Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fata, kayan manyan mata kuwa wannan daga qasashen Larabawa ta ke hada su. Ke dai bari ‘ mu je za ki gane wa idonki” Saudat ta ce, “Ita kuma amarya har wani . gyara na daban ake mata.” , Shukura ta yi wani takaitaccrn murmushi kafin ta ce “In ban da abinki Saudat, idan akwai . macen da ta ke bukatar gyara a bayan amarya ta ke ko kuma macen da ta haihu ita amarya ana bukatar ‘ komai nata ya xama na musamman ne tun ba ke da" Zakiyi aure gidan kishiyaba, ya kamata ta ko’ina , mijinki' ya san da bambanci, tun daga tafukan , hannunki, labbanki, fatar“ jikinki, da kuma fuskarki, sai kuma can ainahin wanda wannan kuma aikin manyan mata ne musamman idan auren na Soyayya ne Abin da dai nake so ki gane shi ne ranar bikin kowace mace to awurinta wannan babban ra'na ce da babu irinta a rayuwarta, musamman idan auren na soyayya ne. A ranar daurin aurenki kowa burinsa ya ga irin kwalliyar da zaki yi, kek0 da ‘yan gidanku ne suna son qare miki kallo a wannan ranar, shi yasa wasu matan tsabagen son gyaran jiki har gyaran ‘sai yazo ya yi yawa, ya feSo musu 'da quraje a fuska k0 da ba bata da wadannan kurajen a da. Don haka a matsayinki na aMarya ya kamata ki kula da kanki, akwai sirrikan abubuwan da ke gyara amare na farko a matsayinki na amarya ana bukatarki da yawan sham ruwa sirrin hakan shi ne, kar jikinki ya yankwane. Sannan ana bukatar amarya da cin “ya yan itatuwa hakan zai taimaka wa fatar jikinta matuka, ‘ sannan ana bukata: amarya da ta yawaita sham , kankana, ita ma za ta taimaka mata matuka wurin gyaran fatar jikinta, haka kuma cin ganye irin su. latas da kabeji, suma za su taimaka kwarai. Ta yinkura ta nufi bandaki tana fadar “Bari in fara watso ruwa mu shirya tun kafin Momy ta sake biyo mu” . Ta zame kayan jikinta ta shige bandakin don watsa wa jikinta ruwa. lko sai mai tsaga ido Allah Almusawwiru, mai yadda Ya so, tabbas na yarda komai nufi ne na Ubangiji, kuma al’amarin aure tamkar layin . kasuwa ne idan layi yazo kanka k0 bakaso sai an maka, kamar yadda arziki bai isa ya guje wa ‘mai shiba, haka shi ma rai bai isa yaqi mai shi ba, haka matar mutum ba ta isa ta guje‘masa ba k0 ana ’ ha-maza ha-mata, auren da Ubangiji ya qaddara to fa sai an daura shi duk tsananin wuya, kuma duk dadi don duk nisan dare gari zai wayr. Hakan ce kuma ta kasance don yau ita ta kasance ranar juma'ar da za a daura auren Saudat a asabar In ka duba gidan Dr. Mariya acike yake da yan uwa da abokan arziki na kusa da na nesa, don ‘ a ranar ne za a yi kamu, wanda Dr. Mariya ta shirya . Biki ne ake ba wai na wasa ba, don kudi ta ke kashrwa tamkar tana tsinto su mafiyawancin abubuwan da ake yin amfani dasu a wurin bikin duk daga qasashen waje ta bada saqonsu aka taho mata‘ ‘ dasu DukvWanda ya ”san Saudat kuwa yancu” idan* ya ganta da wuya idan zai iya ganeta Cikin sati ~daya ta yi wani fitinannan haske, don har wani .yalo-‘yalo ta ke, fatar jikinta ta yi wani luwai- luwai ’sai sheki ta ke tare da daukar ido tamkar jikin tarwada, cikia lokaci guda ta rikide tamkar wadda aka Kara wa kyau da fari. Kodayake irin manyan kudin da Dr. Mariya ta saki wurin gyara ‘yar tata sun isa ace ta maf1 ; haka. don k0 gyaran jiki sau uku aka mata arana, safe da yamma da kuma lokacin kwanciya bacci, don daidai da Kunshi daga Abuja ta dauko mai zanen da ta yi musu, gyaran gashi ne aka yi musu ’ a babban wurin gyaran gashin da ke G. R A,abinka da ma da mai abin don haka gashin ya isa saukowa , har tsakiyar bayanta, ga wani baKi da sheqi da yake na musamman. Haka dinkunan fitar .biki duk a Lagos ta ba da aka dinko mata wasu kuma a -. Dubai sai shaddojin ne ta bada aka dinkosu a Maradi. Yanzu haka Saudat ce da Shukura baje a falo suna duba kayan fitar kamun da za su sanya a yau, Momy ta turo kofa ta shigo da sallamarta, ta ' tsaya daga bakin kofa jikinta a sanyaye ta ce “Direba Ya daWO yanzu‘ amma har yau dai mai . danwake ba ta dawo ba, sai dai maigidanta ya ’tabbatarda cewa, duk abin da aké ciki ba za ta rana ita yau ba tare da ta dawo ba" ‘ Cikin nutsuwa Saudat ke kallon mahaifiyar tata, cikin sanyin jiki da sanyin murya ta amsa da, “Allah ya kai mu Momy, Allah Ubangiji ya bayyana mana shi ma kafin lokacin” . , Momy ta amsa da,“Amin”. Kafin ta dau wani nannauyan numfashi tana kallon Shukura ta * ce “Ya kamata fa ku yi azamar shiryawadon Karfe hudu daidai za a fara kamun”. Shukura ta amsa, “Insha Allahu Momy yanzu za mu shirya”. ' ' Momy ta juya ta fice Shukura kuma ta mike tana fadar, “Tashi‘ yar uwa ki fara shafawa jikinki ruwan lallen nan kafin in fito daga wanka” K0 motsi Saudat ba ta yi ba ballantana ta sa ran amsawarta, hakan ya sa Shukura waigowa ta dubi inda Saudat ta ke, tare da fadar,“Lafiya dai Saudat. " " A hankali ta dago kanta tana kallon Shukura kafin ta ce, “Babu komai”. " Shukura ta girgiza kai, “A’a ban yarda ba Saudat, na lura damuwar fan uwanki na damunki amma ya kamata ki yi wa Momy uzuri, saboda yadda ta ke iya bakin qokarinta bai kamata ki Kara , daga mata hankali da damuwarki ba. Kina kallo tun ‘. ranar daki kace mata yayanki ya‘ bada sako gidan mai danwake a ajiye miki Momy kullum sai ta tayar da direba ya je gidan, amma har yau ba a yi nasarar sa'mun mai danwaken ba, tunda an ce ta je garinsu Ki kara haquri don Allah Saudat, insha Allah zaki ga sako mai dadi wurin mai danwake da zarar ta dawo tashi ki rage kayan jikinki in taya ki shafa ‘ Ba musu Saudat_ ta yun kura ta mike don ta sani haquri ya zame mata dole, k0 da ba a ba ta ba ita. ta ba wa kanta tunda dai babu wanda ya san inda Rabi’ un yake. Shi kansa Dr. Ahmad din yanzu iya kokarinsa yake mata a kan“ cigiyar dan uwan nata' saboda yadda ya ga ta damu a kansa. , ’ Da taimakon Shukura da kuma na matar da ‘ . Momy ta dauko mai kwalliyar amare, aka gyara amarya Saudat cikin wani tsadadden cotton lace mai laushin gaske kalar dark pink an qawata shi da bakaken fulawoyi da wasu qananun duwarwatsu, masu kama da yarfin gwal, daurin kallabin da aka kafa mata duk wanda ya kalla ya san daurin‘shago ne don ba irin wanda muka sabayi bane gashin ’ nan nata an saki kadan gefen fuskarta sauran kuma an nade shi an saki jelarsa a kan gadon bayanta inda aka kawata wuyanta da kunnenta zuwa yatsun hannunta da tsadaddun gwala-gwalai Sannan suka dora ta a kan bakin takalmi mai matsanancin tsini sai ka ce wadda ta hau tsani sai yar qaramar jakarsu wadda ba ta wuce girman tafin hannuba Amarya kam ta fita batun bayyana irin kyawun da ta yi ma bata lokaci ne, don k0 lokacin .da ta ke zama a kan kujerar da aka tanada ' don amarya, saf ta zauna tamkar mutum- mutumi, ko ace aljana don kyau, kai ka zata zana ta aka yi ba ‘ wai mutum bace “Ana kiran sallar magriba aka tashi daga kamun, a lokacin ne kuma Dr. Ahmad da abokansa ' ' suka iso gidan cikin tsadaddun motocinsu, don haka gidan ya kara rikicewa, Shukura ta shiga busy don ganin ta karrama angwayen da abubuwan ciye ciye da tande-tande. Saudat kuwa duk kunya da nauyin Dr Ahmad ne ya hana ta sakewa da kyar Shukura ta samu ta je ta gaishe shi shima sai da ta yi da gaske a lokacin da ta shiga falon da aka sauke su gogan nata yana kishingide saman doguwar kujera abokansa sun sa shi a gaba suna ta hayaniyarsu, ' inda shi kuma yake ta faman kallonsu yana cin , tuffa apple. Saudat ta ji tamkar ta nutse a lokacin da suka hada idanu, sai taga ma tamkar shima kara masa kyau akayi, farin yadin neke jikinsa ya Kawatar Da kyar ta yi ta-maza suka gaisa da abokan nasa sarakan surutu kamar zasu hadiyeta Kowa burinsa ya fadi albarkacin " bakinsa ita dai ta gaza tofawa sabuda kwarjinin da angon nata da ya cika falon, ji take duk girman dakin ya yi mata kadan, sauqinta ma daya Shukura da ta tare ma rigimar domin don kuwa ita wurin dan banzan surutu ba ‘daga baya ba. Dr. Ahmad wanda tunda ta shigo falon bai * ,tanka ba har sai da ya lura zolayar abokan nasa za ‘ ta iya nutsar da Saudat cikin qasa don kunya, ~ sannan ya yunqura ya mike a kasale tamkar wanda aka yi wa dukan tsiya. , Ya nufi inda amaryar tasa ta ke nutse cikin kujera ya sa hannu ya tayar da ita tsaye yana fadar, “taso mu bar nan Madam kada su samin ke ciwon kai Kamar jira suke suka yi kansa, amma bai kula suba yana rike da hannunta suka fice daga falon kai , tsaye harabar waje suka nufa, ya jawo musu wasu fararen kujerun roba suka zauna cikin rumfar da aka tanada don hutawa Dr Ahmad ya yi wani murmushi mai kama ‘ 'da dariya lokacin da yake Kokarin lallai sai ya hada , ido da ita amma ta Ki yarda shi dariya ma ta ba shi, ya tallabe kuncinsa yana fadar, “Oh ni Ahmad na ga ta kaina, haka zamu yi dake kenan?” Ya Kara sa dariya, “Lallai yarinya aiki ya , ganki bama kadan ba, amma fa kin yi kyau don‘ lokacin da ki ka shigo falon sai da nayi suman wucin gadi har wani kishi na ji ya yunkuro min yadda na ga kartan nan na kallonki shi ya sa na harna .gaza magana , Duk yadda zuciyar Saudat ta ke cike da alkunyarsa sai da dariya ta kwace mata jin yadda ya kira wayayyun abokansa da qartai, Dr. Ahmad ya kafe ta da manyan idanunsa yadda ta ke dariyar ’ tata cikih nutsuwa kallon da yake mata ya sa a dole ta gimtse dariyarta, hakan ya yi daidai da sauke wani gwauron numfashin da ya yi tare da lumshe manyan fararen idanunsa ya shafi sumar qeyarsa yana kallon farar moter da take shigowa cikin gate din ’gidan a dan nesa da su kadan aka faka motar daga ita har shi idonsu na kan motar. Zuciyar Saudat ta yi wata mummunar bugawa lokacin da mutumin da ke cikin motar ya fito shi da wata zukekiyar mace kai tsaye inda suke zaune suka nufo har a lokacin kirjin Saudat bugawa yake ta gaza k0 da kwakkwaran motsi. “Hamid dinne k0? ’ , Dr. Ahmad ya watso mata tambayar yana . kallonta Kai kawai ta iya daga masa don a lokacin har sun qaraso cikin sallamarsu inda Hamid ya miqawa Dr Ahmad barin fuskarsa ‘dauice da fara a suka yi musabaha Hamid na riqe da hannun ' Dr Ahmad ya taya shi murna tare da yi masa fatan aikhairi cikin sanyin jiki, Saudat ta gaishe shi amma ga mamakinta har a lokacin da fara,a akan fuskarsa ya amsa mata a. tare da yi mata fatan aikhairi ya nuna zukekiyar macen dake tsaye " wadda akalla shekarunta ba zasu haura ashirin da daya ba . Yacé, “Ga Kausar nan takanas 'muka taho‘ tare don ta taya ni murnar aurenki, ita ce amaryar ' tawa“. Ya juya kan Kausar din, “Kausar ga Saudat ’ Da‘ fara’a a fuskarta ta miqa wa Saudat hannu suka' yi musabiha cikin sigar zolaya ta dubi Dr. Ahmad tana fadar, “Godiya mara: adadi, .ka taimake ni tunda ka kasa‘ angona don da yanzu Kausar ta shiga cikin jerin sahun matan da za ayiwa kishiya a wannan watan,na gode ‘ Dariya suka yi su dukkansu ganin yadda Dr. '"‘ Ahmad ya Saki fuska babu alamar damuwa a yanayinsa ya sa Saudat ta saki jiki ta mike ta riko hannun Kausar tana fadar, “Bismillah‘ yar uwa mu shiga daga ciki mu gaisa sosai " Dr Ahmad ya mike shi ma tare da miqa wa Hamid hannu yana fadae “Ni ma abokina. mu shiga daga ciki gida na kula abin yar wariyar launin jinci ce”. , Duka dariya suka sa suka rankaya suka nufi cikin gidan Zuciyar Saudat fes, ba qaramin dadi tajiba Ganin yadda Dr. Ahmad ya karBi Hamid din cike da ‘ farin ciki. Ba Karamin mamaki‘ ta yi ba yadda Hamid ya samu labarin aurenta, kodayake auren da kullum sanarwa ake a gidajen tal'abijin da radiyo lallai ita kanta ta san ba Karamin matsayi Hamid yake da shi a Zuciyarta ba, har cikin ranta ta ji Kausar ta kwanta mata don kawai tana matar Hamid hatta rasa inda’za ta_saka ta, ta kawo mata wannan ta' kawo wancan har sai da Kausar ta dakatar da ita, ita kuma Shukura ta ci gaba da dawainiya da Hamid din. ' . Ba su suka bar gidan ba sai qarfe goma na dare don sai da suka gaisa da Momy da Alhaji . Ashiru sannan suka tafi a cewar gobe Hamid zai maido , Kausar gaskiya su duka sun yaba da ‘ matar Hamid din don ba qaramar kyakkyawar mace ya samu ba, wayayyiya kuma yar boko. ’ Ba Saudat ba hatta Momy da Shukura sunyi _ mamakin irin makudan‘ kudin da Hamid din ya baiwa Saudat wai ta. siyi abin da ta ke So, tunda ‘bai _ samuya siya mata komai ba. Lallai Hamid ya dauka Saudat da muhimmanci a rayuwarsa, haka da ma al’amarin Ubangiji yake .Washegari ita ta kama ranar asabar da misalin qarfe daya na rana aka daura auren " Saudat da angonta Dr Ahmad Mukhtar ; daurin aure ne wanda ya tara manyan mutane kala daban-daban tun daga gida Najeriya har zuwa sauran Kasashen qetara abbas daurin auren ya kafa tarihi a cikin Dandagoro ‘ Motoci suka dauki amarya da tawagarta zuwa gidan mahaifinta da ke Dandagoro don wai a can ne za,a dauki amarya, kamar yadda Alhaji Ashiru ya bukata ba don ran Momy yasoba ta amince Haka manyan motoci suka kwashi amare aka nufi gidan mahaifinta, amarya’ Saudat dake lullube 'cikin mayafl Kirjinta ya shiga dukan tara-tara don ba tasan irin tarbar da dandazon Jama,ar zasu samu a gidan nasu ba. Haka suka shiga cikin gidan mahaifiyar Shukura da DR murja qawar Momy na riqe da amarya har cikin gidan. Inna Laure da ke durkushe bakin murhu na ganinsu ta zabura ta mike tsaye tamkar sabon kamun hauka ' : Fuskar nan tata dukta gauraye da majina da ' hawaye saboda hayakin wuta ciki kaduwa take fadar, “Wannan dandazon haka fa sai kace na masu zuwa yaqi na menene? ' Dr Murja tace“Au maigidan naki bai Fada miki bane? To amarya ce aka kawo gidan ubanta a dauke ta a ciki”. ‘ Kida a ruwa mai tada haukan dodo tana fadar haka Inna Laure ta yo kanta da masifa, ‘ ‘Amaryar ukan abun uba za a kawo gidan ubanta, k0 ita uwar amaryar bata sanar muku ba ‘yar tata ruwa biyu bace? Ai ba ta da uba don haka an dai daura aure a gidan nan amma babu dan iskan da ya isa ya-shigo min gida don a ci min zarafi Mahaiflyar Shukura ta kwantar da murya ta ce, “Haba baiwar Allah meye kuma abin cin fuska don' dai kawai dan zaman da za a yi wanda bai =wuce na minti talatin ba?” Ai kamar jira ta ke ta koma kanta, “Ke rufe mani baki kin ji tsohuwar banza, ai da ma garin 'banza a farau-farau din wofi yake qarewa, gida dai nawa ne, kuma dole ku bar min abuna in ba haka "ba'wallahi sai in cinna wa gidan wuta mu hadu mu duka mu qone za ku fita k0 kuwa ba zaku fita ba?” Ai kafin wani ya ba ta amsa ta kwaso itacen da ke cikin wuta ta yo kansu * *‘ Malam Bala da ke kokarin shigowa cikin gidan ya yi wani kukan kura ya yi kanta ya rike ta ta 'baya, hakan ya sata fasa wani razanannen ihu tana kokawar kwacewa, ya murde hannunta ya na cewa [8:43AM, 06/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: YAR. TALLAH CHAPTER32 Complete Bakida hankaline ya kwace itatuwan tana ihu tana tirje~tirje da zuba ~ munanan ashariya ya danna ta dakinta ya kulle, ko,a haka aka barta ya ishe ta azaba saboda tsananin zafin da ake kwararawa a garin ga shi dakin ba shi da tagar shan iska k0 kadan ’ Malam Bala ya nufo su yana basu hakuri akan abin da Inna Laure ta yi musu, ita kuwa Saudat idonta na kan mahaifinta, za ta iya cewa tunda take da shi ba ta taBa ganinsa ya yi irin kayan da ya yi ba, saboda tsadadden yadin da ke jikinsa wanda aka yi wa dinkin yar ciki da babbar riga, kayan sun sha aikin hannu. Dr.Murja ce ta ja mayafin Saudat ta rufe mata fuska, wanda haukan da Inna Laure keyi ya sa ta budewaba tare datasani ba Malam Bala ya kwasa ya nufi dakinsa yana yana raWar jiki, sai ga shi ya dawo dauke da manyan tabarmi shi da kansa ya shimfida mnsu a tsakar gidan suka zazzuna shi ‘kuma ya juya ya gita baifi minti sha biyar ba sai ga shi ya dawn do. wasu almajirai dauke da ledojin pure water dana kwalayen ‘ ,lemuka katan-katan‘ aka jibga musu, ita dai Saudat ta cika da mamakin abin da kr faruwa sun kwashe mintina talatin a gidan sannan angwaye suka zo daukar amaryarsu don haka Shukura da mahaifiyarta suka tasa Saudat a gaba har zuwa zaure inda mahaifinta yake don ta roqi gafararsa. Saudat ta durkusa a gabansa jikinta ya yi sanyi ba ta san abin da za tace da mahaifin nata ba, abubuwan da suka faru ne a baya suke dawo mata cikin zuciya, tamkar a yanzu ne suke faruwa. Tamkar Malam Bala ya san abin da ta ke tunani, sai ga shi yana furta, “Don Allah don Annabi Saude ki yi hakuri ki yafe min duk abin da na yi miki wanda ki ka sani da wanda ma ba ki sani ba. Na san na zalunce ku sai dai~ na san sharrin shaidan ne, don Allah don Annabi ki yafe min kafin na mutu wallahi ban san abin da-zan cr da Ubangijina ba, tabbas na ga ishara a rayuwata, kuma na yarda zakaran da Allah ya da chara k0 ana muzuru ana shawo sai ya yi, Saude ki yafr min don Allah don Annabin rahma “sunyi mamakin yadda kuka ya ci qarfinsa ba suboda tun yana maganar muryarsa ke rawa, ba karamin‘ sanyi jikin Saudat ya yi ba jin kukan dattijon. nata don haka ba tareda zuciyarta ta qara tuna mata komai ba ta ce “Ka yi hakuri Baba, ni ban rike ka da komai ba, wallahi na yafe maka’ Cikin kuka Malam Bala yace ‘Wallahi ni “ ba kiyi min komai ba Saude, inma kinmin ba yafe miki Allah Ubangiji ya yi miki albarka, Ya ba ku zaman lafiya da zuri’ a dayyaba Saudat bata iya amsawaba, sai dai Momyn Shukura ce ta amsa sannan ta kama Saudat ta mike suka rankaya aka nufi mota da amarya , Masu kai amarya suka dunguma a motoci, amma abin mamaki sai ga wasu daga cikin jama’ ar , unguwar cikin masu rakiyar amarya babu goro “ ballantana katin gayyata Har motocin daukar amarya zata dags Malam Bala ya kwaso da sassarfa yana daga musu ‘ hannu, suka tsaya ya nufi motar da Saudat ke‘ciki, ta taga ya mikamata wani Kunshi a baKar leda. Ta karBa cike da girmamawa, sannan motocin , suka rankaya da amarya sai garin Abuja, alqawarin, Allah ya cika, don karfe biyu na rana a gidanta ya yi mata wanda yake a unguwar ‘yan majalissu. Saudat ba ta kasa gane gidan ba duk da kuwa canje-canjen da ya qara samu, haka suka rankaya Zuwa bangaren amarya, sai dai mucr barakallahu fihi, masha Allah don Dr.» Mariya ta murza naira wurin fiddo da ‘yar tata don haka‘ tsarin gidan zuwa tsarin kayan ya qawatar da falukan da aka zuba suka yi dace da juna, don komai an sa shi cikin tsari, don haka duk wanda ya je kai amarya sai da ya firgiga wai ahakan ma donyawancinsu sun saba shiga irin gidajen amma ‘yan Dandagoro kuwa sai ga su darshe a kan marbles suna ta faman zare na mujiya, Shukura dai na rike da amarya, Saudat wadda ta ke jinta tamkar a saman gajimare wasu daga cikin dangin ango ne krta faman dawainiya da su tun daga abubuwan ci zuwa na sha harna tande-tande irinsu dambun shinkafa dambun nama, shinkafar kaza, soyayyun kaji, farfcsun kaji, donut, meatpie spring roll, fried rice, hadadden salad chips din kwai da dankalin Turawa, fruits kala-kala har da wanda ba su taBa gani ba da sauran kwalayrn lemuka da robobin ruwa masu sanyin gaske. Saudat dai da ke cikin mayafi tana jin karadin Farida qanwar Ahmad don ta fi kowa kai wa da kawo wa an agama sallar la’asar motoci suka kwashe ‘yan kai amaryar don dawo da su gida bayan an cika su da sha tara ta arziki. Sai a lokacin kuka ya zo wa Saudat ganin duk za su watse su barta, Shukura ce ta rungume ta tare da yi mata rada, sai ga ta tana kuka da dariya, lokaci guda duka suka rankaya suka tafi suka bar Farida rungume da Saudat kowa ya watse Su Farida da wasu ma ’aikatane ke ta faman gyare-gyaren gida, sai ga shi cikin dan lokaci Bangaren nata ya zama very need, babu abin da ke fita a cikinsa sai qamshin room freshner mai sanyin Farida ta dawo bedroom din da Saudat ke ciki ta zauna gefenta cike da kulawa ta ce “Aunty Saudat ki shiga bandaki ki watso ruwa sai ki dauro alwala don lokacin sallar magriba ya yi”: Saudat ta Ki k0 motsawa haka kawai take jin gabanta na faduwa ba ta da wani kuzari. ’ Faridat ta yi murmushi tana fadar, “Ho Aunty anya wannan dari-darin da ki ke a cikin * gidanki zai fisshe ki kuwa?” Ta Kara murmusawa, “To yi hakuri dai muje na raka ki ki watso ruwan” . Ta sa hannu ta riko Saudat din don haka ta sauko daga kan gadon tana Kokarin bin qofar fita, Farida ta ce, “Ina za ki kuma? Ki shiga bandaki din nan mana dama don kar a Bata. mikine ya sa na ce su shiga wancan bandakin da ke dayan falon”. ' Saudat ta dan yi sororo don ita dai ‘a iya ganinta ba ta ga wata‘ kofar bandaki ba don tsakanin falo ma da bedroom gilas ne ya raba ‘ tsakaninsu, don haka duk cikin falon babu wata alamar kofa. , Faridat ta mike ta nufi wurin gilas din ta danna‘ yar wata alama sai ga shi ya raba kansa biyu ya fidda wata‘ yar hanya wadda ta zarce har cikin . bandaki Farida ta shiga ciki, don haka itama: _ Saudat ta bi bayanta. Farida ta gwada mata. yadda Zatayi amfani da komai na bandakin sannan ta fita dan ta samu damar watso ruwan ' Tana fitowa ta samu Faridat ta qara gyara gadon har ta ciro mata kayan da zata saka don haka Saudat ta nufi inda sallaya ta ke ta yi sallar magriba ta zauna, har lokacin isha ya shigo sannan ta yi sallar tare da shafa’ i da wutiri wadda Momy ta . koya mata tare da wasu daga cikin ayyuka na addinin musulunci tana idarwa ta mike ta nufi kan gado inda Farida ta ajiye mata kayan da za ta saka, wasu lallausan yadi ne kalar baki mai taushin gaske wanda aka kawata shi da wasu fararen duwarwatsu masu haske. Saudat ta saka yadin a jikinta Wanda aka yi'wa dinkin riga da siket yadin ya bi jikinta ya lafe a farar fatarta. Farida ta shigo tare da ‘yar siririyar -sallamarta hannunta na rike da wani madaidaicin faranti da ke dauke da ‘yan wasu kananan kwanuka ns tangaram. Ganin Saudat ya sa ta ta saki murmushi, “Yauwa Aunty Saudat k0 ke fa? Ki dan yi make up k0 ya ya ne Murmushi kawai Saudat ta yi ta nufl gaban ,dressing mirro ta ja kujera ta zauna tana kallon gaban madubin .wanda ke shake taf da kayan x kwalliya irin na wayayyun mata da suka san kansu. Body lotion kawai .Saudat ta dauka ta murjawa jikinta, sannan ta murza wa fuskarta wata yar karamar hoda wadda ta ida fito da tsabar kyawun fuskarta, sannan ta shafa wa laBBanta wetlips gloss, sai da ta Kara gyara gashin kanta ta dame shi da farin ribbon kwara guda ta sake shi a baya, sannan ta yi sassaukan daurin kallabi a kanta wanda ya Kara fito da ita, ta dauki ‘yan qananan ‘yan kunnayenta da sarqa na diamond ta maqala a kunnenta ta 'saka ‘yar qaramar sarqa ta dauki turarenta body spray ta mammatsa a‘ gaBObin jikinta, ita kanta ta san ta yi kyau irin wanda ke nutsar da zuciyar maigida, ta juyo ta nufo inda Faridat ke tsaye tana tattara ‘yan komatsanta. Muryar Saudat na rawa ta soma fadar,“ina kuma za ki je don Allah : naga kin yi lullubi kina tattara jaka?” Faridat ta mike tana kallonta da murmushi a kan fuskarta, “Maigida ya yi kira Saudat, amma fa kin yi kyau sosai, nasan yayana zai yaba don Allah kada dai a yi masa rowa". Tayi maganar tana dariya tare da shafar beauty point din Saudat din ta juya a gurguje ta fice tana fadar, “Don Allah ki ci abin da na hado miki, please Auntyna". Saudat da ke tsaye ta bita * da , idanunta masu kama da madara harta ta fice ba yadda ta iya haka ta sadakas ta koma da baya ta zauna a kan gadon nata wanda kr fitar da , sassanyan Kamshin bed freshner Ta miKa hannu ta janyo tiren da Faridat ta ajiye mata ta soma dudduba abin da ke cikin‘ yan kwanukan da kofinan, na farko gasasshen nama ne wanda ya ji kayan yaji, sai na biyu wani' irin nama ne Wanda aka yi wa 'wata irin dahuwa mai danko, sai' kofi na farko tsumin markadaddun ‘ya'yan itatuwa ne, dayan kuma danyar madarar shanu ce , mai kyau. “ Duk da ba ta fahimci amfanin abubuwan a gare ta ba, ta daure ta ci sosai kamar yadda Faridar ta roKa. Ta dauki tiren ta fice da shi ta mayar da shi a kicin da ke falonta na biyu, ta tsaya tana kallon kicin din, komai na ciki tsab.tsab gwanin kyau, ko falon wani mai kudin sai haka, don haka maimakon ta bar kayan a haka, sai ta soma tara ruwa ta wanke ’su cike da sha’awar komai na kicin din Ba ta ji motsin shigoWar mutum a kicin din ba sai dai ta ji an

Chapter 22 of 26