dana turarenta ita kanta a tsaftace take tayi kyau sosai cikin doguwar riga kamar an tsinkareta ta motsa ha?e da bude idanunta taga mutun tsaye a gabanta wani irin mummunar faduwar gaba taji sai dai bata nuna masa ba tayi masa kallon sama da kasa tace "sannu da zuwa ta dauke kanta akanshi ya ajiye jakar hannusa yana cigaba da kallonta cike da takaicinta "wato ma dan samun dama taci ta koshi ta hau bacci ganin yadda yake kallonta kuma bata manta da yadda suka rabu dashi ba ta mike tsam tana kokarin bawa kafarta iska sautin muryarsa taji "tunda nake ban taba ganin wawiyar yarinya irinki ba....."
da hanzari ta tsaya tana dubansa da idanuwanta da suka kada zai sake magana ta katseshi ta hanyar daga masa hannu "enough muradi ya kamata zuwa yanzu kana sanin irin maganar da zaka dinga fada min, karka manta nifa ba yarka bace matakar ce ita kuma mata ba kowace magana zaa dinga fada mata ba, ka lura ka hankalta kuma gane kisna tafi ?arfin wannan tozarci dan haka kayi ka dawo taitayinka , idan ba haka nan kusa zaka tantance tsakanin aya da tsakuwa taja tsaki tana sakar masa harara tayi gaba abinta tana rausaya abinda yafi tsana kenan a rayuwarsa ayi masa tsaki a wuce shi ji yake kamar ya mutu ya gwamaci shi yayi da ayi masa , biyota yayi cikin zafin nama aiko ta kara sauri sai dai akan step ya cafkota ya damki naman cikinta zuciyarta ta soma sarewa da lamarinsa daga dawowarsa abin nasa yafi karfinta hawaye suka gangaro mata "wannan wace irin tsana ce haka" ?
Da kyar ta fixge jikinta tana masa harararsa da yi masa Allah ya isa ta shige dakin mumy tun kafin ta saka key ya banko dakin ya ?auketa da mari "bayan tsaki har da Allah ya isa ni sa'anki ne dukan tsiya mata ,sai da yayi mata lilis sannan ya samu guri akan kujera ya kallonta tana kuka "muddin zai fada ta fada bazai raga mata ba ya dinga gallazawa rayuwarta kenan har sai ta shiga hankalinta" zaki yiwa mutane shiru ko sai na an kawo min kyankyasai ?tana jin haka tayi shiru ta daina zubar da hawaye sai shesheka "shima sheshekan kuka bana son jinsa dan kin cika min kunne kuma na sake jin kin kirani da muradi sai zubar miki da ha?ora wawiya kawai ". tashi tayi gbdy ta shige bayi , tunda ya dawo bata sake bari sun hadu dashi ba ,shima bai fiyye zama a gida ba kullum sai ya fita acikin kwananki harkoki sun masa yawa training da office saboda zasu sake fita German buga wasa yadda ya fita tsabgarta haka itama ta sharesa babu mai shiga tsabgar wani sai ya wuce ta wuce .."
*********
da wani yammaci da misalin karfe hudu tana zaune akan doguwar kujerar hannunta rike da waya tana magana da mommy yayinda idanunta ke lumshe ,kamshi turarensa ne yasa ta bude idanunta suka sauka akan shi yana saukowa daga mattatakala sanye da gajeren wando baki da karamar riga fara irin ta yan kwallon hannusa rike da kwallo yana bugawa har ya sauko daga step ya fita zuwa wajen idanunta na kanshi , sake lumshe kyawawan idanunta tayi" Aliyu ba dai kyau ba komai kyau yake masa cigaba da waya sukayi da mommy daga karshe ta hadata dasu areef ..
Shi kuwa aliyu kai tsaye field din gidan ya nufa inda Samir ke jiransa shima sanye cikin irin kayan dake jikinsa tun kafin ya karaso zee ta hura husir tana karfafawa mijinta gwiwa "karka yarda ya cinyeka kamar sauran lokuta "Kima daina bata bakinki yarinya dan kamar na cinyesa na gama idan dai wannan mijin naki ne da bashi da momora sai aiki cin tsiya Samir yayi dariya yana tafa hannu yace " sharesa baby duk ya gama cika bakinsa daga karshe Allah ya bani Sa'a akanshi ba". Aliyu ya saki kwallo aunty zee ta sake hura husir suka fara wasa da kwallo.."
Ganin har kusan minti goma suna fafatawa a tsakaninsu kuma har lokacin babu wanda yayi nasara cinye d'an'uwansa, sai dariya take ita kadai, idan taga Aliyu zai cinye mijinta da sauri zata sa ihu kamar zatayi kuka ha?e da daura hannuwanta saman kanta ,idan kuma mijinta ke kokarin cinye Aliyu sai tayi ta bashi kwarin gwiwa tana kiran "Samir !Samir !!Samir !!!
Haka nan tayi tunanin taje ta fito da kisna itama tayi kallo koda aunty zee ta shiga parloun ta isketa zaune ta tallafe gwiwar hannuta da filo data daura a saman cinyarta ta tallafe kumatunta da tafukan hannuwanta tana tunanin mijinta da auren da zai yi "kisna stop overthinking "me ke damunki mai yasa kike wannan dogon tunanin"? "Idan kika kashe kanki da tunanin ya Aliyu babu ruwansa ya'yanki zakiyiwa hasara ".
Taja numfashi ta fesar tana sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan ta kalleta "tunanin auren ya Aliyu nake aunty bansan ya komawar rayuwata zata koma ba idan nawal ta shigo gidan nan wallahi har na fara tausayin kaina saboda ba karamin so yake wa yarinyar ba "Mai nawal ta fiki ilimi kyau ko nasaba ko kudi da zaki shiga damuwa akan shigowarta "?"Ki bani amsar tambayoyina numfashi ta sake saukewa ta tsurawa yar'uwata kuma matar yayanta uwa guda uba guda ido sannan ta girgiza mata kai "bata fini ko daya ba sai da munanan kalamansa gareni yana sani jin kamar tafi ni komai tunda ita yana sonta "
"Ciwon rashin sonki shine babbar matsala da zai kawowa rayuwarki shamaki sai dai kisani kowa ne dan adam akwai ciwo acikin rayuwarsa kawo kunnenki kiji wani abu kisna ta mika mata kunnenta murmushi ne ya subuce mata "babu abinda ban masa ba aunty har takai ta kawo ma daidai towel baya son ganina dashi hatta kwanciya guri daya baya yi dani duk abinda nasan zanyi dan na janyosa gareni nayi amman yaki ni gara kawai ayi ayi auren na cigaba da zaman biyayyar da naki yiwa iyayena a tun farko".
"Ai duk kece kika cutar da kanki kisna "uhmmm ta sauke numfashi karki tuna min abinda ya faru aunty wallahi nasani shiyasa wani lokacin idan yayi min wani abu konaji haushinsa sai na dawo na huce "Kinga share tunaninsa da tunanin aurensa taso muje muyi kallon kwallo ta kamo hannunta suka fito zuwa filin kwallo ."
Tun kafin su karaso kisna ta hango Aliyu da Samir sun hada gumi da sauri ta juya" ina kuma zaki ? inji cewar aunty zee "ruwa zan dauko musu ko cikakken minti biyar batayi ba ta dawo hannuta rike da roban ruwa guda biyu da kananan towel ta mikawa aunty zee daya sannan suka karaso gurin a daidai lokacin da Samir ke kokarin cinye Aliyu yayi saurin kwance kwallon da ?afarsa Aunty zee ta dauki husir ta hura tana murmushi "to ku huta haka dan da alamun babu wanda yaci suka tsaya suna fidda numfashi rike da kugu, aunty zeey ta karasa kusa da mijinta ta shiga goge masa fuska zuwa wuyansa ..."
Hakan yasa kisna cikin sanyi jiki ta karasa kusa da Aliyu ta kai hannu daidai kunnesa zata goge masa fuskarsa dake tsiysyar gumi ya juyo ya watsa mata idanunsa masu matukar kyau da haske take gabanta ya shiga dokawa duk ta daburce taji kamar ta saki towel din ta falla da gudu . hannu ya kai ya amshi towel din hannunta idanunshi na kanta ya soma goge fuskarsa bayan ya gama ya mika mata , ita kuma ta mika masa roban ruwa sa?anin aunty zee da a baki ta bawa ya Samir ya sha.
tun daya d'aura bakinsa akan goran ruwan bai sauke ba sai daya sha rabi sannan ya mika mata sauran suka ci-gaba da buga kwallo yayinda su kuma suka samu guri suka zauna a gefe akan fararen kujeru suna Kallonsu a hankali kisna ta tsurawa mijinta ido tana kallon yadda yake sarrafa kwallo kamar dan shi Allah ya haliccesa duk wani siffar karfi dake jikinsa ta gama bayyana burinsa kawai ya cinye Samir cikin sauki , yadda surar jikinsa take cike da karfi haka yake da mazakunta, karfi garesa kamar doki , sautin muryar aunty zee da ya karade gurin ya dawo da kisna daga duniyar tunani" Samir isa goal ta rungumeshi ajikinta tana murna "Allah yayi yau Samir ya cinye ya Aliyu ...."
Aliyu dake tsaye rike da kugunsa da hannunwansa duka yaja dogon tsaki yana kallon kisna dake dafe da goshinta tana kallonsa dan sam bata ji dadin cinyesa da Samir yayi ba shi da yake bugawa wasa kasa da kasa kuma ya cinye har yanzu da yake kan ganiyar buga kwallo babu kasar datayi nasarar cinyesa sai wannan karon da Samir ya lashe aunty zee ta sake hura husir "baby ka kara masa daya dan Allah "aliyu ya ha?e rai bazan yi ba ,a tunda kika dad'd'ako min wannan nasan bazan yi nasara ba ya juya fuuuuuu a zuciye ya soma tafiya Kisna tayi saurin d'agowa tare da dafe kirjinta idanunta suka cicciko da ruwan hawaye "ke dan Allah meye abun kuka "? "Ki barta hawayen ne suka mata yawa inji ya Samir take ta maida kukanta tana sauke numfashi tare da tsuke karamin bakinta tana shesheka sannan ta mike ,tare suka jero suka fito daga filin kwallo suna fitowa haraban gidan ya fito sanye da riga pink da gajeren wando iya gwiwar ya nufi gurin motarsa escort d'insa na ganinsa suka taso yayi saurin daga musu hannu take suka kame ya danna mukulin mota ha?e da bude murfin ya shiga mai gadi ya bude masa ya fita a guje ..
Ganin yadda ya fige motar da gudun maseefa Yasa kisna fashewa da wani kukan mai cin ranta , hankalinta yayi matukar tashi tsoro tattare da fargaba ne sukayi nasarar lullube ilahirin jikinta, abubuwan da yake mata sun fara isarta amman ta rasa yadda za'tayi dashi ita meye laifinta ita tace samir ya cinyesa ko me"? takaicin haka yasa ta durkushe bisa gwiwowinta ta kife kanta bisa cinyoyinta tana sake risgar kuka mai cin rai da suma zuciyar ma'abocin sauraro har aunty zee zata mata magana Samir ya dakatar daita "ki tashi ki shiga ciki kin dai san halin zuciyarsa ba karamin aikinsa bane ya dawo ya sameki agurin nan ya kara miki da duka , yana gama fadar haka ya ja hannun aunty zee sukayi bangarensu .."
A hankali ta mike ta shiga part d'inta tana goge hawaye kai tsaye kitchen ta shiga ranar ma bai ci abincinta ba haka bai yarda ta kusanci inda yake ba dan har gargadi yayi ma tare da rantsuwa "wallahil azim idan na farka na jiki ajikina ko kusa dani sai na miki abinda har ki mutu bazaki manta dani ba tasan shi tasan halinsa shiyasa tana kammala abubuwanta ta kama kanta ta kwanta akan kujera.."
********
Bayan wata uku
Duk wani abinda za'a bukata na kayan auren nawal Aliyu yayi ya sakarwa aunty zee kudi masu yawa domin hada kayan lefe koda ta tambayeshi na kisna cewa yayi bazai mata ba har zatace bazata ha?a masa ba sai taga rashin dacewar hakan , duk abinda ya kama tun daga kan dogayen rigunan da takalma da jakakkuna turaruka anan egypt ta siya ,ta tura kudin atamfofi da lesina da wasu abubuwan daza'a bukata negeria tunda can za'a tura kayan lefen dan amarya ma tuni tana Nigeria safy tazo ganin kayan lefe tayi mamakin bata ga na kisna ba, ba tayi kwaron baki ba ta tambaya aunty zee "ina kayan kisna na fadar kishiya .. "?shiru sukahi mata gabadaya dan rasa abinda zasu fa?a mata "tambayarku nake kun min shiru ina kayan kisna ko ita bazai mata komai ba "?Kisna dake kwance tana tunani ta yunkura ta mike zaune "bai min ba kuma ban damu ba saboda har yanzu ina da tarin kayan da ban yi amfani dashi ba "gaskiya wannan ba adalci bane ke kuma ba hujja bane dan kina da kayan da zakiyi amfani dasu ,yau ace Aliyu bashi da kudin da zai siya muku ku biyu ne sai ki ?auki hakuri amman yana da ninkisu da ko mata dari zai aura a rana daya zai iya hada musu kayan lefe, gaskiya aunty zee ban ji dadi ba ya kuna kallon yadda Aliyu ke wulakanta kisna amman ku kasa ?aukar mataki akanshi sai ma wani lalla'bashi kuke sai ya kasheta kuce zakuyi kuka " idanun kisna ya cika da hawaye , aunty zee ta sauke numfashi tana cewa "safy kenan bazaki fahimta ba, lallashinsa shine mafi alkhairi idan aka yi wani abu na ?acin rai idan dady ji zai iya janyo gagarumar matsala wannan auren iyayenmu na murna dashi fiyye da kowani aure babu yadda zamuyi duk yadda ya tsara lamarin gidansa haka zata hakura .."
"Hakuri hakuri hakuri kullum shi ke kashe mata ko saka su kamuwa da wata mummunar cuta safy ta fada cikin ?acin rai "karki manta hakuri shine jigon rayuwar duniya Allah yace kuyi hakuri lallai ni ina tare da masu hakuri ,hakurin shi karan kanshi aikin lada ne ba kuma kowa allah yake bawa baiwar hakuri ba inji cewar aunty zee.
"Haka ne Allah ya qara mana hakuri sai dai na dade dasanin kisan na cikin damuwa dan Allah ko zaki iya fa?a min abinda tahi masa har yasa yayi mata irin wannan muguwar tsanar "?
Shiru parloun ya ?auka babu wanda ya sake furta komai ",ko kuwa ban kai matsayin da zamu iya sanin sirrin juna bane "?Kisna ta kalli aunty zee fuskarta dauke da damuwa safy ta kamo hannu kisna "dan Allah ki daukeni tamkar yaruwarki ina son sani abinda kika wa aliyu da har ya rikeki a zuciyarsa ya kasa hakuri ya kasa manta komai "?"Shiru still tayi ta kasa magana hawaye na kokarin zubo mata bata jin zata iya fadawa wani tahirinta da abinda yasa Aliyu yake mata wulakanci daya ga dama ."
"Ni da zuciya daya nake zaune da mutum kuma Allah ya sakamun jin damuwarki a ciki raina , bana zama da mutum don in yaudareshi ko qin fada mishi damuwata, abu daya na dauka cewan mutunci ya hadaka da mutum tou kuyi zaman haka. Mutunci na kawo yarda da juna wani zubin tana bada amana ma, kuma amana babban amincewa da mutum kesa aba mutum , kuma baya zama me kar6an amana alhalin bashi da kamala, dattaku, girmama na gaba, girmama na qasa, gaskia da haquri da halin mutane , Ina zaune dake tsakanin da Allah ba wai dan mazajenmu na matsayin aminai ba, amma wariyar da kike ta nunamun yau ya qureni wacce ni a wajenki? Shasha? Ko kuwa sakariya wanda zaki dinga 6ata lokaci daita ? Ko kuwa banza kike kallona? Ko mara illimi? Ko mara tunani? Ko mara sanin ya kamata? Ko kuwa yarinya qarama wacce bata san komai ba? Ko wacce bata san meye rayuwa ba? Duk abin da kike nunamin yana kunshe da wannan sannan rashin daukata yadda na daukeki yasa bazaki fadamun ba saboda kila bazan fada miki kiji ba ko bazan baki shawarar da ta dace ba ko kuma zan fallasa sirrinki ga wasu saboda kina mun kallon wawiya wacce bata san me take ba.
"A yau na yarda zaman da muke bashi da anfani kuma zaman da muke bana amana bane in dai bazamu ji damuwar juna ba ,mu bawa juna sharawa ba zaman munafurci ne.
",Wallahi idan na tambayeki damuwarki kika ki fadamun bakisan zafin da nakeji ba amma sai in barki sbd kar in daga miki hankali ko takura miki, babu komai sabon sanayya game da rayuwa dama nasan irinta ,kuma bazan daina aminta da aminta dake ba , kuma bazan daina jin zafin ciwon dake damunki ba a kan Aliyu nagode sosai da yadda kika nunamun matsayina da kuma yadda kike zaune dani na rashin yarda , na hakura da son jin komai dan ko kin bude bakinki qarshe bai wuce kice "bazan gane abinda ya hadaki da mijinki ba " Nagode sosai wlh tunda ta soma magana kisna take kukan zuci dana zahiri safy ta mike tsaye ta dauki jakarta ta rataya zata wuce kisna tayi saurin riko hannunta cikin zafin nama tana kallon aunty zee hawaye na gangaro mata.."
"alamar tayi magana aunty zee tayi mata dan haka a hankali tace " kiyi hakuri ki zauna safy ba wai naki fada miki labarina ba ne dan ina tunanin wani abu ko zaki fallasawa wani illa bana son Tina abubuwan da suka faru dani sannan asalina ni mai zurfin ciki ce bana fadawa kowa damuwata idan ba mutun ne da kanshi ya fuskanci haka ba safy ta zauna tana kallonta cike da tausayawa " safy abinda ya faru dani ciwo ne dake cin zuciya ,ni kaina na kasa yafewa kaina abinda nayi bare ya Aliyu ,damuwa kuwa muddin Aliyu bai sauko daga dokin nakin daya hau ba haka zan kare rayuwata cikin damuwa da garari tunda nasan dan ra'ayin kanshi bazai sakeni ba sai dai idan iyayena ne suka bashi umarni "safy Kowane dan adam akwai ciwon da Allah ke daura masa wani gurgu wani makaho wani kurma da sauran ciwuka da dama amman ni Allah da ya tashi sai ya jarabeni da ciwon kaunar wani halittan mutun a sheakaru goma sha biyar data gabata a lokacin ina jss one ......."
Waiwaye.....
Mmn sudais
????????????
CUTAR DA KAI
????????
????????????
Page 17
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ?aya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096.
"Aunty zee , aliyu sakina wato ni iyayenmu abu daya ne ,uncle garba shine mahaifin aunty zee , sai uncle yahaya wanda ake kira da bature shima yana da ya'yansa ,sai haroon wanda ya kasance mahaifin Aliyu sai salaha wacce ta kasance mahaifiyata , dukkaninsu uwa ?aya uba ?aya suke gabad'ayasu hajiya sakina ce ta haifesu wacce muke kira da hajiya kayi sanadin aure ne ya kawota garin lagos da zama ita da mijinta alhaji sani sai dai asalinsu ita da mijinta zarma ne wato yaren zabarmawa , haifaffun kauyen ilo ne dake ?ar?ashin hukumar bagudo dake jahar Kebbi , sunan kakata ta gurin uwa nace shiyasa ake kirana da kisna dan boye sunan ."
Alhaji Sani dan canji ne a unguwar yaba dake kusa da ojuelegba a garin Lagos ,yayi rawar ganin gurin bawa yaransa ilimi addinin dana boko sai dai karatun nasu baya wuce iya secondary school yake dakatar dasu ya sanyasu cikin irin sanar da yake wato canji, yaransa maza guda biyu aikin canji suke ban da mahaifin Aliyu wanda ya sakawa ransa son karya da son cin rayuwar duniya , baya zuwa aiki kamar yadda sauran yan'uwansa ke ?o?arin ganin sun gina kansu , kullum shikenan kwanciya a d'aki kusa da hajiya kayi ."
Duk da wannan kwanciyar da yake baya rasa kudin kashewa daga hannu yammatan da yake dasu kala dabam dabam yoroba, Igbo , hausa har ma da yarensa saboda Allah yayisa da tsananin farinjinin yammata saboda shararraren kyawun da Allah yayi masa na bugawa a jarida da ?aukar hankali kusan kyawunsa Aliyu ya d'auko shi din fari ne sol shi da mahaifiyata sa?anin jinsin zarma da mafi yawancinsu bakake ne , suma asalin kyawunsu sun dauko ne daga mahaifiyarsu dan hajiya kayi fara ce sol ko digon baki babu ajikinta haka shima alhaji sani fari ne sai dai ba sol kamar hajiya kayi ba ,bayan kyau da Allah yayiwa haroon har da tarin ilimin boko domin kuwa ?wa?walwarsa naja sosai dan har schoolaship ya samu zuwa uniLag shi da abokinsa damilola , sai dai Alhaji sani ya hanashi , hatta mahaifin dami sai daya saka baki yace "idan rashin ku?i ne yasa zai dakatar da karatunsa gwamnatin ce zata dauki nauyin komai amman Alhaji sani yaki yarda yace "shi iya secondary School kawai yake da bukatan yaransa suyi tunda sun iya karatu da rubutu shikenan , haka mahaifin dami ya hakura ya tura d'ansa ."
Hajiya kayi tayi fama da haroon akan ya tashi ya nemi na kanshi kamar yadda yan'uwansa ke yi tunda bai samu damar cigaba da karatunsa ba amman yayi kunnen uwar shegu daita har daga karshe itama ta dinga biye masa tana bashi cikin kudin da manyan ya'yanta ke bata hakan yasa kyawun haroon sake fitowa saboda tsadaddun kayan da yake sakawa jikinsa ya famtama gari gurin abokai , duk sanda uncle garba yayi masa maganar aiki kuwa ranar babu zaman lafiya a gidan ya dinga nunkurfici kenan yana cewa "shifa ba zai iya harkan canji ba ci baya ne agurinsa dan ba zai iya tsayuwa a bakin titi yana kiran mutane suna masa wulakanci ba su da sukaji zasu iya su cigaba da tsayuwa akan titi bai zai hanasu ba amman shi bazai iya ba , iya gata hajiya kayi ta nunawa haroon , duk abinda yake so tana masa saboda kasancewarsa mai sunan kanin mahaifinta kuma shi ya riketa har aure tana ji dashi sosai .."
" Mahaifina kuwa asalin iyayensa yan kano ne a karamar hukumar kiru , sai dai shima zama ne ya kawo iyayensa lagos , anan cikin garin lagos aka haifeshi a unguwar agege shi da sauran yan'uwansa ,kakana na gurin uba alhaji lukman shararraren mai arziki ne wanda sunansa ya shahara a jahar lagos sannan ya karad'e sauran garuruwan dake cikin nigeria kasancewarsa ?an siyasa , Alhaji lukman yana da tarin ya'ya da yawa wajen su a shirin da shida ya haifa , ya mallaki maza da mata ,maza shabiyar mata goma amman gabad'ayansu kansu a ha?e yake duk da wasu daga cikinsu sun mutu sauran ashirin a raye , mahaifina yana da yawon yan'uwa sai dai yawansu bai sa kansu ya rabu ba , hakan kuma ya samo asalin ne agurin mahaifinsu shi ya ha?a kan ya'yansa ,hakan yasa yaran suka taso kansu a ha?e cikin tsananin son juna babu ruwansu da wannan uwarsu ?aya ubansu ?aya, wannan uba daya ne , suma haka zalika iyayen ma kansu a ha?e yake haka ma jikoki muna matukar qaunar junanmu .."
" mahaifiyata salaha da mahaifina Alhaji realwan sun ha?u ne a wani zuwa bikin abokinsa idiaraba soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu ,sunyi aure bayan gwagwarmayar rayuwa da mahaifina ya sha kafin mahaifin mahaifiyata Alhaji sani ya yarda da aurensu a cewarsa ba zai ?auki tilon diyarsa mace ya bawa bare kuma yare da ban ba zarma d'an'uwansa ba , dan asalin zarma basa bada auren ?a?ansu ga wani yare baya ga yarensu bisa nasu ra'ayin ,dan har yanzu ba kowane bazabarme ke daukan ya'yansa mata ya aurawa bahaushe ba , sai dai zabarmawan dake zaune a garin lagos suna kokarin su bawa bahaushe idan sun san asalin daga ina yake kuma sun san halinsa amman yawancin na kauye basa bada yaransu saboda suna ganin hausawa basa rike aure ga saurin saki , har yanzu har kwana gobe ba kowani zarma ke daukan d'ansa ya bawa bahaushe ba sai dai su kan yarda ?a?ansu maza su auro ya'yan hausawa mata ."
Tun bayan da'akayi auren iyayena Allah bai nufesu da samun haihuwa ba sai da suka kai kimanin shekaru goma da aurensu sannan Allah ya basu haihuwar ya badamasi , yayinda a wannan lokacin tuni uncle garba da uncle bature sun yi aure kuma a rana daya kuma duk yaren zarma suka aura mazauna Idiaraba .
bayan bikinsu bada jimawa ba hajiya kayi ta koma ilo da zama ita da mijinta kasancewar girma ya soma zuwan musu wanda kusan al'adar zamar ne basa karashe rayuwarsu a wani guri sa'banin garinsu na haihuwa , duk yadda suka kai ga neman kudi aguri da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 21