Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da saba,in ake saida ita Cikin sanyin jiki nace yabada kudin babu kuma vata lokzaci ya qirgo kudi a aljihunsa ya _ mikamin nakirgasu naga sun cika sannan najuya nasoma tafiya.Saidaifa inda gizo ke saqar bansan gidanwa zannufaba, gadai kudi ahannuna ammabanda wurin zuwa don haka najana zauna asaman wani' dakalin dake wajen kasuwar na kira mai abinci na .siya na ci na qoshi, na sha ruwa na ci gaba da kallon titi, wannan mota ta wuce, waccan ta wuce a haka fa aka yi sallar magriba da isha, dare ya soma duk ina a zaune a nan fa fargaba ta fara shiga ta. ‘Banyi auneba naji andafani,harna dan firgita ashe mutumin dana siyarwa waya ne. ya zauna a kusa da ni yana tambaya ta, “Wai lafiyarka kuwa Rabi’u?” Jin ya kira sunana ya sa nayi saurin kallonsa, sai a lokacin na shaida shi ashe Yasayyadi ne dan dan oganmu wanda nake aikin Kasa a wurinsa. To in takaice muku nan na sanar da shi halin da nake ciki, na korata da mahaifina ya yi har tsintar wayar da nayi. Ya yi matuqar tausaya min, a nan yace in tashi mu tafi shi zai taimake ni. Yasayyadi ya kai ni shagonsa da yake kwana wanda ke like jikin gidansu ta waje nan na ci gaba da zama, kwanana uku Yasayyadi ya ba ni shawara da na fara sana’a, ni ma ya ga kamar masu shi go da shinkafa a Kasar nan suna samu k0 zan fara? Na amince, ya hada ni da wani abokinsa muka fara safarar shinkafa daga qasar Nijar zuwa Najeriya da ma ina da jari a hannu. Allah Ubangiji kuma ya sa min albarka, sai ga ni cikin fan kankanin lokaci na tara kudi masu kauri a hannuna, a lokacin ne na sanar da Yasayyadi ina son. shiga makarantar boko, shi ma ya yi na’am da shawarata, don shi a lokacin yana shekarar Karshe ta kammala digiri. Shiyayi duk wanicuku- cukun da akeyi na hada takardun firamare natafi js3 kaitsaye cikin yan watanni nazana. JSCE sannan na wuce SS one na maida hankali sosai a karatuna, wanda bai hana ni neman kudina ba. Abin ma kamar harda sa hannu don duk abin da na taba cikin ikon Allah sai ya zama kudi, a haka naci gaba da karatuna zan shiga aji biyar na tsallake na wuce aji shida. Ina kammalawa na zana jamb na yi sa’a kuwa na bugo point din da ake so, wato 200 point don haka ban " samu wani matsala ‘ba wurin samun admission a Umaru Musa ‘Yar 'Aduaa university suka ba ni Mass Com na soma karatuna cikin nasara ina level 2 na fara shigo da motoci daga waje zuwa Najeriya a lokacin ba zan rasa jarin da ya wuce naira miliyan ashirinba, don harnafara aje yara suma sunaci a qarqashina nayi gida nayi mota na tashi daga gidan su Yasayyadi na koma. gidana, a lokacin shi ma ya yi aure ya samu aiki da hukumar zabe ta qasa yana zaune da matarsa a lokwas din kofar: Maruba. A lokacin da na gama digirina aka turani garin Lagos in yi sabis dina, na tattara na tafi watana biyar aka bamu hutu naxo gida mahaifina ya sakemin korar kare a karo na biyu nanna bada sakon' kaya da wayagidan Inna mai danwake a ajiya miki' na juya na tafl ina kuka jin wai an tura ki aikatau, kwanana biyu na koma Lagos. A yanzu haka yau satina guda da kammala sabis dina inda na samu saqon tashin hankali, wai Allah ya yi wa Yasayyadi rasuwa, mutuwar ta gigita ni ba kadan'ba, don haka na dora wa kaina nauyin kulawa da iyayensa kasancewar bai taBa haihuwa ba, sai ga sakon kuma farin ciki ya same ni, wai mahaifiyata .da qanwata sun bayyana, wallahi farin cikin da na tsinci kaina bazai misaltu ba”. Saudat ta cce “Allah sarki yayana ka sha wahala, kuma ka samu duniya, shi ya sa na ga ka zama wani dan lukuti”. Duka suka sa dariya sannan Saudat ta ba shi labari tun daga ranar da ya tafi har ya zuwa aurenta.da Dr. Ahmad, Rabi’ u har kuka ya yi saboda tausayinta, don haka ya ce Dr. ya yi musu .alfarma gobe su je Dandagoro ya ga mahaifinsa, kuma ya ga Hamid; Dr. ya amsa da Allah ya kaimu sannan ya mike ya yi musu sai da safe. Momy ta ce “Au dana. 'zata a nan zaka kwana?" Dr. ya dan yi murmushi tare da fadar, Momy na riga na yi bukin a Katsina Hotel". Momy ta ce, “Amma da ka daure ka kwana Ahmad Abbanka ba ya qasar k0 Bangarensa ba sai ku sauka ba?” Ahmad ya ce, “Ayi haquri dai Momy? da safe zan dawo” " Ta ce, “To Allah ya kai mu” Ya amsa da, “Amin” Ya yi wa Rabi’u sallama ya fice. . Saudat ta sabi takalma ta bi shi da‘ zummar suyi sallah; yana tsaye bakin motarsa har ta Karaso ya bude mata qofar motar yana fadar, “Muje Saudat, wallahi na yi bala’in gajiya”. ‘ Saudat ta waro ido, “Muje fa kace Yallabai? Haba don Allah, ni gaskiya bazan iya binka ba”. ' Dr. ya zuba mata ido a raunane yana fadar, “Kin yi min adalci ke nan Saudat? Kin san dai a ‘ yanzu ina buKatarki kusa dani, ki tuna fa tsawon lokacin da na dauka ba mu tare”. ‘ Saudat ta langwabe kai a shagwabe._ tana , fadar, “Allah YallaBai ni dai kunya nake ji, kuma yau dai daya don Allah ka barni in gaisa da dan uwana". . Dr. ya kada kai tare da fadar, “Shi ke nan Saudat sai da safe”. Ya juya ya fada motarsa ya ja ta a hankali ya fice, zuciyar Saudat ta yi matuqar rauni sai dai ba zata iya yin abin da yake son ba, tajuya ta nufi cikin gidan ta ja ta zauna suka dasa hira da Yaya Rabi’ u da " Momy wadda da ta gaji ta mike ta shige dakinta ‘ Amma su kam yadda suka ga rana haka suka‘ , ga dare, sai da aka kira sallar asuba sannan shi ya tafi ~ , masallaci, ita kuma ta nufl Bangarenta in da ta dauro' alwala ta yi sallah, kana tahau kan gado ta kwanta. Sai dai ta kasa runtsawa, tunanin halin da ta jefa mijin nata a jiya ya tsaya mata a zuciya, ta lura tamkar fushi ya yi da ita don haka ta lalubo wayarta ta soma rubuta masa saqo kamar haka. ‘Tuba nake mai gidana, banji dadin abinda nayi makab wallahi yanxu haka ina kewarka kamar yadda kake kewata, ina bukatarka fiye da yadda kake buqatata, saboda a duk Iokacin da nake manne dakai sai injini na zama kamar wata tauraruwa,a cikin taurari Tana gama rubutawar ta yi murmushi tare da tura masa saKon ta koma ta kwanta, sai dai k0 minti biyu ba a yi ba sai ga amsa ta shigo, ta yi dariya don ta san da ma za a rina ta jawo wayar ta soma karantawa kamar haka. ‘A kodayaushe ki dinga tunawa ke daban ce a cikin duniyata, erro lets go am sorry plz Saudat ta maimaita karanta sakon ya fisau goma kafin ta tura wayar a cikin jaka ta koma ta kwanta, ba ta jima ba kuma bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita, wanda ba ta tashi farkawa ba sai sha daya. na safe. Tana mikewa bandaki ta nufa ta watsa ruwa ta fito, ta sake shiryawa cikin atamfarta ta sannan ta flto Sai dai da mamakinta ta samu Momy da Rabi’ u da Dr a falo suna hira, da alama sun dade suna hirar ; Ta durkusa ta gaishe su daya bayan daya, sannan taja gefe ta zauna tana fadar, “Da ma kun tashi Momy ba ki tayar dani ba?” ' ‘ Momy ta ce “A’a na barki ne ki hantse tashi ki karya maza ku wuce don ku daga can za ku wuce”. Saudat ta yi saurin dagowa ta kalli Dr. sai dai k0 inda ta ke bai kalla ba, hakan ya tilasta mata mikewa ta nufi dinning ta zauna ta karya, sannan ta dawo cikin falon Momy ta dauko mata jakar da Rabi’un ya ba ta, ta qara mata da ‘yan tarkacen tsaraba, sannan ta rako su. * , Saudat ji take tamkar kada ta tafi, sai dai ba ta ~ da yadda ta iya, haka ta shiga motar Dr. shi kuma Rabi’u ya shiga tasa motar sabuwa dal mai suna 206 suka rankaya suka tafi Momy na musu fatan alkhairi. ~ Sai dai lolkacin 'da suka iso gidan Saudat mamaki ya kashe' ta, ganin yadda ya canza ya dawo ginin bulo da bulo aka kawata shi tamkar gidan wani dan karamin ma’aikacin gwamnati, kanta bai ida daurewa ba sai da suka shiga cikin gidan wanda aka canzawa tsari duka falukan gidan aka hade su cikin guda, aka kaWata su da sabbin kayan alatu na rayuwa, duk kan Saudat ya kwance shi kansa Rabi’un bin gidan yake da kallo, ‘Yarbaba wadda ke zaune a““ gidan ita ta yi musu iso cikin falon tana ta faman rawar jiki, sannan ta nufl wata kofa don ta kira musu Malam Bala. Saudat ta cika da mamakin ganin ‘Yarbaban a gidan, lokacin da Malam Bala ya flto ya yi ido hudu da Rabi’u sai ga shi ya. xube ya fadi kuka yake wiwi kamar karamin yaro, yana roKon gafararsu kan Saudat bai ida kwancewa ba sai data ga ‘Yarbaba ta turo Inna Laure a keken tura guragu, Saudat ta rude . ta shiga tambayar abin da ya faru tunda ga Inna Lauren nan dai babu alamar rashin lafiya a jikinta, . amma daga Inna Lauren har ‘Yarbaba kuka ya hana su magana sai Malarn Bala ne ke fada musu. ‘ “Lalurar hawan jini ceta kayar da Inna Laure tun a lokacin da ya kulle ta a daki ranar da aka dauki Saudat zuwa gidanta yana zuwa ya bude 'daki ya ganta a sume hankali ya tashi aka kwashe ta aka tafi asibiti nan fa aka sanar mana jininta ya yi matukar hawa kuma qafafunta sun riqe don inba wani iko daga Allah ba, ba za ta sake taka su ba. Mijinki yaxo Saudat a lokacin muna asibiti, shi ya yi ta dawainiya ya ba da kudi aka wuce da ita asibitin Aminu Kano da ke cikin jihar Kano ya ba da .makudan kudade, kuma shi ya yi mana wannan gyaran, amma a asibitin can ma sun ce iya bincikensu ba su ga abin da ya rike Kafafuwanta ba, don haka suka sallame mu, k0 kwana hudu ba mu yi ba da dawowa gida sai ga ‘Yarbaba cikin wani mummunan ‘ hali, wai mijinta ya kwashe kayan dakinta ya siyar, ta yi magana shine ya yi mata dukan tsiya duk ya raunatata, ya yi mata tsirara ya turota waje ya ce ya sake ta Saki uku, sai dai makota ne suka ara mata tufafin da ta iso gida dashi. Yau satinta guda da dawowa shi yasa ku ka ganta ta yi kyan gani, amma kwanakin baya idan ku ka ganta sai kun zubar mata » da hawaye, ni nasan haqqinku Saudat ba' zai barmu ba matukar ba ku yafe mana ba, don Allah Rabi’u ka yafe mana ba don mu ba ba don halinmu ba”. ‘ Rabi’u ya ce“Ai ni ban' rike ku da komai ba baba, wallahi na yafe har cikin zuciyata”. Inna Laure ba ta da ta cewa, sai kuka sai ma ‘Yarbaba ce ta yi Karfin halin bude baki ta nemi gafararsu. Sun dade a gidan kafinsu yi musu sallama. za su tafi, Dr. ya yi musu kyautar makudan kudade, haka shi ma Rabi’u naira dubu hamsin ya bawa mahaifinsa da zummar idan ya dawo zai’ ga abin da ya kamata ya yi musu, Saudat kuwa dumtsowa kawai ta yi ba tare da ta san k0 nawa ba ne ta bawa mahaifin nata, ta ba wa Inna Laure sannan ta miKa wa ‘Yarbaba ‘yan sauran da suka rage. Ai k0 sun sha godiya da sa albarka, haka suka bar gidan kowa zuciyarsa cike da alhini, da ma haka rayuwa ta Kunsa, idan kai ne yau gobe ba kai bane, idan ba ciwo akwai ajali idan ba ajali akwai tsufa haka rayuwa take tAfiya a kwana a tashi mai maida yaro tsoho. Dr ya dauki matarsa suka koma gidansu suka Ci gaba da rayuwarsu cikin nagartacciyar soyayya da kaunar juna, Saudat tana bawa mijinta irin kulawar data kamata dukda karatunda takezuwa baihanata ba shi duk wata kulawar da ta san zai iya bukata dagagare ta ba. A yanzu karatunta ya yi zurti, don kuwa har ta kammala Basic Illetrate ta karbi certificate ta kuma ci gaba da karatunta na wata tara Wanda za ta karanci Social welfare, don haka ta dage “*dakaratun ta donma canjin jikindata'samu narashin kwarin jiki wanda likita ya tabbatar da ta samu shigar cikin wata uku, wannan albishir din ba qaramin faranta zuciyar Dr. yayi ba, an inda labarin cikin Saudat har a cikin ‘yan uwansa, ‘ saboda tsabar rawar qafarsa a kan haihuwa. Cikin Saudat yana da wata takwas ta kammala karatunta na wata tara a lokacin an soma siyar da form din jarabawar waec external da kuma jamb din ta cike abinta ba su zana jarabawar ba Saudat ta haihu' wata tara daidai ta sunkuto qaton danta mai kama da ubansa sak tamkar ya yi kaki ya tofar ' ‘ Ai k0 a wannan lokacin Saudat ta ga gata da soyayya don Dr, da iyayensa sun saki bakin aljihuna sun mata bajinta, kuma sun gwada mata ita din ta zama tasu ta zama wani Bangare na jikinsu wanda bai kankaruwa Ranar suna tazo yaro yaci sunan mahaifin Dr. wato Mukhtar, suna kiransa da Khalifa. A ranar Saudat ta ga dandazon jama’a ta ko’ina‘ daga danginta zuwa dangin mijinta, hatta Hamid ya kawo matarsa shi ma Rabi’u ya kawo Shukura wanda Saudat ta fahimci soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu, duk da Rabi’u ba wani girman Shukura ya yi ba bai wuce ya bata shekara hudu ba, sai dai Shukura ta ba ta Kwakkwarar amsa cewa yanzu auren met ake yayi, abin da ya sa Saudat dariya matuka, ta kuma tsuke, bakinta daga nan tunda ta lura abin yi za,ayi. . Bayan sati biyu da haihuwar Saudat ta tafi ta zana jarabawa cikin ikon Allah kuma kwalliya ta biya kudin sabulu don kuwa ta samu credit biyar a ciki har da Maths da English a jamb dinta kuwa Allah ya taimake ta ta buga point dari da cas'in da kyar aka sha dai ke nan, don haka Dr bai bata lokaci ba ya samar mata gurbin karatu “ jami’ar Gwagwalada za ta yi difloma dinta a kan social management, karatunta ta ke haikan Khalifa ya girma sosai, don kuwa ba inda bai zuwa da qafafunsa, don haka yana da shekara daya da wata shidda ta yaye shi, Wanda da kyar mahaifinsa ya amince. ' Hajiya Zakiya tana zaune a falonta tana karatun mujalla ta ga Asma ta sauko daga saman ‘ bane tana sanye da baqar jallabiya fuskar nan ta yi kozai-kozai alamar ta sha kuka harta gaji, hannun na" riqe da hand bag sai makullin meta, k0 inda Hajiyar tata ta ke ba ta kalla ba ta nufi hanyar ficewa daga falon Hajiya. Zakiya ta kwalla mata kira, “Ke Gidan wa za ki haka kamar korarriya?” . Asma ta waigo tana kallon mahaifiyarta da idanun da suka ciko da' hawaye, cikin muryar kuka ta soma fadar, “Gidan mijina zan koma Umma, na gaji da zaman da nake a gidan nan marar ma’ana, ni ba mai aure ba, ni ba bazawara ba, tunda Ahmad yayi alkawarin ba zai sake niba Umma tursasawar da ake masa ta isa haka, kuma kema ya isa ki gane mijina yana sona, Umma na gaji da zamA nan gidana zan koma in rungumi Kaddarar da Ubangiji ya dora min tun kafin inyi batan bagatattan”. Hajiya Zakiya ta zuba wa ‘yar tata ’idanu wadda ke ta faman sharar kwalla ta girgiza kai kafin‘ ta ce, “Ke yanzu don zubar da kai Asma mijinki yaqi zuwa bikonki shine zaki debi kafa ki koma da Kafarki wato ki nuna masa. bakida aji a kansa ke nan. ” Asma ta kada kai cikin kuka ta ce, “K0 daya Umma, zuwa biko ya wuce wanda iyayensa suka zo ki kaqi sauraransu, haba Umma ki tuna fa yau shekarata biyu a gidan nan amma kek0 kadan ba ki damu ba, Umma to ni na gaji gidana zan koma in rungumi mijina da abokiyar zamana tun kafin ta mallake min miji ita daya ya aiko min da farar takardar da ke kike buqata, tunda nazo gidan nan sau daya Ahmad ya taba zuwa bai kuma wara dawowa ba sai dai ya turo min kudi ta account dina, haba Umma yaushe kike tunanin zai so inda nake? Wallahi ni ba zan tsaya jira ba. . .” Ta juya a sukwane za ta bar falon. Hajiya Zakiya ta daga murya, “Asma tsaya ki Jl’. . ~ ‘ Asma tajata tsaya itakuma tacigabada fadar,“Kiyi haquri kidaina kukannan indai kina son mijinki na amince ki koma amma ki dan daga komawar taki k0 gyaran jiki ne in kaiki in kuma sake miki kayan bangarenki gabadaya yadda zuciyarki za ta sassauta, ni ba na son ganin kina damun kanki nima sai inji hankalina ya tashi”. ‘ Asma tagirgiza kai,“Wallahi Umma bazan iya tsayawaba saidai duk abinda zakimin ki iskeni da shi daga baya, amma gidana zan koma ni ma ko na haihu na ga gudan jinina don na gama shan kwayoyin planning har abada.. Batajira abinda Umman tata zatacebata fice a guje ta bar falon bata tsaya a ko’ina ba sai cikin mota ta tayi mata key taja ta bar harabar gidan. ‘ Saudat na tsaye a harabar gidanta tana manne da Khalifa a kafadarta duk da kuwa kibar da yaron ya mulka tamkar dan turawa ga shi jajawur da shi kamar « ya hada iri da zabaya. Rakiya cd sukayi wa Dr wanda zai tafi kaduna taron .bude wani sabon kamfaninsa. Saudat na ta zuba masa shagwabar ya tafi da su shi kuwa sai dariya yake mata yana zolayarta wai ba inda zaitafi daita saitayi kiba don Khalifama yafita nauyi, in ya yi wani zillon har kusa kayar da ita yake shi ya sa kullum yana hannun mai rainonsa. ~ Saudat ta ce Allah YallaBai gorinka ya fara isa ta hakanan, kodon kaganka kai yaddakazama wani dankareran katone? Allah ka kai kilo dubu ni Wallahi ma kana kwarata”. _ Dr. Ahmad ya kece dawata irin dariya jin Sharri irinna Saudat Ahaka kuma masu gadi sukabude get motar Asma ta danno cikin gidan dukkansu sukabi motar da kallo, Dr. ya gane ta don ga sunanta nan Baro-baro a saman lambar motar Asma ta faka motar: ta bude ta fito cikin matuqar sanyin jikinta ta nufo inda ~ suke. Kallo daya Saudat tayimata taganeta, k0 kadan 'zuciyarta babu alamar fargaba k0 firgici don kuwa a yanzu tana jinta daidai da kowace kalar mace duk matsayinta k0 iliminta, kuma a yanzu ba ta bakin cikin Asma tadawo su zauna dondama batun yanxu take wa Dr maganar dawo da Asma yana cewa zai dawo da ita,ba amma sai ta yi hankali. Asma na qaraso ta rusuna ta gaishe da Dr wanda mamaki ya kashe shi, wai yau shi ne Asma ke gaidawa, lallai ruwa ya daki babban zakara, ta juya kan ‘ Saudat ta mika mata hannu tana fadar, “Saudat bani dana inganshi”.saudat tamiqa matashi,ammayaro da iya shege yaqi zuwa sai ma ya sa kuka. Dr, yace shi yana fadar, “Kai Khalifa kuka za ka yi wa Antyn taka, ba ka kyauta ba”. Saudat ta juya tana fadar, “Ako ni nayi ciki Aunty Asma ki tafi da shi tunda Kuka zai miki Asma ta yi murmushi cike .da jin dadin karramawar Saudat a gare ta, ta ce“Ai k0 godiya nake Maman Khalifa, kyautar surbudeden 'da kamar Khalifa, aiko nayi da kanaji fa”. Murmushi ya yi tare da fadar “Kema inda vaki sa duniya a gabanki ba Asma da yanzu kin ajiye uku irinsu”. Asma ta langwaBar da kai kafin ta ce, “Ka yi haquri don Allah Ahmad, wallahi duk sharrin zuciya ne, insha Allahu hakan ba zai Kara faruwa ba, don Allah ka yafe min”. Dr. Ahmad ya kade kafada tare da cewa, “Allah yace na yafe miki Asma, ni dai har abada bazan taba sakinkiba don ina sonki, ba zan iya rabuwa da ké ba”. ‘ Zuciyar Asma ta cika da farin ciki ta dafa kafadarsa ta sumbaci Khalifa a kumatu tana fadar, “Na gode kwarai my dear". Al’amarin rayuwa ya sauya, Asma da Saudat sun samu fahintar juna, Asma ta cire duk wani girman kai ta taya Saudat tattalin maigidan nasu, a yanzu haka Saudat ta kammala diplomarta ta ci gaba da digiri cikin kwanciyar hankali, inda ta Kara haihuwar ‘yarta mace akasa mata sunan Asma. Tammat bi hamdu lillahi, Saikuma mun sake haduwa a wani sabon littafin Thanks all my friends Pls my fan's prayer for me Allah ya cikamin burinada kuma Allah ya cika muku burikanku na Alkairi Ameeeeeen *BISSALAM* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 26 of 26