ya gigice ya rasa inda zai nufa dashi kawai ya nufi sama dashi gabad'aya suka biyo bayansa hankalinsu a matukar tashe kofar dakin mommy dake bude ya shiga ya kwantar da yaron yana kiran sunansa tare da ta?a kumatunsa cikin tashin hankali "areef! areef!! dukkaninsu babu abinda suke fa?a sai sunan areef bude idanunka.
aunty zee tace "areef my boy open your eye', amman Shiru ...
kisna data karasa shigowa dakin ta tsaya daga bakin kofa ta kasa k'arasowa inda suke hannuwanta duka dafe da qirjinta dake wani irin mahaukacin buguwa da karfi ,jira kawai taji abinda zasu ce mata ya mutu ko yana raye ....
a guje Aliyu ya shigo dakin sakamakon fa?a masa da nasir yayi yana k'arasowa bai san sanda ya matsar da samir gefe ba ya cicccibi d'ansa ya rungume ajikinsa yana kiran sunansa "areef !arerf !! aunty zee ta d'auko ruwan roba dake ajiye ta mikawa Samir sannan ta amshi yaron daga hannun Aliyu ta kwantar dashi ta amshi ruwa ta shafa masa a fuska ya ?an sauke ajiyar zuciya da kyar yana ?o?arin bude idanunsa amman ya kasa Samir ya fita da gudu tunawa da yayi idan mutun ya samu shock na electric ruwan gishiri ake fara bashi ko cikkaken second biyu bai yi ba ya dawo dakin ya mikawa aunty zee ruwan rige rige safiyya da aunty zee sukayi gurin amsa ruwan aunty zee ce tayi nasarar amsar ruwan ta bashi ya sha tana kiran sunansa "areef plz my dear open your eyes say something to aunty zee ..."
" Nasir Kira doctor plz inji cewar Samir , Nasir ya mike ya fita da sauri, gaba-daya sun rude sun gigice , a mutukar fusace aliyu yace " wai ya'akayi wannan accident din ya faru dashi "?Cikin rawar jiki samir ya sheida masa kamar yadda kisna ta fada masa ta daura ruwan zafi ta manta amman tana tunanin areef yayi wasa da ruwa kafin ya ta?a hot plet din , saurin dafe goshinsa yayi yana furta "ya Salam yaji kamar ya kamota ya rufeta da dukan mutuwa ,
jin yadda suke kiran sunan areef har lokacin ta sadaukarwa ranta cewar ta rasa d'anta wasu zafafan hawaye suka soma turereniyar zubowa daga idanunta ta sake makalewa a jikin bango tana furta kalmar data ji ta fito daga bakin aunty zee wato "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, shi kawai take furtawa tana maimaitawa cikin haka nasir ya shigo tare da doctor rike da briefcase a hannunsa gabad'aya suka matsa suka bashi guri ya cire abun awon daga wuyansa ya auna shi yaga yana numfashi sai dai ba sosai ba Aliyu ya daga kafafunsa daga inda yake tsaye ya fuskanci inda kisna take tsaye "kuka munafurcin me kike wa mutane bayan sakacinki ne duk ya janyo zan rasa d'ana "? Gabanta ya shiga dokawa da karfi ta
Hannuwanta duka ta ha?e guri daya alamun yayi mata afuwa "ki daina nuna kamar kin damu da halin da areef yake ciki kowa yasan baki damu dasu ba saboda tsanar da kike min yayi maganar a fusace yana nuna qirjinsa ..."
"Aliyu dan Allah ka natsu areef zai dawo daidai bai kamata kayi bleming d'inta ba kasan bazata bari wani abu ya samesa da ganga ba inji cewar nasir .. "furzar da iska mai zafi yayi ha?e da rike kugunsa da hannunsa daya "bata sona komai zata iya yi dan ta dakushe farincikina bayan wa?an nan yaran sune rayuwata, sune dangina ,sune komai nawa ya karasa maganar cikin tsananin fushi yana nunata da yatsansa "wannan muguwar babu abinda bazata iya yi akaina ba tun da bata sona ..."...
Doctor ya kai hannu yana ?o?arin bude idanun areef "open your eyes da kyar yaron ya iya dan bude idanunshi da taimakon doctor , haka ma bakinsa ya bu?e ya duba sannan yace "karku damu zai dawo daidai Aliyu yace doctor "kana ganin zai rayu ? "Zai rayu sai dai jikinsa yayi week sosai saboda shock din daya samu me kuka bashi kafin na karaso ?" An bashi ruwan gishiri suka hada baki gurin fadar haka "Yes wannan abu ne mai kyau, abinda ake son abawa duk wanda ya samu shock daga wutar lantarki kenan garin yaya ma karamin yaro kamar wannan akayi careles dashi haka "?"Wannan mahaukaciyar uwar tashi ce tayi sakacin dashi yanzu kalli abinda ya faru dashi bancin yana da sauran yawanci rai da ba abinda za'a fada kenan ba "gaskiya ta dinga kula dashi idan ba haka ba zata iya rasa shi wata rana ,yanzu dai ku bar shi ya huta zuwa wani lokaci duk suka fito daga dakin suka bar aunty zee tana shafa masa kai ....."
Nasir ya dubi Aliyu yace "muradi abinda kayi sam bai dace ba ban ji dadin abinda ka fa?a a daki ba , tun bakasan da zaman yaran nan ba ita ke kula da yaranta dan me zaka yi bleming d'inta without any reason for god sake"dan Allah karka fa?a min babu dadi kulawar banza kulawar wofi ,wacce irin kulawa ce wannan da har za'a yi careless da rayuwar yaro ? idan har tana kulawa dasu bazata bari abinda ya faru yanzu ya faru dashi ba "."karfa ?acin rai ya sa ka furta sabo itafa yar adam ce "ai komai za'a fada akanta ba yarda zaka yi ba kana bayanta ".
"ba haka bane wallahi nasan tayi kuskure tunda tasan yaran suna gidan kuma suna da kiriniyya bai kamata ta barsu a parloun kasa su kadai ba alhalin kofar Kitchen a bude yake sannan kuma bata gurin sai dai ya zamu yi da qaddara "? "Allah ya qaddara haka dole sai hakan ya faru babu tsumi babu dabara kisna ta matso kusa dashi saboda ganin yadda ?acin ransa ya fito fili muryarta na rawa tace "dan Allah kayi hakuri wallahi ba da ganga nayi ba ai jin maganarta yayi kamar garwashin wuta a zuciyarsa ya juyo a fusace yana dakatar daita da hannunsa " baki da abinda zaki kare kanki agurina bare wani hakurinki din banza ,me zanyi da hakuri ?
" kima san wani abu wallahi bazan barki haka ba sai na hukataki bisa gangancin da ki ka min akan yarona ......"
zaro ido waje tayi hawayen dake makale a cikin kwarnin idanunta suka gangaro ya kai hannu zai cafki wuyanta nasir yayi saurin rike masa hannu "haba aliyu meye haka kake kokarin yi "? ya fixge hannunsa da nasir ya rike yana damko tsintsiyar hannunta yayi hanyar waje daita tana biye dashi tana kuka tana kallon bayansa jikinta na wani irin rawa gabad'aya suka biyosa har Samir daya zuba masa ido suna masa magana yayi musu banza bai kula kowa ba sannan bai tsaya a ko'ina ba sai a haraban gidan yana gama k'arasowa yayi cilli da hannunta ta tafi luuuuuuuu zata fadi "ki bar min gidana sannan ki fita a rayuwata bana bukatarki ,Aliyu baya bukatarki arayuwarsa"shiru tayi tana kallonsa zuciyarta na dokawa da karfi kamar zai fasa qirjinta ya fito waje ,"bana sonki bana bukatarki arayuwata da ki kashe min ya'ya gara tun wuri na zareki acikin rayuwarta ya karashe maganar jijiyoyin kansa na mikewa alamun ya kai kololuwa gurin ?acin rai ".
" Aliyu dan girman Allah ka tsaya ka dawo hankalinka idan rai ya ?aci hankali ke dawo dashi abinda kake yi sam bai dace ba haniyarsu ta fito da aunt zee haraban gidansu "kasan Allah bazan saurari duk abinda zaku fa?a min akan wannan ba kawai ta bar rayuwata kafin nima ta kasheni dan babu imani a zuciyarta "no aliyu wannan ba daidai bane aunty zee ta fada tana kallon samir dake tsaye rungume da hannuwansa duka a qirji ya bala'i tsurawa Aliyu ido yana kallonsa yana mamakinsa yana jin wani irin d'aci acikin ransa wanda bai taba tunanin zai ji akan Aliyu ba mutumin da suka taso tare, gurin baccinsu daya komai nasu tare sutura iri daya suke sakawa hatta karatu iri daya suka yi babu abinda ya bambamta su sai karfin zuciya cikin fushi aunty zee tace "ka tsaya kana kallanmu ka masa magana mana nasan idan ka masa magana zai fahimka akan tamu maganar "numfashi ya sauke yayi mata alamar tayi shiru tare da cewa "bana bukatar ki sake cewa komai..."
"Na tsaneki fiyye da tsanar da kika min , duk kalamanki basa shiga zuciyata bare su samu matsuguni sannan karki sawa ranki ni Aliyu zan dawo na soki a wannan duniyar never hakan ba zai ta?a faruwa ba ,bani da lokacin da zan fahimci kowa daga cikinku akan wannan yarinyar ya nuna kisna kinga zamanki acikin gidan bashi da wani amfani dan dake da babu duk daya ne agurin Aliyu gara ki kama gabanki ."
Cike da tsananin tashin hankali tace "dan Allah ka tsaya ka fahimceni ta kai hannuta zata kamosa ya buge mata hannu da sauri "don't don't ever touch me ,karki ga na dawo dake cikin rayuwata ki ?auka ko tsoro ne a'a hallaci na duba if not ke da Aliyu har abada dan ko alahira bana qaunar na hadu dake ,wallahi akan wannan gangancin da kika min zan iya sakinki ......."
kanta ne ya soma juyawa saboda jin kalmar daya fito daga bakinsa take ta soma ganin juya jikinta ya kama rawa sosai fiyye da d'azu gabad'aya tsayuwa ya gagareta jikinta ya kasa ?aukar kafafunta ta soma yin kasa zata fadi aunty zee tai saurin matsowa kusa daita ta rikota jikinta tana girgiza mata kai "aunty zee kina jin abinda yake fa?a akan ya'yan da ni kadai nasan irin azabar dana sha akansu , nasan nayi masa kuskure amman ya kamata zuwa yanzu ya yafe min ko da yake na fuskantarshi so yake ya koreni ya rabani da ya'yana suyi rayuwa tare da wata "exactly abinda nake nufi kenan kuma na gode da kika fahimci haka saboda bani da abinda zanyi dake , jin haka yasa ta sanyawa jikinta jarumta ta mike bisa kafafunta da suke rawa ta goge hawayen idanunta "to ya kake tunanin zan iya rayuwa babu ya'yana"? "Ka barni na rayu tare da yarana karka nisantani dasu , dan Allah kayi hakuri bazan sake ba nasan nayi kuskure bazaka sake kamani da makamancin irin wannan laifin ba, kayi hakuri nayi kuskure bazan sake ba ". tana kuka tana rokonsa ..."
"baki da hankali ki rike hakurinki dan babu abinda zanyi dashi rayuwa dake ne dai bai zai me min dole sai nayi ba dan haka ki kama kanki da kyau dan at any time zan iya rabuwa dake wallahi coz you are nothing to me ya karasa maganar yana huci kamar zakin daya ga abincinsa ya rasa har zai juya ,ya tsinkayi muryarta cikin kuka "yadda baka damu dani ba nima bazan sake damuwa da kai ba ......"
"daya fiyye miki Kinga kin hutar da bakar zuciyarki son Wanda baya sonki yana gama fadar haka ya juya ya shige gidan , kuka take sosai kamar ranta zai fita haka aryan shima kuka yake yana rike da hannunta duk ta fita haiyacinta da kyar aunty zee da safiyya suka kamota suka shigo daita suna rarrashinta "har sai yaushe Aliyu zai ga farina aunty zee "?
"Na kaskantar da kaina na bashi hakuri yaki hakura ,na bishi na bishi yaki saukowa me zan masa aunty zee ki fa?a min abinda zanyi masa ya huce "? ta karasa maganar tana sake rushewa da wani sabon kuka "aunty zee ko hakura zanyi dashi ne na hutawa rayuwa tunda baya sona ya furta min ni dashi ya furta agabanku "wani irin tsana ce haka ? aunty zee ta girgiza mata kai" maganar hakura dashi ma bata taso ba " kai aunty zee wallahi na hakura da Aliyu koda kuwa shine karshen namiji a duniya zan barshi ta mike cikin rawar jiki ta hau sama tana taka step biyu biyu aunty zee ta biyo bayanta da sauri tana kiran sunanta ....."
Mmn sudais
????????????
CUTAR DA KAI
????????
????????????
Free page 11
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ?aya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...????
A matukar harzuke ta shiga dakin zuciyarta kamar ta kama da wuta , tana k'arasa shiga cikin filin d'akin idanunta ya sauka akanshi tsaye a tsakiyar d'akin ya zuba hannunwansa duka a cikin aljihun wandonsa yayinda idanunshi ke runtse yana ciza gefen lip's dinsa na kasa a hankali , duk da bai bude idanunsa ba yasan itace ta shigo dakin duba ga yanayin da yaji bugun zuciyarsa ya qaru."
kallon second biyu tayi masa ta ?auke idanunta akan shi ta k'arasa da sauri ta bude wardrobe ta dauko akwatin kayanta data zo dashi kasar ta ajiye akan gado ta bude ta soma dibo kayanta ?aya bayan ?aya tana zuba aciki ,still bai bude idanunshi ya kalleta ba bare ya dakatar daita daga abinda take ?o?arin yi ya cigaba da ciza lip's dinsa , hakan yasa taji sabon ?acin rai ya mamaye zuciyarta taji muddin bata bar masa gidan a lokacin ba zata iya mutuwa.."
Aunty zee ta shigo dakin cikin tsananin tashin hankali ta k'arasa gareta ta rike hannuta batare da ta kalli inda Aliyu ke tsaye ba hankalinta a matukar tashe ta soma magana "mai kike ?o?arin yin saboda Allah ? "Kiyi hakuri mana
duk fa abun bai kai haka ba, idan fa rai ya ?aci hankali baya bata kisna , ki dawo hankali ki natsu dan girman Allah Karki yi abinda zai janyo bacin rai fiyye da wanda muke ciki yanzu ".Tun da aunty zee ta soma magana kisan bata furta komai ba ta cigaba da zuba kayanta cikin akwati zuciyar na wani irin zafi da ciwo , haka shima Aliyu bai ce komai ba sai sake juya musu bayansa yayi yana furzar da iska mai tattare da bakin ciki ".
Kisna na shirya kaya aunty zee na dauka tana maida wa cikin wordrobe tana bata hakuri , wani sabon kuka ne ya kufce mata , hawaye sai turereniyar zubowa suke daga cikin kwarnin idanunta "mai kike son nayi aunty zee shine fa da kanshi yace na bar masa gida "? Tayi maganar cikin tsananin kuka wanda da kyar muryarta ta fito "nasani amman dan girman Allah kiyi hakuri ko zaki tafi ba yanzu ba saboda tashin hankalin da mommy zata shiga Sam Sam mommy ba zataji dadi faruwar haka ba. tayi maganar tare da juyowa ta kalli inda Aliyu ke tsaye har lokacin tamkar babu wani halitta dake motsi agurin, ya aliyu ka bata hakuri dan Allah sannan ka dakatar daita dan gaskiya kayi kuskure abinda kayi sam bai dace ". Bazan yayi daita qirjinshi na wani irin dokawa da karfin gaske "saboda me zai bata hakuri bayan bai ga abinda yayi mata ba ,idan zata zauna ta zauna idan zata tafi ta dade shi dai bazai wani dakatar daita ba yayi maganar aransa yana furzar da iska mai zafi ....
kisna ta sake rushewa da wani sabon kuka mai matukar cin rai ganin ko kallonsu Aliyu bai yi ba bare ya kula aunty zee dake masa magana ,ta d'aura kanta a kafad'arta aunty zee numfashinta na barazanar daukewa saboda kukan da yaci karfinta "kisna !kisna!! Aunty zee ta ta kira sunanta a rude tare da rungumeta a jikinta suka zauna a bakin gado tana cigaba da kiran sunanta , da kyar kisna ta janyo numfashi ta sauke zuciyar na mata wani irin azababben zafi da ciwo , aunty zee ta mike ta tsiyaya mata ruwa a glass cup ta mika mata "ki sha ruwa kisna ko zaki ji sanyi babu mutsu kisna ta amsa cup din ta kai bakinta ta kurbi kadan ta mikawa aunty zee sauran ,aunty zee ta amsa ta ajiye ta cigaba da bata baki .
cikin haka aryan ya shigo dakin yana kuka aliyu ya juyo a hankali yayi taku daya yana ?o?arin kamoshi zuwa garesa , amman tuni yaron ya karasa gurin uwarsa dake kuka tamkar ranta zai bar gangar jikinta , ya haura saman gadon ya rungumeta ta baya yana furta mata kalmar "sori mommy , papa ne ya saki kuka kou ?" Ki yi shiru Ki daina kuka zan rama miki kinji ".
kukanta ne ya qara akan wanda take tabbas ya'ya rahma ta juyo ta rungumeshi ajikinsa tana sheshekan kuka tamkar ranta zai fita,hawaye tausayinsu ne ya shiga gangarowa aunty zee Aryan ya soma ?o?arin raba jikinsa dana kisna ",mumy bari naje na rama miki "a hankali ta shiga girgiza masa kai tana kuka gumi na tsatsafo mata ta ko'ina ajikinka matse aryan tayi gam saboda kokarin fixgewa da yake kokarin yi ajikinta yadda take kuka haka arayan da aunty zee ke kuka gaba-daya an rasa wanda zai rarashi wani ."
Sautin kukansu ne ya soma damun Aliyu a natse ya fita daga d'akin yana jan dogon tsaki ya shiga d'akin da areef yake kwance ya zauna a gefensa tare da tsura masa idanunshi yana kallonsa, ganin yadda numafashinsa ke sauka a hankali yasa shi sauke numfashi da ajiyar zuciya a tare ya d'aura hannunsa akan sumar yaron yana shafawa a hankali yana jin wani irin sanyi mara misaltuwa a zuciyarsa , dan da wani abu ya samu d'ansa da sai yayi distroye rayuwarta ,sai yayi mata abinda har ta koma ga Allah bazata mantawa dashi ba taimakonta daya d'ansa yana numfashi kuma ko yanzu bazai barta ba har sai yaga mikewar d'ansa tukunan zai saurara mata ..."
"Idan kika ji ancewa mutun yayi hakuri bisa wani abu daya faru to an cucesa ne ,ki qara hakuri kisna idan kika bar gidan Aliyu da sunan yaji ko rabuwa dashi ina zaki "?"kin san dai baki da inda zaki sannan baki da masauki a gidan dady idan kin manta abinda dady yace bari na tuna miki "cewa yayi matukar ba ziyarar arziki ce zata kowaki gidansa ba baya son ganinki da suna matsala dan baki a masauki a gidansa, kuma duk ranar da kika kashe aurenki da Aliyu sai dai ki nemi wani uban amman ba shi ba, zan rokeki da ki kara hakuri kisna ki zauna a d'akinki kada ki ?auki maganar Aliyu da mahimmcin da zai sa ki bar gidan nan ". wani sabon kuka ta rushe mata dashi tare da zubewa kasa bisa gwiwowinta ta kamkame Aryan dake rungume ajikinta "shikenan haka zan kare rayuwata cikin kunci da maseefa da tashin hankali "? "mai yasa dady da mommy suka kasa fahimtata akan ya Aliyu "?
"Mai yasa suka fi son shi akan ni da suka yi silar zuwana duniya "?
aunty zee ta mike tsaye cikin tsananin tashin hankali ta amshi aryan a hannunta sannan kamota ta zaunar daita tace " wannan soyayya daga Allah ce kisna da kuma kyautatawar da yayi musu, kin sani na sani kowa ma ya sani a cikin yan'uwa Aliyu mutumin kirki ne ,ni yanzu babu abinda zan ce miki daya wuce kiyi hakuri sannan kiyi ?o?arin ki adana damuwarki kafin mommy ta dawo gidan nan ta fahimci wani abu , sannan wa?an nan kayan suma ki karasa maidasu cikin wardrobe zanje muyi magana da ya Aliyu ta k'arasa maganar tana fita daga."
kai tsaye parlou'n kasa ta zarce domin yin magana da Aliyu sai dai bata samesa anan ba sai nasir da Samir da Safiyya ta samu zaune shiru tamkar wa?an da aka turo musu da sakon mutuwa , ta Kallesu daya bayan daya sannan tace "ina ya Aliyu ko ya fita ne "?Safiyya da nasir ne suka hada baki gurin ta bata amsa da bai sauko ba yana sama ,
yayinda har lokacin samir ya kasa furta komai sannan ya kasa aiwatar da komai dan jin zuciyarsa yake kamar zata kama da wuta yau da wani ne ba Aliyu ba yayiwa kisna irin wannan wulakanci Allah ne kadai zai rabusu amman akan Aliyu babu abinda zai iya yi ko dady yaji yayi magana akan lamarin sai ya bata masa rai bare matsayin Aliyu ya zarta komai a zuciyarsa ..."
Har aunty zee ta juya zata koma sama ta tsaya batare data juyo ba tace "dan Allah abban Junior ka dawo daidai kar mommy ta dawo ta fahimci wani abu ,wannan matsalar tsakaninsu ne kuma inshallahu komai zai dawo normal yanzu batare da bata lokaci ba , tsakanin miji da mata sai Allah ko mutun ya shiga fa?ansu kunya zai ji tayi masa hannunka mai sanda saboda lura da tayi gaba-daya yanayinsa ya sauya tana gama fadar haka ta hau sama da sauri ta shiga dakin mommy ,nan ta samesa zaune ya tasa areef gaba yana kallonsa hawaye na tsiyayo wa daga idanunshi jin motsin shigowar mutun yasa yayi saurin ?auke hawayensa da hannunsa , sai dai ya makaro dan ta rigada ta gani .
girgiza kai aunty zee tayi sannan ta samu guri ta zauna akan kujera tana kallonsa sai data numfasa sannan ta kira sunansa a natse " ya Aliyu .... Bai amsa mata ba haka zalika bai waigo inda take ba ,sanin datayi yana sauraranta yasa ta cigaba da magana "dan Allah ya Aliyu ka canza ,a zahirin gaskiya ban ji dadin abinda kayi wa kisna ba , kuma nasan ko mommy tana nan kai zata bawa rashin gaskiya akan abinda ya faru "."ina dalilina nayi haka , barinta gidan nan shine abinda zuciyata ta yanke akanta idan taga zata iya ta cigaba da zama a gidan idan bazata iya ba ga hanya nan dan Allah Karki sake bata hakuri akan lallai sai ta zauna ki bari ta wuce duk inda zata dan nima nafi bukatar haka "."Uhmmm Aliyu ka kuwa masan abinda kake fa?a kama ajiye batun aurattayar dake tsakaninku kai da kisna yan'uwa ne na na jini kasawa ranka kisna Aliyu suna tare muddin rai mutuwa ce kawai zata rabasu "stop saying that zainab I don't like what you are doing Ina nugun ganin girma da mutuncinki saboda ke din mai mutunci ce kowa ya sani ...... ".
"bazan daina fadar haka ba ya aliyu saboda bayan jinin na y'an'uwanta akwai wani jini na musamman dake gauraye acikin jininku ko kaki ko kaso kisna da Aliyu abu guda ne "dan Allah ki daina fa?ar haka kina maseefar taba min rai wallahi "",Babu wani ?acin rai hakuri ma ya kamata kaje ka bata saboda kayi mata ba dade ba . "wannan maganar ma ba mai yiwa ba ne dan Allah ki daina fadar haka banaso ina ganin girmanki zainab saboda me zan bata hakuri "? "Laifin mai nayi da zan bada wani hakuri "? yayi mata tambayar ajere ransa na sake ?aci sannan ya cigaba da magana cikin zafin zuciya "bana tunanin abinda nayi ya sa'bawa Shari'a to saboda me kike tunanin zan bata hakuri "? yayi maganar yana rike hannun areef yana jin yadda hannunsa yayi sanyi "yanzu kana son fahimtar dani cewar ba kayi kuskure ba Kenan "?"Yes of course ban yi komai ba wallahi ,kin kasa dai fahimtata ne kawai saboda kina ganin kamar nayi kuskure alhalin ni Kuma nasan babu kuskure dana akan za'a kashe min da.... .....".....
yayi shiru ya kasa karasa maganarsa yana kallon kofar d'akin ,itama aunty zee kofar tabi da kallo ganin kisna ta gani tsaye idanunta na tsiyayar da ruwan hawaye muryarta cikin kuka tace "ki yarda aunty zee bai yi min laifin komai ba ,ni kuma daman na ?auki laifina ya dai kasa min uzuri ne amman nasan nice da laifi wallahi tunda nasan halinsu aryan basa zama guri daya ". ta runtse idanunta wasu hawaye masu zafi da ciwo suka sake gangaro mata .
"ni kaina a yanzu zanso rabuwa dashi
sai dai bazan iya kallon idanunshi nace na tsaneshi ko nace bana bukatar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 21