Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yi hakuni na san Ubang‘iji na sane da mu ba mancewa ya yi da mu ba, kuma shi ya san yanda zai yi da mu, tashin hankalina Saude a yanzu daya ne ' yanda zan tafi in bar ki ban san a wane hali zan barki ba wace irin rayuwa ce za ki fuskanta bayan bana nan, ban sani ba.” Yasa hannu yana goge hawayensa kafin ya ce, ‘Dole zan tafi', dole zan bar garin nan Saude ki yi hakuri ki rungumi rayuwa a duk yanda ta zo miki kar ki yarda ki sabawa Ubangiji a duk halin da kika tsinci kanki ciki, na dadi k0 kishiyar hakan. Na ‘ san insha Allahu Ubangiji ba zai bar rayuwarki ta lalace ba." ‘ Yasa'hannu cikin aljihunsa ya ciro wasu kudi ‘yan, dari biyar~biyar da alama kudin aikinsa ne ya raba biyu ya miqa mata rabi yana fadar, “Ga. wannanki riqe a hannunki kiyi amfani dasu insha Allahu zaki rinqa samun aikena a duk inda na shiga a fadin duniyar nan.” Ya ajiye mata kudin saman jikinta ya mike yana fadar, “Allah ya hada fuskokin mu da alheri." Saude ta yi saurin miqewa ta riqe shi tana wani irin gunjin kuka mai daga hankali. “Don Allah kada ka tafi ka bar ni Yaya wallahi mutuwa zan yi idan ka tafi Wayyo Yayana!” Ta qara fashewa da wani gunjin kukan. Rabi’u ya dafa ta yana kallon idanuwanta kafin ya ce, “Ki yi haquri Saude ni kaina ba dan na so ba zan tafi inbarkiba,da zaiyiwu da dole dake zantafi, amma ba yanda zan yi ne tunda ke macece amma na yi miki alkawarin duk inda make a duniya ina tare da.... Ya kasa fadar abin da yake son fada saboda kukan da ya kwace masa shi ma. Ya zame hannayenta daga jikinsa yana fadar, “In har kina sona da gaske Saude kada ki sake cewa komai ki juya ki koma gida ni na tafl sai wata rana.” Ya dauki jakar kayansa ya juya yana tafiya yana sharar hawayen da ke zuba daga idanuwanshi kamar an kunna famfo, Saude ta duka a gun tana wani irin gunjin kuka tun iya karfinta. Rabi’u na jin ta amma bai waiwayo ba saboda yanda yake jin zuciyarshi na Barazanar tarwatsewa gaba dayanta ga shi a lokacin ba jama’a da yawa a waje saboda safiya ce sosai. Tunda Saude ta duka ba ta sake tashi a gun ba, tun tana kukanta iya karfinta har muryarta ta disashe. ~ Rana ta soma mutane suka fara fitowa daga gidajensu duk wanda zai wuce sai ya yi mata magana, amma ba ta tashi ba, tana duke cikin Kasa tana' kuka, ba ta ankara ba sai dai taji saukar duka ta ko ina’ tana dagowa ta ga Inna Laure, ta mike ta ‘ kwasa da gudu ta nufi hanyar gida, ita kuma ta raka ta da jifa. ' Tana shiga cikin gidan ma nan ma Malam ya dora mata da na shi dukan yana zaginta tare da yi mata mugun baki. Inna Laure ta shigo babu alamun ' tausayawa“ a fuskarta ita ma ta hau zaginta tana fadin * “’Yar iskar ai ba yau suka fara ba, ai dole ta zauna tana~ta aikinkuka karabata da jin dadinta munafuka.” Ta hankade labule ta shiga daki ta dauko mata wasu tsummokaran kayan ‘Yar Baba wadanda ta gama da su ta watso mata tare da wando da tsumman dunzugu, ta gwada mata yanda za ta sanya sannan ta ‘ dora mata tallar wainar. Haka Saude ta dauki tallar ta tice daga gidan tana matsar kwallah. Haka ta je tallar ta dawo ba taci komai ba, sai kukan da take ta faman yi. Haka ma da rana ta dauki alala ta sake tafiya, ruwa kawai ta iya sha a wurin ranar yau, duk inda ta gifta sai ta ga tamkar za ta ga Yayanta amma k0 mai kama da shi bata gani ba haka ta karaci yawon tallar ta ta dawo da yamma likis. Ta samu Inna Laure da dillaliya suna tsakar gida saman kujera ‘yar tsugunne taya ni gulma suna hirarsu har da shewa. Tana shigowa Laure ta nuna ta da baki tana fadar. “Kin gan ta nan fa dillalliya, wan: ai aikatau ga wannan ai tallar cc kawai ta dacc da ita.” Dillaliya ta ce, “Haba dai a ganin ki dai, amma in da ni ce da wannan wallahi Abuja zan tura ta kawai." Saude ta qula ta gaishe da dillaliyar sannan ta mikawa Inna Laure cinikinta ta mike ta wucc dakinta. Tana jin Inna Laure na fadar, “Hmm! Dillaliya kenan ai ni duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha, to shi kuwa k0 miyar ma bai sha ba don in fada miki dama cike nake da shi don har na fara tunanin in zuba masa shinkafar Bera a abinci ‘ya ci kawai, sai dai a wayi gari ya yi mushe. Ai in fada miki ina tashi. da Asuba na 'ga yarinyar jinin ya zo mata, ai a take dabara ta fado mini, ni kaina sai da na shiga daki na yi ta dariyar qeta yanda na ga Malam na sharar ‘yar kwalla.” I Duka suka sa shewa suka tafa. Can Saude ta jiyo diilaliya na fadin “Ke wai ba zaki saro gyada ki soya mata ta rinqa zama kofar gida ba na ga sabuwa ta fara shigowa wallahi ciniki za ta yi ta rinKa zama nan kofar gida da daddare.” Laure ta ce “Ai k0 kin kawo shawara bari gobe Talata inje ‘Yar Kutungu da kaina in siyo mai kyau in zo in soya mata Ai shi yasa nake son ki kawata Akwai ki da bada shawara mai kyau. Saude ta lallaBa ta kwanta tana jin zuciyarta na tuquki wasu zafafan hawaye suka rinka biyowa kuncinta ba ta da mai lallashin ta yau dakin ya yi matA bakikkirin, saboda rashin rabin jikinta, Yayanta a cikinsa Sai yanzu ne ta gane marainiya ce ita marar gata, yanzu ta yarda da maganar Yayanta da yake ce mata bata da. gata a. duniya, ba su da kowa sai Allah. Ashe da gaskiyarsa. Ta sake rushewa da wani sabon kukan lokacin da ta tuna da lokacin da ya dawo daga aiki jiya ya kawo mata kayan kwalliya. * Ta tuna da irin yanda yake lallashinta idan ya ga ta shiga damuwa duk ~ yanda zaiyi sai ya yi ya tsaida hawayen nata, ga shi yanzu baya nan. Tabbas ta rasa gata a duniya ta rasa jigon rayuwarta. don tana ji a jikinta da wuya. idan za ‘ tasake ganinsa tunda shi kan shi baisan inda za shi ba yanzu, wala ya mutu k0 ya yi rai. Shin k0 yana a wane hali yanzun ma? “Wai k0 ba da ke nake ba ne Saude kina ji ina ta faman kiran ki?” Saude ta jiyo muryar Laure, don haka ta zabura ta mike ta goge hawayenta ta yo tsakar gidan a lokacin dillaliya ta tafi Laure ta watsa mata harara kafin ta ce, “’Yar iska duk uban me kike ina kiran ki kin yi min shiru?” Saude ta yi shiru tana kallon yatsun qafarta hawayen da suka taru a idanuwanta suna diga qasa, Laure ta ja tsaki tana fadin. “Ke dai kya kai su in kaya ne wuce ki ki dora mini sanwar tuwo, idan kin dora ki zo ga kayan wankina can na jika ki wanke mini su.” Saude ta yi saurin dagowa ta kalle ta, Laure ta ce, “Bakallona zakiba cewa zakiyi bazakiba kawai sai in san kin isa.” Saude ta juya ta wuce jikinta amace, saboda ita dai ba ta taba yin wanki ba, don kayanta ma kale daya ne, duk wani wankin gidan Rabi’u ne ke yinsa. To ta inn ma za ta fara? Ba ta da zabin da ya wuce ta dora sanwar sannan ta wuce bakin magudanar ruwa ta ci gaba da cuda kayan Sai da ta yi da gaske sannan ta samu ta gama aiyukanta saboda ciwon qirjinta da ya soma taso mata ga mararta da ta kulle da bayanta, ta kwanta tana faman numfarfashi. Rayuwa ta dawowa Saude sabuwa gaba daya, al’amura sun karasa damalmale mata, duk wata .wahala da dawainiyar gidan gaba daya ita ke yin ta, ga yawan tallar datake yanzu hartafi tada tayi ta safe, ta yi ta rana, ta yi ta dare. Duk ta bi ta Kara lalacewa ta fige ta zama tamkar kwarangwal, kazantar da take ciki har tafi ta da, ga alamun girma na zuwar mata, amma kullum rayuwana Kara dagulewa take tana Kara shiga cikin matsi da kunci. Kullum a wurinta jiya ta fi yau. Tun tafiyar Rabi’u bai sake dawowa ba, ba ta kuma Kara samun labarinsa ba. Lokaci ya yi ta tafiya kusan shekara biyu kenan da tafiyarsa kullum sai ta yi kukan rashinsa wanda ba ta da kamar sa. Sai dai ta yi ta share hawayenta ta kwanta ta yi barci, qunci da wahalhalun rayuwa sun yi mata yawa har wani lokacin ta rinqa jin gara mutuwa da irin rayuwar da take ciki. Musamman abubuwan da ‘Yar Baba ke mata ya na damunta, ko'dan ta ga ta fita girma ne duk da Saude a lokacin tana da shekara sha shida, ita kuma ‘Yar Baba na da shekara sha biyar, amma tafi Saude garin jiki, saboda ita irin girman jikin nanne da ita gab-gab mai irin manyan gaBoBin nan. Don ita Saude ‘yar siririya ce sosai, kamar a hure ta 'ta fadi, sai dai tsawo kamar an ja ta. Ita kuwa ‘Yar Baba gajeriya ce mai Kiba sosai tana da manyan mazaune da wadatar na shanu, ba laifi 'ita ma kyakkyawa ce tana da dogon hanci da manyan idanuwa sai dai qaton baki ne kawai ya kware ta mai cike da haqora kamar an watsa wake a miya. ‘Yar Baba har tafi mahaifiyarta wurin‘rashin mutunci da rashin tausayi ga gadara da ' rashin kunya da tsinannan surutu, kamar aku, ga shi' Inna Laure da Malam Bala sun dauki son duniya sun dora mata, duk wani abin da suka samu yana kanta. Shi yasa ‘Yar Baba ta tashi da kwalliya ‘yar gayu ce sosai, suttura komai tsadarta za ka ganta jikin ta, matsatstsu na fitar hankali, kuma ba laifi tana yin kyau matuka, amma idan ka kalli Saude to zaka iya cewa gara jiya da yau. Yanzu haka Saude tafe take rungume da bokitin alala, tana gab kawowa kofar gidansu ta hango wata qaramar mota Joker ta yi fakin mai bakin gilas, ta qurawa motar ido a lokacin da ta ga na cikin motar, dan iya saninta ba su da wasu ‘yan uwa masu 'mashin' ma balle mota Ta Kara gyara rungumar da ta yi wa bokitinta tana kallon motar, ta zo daf da ita ne ta ga an bude an fito. ‘Yar Baba ce da wani saurayi suka fito daga gidan baya na motar hannunta na riqe da irin manyan ledojin nan na shopping. Ba ta ankara ba ta ji ta rafka tuntuBe har takalmin da ke Kafarta ya tsinke dama sun sha duniya duk sun side ga su daban-daban, wato wari da wari, wani ya fi wani. Hakan yasa tasa reza ta ragewa babban tsawo, gaba daya takalman duk sun sha faci da Leda. Ta durkusa ta dauki takalminta ta wuce cikin gidan nasu tana gyarawa, duka suka raka ta da kallo, tana jin saurayin na fadar, ‘Wannan kuma wace ce?” ‘Yar Baba tabe fuska kafin ta ce “’Yar talla ce gidanmu take tana yi wa Baba ta talla. Wani abu ne?” Saurayin ya girgiza kai kafin ya ce “A’a, haka kawai amma dai gaskiya kazama ce, wallahi bakijiba data wuceni harzuciyata saida ta tashi. " Daidai nan Saude ta shige cikin gidan tana jin zuciyarta na mata wani irin kunci. Tana shiga cikin gidan ta ajiye bokitin tallarta, ta miqama Laure kudin cinikinta sannan ta dauki abincin dake ajiye bakin murhu babu k0 murfi sai kudaje ne ke bi yabe yaBe. Saude ta dauka ta nufi bakin qofar dakinsu ta zauna ta soma cin dumaman tuwon. ‘Yar Baba ta shigo niki~niki da ledoji Inna Laure da ke zaune gefen tabarma ta washe baki tana fadar. “Oyoyo! Ga ‘yata, taho nan zauna, zo zauna mu ga me aka farauto mana ‘Yar Baba ta cire takalmanta masu mugun tsini ta ajiye ledojin saman tabarmar, ta cire dan karamin mayafinta mai kamar matacin koko, saboda shara~ sharansa ta zauna, gaban rigar nan an yanke shi sosai, maman nan nata ya yo waje kadan ne kawai ke cikin rigar, Inna Laure na kallonta k0 a jikinta ita ta ledojin ma kawai take. Babu abin da ke cikin ledojin sai kayan makulashe kala- kala, su sweet, cingam, biskit, choculate da sauran tarkace, daya ledar kuma wasu hadaddun kayan shafawa ne irin na manyan mata. Bakin Laure ya Ki rufuwa‘ta dubi ,‘Yar Baba taha fadar, “Wannan kuma ina ki ka same shi ‘Yar Baba, dan wane ne a garin nan?” ‘Yar Babe ta tabe baki tana taunar cingam kafin tace, “Wallahi ban san k0 dan waye ba, nima jiya na hadu da shi na dawo daga makaranta.” Laure ta rafka guda kafin ta ce, “Da kyau ‘yata tauraruwa cikin taurari, mai farin jini, shi yasa. kullum nake Kara son ki dan anan dai haihuwa ta yi rana, Ki dai tsaya ki nutsu ki dage ki shake mana wuyan duk wanda ki Kikeso in ja shi in zaga birni in ratsa Kauye nasa ai masa daurin huhun goro ‘Yar Baba ta sa dariya tana fadar, “Kai shi yasa nake son ki Laure.” ‘ Ta mike tsaye tana fadar, “Hmm! Gaskiya wani abu na ci min tuwo a Kwarya, gaskiya Laure yarinyar can tana zubar mini da aji a gaban samarina.” Laure ta zaro ido “Wace yarinyar?” ‘Yar Baba ta yamutsa fuska kafin ta ce, ‘Yo wace ce in ban da waccan Sauden banzar kullum tana cikin Kazanta wallahi da ta wuce ki har wani wari za kijitanayi. Agaskiya nibazan iyaba indaitaga ina zance ta koma ta samu dakali ta zauna sai na gama, wallahi take ake yi mana daukar matalauta.” Laure ta ce, “Ai waccan mai kama da igiyar shanyar ni kaina abun na damuna da ta tunkaro ki harwani Karni-Karni za ki ji tana yi ita k0 warin jikinta ba ta ji.” ‘Yar Baba ta ja tsaki ta wuce daki tana faman juya mazaune kamar mai rawar taBa-kaka. Wani irin abu ya yiwa Saude tsaye a zuciya, wai harsu sunada bakinda ’zasu kiratada kazama, alhalin sunfi kowa sanin kayanta a duniya kala uku ne sumana Laure ne data gaji da gurza tasakar mata, duk sun sha gamin baki. Daidai da man shafawa bata da shi a gidan, to balle sabulun wanka k0 na wanki, sai idan ita ce ta gaji da yawo da kazantar ta ta siyo omo na goma cikin kudin tallarta idan ta dawo tayi wanki tadiba aciki tayi wanka. Idan ba zata manta ba rabon da fatar jikinta ta ga man shafawa tun kayan kwalliyar da Yayanta ya siyo mata shekaru uku kenan da suka wuce da ‘yan kwanaki. Ta mayar da ‘yar kwallar da ta ciko mata ido ta ci gaba da cin tuwon da ta keji tamkar dutse saboda yanda yake mata tsaye a qahon zuciya. Da rana Saude tana zaune saman bencin cikin tasha ta tasa bokitin alalarta a gaba tana kallon jama’a na ta kai wa da kawowa, can ta hango Garba Gurgu yana nufowa inda take yana faman tsangala kafa da shanyayyan hannunsa guda can gaban qirjin shi a makale yana kadawa irin na wanda ya shanye Saude ta Kara hade fuska dan a duniya idan akwai wanda ta tsana, to bai wuce Garba Gurgu ba, ga shi dattijo dan a Kalla ya kai shekara sittin, ga shegen iyayi kamar wani qarami. Yaro Garba ya qaraso har inda Saude take zaune yana ' faman watso hakora kamar an zana ABCD. Saude ta daukc kanta ta ci gaba da kallon wani waje. Garba ya cangala ya zauna saman dutsen da ke gaban ta. “sannu da hutawa Hajiya Saude ya kasuwar?” Saude ta jiyo muryar nan kamar an kunna injin markade saboda girmanta, ta dago idanuwanta tana Lol i relly feel unhappy for rabiu [1/17, 7:54 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/19, 5:11 PM] I love my mum: *YAR TALLA* *CHAPTER 12* kallon shi sai faman sosa gemu yake wanda ke _ faman yi masa kaikayi duk ya yi wani quda~quda da alama ba za a rasa kwarkwata a cikin saba, saboda tsabar qazanta da kurar duniya da ya sha. Saude ta dame zuciyarta ta amsa masa don k0 kadan ba tajin za ta iya yi masa wulaqanci saboda girman shekarunsa dan ya yi jika da ita. Garba ya Kara watso haqoran nan wadanda su kai kore fatau kamar gansa-kuka yana fadar, “Haba Saude na ga alamar kamar ba ki san magana dani, ki yi hakuri ni masoyinki ne ba makiyinki ba kuma ni aurenki zanyi bawai wasa zaikawoni wurinkiba yanzu haka idankika amince min mahaifinki kawai zan nema a yi magana.” Saude ta watsa masa wani kallo mai kama da harara ta zumburo baki kafin ta ce, “Ni fa ba anre zan yi ba yanzu Ya yaqe baki yana fadar, “Haba Saude ke yanzu idan bakiyi aureba saime zakiyi?idan ki ka amince: ki‘ka aure ni, killa ceki zan yi a‘gidana, kin gama zuwa talla idan ma kina tunanin matana hudu ne to a shirye nake dana saki daya daga cikinsu Ya kikacene Saude?” ’ Haushi ya kamata ta mike afusace tadauki bokitin tallarta ta yi gaba ta bar shi nan zaune Garba Gurgu ya yi dariya yana girgiza kai yana fadar‘ “Yaro yaro ne.” Ya mike yana cangala qafa shi ma ya yi gaba abin sa. Bayan Saude ta gama tallarta da yamma likis ta koma gida a gajiye ta samu ta ci abinci ta yi sallar Magariba, sannan ta dauki tallar dare ta fita kofar gida ta zauna da ‘yar fitilar aci-balbal. Kamar daga sama ta hango shi tsangal-tsangal haushi ya cunkusheta ta bade fuska a zuciyarta ta kudiri aniyar idan ya sake ya zo inda take sai ta cire kunyarsa daga idanuwanta ta yi masa rashin kuunya tunda ta lura bai san girmansa ta gani ba ta daga masa kafa ba Da mamakinta sai ta ga ya yi wa kofar gidansu tsinke, ta saki baki da idanuwa tana kallon shi, ta ga ya kira wani yaro ya tura shi cikin gidansu. Yaron bai jima ba ya fito tana kallon su can sai ta ga mahaifinta ya flto sun tsaya suna gaisawa, gabanta ya yi ’mata mummunar faduwa hankalinta ya yi masifar tashi ba dai Garba wurin mahaifinta ya zoba. Wayyo Allah na shiga uku! Abin da ta iya fada kenan wasu zafafan hawaye suka shiga zarya a kuncinta tana kallon yanda mahaifinta ke ta faman washe bakivyasa hannu ya karBi kudin da Garba Gurgu ya ba shi, sannan suka sake yin musabaha, sannan ya shiga gida shi kuma ya wuce abinsa ba tare da ya kalli inda take ba. Saude ta ta kwashi kayan tallarta ta nufi cikin gida. A tsakar gida ta samu mahaifin nata na fadawa “Laure kin ga wani abun murna k0 wai mutumin nan Garba Gurgu ke son Saude Laure ta rangada kuda ta ce, “Kai amma abun ya yi min dadi wallahi, ka ga sai a hada su su duka da ‘Yar Baba. don ita ma ta ce yaron nan mai zuwa wurinta da jar motar nan ya ce zai turo ai maganar aure Malam Bala ya ce, “Ai ko haka za ai dama ni na amsa masa, yanzu haka ya ce jibi za a kawo kayan nagani-inaso yanzu haka har kudi ya ba ni kin gansu dubu biyu. Kai gaskiya mutumin nan yana da mutunci.” Laure ta ce“To, ai sai ka tsakuro mini nawa tunda ba kai kadai keda diyar ba Malam ya ce, “Kefa tsiyarki ke nan duk abin ki ai kya bari' na mutu sannan ki rufe ni ai k0?” Ya ja tsaki ya cimimiya kwarar dubu guda ya cilla mata ya juya zai tafi ya ga Saude tsaye rungume da kayan tallarta hawaye sun gama bata mata fuska. Malam ya ce, “Ke kuma fa lafiya?” Cikin muryar kuka Saude ta ce “Ka yi haquri Baba don Allah wallahi bana san shi ba zan iya aurensa ba, sabo... Malam ya katse ta ta hanyar fadar, “Ke dalla Saurara mini kin jiki Ba kya son shi sai wa ki ke so?” Saude ta yi shiru tana faman shashshekar kuka Malam ya sake fadar “Na ce idan ba kya son shi, sai ubanwa kike so?Munafukar Allah,nankikaso ki jibge mana kita zama kitsufa a tasha kina talla, tunda kebaki da tunani ko Allah yataimaka kemaya kawo miki dauki, tunda ki ka tashi akwai bakon takalmin da ya taBa zuwa wurin ki da sunan so, iye? Amma shi ne har kina da bakin magana. Shekarar ki nawa yanzu a duniya? Kin zauna kin jibge babu mai taya ki kek0 kishin kanki ba kya yi, kina kallon ‘yar uwarki kullum wannan ya shiga wannan ya fita, harda masu motoci, amma saboda rashin kishin kai ba ki taba damuwa ba.” mts! Ya wuce yana fadar. “Idankinada wandakikeso to saikituro shi ai lokaci bai qure miki ba daga nan har ranar daurin aurenki Wani irin kuka ya Kara kwacewa Saude, ta aje kayan tallar ta yi dakinta da gudunta tana. wani irin kuka mai tsuma zuciya. Laure ta ja tsaki tatattara kayanta tana fadar, “Ke dai kya kai su idan kaya ne dan bakin ciki sai dai ya kashe ki don na gaba ya riga ya yi gaba har abada ba zaki iya kamo taba.” Saude ta sha kukanta har ta godewa Allah bata . da mai lallashinta haka ta kwanta har bacci barawo ya sure ta. Haka ta farka yau idanuwanta duk sun ‘ kumbura sun yi jawur saboda kukan da ta sha jiya. Haka ta je tallanta ta dawo jikinta ba kuzari kana ganinta ka san tana cikin matsananciyar damuwa. Ta yi zaman daBaro kan sumuntin tsakar dakin, don kuwa dakin bai da arzikin k0 qaramar tabarma Saude ta jingina da bangon dakin ta rafka wani ; uban tagumi ko tunanin me take? Oho ‘Yar Baba ta dago labulen tana mata wani shakakken kallo kafin ta ce “Idan kin gama tagumin sai ki fito ga kayana na ki hado ki wanke mini. ‘ Saude ta dago da jajayen idanuwanta tana « kallonta, haushi da baKin ciki suka turnuqe mata zuciya, tuni dama batun yau ba take jin takaicin abin da ‘Yar Baba ke mata ba sai ka ce ita ce babbar, ita ma kuma ita ce karamar. ‘Yar Baba ta ce, “Ki ka tsaya kina kallona da wasu kananan idanuwanki can masu kama da na kwarkwata kixo ki min wanki na ce Takaici ya kuma turnuke Saude cikin fusata ta ce, “Wai ‘Yar Baba me ki ka dauke ni ne jakar ki ko kuma me? Karfa ki manta a girme na girme ki,amma ki rinka! yi min abu kamar wata yar da ki ka haifa. Ai ba ‘yar wanki ki ka aje ba, da ki ka dama can da ina miki Inna ce ke sani, amma ke baki isakisani inmiki wanki ba” “ ‘Yar Baba ta ce ‘Eh, lallai wuyanki ya isa yanka, har ni ki ke gayawa magana yau k0 Saude dan kin ga Laure ba ta nan lallai za ki san kin yi da diya ba shegiya ba, za ki gani.” Ta juya ta yi gaba. Saude ta ja tsaki ta IaIIaBa ta kwanta ta ci gaba da nazarin abindayadameta. Bata ankaraba saidaita ji saukar kayan wanki a jikinta ta zbaura ta mike tana kallon mai wannan aikin. 0000000000 “Wato kenan har‘ yar iska ce har kin yi girman da ‘Yar Baba za ta sanya ki ki mata abu ki zage ta ki ce ba zakiyi ba. ‘ To yau sai na ga uban da ya ,tsaya miki ki dauke su maza ki je ki wanke mata, ki shanya ki zauna su *bushe ki linke ki kai mata daki, tantiriya marar kunya, ai na godewa Allah morewa ta dama na ga rayuwarki ta wulakanta, kuma na yi nasara, in dai ina numfashi kin auri Garba Gurgu kin gama, bankadaddiya yanda na ga bayan uwarki da wannan takadarin ke ma sai na ga naki. ’ " Ta ja tsaki ta wuce tana fadar. “Munafukar banza!” . Wasu irin hawaye masu dumi suka zubo daga idanuwan Saude tasa bayan hannunta ta goge sannan ta' shiga tattara kayan wankin ta wuce tsakar gidan, Ta. wanke su gaba daya abun bakin cikinta har da bireziya da dan paint, saboda kawai tsabar raini da wulakanci. Rayuwa kenan. Kamar yanda mahaifinta ya ce za a. kawo kayan nagani-inaso, haka kuwa aka yi Garba Gurku ya aiko mata da kaya cikin Gari ya yi zafi, dinkakkiyar atamfa ce ta roba riga da zani sai dakakkiyar abaya kwaya daya, sai takalmin roba shi ma guda daya da sinqin sabulu guda da Katuwar ’kwalbar mai dangwali-yaBa, sai naira dubu a sama. Laure ta dauki naira duban sannan. ta mikawa Saude kayan don ba abin da ya yi mata a cikin kayan. Wasu irin hawaye masu zafi suka ziraro daga idanuwanta tasa hannu ta karBi kayan ta wuce daki ‘ da su. Tana shiga ta wurgar da su tsakar dakin ta durkushe tana raira wani sabon kukan mai cin zuciya. Tabbas tana cikin halin da ya kamata a tausaya mata,Yayanta ya ringa yi mata gizo cikin idanuwanta ko wane hali yake yanzu? Saude ta sha kukanta ta gaji ta lallashi kanta ta yi shiru Abu wasa-wasa lokaci ya ci gaba da tafiya, Garba Gurgu ya ci gaba da yi wa Saude hidima, idan abun kirki ne sai Laure ta rike, idan kuma ta gajam tagajan ne sannan za ta ba ta, ita k0 ba ta taba kallon kayan ba don yanda ta tsani mai kayan haka su ma kayan ta tsane su. ‘ Ranar: wata Laraba Saude ta dawo daga tallar safe, misalin qarfe daya na rana, Laure tace yau ba tallar rana ta je

Chapter 5 of 26