gode ta fada ha?e da kamo hannu kisna cikin nata "dan Allah kema ki saki ranki ki daina saka damuwa aranki kalli yadda kika rame gaba-daya kin canza kamar bake ba ,kin fi kyau a sanda naga hotonki gashi naji uncle Aliyu yace next week family dinki zasu zo ? Kisna ta d'aga mata kai alamun "eh . "kinga kuwa ya kamata ki natsu ki kwantar da hankalinki ta yadda idan sunzo su ganki fess a cike, idan mahaifiyarki ta ganki haka a rame bazataji dadi ba "ni dai shawarata komai Aliyu yake miki kiyi hakuri tunda bazaki iya fa?a wa kowa ba bare ki ragewa zuciyarki rad'ad'i , ki sharesa ki cigaba da rayuwarki ."zanyi hakuri na cigaba da rayuwata kamar yadda kikace amman bazan iya sharesa ba ."to shikenan sai ki zauna kina kunsawa kanki bakinciki har wani ciwo ya kamaki koda yake baki ga wahala bane idan kikaga wahala da kanki zaki nemi mafuta nan suka cigaba da tautaunawa har kusan karfe biyu sukayi sallar tayiwa safiya tayi abinci tace a koshi take tayi mata sallama ta tafi."
komawa sama tayi ta cigaba da kukan zuci dana zahiri , ta shiga zagaye d'akin kafin tana zance zuci hawaye na cigaba da gangaro mata "kisna dole ki nemawa kanki mafita to me zanyi "? dole ina bukatar waya gashi bani dashi a hannuna ina zan samu waya ? "Ta yiwa kanta tambayar "babu hanyar da zaki samu waya muddin ba Aliyu ne ya baki ba shi kuma gashi bashi da niyyar sai ta tsagwaron rashin mutunci ." shiru tayi hannunta na tsarke cikin juna ta karasa ta kwanta akan katifa tana sauke numfashi a hankali ta kai hannunta cikin sumar kanta ta yamutsa tana sauke ajiyar zuciya "baki da abun yi dole kawai ki kwantar da hankalinki ki rike sirrin gidanki ki ?auki wannan abu a matsayin kaddararki tana kwance lamo ya shigo d'akin da sauri yana waya ta d'ago ta kalleshi aka ci sa'ar shima idanunshi sun kai gareta suka ha?a ido, kallo ?aya yayi mata ya ?auke kanshi yana jan tsaki "eh gasu nan muna tare ma yanzu ,okay to shikenan yayi maganar cikin harshen tsadadden turancinsa sannan ya katse wayar ya ?auki jakar laptop d'insa ya fita."
Jin hayaninyarsu a kasa tayi tunanin ta sauka ko ruwa ne ta basu tunda sun san yana da mata a gidan bai kamata ta biyewa halinsa ba , a hankali ta yunkura ta fito zuwa parloun tana tuku akan step cike da natsuwa , a hankali ya d'ago ya kalleta ya tabe baki yana yatsina fuska kamar yaga wani mugun abu a karshe yayi mata kallon banza tare da ?auke kansa ya d'aure fuska tamau tamkar hadari ,suna zaune gabad'ayansu suka d'ago idanunsu saboda daddad'an kamshin turarenta da ziyaci hancinsu duk da ba sawar yanzu bace tun wanda tasa da safe ne makale ajikinta idanunsu na kanta har sanda ta karasa saukowa muryarta a raunane tace "sannku da zuwa ina yininku cikin harshen turanci?Gabad'ayasu suka washe baki suna sakar mata murmushi kafin daga baya suka amsa "amarya a she idonki biyu ai dana ji shiru baki fito mun gaisa ba na ?auka bacci kike yi nasir ya fadi haka yana kallonta.?
girgiza masa kai kawai tayi tace "idona biyu na dai dan kwanta ne Aliyu daya dago yanata faman harararta tun data tsaya yace "tsabar koshi da samun guri ne yayi mata yawa " yayi maganar da hausa sannan ya kalli nasir "kai yanzu malam mai ruwanka da fitowarta ne ? "Kuma idan ta fito uwar me wannan wawiyar zata maka da kake ta wani faman washe mata ha?ora ?" Ya k'arasa maganar yana jan tsaki .
shiru Kisna tayi , jikinta ya sake yin sanyi da lamarin Aliyu, wato dai komai sai ya rama ,a hankali ta soma daga kafarta ta shiga Kitchen domin kawo musu abun sha ."
Nasir ya tsina fuska "gaskiya Aliyu ba'a haka abinda kakewa yarinyar nan fa bai dace ba ,bafa Allah ne zai sauko daga sama ya baka hakuri ba, mutane dai irinmu ne zasu baka hakuri komai fa yana da lokaci tunda gashi ta sauya ta dawo yadda kake so gaskiya ni dai ka daina abinda kake mata idan ba haka ba zance ta fara ramawa ka dai san itama ai ba kanwar lasa bace duniya ce ta maidaita haka ya k'arasa maganar yana kwashewa da dariya .
"ka dade wallahi ai abinda nake so kenan ta nuna halinta kowa ya gani daga nan su sake bukatar takardan sakinta a karo na biyu na rabu daita na huta da naci mayyar yarinyar nan ,yarinya kawai ta like min tana takurawa rayuwata har ta fito Aliyu bai daina zaginta ba , ta ajiye ruwan lemu da ruwan sanyi yana cigaba da zaginta yayinda abokan aikinsa ke faman satar Kallonta tamkar zasu cinyeta , tayi matukar yi musu kyau tamkar ba hausa ba , komai na jikinta cassss cassss rohan wanda ya kasance dan kasar India shi yafi Kallonta yana lasar lip's d'insa matsayinta na matar abokinsa ne kawai yasa zai daga kafa amman da a waje ya ganta babu abinda zai hana ya kulata har ma da kulla mu'amula mai karfi a tsakaninsu . "sannu Kisna mun gode fa , ba tace masa komai ba ta juya a hankali ta haye sama ta shige d'aki tana kuka ranta na mata zafi "daman sai daya gargadeni ......"me ma ya kaini sauka ?tayiwa kanta tambayar hawaye na gangaro mata.
"yanzu dan Allah mutanen nan da suna jin hausa haka zakayita magana agabansu "? "Dan Allah malam kayi abinda ke gabanka banason damuwa da kumfar baki ...Har kusan la'asar suna nan suna aiki , bata daddara ba ta sake saukowa domin ta d'aura musu abinci dare ,karfe bakwai daidai ta kamala da komai ta zuba a kula ta d'aura a tire da plet da spoon ta fito daga kitchen ta ajiye agabansu ta kawo musu ruwa tunda ta soma kai kawo rohon ya tsaida abinda yake ya zuba mata ido yana faman Kallonta sai ma yaga kamar tafi dazu kyau ,Aliyu ya lura da irin kallon da rohon ke binta dashi sai dai bai bi ta kanshi ba ,haka abincin data ajiye bai kalla ba bare wacce tayi abincin, nasir yace "gaskiya yunwa nake ji fa bari naci ka?an idan naje gida na qara dan idan na cika cikina anan akwai katuwar matsala idan na koma gida , tsaki aliyu yaja yaki kallon inda yake ."
anan gabad'aya abokan Aliyu suka ci abinci suka sha ,nasir da sauran abokansa nata santi da yaba girkinta barin rohan yafi kowa zakewa dan har cewa yayi a tambayar masa ko tana da kanwa da bata yi aure ba a bashi yana so Aliyu ya yatsina fuska yana zabga masa ?atuwar harara "kai dan Allah ko dan girkin nan nata bazaka sauko ka rungumi matarka ba ku ci-gaba da rayuwa mai dadi ba "?
"a wannan zamani fa bakowace mace ta iya girki irin haka ba ya d'ago a sukwane ya kira sunansa " Abdul nasir ........."
"Na'am abokina mai zuciya da taurin kai kamar mutanen farko "tashi ka wuce gidanka dan Allah na sallaneka bana son damuwa "ko bakace ba wucewa zanyi gurin matata yar albarka mai kyautata min ina jin dadi ina godiya nasan ma yanzu tana can tana jirana ya mike ya kama gabansa yana murmushi ".
****
Daren ranar ma irin baccin da suka saba shi sukayi yana kan kujera yana waya da masoyiyarsa nawal ita kuma tana kan gado tana kukan zuci ta rasa yadda zatai dashi ita bata hana shi yin wayarsa da nawal ba amman ya dinga yi a waje ba sai suna tare ba, kwana yayi yana waya itama kwana tayi tana juyi har goshin asuba ta mike ta shiga bayi ta d'auro alwala ta fito ta soma gabatar da nafilfili har aka kira sallah ta tashi ta gabatar da sallah ta dade zaune tana lazimi tana kaiwa Allah kukanta da neman sausauci ..."
"Yana tsaye a saman gidan sanye cikin farar riga da wando baki ya hangota sanye cikin doguwar riga pinky colour sanye da k'aramin hijab tana share palo, shiru yayi yana kallon bayanta duk da bai ga fuskarta ba yasan tana cikin damuwa dan yana jin haka ajikinsa, tabbas abinda yake tunani din shine tattare daita dan hawaye ne ke tsiyoyowa daga cikin kwayar idanunta tana gogewa da bayan hannunta ,aikin da sai dai ta farka taga anyi komai, ko tabawa masu aiki umarnin aiwatar da duk abinda take so kuma dole subi umarninta suyi yadda take so yau itace take yi hawaye ya ci-gaba da zobo mata tasa hannu ta sake gogewa ta tattara sharan guri daya ta kwashe ta shiga Kitchen duk akan idanunsa, numfashi ya sauke yana furzar da iska mai zafi da ga bakinsa sannan ya juya ya koma d'aki ya rike kugunsa da hannunsa ?aya yayinda d'ayan hannun ke saman goshinsa yana tunanin yadda yake musguna mata ,duk sanda ya ganta cikin damuwa sai yaji kamar ya yafe mata sai kuma zuciyarsa ta hau tuno masa komai ".
*******
Ana gobe su mummy zasu sauka a kasar taji yana waya dasu har dasu aryan yana gama wayar tace " zan bika airport d'aukosu mumy gobe ya watsa mata kallon banza yayi tamkar ba dashi take maganar ba ,washegari tun data idar da sallar asuba bata koma bacci ba ta shiga Kitchen ta soma ha?a musu abinci ,abinci kala uku tayi musu ha?e da cak ta gama ta gyara ko'ina ta feshe gidan da kanshi duk abinda tasan mumy zata gani tayi magana sai data kawar dashi sannan ta hau sama ta shiga wanka ta shirya cikin atamafa super exlusive mai ruwan ja da zanen fulawa baki dinki riga da siket ne sun karbi jikinta ga wani sihirtaccen kamshi na musamman dake fita ajikinta ta d'aura doguwar riga abaya akan kayan tayi rooling kanta da mayafin abayar duk da ta zabge ta rame amman hakan bai hanata kyau ba , shi kanshi har mamaki yake duk yadda take cikin damuwa kyawunta baya dusashewa , tana nan kamar yadda ya santa da tsananin kyau da kamshi mai dadi , dake wa mutune iso a duk sanda suka kusanto inda take, hakika yabon gwani ya zama dole duk da bai jinta acikin ranshi amman yana jinjinawa kamshinta ,mace ce tamkar mahaifiyarta mai tsananin tsabta da iya tsara kwaliya tun bata kai haka ba gwana ce gurin ado ?auke kanshi yayi akanta ya soma ?o?arin shiryawa cikin kanana kaya kamar koda yaushe har ya gama narkakkun idanunta na kanshi ,tana kallonsa ya ?auki mukulin mota zai fita batare daya mata magana ba ,ganin yana ?o?arin fita tayi saurin shan gabansa tana fuskantar shi hancinsa ya shaki kamshin turarenta itama hancinta ya zuko mata kamshin turarensa atare suka lumshe idanunsu zuciyarsu na wani irin bugawa da matsanancin karfin gaske ......"
a hankali ta rigashi bude baki "haba aliyu kaji fa nace maka zani d'aukosu mumy shine zaka wuce ka barni " wata uwar harara ya watsa mata sannan yace "na sha gaya miki bana son shishigi ko amman da yake ke uwar yan shishigi ce sai da kika yi ,dole ne sai kin nemi gindin zama "?ya fa?a yana jan tsaki tare da tsareta da kyawawan idanunshi masu narkar mata da zuciya ."
shiru tayi tana kallonsa tana mamakinsa ita da mahaifiyarta amman kullum sai ya dinga nuna mata ya fita sonta ,ko da yake itama mumy haka take nuna wa tafi sonshi akan ya'yan cikinta sannan tafi yarda dashi fiyye da kowa dake cikin gidansu sake matsoshi tayi ta shige masa jiki har tana gogo jijiyarsa "karka 'bata min rai yau zan ha?u da mahaifiyata bayan wani lokaci dana ?auka ban ganta ba "karki 'bata ranki a banza dan babu inda zani dake na bar nawal dina dan tare daita zamu yayi maganar tamkar bashi yayi ba ya soma ?o?arin fita daga d'akin .
zama tayi a bakin gadon ta zuba tagumi tana mamakinsa "yanzu na sake tabbatarwa kaina cewa baka kaunata Aliyu ta fada tana nuna qirjinta da yatsa , tsayawa yayi cak tare da juyowa ya natse ya sake tsareta da idanunshi , idanunta sun ciko da hawaye ta runtse idanunta sai gasu sharrrrrrr sun gangaro "da kyau kiyi kuka sosai zan fi bu?atar haka wallahi babu abinda nake so kamar naga wannan ya tako ya kai yatsan hannunsa ya dangwalo hawayenta yana kallo murmushin farinciki ya bayyana akan kyakkywar fuskarsa "abinda nafi bukata kenan ranar farinciki ya zame miki ranar bakinciki yana gama fadar haka ya juya ya bar d'akin cike da farinciki " .
Yana fitowa direbansa ya bude masa bayan mota ya shiga suka bar gidan motar escout dinsa suka saka shi a tsakiya kai tsaye hanyar airport suka ?auka daman babu wata nawal din da zata shi daita kawai dan ya kuntata mata ne ya fadi haka kuma yayi nasara bata mata rai , akan hanya ya kira number nasir ya ?auka yace "ya'akayi,?
Aliyu yace " ka shirya ne ? "Eh kai kawai nake jira " okay ka biyomu da motarka mu hadu a airport , kusan a tare suka karaso guri direbansa ya samu guri yayi parking Shima Nasir yayi parking sannan suka fito ,Aliyu ya jingina da mota, nasir ya karaso ya tsaya kusa dashi "dan Allah abokina karka yi abinda zai taba ran kisna a gaban mahaifiyarta kasan tsakanin uwa da d'a sai Allah ba'a shiga tsakaninsu , duk son da mumy take maka bai kai na kisna ba "a ganinka ba , kai ne kake ganin haka amman ni a zuciyata ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba nasan tafi son akanta ,idan ka manta na tuna maka a yanzu ma tana samun kulawa ne agurin mumy saboda tana karkashina ,da a karkashin wani take wallahi bazasu ta?a had'uwa daita ba bare wata maganar fatan baki ta had'asu "duk da haka dai karka yi abinda za'a yi Allah wadai da kai taci darajan mahaifiyarta "naji plz abar maganar nan .."
A hankali cikin natsuwa fasinjojin dake cikin jirgi suke saukowa daya bayan daya ciki kuwa har da ahlina kisna mumy ce a gaba tana taka mattatakala hannunta rike da aryan har suka sauko farfajiyar gurin inda idanunta bai sauka akan kowa ba sai kan Aliyu shima da sauri ya tura wayar dake rike a hannunsa cikin aljihun wandonsa ya nufo inda take ya rungumeta ajikinsa "i really miss you mummuy ,itama rungumeshi tayi tare da sakin hannun aryan "i miss You too muradi , "sannu da zuwa mamana maganin kukana ."
" yauwa d'ana mai tausayina yau ina cike da farinciki ,"nima haka mamana "dady ......"..
aryan ya furta yana rike masa gefen riga a hankali ya saki mummy ya ?auki aryan ya rungumeshi "babana i miss you so much tare da kissing din goshinsa daya bayan daya ya rungume yaransa cikin tsananin farin ciki sannan ya rungume Samir "ai na ?auka ni baza'a min sannu da zuwan ba ? "ni na Isa bayan kai din na dabam ne kuma ajikin farko a zuciyata "zainab ya akayi ne me wannan dan'uwan nawa yake baki naga kinyi bulbul haka ?"
dariya suka sukayi gbdy suka jero har gurin mota nasir ya durkusa har kasa ya gaishe da mummuy cikin girmamawa ta amsa tana tambayarsa matarsa ."
Aliyu yasa hannu ya budewa mumy murfin Mota Yana tsaye ta shiga ta zauna tare dasu areef su kuma Samir da zainab suka shiga motar nasir suka dauki hanyar gida ,Hayaniyarsu ce ta fito da kisna da sauri biyu biyu ta dinga taka step tare da ihun murna ganin mahaifiyarta tana faman kiran sunanta mommy!mumy !! Oyoyo daidai tsakiyar parloun suka ha?e ta rungumeta tana sauke numfashi da ajiyar zuciyarta mumy ta daura hannunta a kanta tana shafawa cike da matsanancin tausayin yarinyarta wacce kallo ?aya tayi mata tasan tana cikin tsananin damuwa ,kusan minti biyar suna rungume da juna sannan Kisna ta zare jikinta ta durkusa har kasa ta gaishe daita tana murmushi ganinta mumy ta mikar daita ta sake rungumeta tsam ajikinta itama Kisna rungumeta tayi sosai ,mumy ta cigaba da shafa kanta zuwa bayanta " fatan na sameki lafiya diyata "?
"Lafiya qalau mommy "da kyau Allah yayi miki albarka "ameen mommy
fuskarta ?auke da matsananci farinciki ta sake rungume mahaifiyarta tana jin wani sanyin dadi yana ratsata "lallai uwa dabam ce arayuwar ya'ya bata qara sanin mahimancinta ba sai datayi nisa daita ,ita kuwa mommy tunda ta rungume diyarta dumin jikinta da yanayinta ya tabbatar mata da tana cikin tsananin damuwa ta zareta daga jikinta a daidai lokacin da hawaye ya cicciko a idanun Kisna tayi saurin zare jikinta ta rungume aunty Zainab "oyoyo aunty zee sannuku da zuwa kunzo lafiya ?"lafiya qalau auta mumy fatan kina lafiya "?"lafiya lau nake aunty zee .
mummy tayi shiru ta kasa zama sai kallon bayan kisna take tana son ta sake kallonta Dan ta karewa yanayinta kallon tsab , sai dai tana juyowa murmushi ta gani kwance akan fuskarta "mumy Ki zauna mana Aliyu ya fa?a yana soso keya , zama mommy tayi kamar yadda ya umarceta , dukkaninsu suka zauna aryan da areef suka zube a jikin mamansu suna zuba mata surutu "mumy shine kika gudu kika bar mu ko kullum sai ni da areef muyi kuka" ?
Ta Kallesu tausayin yaranta ya kamata , bata san sanda hawaye ya gangaro mata ba," ta bar su ne saboda mahaifinsu gashi bata tsinci komai a zamanta dashi ba sai tarin damuwa da bakinciki ".
"Allah sarki babana ban gudu na barku ba , na zo gurin dad dinku ne amman very son zamu kasance tare kunji yarana i love You so much do you love's me "?"yes mommy suka hada baki gurin furta mata haka sannan suka kwanta ajikinta , ta kai hannuwanta duka tana shafa kansu tare da manna musu kiss , sannan ta mike ta shiga Kitchen manya manyan kuloli ta shiga fitowa dashi tana ajiye wa a gabansu tare da plet tana fadar "ranki shi dade hajiya mommy ga abinci .
mommy tayi dariya tare da cewa "yau kuma har da ?arin girma na samu ? tayi maganar tana dariya suma dariya suka yi gaba-daya "ai dole mummy kin ma fi ranki shi dade din ai Samir ya janyo kuloli "bari muga irin abinci da dan'uwana ke ci ya narka kiba haka yayinda kanwata take ramewa....."
tsam Aliyu ya sha jinin jikinsa har kisna,Samir ya bude kula miyar stew Wanda yaji kayan kamshi da soyayyiyar naman kaza da kuma kamshin romon jelar sa dake tashi a cikin wata kular , sai wani plet da aka jera cake wanda yaji kayan hadi, ya saki murmushin jin dadi yana fadar "lallai dole danuwana ya dinga narka kiba har da wani fresh na musamman idan na soma cin abinci nan kar wanda ya rike min hannu dariya suka saka gabad'ayasu banda Aliyu dake wasa da yaransa kisna ta mike a ranta tace "dama yana wani cin abinci ne mutumin da sai akai ruwa rana yake ci shima yana ci yana zagin mutane ,
saman kujera da mumny take zaune ta zauna gefenta ta d'aura kanta a saman kafad'anta "mumumy me za'a zubo miki ko duk abinda na dafa zakici?Mummuy ta ?an kalleta "ai ban ga gurin cin abinci ba sai naji dalilin wannan ramar ? tayi maganar can kasa kasa ta yadda babu mai ji "gaskiya banji dadin ganin yadda kika dawo ba, kinki kwantar da hankalinki ko har yanzu zuciyarki na wani guri ko"?Tunda mumy ta soma magana qirjinta ke bugawa tayi saurin kawar da damuwarta ta mike dan bata son ta fahimci komai cikin sanyi jiki ta shiga zuba mata abinci ta mika mata sannan tai saving sauran har Aliyu bai ce komai ba ya amsa dan babu yadda zai yi ya soma ci har suka gama hankali mummy yaki kwanciya tana son Jin dalilin ramar Kisna ..
ha?a kuloli da plet plet din da suka yi amfani dashi ta bar gurin zuwa kitchen , bayan Wasu sakonnin ta dawo wanda zuwa lokacin tuni Samir da matarsa zainab da Aliyu da yaran sun fita zuwa gidan Samir dake cikin haraban gidan ,Kisna ta zauna kusa da mummy ta ?an kwanta a jikinta cikin shagwa'ba tace
"Mummy nah duk naga kinyi wani iri karki damu da ramata dan babu abinda ke damuna .. ....."
Mmn sudais
????????????
CUTAR DA KAI
????????
????????????
~TRUE LIFE STORY~
Free Page 9
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ?aya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...????
.....Shiru ne ya biyo baya , parlou'n ya ?auki shiru kamar babu mutane a cikinsa , yadda kisna bata sake cewa komai ba haka ma momy har tsawon minti goma sannan sautin muryar momy ta doki dodon kunneta, "dole zan damu da ramarki mamana ,ni dai fatana ki kwantar da hankalinki , ki kasance cikin farinciki , ki zauna da mijinki lafiya bana son rayuwarki tare da wani mutun bayan muradi a nan duniya saboda nagartarshi , gashi mutumin kirki, mai dattako wanda kowace uwa zata yi alfahari dashi a matsayinsa na surukinta ".
"haka ne mommy duk abinda kika fa?a akan shi gaskiya ne , duk inda ake neman mutumin kirki dole a ambaci shi , kisa a ranki a gidan ya aliyu zan k'arasa sauran rayuwata data saura bani da burin rayuwa da kowa a halin yanzu sai shi , tana gama fadar haka ta mike tsaye tare da kamo hannun mahaifiyarta "muje sama mumy an gyara miki daki".
"zan so na zauna a bangaren dadynku " no no mummy dan Allah ki zauna a nan nafi son na jiki a kusa dani ta karasa maganar cike da shagwa'ba ,momy tayi murmushi kawai batare da ta sake cewa komai ba saboda farincikin diyarta shine nata ,ta mike suka nufi sama madadin ta kai ta dakin da zata zauna kai tsaye d'akin baccinsu ta shiga daita ta zaunar daita akan kujera zata juya momy tayi saurin riko hannuwanta duka cikin nata tana sake kallon cikin kwayar idanunta tana sake karewa jikinta kallon kallo ,wuyanta duk kashi ,tayi wata irin ramar kamar bata cin abinci "ina son ganinki cikin farincikinki mamana sai dai ban ga alamun kina cikin kwanciyar hankali ba , kin rame sosai mamana ko baki da lafiya ne?" ko kuma akwai abinda ke damunki "?
Numfashi kisna ta sauke zuciyarta na wani irin rawa da tsinkewa Wanda kallo daya zaka mata ka fahimci tana cikin damuwa da kyar ta sanyawa jikinya jarumta tace "mommy na fa?a miki babu abinda ke damuna , ina cikin koshin lafiya, ina farinciki a gidan nan , bani da damuwar komai ,duk abinda nake so shi nake yi , shima ya Aliyu duk abinda ya gani zai siyo min, ga tsantsar kulawa da soyayyar da yake bani ,baya qaunar abinda zai nisantashi dani yana bani kulawa sosai ...."tayi maganar hawayen da take ?o?arin boyewa ya cika idanunta tayi saurin zare hannuwanta cikin na mumy ta mike ta juyawa momy baya dan bata son taga zubar hawayenta , ta k'arasa jikin wordrobe ta bude inda kayanta suke ta ciro dogayen riguna guda uku da nasir ya siyo musu ita da safiyya ta juyo a sukwane tana nunawa momy tana takowa zuwa gareta "momy kinga wad'an nan dogayen rigunan duk shi ya siya min ta d'aura akan cinyar mommy ita dai momy binta Kawai take da Idanunta da suka cika da ruwan hawaye ta sake juyawa ta d'auko agogo" wannan ma shi ya siyo min ta d'aura mata akan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 21