Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
koma asibitin Lokacin da rabiu ya gama koro masa bayani Mamaki ya kama, likita yace ynxu yarinya kamar Saude a kasa samun wanda zaiyi Jinyarta ‘ba shi da mafita haka ya. Rubuta masu sallama aka ba shi allurai da magunguna Ta ji sauki sosai, dukda ba Karfi jikinta sosai. Suna dawowa gidan laure ta watsar dasu watsar k0 kallonsu batayiba Rabi‘u ya dauki naira hamsin ya fita ya siyo mata shinkafa da wake da mai da yaji ya zauna ya ba ta ta ci sosai, .sannan ya ba ta magungunanta ta sha, ba ta jima ba bacci barawo ya sure ta, shi ma ya raba gefe ya kwanta Washe gari tunda safe laure ta hau tuyar waina markadan ma da kanta ta kai shi, mamaki ya kama Rabi’u to wa take tunanin zai daukar mata tallar wainar? Ba ta tankawa kowa ba har sai da ta gama tuyar . Wainar ta daddaura sannn ta mike ta nufi dakin da suke Saude ce kawai zaune tana shan ruwan shayi da biredin da Rabi’u ya siyo mata a waje. Laure ta tabe baki kafin ta ce, “Aikin banza harara cikin duhu da kuwa cikin babbar riga, saiki tashi ga tallar waina’ can na jiran ki idan kin gama Saude ta yi saurin dagowa tana kallonta idonta ya kaWo kwalla Laure ta daka mata tsawa. Ko ba za ki tallar ba ne kika noqe kika kwalala min“ Wasu ‘yan iskan idanuwan ki can masu kama” ; Dana kwarkwata, maza ki taso ke nake jira.” Ta saki labulan ta juya ta yi gaba abin ta. Hawayen da suka taru a idanuwan Saude suka ziraro suka biyo kuncinta take shayin ya fita daga ranta ta ajiye ta mike ta flto har a lokacin babu Karfi ajikinta, donji take tamkar iska za ta dauke ta. Inna Laure ta miko mata tiren wainar tana fadar, “Ga ta nan ta Murtala goma ce ki kawo min kudina cas ban ceki Batar min da k0 sile biyar ba.’ Saude ta duqa ta dauka tana sharar kwalla, Rabi’u daya shigo ya sauke jarkar ruwan da ke kansa yana kallonta jikinsa a sanyaye ya ce, “Ina kuma zakije keda bakida lafiya?" , Laure ta hayayyako masa -“To marar kunya ga kai ga fata ai ba a tambayar me aka yanka k0 idon ka bai gane maka talla ta dauka bane?” Rabi’u ya hadiye abin da ya zo masa iya wuya ' kafin ya ce “A gaskiya daukar alhakin zai yi yawa, yarinya daga sallamo ta daga asibiti jiya, yau kuma a daura mata talla gaskiya da sake ai ba ita kadai ba ce diya cikin gidan nan ba, ita ma ‘Yar Baban ai ta isa tallar a dora mata mana k0 k0 ita kadai ce diya, amfanin nawa ake mata a cikin kudin tallar?” “Eh lallai wuyan ka ya isa yanka, tabbas wato kai nan har girman ka ya kai ka fada mini magana. To ubanka ma ya yi kadan ballantana kai, uwarku ma ba ta yi min wahalar kawarwa ba ballantana kai qaramin kwaro tallar za ta tafi idan ta tafi ka hanata Rabi’ u ya ce, ‘In dai cin zalin dan wani wani abun a zo a gani ne ai sai a yi mu gani idan abun na tsakani da Allah ne ni me yasa ba za ki dora mini tallar ba sai ita mace?” Ta zaburo ta yo kansa tana fadar, “Kai kar fa ka yi min rashin kunya kaji bari ganin ka ka kawo Karfi wallahi hakan ba zai hana in dake ka ba, wallahi wancan faskaren zan sa maka dan iska kawai. Bari uban naka ya zo in ji idan shi ya sanya ka kai min rashin kunya idan kuma wani ke zoga ka sai in ji.” Rabi’u ya qure ta yana fadar, “Ai wallahi na gama zama wata Katuwa ta dake ni yanzu tunda na gane abun duk rashin kunya ne dan an ga babu uwarmu a gida don haka nima zagewa zan yi yanzu mutum na dukana ina Bare masa kai sai dai a kwashe shi a sume wallahi.’ Laure ta saki baki tana kallonsa cike da mamaki, yaushe yaron nan ya zama haka? Yaushe ya koyi ' rashin kunya irin wannan? Lallai dole ta dauki ' mummunan mataki a kansa. Bayan sati daya da sallamar Saude daga asibiti da maraice ta dawo daga tallan alala, tana ajiye tiren Inna Laure ta mika mata tsintsiya tana fadar, “Maza ki share gidan nan ki dora sanwar tuwo da miya ki yi Wanke-wanke.” Saude ta amsa da , ta dauki tsintsiyar ta share gidan tas sannan ta dora sanwar tuwon ta tafi tana wanke-wanke, Rabi’ u ya yo sallama ya shigo, Saude ta bi shi da kallo duk ya yi gaje-gaje yana rike da bakar leda Saude ta yi masa sannu da zuwa ya amsa cike da kulawa, sannan ya wuce ya shiga dakinsu. Sannu a hankali Saude ta kammala ayyukanta saboda ciwon qirjin da ya addabe ta. ‘ Ta nufi dakinsu a gajiye ta kwanta tana faman numfarfashi da kyar, Rabi’u ya tsura mata idanuwa gaban shi ya yi wata masifar faduwa ganin yanda alamun girma suka fara tsirowa daga jikinta, tabbas girma ya fara zuwar mata ya zame masa wajibi ya zage ya nemi kudi ya hadiye wani yawu mai daci wanda ya tsaya masa a makoshi, sannan ya janyo ledar da ya shigo da ita ya miqa mata, ta amsa, ta mike tana dubawa. * Kayan makaranta ne riga da wando da hijabi, dadi ya kama Saude cike da zumudi ta ce, “Yaya nawa ne?” Kai kawai ya daga mata ta mike cikin zumudi za sanya Rabi’u yayi saurin hanata yana fadar, ‘Kar kisa karki sakasuyanzu.”Tazumburo baki tana fadar “Kaidon Allah gwadawa fanyi Harareta kafin yace. “Ba dai anan ba, idan gwadawa zakiyi fita tsakar gida sai ki gwada.’ Ta narke masa. “Kai don Allah Yaya saboda me?” Rabi’u ya zuba mata ido kafin ya ce ‘Wai ke ba ki san kin girma ba ne wai har yanzu ?” Saude ta yi saurin kallon kanta kafin ta ce, “Ni din na girma Yaya?” Ya ja wani dan gajeran tsaki ya koma ya kwanta ya juya mata baya. Saudc ta zauna kusa da shi tana fadar, “To yaushe za ka kai ni makarantar Yaya?” “Gobe da safe.” Ya ba ta amsa ba tare da ya kalle ta ba. Ta yi wani ihun murna. ta kwanta gefen shi kanta saman kafadar shi tana fadar. “Wallahi harna qagara goben ta yi Yaya, in gan ni a makaranta. To wai kuma Yaya me za a koya mini?” Rabi’u ya juyo Ya ja kunnenta yana fadar, “To sarkin tambaya, bari in kin je kya gani, barci nakeji karki matsa mini da tambaya ki Juya ki kwanta kawai Saude tace Ai ba ka ci abincin ka ba.” Jeki“ ‘ dauko idan ta gama . . kwasan nina koshi Ta dan zuba masa ido ‘To me kaci Ya zaburo mata, “Kin ga tashi Kije kin. ji, ban san yawan tambaya.’ ldonta ya ciko da hawaye, muryarta a sanyaye tace “To yanzu da yunwa za ka kwana kenan'?" “Oh! Kaina Saude na ci abinci, naci abinci naci abinci a waje haba." Ta yi wani takaitaccen murmushi sannan ta juya ta fita. A bakin murhu ta iske nasu abkin murhu a Wata danéakaiiiyw lmga wadda ta gaji d1 Salan gandi taga tuwon wanda bai wuce cin mutum daya ba, shi ma ba dan ya qoshi ba. Haka Saude ta ta koma daki ta cinye tas sannan ta fita ta maida kwanon ta dauro alwala ta dawo daki ta yi salla sannan ta kwanta Washe gari tunda safe Saude ta yi Shara ta kai markade, ta dawo sannan ta debo ruwa cikin rijiya ta rafta tayi wankanta babu soso babu sabulu, ‘ tana gamawa ta fito ta nufl dakinsu Laure na kallonta bata dai tanka mata ba, sai Ma tsakin da take ta faman ja akai akai. Saude ta dauki kayanta ta sanya sababbi tas sun mata kyau sosai, Rabi u da ya dawo daga dibar ruwansa ya shigo yana kallonta cike da sha’awa yace“tace yya nayi kyau Yace eh mana Saude ai ke kyakkyawa ce ”Ta kada kai tana fadar, “Amma kullum mutane sai su rinka ce mini Kazama mummuna har yaran unguwar nan wai ba za su yi kawance da niba, sai dai da ‘Yar Baba, wai ita ce Kawarsu mai tsabta, ba ‘yar talla ba, amma Yaya ai ka ce ina da kyau k0?” Tausayinta ya kara kama Rabi’u, yaji tamkar zai mata kuka ya daga mata kai alamar eh, babu alamar kuzari a jikinsa. Saude ta sanya takalmanta sannan ta mike ta dube shi. “Taso mu jc Yaya, kada rana ta yi.” _ ‘Rabi’u ya mike suka fita yana riqe da hannunta zuciyarsa cike da tausayawa. Laure da ke zaune saman kujera ‘yar tsugunne gaban murhu tana qukkulla waina, ta ga sun fito, ba ta san lokacin da ta ture tiren ba ta tashi tsaye idonta a warwaje tana fadar. “Me nake gani ni Laure, me zan gani haka?” Rabi’u ya kafa mata idanuwansa kafin ya ce “Makaranta zan kai ta baki gani ne kayan makaranta ne a jikinta." ‘ ' Laure ta ce, “Karya ka ke wallahi idan ka ga Saude ta yi makaranta to ba na numfashi ne, don har abada ba za ku taBa morar‘ rayuwar duniya ba, in dai ina raye kuma Saude talla za ta yi min ban yi niyar ta yi karatun bokon ba, wato abun ma ya zama gasa kenan, tunda an sa ‘Yar Baba kai ma bari ka kulla ka sanya ta. To ba ka isa ba wallahi ka yi kadan ka nuna mini iyakata ban ga bayan ka ba kowaye kai wallahi.” Rabi’u ya gifta zai wuce yana fadar, “To sai ki gayawa kaji dan su tantabaru tashi suke." Laure ta sa hannu ta riko Saude da qarfi tana fadar qarya ka ke wallahi ba za ka kai ta makarantar ba talla za ta yi min yau sai na ga qarshen danyan kanka ba dai kai dan rashin kunya ba ne. Rabi’u ya ce “Sakar ta kar ki karya ta, tunda ba ke ki ka haife ta. ba, ba ki san ciwon taba.” Laure ta ce, “Aikin banza ruwa biyun k0 ka manta nan aka karma uwarku da kwarto cikin daki?’ Ai dama shi dan zina har abada bai ganin kowa da mutunci, dan iska dan asara.” Bakin ciki ya cika Rabi’u zuciya ta zo masa iya wuya cikin Bacin rai ya ce ‘Wallahi ni ba dan asara ba ne kuma uwarmu ba mazinaciya ba ce face ke ce babbar la’ananniyar da ki ka tura mata sharri, kuma insha Allahu a sauna sai sharrinki ya qare Tun kafin ya rufe bakivLaure ta share shi da wani gigitaccen mari mai kummatar da qaramin yaro cikin zafin nama Rabi’u ya. dago Zai shara mata nasa marin ya ji an rike hannunsa, cikin Bacin rai Malam Bala ya shiga dauke shi da nashi marin hagu da dama. , Rabi‘u ya dafe kunci da baki wanda tuni har ya fashe jini ya kwararo cikin qunar zuciya Malam ke Lol ya abin ya kene mu kubiyonii donjin ci gaba sannan idan naga comment da yawa dan anjima xan iya sake muku post. [1/17, 7:44 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/17, 7:48 AM] A A Dboy: *YAR TALLA* *CHAPTER 10* Dan iska wulakantacce Allah ya tsine maka Rabi’u ban ga amfanin rayuwar ka ba. Yanzu uwar taka ce za ta mare ka har ka daga hannu za ka rama, don kana marar kunya lalatacce. To bari in tsine maka ka je can ka Karasa lalacewar ka tunda kai din ba dan mutunci ba ne, yaro jinin sunna ya yi haka alhalin kana dan iska kishiyar uwa ba uwarka ba ce, k0 k0 hudubar da uwar taka ta tafi ta bar maka kenan? In ban da na shigo da yanzu marinta zakai da gaske, « don kana marar kunya.” Laure ta sa kukan munafurci tana fadin, “Kuma Malam wai kan abin da bai taka kara ya karya ba yaron nan ya dinga marina har yana fadar shi zai zamo ajalina wai dan kawai na ce bai kamata ya sanya Saude makaranta ba da kan shi ya bari har ka zo ya yi maka magana. Shi kenan yaron nan ya shiga zagina ta uwa ta uba wai har: yana fadar shi zai zamo ajalina....” Ta Kara fashewa da kuka, ‘Wallahi Malam bazan iya zama ba, yaron nan ya kashe ni a banza a woli ba, wallahi tafiya ta zan yi in bar masa gidansu tunda yana da gaskiya gidan ubansa ne Malam ya ce ‘Da alla bar' wannan magamar Laure kar ma ki ja yaron nan ya Kara raina ki gidan ubansa da wa ya fada masa, ina uban nasu yake nan yaranda akaimin wuru-aka manna min tsiya~ Ya juya yana kallon Saude da Rabi’u yana fadar, “Baku sanibane koba a taba fadi maku bane kama uwarku da kwarto Kiri-kiri akayi iyayenta suka koreta dalili kenan tabarku tatafi yawon karuwanci yace wlh kukaci gaba da takuramin ko matata a shirye nake dana koreku daga gidannan Rabi’ u ya riqo hannun Saude suka nufi dakinsu suna: shiga ya jingina kansa da bangon daki yana wani irin kuka maicin zuciya. Itakanta Sauden kukan take yanzutafara fahimtar suwayesu dakuma matsayinsu acikin gidan duk da qarancin shekarunta hakan bai hana ta fahimci dalilin tsanar da ake masu ba tasa hannunta ta riko hannun Rabi’ u tana fadar “Wai Yaya da gaske ne abin da aka fada? Yaya da gaske mahaifiyarmu karuwa ce mu ma bamu da iyaye?” Rabiu: ya waigo yana kallonta hawaye sun gama bata masa fuska ya Kara riko hannunta yana girgiza Ya girgiza mata kai cikin muryar kuka ya ce, “Karki soma wannan tunanin Saude nasan kowacece mahaifiyarmu don ni na rayu da ita :nasan kowace ce ita, ita din mutuniyar kirki ce knma ‘yar manyan mutane. Saude ta ce, “Yaya idan har mahaiflyarmu mutuniyar kirki ce to me yasa ta watsar da mu ‘yan uwanta suka guje mu ta bar mu mu kadai mina rayuwa cikin qunci da wahalar rayuwa?” Rabi’n ya ce, “Saude mahaiflyarmu na son mu kamar yanda kowace uwa ke san danta, dole ce ta dolece ta rabata damu badan tasoba kiyi mata uzuri Saude duk qunci da wahalar da ki ke ciki bai kai wanda ita . ta shiga ba.” . Saude ta ce, “To,amma ” Ya daga mata hannu da sauri alamar ba ya san jin abin da zata fada, sannan ya juya ya fice ya bar mata dakin Wani kuka ya qara zuwar mata ta kwanta ta ci gaba kukan abinta. tanajin zuciyarta. na suyakamar garwashi,yamaza ai Rabi’u yace mata qarya ne abin da su Baba da Laure suka fada a , kan mahaifiyarsu alhalin almomi sun nuna gaskiyar Shin idan har mahaifiyarsu tana son su me yasa ‘ ta tafi ta barsu babu k0 waiwaye? Shin idan mahaifiyarsu mutuniyar kirki ce me yasa ‘yan uwanta suka kore ta? Shin idan har ta tsare kanta me Zaisa mahaifinsu ya zargeta harya kyamacesu da zama yayansa? Tambayoyin data jeroma kanta kenàn Wanda bata da mai amsa mata su 1 page is missing am sorry ya farkar da ita, don haka ta dauki kayan ta koma gida babu cinikin ko sisi. K0 da ta maida alalen Laure ta yi ta masifa, tun fadar, “Na lura mugunta ce kawai yau ki ka sa mini kuma ‘yar iska ke zata karewa a je min kayana ki.’ wuce Saude ta samu ta ajiye kayan ta yi daki da hanzarinta, don dama barci ne fal a cikin idonta ta samu ta kada kafadunta ta kwanta, wani bacci mai nauyi k0 ya yi awon gaba da ita. Inna Laure ba ta ba su alalan ba sai da gari ya ' waye a lokacin ta lalace sannan ta miqo masu ita waisu karya da ita. Rabi‘u ya kai ya zubar ya ciro kudi ya siyo masu koko da qosai suka karya, sannan ya tafi wurin aikinsa, Saude kuma ta tafi talla. Da yamma likis Saude ta dawo daga talla, Laure ta ba ta dakan kunnun jego wanda ta karBo a makotansu da akai haihuwa, kawai saboda neman suna, shishshigi cusa kai ba kwarjini. Saude na cikin dakan ta debi gyalenta ta fice ita da ‘yarta. Suna fita Saude ta ajiye dakan ta kwanta bakin turmin tana hutawa a lokacin Rabi’u ya dawo daga ‘ wurin aikinsa shi ma ya kwaso gajiyarsa ya zauna kusa da ita cikeda tausayawa ya ce, “Sannu ya jikin na ki ne?" Saudc ta ce, “Da sauqi sai dai ciwon kirjin da ya matsa mini yanzu." Rabi‘u ya ce, “Allah ya sauwaqe karbi wannan bari inje chemist na siya miki magani." . Saude tayi saurin sa hannu ta karBa tana: dubawa leda ce baqa guda sai farar leda guda. Ta bude: soyayyar doya ce da kwai a ciki, dadi ya kama ta yauzu: itce zata ci doya da kwai. wanda tunda take a duniya bata taba cinta ba. Ta yi saurin kallonsa da Washe fuskarta tana fadar. “Wayya Allah na Yaya, yau zan ci doya, tunda nake fa ban taBa cin taba wallahi.” Rabi‘u ya yi murmushi yana kallon ta, sai da ya tashi zaibar wurin sannan ta bude baqar ledar. Ta yi wani tsalle ta tashi tana fadar. “Wayyo dadi, Yaya kayan kwalliyana ne?" Ya daga mata gira, ta buga wani uban tsalle ta dafa shi taba fadar. “Wayyo Yayana na gode kwarai wallahi dama ina so nima in rinka lrin kwalliyar su ‘Yar Baba, inyi; kyau k0 Yaya?” Ya daga mata kai alamar eh, tasa dariya ta ciro madubi tana kallon kanta tana ta faman gwalegwalen idanuwa. “Kai Yaya wai dama haka nake, Yaya kalli idanuwana ‘yan qanana-qanana, yanzu kuma Yaya wannan bakin nawa har cokali yana iya shiga ciki?" Ya buga hannun shi saman tafin hannun shi alamar oho tayi daria Tace yaya ji haqorina har yayi tsaho da yawa' Rabl'u ya kwace madubin yana fadar, “Ke tashi kiyi aikinki saude ta shagwabe masa “kai Yaya don Allah ka bari in gani wallahi ban gama ganiba Rabiu ya saka madubin cikin ledar yana fadar, “Idan kin shigo dakin kin gani ai naki ne bana: wani ba, kin ta gani harki gaji. Dauki doyarki ki ci kinji Ta ture doyar can tace tana turje-turjen qafafuwa, Rabi’u ya dauki doyar yana fadar, “bazakici ciba ke nan to bari in cinye abuna dama ba qoshi na yi ba rago miki.” nayi Saude ta yi saurin riqo rigar shi tana fadar. ‘Yi haquri' don Allah ka ba ni :na daina.‘ Rabi’u ya sakar mata ya wuce yana dariya, ta zauna tana ci tana lumshe ido har ta gama, sannan ta mike ta ci gaba da dakan yajinta iya qarfinta. Ta samu ta gama, sannan ta wucc daki ta janyo kayan kwalliyan tana duddubawa, ta zauna ta manne fuskarta radau da kwalliya abin kada sabon shiga, duk ta yi wa fuskarta dame-dame man da kwalli Washe gari ma tana gama sallar Asuba ta janyo kayan kwalliyar ta hau ranbadawa a fuska, shi dai Rabi’u yana zaune yana kallon ikon Allah. Tana gamawa ta mike ta nufo shi tana fadar. “Yaya duba ka gani wai nayi kyau?“ Rabi‘u ya yi wani takaitaccen murmushi kafin yace. “Sosaima, don sai yanxu na Kara tabbatar da kamar ki da Mamar mu daya, sak kamar an tsaga kara wallahi.” ' Saude ta gyara zama tana fadar, ‘Wai Yaya don Allah ya Mamarmu take, baqa ce k0 fara k0 doguwa k0 gajeriya?" Rabi‘u ya yi murmushi kafin ya ce “Mamanmu fara CE fat don har ta fiki . kuma doguwa ce mai Dan jiki kadan, yadda. Kika ganki haka take.” Ta ce “To yaya tana son mu?" Rabi‘u yace, “Sosai ma kuwa don ranar da zata rabu damu tasha kuka fitar hankali keko saida a kai da gaske sannan aka Banbare ki daga jikinta kina ta tsalla ihu a lokacm kina da shekara shida a duniya.” Saude ta yi wani murmushi kafin ta ce “To Yaya yanzu tana ina?” . Ya girgiza mata kai yam: fadar, “Allahu a‘alamu." Ta dan yi jim kafin ta ce “To Yata tafitabar mu?” me akai mata? Kafin ya kai ga ba ta amsa Inna Laure ta hankado labule tana fadar, “To tif da taya ‘ talla sai a tashi a tafi tallah hakanan Saude ta mike cike da alamun gajiyawa a fuskarta ta fice ba dan ta so ba. Ta tafi tallar da ta zame mata waki’a farilla. Da daddare ciwon mara hade da ciwon ciki mai tsanani ya rufe Saude tamkar ba za ta kai ba, ta ringa murkususu a tsakar daki ita daya a lokacin Rabi’u bai dawo ba. Laure na jin ta, amma k0 ta kula ta kanta. Haka Rabi’u ya dawo ya same ta hankalin shi ya yi masifar tashi, ya juya ya koma ya siyo mata magani ya ba ta, amma a banza, sumanta biyu cikin dare. Yanda suka ga rana haka suka ga dare daga ita sai Rabi’u cikin daki babu wanda ya leqo balle ya ji halin da take ciki, don Malam ma bai san abin da suke ciki ba. Cikin ikon Allah ana kiran sallar Asuba, jini ya zowa Saude, a take kuma ciwon marar ya dauke, don haka ko motsi ba ta iya yi ba daga inda take ta kwanta sai bacci mai nauyi ya dauke ta. Sai a lokacin Rabi’u ya samu kwanciyar hankali ya tisa ta a gaba ya rabka uban tagumi yana kallonta hawaye masu zafi suna biyo kuncinsa zuciyarsa ta cika da tausayinta, har gari ya fara haske sannan ya “farka ya mike ya je ya yi sallah ya dawo ya samu ya dan kwanta saboda baccin dake cike cikin ldanuwansa. Cikin barcinsa ya ji tamkar ana rabka sallallami, Rabi u ya bude idanuwansa da su kai masa wani irin nauyi saboda bacci, ya ga Inna Laure na fadar “Malam! Malamll zo ka ganewa idon ka ikon Allah Malam zo ka gani.” Malam Bala ya fito daga dakinsa yana fadar, “Ni ko kinsan bansan irin wannan kiran natashin ”hankali.” Laure ta qara hankade labulen dakin sosai tana fadar, “Ai wannan idan ma akwai abin da yafi tashin hankali to shi ne dubi yarinyar nan Saude kalli siket dinta.” Malam ya qara tura kai cikin dakin tsawon wasu ‘yan sakanni kafin ya ce ‘Kamar jini nake gani Laure?” Laure ta turo wuya gaba tana fadar, “To duba da kyau jini ne daman tun jiya nake jin ihun yarinyar nan na dauka wani iya shege ne ashe yaron nan ne ya haike mata.” Gaban Malam ya yi wata mummunar faduwa ya juya yana kallonta a razane bakinsa na fadar, “Ki bari don girman Allah.” Laure tabe baki tana fadar, “Ga alama nan.” Idanuwan Rabi’u suka yo waje don sai a lokacin ya lura da yanda jini ya Bata siket din Saude sosai kamar anyi Barin manja a jikinta abin kaga kaya masu haske da santsi, hankalin shi ya yi masifar dugunzuma. Malam ya ce “Lallai kam yaran nan ka cika la’anannen Allah yau kam sai na gwada maka irin nawa rashin imanin ni za ka jawa abun kunya, ka yiwa qanwarka fyadeee dan iskan to wlh daga rana irin tayau ka gama haikewa ‘ya’yan jama’a.” Ya juya a zafafe sai ga shi ya janyo wani qaton faskare, Laure ta riqe tana fadar. A,a don Allh kayi haquri Malam karka kashe shi.” Malam ya goce yana fadar, ‘Wallahi yau sai dai akwashi gawarsa cikin gidannan inya so nima a kashi yayi kukan kura gamida yin kansa da faskaren Wooooohoho jama,a wai ya abin yakene mu kubiyo ni donjin yaddah wannan taqaddama zataci gaba da kayawaaaaaa [1/17, 7:49 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/17, 7:54 AM] A A Dboy: *YAR TALLA* *CHAPTER 11* ya janyo wani qaton faskare laure ta riqe tana fadar. a a dan Allah ka yi hakuri Malam kar ka kashe shi.” ° Malam ya goce yana fadar, ‘Wallahi yau sai dai akwashi gawa'rsa cikin gidannan inyaso nima a kashe ni.” Ya nausa cikin dakin ya hau Rabi’u da duka kamar Wani zautacce, bakin ciki, mamaki da tsantsar tashin hankali su suka hana Rabi'u komai saidai kare kansa da yake, sai da yaga Malam makasar sa yake: nema sannan ya mike ya yi waje Hayaniyar su ce ta tayar da Saude daga baccin da take, ta tashi sai zazzare idanuwa take, don ita ba ta San abindake faruwaba,taga dai Malam nata faman shan kwalla yana dukan Rabi’u ta tashi itama cike da . tashin hankali kafin ta motsa ‘ Rabi’u ya ruga malam ya bi shi har , “Sai na kashe ka la’anan nan Allah, Allah ya isa tsakanina da kai, wallahi kar in sake ganin ka cikin *gidan nan, kai cikin garin nan ma idan ka bari muka hadu sai na halaka ka munafukin Allah.” Ya juyo ya dawo gidan ya tattara masa ‘yan zummokaransa ya fito kofar gida ya watso su yana fadar, “Ka san inda dare ya yi maka, ka ji na fada maka, Allah ya yi wadaran ka, yasa ka hadu da mummunan hatsarin da za a kasa gane ka, Allah ya wulaqanta ka yanda kai min Allah ya yi maka wanda . ya fi shi, dan iska. Insha Allahu sai ka wulakanta, Allah ya daga maka hakali ya hana nutsuwa a duk inda ka ke” Laure ta fito tana fadar, “Don Allah Malam ka shigo gida haka nan tun'da dai ka kore shi ka ga har ‘ mutane sun fara taruwa.” ' Malam Bala ya dawo gidan ya ci gaba da 'zazzaga masifa tamkar wanda ba ya cikin hankalin shi, Saude dai na kallon su kuka kawai take tamkar ranta zai fita, ga jinin da ya bata mata jiki wanda har a lokacin bai daina zuba ba Ta lallaba ta mike ta saka hijabinta ta fito wajen tana neman Rabi’u can ta hango shi zaune saman dakalin Kofar gidan Malam Akilu mai Rauhanai ya hada kan shi da gwiwa da ‘yan kullin tsummokaransa a gaban shi. Wani sabon kuka ya Kara kwacewa Saude ta nufi inda yake tana kiran sunan shi, Rabi’u ya yi saurin dagowa yana kallonta fuskar shi sharbe-sharbe da hawaYe, ya yi mata nuni da hannu ta Karaso inda yake. ' Saude ta karasa ta durkusa gaban shi ta fashe da 'wani irin kuka mai ban tausayi, tausayin kansu ya kara kama Rabi’u ya samu da kyar ya iya tsaida nasa kukan, muryar shi a dakushe ya soma magana ba tare da hawayen sun daina zuba daga idanuwan shi ba. “Saude kin ga yanda Allah ya yi damu kuma k0? , Ki

Chapter 4 of 26