Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
baki Dr. Ahmad ya rufe matashi da’wani zazzafan marin daya rudarda ita, ya nuna mata hanya. ‘get out stupid girl Bace' min da gani bagidajiya kawai.” Saude ta dafe kunci cike da kaduwa ta juya simisimi ta fice Tana fitowa daga falon tamkar wadda aka zungura ta fashe da kuka mai ban tausayi, ta kifa kanta akan kujera tana kukan ta babu mai lallashinta, ita kanta bata san tsawon lokacin da ta dauka ba sai dai ta jiyo motsin mutane alamar za a tito. Ta zabura ta boye: bayan kujera tana jin su sàida suka gama fita gaba daya, sannan ta fito cike da tsoro. Kai da _ ganinta kasan tana‘cikin tashin hankali dan bata san irin hukuncin da zai yanke mata ba yau, duk da bata ga laifinda‘tayi’masa ba, ammata lura ya dau zafi da * ita ta qara fashewa da kuka Ya Allah Ka fidda ni tausayin kanta ya kama ta. Ita dai batayi sa,ar zuwa duniya ba tunda tazo batasan masoyanta ba duk inda ta shiga da. [1/24, 10:13 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/25, 9:29 AM] A A Dboy: *YAR TALLA* *CHAPTER 17* masu Kin ta take haduwa, a duniya yayanta ne kawai ya taBa sonta, sai kuwa Hamid, mutum na farko da ya nuna mata qauna da soyayya ita kanta duk da ba ta san meye so ba, amma ta san tana san Hamid dan ta san wahalar da take sha gidan su ta linka ta nan gidan sau goma, amma kullum burinta ta samu ta bar " gidan ta koma gida k0 ta hadu da Hamid dibta kuIlum addu’arta kenan musamman idan ta zo kwanciya bacci. “Wayyo Allah ya Ubangiji gani gare Ka Jin alamun taflyar da ta yi, ya sa ta saurin dago kai. Dr. ne ya dawo daga rakiya, gaban Saude ya yi Wata mummunar faduwa ta yi saurin ja da baya tana ba shi hakuri, da kukanta dan gani take dukanta zaiyi Dr... ya ja ya tsaya cak yana kallonta ya ma rasa me zai mata ya huce haushinsa, ya lumshe idanuwansa lokaci guda ya bude ba tare da ya yi magana ba ya matsa da niyar isa inda take ashe bai sani ha ta ajiye tiren kayan abinci a gun « Sai dai ya ji ya yi karo da wani abu, ya fasa wata ‘yar siririyar qara ya durkusa, ya rike babban dan yatsansa, wanda tuni har ya soma zubar da jini abin ka da lallausar farar fatar da hutu ya jika, hankalin Saude ya yi masifaffan tashi, tayi kan shi tana _ fadar ~ ‘Wayyo Allah na shiga uku na lalace "ta rike kafar tana kuka, ‘Wallahi ba da gangan na ajiyeba Na rantse da Allah ” ya runtse.idanuwansa ba tare da yace da ita komie ba “ta rasa yanda za ta yi ta kalli kan kayan abincin ashe, da yar qaramar wuqar yanka cake da ita ya ‘yi karon harta yankeshi hankalinta ya qara masifar tashi yanda ta ga jini na zuba ba wai kadan ba; ta rude ta cire himar din » kanta tasa hakori ”ta"yaga shi ta yagi kadan ta daure masa dan yantsan Dr ya bude idanuwan shi da Kyar yana kallonta yanda tabi ta gigicc ta rude fada take, ‘Sannu Wallahi bada gangan na ajiyeba, ganin yanda ta fita hayyacinta yasa ya nemi fushinsa, ya rasa. Ya'sake lumshe idanuwansa sbaoda radadin da qafar kemasa yce ‘Dauko min wayata in kira likita. ” .Hankalin, Saude ya: qara "tashi da taji an ambaci likita, ashe abin mai girma 'ne. Ta. sake rushewa da :kuka ita ko yau ta san hukuncinta mai girmane taje ta dauko masa wayar ta rankwafa ta mika masa, ita ta zauna daga gefe tana 'kallonsa Hankalin ta ya kara tashi tsoronta daya kada ’ jininsa ya qare, don ta ji ance jinin mutum na Karewa mutuwa zai yi, ta sa hannu ta gage hawayenta cikin muryar kuka ta “ce“K0 in kawo ‘maka gishiri ka barbada tunda jinin yaqi tsayawa?” Dr. ya waro ido yana maimaita gishiri kuma? Saude ta qara marairaicewa “Don Allah in kawo maka kada jinin ka ya qare.” Yanda ta yi maganar a shagwabe shi ya narkar da zuciyarsa ya ji har cikin tsikar jikin shi. : Ta sake langwaBe kai “In kawo?”-. Bai san lokacin da ya daga mata kai ba, Saude ta zabura ta mike da gudu ta fice, Dr. ya raka ta da manyan idanuwansa masu saurin daukar hankalin‘ yan matan zamani ‘ Meke son faruwa da ni ne? Ya tambayi kansa. Tambayar da ba shi da mai amsa masa. Saude ta dawo da sallamarta, ta durkusa ta mika mesa gishirin, ya lusmhe idanuwansa ba tare da ya yi magana ba, ta ce, “In barbada maka?" ' Ya daga mata kai alamar eh, ta durkusa ta ‘ ‘warware danrin' sannan ta soma barbada masa gishirin, inda naman ya Bantale, bai san lokacin da ye saki qara ba ya rike hannunta saboda azaba. » ‘ Saude ta watsar da gishirin cikin’ ta rike qafar tana fadar, “Yi hakuri don Allah‘da zafi ko?” Ya girgiza mata kai alamar a’a, ita kanta ta san ya fada ne kawai. Ta rankwafa kanta ta shiga hura masa .da iskar bakinta , tana yi tana sharar kwalla yau Allah kadai ne zai crce ta a gidan. ' Wani irin‘ tausayin; yarinyar ne ta kama kowace Kofa ta 'jikin sa tausayinsa da ya gani Karara a idanuwanta ya narkar da zuciyarsa, ya ji tamkar yasa hannu . ya shafi gashin kanta wanda kana kallon shi kaga gashin Fulani‘: ta daure shi tamau kamar gammo a kanta, ya Kara laushe idanuwansa a hankali. ;*A haka har likitan yazo ya same su, ta yi saurin , share hawayenta tare da gaishe da likitan ya amsa cikeda kulawa sannan suka gaisa da Dr. ya zauna yana fadin garin yaya haka? Dr cikin sanyayyar muryar shi ya ce ‘Tsautsayi kawai likita yace to allah ya kiyaye gaba .” Ya fada yana kallon shi cikin kulawa ya Janyo yar akwatin‘sa ta duba marasa lafiya, ‘ saude ta miqe da hanzarinta, Dr ya, dubeta. . ‘ Yace ina zaki kuma Cikin sarkewar murya irin ta wanda ya gaji da kuka ta ce, “Zan fita ne ba zan iya kallo ba.” Ya zuba mata idanuwansa yanda take maganar yaf8 komai daukar hankalinsa, ganin bai ce komai ba yasa ta juya ta fice ita kanta ta soma tsarguwa da kallon da yake mata yau, wanda ta kasa hada shi da irin Wanda ya saba yi mata a da. Kai tsaye Saude ta wuce daya Bangaren, tana shiga falon ta yi karo da Dillaliya a rabe gefen kujera ita kadai sai ka ce munafuka. Saude ta karaso da azamarta cikin doki ta zauna tana fadar “A’ a Dillaliya kece yau a gidanmu, sannu da zuwa, ina wuni?" Dillaliya ta watsa mata wani kallo mai kama da harara, kafin ta ce“Ina ne gidan naku? Lallai samun wuri tusar asuba, ashe ke nan har gidan , ya zama naku, kai gaskiya ne, an zo birni an asha jar 'miya ai dole a mance mafari. To idan kin manta bari in tuna miki gidanku na Katsina, a Katsinar ma qarshen gari inda k0 wutar nefa ba ta wadaci unguwarku ba, gidanku na nan gidan qasa an masa faci da buhu yana nan yanda ki ka bar shi kuma za ki koma ki same shi munafuka an samu wuri an Bade sai juya mazaunai ake ke da matar gidan baku da bambanci, fata ta murje anyi * kilin To ki sani kin kusa komawa gida,'dan an sa ranar auren ki wata biyu yau saura wata guda, keda Garba Gurgu, yana nan yana jiran ki." Gaban Saude ya yi wata mummunar faduwa ta ji ‘ tamkar ta dora hannuwa aka ta rusa kururuwa, saboda tashin hankali da kaduwa. Ta kifa kanta da kujera ta saki wani irin kuka mai ban tausayi. Dillaliya ta’ tabe baki tana fadar, “Kuka kama yanzu’ ki ka fara ni kam ina amsar albashin ki zan wuce yanzun nan don tun safe nake nan a jibge kamar kayan wanki, ungo wannan nataccen saurayin ki Hamid ya ce a kawo miki.” Da sauri Saude ta dago kanta don ganin abin da take mike mata. Wata doguwar ambulan ce, ta sa hannu ta karBa jiki na rawa. Dillaliya‘ ta ce, “Har na shiga mota ya zo da kansa har tasha ya kawo mini, ya gama ni da Allah ,in kawo miki,‘ ke kin san in bacin ya biya ni kudi masu kauri ai ba zan kawo ba. Saude dai jujuya takardar kawai take, tana jin wata irin soyayyar Hamid na mata yawo a zuciya, jin bai manta da ita ba shi ya mantar da ita kukan da take. Ta mike cike da dokin san ganin abin da ke cikin *‘ambulan din, Dillaliya ta dube ta, ‘Gidan wa za ki ai ba mu gama ba, kiyi maza ki tattaro mini abin da kika tara ko‘kina nufin haka nan ki ka zauna ki ka saki baki da ciki kina ta kwasar dadi ke da ki ka iya cin dadi.” Cikin sanyin jiki Saude ta ce ‘Ki yi hakuri Dillaliya wallahi ban ajiye komai ba, tunda na zo babu abin da aka ba ni.” Dillaliya ta cce“Ke dalla tashi' can har sai an ba ki keba ki iya ‘yan tattare-tattare ba, duk dan wani abinda kikaga anyi sake dashiki tattaraki boyeba Saude ta ce “Subhanallahi! Haba Dillaliya sata fa kenan?” Dillaliya ta ce “Ke gafara can sakarya ai idan ba ki sata kin Boyeba bikinki yazo ke za a bari da abin kunya, idan ko kin sata kin bada an boye miki ai kin san abin da ki ka yi ” Wani inn takaici ya kama Saude wai a tura mutum sata yanzu idan‘ yar tace ta sanya ta? Cikin sanyin muryarta ta ce, “Bari in shiga Dillaliya ki gaida gida ki gaida su ‘Yar Baba da Inna Laure da Baba na gode Dillaliya ta hayayyako mata cike da masifa “Idan ubanki ya ba ni kudin motar ba saiki tilasta ni na gaishe su ba, munafuka, mutuniyar banza, ai duk kyan gawa dai cikin Kasa za a turbune ta sai mu ga qarshen jin dadi da kyau.". Saude dai ba ta kula ta ba ta fice abin ta, tan shiga bangaren ta, ta fada kan gadonta ta zauna zaman Dirshan ta balle ambulàn din ta zazzago abinda ke ciki Wasu kudi suka fado yan dari bibbiyu rafa guda tare da yar qaramar wayar saluka Saude ta shiga jujjuyawa cike da mamaki ta qara zazzagawa saiga wani zobe ya fado tare da wata yar takarda da aka cika da kyakkyawan rubutu ta zubama rubutun ido dukda batasan abinda aka rubuta dinba amman rubutun ya burgeta ta dauki zoben nabazurfa dan sirir tana jujjuyashi shima zoben ya birgeta ta zura zoben a dan yatsanta qarmi na hagu Zuciyarta ta kwadaitu dason sanin abinda ke rubuce a cikin takardar Ta linketa da kudin ta boye sannan ta dauki wayar tana lallatsawa dukda bata iya wayaba amman zuwanta gidannan ta iya kunnawa da kashewa da kuma amsa kira sbd akwai wayar tarho da akasa a dakin don kiran gaggawa Saude ta kunna wayar tana qara jujjuyata wayar na kunnuwa kira na shigowa dukda batasan lambar wayarba amman zuci yarta ya bata hamid ne don haka hannunta na kyarma ta daga kiran ta kara wayar a kunne tareda sallama Wani sanyin dadi ya bugi zuciyar hamid lokacin da siririyar muryarta ta daki kunnensa muryar da har ya fiddah rai da sake jinta a duniya cikin doki dajin dadi yake magana Amin wa,alai kumussalam ya habibati saudat nasan zuwa yanxu saqona yaxo gareki hakane? Murmushin dake fuskarta ya qara qawatuwa kafin tace hakane yaya hamid dillaliya ta kawomin dazu ashe baka mance daniba yaya hamid? Hamid yace wat? Haba sudat ai idan har zan iya mancewa dake to wlh zan iya mancewa da kaina saudat soyayyata gareki ta gaskia ce kuma ta ginu ne tun daga lokacin dana fara ganinki kuma inhar ba daina numfashi nayi ba sudat bazan taba barinki ba sainaga kin taka wani matsayi a rayuwa na miki wannan alqawarin Cikin farin ciki dajin dadi saude tace na gode yaya hamid Yayi wani murmushi wanda har saida ta jiyo sautinsa yace gaskia saudat dina ta fara girma haka bakinki ya bude ? Murmushi kawai tayi bata tankaba hamid yace saudat nasha wahala lokacin dana dawo na iske bakyanan wlh saida nayi tamkar zan haukace kamin in samu insan inda aka kaiki amman bansan ko waccce anguwa bace ba a cikin abuja saida na biyo ta hannun wannan matar yanxu ya kike ganin za,ayi don muna cikin matsala fa Saudat an fada miki ansa ranar aurenki? Saude tace eh an fada mini Toya kike gani abuja zanzo in sameki ko ko ya za,ai ? Cikin kidima saude tace ina? Ka rufamin asiri masu gidan bazasu bariba Saidai kawai ka bari inna samu dama kawai na gudo Hamid yace to yaushe ?donni nanda sati daya jirginmu zai tashi zuwa qasa mai tsarki aikin hajji birina kafin satin duk yaddah za,ai ayi kawai a daura mana aure don wlh saudat ina tsoron in rasaki Saude taja‘numfashi kafin ta ce, “Insha Allahu Yaya Hamid duk yanda zan yi kafin satin zan yi ba za ka rasa ni ba da yardar Allah.” ' Dadi Ya kama Hamid nan ya ci gaba da jan ta da hira, su kan Su ba su san sun ci lokaci ba sai da suka jiyo ana kiran sallar Magariba.” Hamid ya ce “Lah! Saudat kin ga kin shagaltar dani mun ci lokaci har haka, bari in je in yi sallah zan kira ki zuwa dare kin ji sweaty na?” Dariya kawai ta yi shi kuma ya kashe wayar, wani sanyin dadi ya cika masa zuciya. Ta murgina ta sake mirginawa cike da shaukin soyayya kusan sai nace ban taba ganinta cikin irin wannan farin cikin ba ‘ ’ “” Washe gari Saude na cikin shirin tafiya aikinta, ta ji karar wayarta, ta matsa inda ta Boye ta ta dauka ta kara a kunne tare da rairo sallama Hamid ya amsa tare da gaishe ta, ta amsa ba sai dai ta maido masa da gaisuwar ya amsa suka gaisa sosai, can ya nisa kafin ya ce“Kin san me wai ashe jiya yayanki yazo gidanku, ban sani ba sai daga baya na samu labari?” Cikin zakuwa Saude ta ce, ‘Kai don Allah Yaya hamid yanzu yana ina don Allah?” ~ Hamid ya ce“Nima abin da yasa na baro Kaduna ke nan cikin daren na zo Katsina, amma sai na samu wai matar gidanku ta sa mahaifinku ya yi masa korar kare, suka dinga watso masa kaya waje cikin daren ya bar Katsina, amma ya barma maqotanku saqo baki Saudat ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya ji take tamkar ta shake kanta saboda baqin ciki Hamid ya ce, “Ai kuma nifa ba wai na fada miki ba ne don ki tayar da hankalin ki ba, ki yi hakuri tunda ya dawo yanzu wata rana ma , zai sake dawowa, don wallahi tallahi na yarda da Kaunar da ke tsakanin ku na san in har yana da rayuwa ba zai mance da rayuwarki ba Saudat ki yi haquri don Allah kin ji?" Haka dai ya yi ta lallashinta sannan ya kashe wayarsa. Saudc ta qara fashewa da kuka mai cin zuciya dama she Yaya Rabi’u yana raye? Ashe ‘dama bai mance da niba? Shin kowace irin rayuwa yake yi a Lol labari dai nata tafiya cikin kwanciyar hankali kuma ta wani barin sai nake ganin kamar Dr Ahmad nason ya fada tarkon sofa idan ya fara son saude ya kuke ganin zata kaya tsakanin asmau da sauden hamid da saude da kuma garba gurgu da saude kai akwai rikici fa mu tara donjin ci gaban wannan qaya taccen labarin idan naga comment sosai zanci gaba anjima idan kuma kukaqi to sai gobe kenan naku har kullum Admin Dboy🤔 [1/25, 9:29 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/25, 10:39 AM] A A Dboy: *YAR TALLA* *CHAPTER 18* 1page is missing Gaban Ahmad ya yi wata mummunar faduwa cikin sanyin jiki yace, “Lafiya kuwa me ke damun kine? Tamkar ba zata tanka masa ba saboda yanda kukan yake. neman Kin tsayawa, sai da ya sake‘ maimaita mata tambayar, sannan ta samu ta tsaida , kukan cikin shakakkiyar muryar da ta gaji da kukan Tace “YallaBai me yasa rayuwa take zuwa da abubuwa marasa dadine irin haka? YallaBai me yasa rayuwata kullum ba na ganin haske sai duhu a cikinta? Me yasa rayuwa ta kullum take neman rugujewa ne saboda wahala?” YallaBai shin ..... ” Kuka ya ci Karfinta ta kifa kanta a kan cinyarta ta ci gaba da raira abin ta. Wani irin tausayin ta ya mamaye zuciyar Dr. Ahmad, ya durqusa gabanta a hankali har tana jiyo kamshin turaren da ke fatar shi. Muryarsa a sanyaye ya kira sunanta ‘Saudat Wanda ya sa ta dago kanta da sauri don bata taBa zaton ya san sunan ta ba, kuma yau ne karo na farko da ya taBa kiran sunan nata. Ya ci gaba da magana, ‘Saudat k0 me rayuwa ta ' bada hakuri aka a karba, ki karBa' duk abin da rayuwa ta zo miki da shi ki rungume shi, sai ki ga Ubangiji ya taimake ki a duk inda ki ke, yawan kuka ba zai kare ki da komai ba sai ma ya haifar miki da . wani ciwon. Kalle ni Saudat.” Ya fada da siririyar » murya, ta dago da jajayen idanuwanta tana kallon , shi, ya mika lallausan hannun shi yana goge mata hawayen: “Ki daina zubar da hawayen ki irin haka, alhalin ba ki tanadi mai share miki shi ba.” Saude ta’ yi saurin janye fuskarta cike da jin kunya da nauyi, ya dan razana tare da fadar “Oh am sorry Ya mike ya ciro hankicif daga cikin aljihunsa ya mika mata. Ta karba ta soma share hawayen ta gama ta miKa masa ya karBa ya mayar aljihu, sannan ya ce “Tashi mu je ciki, kin ci abinci kuwa?” Shiru ta yi don rabonta da abinci tun jiya don haka ba musu ta mike, suka nufi falon kai tsaye Suna shiga ta nemi gefen kafet ta zauna bai tanka ‘ba Ya wuce kai tsaye wurin firij din da ake aje kayan gwan'gwani ya bude ya ciro wani qaton cake tare da ~ lemo guda da fresh milk ta kwali, sai chips a wani Qaramin plate wanda ya ji dafaffen kwai da madara ' ga shi ya dauki sanyi. Ya nufo inda Saude take zaune ya ajiye mata a gabanta, sannan ya ja gefe ya zauna saman kafet din yana' fuskantarta, da hannu ya yi mata nuni da ta ci, ba musu ta sa hannu ta dauki milk din ta fasa, ta bade cake din ta rinqa hadawa tana ci. Cake din * ya yi mata wani masifar dadi don sai ta ce tunda take “ ba ta taba cin abu mai dadinsa ba ita kanta ta yi mamakin wanda ta cinye, don chips din kasa cin shi ta yi don ba ta saba cin irin shi ba. Ta daga madarar ta shanye tas, don sai da ta ji babu wuri a cikinta, duk abin da take yana zaune yana kallonta tana gamawa ta mike da niyar tattara kayan, ya daga mata hannu. “Bar shi kawai za a tattara.” Kallon shi kawai ta yi sai dai ta gaza magana. Don haka shi ya katse shirun ta hanyar fadar, “Kije kawai ki huta', kin'ga kin sha kuka kada kan ki ya yi ciwo, kin ji?’ ' Saude ta amsa da to a hankali, sannan ta juya zata tafi hartakai bakinkofa tajiyakira sunanta ta' waigo tana kallonsa. Tamkar wanda aka matse bakinsa aka ce dole sai ya fadi abin da yake son fada ~ ya ce, “Please kar ki sake yin kukan nan don Allah.” Saude ta daga masa kai alamar to, ya ce, “Kin yi alkawari?’ Da kai kawai ta amsa masa, sannan ta . juya ta fice A yanzu mamaki yake ba ta ba ta taba tunanin yana da tausayi da jin Kai irin haka ba, ashe dama yana da kyawawan halaye irin haka ya Boye su, Allah Sarki, ko da yake ai rayuwarta abin tausayi ce ga duk wani mutum mai imani. _ ' . Ta zauna bakin gadonta ta janyo Wayarta miss ‘ call biyar ta gani, ta san kuma duk aikin Hamid ne, ‘ Allah Sarki soyayya. Ta ajiye wayar karkashin Kanta ta kwanta. Hirar ta da shi jiya cikin dare ta dawo mata tamkar yanzu ‘suka yin ta, ta yi wani ”murmushi tare da yin wani juyi . Da safe misalin Karfa takwas ta nufi Gangaren Dr Ahmad da mamakinta yau kwance ta same shi cikin falon Kasa, saman doguwar kujera da News paper a hannunsa yana dubawa, yana sanye da wando three quater wanda ya wuce gwiwarsa sai bakar singileti a jikinsa. Saude ta durkusa tare da ‘ ”gaishe shi.’ Ba tare da ya dago kansa daga karatun da yake ba ya amsa mata gaisuwar. Saude ta mike ta soma aikinta kamar yanda ta saba, sai da ta kammala tsaf sannan ta soma turare falon da turaren wuta, kamar wadda aka cewa dago kanki, karaf su kai ido hudu, ‘gaba daya idanuwansa da hankalinsaya tattara su a ‘kanta.~ ‘ ’Saude ta ji ta yi wata masifaffiyar tsarguwa, cikin basarwa irin ta gogaggun maza ya‘ yi mata alamar kira dakansa, jikin Saude ya Kara yin sanyi ita dai ta fara tsorata da irin kallon da yake mata, ba yanda ta iya haka ta ajiye bonar din ta nufl : ' inda yake ta dan durkusa kusa kadan tare da fadar, _ “Ga ni‘ Yalla Bai.”. Idonsa na' kanta kamar mai san karantar wani abu cikin idanuwanta ya ce“Ya kamata a tsaya da aikin nan haka a kawo mana abun karyawa k0 ke ba ki soma jin yunwa ba ne?” Yadda ya yi maganar cikin "salon nuna tausayinsa a kanta shi ya ba ta mamaki Saudat ta sunkuyar da kanta qasa‘ tana kallon yatsun hannunta, sannan ta amsa, da to muryarta a sanyaye, bai tanka. mata ba har ta mike ta fice daga falon, ya koma ya kwanta ya dora hannun shi guda a kan shi ya lumshe idanuwansa komai yake tunani? Oho. Saude ta karBo break din ta kawo da sallamarta ta ajiye masa. tiren kayan abincin a gabansa tare da fadar, ‘Ga abincin. ” Dr. Ahmad ya yunkura ya tashi zaune ya sauko daga kan kujerar ya zauna a gabanta tare da harde qafafuwa tamkar wani karamin yaro ya ce, “Zubo mana. ’ Saude ta yi saurin kallonsa tana san tambayarsa shi da wa amma kwarjinsa ya hana, don haka ta sunkuyar da kanta. Ta dauko ' plate biyu za ta zuba Dr. ya sa hannu ya janye dayan yana fadar, ‘Plate guda za ki zuba mana.” Ba ta musa ba ta dauki saving spoon ta , debo soyayyar agada (Plaintain) tare da alalar nama da kwai sai soyayyar da nama cikin dankali ta zuba su kowane gefe da gefe a tsakiyat plate dim sai ta zuba wata hadaddiyar miya kadan sannan ta tura plate din a gabansa ta rufe kulolin, sannan ta dauki kofi guda biyu ta zuba kunun madara da gero tasa ‘cokula ta miqa masa. Dr. Ahmad ya zuba mata manyan idanuWansa da dan murmushi a fuskarsa ya ce, “Sannu.’ Ba ta amsa ba saboda yanda ta ji nauyin yanda ya mata sannun, kamar ba yallaBan da ta sani ba. . Da kan shi ya matso da plate din a gabanta shi ma ya matso tare da miqa mata kofl guda na kunun Gaban Saude ya yi wata mummunar faduwa ta yi saurin matsawa tana girgiza masa kai alamar a’a. Dr. ya hade fuska tare da fadar. “Karbi mana meye haka?” Yanda ya yi maganar cikin tsawa ya sa ta saurin mika hannu ta karBa. Ya ce “To sa hannu mu ci maza.’ Ta yi saurin kallonsa idonta 'ya ciko da kwalla ta gaza yin magana, Dr. Ahmad ya girgiza kai cikin damuwa ya ce “Abincin ne ba zaki ci ba shi ne za ki yi kuka?” Ta yi saurin girgiza masa kai,alamar a’ a Ya kada kai cike da damuwa ya mike ya koma kan kujera ya kwanta ya lumshe idanuwansa ba tare daya yi magana ba. ~ Wani irin abu yayi wa Saude tSaye a zuciya, shin wai ita me ya maida ta ne? Yanzu abincin ma da zai ci sai ya wahalar da rayuwarta a kansa, abin da yake mata ya soma ba ta tsoro. Ji take tamkar ta mike ta bar masa falon, in ya ci ma k0 bai ci ba ruwansa. Bude idanuwansa da' ya yi shi ya katse mata tunanin take cikin sanyayyar muryarsa ya ce “Na takura ki k0? Ki yi hakuri kina iya tafiya kawai. ’ ‘ Gaban Saude ya yi wata irin masifar .faduwa cikin muryar kuka ta ce“Ka yi haquri dan Allah ’ Ya dauke kansa kafinn ya ce “Aini banyi fushi ba.” ‘ . . Damuwar da ta gani qarara a fuskarsa ne ta Narkar da zuciyarta, ita kanta tana mamakin kannta -. yanda hankalinta ke tashi idan suna tare bata san lokacin da bakinta ya bude ba sai dai ta ji tana ‘ fadar “Ka yi hakuri yanzu ai zan ci.” A hankali ya dago yana kallonta, ta ta" sunkuyar da idanuwanta kasa, wani takaitaccen murmushi ya yi tare da saukowa daga kan kujerar ya: zauna gefenta. Da kan shi ya dauko kofi din kunun ya mika mata, ta sa hannu ta karBa cike da jin nauyi ta soma sha, dadin kunun ya ratsa mata kwanya ashe haka yake da dandano a baki, tun tanajin nauyi har ta dake ta ci sosai tana cire hannunta yana cire nasa.‘ a Ta dan zuba masa idanuwanta, ya daga mata gira, alamar ya aka yi? Shiru tayi “ta kwashe kayan ta dawo ta gyara wurin da sukaci abincin sannan ta qarasa inda yake zaune yanacikin karant jaridarsa, ta dan durkusa. _ “Zan tafi Yallabai ko akwai wani abin da~ ka ke so?” ' Dr. Ahmad ya dago da kansa ya kalle ta a nutse~ kafin ya ce, “Me yasa za.ki tafi nan ba falo ba ne? Me yasa ki ka kasa sakin jiki?” Saude ta yi shiru ba tare da ta iya cewa komai ba Dr. ya girgiza kai tare da fadar samu guri ki zauna ina san mu yi magana.’ Ba musu ta samu gefen kujerar da yake zaune ta

Chapter 10 of 26