Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
taso masa, shi da ya sani Allah ya jarabce shi da soyayyar Saudat, irin son da ba zai iya misaltuwa ba, wai yau Saudat dinsa ce ta zama haka? Rayuwa kenan. Ana kiran sallar azahar suka iso gida, don haka Alhaji Ashiru na sauke su ya wuce masallaci don ya bada farali, su kuma suka shige gidan, Momy ta wuce bangarenta su ma suka nufi nasu Bangaren don gabatar da sallah a cikin lokaci. Bayan sallar la’ asar kuma Shukura ta koma gida saboda gobe tana da lecture a school. Kwanansu uku da dawowa ya kama ranar alhamis, Saudat na kwance a falonta ita da Nabil da Nabila tana kallonsu suna home work da aka ba su daga makaranta, Momy ta shigo felon kafadarta na rataye da katuwar jaka, ‘sai rigar likitoci sagale a dayan hannun da alama dawowarta daga ofis ke nan. Duka yaran suka zabura suka nufe ta a guje suna fadar, “Oyoyo my Momy, welcome". Ita ma da fara‘a a kan fuskarta ta rungume yaran a jikinta tana shafar kawunnansu. Saudat ta yunkura ta mike ta nufi inda " ' Momy ta ke ta karbi jakar hannunta da Iafkwat dinta: ‘da mayafin jikinta ta nufi Sangarenta kai tsaye kicin ta nufa ta jero kulolin‘ .abinci a babban faranti tareda kwalin lemo', da ruwa masu sanyi ta nufo falon, inda ta samu’ . Momy har ta yi wa kanta masauki saman tallausan ' kafet din falon, yaran duk sun zagaye ta suna ta_ shirmensu. ‘ Saudat ta ajiye mata kayan abincin a gabanta, ta soma bude kulolin tana mata sannu da zuwa. Momy ta rike farantin tana fadar. “Barshi kawai Saudat, kije falon waje Hamid nanan ya zo zaku gaisa” . . Saudat ta washe baki tana fadar. ' ~ “Kai Momy, ashe bai mance dani ba, yau fa kwana uku . ke nan da dawowarmu daga -Dandagora, amma bai zoba shi da ya ce ‘a * washegari zai zo?” Momy ta ce “Ah to, ni kaina da na ganshi a yanzu sai da nayi mita, amma dai yace ba ya garine shi ya sa, dawowarsa kenan. Tashi ki je kar yaga an barshi shi kadai. _ ‘ Saudat ta yunkura ta mike ta nufi kan gadonta ta jawa farin mayafinta ta yafa, ta saka takalminta flat Shoe shi ma fari A tsaye ta same shi cikin falon ya nannade hannayensa a qirji ya zuba wa qaton hoton da ke jingine a bangon daki ido, na su Nabila da Nabil ne wanda .aka yi musu a harabar wurin shakatawa da ke cikin park dukkansu sun yi matukar kyau tamkar ‘ya’yan da ke rayuwa cikin dusar qankara. Saudat ta qaraso cikin falon da ‘yar siririyan sallamarta, bakinta na dauke da murmushi. Hamid ya yi saurin waigowa yana kallon mai shigowarr tare da amsa mata sallamar Saudat ta tsaya dan nesa da shi tana fadar, “Saudatu ya tabbata kan Yaya Hamid wanda ya manta da ita tsawon kwanaki uku babu shi babu alamarsa”. . Tunda Hamid ya waigo ya ganta ya kasa koda kyafta idanunsa balle ya janye su daga kanta, girman da Saudat ta Kara da cikar jikinta shi ya fi . komai daukar hankalinsa, da kuma shigar alfarmar da ke jikinta. Ba komai bane a jikinta, illa wani tsadadden code lace dark blue mai ratsin fad-fad a jiki, dinkin riga da siket, kalar leshin ta dace da yanayin farar fatarta, don haka dinkin ya yi matukar kwantawa a jikinta. Yafi mayafin da ta yi Ya zauna kafadarta ya dace da ita, ya fito da sigarta ta nutsattsiyar budurwa. : Hamid ya lumshe idanunsa ya bude guda yana fadar, “Allah ya huci zuciyar Saudat, wai kin ga yadda kika ka koma kuwa?’ ‘ ‘ ‘ Saudat ta yi murmushi har da sunkuyawa ta zauna tana fuskantar katon teburin da aka qawata da kayan ciye-ciye dana sanyaya makoshi. ~ ~ “ ' ‘ Hamid ya durqusa a gabanta yana kallonta da idanunsa dake fallasa asirin zuciyarsa, ya kira sunanta . “Saudat, wallahi ina sonki, irin son da ba zai . misaltu ba, daidai da daqika guda ban taBa ' mancewa da keba a rayuwata, kina nan makale a zuciyata wallahi ranar da kuka zo gidanmu a ranar na bar Katsina na tafi Abuja, isowa ta ke nan wallahi. Saudat zuciyata ta gaza hakuri sai da nazo ki yarda da ni don Allah kyakkyawata". Dariya ceta kwace wa Saudat saboda ganin yadda duk Hamid din ya bi ya rude kamar wani zautaccce, shi ma ‘yar dariyar ya yi yana sosa qeya alamar ya danji kunya shi ma. A daidai nan ne kuma Dr. Ahmad ya sawo kai cikin falon da‘ yar siririyar sallamarsa, waddai ta makale amakoshi. * ' Saudat ta dago kanta a dan razane ta dubi ' inda yake Wani razanannen kallo ya watsa mata ta cikin siririn farin gilashin da ke manne a fuskarsa, Lokaci guda ya dauke kansa tamkar allah bai ajiye ’ Awajen ba, haka ya gifta su ya shige falon cikin gidan. Saudat ta sauke wani gwauron numfashi tare da maida hankalinta inda Hamid yake Murmushi ya sakar mata tareda fadar, . “Wannan shi ne abokin takarar tawa kenan?” Saudat ta sunkuyar da idanunta qasa tana dan wasa da bakin gyalenta don har ga Allah Hamid yana da muhimmanci a rayuwarta, duk da ta sani sarai ba za ta iya hada soyayyar Dr. Ahmad da ta kowa a zuciyarta ba. Hamid ya yunkura ya mike hannayensa zube a cikin aljihunsa yana kallonta da fararen idanunsa. Saudat ta yi qasa da idanunta ta kasa hada ido da Hamid din sai kawau ta tsinci kanta da jin matukar nauyinsa. Hamid ya yi wani malalacin murmushi Wanda ya tsaya iya labbansa kawai, muryarsa na dan sarqewa ya ce “Tsananin son da nake miki Saudat, da dumbin qaunarki da ke zuciyata ba zai ingiza ni ga take gaskiya ba. Saudat na yi miki rantsuwa da Allah ke ce kadai macen da na tabaa so a rayuwata, kuma haryau bana tunanin da akwai kwatankwacinki. A ranar da kuka zo gidanmu kuka ganni a ranar aka daura aurena da Kausar ‘yar qanin mahaifina 'Amma nasa qafa na bar Katsina zuwa Abuja‘ ban“ sonta, banida muhallin da zan iya :ajiyeta a a zuciyata, tunda na. tafi sai jiya na dawo. A yanzu haka mahaifina ya yi fushi , , don haka mahaifiyata ta ba ni shawara na tafi Kaduna Wurin matata, wannan ne ‘ kadai abin dazai Shirya tsakanina da mahaifina. Yanxu’ haka tafiyar tawa ce zuwa Kadunan shine na kasa daurewa har sai na tsaya na ganki sannan na wuce. Saudat ba zan shiga haqqinki ba, idar har kin ji zaki iya aurena a yadda nake a ‘ yanxu na ba ki sati daya ki yi shawara duk abin da ‘ kika ”yanke zan dawo sai ki sanar dani”. “' Ba tareda ya tsaya sauraran abin da zata cebaa ya zaro ambulan daga cikin aljihunsa ya dora mata a hannu sannan , ya juya ya fice abinsa. Saudat ta mike jikinta a kasale ta ‘ nufi qofar shiga babban falon gidan. Ba ta ankara ba sai dai ta ji sun yi karo yana qokarin fitowa ita tana qokarin shiga, ta yi saurin ja da baya tare da dafe goshi, kallo daya yayi mata ya Juya ya dauke kai da sauri ya raBa ta zai wuce. . Saudat ta yi saurin rufa masa baya tana ' kiransa baida alamar tsaya ba balle harya .sauraré ta hakan ya sa ta Kara da gudu~gudu ta , sha .gabansa. 'Don Allah ka tsaya ka saurareni Ta yi magar tamkar zata rusheda kuka. Dr. Ahmad yasa ya tsaya a gabanta yas‘hannayensa a aljihu tare da kafa mata ido. Saude ta langwabar da kai ' “Don Allah kar ka horar dain da fushinka, wallahi ba zan iya jurewa ba” . . Dr Ahmad ya watsa mata harara kafin yace“Idan har ni ban horar da zuciyarki da fushina ba, ai ke kya tarwatsa tawa zuciyar da masifar kishinki kauce ki bani hanya in wuce : Ya qarasa maganar tare da sa hannu yana ture ta daga gabansa Saudat ta Kara tokare hanyar cikin muryar ' son fashewa da kuka ta ce “Haba don Allah yallaBai, Yaya Hamid ne fa ba wani ba”. Dr. Ahmad ya qara watsa mata. wani kallo, “Okey, Yaya Hamid ne shi da yake ba namiji baneba k0? K0 kuma shi din ba sonki yake ba ko? Da Allah matsa bani wuri malama na wuce”. Wani irin qululu ya tokare zuciyarta ganin yadda ta ke rarrashinsa yana qars botsarewa. ta juya da hanzarinta tana sharar kwalla ta shiga ciki. Dr Ahmad yabita da idanunsa dukda ‘ zafin da zuciyarsa keyi bai hana shi jin tausayinta ba, sai dai shi kansa bai san kalar zuciyar shiba da kishi yakan sa ya kasa sarrafa kansa ba yadda ya ' iya haka ya juya ya fice daga falon YAR. TALLAH CHAPTER30 Saudat'na Shiga falon taga Momy zaune hannunta rike da waya da alamar. magana ta gama tana shirin giftata. ta wuce, Momy ta rika , hannunta. saudat ta waigo da sauri tana kallonta, 'don haka ta dawo ta raBa ta zauna zuciyarta babu "dadi. , ~ Momy ta kira sunanta, “Saudat dan rigimar nan naki ba zai miki haqurin ki fara karatu ba, naga alamar rigimamme ne na gaske, don haka nayi tunanin a tsaida magana kawai in yaso ko a gidanki kya yi karatunki idan kina da rabo har gaba da sakandire sai ki wuce a gidanki don haka yanzu zabi yana wurin ki shin tsakanin Hamid da shi Ahmad din waye kike jin kina so a cikinsu” Saudat ta dago a sanyaye ta dubi Momy kafin ta ce, “Duk ina sonsu”. Momy tayi wata tatacciyar dariya ta ce, “To idan kina sonsu duka Saudat wa ki ke son aura A ciki kuma?” Saudat ta yi shiru zuciyarta naci gaba da ' harbawa, ta. sani sarai soyayyarta a yanzu tanaga ’ wurin Dr.“ Ahmad, to amma ta juya wa Hamid baya ‘ ' anya ta yi wa soyayyar da ya yi mata adalci? To shi kuma Dr din fa? ‘ ‘ “ Momy ta katse mata tunanin da cewa . “Ki yi tunani da kyau Saudat, duka mutanen biyu duk suna qaunarki amma ni a nawa gamin Ahmad shi ne wanda ya cancanta ki aura, amma ki yi tunani da zuciyarki". Saudat ta dago kai tana kallon Momy zuciyarta na faman harbawa ta ce “Momy na zabi Dr din in har ke ma ya yi miki Momy ta dora hannu saman kafadarta ta dafa ta tana fadar, “Hakan shi yafi cancanta Saudat, tashi kije Allah ya yi miki albarka". Saudat ta amsa da, “Amin”. Sannan ta mike cikin sanyin jiki ta nufi dakinta, ta fada kan gadonta a rufda ciki ta dafe kanta da hannaye biyu tamkar mai shirin kurma ihu, ta lumshe idanu tana jin zuciyarta na bugawa da qarfl, tamkar za ta ballo Kirjinta ta flto waje. Sai dai ta samu taimakon wata dunkulalliyar damuwa da ta tokare ta ta hana ta baro kirjin harta fito fili, tana so ta ji halin da Dr. Ahmad yake ciki, amma kuma tasan babu dama. Tana nan kwance har aka kira sallar magriba don haka ta miqe ta nufi bandaki ta dauro alwalla ta fito ta nufi kan sallayarta ta zura dogon hija‘binta ta tayar da sallah, tana gamawa ta kishingida a saman sallayar ta Iumshe idanunta tamkar mai jin bacci, amma babu komai a zuciyana sai dumbin damuwa. . Ta yi nisa a duniyar tunanin da ta lula ta ji an kwalla kiran sallar isha’I, a dole ta mike don ba ‘ da farali. ., saida ta gama sallar harta mike ba, zata Kara kudundunewa akan sallayar tamkar mai jin ‘ sanyi, inda rai da zuciya keta aikin rarrabe tsakanin Aya da tsakuwa anya dana dauki Dr. Ahmad ta bar Hamid ta'yi wa soyayya adalci? ‘ ‘ Ba ta ji shigowar Nabila ba, sai dai ta ji ta dafa ta tana fadar, “Aunty kizo inji Ya‘ya yana falo yana jiranki” ' Saudat ta yi saurin tashi zaune tare da rike hannun Nabilar tana fadar, “Wane falon Nabila?” ‘ “Falon Daddy da baki”. Ta ba ta amsa. » Saudat ta dan yi jim tamkar mai nazarin wani abu tamkar kuma wadda aka tsikara ta zabura ta mike ta shuri takalmanta ta fice ta nufi falon da yake ta sa kai ta shiga tare da ‘yar siririyar sallamarta, ba don Allah ya yi ta ita din mai ji bace sosai daba yadda za a yi ta iya jin amsa sallamar da ya yi a can qasan makoshi irin ta wanda damuwa ta galabaitar da shi. ‘ Jikin Saudat ya yi sanyi matuqa, ta zubawa fararen idanunsa ido, yana zaune saman kujera ya , tallabe kansa da hannaye biyu ya zuba wa kaifet ido. Jikinta a mace ta IallaBa ta zauna. saman kujerar da ke gefenta, ta kasa dauke idonta a kansa. sawon mintuna biyar falon tsit baka jin motsin komai a ciki sai iskar A. C zaman shirun ya fara damunta tana son kawar da shirun, amma kuma bata san k0 ta Wacce hanya zata biba, to k0 hakuri zata ba shi? Idan ma hakurin ne ta ya ya za ta ba shi? K0 Shukura za ta kira ta bashi kan wayar ta "lallasar mata shi.. ' Ba ta ankara ba sai dai ta ganshi a durkushe a gabanta, kirjinta ya yi wani mummunar bugawa saboda yadda yawa Kafafuwanta, ta yi saurin ja da baya cikin kujerar, hakan ya yi daidai da riqo hannuwanta duka biyun da ya yi, tare da kiran sunanta cikin wata irin kasalalliyar murya wadda ta tilasta mata dago kanta ta kalle shi, gabanta ya yi wani mummunar faduwa, fararen idanun nan nasa tamkar an watsa barkono, gabadaya ya birice, ya canza tamkar ba shi ba ne wannan tsayayyen daktan jarumi mai razanar da ita ba. Ta runtse idonta da karfi saboda wani irin abu da ta ji yana tsurga mata zuciya. Dr. Ahmad ya kira sunanta da wata irin dakusasshiyar murya, “Saudat ki bude idonki ki kalle ni don Allah, kar ki tsane ni wallahi ina sonki, irin son da duk duniya babu mai yi miki kwatankwacinsa. , Saudat ki taBa zuciyata za kiji ki saurari zuciyata zakiji, ki kalli zuciyata za ki game irin guguwar da ke binne a cikinta, Saudat ina sonki son da zan iya salwantar da rayuwata a kanki, .. wallahi Saudat ina cikin fargaba tunda na bar gidan ' Karkiji yaddah zuciyata kr cikin baqin ciki a dole na dauro alwala na zauna ina ta ambaton Allah Saudat na yi sa’ a bakin .cikin ya gushe, amma damuwar da nake ciki ba ta barni ba har a lokacin nan na kasa runtsawa, gani nake zuciyarki na wurin‘ Hamid; da alama kuma za ki iya barina ki “ koma gare shi a kowane lokaci, wannan tunanin ne ya tilasta min dawowa Saudat don in sanarda ke cewa, idan har kika kuskuren juyawa zuciyata baya, to tabbas’ a ranar zakiji mummunan labari ~cewa na rasu, don ba zan iya rayuwa ba matukar babu ke a tare danibs Shirun da Saudat ta ji ne ya tilasta. mata bude idanunta tare da kallon inda ta ke sa ran' yana zaune, amma da mamakinta tuni har ya kai bakin kofa, ba ta san lokacin da ta mike ba, tare da kiran sunansa. Ya waigo da sauri tare da daga mata hannu. Karki ce komai Saudat soyayya ta zarce duk yaddaki ke tunaninta, don soyayya gamon jini ‘ ce ba wai gamma gambiza ba, so haduwar zuciyane ba wai tilasta shi akeyi ba Kuma linzamin so ' hankaline ba wai son rai ba. Saudar kar ki tilasta wa kanki ki soni don kawai kina tunanin ya kamata ki so ni, ba zan kasance mai son raiba na tilasta miki aurena ba alhalin ba nine a zuciyarki ba. Tun ranar da na soma sonki na kasance bani da. wani buri da Daya wuce son nagana dauwar dafarinciki ‘ zuciyarki, na dandana miki zaqin rayuwar da ba ki taBa dandana ta. Va Kuma kp a yanzu haka abin yake Saudat, dolene na baki farin cikinki k0 da hakan yana nufin rugujewar tawa rayuwar dole zan ba ki shi, kuma na yi miki alkawarin sadaukar wa Hamid da soyayyata matukar shi ne farin cikin rayuwarki”, Saudat taji wani abu ya tsarga mata zuciya mai kama da tsinin mashi, hawayen da suka tarar mata a idanu tun dazu suka samu damar biyo kuncinta, kuka nena gaske ya kwace mata, Wanda ta rasa dalilin yinsa. Dr. Ahmad ya yi saurin nufo ta, jikinsa na. kyarma yana Kokarin riko ta, ta yi saurin ja da baya tare da fadar “Karka taBa ni don Allah na rokeka, idan‘ har son da nayi maka bai gamsarda dodon kunnenka ba don Allah ka fadamin kalaman da zan yi amfani da su don su gamsar da kai, ni dai in har na san abin da so yake nufi, to saboda kai 'ne in har dai abin da nakeji a zuciyata shine so, to YallaBai na soka, so kuma kai kadai irin wanda ba zai taBa Karewa ba har abada" Shi ‘kuma hamid din fa ya zaki yi da shi Saudat? Yana sonki kamaryadda nake sonki, babu wani dalili da zaisa ki amince da daya daga acikinmu don kawai kina ganin rashin kyaumtawar ki guje masa Saudat ni na fadada bakina na aminca miki ki zaba wa 'zuciyarki abin da take so, k0 da ‘ kuwa hakan yana nufin bani za ki zaBa ba, kuma hakan ba zai sa na karya alkawarin dana dauka ba, na daukaka darajarki da duk....... “Ya isa don Allah ya isa haka!” Saudat ta yi maganar muryarta a sanyaye cikin kuka ta ci gaba da fadar, “Don Allah ka kyale ni haka, idan na ce ban so Hamid ba YallaBai karya nake, sai dai ina so ka gane abu guda shine, irin son da nake wa Hamid ba shi nake maka ba, sonka a cikin zuciyata ya sha bamban da irin nasa, don kuwa ka san shi murmushi yafi dariya. _ Abu guda kawai na sani shine, ba zan iya rayuwa ba inba tare da kai ba, idan har ina da rabon samun farin ciki da ‘ jin dadi a rayuwata to kai ne farin cikina, kai ne jin dadin rayuwata”. Da sauri ya nufe ta tamkar ‘zai kamo ta, sai ka ce wani zautacce, muryarsa harsarkewa ta ke Wurin fadar, “Da gaske Saudat kin amince za kl “ zama tawa? Za ki kasance da ni yanzu da har abada? Saudat don Allah ki amince ki zama tawa ni . kadai, wallahi a yanzu kece farin cikina, ke kadai kika ragemin, kin amince min na turo da ‘ da sadakinki gobe, ki fada min Saudat, ke nake saurare”. Kai kawai ta iya daga masa ba tare da ta bar zuciyarta ta yi wani dogon tunani ba Farin cikinsa ba zai misaltu ba a lokacin ita kanta Saudat ta tabbatar da hakan saboda yadda ta ga ya dawo cikin nutsuwarsa lokaci guda ya koma kan kujera ya zauna tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. Ya jingina kansa akan makarin kujerar yana sauke numfashi cikin nutsuwa, idonsa na kan Saudat wadda ta kasa zama. Dr. Ahmad ya qakaro wani dan murmushi kafin ya ce, “Kin min tsaye akai kina kallona k0 so ki ke ki gano munina ne?” Saudat ta yi saurin janye idanunta a kunyace tare da‘ yar dariyarta Kasa~qasa. Dr. Ahmad ya dan. kishingida kadan a kan kujcrar yana fadar, “jeki samo min dan wani abu in ci kada yunwa ta san yadda ta yi dani A, dan sanyaye Saudat ta kalle shi, shi ma 'idanunsa a kanta suke adole ta juya ta nufl kofa don kwarjininsa ba zai barta ta furta abin da ke bakinta ba. Kai tsaye kicin ta nufa ta soma dawainiyar sama masa can abin da ta san zai iya ci, sai dai babu komai akicin din sai sauran farfesun dare wanda ya ji kayan yaji, don haka ta zubaruwa a kettle ta kawo garin citta da karunfari da ganyen ta zuba, sannan ta jona a wuta ‘ Tana nan tsaye harya tafasa sannan ta juye masa“ta dora saman tire ta dora kofi daya tare da cokalin shan tea, sannan ta dora kular farfesun tasa filet da madaidaicin spoon sannan ta bude tirij ta dauko cake manya guda biyu ta dora a gefe, sannan ta dauka ta shiga falon da yake da sallamarta har a lokacin yana nan a kishingidensa; . Saudat ta durkusa a gabansa ta zuba masa tare da tsiyaya’masa ruwan zafl a kofi ta sa masa lipton da coffe tare da madara da sukari kadan ta juya ta miqa masa ya sa hannu ya karBa, bakinsa dauke da murmushi ya ce “Na gode kwarai” Murmushi kawai ta yi ta mike ta koma kujerarda ke fuskantarsa ta zauna. Tana kallonsa sai da ya cinye komai ita kanta ta yi mamakin irin yunwar da ya kwaso, shi .kansa ya lura da irin kallon da ta ke masa. Ya mike tsaye da dan murmushinsa yana kallon agogon dake daure a hannunsa, ya ce “Ni zan wuce, idan har kallona da ki ke me cike da tuhuma ya wadatar da ke Murmushi kawai ta yi, ta mike tana tattara, kayan daya ci abincin, ya dan mirgina kai ‘ ”‘idan kin shiga gida ki sanar da Momy manya zasuzo gobe insha Allahu misalin qarfe hudu na yamma” Allah ya kai mu’ amsa a takaice tare da bin gefensa za ta wuce saboda kwarjininsa da takrjin ya cika mata falon. Shi kansa ya lura da hakan, cikin zolaya ya ce. “Ba sallama kuma Madam ko har na angwance tun yanzu ne?” Ba ta juyo ba ta yi gaba abinta saboda dariyar da ta ji yana mata, ta tabbatar zolayarta yake son yi, don haka ta yi cikin gida abinta. Washegari misalin karfe sha daya na ‘safe; Saudat na kwance a falonta saman kafet ta' yi matashi da filon kujera tana kallon wa'azin Shekh Ja’afar da aka sanyo na Sunna T.V mai taken‘ ‘Suffatus salatun nabiyi'. ' A Kasan zuciyarta kuma tunani ne barkatai, tun jiya data yi mafarkin Yaya Rabi‘u’ ta kasa nutsuwa, tunanin dan uwan nata ya addabi ' zuciyarta k0 karyawa ta kasa yi, burinta bai wuce na ta koma Dandagoro bA don ta karb saqon da Hamid ya sanar da ita Yaya Rabi’ u ya bada makotansu a ajiye mata, ta san gidan ba zai wuce gidan Inna mai danwake ba, don gidanta ne ke manne da nasu, kuma nan ne kadai gidan da suké ' shiga ita da Yaya Rabi u alokacin suna tare Bataji shigoWar Momy a falon ba, sai dai‘ ta ji ta dafa ta tana fadar, “Bacci ne k0 kuma dogon tunani?’ “” Saudat ta yunkum ta tashi zaune tana kallon , mahaifiyar tata wadda ke kokarin zama a kan kujera, ta ja remote ta rage sautin akwatin talabijin ‘ din tana fadar. ‘ “Yanzu Alhaji ke sanar da ni yau za su je wurin Babanki don nema wa Ahmad aurenki, ni dai cewa ma, na yi,,kawai a kyale shi aCi gaba da ,hidima a nan, Alhaji ya ce ba zai yiwu ba, dole a ba shi hakkinsa a matsayinsa na mahaifi. * Ya ki ke ganin za a bullo wa tsarin bikin, don rana kawai za akira ban da asabar din gobe ta sama za a daura auren, kin ga dole musan abin da za a shirya don kar IOkaci ya qure mana. Ki min lissafin duk abin duk abinda kike so, don zan tura a Dubai . za a hadp komai” ,. . ' Saudat ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsu. Momy ta kafa mata idanu muryarta a saayaye ta ce, “Saudat lafiyarki kuwa, me ke damunki?” ‘ A hankali ta d‘ago kanta ta kalli mahaifiyar ' Kata da idanunta, wadanda suka ciko da kwalla, ta , hadiye dunkulalliyar damuwar da ta ‘tokare mata . zuciya, kafin tace “Momy yanzu shi kenan Yaya Rabiu ya bace kenan har abada?” YAR. TALLAH CHAPTER31 Momy taja wani gWauron numfashi kafin tace “Inji wa ya fada miki Saudat? Ni naji a jikina Rabi,u yana raya, kuma yanzu haka na_ baza ‘ *cigiyar‘sa tun daga gidajen talabijin, radiyo, mujallu da kuma jaridu tare da ofisoshin jami,an : tsaro insha Allahu Saudat zai bayyan, ki kwantarda hankalinki kinji Saudat ta daga mata kai kafin ta ce, “Tun *’ ina Abuja Hamid ya sanar da ni Yaya Rabi’ uv ya ba da sako a makwabta a bani nasan gidan Inna mai danwake ne shine nakeson inje inkarbo Momy ta ce, “A‘a ba zan iya barinki ki je ba, sai dai inwa Alhaji magana ya sa k0 direba ne yaje ya karbo miki hakan ya yi miki?" ‘ Kai kawai Saudat ta iya daga mata alamar eh. ’ . ' Tace “Okay lissafo min abubuwan da ki ke *bukata, kodai kin bani wuqa da nama ne? . Saudat ta amsh da, “Eh Momy”. Dariya Momy ta yi kafin ta ce ‘Wannan fillancin naki ya yi” yawa Saudat, anya kuwa?” ‘ ‘ Dariya kawai Saudat ta yi mahaifiyar tata ta fita ta barta , Misalin karfe budu na yamma Shukura taxo , “ gidan da‘ yar qaramar jakar kayanta, dadi ya cika' Saudat don kwana biyun da tayi babu ita ba’ " 'qaramin kewarta tayiba Shukura ta sauke jakana a kan gado tana fadar “Amarya kin sha kamshi, wannan fara arfa duk ta murnar amarcin ne?” Saudat ta waro ido cikin dariya ta ce“Kai _ don Allah meye na zolaya kuma? ’ ‘ ' Shukura ta fadakan gadon tare da rungume ta tana fadar, “Ba wani nan zolaya, gaskiya na fada” ' Saudat ta tabe baki ta zauna a kan kujera tana fadar, “Ai da ma Hausawa sunce idan baka iya sharri ba ka koyi kage” ., Shukura ta ce, “Ba wani nan, haka nan ki ke nuna wa Momy kauyanci amma irinku sululu kasau kunfi kowa iya shege Saudat ta yi dariya tana fadar, “Yau kuma da mita ki kaxo gidan kenan?” Shukura ta ce “Ai dole in miki iya shege, don Momy ta kira ni wai na tattaro na taho mu zauna don ta lura kina bukatar huduba ta, ni kuwa Tasan ba wani nan k0 karya na fada?" Saudat ta mike tayi hanyar‘fita daga falon tana fadar, “Ni ban iya abin da kika iyaba”. 1 Shukura ta tuntsure da dariya don ta san ta Qular da ita. , Washegari da safe suna zaune a falo Shukura na karanta wa Saudat wani littafin Hausa mai suna KADANGARUN BARIKI, Momy ta turo Ta turo .Kofar ta shigo tare da fadar, “To sai ku tashi ku shirya yanzu maza direba ya kai ku gidan Maman ‘ Sumayya maida tsohuwa yarinya” . ' ' Shukura ta zabura tana fadar, “Wow Momy! Da gaske?” . ‘ Momy ta yi murmushi tare da Juyawa tana fadar, “A’a da wasa”. , ~ Shukura ta dafe Saudat tana fadar, “Kai . amma wallahi Momy tanaji dake Saudat, lallai zaki rudar da DR wai baki taba jin labarin Maman Sumayya a Abuja ba?" Saudat ta girgiza mata kai a hankali, don ita ‘ dai ba ta fahinci inda maganar tasu ta dosa ba. , Shukura ta ce, “Lallai, da mamaki don a * fadin Nigeria babu jihar da sunan matar nan bai , zaga ba, kaya ta ke siyarwa ‘yan gaskr, tun daga kan, gyaran gashi, gyaran fata, sabulluka zuwa mayukan gyaran

Chapter 21 of 26