Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zauna a saman kafet. Dr. Ya wurgar da jaridar kan kujera tare da gyara zama ~sosai ya harde yatsun hannunsa guri guda sannan ya kira sunanta. ‘ “Saudat, kiyi hakuri da takura ki da nake ki daure ki ba ni labarin ki ina san in ji labarin ki na damu da in san wace ce ke kuma me ye dalilin kawo ki aikatau maimakon a inganta rayuwarki da ilimi k0 dan ke ma ki amfanar da wasu a gaba?” Saude ta yi shiru tana tunanin dan abin data sani a cikin rayuwarta, idonta ya ciko da kwalla-ta dago tana kallon shi da sarqaqkiyar muryarta ta ce “YallaBai babu komai a cikin rayuwaba sai duhu, . babu abu guda na haske a cikinta, idan ma na samu to ya suBuce mini. ban san komai a cikin rayuwata ba sai wahala da. Qaskanci, haka rayuwar tawa ke tafiya... ‘ Kukan da take riqewa ya soma kwace mata, ta sa hannu tana goge hawayen kafin ta ci gaba ‘ “Ni dai nasan ance an haifeni ne a gafin Katsina, kuma na bude idona a cikinta, don haka na ci gaba da rayuwa a yanda tazo mini a ciki, "tunda nayi wayo na ganni a: gabana Yayana Rabi’u sai mahaifina Malam Bala, sai kishiyar mahaifiyata Inna Laure da yarta iKilima wadda ake ce mata ‘Yar Baba.’ » A nan ta Iabarta masa gaba dayan labarin rayuwarta har ya zuwa yanzu. Tana gamawa ta kifa kanta a saman cinyarta tana kuka. Tausayinta ya qara kama Dr Ahmad wanda yake jin tamkar ya". zubar mata da hawaye, ya tausayawa halin da ta ’ tsinci rayuwarta tun tana yar karamarta har girma ta mallaki hankalinta, amma Inna Laure ba za ta bar ta haka ba wannan wace irin macece? ‘ ; Ya kira sunan ta cike da damuwa ya ce.“Ki yi hakuri Saudat insha Allahu sai kin yi,alfahari da rayuwarki ni zan maye miki gurbin Yaya Rabi’u da kuma Hamid in dai ina numfashi. Saudat sai kin yi ‘ dariya da farin ciki kamar kowace mace, ki kwantar”da hankalin ki ki daina kuka haka kinji?” ‘ _ Kai kawai ta daga masa alamar eh ya zaro ~ hankicif cikin aljihunsa ya mika mata ta karBa ta’ share hawayenta sannan ta mika masa ya karba kafin yace, “Yanzu ki tafi kije Ki kwanta daga masa alamar eh? Ya ce to shi kenan,‘kidab bani lokaci zan danyi tunani a kan matsalarki kafin. in “ samar miki mafita da fatan‘dai ba zaki yi fushi da; Duk abinda rayuwa ta sake baki ba zaki karba da hannu biyu Saude ta daga masa kai alamar eh yace to allah ya kaimu Jin yayi shiru yasa ta miqe ta nufi hanyar fita har takai bakin korar taji ya kira sunanta ta waigo tana kallonsa yace ki kawomin coffe yau da daddare kai kawai ta daga masa ta juya ta fice abinta koda ta koma bangarenta ruwa kawai ta watsa ta koma ta kwanta a binta wani barci ya dauketa ba ita ta farkaba saida wayarta ta dameta da qara tasa hannu ta dauka cikin magagin barci jin muryar hamid yasata saurin watstsakewa daga baccin suka shiga hira sunfi awa biyu a haka sannan sukai sallama da niyyar zai qara kira zuwa anjima misalin qarfe goma daidai saude ta fito daga bangarenta ta fita kai tsaye kichin ta nufa ta dauko flasks din coffe da qananun kofinan da yakesha dasu ta nufi bangarensa dasu saidai tun kafin ta qarisa ta hango bangaren nasa dun dum babu alamar hasken wuta tsoro ya kamata gashi bata taho da wayartaba ballentana ta haska kuma babu damar ta koma Wayyo allah taji tamkar ta fashe da kuka Taja ta tsaya cak tana tunanin abinyi tun kafin ta Qarasa nazarin taji wani haske mai Karfi ya taso da saukar ruwan sama mai Karfi ai bata san lokacin data kwasa da gudu ba ta yi Bangaren nasa, ba ga shi duk ta jike Tamkar daga sama ta ji ta yi tuntuBe da wani abu ta fasa wata uwar qara ta saki kayan ta kwasa a guje, karaf sukai kicibis ta da mutum, ta sake kwala wani qara mai qarfi cikin dabara ya rungume ta sosai a jikinsa yasa hannu ya kunna wutar falon. Amma har a lokacin ‘ ihu take tana, zullon kwacewa, hannu yasa ya tallabo qeyarta ya juyo da fuskarta saitin tasa su kai ido hudu. Sai Alokacin ta tsaya da ihun ta saki wata _ . ' nannauyar ajiyar zuciya cikin muryar kuka ta ce ‘Wallahi ka tsorata ni na zata, na zata... ’sai kuma tayi Shiru Yanda take maganar a shagWaBe ya barge shi har bai san lakacin da ya saki wani murmushi ba yasa dan yatsunsa ya lakace mata hanci yan fadar, . “You ar so beautiful Ya lumshe idanuwansa tare da mata wani murmushi,wadda ta tsaya iya makoshinsa kawai ' Sai a lokacin Saude ta lura da irin rikon da ya yi mata ta yi saurin zame jikinta da na shi a kunya ce saboda yanda ruwan. ya jika kayanta duk suka mammanne a jikinta tamkar ba ta sa komai ba ta juya da gudunta ta bar falon tana ji yana kiranta amma ba ta tsaya ba, haka ta koma sashin nata cikin ruwan. ' Tana shiga ta hada kanta da bangon falon tana jin tamkar qasa ta tsage ta shige ciki, saboda kunya da nauyi. Ai k0 ba za ta sake yarda su hadu ,ba duk rintsi kai dole ma in bar gidan. nan, wannan abun " kunya har ina, musamman idan‘ matar gidan ta samu labari ai ita ta san ta kade har ganyen ta. Kunya ta isheta tarinqa jin tamkar tarusheda kuka. Ta samu ta yi ta maza ta cire kayan ta dauko tsohon zaninta ta yi daurin Kirji da shi ta haye kan ‘ gadonta ta ja bargo ta kwanta. Amma sai me? Da ta rufe ido sai ta ga tamkar ga Dr. Ahmad nan zai rungume ta, ta zabura ta tashi zaune tana muzurai, ga qamshin turarensa da ya mamaye ta, ta yi wani gajeran murmushi tare da komawa ta ‘kwanta: ta runtse idanuwanta a haka bacci mai nauyi ya dauke ta. Washe gari tunda ta farka take zaune tana san zuwa wurin aikin nata, amma kunya ta hana ta, ji ‘ take ba za ta iya sake hada ido da shi ba, don haka ta gidan. Ita kanta ba ta san ta dan lokaci ba sai da ta soma jin cikinta na kukan yunwa, ta daga kanta ta kalli agogo. Sha daya da mintina, tana shirin tashi zaune ta ji an turo Kofa an shigo. Ta yi saurin tashi tana fadar, “Sannu Aunty.". Ta amsa da “Yauwa Saudat laflyadai ki kek0?” Saude ta ce “To da sauqi dai kaina neke dan ”ciwo.” ‘ . Ta ce, ‘Ayya, Allah Sarki kije Hajiya na neman ki tana falo.” Gaban Saude ya yi wata mummunar faduwa, ta ce, ‘Lafiya dai k0 Aunty? Allah yasa ba wani laifl na yi ba. ‘ Aunty ta ce “To laflya, YallaBai ne ya aiko kiranki.’ _ Hankalin Saude ya Kara tashi alamun tsoro ya . bayyana karara a fuskarta, ta mike jiki amace tana fadar, “Ga ni nan zuwa.” Cikin sanyin jiki ta canza kayan jikinta sannan ta fito zuciyarta na faman bugun dardari. harta qarasa .falon ta hango’Asma, tsaye riqe da Kugu, tana sanye da wasu riga‘da siket sari tare da 'mayafinsu tamkar wata .Ba’indiya, takalmin nan mai shegen tsini a qafarta. A danyi nesa da ita Saude ta tsaye ta durkusa tare ‘ da fadar, ‘Ina kwana Haj iya.” . Asma ta watso mata wani razanannan kallo kafin ta ce ‘Shut up ke nan har marar kunya ce wace ce ke? Uban waye uban ki a garin nan da har za kiqi zuwa aiki saboda jin dadi har Dr. ya aiko kiran ki, me ki ke ji da shi a cikin gidan nan? Me ki ka taka'? , Banza sakarya jaka‘ yar qauye. Yau k0 rashin lafiya ki ke dole za ki sanar in ba daibakisan inda kankiyake ba, tunda an ajiye miki wayar tarho da za ki iya kira da ita ki sanar, amma ke isasshiya kin yi shiru abin ki wato idan ana so a neme kito ki -sani wannan shi ne laifinki na biyu cikin manyan laifukan da ki ka aikata a gidan nan duk ran daki kikai na uku,kisani aranar”zakikarbi takardar sallamar ki kinji na fada miki” Tana gama fada ta juya ta haye sama a zafafe Jikin Saude ya yi sanyi matuqa, ta lallaba ta mike ta fice zuciyarta a cunkushe da baKin cikin yanda aka wulaqanta ta ba tare da an saurari uzurinta ba. Rayuwa kenan , Haka ta sa kai ta shiga falon tare da sallamar’ta, tsaye yake tsakiyar falon ya goya hannayensa a baya yana jin sallamarta ya yi saurin waigowa ya nufo ta da hanzarinsa Lafiya Saudat me ya same ki? Ba dai ruwan jiya , neya saki zazzaBi ba?” Saude ta girgiza kai alamar a’ a, sannan ta durkusa tana gaishe shi, bai iya amsawa ba ‘ ya sake jefo mata wata tambayar ‘Ban yarda ba Saudat idan lafiyarki qalau me yasa yau ba ki zoba?" Saudat ta Kara dukar da kanta qasa tare da fadar, ‘kaina ne yake ciwo kadan shi ya sanya.’ Dr. ya ce ni dai na sani, :nasan baki da da lfy Saudat bari in kira likita ya duba ki, kin ci abinci ' ‘ kuwa? . Da sauri ta ce ai na warke. Dr ya. girgiza mata kai a’a Saudat ban san wasa da lafiya, taso ki ci abincin kafin yaz0. Ganin yana shirin riko hannunta yasa tayi saurin tashi da kanta ta bi shi ya nuna mata tsakiyar kafet ta' zauna sannan ya nufi dining ya dauko kayan abincin ya kawo mata, yau da kan shi ya zuzzuba mata ya tura mata a gabanta tare da fadar. , ‘Don Allah ki daure ki ci.” Kai kawai ta daga masa, sannan ya wuce ya dauki wayarsa ya kira likitansa. Yana cikin wayar ne Asma ta sawo kai falon tana wani taku sai ka ce wadda take filin. gasar iya taflya, Dr. ya zuba mata idanuwansa cike da tuhuma. ‘ Karaf idonta ya sauka kan Saude wadda tuni hanjin cikinta ya shiga juyawa saboda tsananin firgita da tashin hankali, Asma ta ja ta tsaya tana ,fadar. “Me nake gani haka Dr? ‘Yar aikin ce kecin abinci a faod flask dinka, kam babban ....... ’ Kai jama,a akwai rikici fa sai kunjini agaba donjin yaddah zataci gaba da kayawa naku har kullum admin Dboy🤔 [1/25, 10:39 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/27, 10:11 AM] A A Dboy: *YAR TALLA* *CHAPTER 19* “Me nake gani haka Dr? ‘Yar aikin ce ke cin abinci a food flask dinka, kam babban ....... ’ Ya watsa mata wani kallo lokacin da ya kashe wayar ya ce “To k0 rai ya yi baki ne? Ai dai anawa take ci ba a baki ba k0? Ya yi mata tambayar cike da ‘ isa da gadara. _ “ Asma ta qara shaqa kafin ta ce ‘Hmm! Dr. kenan amma dai .ka san wannan ba qaramin kaskanci bane da zubdawa kai girma ka yi bak0? A. Zo a iske yar aikin ka na cin abinci a kwanan ka, ‘yar aikin ma ‘yar Kauye, jaka dakikiya, wadda talauci ya yi masu daurin ..... Dr. yayi saurin daga mata hannu ‘ya isa haka Asma, kin sanni sarai ban san cin fuska don Allah tunda ban aika miki da katin gayyata ba ki bar nan, banasan ciwon kai.’ ' Takaici ya kashe Asma, ta matsa daf da shi tare da sassauta mur'ya ta ce ‘Yanzu Dr saboda ‘yar aikin ka ka ke cimin fuska haka?” ‘ Ya ce ‘Amma kin sani Sarai ba a gaya mini yanda zan yi ko?’ Haushi ya kama ta ta juya a zafafe ta bar masa falon, ya taBe baki ya juya wurin Saude wadda “ lomar abinci ta yi wa tsaye a maqogaro tun dazu ta gaza hadiyewa, saboda tsabar firgici da tsoratar da ta Dr. ya zauna bakin kujerar dake fuskantar ta yana fadar. “Ki nutsu ki ci abincin ki sosai ga likita nan zuwa.’ Hawayen da suka taru a kwarin idanuwan ta suka gangaro cikin kuka ta ce, ‘Wayyo Allah na ka ja mini Allah kadai ya san abin da za ta yi mini yau na banu na lalace! ’ Dr. yace ‘Kuka kuma Saudat? Yanzu nan har an yi abin kuka? Lallai ashe kina da kukan jini nan gaba. ’ Saude ta Kara rushewa da kuka, ‘Wallahi gida zan tafi” Dariya ta kama Dr. ya ce, ‘Ashe matsoraciya ceke lallai Saudat na tabbata da Asma ta ji haushin ki da k0 sama da qasa za ta hade anan ba za ta kyale ki ba, ta riga ta san halina ne sarai don haka ba ta damu da ke ba ta kaina za ta dauki matakin don haka ki ma kwantar da hankalin ki ki ci abincin ki ’ Saude ta ture abincin tare da fadar, ‘Na qoshi.’ “Me? Ai wannan ne baki isa ba k0 ki dauka ki cinyc shi ko yanzun nan in kira ta ince kin cetazo ta kwashe kwanukan kin gama.’ Saudc ta yi saurin waro ido waje tare da janyo abincin da saurinta ta ci gaba da ci, ya yi dariya a , zuciyarsa sosai ya ce matsoraciya. Tun kafin ta gama cin abincin likitan yazo ya duba ta sosai tare da rubuta mata wasu magunguna, ya kira direba yasa ya je ya siyo mata su, ya dinga lallashinta yana rokon ta a kan ta rinka shan magungunan, sannan ya ba ta ta tafi Cikin tsoro ta shiga sashin nasu don gani take Asma na nan na jiranta. ' . Tana shiga sashinta ta maida qofa ta rufe ta ajiye magungunan ta haye kan gado ta janyo wayarta da .taketa faman ruri tun dazu ta ci gaba da wayarta. Washe gari da yamma tana zaune a bangaren Dr. tana aiki, zuciyarta sai faman sake-saken neman mafita take saboda wayar da su kai da Hamid jiya da daddare Dr. ya sauko daga samansa yana sanye. da qananan kaya irin na hutawar turawa, ya tsaya daga gefen kujera yana kallon Saude wadda ke durkushe tana 'goge goge ‘ . Jikinta ya ba ta tamkar ana kallonta, don haka ta yi ‘saurin waiwayawa, tsaye ta gan shi a gabanta ya harde hannuwansa a kirji tamkarmai nazarin wani abu. Saude ta yi saurin durkushewa tana masa sannu da fltowa, bai amsa mata. ’ba‘ sai ma ya sake gyara tsayuwarsa. “Me yasa baki san hutawa?” Saude ta dan kalle shi kadan kafin ta ce ‘Ai aikina ne shi yasa.’ Dr. yadan dauke kai kafin yace, ‘Ai kin kusa barinsa, saki wannan aikin ma taho mu fita mu sha iska.” Bai jira abin da za ta ce ba ya yi gaba abinsa, Saude ta raka shi da idanuwanta. To me yake nufi da ita? Ba dai korarta za su yi ba? Da sauri ta zabura ta bi bayansa. . Hadaddan wurinn shakatawa ne wanda aka kashewa dubban nerori wurin Kawata shi, don an zuba abubuwan ban sha’awa da debe kewa. Saude ta . koma jikin wani dodon roba, tana kallon Dr. wanda ke wasa da dan biri, can ya dago ya yafito ta da hannu alamar ta zo duk da tsoron da ya cika mata zuciya haka ta dake ta tafi inda yake, ta tsaya daga gefe tana kallon su, ba ta ankara ba ta ji ya fizgo hannunta ya hada da na birin, yana wa birin magana cikin harshen turanci. Mutuwar tsaye ta yi don tana bala’in tsoron sa sosai, don ma yana dan Karami, sai ta ga ya ’fadi' Kasa alarnar gaisuwa. Dr. ya yi dariya yana kallonta ya ce “Ana gaishe kifa?” Kallonsu kawai take bata ‘ iya yin magana ba, birin ya mike yana ta faman zazzagaya ta yana tsalle-tsallen murna. ' , Dr. ya janyo hannunta suka nufi wani.‘ qaton lilo na roba mai matattakala ya dan kalle ta da murmushi a fuskarsa ya ce “In hau za ki jujjuya ni’?’ ‘Duk da haushin riKon da ya yi mata ya kama ta sai da ta yi dariya saboda yanda ya yi maganar. Ya ce, ‘Okoy, dariya ma na baki to bari in dora ki in jujjuya ki.’ Tun kafin ta yi wani yunkuri ta ji ya sure ta ok ya dora saman lilon. Saude ta fasa wata uwar kara saboda razana, don ita gaba daya ma lilon tsoron shi take yi, dariya ta bawa Dr. sosai na kauyancin nata, don haka yana dariya yana jujjuyawa da ita, mutuwar zaune ta yi ta . runtse idanuwanta tana sauraren ikon Allah, shi kuwa dariya kawai yake mata, yana zolayarta ganin ba shi .da niyar daina juya ta yasa ta bude idanuwanta tana shirin kuka, ta hau rokonsa. ‘Don Allah don Annabi ka sauko da ni.’ Dr. ya tsaya da lilan ya matsa yana fadar, ‘To sauko tunda ba kya so.’ Saude ta waro idanuwa don ta san ko da kudi aka bata bazata iya saukowa ba, ya yi murmushi tare da mika mata hannunsa ta rike sannan ya sauko da ita, yana mata dariya yace matsoraciya duba ki ga aku na .kallon ki. ’ Saude ta yi saurin juyawa, caraf ya riKo hannunta ya ja ta da saurinsa. Haushi ya kama ta yanda ya maida ita kamar Karamar yarinya. Saman wasu kujerun roba ya zaunar da ita shi ma ya zauna, suka sa zagayayyan tebur din a tsakiya. Saude ta bi abin . da aka dora' saman tebur din da kallo, wanda a kai ‘ ‘ rafin din shi gwanin burgewa. Dr. ya miKa hannu ya dauko ya mika mata ta tsaya tana kallon shi ya miqa mata tare da fadar. “Karba mana.’ Ta mika hannu ta karba,tana kokarin bude rafin leda din. Dr. ya yi saurin tsaida ita yana fadar, ‘tsaya tsaya waya fada miki idan aka bawa mutum gift budewa yake'a take bakauyiya ai bari ake sai an tafl.’ Yana maganar cike da zolaya. . Saude ta zumBuro baki" jin ya kira ta da bakauyiya, dariya ta kama shi ya ce, ‘A’a ‘yanmata ashe kin iya fushi irin haka?” Ta dauke kanta ba tare da tace Kala ba. Ya ce, ' ‘Wai fushin ki keyi da gaske am so sorry, tuba nake -kaina bisa wuyana.’ Dariya ta kubce mata yanda ya yi maganar a ladafce sai kace ba YallaBai din da ta sani ba, ganin dariyarta yasa ya mikc yana fadar “Taso muje kin ji ana ta kiran sallah a_ masallaci.’ ‘ Saudeta tashi ta mika masa gift din da ya bata, ‘ya dan zuba mata idanuwansa babu alamun wasa a fuskarsa ya ce ‘Da shi za ki tafi kyauta ce daga gare‘ ni.’ Yana gama fada ya juya ya yi. gaba abinsa, ba tare da ya saurare abin da za tace ba. Tsabar mamaki da kaduwa su suka hana Saude furta komai, har sai da ya kusa bacewa ganinta saunan ta iya wage murya tana fadar, “Na gode kwarai.’ Hannu kawai ya daga mata ba tare da ya juyo ba ya Bace abinsa, ita ma ta yi gaba cike da zullumin abin da aka nannade haka. Tana .shiga dakinta ta fada kan gadonta ta yi zaman dirshan ta shiga bude kyautar, ta ciro wani kyakkyawan kwali mai kyan gaske da zanen waya waya a jikinsa. Saude ta bi hoton wayar da kallo kai da gani ka san ta yi tsadar gaske, a zuciyarta ta furta ‘Allahumma arzuquni" tasa hannunta ta bude kwalin. Gabanta ya yi wata mummunar faduwa ta yi ‘ masifar firgita ganin sabuwar wayar kwance cikin kwallin, ta ciro ta tana jujjuyawa, touch screen mai shegen kyau, wadda ta san ko da kudl aka hada ta ba za ta iya kunnata ba. Saude ta riqe wayar tare da dafe kai, yau na shiga uku ni Saude, wai me ke shirin faruwa da nine? Wasu irin hawaye suka ziraro daga idanuwanta ta lura mutumin nan so yake ya jaza mata bala’in da ba zata iya dauka ba, yanzu tsautsayi yasa Hajiya ta samu labari ya kenan? Motsin taflyar da ta ji ne ya sa ta zabura ta maida wayar cikin kwalinta ta tura a qarkashin filonta, tana faman‘muzurai. Aunty ce ta shigo da sallamarta suka gaisa sannan ta ajiye mata wata leda Saude ta mika hannu ta janyo ledar tana duddubawa. Sabulan wanka ne dana wanki tare da kayan shafawa da mayuka, ta ajiye‘ leadar gefe ta koma ta kwanta tana fatan gari ya waye ta je ta maida masa wayarsa, don ba zata yarda ba ya jaza mata tashin hankali da bala’in da ba za ta iya dauka. Ba Dole nema ta runtse ido ta fada masa‘ ya fita daga rayuwarta ita dai ba kowan kowa bace hakan kuma ba yana nufin ba ta san mutuncin kanta bane da wannan tunanin bacci barawo ya sace ta. Washe gari da safe Saude ta tafl Bangaren Dr. Ahmad babu kowa a falon nasa don haka ta zage ta shiga aikace- aikacenta qarfe goma daidai ya sauko daga samansa yana sanye da jallabiya sabuwa ruwan toka mai hade da hularta Suna hada ido da Saude ya yi saurin qarasa saukowa daga matattakalar yana fadar, “Zo. nan Saudat." * A hankali ta dago ta kalle shi tare da gaishe shi cikin girmamawa kamar yanda ta saba. Ya amsa' a tsanake sannan ya jefo mata tambayar da ta sanya ta saurin dagowa tana kallonsa, ya qara‘gyara tsayuwarsa tare da maimaita mata tambayar. “Na ce laflya ba ki bude kyautar da nayi miki ba Ko baki iya bane?” Ya karasa maganar cike da tuhuma. ; Saude ta dukar da kanta tana kallon kafet din dakin cikin nutsuwa ta soma magana. “Kayi haquri Yallabai ba wai ban yaba ba ne kawai dai na ga kyautar ba ta cancanta dani bane shine yasa nayi' tunanin maido maka, amma ka yi hakuri Dr. Yayi wani takaitaccen murmushi tare da zama saman hannun kujera ya zauna yana kallonta a nutse kafin ya ce ‘Dama ita kyauta cancanta ce ke sawa ayita idan kuwa cancanta ce to ke kuw kin ' wuce wadda a kai miki kinfi qarfin hakan. Kuma idanma ba ki sani ba ina so yau ki sani dangantakata dake tamkar hannu da ido ne yanzu sannu a hankali zan shafe hawayen da ke kwaranya daga idanuwanki insha Allahu sai na wanzar da dariya a idanuwan dake ta zubar hawaye, kin fahimta?” Saude ta girgiza masa kai tana fadar, ‘A’a Yallabai yin hakan yana nufin zaka tsamo ni daga rijiya ka jefa ni kogi ne Yallabai ka yi tunani zan iya shiga matsala wajen Hajiya, na tabbatar idan ta samu labarin kudirin da kake nufo ni da shi zata dauki kowane irin mataki a kaina, Dr Ahmad ya kada mata kai yana fadar, 'Ko kusa Saudat babu wandu ya isu ya yi wu mutum ”abinda Allah bai masa ba haushin me Asmu za ta ji don kawai ina kokarin taimaka miki meye abin da zai tunzura ta a ciki? Ni ban ganshi ba, kuma koma akwai ba zai dame ni ba, zan yi Kokari har sai na sauke alkawarin da na dauka.” Idon Saude ya ciko da hawaye cikin muryar kuka ta ce, ‘Na san ba zai dame ka ba YallaBai amma ni zai dame ni, wata qila ma ya zamo silar barina duniyar gaba daya. ’ Dr. Ahmad ya ce, ‘Hakan ma ba za ta kasancewa ba Saudat ki daina ma fada.’ Saude ta ce, ‘Idan ya kasance fa?” Shiru ya yi yana kallonta Saude ta yunkura ta mike hawayen da suka ciko daga idanuwanta suka samu damar zubowa cikin kuka ta ce, ‘Zan bar gidan nan dole zan bar shi, dan ina tsoron abin da zuciyata ke hangowa ina jiyewa kaina, dan idan ma wani abu ya same ni babu wanda Zai yi kukan rashina, babu ba ni da shi.... Kuka ya ci Karfinta sosai. Dr. Ahmad ya yunkura ya zagayo ta gabanta yana kallonta cikin sanyayyar muryar shi ya soma magana. ‘Duk inda ki ka nufa a fadin duniyarnan sai na nemo ki, babu inda za ki shiga ki layance min. Ina tare da ke Saudat har: sai na ga kin yi dariya sai na ga rayuwarki ta inganta kin samu farin ciki mai dorewa na yi wa kaina wannan alkawarin kuma zan cika shi ko da hakan yana nufin rasa komai na a rayuwata.’ Saude ta yi saurin juyawa tana kallonsa ya daga’ mata kai yana fadar, "Tabbas kisa ido kiyi kalio.’ ‘Ya juya a sukwane ya fICe daga falon ya bar ta nan tana kallon qofar da ya fita. Wani irin kuka ya zo mata, tsoronta daya a duniyar nan matarsa Asma; don ta san ba lallai bane ta yi musu kyakkyawar .zargi ba, tana tsoron ta yi musu mummunan zargin da zai‘sa ta yanke mata hukunci daidai da zarginta. Saude ta Kara rushewa da kuka don har ta hango irin bala” in da za ta iya fuskanta Haka ta karasa aikinta tas ta bro Bangaren nasa, yinin yau haka ta yi sa a kwance. Da daddare kuma Hamid ya kira ta ya Kara caza mata Kwakwalwa. “Wai Saudat me ke damun ki ne shin k0 kin mance da yau saura sati uku auren ki? Na lura hankalin ki kwance yake tun yaushe nake fama da ke kina gocewa. Saudat idan harkin soma san Garba ne ki fad'a mini in fidda raina kawai, amma don me za ‘ki ta yi min yawo da hankali ki ce yau ki ce goba, idan kin san ba zaki iya fitowa daga gidan ba ki 'fad'a mini ni in zo da kaina in dauke‘ki.’ 'Saudat ta ja numfashi ba ta taba tunanin ya iya bude wuta haka ba, ta ma rasa ta indaza ta fara, don . haka ta kwantar da murya ta ba shi hakuri tare da yin . masa alkawarin duk rintsi gobe za ta gudu ta bare ‘ Abujar. » , Abun duniya duk ya ishi Saude tunaninta daya yanzu hanyar da za ta bi ta bar. gidan ga YallaBai yana nema ya taso ta gaba tsoronta daya ma yanzu kar ya ruguza mata al’amuran ta, wannan tunanin ne ya hana Saude barci da wuri sai kusan biyu da wani abu na dare ta kwanta, don sai da ta harhada kayanta tsab na barin garin. . Sallar Asuba ma da kyar ta iya yin ta saboda baccin da yaci qarfinta. A kan sallayar ma wani sabon baccin ya sake dauke ta. Ba ita ta farka ba sai qarfe sha daya da mintina. Ita kanta ta yi mamakin tsawon lokacin da ta dauka tana bacci, don haka ta

Chapter 11 of 26