kyakkywar fuskar da kike takama dashi ya karasa maganar yana kwafa da kyar ta samu ta sauke ajiyar zuciya da karfi ta rike wuyanta da har lokacin take jin rad'ad'i wani sanyi taji yana tsiyoyawa daga hancinta ta kai hannu ta tabo tana dubawa jini ta gani "ka?an kika gani muddin bazaki fita daga rayuwata kiyi rayuwarki ba irin wannan izayar sune hukuncinki ,kiyi rayuwarki nayi rayuwata shine zaman lafiyarki a cikin gidan sabanin haka kuma kinsani ". yana gama magana yayi parlou'n kasa ya kwanta yayi pillow da hannunwansa duka ya daura ?afarsa daya akan daya yana girgizawa baya jin zai iya fita zuwa ko'ina saboda zazza?i da yake ji itama kwanciya tayi akan gado wasu zafafan hawaye na bin kuncinta "na *cutar da kaina* me yasa nayi masa abinda nayi ?"Me yasa banji maganar Samir ba a lokacin da yake nuna min illar abinda nake ? me yasa baji maganar aunty Aysha ba "? yar'uwata ta fada min gaskiya tayi min nasiha ta fada min wata rana zanyi dana sani gashi ina yi ..."
" mai yasa na biyewa aunty Afra gashi ta Kai ni ta baro ta barni Ina girban abinda na shukawa zuciyarsa ni ?aya , kuka take sosai har da shesheka ta mike zaune tana tunanin abinda zai ci "ko kinyi masa tayin abinci bai zama lallai yaci ba zuciyarta ta fa?a mata haka "amman ai bashi da lafiya ? ta yiwa zuciyarta tambaya "ki rabu dashi har zuwa sanda zai huce umarnin zuciyarta tabi ta koma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya tana tunanin kalmamin daya fa?a a sakwanin da suka gaba "babu soyayyar kowa a cikin zuciyarsa kenan itama nawal din ba sonta yake ba ? ba sonta yake ba zai aureta yana duk sonta "ina ma zai zamo da gaske babu soyayyar kowa a zuciyarsa kamar yadda ya fada haka ta dai dinga saka da warwara a hankali har bacci ya ?auketa ."
sai kusan karfe ?aya na rana ta farka ,taji fuskarta tayi mata nauyi ta zuro kafafunta ta sauko ta tsaya gaban mirrow gabanta ya fadi ganin bakinta da hancinta sun kumbura har ma da idanunta girgiza kai tayi ta shige bayi tayi wanka ta d'auro alwala ta fito ta sauya kaya zuwa doguwar riga pinky colour tayi sallah ta sauko kasa dan shiga Kitchen mamaki ganinsa kwance tayi hannunsa daya da abun qarin ruwa yayinda likita ke gabansa yana ?o?arin bashi kulawa daga gefe guda kuma nasir ne zaune yana kallonsa sam hankalinta bai kai ga nasir ba har ta karasa saukowa idanunta na kanshi kunnensa manne da waya daga jin yadda yake wayan tasan da Samir ne ,da sauri ta karasa zuwa inda yake kwance jikinta na rawa "sannu a she zazza?i yayi karfi haka ?" sannu Allah ya baka lafiya ina ke maka ciwo ? "Ya tsani jin sautin muryarta duniya da lahira " kai hannunta daidai saitin wuyansa tai ,ta shafa zafi taji ya ratsa tafin hannunta shi kuwa saurin runtse idanunshi yayi yana jan tsaki sai dai ya kasa dakatar daita saboda ya badamasi daya amshi wayar a hannun Samir , kanshi ta d'aga ta d'aura a saman cinyarta tana shafa sumar kanshi "doctor meke damunsa plz "?"Fever ne amman nan da zuwa wani lokaci zai ji sauki tunda anyi masa allura ta cigaba da shafa sumar kanshi tana sauke numfashi"sannu Allah ya baka lafiya gaba-daya duk ta rud'e shi kuwa wani tuttukin bakincikin ne ya tokare masa kahon zuciya, yana gama wayar yace " ke maza ki tashi ki bar nan.." yayi maganar a dan zafafe , babu mutsu ta d'aga kansa ta maida kan pillow ta Mike tsaye sai lokacin taga nasir dake zaune , jiki a sanyaye ta gaishesa ya amsa mata cikin sakin fuska "ya gida kisna ? "Lafiya ta furta masa a hankali tana tambayarsa safiyya yace" tana gida zuwa anjima zata zo, ta gyada masa kai sannan ta nufi hanyar Kitchen har ta kusan shiga likita yace "madam akawo masa abinci ya ci ya sha magani .."
"No likita ba sai naci komai ba ka bari na sha maganin kawai "ba zai yiwu ba ,idan ma bazaka ci ci abinci ba kasha ko ruwan zafi ne , ki kawo masa tea "okay ta fa?a tana karasa shigewa kitchen ,bayan kamar second biyar ta fito hannunta rike da cup ta karaso gabansa ta durkusa wanda zuwa lokacin ya mike zaune "ga tea "ki ajiye a kaina mana " ya fada a zafafe yana nuna kansa "ban ta?a ganin sakariyar dakikiyar mace irinki ba komai baki iya ba ". ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ajiye cup din akan table din dake gabansa ta sake juyawa ta koma kitchen zuciyarta na wani irin zafi .."
A tsanake ta fara ha?a priderice tana cikin aikin safiyya ta shigo bayan ta gaishe da Aliyu tare da yi masa ya jiki ta shiga Kitchen saboda jin motsin kisna da tai "har kin karaso? Kisna tayi magana tana kawar da fuskarta gefe dan bata son safiyya ta fahimci wani abu amman sai data fahimta ,ta dawo gabanta ta tsaya tana kare mata kallo fuskarta dauke da tambaya sake kawar da fuska kisna tayi tana juyawa gurin wanke wanke Safiyya ta biyota tare da juyo daita suka fuskanci juna "me ya samu fuskarki haka naga ta kumbura ?"
"babu komai ta bata amsa atakaice" babu komai fa kikace ko dai uncle Aliyu ne ya 'bata miki fuska haka "? tayi saurin girgiza mata kai "ko daya faduwa dai nayi a bayi d'azu da safe ta bar gurin ta karasa jiki frizer ta bu?e ta dauko naman kaza tana juyowa taga safiyya a gabanta tana kallonta idanunta sun cicciko da ruwan hawaye kafin kace me har sun fara zubowa "meye abun kuka babu komai fa faduwa nayi "babu wani faduwa da kikayi wallahi kina dai boye min ne kawai, amman dagani fuskarki mari ne" ta karasa maganar cikin rawar murya , "tam shikenan kije parloun ki jirani ina zuwa ta fa?a tare da ra'bawa ta gefenta ta wuce duk yadda safiyya take son su tautauna akan lamarin zamanta da aliyu kisna taki, aikinta kawai take tana dauko mata wani zance dabam , daman kuma ita ba mai yawon magana bace ."
A parlour ma magana nasir yake wa Aliyu "kayi hakuri Aliyu hakuri ake da mata haka kowa yake fama dan Allah ka manta komai sannan ka daina dukanta, da iyayenta sunsan irin wannan zaman zakayi daita da basu sake baka ita a karo na biyu ba , ka saka wa zuciyarka damuwa, kullum kana cikin damuwa da zubar da hawaye nasan kana son kisna duk da baka ta?a furta min hakan ba amman wallahi ko rantsuwa nayi bazan yi karfafa ba kana sonta kuma so mai tsanani laifinta ne ya hana soyayyar tasiri ".
"zaka yi kaffara kuwa abdul-nasir saboda ban taba sonta a cikin zuciyata ba ,muyi zama ne ba irin zaman da zamu so juna daita ba, nasir ya karaso inda Aliyu yake zaune ya dafa kafad'ansa "naji amman kayi hakuri dan Allah taci darajan iyayenta ka saukaka mata ba dole sai ka sota ba amman ka daina wulakantata kana dukanta akan abinda bai kai ya kawo ba ,kalli yadda ka mayar mata da kyakkyawar fuskarta akan ta rike hannuka kawai ....."
Aliyu ya ja tsaki ka?an yace "gaskiya nasir ka cika min ido dayawa ,nasir yayi dariya mai nuna cin nasara akansa yace "na gode duk abinda zatayi ka barta dan Allah ka daina dukanta kisna da safiyya suka karaso parlour'n hannunsu rike da manya manyan kuloli suka ajiye akan dining tare da plet kisna ta karaso gaban Aliyu ta na cewa "ranka shi dade abinci yayi ready nasir yayi dariya yace "an gaishe da uwar gidan Aliyu sannu da ?o?arin zubo masa kawai ki kawo masa nan "murmushin jin dadi tayi taje ta zubo masa ta dawo ta ajiye a saman table din gabansa taje ta dauko masa lemunsa na gado da ruwa ta dawo nasir ya mike ya koma mazauninsa "sannu yaya kake jin jikin naka yanzu"? Yayi mata banza tamkar ba dashi take magana ba , ta dauki plet din abinci ta dibo had'ad'd'en priderice ta kai bakinsa "kallon cikin kwayar idanunta yayi yana jin zallar ?acin rai "ka bude baki kaji , kaga baka da lafiya rashin cin abinci yana bari ciwo ya samu matsuguni ajikin mutun".tayi maganar tana lumshe masa idanuwanta , fuskarta data dan kumbura yake kallo ta dan bashi tausayi kadan "ka bude baki " ta sake maimaitawa "jikinsa a sanyaye ya bu?e ba dan yaso ba ta soma bashi abinci abaki spoon uku yayi ya kawar da kanshi, ta ajiye plet ta tsiyaya masa lemun ta kai bakinsa ya bu?e ya sha ta jiye cup din, kallonsa tayi taga gumi ya ?an tsatsafo masa a fuska tasan gumin abinci mai zafin daya ci ne, tasa gefen rigarta ta soma goge masa "ba muna da towel ba "? Yayi maganar muryarsa can kasa kamar baya son magana , ta gyada masa kai sannan ta mike cikin sauri ta hau sama."
bayanta safiyya tabi da kallo dan gabad'aya dawowa tayi kamar wata wawiya ta kasa zubawa mijinta abinci tana kallon kisna dake rawar jiki akan mutumin da bai san darajanta ba ,ko cikakken minti biyu batai ba ta dauko towel ta dawo ta zauna kusa dashi zata goge masa ya amsa "zanyi da kai numfashi ta sauke ta cigaba da kallonsa ,yadda safiyya ke Kallonsu haka nasir ke Kallonsu kisna ta bala'in burgeshi kuma yaji dadin yadda ta sauya ta rusunar da kanta ta zubar da makan yakinta domin kyautatawa mijinta sai gurin yamma su nasir suka bar gidan ."
A cikin mota safiyya ta waigo inda nasir yake zaune yana tuki "sweet heart Wai me ka fahimta yau ne a gidan aliyu "? "Kamar me kenan ?shima ya tambayeta yana sake maida hankalinsa ga tukin da yake "kamar duka yayiwa yarinyar mutune fa , wallahi ban ta?a tunanin haka daga Aliyu ,ban san haka halin aliyu yake ba ,mutumin da nake ganin ya fika kyawawan halaiya ,mutumin da nake ganin babu kamarsa a fadin duniyar nan ,mutumin da nake kismawa a raina duk matar data sameshi a matsayin miji tayi sa'a duniya da lahira, mutumin da nayiwa kanwata kwadayin aurensa saboda kyawawan halaiyensa yau shine yake musgunawa matar aurensa kuma uwar ya'yansa why nasir "?
"Duk abinda kika lissafa akan Aliyu gaskiya ne domin kuwa Aliyu mutumin arziki ne mutumin Karki ne ,muyi karatu dashi a kasar nan tunda muka zauna bamu ta?a samun matsala dashi ba, mutun ne na gari bai ta?a aikata laifin komai ba ,mutun ne shiru shiru wanda yasan darajan dan adam da duk wani hukunci da'aka tanada domin mu'amula ."
"ita kuma kisna da kike ganinta yar ta'adda ce kamar yadda duk wani dake cikin danginsu ya san da haka ,duk wannan tashin hankalin da take fuskanta ita tajawa kanta da taimakon Afra ,wannan halin da yake nuna mata tayi masa fiyye dashi , wallahi idan na fa?a miki abinda tayi masa har duniya ta nade bazaki sake ganin kima da girmanta ba yanzu ma wannan ladab din da kikaga tayi na wuya ne , saboda taga babu wanda zai iya rufawa rayuwarta asiri sai shi .....
" dan haka ki daina magangun bazan akan abinda baki sani ba ,naki kiyi kokarin kwantar mata da hankali tunda yanzu tayi nadama ki nuna mata ta cigaba da hakuri wata rana zai dawo mata yadda take so . numfashi Safiyya ta sauke tace "kenan shiyasa bata son ana fadar laifinsa saboda tasan itace bata da gaskiya? "eh ya bata amsa a takaice dan duk ya gaji da tammayoyinta "shikenan zan tayata da addu'a Allah ya daidaita tsakaninsu "ameen addu'a mai kyau kenan ."
Mmn Sudais
????????????
CUTAR DA KAI
????????
????????????
Free Page 6
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalmi, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga bukatar siyan ?aya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...????
"Tunda nasir da matarsa suka bar gidan ta bashi magani ya sha ta kwantar da kanshi akan cinyarta ta d'aura hannunta ?aya a qirjinshi tana shafawa a hankali zuwa fuskarsa tana yi masa sannu tana jin kamar ta cire masa ciwon ta dawo dashi kanta , idanunshi ya runtse gam yana sauke numfashi sama sama batare daya amsa mata ba "
"wani iri ya dinga ji a gaba-daya sansar jikinsa a lokacin daya tsinci laulausan tafin hannunta a saman qirjinshi tana shafawa ga kamshin turaren jikinta dake gauraye dana parlou'n duk sun buwayi hancinsa , itama hakan ce ta kasance gareta kamshinsa ya buwayi hancinta ji take tamkar su kasance haka har abada , sake runtse idanunsa yayi sosai har bacci mai nauyi yayi nasarar d'aukarsa a cikin mintunan da ba su wuce goma ba, ya d'aura laulausan hannunsa a saman nata yana sauke numfashi a hankali .
kyawawan idanunta ta zuba masa tana kare masa kallo tsab wani irin yanayin ta dinga ji a jikinta, da kyar take janyo numfashi tana fesarwa , dayan hannunta ta kai gefen wuyansa ta shafa har lokacin jikinsa da sauran hucin zafi ,kanta ta rankwafo ka?an daidai fuskarshi tayi shiru tana sha?ar numfashinsa ,abinda ta tsani shakarsa ada shine yanzu ya zama muradin ranta , ko iya sha?ar numfashinsa ka?ai ya bata dama ya isheta k'arasa sauran rayuwarta da tai saura a duniya .
" a hankali take addu'ar akan Allah ya sausauto mata da zuciyarsa tare da fatan samun soyayyarsa koda bai kai wanda take masa ba , kusan minti talatin tana zaune tana kallonsa yana sharar bacci da alamun kamar akwai maganin bacci acikin magungunan daya sha dan ko daga hannunsa bai iya wa , sosai suke musaya numfashi juna batare daya sani ba , mutuwar da jikinta yayi ne yasa ta sake kusanta kanta dashi har lip's dinsu na had'uwa da juna ,
tsawon lokaci ta ?auka tana zaune tana kallonsa tana sha?ar
numfashinsa tana jin kamar ta kamo lip's d'insa ta tsotsa ko ka?an ne ,dan tana kwadayin sake jinsu cikin bakinta sai dai tsoro da tsananin fargaban abinda zai faru idan ya bude idanunshi ya kamata ya hanata aiwatarwa."
da kyar ta daidaita natsuwarta cikin sanyi jiki ta zare jikinta ta d'aura kanshi akan pillow ta hau sama ta d'auko bargo mai taushi ta lullu'beshi sannan ta koma d'aki ta shiga bayi ta tsalla wanka ha?e da alwala ta fito ta goge jikinta ta bu?e wordrobe ta ?auki wasu kayan ta canza tayi sallah ta sake gyara ko'ina a d'akinta ta d'auko turaren da take amfani dashi ajikinta ta feshe ko'ina , duk inda tasan yana kwanciya a cikin dakin sai data fesa turarenta har cikin bayi, ko'ina ya ?auki kamshi turare sannan ta ajiye kwalban turaren ta sake dawowa parloun."
A gabansa ta tsaya tana kallon yadda yake sauke numfashi yayinda a hankali zuciyarta ke bugawa tamkar zata fasa qirjinta ta fito waje ta ?auke idanunta akanshi sakamakon wayarsa dake ringin cikin sanyi jikin nan nata ta kai hannu ta ?auki wayar tana dubawa sunan Samir ta gani yana yawo akan screen ?in wayar da sauri ta d'auka "hello ya samir barka da warhaka" ?
"Yes my lovely sweet sister ya kike ya mai jiki fatan ya samu sauki"?
"Alhamdulillah ya samu sauki gashi nan yana bacci ,"jikin dai nashi da sauki sosai ko"? "da sauki yaya mummy ta amshi wayar "kisna ya jikin d'ana "? kisna ta kwa'be fuska kamar zatai kuka "mummy ai ni fushi nake dake tunda na sauka a kasar nan baki kira kin nemi ba kullum sai dai kiyi waya da muradi "kinga sarkin shagwa'ba ajiye batun fushi nan muyi maganar jikin d'ana , ya jikin dana ? "ya ji sauki doctor yazo ya dubasa Kuma yace da zarar ya tashi a bacci zai sake samun sauki yanzu haka bacci yake" "okay naji dadi sosai dan nasan wannan mayatattacen ciwon kan nashi zai iya kai shi ga kwanciya asibiti Allah dai ya bashi lafiya ,ya dai zaman naku fatan dai babu wata matsala babu damuwa "?"Yes my sweet mummy babu damuwar komai , muna zaune lafiya dashi ,d'anki yana matukar bani kulawar data dace , baya son ganin ?acin raina ,duk abinda nake so shi yake min ina jin dadin zama dashi sosai ,ko'ina zashi idan ba gurin aiki ba tare muke zuwa ,tare muke zuwa tsiyaya , babu abinda zance miki mummy sai godiya Allah ya qara nisan kwana na gode bisa ?o?arinki gareni, hakika samun uwa irinki a waannan duniyar tamu da kamar wuya ta karasa maganar tana sauke numfashi da ajiyar zuciya a tare ".
dariya mumuy tayi tace "iye lallai kin zama yar gatan haka muradi yake ji dake ni ina can cikin damuwar yanayin zamanku , duk da nasan zaki samu kulawa fiyye da haka daga garesa," muradi yaron kirki ne ya fita dabam acikin mutane. " "a saninki da tunaninki ba amman wannan dan naki mugu a duniya babu kamarsa tayi maganar a kasan zuciyarta tana jan numfashi da kyar .
"hello kisna kina jina "?
Numfashi ta sauke da karfi tace "ina jinki mummy , maganarki haka ne samun mai kyawun hali irin nasa da wuya ta fada tana dariya.
"ki zauna lafiya da mijinki kiyi masa biyayya kiyi masa duk abinda kika san zai faranta masa, yanzu muna wani zamani ne da ake lalla'ba maza bare miji irin naki mai tsananin tsada da samun irinsa da wahala, shiyasa kikaga bana son ki bar karkashinsa, dan Allah ki zauna lafiya da mijinki , ki rike shi amana sannan ki rike sirrin gidanki nasan kina da zurfin ciki ki ?ara akan wanda nasanki dashi muma inshallahu zuwa karshen wata ko sabon wata zamu shigo Cairo".
wata irin qara ta saki na farinciki tare da furta "dan Allah mummy nah ?"inshallahu kuwa "kai amman mummy naji dadin wannan maganar sosai kamar ance ta d'ago idanunta inda yake kwance taga idanunshi fesa akanta ya bala'in ha?e rai tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa tunda ta soma wayar ya bude mayatattun idanunshi akanta rungume da hannyensa a qirji yana kallonta, duk maganarta babu wanda bai yi nasarar shiga kunne shi ba ,haka nan ya tsinci kanshi da jin dadin abinda ta fad'awa mummy ko babu komai ta rufe wani sirri dake tsakaninsu "lallai kisna ta canza irin canzawar da'ake so, ina ma zai iya daya bata wani gurbi a cikin zuciyarsa kamar yadda ta bukuta sai dai ba zai iya ba dan shi yanzu burinsa bai wuce ya auri nawal ba saboda zamansa haka without having sex ya soma damunsa , kuma nawal itace matar data fi dacewa da rayuwarsa duk da bai tsananin sonta amman haka zai aureta ".
Idanunshi dake tsaye kyam akanta yasa gaba-daya ta rud'e , ta gigice a matukar tsorace tayiwa mummy sallama ta katse kiran ta mike tsaye jikinta na rawa ta k'arasa inda yake kwance ta ajiye wayar a inda ta ?auka taja ta tsaya gabanta na faduwa da matsanancin karfi "ka....kayi hakuri dan Allah mummy ce ta kira kana bacci shine na ?auka tana gaisheka " ta karasa maganar a matukar tsorace ."
?auke kanshi yayi batare da ya ce komai ba yana ?o?arin mikewa tsaye , tayi saurin rikoshi ta karasa mikar dashi tsaye ta sanya hannuta daya a kugunsa sannan ta zagaye hannunta ?aya a wuyansa wani irin shock suka ji a tare , a hankali
suka fara takawa suka nufi hanyar sama akan step taji ya dafa kafad'anta sosai ?an ya samu damar takawa ta tsaya cak tare da waigowa a tsorace suka ha?a ido fuskarsa babu walwala ya d'age mata girarsa ?aya alamun tambayar kallon mai take masa ? kawar da idannunta tayi da sauri ,yayinda shi kuma ya daga ?afarsa ?aya da kyar wani sanyin dadi taji yana ratsata kamar wata wawiya ta dinga daga kafafunta har suka shiga daki , kai tsaye bayi ta nufa dashi saboda tasan bai yi Sallar magrib ba ga isha'i ta karato ta taimaka masa yayi alwala suka fito ta kaishi gurin sallah "ka zauna kayi sallah a zaune saboda jikinki babu kwari".
banza yayi mata ya tsaya bisa kafafunsa ya soma tada ikama ita kuma ta koma falon kasa ta gyara ko'ina ta shiga Kitchen ta wanke plet din da suka yi amfani dashi ,ta goge ko'ina dan tasan halinsa da rashin son kazanta sannan ta dawo parlou'n ta tattara kan magungunsa ta dawo sama wanda zuwa lokacin har sallar isha'i yayi yana ?o?arin tashi ta shigo d'akin ta karaso da sauri ta taimaka masa ta kwantar dashi akan gado tana yi masa sannu "sallar isha'i tayi ta dawo gefen gadon ta zauna tana sake jin tausayin kanta dan batasan ranar da zata fita daga cikin wannan kangin damuwar ba, ganin sai faman mika yake yana juyi alamun jikinsa yayi masa tsami , ya juya a hankali ya kife yayi ruf da ciki ,hakan yasa ta hau gadon sosai, hannunta na tsananin rawa ta kai bayansa ta fara shafawa a hankali jin bai yi magana ba , yasa ta canza salo zuwa massaging a natse ta dinga mammatsa masa sansar jiki tun daga bayan wuyansa da tsakiyar bayan kanshi har zuwa kasa gurin gwiwowinsa zuwa kafafunsa da tafin ?afarsa "ya salam ya furta a kasan ransa dan sakonta yaje masa inda bai yi expecting ba , jin reaction din jikinsa ya fara sauyawa yayinda zuciyarsa ta fara bugawa da tsalle na kaiwa kololuwar sha'awa , cikin dakakkiyar muryarsa yace "stop......"
ya fada tare da sauke wani wahalallen numfashi."ka bari nayi maka massagin zaka ji dadin jikinka ya juyo a zuciye cikin rashin sani gaba-daya ya zubo jikinta sai gashi a saman ruwan cikinta ita kuma tana kasan shi hannunta duka a saman qirjinsa daidai kan nipple's d'insa , ya tsura mata idanunshi tare da ha?e rai , a tsorace ta cire hannuwanta ajikinsa ta zuba masa ido tana kallonsa , ya lumshe idanunsa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa kusan minti goma suna kallon juna tare da sha?ar numfashin juna batare da yayi magana ba, ya
kai hannu ya ?auki pillow yayi cilli dashi kasa ya lalubo bargo ya jefar sannan ya gyara kwanciyarsa ya lullube jikinsa tun tana ganin motsinsa har bacci yayi awon gaba dashi ta lalla'ba ta d'auko bargo da pillow ta kwanta a dayan gefen , ta lullu'be jikinta ta runtse idanunta itama bata ?auki dogon lokaci ba bacci ya ?auketa ..
Washegari
A hankali ya soma bu?e idanunshi kawai ya jishi ajikinta da sauri ya k'arasa bu?e idanunshi yaji ?afarsa akan kafafunta ya kanainayeta yayinda hannunsa daya ke saman kirjinta daidai dukiyar fulaninta da sauri ya cire hannunsa da ?afarsa ya mike tare da matsawa baya ,yaji kamar ya sakar mata mari dan bakinciki ," shiyasa fa baya son su kwanta guri daya waya sani ma ko yayi wasanin da jikinta "?
"Oh my goodness yarinyar nan tana son damun rayuwata saukowa yayi ya shiga yayi alwala yazo yayi Sallah ya koma kan doguwar kujera ya kwanta bata tashi ba sai gurin tara wanda wayarsa ce ta tasheta a bacci, ya kasa tashi ya ?auki wayar har ta katse wani kiran ya shigo ta sauko ta dauki wayar ta mika masa ta shige bayi "hello my love aka fa?a daga can bangaren da kyar ya iya bude bakinsa yace "nawal ya kike "?
" Sorry na tasheka a bacci ko ya karfin jikin "?"Naji sauki ya za'a yi nazo na ganka ina son ganinka plz naga yanayin jikinka "
"Karki damu zaki gani dan nima ina son ganinki akwai abinda nake son muyi magana akai yana cikin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 21