Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wannan abun ya razanar daké, na san za ki iya yin abin da ma yafi wanda aka saka ki, idan dai har kin sawa ranki zakiyi, za ki yi Saudat, please zo muje.” Saude dai ba ta tanka mata ba ta juya ta bi ' bayanta suka nufi wani sashi daban, ta tura wata '» kofa sai ga su sun fada wani dan falo irin na ' Sauden. ‘ Aunty ta bud‘e wata loka da ke jikin bango sai ga kayan kwalliya kamar su ci kansu, ta dauko leda ta dibar mata masu yawa, tun daga man shafawa, sabulan wanka, kayan kwalliya har da turarurmka, sannan ta bude wardrobe ta ciro dan qaramin hijabin nan mai tsayawa iya wuya wato himar kalar ja ta mika mata tana fadar “Ki yi sauri ki je ki gyara ki tafi, dan na san yanzu haka akwai abubuwa da dama da yake buqata.” Saude ta karBa ta fice jikinta amace. Sai data sake wani wankan sannan ta fito ta shafa mai a jikinta ta kawo wata ‘yar qaramar powder fara ta shafawa fuskana, ta sa man lice a bakinta, sannan ta mike ta mayar da kayan jikinta, ta dauki qaramin hijabin ta rufe kanta. Wani irin abu ya cunkushe mata zuciya, tunda take a duniya bata taba irin wannan shigar ba ace kana dan Musulmi amma ka flta a haka, kai duniya! Takaicin kanta ya kamata, k0 tsayawa ta dubi kanta ba ta iya ba ta dauki turare ta fesa guri uku kawai sannan ta fice zuciyarta na faman kai kawo. Tsoronta ya qara tsananta lokacin da ta iso bakin sashin nasa ta daure ta yi ta maza ta sa kai cikin falon cike da fargaba. Turus! Ta ja ta tsaya ‘yar sallamar da take shirin yi ta makale mata a makoshi, wani irin tsoro da fargaba mai tsanani suka dirar mata Kwance yake tsakiyar falon saman kafet ya yi daidai. daga shi sai gajeran wando ba k0 singlet jikinsa, ya yi matashi da hannayensa fuskarshi na kallon sama, idanuwan shi a lumshe suke kamar mai barci. Saude ta runtse: idanuwanta ba ’tana shirin ta juya da sauri ta-«koma sai kuma ta tuna Da maganar Asma da take fadi“Wallahi idan kika sake Yaqi amincewa dake a matsayin yar aikinsa sai kin fuskanci fushina. " [1/24, 9:31 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/24, 10:13 AM] A A Dboy: *YAR TALLA* *CHAPTER 16* Saude ta ja ta tsaya tare da juyowa , muryarta na rawa ta sake yin wata sallamar, Ahmad ya bude idanuwansa wadanda suka kada sukai jawur, yana kallonta, kallon da ke tabbatar da tsananin tsananta cikin idanuwansa ya sake she idanuwansa kafin ya soma magana tamkar wanda yake sanyin rada. “Ba cewa nayi kar ki bari in sake hada hanya da ke ba? Okay ba kiji ba kenan, shi ne ki ka dawo k0?” Muryar Saude na rawar disko ta ce hajia ce tace min Ba ta qarasa fadar abin da za ta ce ba ya zabura a Qufule yana fadar, “Wuce ki bar falon nan,‘idan kuwa ki ka bari raina ya baci za ki hadu da abin da baki yi tunani ba. Gate out! ” ‘Yan cikin Saude suka Kara Juyawa, wannan shi ne gaba kura baya hayaki, wasu irin hawaye suka biyo kuncinta ta durqusa a gabansa cikin kuka tana ‘ fadar, “Don Allah don Annabi ka‘yi min rai ka yi haquri wallahi idan na koma na ce mata ka kore ni kasheni za ta yi don Allah ka yi hakuri ” . Ahmad’ya tsaya yana kallonta tsawon lokaci yana jin tamkar ya shake ta saboda takaici, don a duniya idan akwai abin da ya tsana‘to bayan kuka Ne k0 cikin film baya Kaunar ya. ga ana kuka, ' Ya ja tsaki mts! Tare da fadar “Tashi na ji ya ishe ni haka.” Muryarta a raunane ta ce “Na gode. ”* Bai tanka mata ba ya juya ya koma kan kujera ya yi kwanciyarsa abinsa tsawon Iokaci babu wanda ya Tanka can dai Saude da ta lura idan za su kwana a haka bai damu ba sai ta mike ta dan matsa kusa da shi kadan ta durkusa tana fadar, ‘Ko kwai abin da ka ke buqata in kawo maka?” Ahmad ya dan tsura mata ido= kadan, kamar wadda ta zage shi sannan ya juya tare da kada mata yatsun hannun shi ba tare da ya yi‘ magana ba, zuciyar Saude ta Kara tsurewa, don ta lura mutumin ya tsane ta da wuya idan kuma zai bata mazaunin mai aikin nasa. Kwalla ta cika mata idanuwa cikin muryar kuka ta soma magana, “Don Allah to in kawo maka wani abu mai sanyi.” " ‘ “Na ce miki a’ a, a’a shin wai k0 dole ne?” Yanda yake mata maganar ya firgita ta, saura kadan da ta fadi saboda razana. hawayen da suka taru a kwarin idanuwanta suka samu damar biyo kuncinta. ' Ahmad ya ja wani gajeran tsaki yana fadar, “Oh! My God, jeki kawo mini koma meye zaki kawo, k0 baki Jiba?” Ya fada a harzuke Saude ta mike a razane ta nufi gurin firij din ta , bude, lemuka ne kale-kale sun fi kada ashirin jikinta sai rawa yake ta rasa wane za ta dauko masa, can idonta ya sauka kan fresh milk ta kwali, tasa hannu ta dauko masa tare da kofi na tankaran guda mai gindin turmi ta rufe firij din ta nufo inda yake. Ta durkusa a gabansa tasa hannu ta gage hawayen da ke zuba a idanuwanta sannan ta balle murfin ta tsiyaya masa fiye da rabin kofi din, ta miqa masa, ba musu ya sa hannu ya karba Saude ta sauke wata nannauyan ajiyar zuciya, wadda ta janyo hankalinn Dr. Ahmad ya dan zuba mata idanuwansa kadan sannan ya dauke kansa. Ta yunkura ta mike tana fadar, ‘Sai da safe.” K0 uffan baice mata ba har ta fice Kai tsaye dakinta ta nufa ta kwanta zuciyarta ta lula duniyar tunanin abin da ya faru dazu ya rinqa dawo mata ita kanta ta ba kanta tausayi dan zama tare da miskilin mutum irin wannan ba Karamin aiki ba ne, shin k0 yaci abincin ma ko k0 haka nan ya kwanta? Allahu ‘A'a lamu. Ta daga kanta tana kallon agogon dake manne a bangon dakin karfe goma da‘ yan mintina, ta qara ' juyawa sosai a kan gadon, dan to san saura ‘yan mintina lokacin shan coffee dinsa ya yi, yanzu dan kawai zai sha wani coffee har sai wani ya je ya hado masa saboda san kai kawai irin na masu kudi 1page is missing Saude ta zabura ta durgusa tana gaida shi, k0 inda take bai kalla ba ballantana ta sa ran zai amsa, don haka taja bakinta ta tsuke tana kakllonsa ya isa gaban firiji ya bude ya dauko robar ruwa guda, ya murde murfin ya daga sama yana kwararawa cikinsa ya sha ya kusan rabi sannan ya ajiye ya waigo da niyar wucewa. Saude ta yi saurin sunkuyar da kanta ta ci gaba da abin da take, don tsoron kar ya ‘ kama ta tana kallonsa. ' Bai kula ta kanta ba ya haye sama abinsa. Saude ta girgiza kai a zuciyarta tana mamakin miskilanci irin nasa, don har ma ya zarce matar tasa , ' tunda ita duk abin da kai za ta yi magana, amma shi sai dai ya kore ka. Ta girgiza kai ta ja gefen kafet ta zauna tana muzurai; , Da misalin Karfe goma saura minti biyar Ahmad ya sauko daga sama kamshin turarensa ya mamaye falon gaba daya, Saude ta dan dago a hankali ta saci kallonSa sanye yake da wani yadi mai laushin gaske sky blue, ya sha aiki da farin zare. Yadin mai Sharashara ne hakan ne yasa akan iya hango farar singlet dinsa da short nirker din da ke jikinsa, farar fatar . nan ta yi wani luwai-luwai kamar jikin Jariri. * * Ya ja ya zauna kan kujera da waya rike a 'kunnensa yana magana cikin harshen Turanci, Saude ta yunknra ta mike ta fita daga falon ta bi wata ‘yar kwana da ke gefe sai ga ta ta Bude qaton dakin dafa . abinci wanda ma‘aikata ke ciki, harsu uku duka mutum daya ne Bahaushiya a cikinsu. To su wai me yasa ba sa son daukar Musulmai zalla aiki ne? Ba ta da mai amsa mata wannan tambayan, don ‘ haka ta karb0 break din yallaBai din sannan ta fito. A bakin kofa su kai karo da Aunty ta zo daukar wa Hajiya nata suka gaisa, sannan ta wuce, ta nufi falon nasa. : : Yana zaune kamar yanda ta bar shi har yanzu bai gama wayar ba, Saude ta dora tiren kayan abincin saman dinning table sannan ta koma can gefe nesa da shi ta zauna tana jiransa ya gama wayar amma da alama bai da niyar gamawa har wani kashe murya yake yana zuba shagwaBa, sai. kace wani qaramin yaro, duk kunya ta ishe ta, ji take tamkar ta zuba da gudu, don duk da ba ta. san abinda yake cewa ba, ' amma zuciyarta ta ba ta da matarsa yake wayar Ashe dama yana dariya irin haka? Lallai k0 da wa yake wayar nan, to an jiKa ta a shanye Ba ta ankara ba tana duniyar tunani sai dai ta ji muryarsa na fadar, “Kawo abincin nan Saude ta zabura har tana neman faduwa ta mike, ta nufi dining din ta dauko kayan karyawar tazo ta gabansa ya nuna mata kan kafet din ta aje masa anan sannan ta koma ta zauna Ya watsa mata wani kalla mai, kama da harara kafin ya ce, “Waye kika ajiye ya yi serving din. " Saude ta waro ido tana kallonsa cike da razana don ita dai ba ta san abin da yace ba, ya ja tsaki tare da fadar, “Na ce waye zai zuzzuba abincin?” . Saude ta yi saurin matsowa tana fadar, “Yanzu zan zuba.” Ta dauki kofi ta zuzzuba kayan tea, sannan ta zuba ruwan ta cika kofin d taf-taf ta juya da cokali ta mika masa. Ahmad ya zuba mata dara-daran idanuwansa cike da takaici ya ce, “Yanzu duk wannan Waye zai shanye shi? Kin tattakura kin shaqare kofl da ruwan tea dan rashin hankali mts!’ Ya karBi shayin ya rage fiye da rabi a wani kofl din, sannan ya soma sha. Jikin Saude ya Kara yin sanyi, tana tsoron ta zuba masa abincin ya gwasale ta, muryarta a sanyaye ta‘ ce, “Abincin kamar yaya za a zuba?” Bai kalli inda take ba ma ballantana ta sa ran zai tanka mata, zuciyar ta ta Kara tsinkewa, ta yi ta maza ta dauki plate da cokali ta bubbude kulolin, soyayyar doya ce da miyar swse sai daya kular yam ball ne Wanda ya ji nama da kwai, sai dayar farfesun nama ,ne da dankalin turawa, wato~ papper chicking, sai gasashshen biredi an masa wani yanka mai kyau an dora saman plate, wato sandwich. Saude ta turo masa . plate din biredin, sannan ta zuba masa farfesun naman a plate din sai ta debi yam ball din ta zuba masa a gefen bredin, ta maida saman ta rufe. “Bai tanka mata ba ya rinqa cin abincinsa sannu a hankali har ya gama, sannan ya dago ya dube ta kamar wanda aka tilastawa sai ya kalle ta ya ce, “Tashi kawo mini morning fresh ‘Yan hanjin Saude suka duru ruwa, yau na shiga uku! Wani abu ne kuma haka? Yanda ya kafa mata idanuwa yasa a dole ta yunkura ta mike. To ina za ta dosa? ‘ Ta tsaya cikin falon tana faman diminiya, tadan juyo kadan ta ga idan yana kallonta su kai ido hudu, gaba daya ya tattara nutsuwarsa a kanta, ai kuWa take ta Kara tsurewa to k0 dai tsintsiya yake nufi, don ta lura da ya yarda wani dan qashi a kasa. ‘ Ta ja wata ajiyar zuciyar samun mafita, sannan ta dauko ‘yar tsintsiyar da take share-share da ita a falon ta nufo shi, ta durkusa tare da fadar, “Ga ta.” Haushi da takaici suka kashe Ahmad. ya watsa mata wani mugun kallo wanda yasa duk wata laka ta! jikinta ta mutu ya ja tsaki mts! Yana fadar. ‘ “Ke jakar ina Ce? Wannan ita ce morning fresh din? Idan ba ki sani ba ba za ki tambaya ba, sai kawai ki je ki ta shashanci, ki kawo mini tsintsiya inyi tsiyar me da ita?” Ya girgiza kai cike da takaici yana fadar, “Kai Allah dai ya wadaran dakikin mutum stuppid girl ni Fice ki bani wuri, na daina hada ido da ke, sakarya kawai.” Zuciyar Saude ta Kara karyewa idanuwanta suka ciko da hawaye muryarta na rawa tace, “Ka yi hakuri don Allah. ” Ya watsa mata idanuwansa tare da Jan wani dogon tsaki “Mts!” ‘ Saude ta yi saurin sunkuyar. da kanta Kasa, yana kallonta cikeda tsanarta ya ce, “Ki fadawa Madam, ina da meeting yau kar ta ga ban sa an kawo mata sakon nan ba sai, zuwa gobe komai kr nan mu hadu ta network.” Yana gama fada ya mike ya sa kai ya fice ya bar Saude a tsaye, wasu siraran hawaye suka biyo kuncinta tadurkushe a gun. Wayyo ni Allah na ya. Ubangiji ga Saude na san baka mance da ita, ba ya Allah Ubangiji ka cire ni daga' wannan rayuwar qangin“ bautar da rashin galihu.’ A hankali ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya, sai da ta yi mai 'isarta bata da mai lallashinta sannan ta share ’hawayenta. Ta diba tiren abincin dake gabanta t duba ba wani da yawa yaciba sannan itama ta zauna ci tsakura kawai tayi saboda yanda take jin zuciyarta babu dadi. Tana gamawa ta mike ta fita da kwanukan sannan ta dawo ta gyara falon tamkar ba a taba shigowa ciki Ba sai da ta gyara ko’ina ta yi turaren Wuta ta sassaki labulayen tagogin ta qara gudun AC ” a koina sannan ta rurrufo falukan ta fice, ta nufi can Bangaren. , Babu kowa a falon qasan sai Aunty tana turaren wuta, ta gaishe ta cike da girmamawa, Aunty ta bi ta da. kallo tamkar mai karantar, wani abu. Muryar Saude a sanyaye ta ce “YallaBa‘i ya ce“A fadawa Madam ba zai dawo ba sai gobe Aunty ta ce, “To ki hau sama ki fadawa Hajiyar da kanki.” Saude ta dan yi jim cike da tsoro. Aunty ta katse mata tunanin da fadar, “Kije mana Saudat tunanin me ki keyi haka?” Saude ta girgiza kai sannan ta wuce ba tare da ta ce uffan ba, ta tattaka matattakalar benen ta haye sama. A karo na farko kenan da ta fara hawa saman. ‘ Haka kawai ta tsinci gabanta na faman faduwa,_ wani irin tsoro mai tsanani ya dirar mata, ta rinqa bin falon da kallo aljannar duniya, lallai ba banza ba masu kudi ke mantawa da ni’imar da Ubangiji ya yi masu ba. Muryarta na faman sarkewa ta yi sallama‘ har sau biyu. Babu wanda ya amsa ga shi kuma tana jiyo hayaniyar mutane a falon da ke gefe, don haka ta Kara matsawa tare da yin wata sallamar. Tun kafin ta karasa rufe bakinta ta ji an watso mata wata dunkulalliyar ashariya cikin ta ya duri ruwa, kafin ta yi tunanin juyawa ta ga Asma gabanta, tun kafin ta karasa tantance ta, ta ji saukar wani mahaukacin mari a kuncinta gefen dama da hagu. Saude ta durkusa ta dafe kuncin lokacin da ta ga wata wuta ta gifta mata a idanuwa, cikin takaici Asma ke fadar, “You are very" stupid, ke jakar ina ce? Da ina meeting za ki shigo ki distubing dina banza sakarai shashasha, uwar me aka yi ne da ta sa ki ka shigo mini har falo?” Saude ta durkusar da kanta qasa daga duqen da take, hawaye suka soma zarya a kuncinta, cikin muryar kuka ta ce “Ki yi haquri dama Yallabai ne ya aiko ni, ya ce ya yi tafiya sai zuwa gobe da yamma za.. ‘So What! Na ce sai me? Da ya aiko ki sai ya ce ki iske ni duk inda nake ki fada mini, iye?’ Ta ja wani dogon tsaki mts! Kafin ta ce, “Da alla gate out on my parlour’ Ta sake kwatsa mata tsawa, “I say gate out k0 ba kya jine?” saude ta zabura ta mike ta bi hanyar da take nuna mata jikinta na rawa, Asma ta sake jan wani tsaki tana fadar, ‘Stupld kawai.’ Sannan ta juya ta koma ciki abin ta. Saude na fita kai tsaye bangarenta ta fada kan gado ta fasheda Wani irin kuka mai cin zuciya wayyo Allah yau ta ga ta kanta, wannan wace irin rayuwa ce ta samu kanta a ciki me cike da qaskanci da wulaqanci ni Saude? Kuka take ‘sosai bata da mai lallashinta. Rayuwa kenan. ,,,,,,,,,,,, ,,,,,,,,,,,,,, Haka rayuwar Saude ta ci gaba da tafiya cikin kaskanci da rashin galihu, kullum tana cikin bauta, ita da bayi ba su da bambanci, ’sauqin‘ ta ma tun a gida ta riga ta saba da wahala. Yanzu haka rakube take gefen kujera bayan ta gama. gyara falon ta gaji, ta rakube gefe tana kallon tashar Saudiyya, wani shiri da suke yi duk karfe biyar na yamma. ‘ Dr. Ahmad ya sauko daga sama yana sanye da kayan wasanni na kwallo, gajeran wando da singleti sai takalmin ‘yan kwallo, Saude ta saci kallon shi kadan. Kayan sun masa kyau sai ka ce irin turawan , nan da ke buga wasan kwallon kafa, ba tare da ya kalli inda take ba ya wuce abinsa yana fadar. “Ki biyo ni da robar ruwa mai sanyi.” Saude ta zabura ta mike ta nufl wurin kantar da -ake ajiye lemoka ta bude ta Ciro robar Faro guda kwalin lemo guda tare da kofi guda daya tabi bayansa A qaton filin wasan‘ dake gefen lambun gidanta“ same shi yana ta faman tika kwallo shi daya, duk ya hada gumi, Saude ta rakube gefe rungume da tirenta hannu tana kallon ikon Allah, zuciyarta na _ raya mata wasu abubuwa da dama cike tàke da mamakin Yallabai din tana mamakin yadda duk abin da ya yi sai ya yi masa kyau, tunda take bata taba ganin muninsa ba, kullum ma kamar~kara masa kyau ake. Shin dama akwai mutum irin haka? Ba ta ankara ba sai dai ta jiyo sautin muryarsa na fadar. “Wai ke k0 kurma ce ne?’ Saude ta zabura da saurinta ta nufe shi jikinta na rawa, ta durkusa‘ gabansa cikin rawar murya tana ~ fadar, “Ga ni.” Ya ja tsaki cike da takaici kafin ya ce, “Hankalin ki yana ina ne lokacin da na wage murya nake ta kwalo miki kira? Me ki ke kallo ne a jikina wanda har ya dauke miki hankali? Tunanin me ki ke’?” ‘ ' Ya sake jan wani dogon tsaki ya gif‘ta ta ya‘wuce yana sharce gumin goshinsa da hannunsa, ya bar ta a duke da tiren lemuka tana faman rarraba idanuwa, tsoro ya kama ta dan ba ta san irin hukuncin da zai yanke mata ba. Haka ta daure ta dake zuciyarta ta bi bayansa, tsaye yake gaban na’urar sanyaya ruwa, ya tara kofinsa yana zubowa, Saude ta durkusa. gabansa muryarta a raunane ta ce, “Don Allah don Annabi YallaBai ka yi hakuri, insha Allahu na yi maka alkawarin ba zan Kara ba.” nazarin wani abu a fuskarta, ba tare da yace uffan ba ya dauki ruwansa ya durawa cikinsa ya ajiye kofi din ya yi mata nuni da hannu alamar ta wuce kawai, ya yi gaba abinsa ya haye sama. Saude ta girgiza kai zuciyarta na cike da mamakin miskilanci irin na dan adam. Duniya kenan. ‘ Da misalin Karfe tara na safe Saude ta kammala ayyukanta gaba daya, ta kunna turarukan wuta a ko’ina sannan ta dauko room freshner ta faffesawa labulayen falukan da kujerun‘ Dr. Ahmad ya shigo falon daga shi sai dan qaramin gajeran wando duk ya hada gumi, da alama daga motsa jiki yake. Kai tsaye ya wuce ya tsiyaya ruwa a kofl ya sha kusan kofi biyu, sannan ya wuce abin sa. Har ya taka step din da zai kai ka falon shi na sama ya waigo ya kalli Saude fuskarsa ba yabo ba fallasa yace “Kije ki sanar da kuku yau ina da baqi da misalin qarfe sha daya na safiyar nan ya tanadi duk abin da ya san za a iya bukata." Yana gama fada ya yi gaba ba tare da ya tsaya ya saurari amsawarta ba. Saude ta maida kayan sannan ta fice da sauri dan isar da sakon da aka aike ta. Tana dawowa ta same shi tsaye a falon sanye da farar jallabiya a jikinsa yana waya ta ja gefe ta zauna. Ya‘yi wayarsa ya gama sannan ya matso inda ~ take ya‘ mika mata wani key yana fadar, “Karbi wannan key din ki bude wancan falon ki gyara anan zan sauke bakin nawa.” Saude tasa hannu biyu ta karba, ya juya ya koma sama, ita kuma ta mike ta nufi kofar: da niyyar budewa, amma abun ya faskara, saboda gaba dayan kofofin gidan odar waje ne in ba wanda ya saba ba. ’don ko wancan karan da za ta shigo falon nasa ’anty ce ta“ bude mata, Ta dan nutsu tana tunanin * .yanda Suka bude a wancan karon', cikin ikon Allah ta ~samu ta bude kofar sannan ta shiga. Katafaren falo ne dogo mai girma wanda ya ji kujerun silba masu kyau sunkai ashirin sun sa wani dogon char a tsakiya. Kai da ganin haduwarsu ka «san odar waje ne. Ga falon ya ji wani lallausan kafet ya mamaye gaba dayan falon wanda aka Kawata shi Dukda falon ba wani datti ya yi ba, amma haka Saude ta gyara shi sosai ta goge ko’ina da ina ,hatta jikin bangwaye wadanda gaba dayansu “tayil ne sai da ta goge, gaskiya ta sha wahala sosai harta samu ta gama, ta zauna ta turare falon da turaren wuta ta feshe shi da air frshner masu kamshin. gaske ta kunna A.C din falon, gaba daya falon ya shiga fitar da wani sanyayyan kamshi mai ni’ima. . ” Saude ta juyo da niyar tifowa shi kuma ya shigo ta yi saurin matsawa ta zube Kasa tana'fadar, “Sannu da fitowa YallaBai an kammala.” Bai tanka mata ba ya Wuce ta yana bin falon da kallo da alama shi ma yanda falon ya dauki qamshi ya burge sa, shi yana kallon falon ita. kuma tana kallonsa, tunda take da shi ba ta taBa ganin yasa qananan kaya ba sai yau, dan sai ta gama yafi mata kyau fiye da kullum. Ganin zai juyo sai ta yi saurin dauke idanuwanta tamike tayi gaba, bataredata bariya kamata tana satar kallonsa ba. Tana fitowa ta ja gefe ta zauna a falon tana kallonsa ya fito yana wani takawa tamkar wanda ba ya san taka qasa. Ba tare da ya qaraso inda take ba ya ja. ya tsaya hannayensa zube cikin aljihu, cikin sanyayyar muryarsa ya ce, “Akwai katon din lemma da , robobin ruwa da aka kawo suna cikin‘ kanta, za mu shiga meeting karfe sha daya, kin ga yanzu Saura minti goma ina so sha daya da rabi ki dauko lemu da ,ruwa kizo ki jajjera a gaban kowacce kujera, lemo daya robar ruwa guda. Akwai meat pie an nadeshi guda biyu cikin tissue sai ki ajiyewa kowacce kujera guda'a gaban teburinta. Ina fatan kin gane?” ‘ Saude. Ta daga masa kai alamar eh ya ce “Okey, kuma idan za ki shiga ban da surutu, ban ce ki yi wa kowa magana ba da akwai kayan da zaki karba ki canza.’ Oya ban san wasting din time je ki.” ‘ ‘ Saude ta lallaBa ta mike ta fice abin ta tana jinjina girman wadannan bakin a wurinsa. Tana shiga'Aunty ta miko mata leda ta karba ta nufi ciki, ta watso ruwa ta flto. A tsaitsaye ta shirya duk da yanzu ta dan nutsu ta shafa hoda da dan mai ‘a labbanta, ta sawa idanuwanta kwalli, tunda ta lura bakin kunya ne za a yi, ta zazzage kayan daga ledar Suit ne irin na jikinta, amma na yanzu wando ne da siket ba, kuma bakake neba sai rigar.cikin ce mai kalar jini,‘ harda belt irin ta mata. Mamaki ya. kama Saude shin k0 sun manta ita diyar Musulmai ce ba arniya ba? Taja ta zauna gefen gadon tana mamakin yanda za ta ratsa mutanen nan da wadannan kayan, ta dafe kai tana jin tamkar ta zabga da gudu. Bugun agogon dakin yasa ta yi saurin dago kai qarfe sha daya daidai ta buga, Saude ta yi saurin miqewa ta saka kayan wanda suka zauna mata a jiki cif da cif tamkar dama an auna ta, ta saka bakin takalmin kayan sawuciki bakake marasa tudu Ta janyo karamar himarta ta saka, wadda take ganin ta yi mata qankanta nesa ba kusa ba, bayan da ta Karasa ta fice da hanzarinta, tana faman rawar jiki, sai kace angon kare Karfe sha daya da rabi daidai ta dauki katon din lemo guda da katan din faro tan nufi falon taron wanda take jiyo sautin magana sama-sama a yi da Hausa a yi da Turanci. Saude na shiga ta ji tamkar ta zabga da gudu, saboda yanda ta ga mutane sun kai ashirin Turawa bakar fata, shi kuwa uban gayyar yana zaune a kujerar da ke tsakiyarsu, da abun magana a gefen teburinsa, tsoro ya kama ta abin ka da bagidajen mutum ta samu ta yi ta maza, ta shiga zabga sallama, babu wanda ya amsa a cikinsu, mamaki ya kama ta to su kuma wadannan wane irin mutanene da ba su amsa sallama? Ta sa kai ta shiga tana faman muzurai kamar wata marar gaskiya. ‘ Ta durkusa “Ina kwananku?" Babu wanda ya . kalli inda take ma balle ya san abin da‘ take hankalinsu na kan jawabin Dr., wani irin abu ya yi wa Saude tsaye a Kahon zuciya, don ita a ganinta su ma sun yi niyar ci mata fuska ne. Don haka ta shiga jera ruwa da lemon kamar yanda ya fada mata, ta koma ta Kara dauko wasu sannan ta qarasa jerawa ta koma ta dauko meat pie din su ma ta jejjera. Tana gamawa ta tsaya gaban Dr. wanda ke dan rubuce‘ rubuce a saman wani Karamin littafl, sannan ta dan rissina. YallaBai a kawo maka abincin ka nan ko sai ka fito zakaci Wani irin kunya da haushi da takaici suka taruma Dr Ahmad ya ji tamkar qasa ta tsage ya shiga ciki. Jin ya yi. shiru yasa Saude tunanin k0 bai ji bane ta sake maimaitawa. “Yallabai nan za a kawo ma abincin ko,,,,,,,, Tunkafin ta karasa rufe

Chapter 9 of 26