da zazza?i ta kwana a jikinta ta aika masa sako ya dawo gida ya bar harakar da yake duk abinda yake so zata masa amman yaki yace shi yanzu bazai iya rayuwar gida ba ..."
Numfashi kisna ta sauke a lokacin data zo nan sannan ta fuskanci safy fuskarta cike da tsananin damuwa tace "a iya nan zan dakata bazan iya cigaba da bakin labarin ba saboda akwai wani boyayyen sirri akan ya aliyu ba kuma zan so wannan sirrin ya fito daga bakina ba ta karasa maganar wasu hawaye na gangaro mata safy ta numfasa tace ,"to ai baki fa?a min yadda kuka yi aure da Aliyu ba dangantakanku kawai kika fada min ni rayuwar aurenku nake son ji " "Muddin zan fa?a miki yadda muka yi aure dashi dole zan bayyana wannan sirri " .
murmushi safy tayi sannan tace" kisna kenan ba dai zurfin ciki ba sai naji kin sake shiga raina ina matu?a son mutun mai rike sirri wanda samun irinku yanzu kuke da matukar wuya, kisna ta gyada mata kai kwayar idanunta na kallon sama dan ita ka?ai tasan yadda take jin zuciyarta a hankali ta mayar da idanunta zuwa ga safy ta cigaba da magana "ciki ba'a yisa dan abinci kawai ba duk mutumin daya kasa rike sirrinsa karka yi tunanin zai iya rike na waninsa ta karasa maganar hawaye na sake gangarowa daga cikin kwarnin idanunta "wannan magana taki haka take amman naso naji yadda kuka yi aure da Aliyu gaskiya " parlou'n ya d'auki shiru babu wanda ya sake yin magana har aunty zee wacce ke aikin mayar da kayan lefe cikin jakunkuna, " Kisna kiyi hakuri ki daina kuka bana son ganin hawayenki yana sani jin wani iri wallahi "ai indai kisna ce yanzu haka take abu kankani ke sata kuka sa?anin da ta mike ta karaso kusa da kisna ta rungumeta suna kukan tare wani abu ya tokare makoshin Kisna dan komai daya faru ya shiga dawo mata daki daki suna cikin kukan muradi ya shigo parlou'n ya iske su
cikin wannan halin suna kuka safy na basu hakuri saurin katse sallamar yayi daidai lokacin da aunty zee ke magana murya can kasa tana gogewa Kisna hawayen " .
kyawawan idanunshi masu matukar kyau da haske ya sauka akan kisna dake zaune tana matso ruwan hawaye tamkar wacce aka yiwa mutuwa tare da kare mata kallon tsab idanunta sun canza daga fari zuwa kore , a hankali ta d'ago idanunta suka hade da nashi wani irin mummunar faduwar gaba taji ,take gaba-daya ilahirin jikinta ya dauki rawa lokacin da kwayar idanunta ya ha?e da nashi kallonsa ka?ai nasata jin abu biyu a lokaci daya, faduwar gaba tare da alfahari kasancewarsa uban ya'yanta .
kusan minti biyar ya dauka tsaye a bakin kofar dakin yana Kallonta sannan ya soma takowa a hankali yana mata kallon kasan ido ,nazarin yanayinta yake, wannan yanayin daya gani a tattare daita yanayi ne na damuwa dan kuwa idanunta sun tabbatar masa da haka guri ya samu ya zauna akan kujera yana kallon safy dake faman zuba sannan yana kallon kisna ta gefen idanu muryarsa a kasalance ya soma magana cikin tsigar tsokanar safy "ya kika ga kayan amaryarta sun bugeki ko "?"Sosai kuwa duk sun burgeni sai dai gabad'aya kayan sunfi dacewa da kisna ba wannan mai kama da busashen bishiya ba, ko ka taba ganinta da irin wannan wa?an kaya"?ta karashe maganar cikin tsigar wasa tare da yunkurawa ta tashi "wannan kuma son ranki kika fa?a saboda kina da wata manufar munafurci a ranki ai sai na zuga mijinki ya qara aure " kalmar munafurcin daya dangantata dashi ya mugun bata rai murmushin takaici tayi tana rataya jakarta "kai ma daka hakura mai mata kamar kisna mai zai yi da wata nawal din banza mai siffar munafuka "? Ta fada tare da nufi kofar fita tun kafin ya antayo mata bakar magana data fi na farko tana cewa "sai anjimanku " aunty zee ce ta mike tayi mata rakiya har haraban gidan kalmar ta bala'in bata masa rai zuciya tazo wuya a hankali ya dinga girgiza ?afarsa daya ...."
Kisna ta mike tsaye ta karasa inda yake ta durkusa muryarta cike da rauni tace "sannu da zuwa " ta'be baki yayi batare daya amsa mata ba , bata damu da rashin amsawarsa ba tunda idan da sabo ta saba da halinsa .
ta soma cire masa canves din dake sanye da kafafunsa hawaye na ziraro mata sanda ta karasa cire masa kafafunsa ya saura da safa kawai , ita kanta aunty zee data dawo parlou'n ta ganta durkushe a gabansa kasa daurewa tayi sai da wasu suka qwalla zubo mata ta kawar da kanta tare da danne abinda taji bawai shishige masa da kisna take bane yafi damunta irin banzatar da rayuwarta da yake kai tsaye juyawa tayi ta nufi kofar fita tana goge hawaye "zainab ya kira sunanta muryarsa a dake cike da ?acin rai tsayawa tayi cak batare data juyo ba "kowa murna yake akan auren nan da zanyi banda ke da wannan yar iskar me yasa kika manta abinda yar iskar nan ta aikata ga rayuwata kunnuwan Kisna suka jiyo mata sautin muryarsa yana fadar haka a can kasan makoshi , kamar ta cigaba da durkuso a gabansa ta cigaba da sauraronsa tare da rarrashinsa da bashi hakuri sai zuciyarta ta haneta dan haka ta mike hannuta rike ta canves dinsa tana kokarin hawa sama kamar zai mata magana sai kuma ya fasa ya cigaba da magana "wallahi kina biyewa son zuciyarki dana wannan abar sai dai bata isa bakincikinta ya kasheni ni kadai ba kamar yadda taso faruwar hakan kafin taga mutuwata ina tabbatar miki ni ne zan soma ganin nata duk da nima nasan bazan cigaba da zama ba amman wallahi tallahi ba zan barta tayi rayuwa mai dadi ba ina nan akan bakana har sai nayi magani iskancin data min numfashin Kisna ya soma fita da sauri da sauri , ta kasa cigaba da daga kafafunta aunty zee ta gigice ta juyo tana kallonsa cikin tsananin damuwa itama Kisna ta juyo tare da tsura masa ido canves din hannunta ya subuce shima kallonta yake cikin tsana muryar a zafafe Kisna ta soma magana cikin kunar rai "kai cika mutun mara imani hakika na soma danasanin kasamcewa mata kuma uwar yayanka a rayuwata ,alfaharin da nake na kkasancewarka ubansu Aryan reef da janye domin sun yi hasarar uba wallahi ,kasani wani bakincikin ne dabam zai kasheni ba sanadin ciwon zuciyar da kake kokarin haifa min ba kuma duk abinda kake yi Allah yana kallonka zai saka min sannan auren nawal da kake ganin yana cikin bakinciki da zaka kunsa min wallahi ko ajikina saboda banga abinda zai sa na daga hankalina akan matar da tsinannu kadangarun bariki suka gama da rayuwarta yar iska da kowa yasan ba yar mutunci bace kawai bakar zuciyarka ce ta hanaka ka fuskanci komai ni kuma da kake kira da yar iska duk iskancina ban bari yan iskan kadangaru bariki sun .........."
shiru tayi sakamakon toshe mata baki da aunty zee tayi tana girgiza mata alamun tayi shiru saurin cire hannu aunty zee tayi a bakinta "ki bari na fadi abinda ke raina ta yaya zai dinga dangantani da kalmar iskanci wallahi duk matakin da kake shirin dauka akaina ka dauka amman ka kwana da sanin cewa Allah bazai barka ba saboda ina da hakki akanka kuma babu inda Allah yace dan nayi maka laifi ka tauye hakina daya rataya a wuyanka ya mike a zuciye yayi kanta yana huci ya daga hannunsa zai doketa yana auna mata zagi aunty zee ta kare "haka zaki kare cikin tsananin bakin ciki a gida nan rayuwar farinciki sai dai kiga ana yinsa a wani gida .."
"da ikon Allah sai Allah ya kunyataka, karewa cikin bakinciki tana gurinka mutumin da baya yafiya tunda har nadamata bata sanya kaji zaka iya hakura da abinda nayi ba hakika zaka ga yadda rayuwa zatayi da kai hakina dana yayana bazai barka ka zauna lafiya ba aunty da zee ta rikesa gam da hannuwanta duka tabashi hakuri saboda jikinsa dake tsuma da kyar ta samu ya zauna yana huci duk cikin maganganun ta babu wanda ya taba zuciyarsa da tsaya masa arai kamar kalmar data danganta nawal daita take gumi ya rufeshi gabadaya ya nemi natsuwarsa ya rasa ji yake kamar zuciyarsa zata buga a yanzu da ya soma jin soyayyar nawal na dan shigarsa shine zata fadi mummunar kalma akanta yasan tayi haka ne dan kawai ta bakanta masa amman bazai yi sakacin da zuciyarsa zata amince da kalamanta ba,cikin tsananin zafin rai Kisna ta juya cikin sauri ta hayewarta sama zuciyarta kamar zata buga ,itama aunty zee ta fita ko dan rarrashin data saba yi masa a duk sanda ya hau sama bakinciki yasa ta kasa sannan taki masa magana akan yadda za'a yi da kayan lefe dan nan ta barsu yasan yadda zai yi dasu ai ta gama mai wuyar , duk yadda zuciyarsa taso ya yarda da kalaman Kisna akan nawal kin yarda yayi domin ganinsa yana yin nasara akan komai dan tun daya taso yake samun nasara arayuwarsa yana da tabbacin zai yi nasarar samun nawal cikakkiyar mace a gidansa kamar yadda ya saba nasara dogon tsaki yaja wayarsa dake qara ya ciro yanayin yadda ya soma magana kasan shi da mommy ne.."
Tana tsaye a dakin tana datasanin abinda tayi ya shigo dakin yana cire yar saman rigarsa ya ajiye akan gado ta karasa zata tayashi cire sauran ya dakatar daita yana zabga mata harara taja ta tsaya tana kallonsa ta madubi gabanta na cigaba da faduwa ",sannu tantiriya Kinga ma ci min mutunci ke da wancan yar rainin hankalin yanzu shine ?an iskanci zaki wani nuna ke mutuniyar arziki ce yayi maganar yana ajiye rigar akan wanda ya cire ya ?alle agogon diamon din dake daure a tsintsiyar hannunsa ya ajiye "bai kamata kaji ciwo ba , babu inda maganata ta shafi ta safy data biyayyar aurena da kai ,magana ka fada na baka amsa daidai da maganarka meye abun daukar zafi? "shiyasa fa idan baki yasan abinda zai fada bai san abinda za'a maida masa ba idan baka son ina fada maka babu dadi akan komai kaima ka canza dan Allah ma daya haliccemu muna saba masa kuma mu dawo mu rokeshi ya yafemana bare mu yan adam yakamata ka canza ka manta abinda ya faru mu rungumi rayuwarmu idan kuma rayuwar daka zaba mana kenan shikenan sai mu cigaba tunda ta soma magana bai kulata ba haka bai dago ya kalli inda take ba zai shiga bayi tace "ranka shi dade akawo coffe ko akwai abinda kake .. ....?"
Bai tsaya jin abinda zata fada ba ya shige bayi ya rufo kofar da karfi ya shiga bathtube ya tsaya tare da kuna showel a hankali ruwa ke tsiyaya ajikinsa a hankali komai ke dawo masa tun daga maganar safy har zuwa wanda Kisna ta furta masa tsaki yaja yana furzar da iska safy tana yiwa rayuwar gidansa shishigi kafin ya dauki mataki zai fara fadawa mijinta daya ja mata kunneta sannan ya dakatar daita daga zuwa gidansa har ya kammala zuciyarsa na masa zafi da tuttukin bakincikin "ko ina ruwan ta da rayuwar gidansa "?
Ya fito kungunsa daure da towel fari hannunsa rike da wani ,ga gabobin kirjinsa da damtsen hannunsa sun bude kana ganinsa kaga dan kallo dan alamun motsa jiki ya bayyana ajikinsa saurin ?auke idanunta tayi dan kallonsa na haifar mata da damuwa muryar a sanyaye tace "me zaki ci "?yayi mata banza ya wuce ta ya karasa ya bude wardrobe kayan shan iska ya dauka gucci farare tass wando da riga ya saka rigar ta kama jikinsa sosai dam ana iya hango murdewar jikinsa da yadda karfin jikinsa yayi tasiri sumar kanshi sai kyalli take ya sanya fillifas fari da facing cap fari ya dawo gaban madubi yana kallon jikinsa yana fesa turare ya ajiye kwalban turaren ya dauki system dinsa zai fita ta sake sanyawa jikinta jarumta tace "inda ka dawo mai zaka ci ?" dan ina son na dafa maka abinda zaka ...... .."katseta yayi ta hanyar ce mata "enough kisna kinsan bana son damuwa da yawan naci ko ? " dole sai na fadi abinda zanci "? Ke baki san abinda ya dace ba saboda hauka ne acikin tunaninki kike tambayata ya karasa maganar yana k nufar kofar dakin . "
"Allah ya huci zuciyarka
ta hanzarta bude masa kofar fuskarta babu alamun damuwa tayi masa rakiya tana tsaye har sai da taga tashin motarsa sannan ta dawo zuciyarta cike da tunanin , sosai take jinsa ajinin jikinta bazata iya rabuwa da shi ba sai dai ta daina daukar duk wani iskanshi yana mata zatayi masa zata bashi mamaki dan bazata saba alkawarin da tayiwa kanta ba sai ya dawo ya rusuna mata kafin wata biyar dinsu ya cika ..."
Bayan muradi ya bar gidan gidan nasir ya nufa bai shiga cikin gidan ba ya tura mai gadi tare da mai gadi nasir ya dawo nasir na sanye da kananan kaya wando tree quater sai shirt yaja ya tsaya yana binsa da mugun kallo cikin tsananin zafin rai "muradi lafiya ka tsaya daga waje kamar wani bako?a fusace muradi ya katseshi nazo in sanar da kai kajawa matarka kunne ta daina yiwa rayuwar gidana shishigi idan ba haka sanadin ta'adancinta zai haddasa gagarumar matsala a tsakaninmu "haba muradi me yasa zaka fadi haka bayan ba ita bace silar haduwarmu tare fa matanmu suka bude ido suka ganmu bai dace ka fadi haka ba na maka alkawarin zan dauki mataki akanta da kyar nasir ya shawo kanshi sai dai yaki shiga gidan daga nan yayi masa sallama ya wuce inda zashi
A daren kasa runtsawa yayi duk yadda zuciyarsa ke bukatar natsuwa, gashi yanayin garin yayi sanyi zai yi dadin bacci amman ya kasa samu ajiyar zuciya ya dinga saukewa wanda duk Kisna tana iya juyowa , abubuwa zuciyarsa ke tunawa zuciyarsa ta jagule kamar ya daura hannu aka yasa ihu ko zai ji sau?in zafin da take masa gani zai juyo inda take tayi saurin kawar da idanunta tare da runtsewa sai da yayi mata duban tsanake ya tabbatar da bacci take sannan ya mike ya karasa inda yake ajiyar abubuwansa masu mahimmanci ciki har da sirrin daya shafi rayuwarsa tun daga kan mahaifiyarsa har zuwa rayuwarsa da Kisna bude karamin akwatin zinarin yayi wanda agurin gasar kwallon duniya yaci ya cire wani kyakkyawan diary mai tsananin kyau ya mike ya fito daga dakin ya nufi parlou'n sama ya zauna idanunshi na kan diary yadda yake kallon diary haka komai ke dawo masa a hankali kamar yanzu abun ya faru ya bude ya soma bin komai daki daki har yazo inda mahaifiyarsa ta hadu da mahaifinsa mutumin da yake jin tsanarsa fiyye da kowa a duniya, bayan shi sai Kisna da afra wadan nan mutanen bazai taba manta su a rayuwarsa ba domin kuwa sune mutanen da suka hujijiga rayuwarsa ..."
BENUE
daga garin jos benue haroon mahaifin Aliyu ya nufa ya cigaba da fantamawa yadda ransa ke so ga mata ga kudin holewa da yake samu daga gurin yammatansa dan ta kai ta kawo baya kula ya'yan talakawa sai ya'yan masu kudi ,yayan talaka sai dai su kalleshi su kyasa amman babu fuskar da zasu kusanci inda yake ba dan suna jin tsoro ko bazai saurarensu ba kawai kwarjinin yake musu cikin haka ya hadu da wata yarinya mai suna Benedicter gebrel asalinta yar kauyen gishiri ce amman suna zaune acikin benue ,
benedicter dai diyar mai kudi ce sosai a garin Benue wacce ta kammala da karatunta na gaba da secondary a kasar enugu tana aiki ne a karkashin pot-ortority ne a garin benue, tana samu kudi sosai ,mahaifinta ya jima da rasuwa dan a lokacin yana nema shekara goma ,ba wani girma tayi ba amman a lokacin mahaifiyarta ta damu tayi aure dan lokacin shekarunta bazasu fi 25 ba kullum sai mahaifiyarta tayi mata mitar ta fidda miji sai tace mata ita bata samu wanda take so ba ,a lokacin akwai wani dan kawar momynta dake maseefar sonta dan kusan gaban kowa yake nuna yana sonta tun daga lokacin dataji yana sonta ta dauki tsanar duniya ta daura masa ga wasu bad habit d'insa data tsana shaye shaye ga bala'in son mata duk macen daya ganin sai ya kyasa wata rana mahaifiyarta ta sameta akan nanyak domin son sanin ko tana da ra'ayinsa bata mata mutsu ba ila kalma daya data fahimtar da mahaifiyarta bata son nanyak ya nemi matarsa a gaba itama zata kawo nata miji kwatsam ta ha?u da haroon
sanadiyyar saurayin kawarta , kallo ?aya tayi masa taji ya shiga ranta har taji zata iya aurensa a lokacin da bai wuce shekara 30 a duniya ba, tashin farko ta nuna masa tana son shi kuma da aure sai dai ya nuna mata shi bashi da ra'ayin yin soyayya ko aure a halin da yake ciki
a lokaci kawarta Elizabeth tace " dicter Karki wahalar da kanki wannan guy din bashi da lokaci soyayya bare lokacin wani aure , gashi baya zama guri daya kamar mai aljanu haka yake bashi nan gari bashi wancan gari gashi duk abinda kika tsana daga nanyak yana aikatawa yana shan sigari kamar hauka kuma yana mu'amula da mata dabam dabam nasan kyawunsa ne ya rud'eki ko "? dicter ta girgiza mata kai alamun ba haka bane "ba kyawunsa bane ele har ga Allah ina son shi kuma zan iya muslinta saboda shi matukar zai aureni halinsa kuma zan sauya shi "da digiri dinki da kyawunki dicter zaki tsaya 'batawa kanki lokaci akan wannan "?" jobles ne fa bashi da aikin yi sai zaman banza da shaye shaye "koma dai menene ele ina son shi haka kika sani ko ta dalilina ya samu natsuwar zuciya ya zauna guri daya har ma ya daina abinda yake gyada kai kawai Elizabeth tayi tare yi mata addu'ar fatan samun nasara tunda taga ta zurma .
a hankali dicter ta dinga shigewa haroon tana fahimtar dashi yadda take jinsa a zuciyarta dariya maganarta ta bashi tare da mata wani irin kallon kasan ido wanda ya zame masa jiki dan ya sha jin ire iren wannan banzar kalmar daga bakin yammata dayawa wanda shi sam bai d'aukesu da wani tasiri ba, dan gani yake har lokacin ba'a haifi matar da zai aura ba,duk yawon garuruwan da yayi bai samu macen da tayi masa ba bama zai kirga mata nawa suke binsa da sunan soyayya ko aure ba ,har tambayar kanshi yake yaushe ma zai samu wacce zata sace zuciyarsa kamar yadda yake sace zuciyar yammata ? face to face ya fitowa dicter ya nuna mata bai sonta .
taji zafin ciwon furta mata haka a ranta sai dai ta danne taki hakura da shi ta cigaba da binsa dan su shaku a hankali har shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu tana zuwa inda yake shima idan ya bushi iska yana kai mata ziyara ganin yadda haroon ke kawo mata ziyara yasa mahaifiyarta ta soma mata mitar akan lallai tace wa mai zuwa gurinta ya fito suyi aure, ta cewa mahaifiyata ta bata lokaci zata masa magana wanda ita tasan har ga Allah ko tayi masa maganar kamar dagulawa kanta lisafi zatayi dan ba aurenta zai yi ba tunda ya sha fa?a mata baya shaawar yin soyayya dan baya son ayi breaking heart d'insa ko aure zai yi sai dai yayi kawai ba dan yana son matar ba ,ganin kyawunta da tarin ilimin bai dauke hankinsa ba yasa ta shiga kashe masa kudi kullum cikin siya masa kaya take tace zata maida shi karatu saboda lura datayi yana da tsananin ilimi sai dai bashi da kwalin da zai samu nagartaccen aiki shirme ya dauki maganarta tare da sharewa , a tsarinsa wata biyar zai yi a benue sai gashi ya kusan lasar shekara ,
sosai suka shaku da juna a cikin irin shakuwar da sukayi ne dicter ta bashi labarinta ta karashe da tambayarsa nashi labarin da garinsa ganin yadda ta ajiye batun soyayya gefe take bashi kulawa da kashe masa kudi duk kayan data gani muddin zai yi masa kyau sai ta siya masa haka albashi ta idan ta amso shi take mikawa ,shi yasa ya sakankace daita ya fada mata shi dan wani gari ne da yadda ake zuwa garin ilo ."
Haroon bai iya neman kudi ba amman ya iya kashewa dan baya d'agawa kudi kafa duk yawansu suna shigowa yana cinyesu kamar wani dan caca a haka dai shakuwarsu ta juye zuwa sha'awa agurin haroon dan har suna romancing sosai lokacin daya nemi ya kusanceta bata hanashi kanta ba dan ganinta kamar wata dama ce ta samu tunda dicter ta d'an d'ana haroon ta sake rikicewa akansa ta makale masa taji duk duniya babu abinda ya isa ya rabata dashi ....."
Aiko shigar farko sai ciki bata fahimci ciki gareta ba haka suka cigaba da muamula har abin ya zame musu jiki kullum suka ha?u sai sun kusanci juna sai biyu sau uku sai da tayi wata uku dauke da cikinsa ta fahimta cike da murna tazo masa da labarin ciki yayi mata wani banzar kallo tare da cewa "a she wawiya ce ke ban sani ba"?" me zanyi da wani ciki yanzu da zaki wani kwaso
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 21